Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dai wannan lokacine aljani huraisul marwas ya dawo cikin gidan. Koda ya shigo ya iske tsoho humzalu yana yin sallah tare da uzaifa sai ya cika da tsananin alajabi ya kasa koda motsa dan yatsansa kuwa, tamkar gunki aka ajiye a wajen. Bayan uzaifa da tsoho humzalu sun Isar da sallar sai uzaifa ya waigo baya yayi arba da huraisul marwas a zaune kikam ya wangame baki yana kallonsu kawai. Koda ganin haka sai uzaifa ya fahimci halin da huraisul marwas ke ciki sai ya girgizashi, kamar huraisul marwas ya farka daga bacci mai nauyi haka yayi firgigit ya risina agaban uzaifa yana mai cewa yaya akayi wannan mutumin ya karbi addininmua? Koda jin wanann tambaya sai uzaifa yayi murmushi yace ai dama komainna duniya rabone. Wani zai iya kasancewa kafiri a rayuwarsa amma a karshe idan bashi da rabo sai ya zama kafiri koda kuwa saura dakika daya ta rage masa a duniya. Tabbas humzalu yana daga cikin masu rabo a wannan lokaci. Ina mai farin cikin sanar da Kai cewa daga yanzu humzalu ya zama dan uwan mu kuna ya amince ya taimaka mana bisa bisa abinda ke gabanmu kuma a gobe zamu ci gaba da gabatar da wanann al'amari. Koda jin wannan al'amari sai aljani huraisul marwas ya cika da tsananin farin ciki ya mikawa humzalu hannu da nufin su gaisa. Humzalu ya none hannunsa sakamakon gainin girman hannun tamkar an shimfide katon dutse a kas kuma ya tuni da irin mummunar azabar da yayi masa a baya da hannun. Koda ganin abinda ya faru sai uzaifa yayi murmushi yace yakai humzalu ka Kwantar sa hankalinka kasani cewa har abada huraisul marwas ba zai sake cutar da kai ba domin kun zama yan uwan juna. Koda jin haka sai tsoho humzalu ya saki murmushi ya mikawa huraisul marwas hannu sa suka gaisa ba tare da fargabar komai ba. Kashe gari kuwa bayan sunyi sallah a cikin gidan humzalu su uku sai suka yi addua suka nemi taimakon Allah bisa gagrumin jihadi da zasu fita a sannan na tunkarar kurkukun kasar. Koda suka hattama adduar sai suka shiga kimtsa kansu da Samara suna zuba makamai iri iri a jikinsu. Bayan sun gama kimtsawa sai duk suka lullube jikinsu tsaf yadda babu mai ganin makaman dake jikinsu. Ba sannane humzalu ya dubi uzaifa da huraisul marwas yace, Tofa shi yaki dan zamba ne, dole sai da dabarun ake samun nasararsa. Yanzu daga nan kofar gidana izuwa can inda kurkukun yake tafiya ce ta a kalla sa'a hudu da rabi kuma idan bamu ya hikima ba zuwa can din zai iya gagararmu domin akan hanyar akwai dakaru tsubi tsubi masu bincike. Abinda zamuyi shine, tunda dai ni na kasance fitaccen badakaren sarki zamu sanyawa uzaifa sarka mu daureshi tamkar mun kamo mai laifi ne mu tura keyarsa gaba. Kai kuma huraisul marwas zaka yi bad da kama kayi shiga irin ta mugayen aljanu kamar kaine ka kamo uzaifa ka kawoshi gareni ya zamana cewa muna kokarin kaishi can kurkukun ne a ajiyeshi kafin sarki sha'aran ya dawo a yanke masa hukuncin. In dai muka yi haka tabbas zamu sami nasarar shiga har cikin kurkukun lafiya kalau a cikin salin alin. Koda jin wannan batu sai uzaifa da huraisul marwas suka cika da matukar murna domin sun ji a jikinsu cewa lallai wannan dabara zata yi aiki. Nan take tsoho humzalu yaje ya debo wadansu manyan sarkoki irin wadanda ake amfani dasu a kurkukun kasar ya durawa uzaifa a kafafunsa da hannayenasa sannan suka fita daga cikin turakar tasa suka nufi a cikin harabar a gidan inda bargar dawakai take. Da zuwa sai humzalu yazo dashi ya dubi huraisul marwas ya ce maza ka dora uzaifa