Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da gumurzu ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka ba kakkautawa amma aka rasa bangaren da zai samu nasara. Su dai masu jajayen tufafi duk saadda su Habinullahi suka sari jikinsu sai suji kamar dutse ko karfe suka sara sai dai kaji kara kal ta tashi, suna kuna idan suka sari su hirama ko suka sokesu da takobi bata tasiri a jikinsu saboda karfin addua. Babban abinda ya daurewa su hirama kai shine akwai lokacin da hirama ta shammaci abokin fadanta ta soka masa takobi izuwa cikin hular karfen da ke kansa. Takobin ta shige cikin hular ta bullo ta bayan hular amma a ta zare takobin sai taga babu ko digon jini a jikinta dama kuma sadda ta soka takobin taji kamar iska ta soka. Nan fa hirama ta fara tunanin cewa ba da mutane suke wannan yaki ba kuma ba aljanu bane sai dai a dauke su a matsayin fatalwa abar da bata da gangar jiki sai dai Inuwa. Nan take hirama ta ja da baya ta gyara tsayuwarta. Koda ganin haka sai uwar mayu da habinullahi suma suka ja da baya suka tsaya daf da hirama ta dubesu tace, wadannan abokan gabartamu fa ba mutane bane kuma ba aljanu bane. A jikinsu babu tsoka kuma babu kashi idan zamu kwana muna yaki ba zamu iya cutar da su ba, sai dai mu nemi taimakon Allah. Koda jin haka sai habinullahi yayi ajiyar zuciya yace, tabbas kuskuren da mukayi kenan tun farko. Yanzu gashi sun kashe mana gaba dayan jama'ar mu dari tara da casain da bakwai mu uku ne kacal muka tsira. Koda jin haka sai duk su ukun suka dubi juna. Kamar hadin baki sai suka mikar da hannayensu a tsaye takubban su na yin nuni izuwa kirjin abokan gabar sannan suka zaburi dawakansu da gudu izuwa kan abokan gabar tasu. Koda ganin haka sai suma suka zaburi nasu dawakan domin su tare su. Tun daga nesa kadan su hirama suka budi baki suka kira sunan Allah suna masu neman agajinsa. Nan take wani irin Jan haske yayi tsiro daga cikin takubban su hirama ya soki kirjin wadannan dakaru uku kawai sai aka ga sun fado kasa daga kan dawakansu, kawai sai suka kumbura suka yi bindiga suka farfashe tamkar an daddatsa sassan jikinsu a mahauta yai gutsi gutsin. Koda ganin abinda ya faru sai gaba daya dakarun musulunci dake tsaye suka rude da kabbara cikin tsananin murna. Su kuwa dakarun kafirai sai suka firgice ainun sakamakon ganin abinda ya faru da kuma sautin kabbarar da musulmi sukayi wacce tacika dodon kunnensu. A dai dai wannan lokacine yarima ukasha ya farfado daga bacin da yake mai nauyi yayi arba da sarki uwaisul karni zaune a gabansa yana ta murmushin farin ciki domin ya juyo wanann kabbara da musulmi keyi ya tabbatar da cewa nasara ce aka samu. Cikin tsananin firgici ukasha ya yunkura domin ya mike tsaye sai yaji hannayensa da kafafunsa a daure tamau cikin sarka ya girgiza su suka yi kara kwacam kwacam! Koda ya tabbatar da cewa ba zai iya kwancewa ba sai hankalinsa ya dugunzuma kuma ya cika da mamakin yadda akayi aka kamashi har aka kawoshi nan cikin tantin sarki uwaisul karni ba tare da ya sani ba. Take kunya ta rufe ukasha ya sunkui da kansa kas ya kasa hada idanu da sarki. Sarki uwaisul karni Yaqui yayi ajiyar zuciya Lokacin da hawaye ya zubo masa saboda takaici sannan ya dubi ukasha yace, ya kai dana hakika ka bani mamaki kuma ka bani kunya domin ka tozarta darajar ka da darajar ta da kuma girman addinin mu. Yanzu ashe saboda kwadayin duniya zaka iya kin addininka yan uwan kada kasarka? Ukasha yayi shiru baice komaba kuma ya kasa dago kai ya dubi sarki. Tsawon yan dakiku sarki bai yi magana ba, daga can sai yai gyaran murya yace ya kai dana yanzu zan yi maka tambayoyi guda uku lallai ka bani amsarsu idan kana son ka tsira da rayuwarka. Ka sani cewa Allah ya sanar da ni komai dangane da al'amarinka a cikin mafarkina don haka idan ma ka yi mini karya zan sani. Tambaya ta ta farko itace shin kayi ridda ne ko kuwa har yanzu kana nan a cikin musulunci? Koda jin wannan tambaya sai ukasha yai sauri ya dago kai yace ina nan a cikin addinin musulunci ban fita ba. Sarki uwaisul karni yayi guntun murmushi yace naji wanann. Tambaya ta biyu shin gaki gaskiyane ka sha