Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
takawa. Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya juya yaci gaba da tafiya yabar Abul shaja'a a zaune a wajen, kawai sai Abul shaja'a yaga Lafirat ta waigo tana yi masa dariya. Nan take Abul shaja'a ya fusata ya kama wannan ice dake hannunsa da kyau cikin tsananin juriya ya yunkura ya tashi tsaye da kyar, sannan ya fara dogara sandar yana dogarawa da kyar yana cijewa, a wannan lokaci ji yakeyi kamar kafar zata gutsure saboda tsananin zafi da zugin da yake ji. Haka dai ya jure ya ci gaba da dogarawa yana bin Uzaifat a baya har hawayen wahala na zubo masa. Koda Uzaifat ya juyo yaga halin da yake ciki, sai da tausaya masa, amma sai ya dake bai nuna ya ji tausayin nasa ba. Haka dai suka ci gaba da tafiya, bayan 'yan sa'o'i sai suka tsaya su huta, sannan su ci gaba da tafiya, har dai suka iso bakin dajin masaharul kais. Da zuwansu sai Lafirat tace, ya kai gwarzon jarumi kada ka shiga cikin wannan daji yanzu, mu zauna anan tsawon kwana uku, domin ni da Abul shaja'a mu kara samun sauki. Komai kankantar taimakon da zami iya baka yana da muhimmanci. Na tabbata cewa, nan sa kwana ukun zamu iya samun karfin jikinmu, mu iya agazawa da wani abin. Sa'adda Uzaifat yaji wannan batu, sai ya yi shiru baice komai ba, ya dubi Abul shaja'a. Abul shaja'a ya jinjina kai yana mai yi masa nuni da cewa ya karbi wannan shawara ta Lafirat. Ba tare da gardamar komai ba Uzaifat ya je jikin wani dutse ya tsugunna ya sauke bayanta ya dubi raunin nata yaga ya fara kamewa, amma kuma akwai bukatar tayi mata addu'a ya tofa akan ciwan. Har ya yunkura zai fara adduar sai ya tuna cewa, ai Lafirat ba musulma bace, don haka sai ya fasa, ya dawo wajen Abul shaja'a ya tsugunna ya kwance raunin yaga shima nasa ya fara kamewa harma yafina Lafirat warkewa. Cikin mamaki Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace yaya akayi raunin naka naga yayi saurin warkewa haka. Abul shaja'a yayi murmushi yace, albarka cin addu'a ne ya kawo haka. Me yasa ka fasawa yiwa Lafirat addu'a dazu alhalin da naga kayi niyyar yin haka? Koda jin wannan tambaya, sai Uzaifat yayi shiru bai ce komai ba, kuma ya juya ya dubi Lafirat wacce ke can gefe daya a zaune, tsakanin su akwai tazara bata jiyo abinda suke tattaunawa. Uzaifat ya juya ya sake fuskantar Abul shaja'a yace, kasan cewa Lafirat ba musulma nace, don haka banga dalilin da zai sa nayi mata addu'a ba. Abul shaja'a yace, wannan gaskiya ne, amma ina Fatan ta samu lafiya da wuri, domin tana da mutukar muhimmanci a cikin wannan tafiya tamu. A dai dai wannan lokacine Lafirat tayi tati ta kira sunan Uzaifat. Cikin sauri Uzaifat ya mike tsaye ya ruga gareta yace, me kike bukata? Lafirat tace, ina mutukar jin kinshirwa, kuma na duba salka ta naga babu komai a ciki. Uzaifat na jin haka, sai ya duba tasa salkar ya ga itama ko digon ruwa babu a cikinta, kawai sai ya sake rugawa wajen Abul shaja'a ya duba tasa salkar, ita ma babubkomai a ciki. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ya rasa me zaiyi. Kawai sai ya dubi Abul shaja'a yace, ya zama dole na shiga cikin wannan daji na mashaarul kais domin neman ruwan sha tunda wajen dake da ruwa a bayanmu yana da nisa sosai. Zan tafi na barka a nan tare da Lafirat. Ka sani cewa, Lafirat ba zata iya yiwa kanta komai ba, amma kai da sauran kwarinka. Koda wani abu zai taso muku kayi iya kokarinka wajen kare lafiyar ku, kafin na dawo. Koda gama fadin haka, sai Uzaifat ya koma wajen Lafirat ya tsugunna a gabanta, ya ce, zan shiga cikin dajin mashaarul kais domin na samo mina ruwan sha, zaku ci gaba da zama a nan har dawo. Koda jin wannan batu, sai idanun Lafirat suka zazzaro ta dubi Uzaifat cikin tsananin damuwa da fargaba tace, in dai saboda ni zan tafi neman wannan ruwa ka barshi zan iya jure kishirwata har tsawon kwana ukjn da zamuyi anan. Uzaifat yayi murmushi yace, haba Lafirat yaya za'ayi ki rayuwa tsawon kwana uku cikin kishi, ai bazaiyiwu ba. