Ya kai dan uwana yanzu mecece shawararka, me kake ganin ya kamata.
Saadda aljani huraisul Marwas yaji wannan tambaya sai ya murtuke fuska ya dubi uzaifat cikin fushi yace, wai shin ku mutane me yasa kuke da matukar mantuwane?
Shin ka manta da dokokin da na kafa maka ne guda uku kafin mu fara wannan tafiya?
To ka saurara da kyau yanzu zan tunasar da kai amma ka sani cewa daga wannan karon ba zan sake tunasar dakai ba.
Doka ta farko itace, babu taimakekeniya a tskaaninmu sai dai kowa tasa ta fissheshi.
Saboda haka ban ga dalilin da zaisa ka nemi shawara ta ba bisa wannan abu da ya zame maka duhu.
Doka ta biyu itace, duk abinda na ga zakayi ko ka ga zanyi bazamu hana juna ba kuma bazamu umarci juna da yin abu ba.
Doka ta uku itace ta karshe shine, in dai muka yi gaba tofa babu komawa da baya.
Saadda huraisul Marwas yazo nan a zancensa sai uzaifat ya jinjina kai yace, to shikenan muje zuwa mahaukaci ya hau kura, Insha Allahu ni ba zan sake yi maka magana ba har sai mun kammala abinda ya kawo mu garin nan.
Kod gama fadin haka sai uzaifat ya wuce gaba yana mai durfafar kofar birnin shumbul ba tare da fargabar komai ba. Shima huraisul Marwas ya bishi a baya da sauri.
Har suka sa kafafunsu a cikin birnin basu ga komai ba kima basu ga kowa ba kuma gaba daya gidajen gari a kulle suke kofofinsu da tagoginsu tamkar babu sauran mutum daya ragagge a garin.
Abinda ya fi daurewa su uzaifat kai shine, ko irin kananan dabbobin gida ma basu ga guda daya ba.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ga garin gaba daya ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a ciki, kawai sai suka tsinci kansu a cikin wani kato kogin mai cike da kadoji suna ta gurnani sun yi musu kawanya.
Nan take uzaifat da huraisul Marwas suka gane cewa rufa ido akayi musu kwata kwata basu iso cikim ainahin birnin shumbul ba lallai sun iso wank kogine wanda tazararsa sa birnin shumbul ya Kai tafiyar sa'a uku.
Nan fa wadannan kadoji suka fara matso wa garesu.
Aljani huraisul Marwas yunkura da nufin ya bude fuka fukansa yayi sama ya bar cikin kogin sai yaji ya kasa tamkar ma fuka dukan ba a jikinsa suke ba, kwata kwata ya kasa sarrafasu, don haka sai ya dunkule hannayensa biyu ya fara waige waige yana kallon gabansa dabayansa da gefensa hagu da dama don ya ga ta inda za'a kawo masa hari.
Shikuwa uzaifat sai ya zare takobinsa shima ya kama kallon gabansa da bayansa da kowanne gefe don ya tari duk kadan da zai kawo masa hari.
Babbar matsalar itace, a cikin ruwa suke kuma ruwan ya shanyesu iya wuya ta yaya zasu iya yaki da kadojin a haka?
Lokacin da kafojin suka cimmusu sai uzaifat da huraisul Marwas suka yi nutso izuwa can karkashin ruwan suka taresu aka fara bakin gumurzu. Uzaifat ya dinga kaiwa kadojin sara da suka yaji kamar karfe yake sara, su kuwa suka rinka bude baki suna kokarin cniyeshi yana zillewa cikin zafin nama.
Shi kuwa Huraisul Marwas sai ya rinka naushin su da bugunsu da kafa da nufin ya kakkaryasu, amma shima sai yaji kamar duwatsu ya ke nausa.
Alamarin da ya dugunzuma hankalinsu ke nan duk su biyun musamman ma shi uzaifat da baya iya dacewa a karkashin kogin dole ya rinka fadowa saman ruwa domin ya samu damar shekar numfashi.
In badon uzaifat da huraisul Marwas sun kasance jarumai ba da tuno kadojin sun hallakasu a cikin dakiku kadan saboda wani lokacin ma sai kaga kadoji sun sa jelarsu suna dukansu.
Mu Hadu a DAKARUN MUSULUNCI na hudu PART C Don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar Hikayar...