akan wannan doki ni kuma sai na hau bayanka na zauna mu sashi a gaba har izuwa can kurkukun. Ba tare da gardamar komai ba huraisul marwas ya dora uzaifa akan dokin sannan ya rankwafa bayan, humzalu ya hau ya zauna wanann ya cafo akalar dokin da uzaifa ke kai ya zunguri cikin huraisul marwas yaci gaba da tafiya a kas bisa kafafunsa, mai makon ya bude fuka fukinsa yayi sama. Tunda suka fara wannan tafiya a cikin birnin shumbul suka zamo ababan kallo domin duk inda suka gifta sai su ga ana ta kallonsu. Hakika in bacin albarka cin an gansu tare da humzalu ba da tabbas za a iya rufesu da duka ayi musu rubdugu Lokacin da suka iso matsaya ta farko inda dandazon dakarun yaki ke tsaye a bakin wata kofa da za'a shiga wata unguwa sai zuciyar uzaifa da ta aljani huraisul marwas ta buga da karfi suka razana a cikin ransu sakamakon ganin kwarjinin dakarun da ke wajen. Su dai wadannan dakaru sun kasance mutane da aljanu manya manya masu kirar mutanen farko domin girmansu ya wuce misali. Shi kansa aljani huraisul marwas duk iyakar yawon da yayi a duniya bai taba ganin aljanu masu girma ba irin wadannan domin dan autan cikinsu ma zai iya kifeahi da hannunsa guda ya rufeshi yadda ba zai iya ganin sa ba. Shikuwa uzaifa shi da dokin da yake kai duka da suka iso gaban daya daga cikin dakarun biladaman sai suka zamo kamar an ajiye zomo a gaban kare. Cikin tsawa **DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA HUDU 4 part F ✋💯 MARUBUCI :- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI Typing :- UMAR FAROUQ ZANGO. Posting: Najibullah Muhammad 🥷🥷 Marubucin yaci gaba da cewa.. Haka dai su uzaifa suka ci gaba da tafiya ana bude musu kofofi suna shigewa har suka ratsa ta cikin kofofi bakwai. Saadda suka iso bakin kofar kurkukun ne labari ya sauya ya zamana cewa sun raina kansu domin sun cewa hujjar da suka zo da ita ba zata sa a barsu su shiga ba kuma irin dakarun da suka gani a kofar kurkukun wadannan zakwakuran dakaru gudu uku sun san cewa babu wargi bare su sami wata alfarma. Da isarsu bakin kofar kurkukun suka tsaya cak suka yi cirko cirko aka fara kallon kallo tsakanin su da dakarun. Duk da cewa aljani huraisul marwas ya kasance jarumin gaske mai dakakkiyar zuciya sai da yaji kyarma yaji kamar ya juya da baya ya hakura da wannan jihadi da ya fito. Har tsoho humzalu ya budi baki zai ce wani abu sai shugaban dakarun ya daka masa sawa yana mai tarar numfashin sa yace, kai tsoho humzalu kada ka zo mana da wata magana daban sabanin dokar da sarki yabar mana anan domin kuwa zamu yi maka wata alfarma ba. Ina mai sanar dakai cewa babu wani mahaluki da y isa ya shiga cikin wannan kurkuku ko kuma ya fito daga cikinsa muddin muna numfashi a doran kasa, face sarki yazo nanda kansa ya bada umarnin yin hakan. Na baku dakika ashirin kacal kai da jama'ar ka ku bace daga nan ko kuna ku zama tarihi a wannan duniya. Saadda tsoho humzalu yaji wannan batu sai ya juya ya dubi uzaifa da aljani huraisul marwas cikin alamun karayar zuciya yace, yanzu mene ne abin yi? Maimakon uzaifa yace da shi wani abu sai kawai ya yunkura ya kwalla kabbara da karfi ya tsittsinka sarkar dake jikinsa gaba daya sannan ya zare takobinsa ya zaburi dokinsa ya afkawa wadannan zakwakuran mayaka suma kuwa sai suka taso masa aka runguntsume da azababben yaki. Koda ganin haka sai shima aljani huraisul marwas ya kwalla kabbara mai karfi wacce ta addabi dodon kunnen kowa ta haddasa karamar guguwar kuma ya afkawa dakarun wato ya kaiwa uzaifa dauki aka rinka