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai sameni, da izinin ubangijina. Na yi miki alkawarin zam dawo nan da sa'a uku. Ga Abul shaja'a nan zai debe miki kewa kafin na dawo, kuma na tabbata cewa, zai iya baki kariya dai dai gwargwado. Sa'adda lafirat taji haka, sai ta yi yake tace, bazai iya debe min kewar da zaka iya debe min ba, kuma bazai iya bani kariyar da zaka iya bani ba. Babu abinda zan iya cewa tunda nasan cewa bazan iya hanaka tafiya ba, amma zan kasance a cikin tsananin bakin ciki idan har baka dawo ba kariskeni a raye ba. Koda jin wannan bayi, sai Uzaifat ya cika da tsananin mamaki, yace ni fa ban fahimci komai ba dan gane da duk wannan bayani naki ba. Lafirat tayi murmushin yake tace, ai bazaka fahimta ba, domin lokacin fahimtar baiyiba. Fatana kawai shine, ni da Kai mu sake saduwa, kuma mu rayu har zuwa lokacin da zamu cika burikan zukatanmu. Maza ka tafi neman wannan ruwa domin ka dawo da wuri, kasan cewa yanzu fa lokaci abune mai mutukar muhimmanci a garumu. Uzaifat yace, kwarai kuwa, nan take ya mike tsaye ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi cikin dajin mashaarul kais. Koda ya juyo ya hada ido da Lafirat, sau yaga idanunta sun ciko da kwalla sannan fuskarta na nuna tsananin damuwa karara. Kuma tana yi masa kallo mai dauke da alamar tambaya. Kawai sai Uzaifat ya ji tsikar jikinsa ta tashi gaba daya, zuciyarsa ta buga da karfi, ya kaimu da was wasu gami da jimami a ransa, nan take yaji kamar bazai iya tafiya baya bar lafirat a cikin wannan hali ba, amma sai ya daure ya juya ya kunna kai cikin wannan dajin na mashaarul kais, bai yarda ya sake juyowa sun hada idanu da Lafirat ba, kada zuciyarsa ta karye. ****""""*****"""******""" Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 *****""""******"""""*****"" Bayan kamar dakika dari uku da sittin da tafiyar Uzaifat, Abul d Lafirat na zaune shiru dayansu baice kala ba, sai dai su kalli juna su kau da kai, kuma ga shi akwai tazara a tsakanin su, koda zakuyi magana da juna sai dai su daga murya. Kawai sai Lafirat ta yafito Abul shaja'a da hannunta tana mai nufin ya taso ya dawo inda take. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Abul shaja'a ya dauki wannan dogon icen da yake dogarawa ya mike tsaye da kyar ya dogara yana tafiya a hankali har ya isa inda Lafirat take, ya zauna daf da ita. Lafirat ta dubeshi cikin murmushi tace, hakika mutanen birninku sunyi babbar sa'a. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Abul shaja'a yace, ke kuwa saboda me kika fadi haka? Lafirat tayi murmushi ta ce, saboda kun sami magajin sarkinku yarima uzaifat domin na fuskanci cewar, yana da dakakkiyar zuciya ta rashin tsoro irin ta mahaifinsa, kuma sannan yana da tausayi da adalci ga tsagwaron jarumta. Akwai alamun cewa, nan gaba zai iya yin shahara a duniya, idan har ajali bai yi masa gaggawaba. Uzaifat mutumne irin wanda kowace 'ya mace lo son ta mallaka domin zai share mata hawayenta a duk sa'adda yaga yana zuba. Wai shin kuwa Uzaifat na da macen da yake son aura a rayuwarsa? Koda Jin wannan tambaya, sai Abul shaja'a yayi murmushi yace, ai Uzaifat bai taba yin soyayya ba, duk cewa 'yan matan garin mu da yawa sun shiga mugun hali bisa kamawa da sonsa. Abinda ya kan gaya musu shine, bazai taba yin soyayyaba, ko Aure face yacika burin mahaifinsa, wato yaci birnin shumbul da yaki. Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta cika da farin ciki ta kama murmushi, kuna ta yi shiru batace komai ba. Shi kansa Abul shaja'a da ya ga tana wannan murmushi sai da ya tsargu yace a ransa, anya kuwa babu soyayyar Uzaifat a cikin zuciyar Lafirat? Idan ma akwai zan gane nan gaba, domin an ce somi somin hauka zuba da yawu ne. Ga ma aiyana hakan ke dawuya a cikin zuciyar Abul shaja'a sai kawai sukayi gaba daya dajin ya kama girgiza kasa na neman darewa ta rufta dasu ciki, al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalin Lafirat da da Abul shaja'a kenan suka kama kalle kalle da hange hange ko zasu ga abinda ke shirin aflo musu amma shiru basu ga komai ba. Cikin karfin hali Abul shaja'a ya mike tsaye yan dogara wannan ice da hannun hagu, sannan ya zare takobinsa da hannun dama ya tsaya yana saurare. Ita kuwa Lafirat da tasan cewa bazata iya komai ba, sai ta zuba idanu kawai tana sauraron abinda zai wakana. Doke dai tasan cewa, cikin biyu sai abu daya ya faru. Ko su hallaka, ko kuma su tsira da rayuwar su. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ga wani garjejen maridi ya durfafosu, wanda hucin isar bakinsa ta haddasa karamar guguwa, ashe karfin takun sawayensa ne ya haddasa wannan girgizar kasa. Girman kansa kuwa ya kai na wani dan babban dutse wanda karti shirin bazasu iya rabashi da kasa ba. Maridin yana da manyan idanuwa kwala kwala guda hudu, biyu a kwan girar ido, biyu kuma a daman girar. Yana da wawakeken baki tamkar an fafe ganga, gami da dan mitsitsin hanci, wanda ko karamin dan yatsa bazai shiga ba. Fuskarsa gaba daya a cike take da gashi, babu kyan gani. Hakika munin wannan maridi ya wuce misali, sai abinda ido ya gani. Koda Lafirat tayi arba da wannan maridi sai ta figita ainun, ta kamu da tsananin tsoro, domin duk iya saninta da sirrin wadannan dazuka ba ta taba sanin cewa akwai ba. Kai ko a labari nata taba jin cewa irinasa ya taba wanzuwa ba. Inda tasan dashi wata kika tasan hanyar da za a bi a hallakashi. Lokacin da Abul shaja'a yaga wannan maridi ya taho kansu gadan gadan da nufin ya hallakasu, sai yayi jifa da sandar hannunsa ya take kafar tamkar bai taba samun rauni ba, ya ruga ga maridin da dukkan karfinsa, yana kururwa irin wacce ke firgita mazaje a filin daga, ya kaiwa maridin sara da takobinsa a ciki. Take maridin yasa hannuna ya kare saran, ai kuwa sai takobin Abul shaja'a tayi tsalle sama ta fadi can gefe daya, kafin Abul shaja'a yayi wani yunkuri tuni maridin ya mangareshi da daya hannun nasa. Saboda karfin mangarar sai da Abul shaja'a yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya yaje ya gwara Kai d wani dutse, kansa ya fashe jini yayi tsartuwa ya fado kasa magashiyan tamkar gawa, ko motsawa bai sake yi ba. A sannane maridin ya tunkari Lafirat. Koda taga ya yo kanta sai ta tsandara ihu tana mai kwalawa Uzaifat kira. Sautin ihun nata ya cika dajin gaba daya, yana mai amsa kuwwa. Wannan shine abinda ya faru ga Lafirat da Abul shaja'a, bayan yarima Uzaifat ya barsu a bakin dajin mashaarul kais ya tafi neman ruwa sha. * * * * * * * A can birnin shumbul kuwa, a cikin masarautar, sarki shaaran ya ga duk abubuwan da suka