Najibullah Muhammad & Umar Farooq Zango ke maku fatan Alkhairi 🙏🙏🙏✍️✍️**DAKARUN MUSULUNCI**
Littafi Na Hudu 4 ♥️
Part C ✍️♥️
Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini🧔
Typing:- Umar Farouq Zango🏃✍️
Posting: Najibullah Muhammad 🥷🥷
Marubucin yaci gaba da cewa...
Nan da nan kadojin suka fara farfasa jikin su uzaifat sai ga jini na zuba cikin kankanin lokaci kadojin suka samu lagon su uzaifat suna kokarin hallakasu.
A dai dai wannan lokaci ne uzaifat ya tuna cewa ko kadan fa bai nemi taimakon ubangiji ba, tun da ya fara wannan gumurzu da wadannan kadoji, don haka nan take ya fara da yin istigfari yana mai neman gafarar Allah, sannan yaci gaba da yiwa Allah kirare yana ambaton sunyensa tsarkaka gami da neman agajinsa cikin gaggawa. Aikuwa nan take yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi yayi fitar burgu daga cikin karkashin kogin ya taso sama yana mai cafo aljani Huraisul Marwas da hannu daya tamkar dan jariri ya dauko, kawai sai yaga Huraira Marwas a bayansa, ya kama gudu akan ruwan kogin tamkar akan kasa yake, har ma yana taka kadojin.
Shi kansa sai da ya cika da tsananin mamaki bisa ganin irin azababben gudun da yake yi tamkar walkiya. Nan da nan yaga har ya iso karshen kogin ya fita daga cikin sa sannan ya juyo ya tsaya cak ya ajiye aljani Huraisul Marwas a kasa ya dubi wadannan mugayen kadoji dake cikin kogin wadanda suka taho gaba dayansu izuwa karshen gabar kogin suka tsaitsaya suna kallonsa kawai, shima yana kallonsu irin kallon kar ta san kar.
Shi kuwa aljani Huraisul Marwas sai yaji ya kamu da tsananin kunya tunda gashi ya kasa tsinana komai kuna in ba don uzaifat ya ceci rayuwarsa ba da tini ya hallaka.
Cikin alamun kunya ya sunkui da kansa kas ba tare da ya dubi uzaifat ba yace, ya kai uzaifat kayi sani cewa daga nan tafiyata da kai ta kare, sai dai ni na dakata kai kuma ka co gaba ka wuce izuwa cikin birnin shumbul.
Saadda huraisul Marwas yazo nan a zancensa sai uzaifat ya dubeshi cikin tsananin mamaki yace, ya kai dan uwana ina dalilinka na cewa ba zaka ci gaba da tafiya tare da ni ba?
Ka sani cewa ko ba komai kana debe mini kewa ta kadaici kuma ina samun Karin karfin gwiwa idan muna tare.
Koda jin haka sai aljani Huraisul Marwas ya dago kai ya dubi uzaifat cikin wani irin yanayi kamar zai fashi da kuka yace, ai dole ne mu tabu anan domin ka karya dokoki guda biyu daga cikin guda ukun da na gindaya maka a cikin wannan tafiya tamu.
Na gargadeka da cewa kada ka taimakeni komai irin halinda na shiga amma sai gashi ka ceci rayuwata daga sharrin wadannan kadoji.
Abu na biyu ka hanani ci gaba da yaki dasu, alhalin na gargadeka da cewa duk abinda ka ga zan yi kada ka hanani ko kuma ka ce nayi.
Da wannan furuci nake yi maka bankwana sai wata rana idan da rabon mu sake saduwa.
Ina maka Fatan nasara bisa wannan gagarumin aiki da ke gabanka.
Koda gama fadin haka sai aljani Huraisul Marwas ya mike tsaye ya durfafi wata hanya daban sabanin wacce zata kaishi izuwa inda birnin shumbul yake ya bar uzaifat a tsaye yana mai binsa da kallo kawai cikin tsananin mamaki.
Uzaifat yace a ransa, to shi kuwa wannan aljani wane irin shi?
Saboda me zai yi fushi dani alhalin na ceci rayuwarsa?
Yanzu fa in ba don Allah ya nufeni da ceton sa ba da tuni ya hallaka, kuma ya mike yaci gabada tafiya abinsa ba tare da fargabar komai ba ga raunika da yawa a jikinsa.