dauki ba dadi. Inda matsalar take shine su dai wadannan dakaru guda dari uku zafin namansu ya ninka na su uzaifa. Shima kuwa aljani huraisul marwas nan take ya raina kansa domin cikin kankanin lokaci suka kuntatashi, ya zamana cewa ko kai hari baya iya yi sai kokarin kare kansa duk da cewa shi aljani ne su kuma gasu mutane, abin da bai sani ba shine suma ba mutane bane aljanu ne yan uwansa amma sun juye izuwa siffar biladama. Shi dai uzaifa ya sami damar kaiwa dakarun harine uzaifat da kare kansa albarkacin wata addua yake ta karantawa a ransa amma da tuni shima ya shiga cikin masifar. Babu abinda zai daurewa mutum kai face yadda suke fatali da huraisul marwas tamkar suna wasan tamola. Wani Lokacin idan suka naushe shi sai ka ga an yi cilli da shi sama kai kace takarda ce take yawo a sararin sama sai dai kaji ya fado kasa tim tamkar dutse ne ya fado daga sama wanda zai dagargaje nan take amma sai ka ga ya mike zumbur saboda juriya da naci. Cikin kankanin lokaci aka hadawa aljani huraisul marwas jini da majina ya fara galabaita amma sai yaki yarda su yi masa rubdugu a Lokaci guda. Al'amarin yarima uzaifa kuwa Lokacin da ya ga ya na ta gumurzu da wadannan masifaffun dakaru har izuwa tsawon lokaci shi bai sami nasarar koda yanakar jikin dayansu ba suma kuma kun kasa yi masa komai sai hankali Ya dugunzuma ainun saboda sanin cewa hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda sanin cewa idan aka sake jimawa a haka zai iya gajiya idan kuma ya gaji shikenan an samo lagonsa. Shi kansa uzaifa yayi mamaki matukar bisa ganin yadda wadannan dakaru basa gajiya har ya tambayi kansa a cikin zuciya yace, anya kuwa wadannan mayakan muatanene su? Ai dukkan biladama mai jini kashi da tsoka a jikinsa dole ne ya kasance yana gajiya? To menene yasa su wadannan mutanen basa gajiya? Kafin uwaisul ya baiwa kansa amsar wannan tambaya sai ya hango an yiwa aljani huraisul marwas sai ya hango an yiwa aljani huraisul marwas kama kama n Kwantar da shi a kas an bankareshi tamkar dan karamin yaro ko kyakkyawan motsi ya kasa domin an take hannayensa kafafunsa da fuka fukinsa. Kawai sai wani daga cikin dakarun yazo kansa ya tsaya ya zare wani dogon mashi na sihiri ya daga sama zai caka masa a tsakiyar kirjin sa. Cikin dimauta uzaifa ya daka wawan tsalle sama yana mai kiran sunayen Allah tsarkaka, ya baiya na a sama wannan badakaren mai mashi a hannu ya gabza masa sara a wuya. Nan take kan badakaren ya cire fit yai sama, jini yai tsartuwa sannan gangar jikin ta rugurguje kuma ta kadaidai ce a cikin iska. Koda ganin wannan al'amarin sai uzaifa ya gane cewa lallai wadannan dakaru aljanu ne ba mutane ba ne don haka sai ya ci gaba da ragargazarsu tamkar yana sassabe a gona, al'amarin da ya baiwa huraisul marwas kwarin gwiwa kenan shima yaji ya sami sabon karfi a jikinsa yaci gaba da yakin amma kuma har a sannan ya kasa kashe koda mutum daya daga cikin dakarun sai dai wannan karon yana iya kare hari da mai da martani. Duk wannan gumurzu dake wakana tsoho humzalu ya koma can gefe ya rakabe yana leken abinda ke faruwa. Sai da aka shafe Saa guda cur ana wannan yaki, sannan uzaifa ya sami nasarar kashe gaba dayan dakarun sannan suka kara gaba izuwa kofa ta biyu, anan ma sun shafe Saa guda ana BAKIN ARTABU suka sami nasarar wucew. Haka dai suka tayaki ba saurarawa, wani karon suyi gumurzu da aljanu, wani karon da mugayen dabbobi, wani karon kuma da masifaffun aljanu. Shi kansa uzaifa kafin su isa kofa ta bakwai ya sami rauni a jikinsa a