giya? Ukasha yayi dan shiru sannan yace gaskiya ne na sha giya. Shin kayi zina ? Ukasha ya fashe da kuka yace nayi zina ya kai abbana. Hakika na aikata wadannan laifuka. Sarki ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace tunda kayi furuci da bakina lallai hukunci ya hau kanka kuma Wallahi summa Wallahi sai nayi maka hukuncin irin wanda addini ya zo da shi. Inda ace ka karyata abinda na tuhumeka dashi, wato baka amsa laifin ka ba ba zan maka hukunci ya tabbata tunda kayi furuci. Ya kai dana ina tunaninka da hankalinka suka tafi har ka cire tsoron Allah a zuciyar ka aikata wadannan munana ayyuka? Hakika zuciya uda shaidan sun ribaceka kuma mahaifiyar ka ta cuceka da ta doraka aka wannan tafarkin na kaucewa gaskiudon son zuciya. Shin ka manta ne da azabar da Allah ya tanada akan mazinata da maabota shan giya? Shin ka manta ne cewa koi musulmi ne kuna dan sarkin musulmi na babbar kasar musulunci da babu kamarta a wanann nahiya? Ai wanann abu da ka aikata abin gori ne kuma abin kunya a garemu baku daya domin ka zubar mana da mutunci da kimarmu a iron duniya. Ashe duk tarbiyya da na baka tun kana yaro karari ta zama ta banza ? Lallai a gobe da safe kafin aci gaba da yaki zan yi maka hukunci bisa wadannan laifuka da ka aikata kamar yadda Allah yace a hukuntaka. Bayan nan zan sa a kwanceka daga cikin wannan sarka. Idan ka ga dama kuma idan har ka rayu ka koma cikin abokan gabarmu ka yakemu tare da su, idan kuma ka so ka zauna a cikin mu ka tayamu yakarsu. Zani ya rage gareka. Koda gama wannan furuci sai sarki uwaisul karni ya kira wadansu dakaru guda biyu dake tsaye a wajen tantin yace dasu su dauki ukasha su kaishi can tantin dan uwansa uzaifa su ajiye shi kuma a zuba ido a kansa nan take wadannan dakaru biyu suka cikin umarn. Lokacin da aka je aka warbar da yarima ukasha a cikin tantin dan uwansa uzaifa sai aka fita aka barshi kadai sai nan take yaji nadama tazo masa bisa dukkanin abubuwan da ya aikata. 🏃🏃🏃🏃🏃🥷🥷🥷🥷🥷 Maganganun da sarki ya fada masa suka rinka dawo masa a cikin zuciyar sa kawai sai yaji duniyar gaba daya tayi masa zafi bai san saadda ya fashe da kuka ba cikin matsanaicin bakin ciki. Har dare ya raba ukasha bai daina kuka ba, hatta sarki uwaisul karni sai da ya jiyo sautin kukansa daga tantinsa amma sai yayi biris da shi duk da cewa yaji tausayinsa ya kamashi, burinsa kawai shine gari ya waye ya tabbatar da wannan hukunci a kansa koda kuwa hukuncin zai zamo sanadin ajalinsa. Kashe gari da sassafe sahun dakarun musulmi ya dai daita a filin yaki. Haka ma na kafirai. Mai makon a fara yaki sai rundunar kafirai suka ga anfito da yarima ukasha a daddaure a cikin sarka. Nan take aka Kwantar da shi bisa wata katuwar bishiya da aka sareta yayi rub da ciki akanta sannan aka dada daureshi tamau a jikinta yadda ko motsin kirki ba zai iya ba. Kawai sai aka ga wani narkeken katon mutum daga cikin dakarun musulmi ya taho izuwa kan ukasha rike da wata zabgegiyar bulala mai kauri wacce aka mulketa da man shanu sai kyalli take. Bayan mai bulalar ya tsaya akan ukasha sai ga sarki uwaisul karni ya taho garesu. Da isowarsa daf da su sai ya tsaya ya dubi wannan narkeken katon mutum mai bulala a hannu yace dashi maza ka yiwa dana ukasha bulala tamanin bisa laifin shan giya da ya furta da bakinsa yayi. Sannan ka kuma sake yi masa wata tamanin bisa laifin aikata zina da ya furta da bakinsa yayi. Kafin sarki uwaisul karni ya gama rufe bakinsa tuni wannan narkeken kato ya fara aikinsa. Al'amarin da ya mutukar girgiza kafirai kenan suka cika da tsananin mamakin yadda sarki guda zai sa ayiwa dansa na cikinsa irin wanann hukunci. Dukkanin su sai jikinsu yayi sanyi. Koda aka fara shaudawa ukasha wannan bulala sai ta rinka fasa rigar jikinsa har da fatar jikinsa gaba daya, jini ya dinga fallatsi. Duk da tsananin jarumta irin ta ukasha sai da ya kasa jurewa azabar wannan bulala ya dinga mutsu mutsu. Koda aka kai bulala arbain sai ya fara ihu. Kafin a cika tamanin din sai ya suma kuna ko ina a jikinsa yai fatafata da jini ba kyan gani. Jama'a da yawa a cikin filin yakin sai da suka zubar da hawaye