Shin baya tsoron ya sake haduwa da wani mugun abun ne ya karasa hallaka shi tunda a galabaice yake? To wai shun ma mece ce hikimar sa ma ta kafa mini wadannan dokoki a cikin tafiyar mu?
Koda gama aiyana haka sai uzaifat ya ga Huraisul Marwas ya juyo sun hada idanu hawaye ya zubo ai idanunsa.
Alamarin da ya kara jefa uzaifat cikin tsananin mamaki ke nan ya tambayi kansa a cikin zuciyar sa yace, to yanzu kuma menene dalilin zubar wannan hawaye a idanun sa?
Kash bani da ikon sanin amsar wannan tambaya tunda gashi mun rabu kuma ga dukkan alamun ba zamu sake saduwa ba tunda mun raba hanya.
Ai kuwa inda da hali da na bishi da gudu na tambayeshi abubuwan da suka shige min duhu a tare da shi kuma dalilin da yasa ya tafi ya barni saboda na karya dokokin da ya gindaya mini.
Su kansu dokokin da ya gindaya mini ina son na san dalilinsu.
Kafin uzaifat ya gama furta wannan batu a cikin zuciyar sa sai ya nemi aljani Huraisul Marwas Sama da kasa ya rasa tamkar daukewar ruwan sama wato ya bace.
Alamarin da ya kara bashi mamaki ke nan amman da ya tuna cewa ai Huraisul Marwas ba mutum ba bane sai hankalinsa ya kwanta.
Ba tare da bata lokaci ba uzaifat ya kara sa karkashin wata bishiya ya zauna sannan ya tube rigar jikinsa wacce ta yayyage kuma tayi kaca kaca da jinisa sakamakon artabun da suka yi da kadojin a cikin kogi yayi jifa da ita sannan ya dauko garin magani ya shasshafa akan raunikan dake jikinsa sannan ya dauko battar ruwan shansa ya kwankwada.
Faruwar ke dawuya sai ya jingina bayansa a join bishiya ya fara gyangyadi, kafin anjima barci ya saceshi.
Jim kadan da faruwar hakan sai aljani Huraisul Marwas ya baiyana tsulum a gabansa kawai sai ya kura masa idanu yana mai zuba da hawaye ya sake bacewa.
Bacewar Huraisul Marwas ke da wuya sai kamannin uzaifat suka jirkice gana daya ya zama tsohuwar mace tukuf ya zamana cewa fatar jikinsa ma duk ta yakune. Takobinsa kuwa itama sai ta rikide ta zama sanda.
Sai da uzaifat ya shafe sa'a guda da rabi a cikin wannan hali yana shara bacci bai san abinda ya wakana ba sannan ya farka daga barcin.
Koda ya bude idanunsa yaga bai ga dokinsa ba a kusa da shi sai wata tsohuwar sanda sai ya cika da tsananin mamaki.
Abu na biyu da ya firgatashi ya dugunzuma hankalinsa shine, yaga jikinsa a lullube da wani Farin babban mayafi alhalin shi a saninsa babu komai a jikinsa face wando domin rigarsa ta yayyage tayi fata fata da jini da kansa ya cireta ya jefar da ita.
Kawai sai uzaifat yayi salati sannan ya yunkura da nufin ya mike tsaye sai yaji ya kasa domin kuwa ko kadan babu karfi a jikinsa.
Cikin figici ya shiga shafa fuskarsa da dukkan sauran jikinsa yaji ko ina a yakune yake. Nan fa uzaifat ya rude ya fada cikin kogin tunani mai zurfi.
A abinda ya fara fado masa a rai shine, anya kuwa kishingdar da yayi a jikin wannan bishiya ba barci ya daukeahi ba?
Wata kiladogon barci yayi na shekara da shekaru har ya tsufa a wajen bai sani ba domin ikon Allah yafi ga haka.
Gana aiyana hakan ke da wuya sai ya dubi bishiyar da ya kishinigida a jikinta ya ga ko kadan bata sauya komai ba yadda ya risketa kafin kishingidarsa haka take.
Nan fa ya tabbatar da cewa bai yi barcin shekaru ba. Uzaifat ya taba gashin kasan sai uzaifat yaji ai Sam ba nasa bane domin yawan sa ya rafi ainun kuma duk ya tsufa furfura ta yi masa yawa.