kalla guda biyar shi kuwa aljani huraisul marwas ya sami raunika a jikinsa sama da guda ashirin, kai in badon ma ya kasance aljani ba mai tsawon rai da tuni ya hallaka. Bayan sun gama hallaka dakarun dake gadin kofa ta bakwai ne suka tsaya suka zauna suna hutawa kuma a sannane suka sanya magani a ciki raunikansu. Gama hakan ke da wuya ai tsoho humzalu ya dubesu yace, ku tashi da sauri mu ci gaba da tafiya nan da rabin sa'a kacal zamu isa kofar kurkukun birnin nan. Zamamnmu anan abune mai hadarin gaske domin kun yi barna mai yawa a baya, idan wakilin sarki ya sami labarin abinda ya faru zai fito da kansa yazo ya taremu gami da sauran zakwakuran mayakan sa. Idan kuwa suka zo suka riskemu anan lallai kashin mu ya bushe. Kafin tsoho humzalu ya gama rufe bakinsa tuni huraisul marwas ya tari numfashin sa cikin fushi yace, ni da uzaifa ne muka yi barna a baya ko kuwa harda kai? Koda jin wannan tambaya sai humzalu yayi murmushi yace, ai tunda ina tare da ku duk laifin da kuka aikata koda babu sa hannuna ai bani da mafita. Kuma abinda nake so ka fahimta shine, fiye da kaso tamanin a cikin darin nasarar da aka samu a wannan gumurzu daga kokarin uzaifa ne amma ba naka ba. Dajin haka sai kunya ta kama aljani huraisul marwas yai shiru yana mai sunkui da kansa kas. Nan take uzaifa ya sanarwa dokinsa linzami yai gaba, humzalu ya bashi a baya yai sama har ya wuce ta saman uzaifa ya basu rata mai yawa. Humzalu ya daga kansa sama ya dubi huraisul marwas kawai sai yayi murmushi yace, on dubiin ba don kai ba uzaifat uzaifa da tuni yanzu mun halaka. Uzaifa ya maidawa tsoho humzalu martanin murmuajin da yayi yace, haka kuma ba din shi ba da yanzu haka kaima baka bamu hadin kai ba ba da kuma bamu samu nasarar da muka samu ba. Ina son ka fahimta cewa ni da aljani huraisul marwas mun taimaki juna kuma muna bukatar juna da nan har izuwa Lokacin zamu gama abinda ya kawo.mu birninku. Koda gama fadin hakan sai uzaifa yai wuf ya dauko humzalu da hannu daya ya dorashi a bayan dokinsa ya sake zaburar dokin cikin matsanicin gudu abin misali. Bayan uzaifa ya tsaka gudu akan dokin dauke da humzalu tsawon wani lokaci sai kawai yayi tirjiya sakamakon hango abinda ke gabansu. Ba wani abu bane face kofar kurkukun kasar wadda ke cike da dakarun yaki na mutane aljanu da mugayen dabbobin daki duk a gwamutse a waje daya. Koda wannan runduna ta hango mutum biyu kacal daga can nesa gami da aljani huraisul marwas sai suka kama muzurai gurnani da kai kawo tamkar jira suke a basu umarni su ruga garesu. Uzaifa ya dubi dandazon wadannan dakaru ya tuna irin tsananin wuyar da da suka sha a baya kafin su zo bakin wannan kofa ta kurkuku, sai yaji zuciyar sa ta karaya domin wannan runduna yawanta da kwarjininta ya ninka na dukkanin dakarun da suka baje a baya sau goma. Daga can sai uzaifa ya tuna duk fa nasarar da suka samu a baya ba dabararsu bace ko wayonsu Allah ne ya kawo musu agaji. Ba tare da jiran komai ba ko neman wata shawara kawai uzaifa ya sake zare takobinsa ya sakarwa dokinsa kaimi ya durfafi dandazon dakarun, ai kuwa suna sai suka taso masa gaba dayansu da mugun nufi, tamkar zasu cinyeshi danye. Dabbonbi na gunji da gurnani mutane na ta kirari sa ihu. Koda ganin haka sai shima aljani huraisul marwas ya taresu ya kutsa ta cikinsu yana mai karanta wata a addua ta musamman din neman taimakon Allah. Bisa mamaki kuwa sai yaga yana tarwasta su yana mammmakesu da hannayensa da kuma fuka fukinsa suna bajewa a kas sumammu, wasu kuma karyayyu. Shima