faru ga su Uzaifat a cikin madubin tsafinsa, wato yaga lokacin da yarima Uzaifat ya afka cikin dajin mashaarul kais don neman ruwan sha, kuma ya ga lokacin da wannan garjejen maridi ya mangare Abul shaja'a yayo kan Lafirat, tana ta kwala ihu. Koda ganin wannan al'amari sai sarki shaaran ya kyalkyale da dariyar farin ciki kamar bazai daina ba. A wannan lokaci ukashat da gimbiya sazirat na zaune a gefe daya bisa kujerun daraja suna kallosa kawai. Bayan sarki shaaran yayi dariya har ya gaji sai ya hade fuskanci ya dubi sazirat da ukashat yace, ku tashi kuke kuyi shiri yanzunnan zamu kama hanya mu tafi izuwa birnin Darul husuf domin cika burinmu. Tabbas dan uwanka Uzaifat sai ya hallaka a cikin wannan daji na mashaarul kais, ita ma Lafirat nasan cewa tuni wannan maridi ya gama da ita. Hakika yanzu ne muje da cikakkiyar dama, wacce zamu iya tafiya mu ci birninsu da yaki ba tare da mun fuskanci wata matsala ba. Koda jin wannan batu, sai ukashat da sazirat suka mike zumbur cikin murna suka nufi hanyar fita daga cikin fadar. Har sunje bakin kofar sai ukashat ya juyo ya dubi sarki shaaran yace, ya shugabana me zai hana yanzu ka duba mana a cikin madubin tsarin ka mu ga halin da birnin Darul husuf ke ciki. Nasan halin mahaifina yana da wata irin baiwa tayin mafarki bisa duk irin abinda zai same shi. Babu mamaki a halin yanzu tasan da zuwanmu, kuma ya dauki mataki akan hakan. Koda jin wannan batu, sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta, sannan ya tako kafafunsa yazo daf da ukashat ya tsaya ya dafa kafardarsa, yace, kwantar da hankalika ya kai sarkin Darul husuf na gobe. Ina tabbatar maka dacewa, duk irin sihirin da sarki uwaisul karni zaiyi, sai mun sami nasara a kansa domin abin dogarona ya bani sa'a. Abinda nakeso da kai kawai shine ka tabbatar da cewa ka tone wadannan layu guda hudu da aka binne a kasar katangun birninku kafin mu fara Yaki dasu. Ka sani cewa a duk sa'adda na yi yunkurin ganin abinda ke faruwa a birninku, sai mudubin tsafina ya fashe nayi asararsa saboda karfin sihirin mahaifinka. Sa'adda ukashat yaji wannan batu, sai yayi shiru bai ce komai ba, ita kuwa sazirat sau ta kama hannunsa ta jashi suka fice daga cikin fadar da sauri suka wuce izuwa can harabar gidanta, inda suka shiga shiri da kimtsawa domin gagarumin yakin da zasu tafi. Shi ma sarki shaaran sai ya shiga hada dakarunsa aka rinka fito da makaman yaki iri iri ana rabawa dakarun, sannan aka yi ta shirya dawakai da guzuri ba adadi. Idan mutum ya ga yawan dakarun sarki shaaran wadanda zasu tafi wannan yaki da kuma yawan dawakan da aka ta Nada da guzuri, dole ne ya cika da mamaki, domin an kashe dukiya mai tsananin yawan gaske. Wannan shine mugun tanadin da sarki shaaran sukayi, abinda basu sani ba shine abokan gabar tasu ma sunyi shiri, sun taho gareku saboda haka sai dai a hadu akan hanya a gwabza kazamin yaki da za a fidda raini mai sa'a ya cika burin sa. * * * * * * Al'amarin yarima Uzaifat kuwa, lokacin da ya kunna kai cikin dajin mashaarul kais yana neman ruwa, sai ya shafe sa'a guda bai ga wani tafki ko koramaba, al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ainun, saboda tunanin halin da ya Bari Lafirat a ciki, don haka sai ya kara kaimin tafiya, har ma yana gudu gudu yana waige waige ko zai hango rafi ko korama. A wannan lokaci Uzaifat ya ma manta da cewa a cikin dajin mashaarul kais yake, dajin da Lafirat ta basu labari cewa, akwai wadan su muggan tsuntsaye a cikinsa manya manya masu tsananin karfi da hikimar kai hari. Uzaifat yaci gaba da gudu yana waige waige har tsawon wata rabin Saar. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ya hango wata babbar fadama a gabansa ruwa na ta gudu a cikinta. Cikin tsananin farin ciki ya karasa cikin fadamar wacce ruwanta ke kwararowa daga sama takan duwatsu. Da shigar Uzaifat fadamar sai ya tsuma salkarsa a cikin fadamar da nufin ya cikata taf da ruwa, sannan shima yasha ya koshi. Kwatsam uzaifat yaji wata irin gagarumar iska kafin ya dago kai yaga ko menene sai kawai yaga wadansu irin jibga jibga tsuntsaye guda biyu dai dai kansa. Tun da Uzaifat ya zo duniya bai taba ganin irin su ba. Kafin Uzaifat yayi wani yunkuri tuni tsuntsayen sun cafi kafadunsa sunyi sama da shi, sun luluka. Uzaifat ya yunkura da nufin ya zare takobinsa daga cikin kufenta, amma sai yaji ya kasa motsa hannayensa duka biyun, sakamakon mugun rikon da tsuntsayen suka yi Masa da kafafunsa, kawai sai ji yayi yana ta wutsil wutsil da da kafafunsa, amma babu mafita ko dabara. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya saduda ya zubawa sarautar Allah ido kawai yana jira yaga inda tsuntsaye zasu kaishi. Sai da tsuntsayen suka yi doguwar tafiya da Uzaifat a sama, har gaji likis yaji kamar kafadunsa zasu gutsure, sannan tsuntsayen suna ido kan wani dogon katon tsaunin wanda akan sama akwai wadansu manyan duwatsu. Kwatsam sai Uzaifat ya hango wata babbar sheka ta tsuntsayen cike da jira jiran 'ya'yansu. MU HADU A DAKARUN MUSULUNCI NA 2 PART C don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARIN ✍️✍️✍️🤝🤝🙏🙏🙏🙏🙏**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA 2 PART C 💯💯❤️ Na:ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING UMAR FAROUQ ZANGO. Posting: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.. Bayan kamar dakika dari uku da sittin da tafiyar Uzaifat, Abul d Lafirat na zaune shiru dayansu baice kala ba, sai dai su kalli juna su kau da kai, kuma ga shi akwai tazara a tsakanin su, koda zakuyi magana da juna sai dai su daga murya. Kawai sai Lafirat ta yafito Abul shaja'a da hannunta tana mai nufin ya taso ya dawo inda take. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Abul shaja'a ya dauki wannan dogon icen da yake dogarawa ya mike tsaye da kyar ya dogara yana tafiya a hankali har ya isa inda Lafirat take, ya zauna daf da ita. Lafirat ta dubeshi cikin murmushi tace, hakika mutanen birninku sunyi babbar sa'a. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Abul shaja'a yace, ke kuwa saboda me kika fadi haka? Lafirat tayi murmushi ta ce, saboda kun sami magajin sarkinku yarima uzaifat domin na fuskanci cewar, yana da dakakkiyar zuciya ta rashin tsoro irin ta mahaifinsa, kuma sannan yana da tausayi da adalci ga tsagwaron jarumta. Akwai alamun cewa, nan gaba zai iya yin shahara a duniya, idan har ajali bai yi masa gaggawaba. Uzaifat mutumne irin wanda kowace 'ya mace lo son ta mallaka domin zai share mata hawayenta a duk sa'adda yaga yana zuba. Wai shin kuwa Uzaifat na da macen da yake son aura a rayuwarsa? Koda Jin wannan tambaya, sai Abul shaja'a yayi murmushi yace, ai Uzaifat bai taba yin soyayya ba, duk cewa 'yan matan garin mu da yawa sun shiga mugun hali bisa kamawa da sonsa. Abinda ya kan gaya musu shine, bazai taba yin soyayyaba, ko Aure face yacika burin mahaifinsa, wato yaci birnin shumbul da yaki. Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta cika da farin ciki ta kama murmushi, kuna ta yi shiru batace komai ba. Shi kansa Abul shaja'a da ya ga tana wannan murmushi sai da ya tsargu yace a ransa, anya kuwa babu soyayyar Uzaifat a cikin zuciyar Lafirat? Idan ma akwai zan gane nan gaba, domin an ce somi somin hauka zuba da yawu ne. Ga ma aiyana hakan ke dawuya a cikin zuciyar Abul shaja'a sai kawai sukayi gaba daya dajin ya kama girgiza kasa na neman darewa ta rufta dasu ciki, al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalin Lafirat da da Abul shaja'a kenan suka kama kalle kalle da hange hange ko zasu ga abinda ke shirin aflo musu amma shiru basu ga komai ba. Cikin karfin hali Abul shaja'a ya mike tsaye yan dogara wannan ice da hannun hagu, sannan ya zare takobinsa da hannun dama ya tsaya yana saurare. Ita kuwa Lafirat da tasan cewa bazata iya komai ba, sai ta zuba idanu kawai tana sauraron abinda zai wakana. Doke dai tasan cewa, cikin biyu sai abu daya ya faru. Ko su hallaka, ko kuma su tsira da rayuwar su. Kwatsam ba zato ba tsammani sai ga wani garjejen maridi ya durfafosu, wanda hucin isar bakinsa ta haddasa karamar guguwa, ashe karfin takun sawayensa ne ya haddasa wannan girgizar kasa. Girman kansa kuwa ya kai na wani dan babban dutse wanda karti shirin bazasu iya rabashi da kasa ba. Maridin yana da manyan idanuwa kwala kwala guda hudu, biyu a kwan girar ido, biyu kuma a daman girar. Yana da wawakeken baki tamkar an fafe ganga, gami da dan mitsitsin hanci, wanda ko karamin dan yatsa bazai shiga ba. Fuskarsa gaba daya a cike take da gashi, babu kyan gani. Hakika munin wannan maridi ya wuce misali, sai abinda ido ya gani. Koda Lafirat tayi arba da wannan maridi sai ta figita ainun, ta kamu da tsananin tsoro, domin duk iya saninta da sirrin wadannan dazuka ba ta taba sanin cewa akwai ba. Kai ko a labari nata taba jin cewa irinasa ya taba wanzuwa ba. Inda tasan dashi wata kika tasan hanyar da za a bi a hallakashi. Lokacin da Abul shaja'a yaga wannan maridi ya taho kansu gadan gadan da nufin ya hallakasu, sai yayi jifa da sandar hannunsa ya take kafar tamkar bai taba samun rauni ba, ya ruga ga maridin da dukkan karfinsa, yana kururwa irin wacce ke firgita mazaje a filin daga, ya kaiwa maridin sara da takobinsa a ciki. Take maridin yasa hannuna ya kare saran, ai kuwa sai takobin Abul shaja'a tayi tsalle sama ta fadi can gefe daya, kafin Abul shaja'a yayi wani yunkuri tuni maridin ya mangareshi da daya hannun nasa. Saboda karfin mangarar sai da Abul shaja'a yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya yaje ya gwara Kai d wani dutse, kansa ya fashe jini yayi tsartuwa ya fado kasa magashiyan tamkar gawa, ko motsawa bai sake yi ba. A sannane maridin ya tunkari Lafirat. Koda taga ya yo kanta sai ta tsandara ihu tana mai kwalawa Uzaifat kira. Sautin ihun nata ya cika dajin gaba daya, yana mai amsa kuwwa. Wannan shine abinda ya faru ga Lafirat da Abul shaja'a, bayan yarima Uzaifat ya barsu a bakin dajin mashaarul kais ya tafi neman ruwa sha. * * * * * * * A can birnin shumbul kuwa, a cikin masarautar, sarki shaaran ya ga duk abubuwan da suka faru ga su Uzaifat a cikin madubin tsafinsa, wato yaga lokacin da yarima Uzaifat ya afka cikin dajin mashaarul kais don neman ruwan sha, kuma ya ga lokacin da wannan garjejen maridi ya mangare Abul shaja'a yayo kan Lafirat, tana ta kwala ihu. Koda ganin wannan al'amari sai sarki shaaran ya kyalkyale da dariyar farin ciki kamar bazai daina ba. A wannan lokaci ukashat da gimbiya sazirat na zaune a gefe daya bisa kujerun daraja suna kallosa kawai. Bayan sarki shaaran yayi

Chapter 7 of 21