Uzaifat yayi shiru yana tunani da nazari daga can sai yace, kai koma menene ya sameni ai ubangiji yana sane da ni bai manta dani ba kwai bari na mike na ci gaba da da gabatar da abinda ke gabana.
Cikin karfin hali ya janyo wannan tsohuwar sanda dake kusa da shi ya dogara ta ya Mike tsaye ya ci gaba da tafiya irin ta tsofaffi yana dogara sandar da kyar har ya shafe sa'a guda da rabi.
Shi dai uzaifat tafiya yake kawai amma zuciyar sa cike take da was wasu da tunani iri iri. Abinda ta fara fado masa a rai shine wai shin anya kuwa nine da kaina kuwa?
A sanina akwai raunika a jikina wadanda na samesu sakamakon fafatawar da mukayi da kadoji a cikin kogi amma yanzu gashi babu ko daya a jikina.
Bai gushe ba yana wannan tunani sai kawai ya hangi birnin shumbul a gabansa ga dakarun yaki tsaitsaye sama da mutum dubu arbain a kofar garin rike da muggan makamin yaki, wasu a kasa wadansu kuma bisa dawakan.
Tun daga nesa da wadannan dakaru suka hango tsohuwar mace a tafe ta tunkaro su sai duk suka za'a makamansu.
Kusan mutum hamsin ne suka zaburi dawakansu suka rugo izuwa inda uzaifat yake suka yi masa kawanya.
Shi kuwa sai ya tsaya cak yana kallonsu daya bayan daya cikin alamun razana.
Wani daga cikin dakarun ya daka masa tsawa ya ce, yake wannan tsohuwa mutum ce ke ko aljana?
Yaya akayi kika fito da cikin daji ke kadai kika iso nan?
Idan amsarkj ta gamsar dani kin tsira, idan kuwa bamu gamsu ba yanzu nan zamu gididdibaki da makamanmu domin babu mamaki kina daga cikin abokan gabanmu, sihiri kikafi kika batar da kamanninki.
Saadda badakaren yazo nan a zancensa sai uzaifat ya dago kai ya dubeshi ba tare da fargabar komai ba sannan ya budi baki ya fara magana, kawai sai yaji gaba dayan mutyarsa ta sauya yanayi daga muryar maza izuwa ta mata kuma wata irin siriryar murya ce mai zaki da taushi.
Uzaifat yace ni mutum ce kamarku kuma na kasance a cikin ayari na fatale masu zuwa wannan birnin naku mai albarka don gabatar da ciniki wanda muka saba zuwa yi duk shekara amma wannan karon da muka shigo cikin yakin kasarku sai muka rinka haduwa da masifu iri iri wadanda da can bamu san da su ba.
A takaice dai gaba dayan abokan tafiyata sun hallaka kuma dukiyarmu gaba daya ta salwanta a cikin wani kogi wanda ni kadai ce na Ke tareshi.
Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun suka cika da mamaki domin a sanin su sarki shaaran ya tabbatar musu da cewa babu wani mahaluki da ya isa ya ketare wannan kogi na kadoji komai jarumtarsa da karfin sihirinsa.
To ya ya akayi wannan tsohuwar ta iya Ke tareshi alhalin babu alamar jarumta a tare da ita ta karfin sihiri.
Nan take shugaban dakarun ya fiddo wata isgar tsafi ya karata a jikin uzaifat sai ya ga isgar bata sauya launi ba. Kawai sai ya jinjina kai ya dubi uzaifat yace, yake wannan tsohuwa kiyi sani cewa tabbas yanzu na gamsu cewa ke ba matsfiya bace, to amma ta yaya kika iya haye kogin nan na kadoji ? Ki fada mana gaskiya ko kuna yanzu nan mu hallakaki.
Jikin uzaifat na karkarwa ya nufi baki a cikin murya irin ta mace yace, ni kaina ban san yadda akayi ba na ketare wannan kogi ba domin na suna a cikinsa saadda nayi arba da kadojin dake cikinsa, ni dai kawai na farfado ne na tsinci kaina a bakin gabar kogin su kuwa abokan tafiyata akan kogin kaga gawarwakin su kadojin na ci.
Koda jin wannan batu sai shugaban dakarun ya kyaljyale da dariyar mugunta sannan ya dubi sauran dakarun yace, tabbas wannan tsohuwa ba abokiyar gabanmu bace, kuma ba ta kasance daya daga cikin irin mutanen birnin Darul Husuf ba.