uzaifa sai ya ratsa da karfin tsiya ta tsakiyar su yana saransu dama da hagu gaba da baya suna bajewa a kas. Duk wanda uzaifa ya sara da takobinsa sai dai kaga ya rabashi gida biyu walau mutum ko aljan ko dabba. Ba komai ne ya baiwa uzaifa wannan gagarumin karfi ba da nasara face adduoin da yake ta karantawa a cikin zuciyar sa. Duk wannan abu dake faruwa tsoho humzalu ya tsaya daga baya ya zuba idanu yana kallon sarautar Allah. Koda ya ga irin gagarumar jarumtakar da su uzaifa sukeyi sai imani ya kara shigar sa ya kara tabbatar da cewa babu wani ubangiji daya cancanci a baiya masa face ubangijn musulunci domin ko a tarihi bai taba jin jarumata irin wannan ba. Cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba kofar uta cika da gawarwakin aljanu da wadannan dakaru da ke tsaro ya zaman cewa babu daya a cikinsu wanda ya tsira da rayuwarsa. Nan take uzaifa ya sauko daga kan dokinsaya nufi inda kofar take wadda ta kasance a rufe ruf. Shima aljani huraisul marwas sai ya sauko kasa ya nufi bakin kofar. A Lokacin da tsoho humzalu ya rugo da gudu domin ya riskesu. Saadda uzaifa da huraisul marwas suka zo gaban kofar suka tsaya sai suka kurawa kofar idanu. Nan take zuciyoyinsu suka karaya saboda ganin kaurin kofar tsawonta da fadinta. Shi dai uzaifa tun da yazo duniya bai taba ganin kofar sa aka yi mata kira ta musamman ba irinta. Shi kansa karfin da akayi ta dashi kwarin sa ya wuce misali domin babu wani karfe da zai iya yi mata illa. Lokacin da aljani huraisul marwas yazo ya tsaya kusa da uzaifa sai ya dubeshi yace, ya kai dan uwana mu hada karfi mu jarraba bude wannan kofar ko zamu samu nasarar budeta. Ba tare da gardamar komai ba kuwa huraisul marwas ya amince da wannan shawara kowanne su sai ya kama marukin kofar guda suka tattara karfin su gaba daya kowannesu ya fara ja. Wohoho! Mai karfi sai Allah ya isa! Nan take kwanjin su ya kumbura jijiyoyin jikinsu suka tashi suka yi burdin burdin amma wani abin mamaki ko motsawa kofar batayi ba bare ta bude. Sai da suka jarraba bude kofar har sau uku amma abu ya gagara. Kawai sao suka ga tsoho humzalu ya dubesu ya kyalkyale da dariya. Al'amarin daya basu mamaki kenan suka koma gefe daya suka zauna. Mu hadu a part G don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari ✍️✍️♥️**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA HUDU 4 ✅ PART G ✍️♥️ MARUBUCI :- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI🧔🧔 Typing :- UMAR FAROUQ ZANGO✍️ Posting: Najibullahi Muhammad 🥷🥷 Huraisul marwas ya dubi tsoho humzalu a fusace yace tunda dai mu mun kasa bude kofar ai sai kai ka jarraba din mu gani. Kai tsaye tsoho humzalu ya nufi kofar ba tare da shakkar komai ba ashe a cikin zuciyar sa cewa yake, ya ubangijn musulunci ka karfafeni da karfinka kuma ka agajeni da agajinka na iya bude wanna kofa. Tabbas na sani cewa uzaifa da huraisul marwas sun shaafa da neman taimakon ka shi yasa suka kasa bude wannan kofa. Ni kan ban manta da kai ba ya ubangiji na. Ka nun amin isarka ni bawanka ne makaskanci wanda ba zai iya tsinanawa kansa komai ba. Gama.fadin hakan ke da wuya a cikin zuciyasa ya iso gaban kofar. Da zuwa sai ya sa hannayensa biyu ya kama marikin kofar yana mai yin bisimillah, ya ja kofar ta bude tamkar dama can a bude take ba a rufe ba kuma kamar labulen bunu ya yaye. Saboda tsananin mamaki bisa ganin abinda ya faru sai da uzaifa da huraisul marwas suka tsugunna kasa suna masu wangame baki kamar suna jira a zuba musu wani abu a ciki suka kurawa humzalu