Maza ku dauketa ku kaita wajen wakilin sarki ku sanar dashi duk labarin da ta bamu yanzu.
Koda jin haka sai daya daga cikin dakarun tua dubi shugaban nasu cikin alamun firgici yace,
Haba ya shugabana shin ka manta ne cewa kafin sarki shaaran ya fita wannan yaki yace, mu tsare kofar garin ya zamana cewa ba shiga ba fita har sai ya dawo daga yaki?
Koda jin haka sai shugaban dakarun ya dubi mai maganar ya daka masa tsawa yace, shin kaine zaka koya mini aikinka ko kuwa nine zan koya maka?
Fadin hakan ke da wuya sai aka yi sauri aka dauki uzaifat aka dorashi akan dokin aka tafi dashi izuwa kofar birnin shumbul.
Da zuwan sa kofar birnin sai aka bude kofar suka shiga sannan aka maida kofar aka rufe.
Dakaru biyu ne ke tafe da uzaifat daya na rike da dokin da aka dora uzaifat akai, daya kuma na biye da su akan wani dokin daban.
Tun daga bakin kofar uzaifat yaga an tanadi dakarun yaki a jere , sahu sahu rike da makaman yaki don tabbatar da tsaro sannan aka tanadi wadansu manya manyan karnuka, kuraye, damisoshi da zauna barkatai wadanda aka sihircesu sai kai kawo sjme a cikin garin gaba daya suna shin shine shin shine, kai da gani ka san cewa ko yaya suka ji basu aminta da mutum ba nan take zasu yagalgashi.
Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI na hudu PART C Don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi 🥰🥰🥰**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA HUDU 4
Part D ✍️✍️♥️
MARUBUCI :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini
TYPING :- Umar Farouq Zango🤸
Posting: Najibullahi Muhammad 🥷🥷
Abinda ya daurewa uzaifa kai shine wadannan mugayen dabbobin suna ta zuwa suna shinshina dakarun dake yi masa rakiya amma shi ko daya bai rabeshi ba. Kawai sai Yau ajiyar zuciya gani da hamdala a cikin ransa domin ya san cewa kawai Allah ne ya tsare shi.
Haja dai aka ci gaba da tafiya da uzaifa har aka iso fadar sarki sha'aran wacce aka kawatata ainun tamkar ba a duniya take ba.
Su inda suka zo baayi musu shamaki sai dai a basu hanya su wuce har suka isa cikon ainahin fadar inda suka yi arba da wani garjejen mutum zaune akan karagar mulki, fadawa da sauran mutanen gari sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulki.
A gabansa an ajiye wani katon gasasshen rago sai yagar naman yake da hannu yana ci har ya kusa cinyeshi duka, a gefen hagunsa kuma wani dirkeken tulun giya ne, idan taci naman mai yawa sai ya daga tulun sama da hannunasa daya ya kwankwada sannan ya ajiye shi yaci gaba da cin naman.
Yayin da uzaifa ya karewa wannan mutum kallo sai ya ce a ransa hakika musulunci addinine mai tsafta.
Yanzu in banda kafirci da jahilci ya za'ayi ace wanda ke shugubantar mutane shine yake irin wannan cin abinci na rashin da'a a gaban jama'ar sa kuma yana mugun ci kamar jaki?
Saadda shirgegen mutukin ya hango an nufo gareshi da bakuwar mace tsohuwa sai Yai wurgi da tulun cinyar dake hannunsa ya fasa tulun giyar dake gabansa ya mike tsaye cikin fushi ya dubi dakarun biyu da suka zo da tsohuwar ya daka musu tsawa suka firgita ainun sukaji kamar hantar cikinsu zata fito waje.
Mutumin yace, saboda me kuka shigo da bakuwar mace cikin birnin nan? Shin kun manta ne da dokar da mai girma sha'aran kafin ya bar gari ya tafi yaki?
Kafin daya daga cikinsu ya budi baki yace wani abu sai uzaifa ya ga daya wani daga cikin dakarun da ke cikin fadar ya fito tsakiyar fadar ya dubi shirgegen mutumin yace, ya kai wakilin sarki kayi sani cewa ai wannan tsohuwar ba bakuwa bace ba a garin nan.