idanu kawai. Huraisul marwas ya dubi uzaifa yace, yaya akayi wannan tsohon da karfinsa ya kare y iya bude wannan kofa wacce mu ta gagaremu budewa. Uzaifa yayi shiru yana tunani, bai gama tunanin ba humzalu ya gama bude kofar gaba daya suka yi arba da wata sabuwar ta wadannan manyan karnuka masu matukar kwarijini da ban tsoro. Saboda tsananin razana da tsoho humzalu yayi bisa yin arba da karnunakan sai ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme. Uzaifa da aljani huraisul marwas kuwa sai suka ji kamar su mike su juya da baya aguje, amma saboda dakewar zuciya irin ta mazan kwarai sai suka mike tsaye suka kurawa karnukan idanu aka fara kallon kallo. Karnukan suka fara zazzago harsunansu waje tamkar an shimfida darduma suka kama gurnani. Shi kansa gurnanin da suke abin tsoro ne domin ya cika birnin gaba daya yana amsa kuwwa. Wannan shine abinda ya faru ga su yarima uzaifa bayan sunsami nasarar bude kofar kurkukun birnin shumbul domin ceto rayuwar yan uwansu dakarun musulunci musulmi wadanda aka tsaresu a ciki. * * * * * A can sansanin yaki kuwa Lokacin da aka fito da dakaru dubu dubu daga kowanne bangare sai aka tsaya ana kallon kallo a tsakanin wadannan dakaru aka rasa wadanda zasu fara afkawa wadansu. A bangaren dakarun musulunci akwai habinullahi hirama da uwar mayu wadanda sune akan gaba. Shi kuwa sarki uwaisul karni bai fito filin yakin ba ya na can a cikin tantinsa a azaune yasa ukasha a gaba yana kallonsa kawai cikin tsananin takaici, kawai jira yake yi ya farka daga baccin da yake yi sunyi wadansu maganganu. Lokaci guda habinullahi hirama da uwar mayu sukayi kabbara suka ruga da gudun tsiya izuwa kan abokan gaba. Koda ganin haka sai suma abokan gabar suka rugo garesu ana haduwa a tsakiya aka ruguntsume da a azababben yaki. Wohoho! Nan fa jini ya rinka tsartuwa da fantsama a sararin samaniya yana zubowa kasa. Komai kallon kurillar mutum bai isa ya iya gane bangaren dake samun nasara ba sai dai yace ana kare jini biri jini. Abinda ya daurewa kowa kai a wannan ranar ta Yau shine, ina sarki sha'aran da sarki uwaisul karni? Menene ya hanasu fitowa filin yakin? Haka kuma ina uzaifa da ukasha ina lafirat da sazirat ? Gaba daya wadannan manyan sadaukai ababan tsoro ga kowa ba a gansu ba kuma babu wanda zai iya yin bayanin halin da suke ciki. Duk inda uwar mayu hirama da habinullahi suka sa gabansu a cikin wadannan abokan gaba da suke fafatawa da su sai dai kaga mazaje na zubewa kasa. A bangaren mutanen birnin shumb ma sai aka sami wadansu zakwakuran mayaka guda uku masu jajayen kaya bisa jajayen dawakai wadanda suma sune suke ta ragargazar musulmi anayin ragas. Koda su hirama suka fahimci cewa wadannan mutane uku sune suke yiwa yan uwansu musulmi mummanar barna sai suka taresu kowa yaja abokin gwaminsa aka fara sabon bakin gumurzu. A wanann lokaci ne ya zamana cewa an kashe musulmi dari bakwai da arbain daga cikin dubu da suke yakin. Su kuma kafirai an kashe mutum dari takwas da ashirin. Haka dai aka ci gaba da yakin har ya zaman cewa a cikin mayaka dubu biyu saura shida kacal. A bangaren musulmi habinullahi hirama da uwar mayu kawai. A bangaren kafirai kuwa wadannan masu jajayen tufafi ne su uku wadanda suka rufe fuskokin su da wata irin bakar hular karfe wacce baa ganin komai na fuskokinsu, haka kuma sun rufe hannayensu da bakaken tufafi ko kalar jikinsu baa gani haka ma kafafunsu a rufe suke cikin bakaken takalma. Haka dai su hirama da masu jajayen tufafin aka ci gaba

Chapter 20 of 21