Tafi shekara arbain tana fatauci a tsakanin manyan kasashen dake wanann nahiya kuma asalinta ma haifaffiyar nan kasance sunanta ishal ibin sauraf.
Koda jin wannan batu sai wakilin sarki sha'aran Yai shiru yana mai kallon badakaren wanda ya kasance shima ya fara manyanta yace, ya kai humzalu ka sani cewa sarki sha'aran ya aminta da kai ainun don haka ka tabbatar da cewa wannan abu da kake shirinyi babu matsala a cikinsa? Ni kan ba zan baiwa wannan tsohuwar masauki ba anan fada sai dai kai ka sauke ta a gidanka kuma duk wani abu da ya biyo baya ba dai dai ba laifin na kanka, ga mutanen sune shaida. Shin ka yarda da haka?
Humzalu ya gyada kai yace, na amince da hakan.
Wakilin sarki sha'aran yace ai shikenan yanzu sai ka tafibda bakuwarka izuwa gida domin na fuskanci cewa a galabaice take kuma akwai yunwa da kishirwa a tare da ita.
Cikin murna tsoho humzalu ya dubi wakilin sarki yace, godiya nake ya Shugaba na.
Nan take humzalu ya kama dokin da uzaifa ke kai ya jashi suka fice daga cikin fadar a Lokacin da kowa ya bisu da kallo.
Bayan humzalu yai nisa ga barin fadar suna ta tafiya a cikin gari har ya zamana cewa sun kai can karshen gari inda babu gida gaba kuma dayansu bai ce uffan ba amma zuciyar uzaifa a cike take da wasi wasi gani da mamaki, sai yai gyaran murya da nufin yace wani abu.
Caraf sai tsoho humzalu ya tari numfashin sa ya ce, Haba dan uwa me kake ci na baka na zuba? Ka kara hakuri kadan saura kiris mu isa gida?
Koda jin wannan batu sai uzaifa yaji zuciyasa ta buga da karfi kuma ya cika da tsananin mamaki. Ba komai ne ya Hadda sa hakan ba face sauyin murya da yaji wadda tazo dai dai data aljani huraisul marwas.
Uzaifa yai shiru bai cekomai ba har suka iso wani dan karamin gida wanda shi kadai ne gidan da ya rage a wajen gaba daya.
Gidan a kewaye yake da katangar itatuwa kuma a gefe daya anyi wani dan karamin garken dawaki da dabbobi ana kiwo .
Da isarsu kofar gidan sai humzalu ya tsaida dokin uzaifa ya sauko sannan ya shigar da dokin cikin garken ya daureshi ya dawo wajen uzaifa ya kama hannunsa suka shiga cikin gidan.
Da shigar su uzaifa yai arba da wanin dattijo kwance a kas an daureshi tamau da igiya hannu da kafa.
Kofa ya dubi tsohon da kyau sai yaga kamarsa daya san da tsoho humzalu wanda suke tare tamkar an tsaga kara.
Cikin razana uzaifa ya dubi humzalu yace wane ne kai?
Maimakon humzalu yace. Wani abu sai kawai ya budi baki ya kira sunayen ubangijin musulunci tsarkaka.
Nan take kamanninsa suka juye izuwa na aljani huraisul marwas.
Saboda tsananin mamaki Uzaifa bai san saadda ya bushe da dariyar farin ciki ba. Shikuwa humzalu dake kwance a kas a daure sai ya dinga raba idanunsu akansu cikin matukar tsoro.
Aljani huraisul marwas ya dubi uzaifa yace barkanmu da sake saduwa ya kai dan uwa.
Idan Baka manta ba dama na gaya maka cewa baza ka iya shigo wa cikin birnin nan ba kai kadai domin ni nasan abinda kai baka sani ba.
Uzaifa ya gyada kai yace, tabbas na gamsu da haka, yanzu dai kafin kayi min bayanin komai ina son na nemi wata alfarma guda daya a wajenka. Ina dan tambaya a zuciyata wacce nake son nayi maka ita tun a wancan lokaci da muka hadu ina fatan zaka bani amsarta yanzu.
Dajin haka sai aljani huraisul marwas yayi murmushi yace fadi tambayarka naji da izinjn Allah zan baka amsarta.
Uzaifa yai gyaran murya yace tambaya ta farko a agareka itace, menene dalilin da yasa ka kafa mini dokoki guda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 21