saboda tausayi. Lokaci da sarki uwaisul karni yaga ukasha ya suma amma an sami nasarar kammala yi masa bulala tamanin ta laifin shan giya sai cika da murna. Kawai sai ya dubi mai yi bulala yace watsa masa ruwa ya farfado. Idan har ya farfado bai mutuba sai kayi masa bulala tamanin ta laifin zina. Shi kansa mai bulala sai da yaji tausayinsa ya tsaya yana nuku nuku da bata lokaci sarki uwaisul karni ya daka masa tsawa yace, maza kayi abinda muka umarceka idan kuma ba zaka iya ba muyi da kanmu. Koda jin haka sai jikin mai bulala ya kama tsuma cikin fushi sarki uwaisul karni ya debo ruwa ya watsawa ukasha a fuska. Take ukasha ya farfado yana mai fatar da numfashi sama sama. Kawia sai sarki uwaisul karni ya fisge bulalar daga hannun wannan katon mutumin ya ci gaba da zabgawa ukasha iya karfinsa fiye da yadda ma katon ke yi masa har sai da yayi masa bulala tamanin cif. Wannan Karon sai da ukasha ya suma sau uku. A suman karshene numfashinsa ya dauke gaba daya idanunsa suka rufe kuma jikinsa ya sandare. Sarki uwaisul karni ya kau da kai ya juyawa ukasha baya yana mai zubar da hawaye yana cewa ko ba komai muna kyautata maka zaton rahamar ubangiji. Sannan ya dubi dakarun yace ku daukeshi ku je kuyi masa wanka da sallah a binneshi. Koda aka kwance ukasha daga jikin wannan bishiya aka tafi da shi sai filin yaki gaba daya yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta. A sannane sarki uwaisul karni yaji idanunsa sun ciki da kwalla saboda sanin cewa ya rasa dansa ukasha ba kenan har abada amma da ya tuna cewa ukasha ba zaije gaban Allah da laifi ba sai farin ciki ya lullubeshi bai san saadda hawaye murna ya zubo masa ba. Su kuwa rundunar kafirai tun da suka ga an dauke gawar ukasha an tafi da ita sai gaba dayan su suka kamu da tsananin tausayi kowa jikinsa ya kara yin sanyi bisa ganin yadda ake tsantsar adalci irin wanda sarkin su bai taba kamantawa ba. Da yawansu sai suka kama kwallah wasu ma har sai da suka zubar da hawaye. Suma sauran dakarun musulmi da yawan su suna ta kuka saboda tausayi da ganin karamcin da sarkin su ya nuna. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai aka ga WSU daga cikin rundunar kafirai suna fara zubar da makamansu a kasa kuma suka rinka tahowa wajen sarki uwaisul karni suna durkusawa a gabansa suna cewa, muzo mu yi mubaya'a a gareka. Tabbas wannan addini naku shine addinin gaskiya. Kafin anjima kaso biyu na kaso ukun dukkan dakarun kafirai sun hallara a gaban sarki uwaisul karni kuna sun durkusa masa suna kuka suna cewa sunyi imami da addininsa. Koda ganin wanann al'amari sai sarki uwaisul karni da jama'ar sa suka cika da tsananin farin ciki. Wadancan jama'ar kuwa da suka ki karbar addini sai suka zaburi dawakansu da gudu suka gudu daga filin yakin suka bazama izuwa cikin daki ba tare da sanin inda suka dosa ba domin sun san cewa idan suka tsaya dukkanin su sunansa gawa. Ana cikin wanann farin ciki ne wani badakaren sarki uwaisul karni ya rugo da gudu izuwa gareshi ya fadi gabansa yana mai haki yace, ya shuganana danka ukasha bai mutu ba dogon suna yayi sakamakon jinin da ya duru a jikinsa. Yanzu haja ya farfado kuna ana kan yi masa magani a cikin tantin dan uwansa. Koda jin wanann batu sai sarki da sauran jama'ar sa suka rude da kabbara cikin tsananin farin ciki nan take sarki ya hau dokinsa ya zabureshi izuwa inda tantin ukasha yake. Da Isar sa aka ruke masa doki ya sauka saban ya shiga cikin tantin inda ya iske ana gasa dukkanin jikin ukasha da ruwan dumi don magance kumburi kuma ana sa masa magani. Ukasha ya juyo da fuskarsa izuwa kofar shigowa cikin tantin. Koda yayi arba da saki sai ya yi murmushi a gareshi yace Madallah da mahifi mai matukar kaunar dansa. Ya kai Abbana hakika kayi mini babban gata a wanann duniya da kasa aka yi min hukunci bisa zunubin da na dauka. Inda ka barni da zunubina kuna na mutu a haka da na rasa lahirata. Ina mai neman gafara a gareka bisa bijire maka da nayi kuma inaso ka roka min Allah ya yafe mini laifin da na aikata. Tabbas na yi nadama kuma nayi bakin ciki matuka. Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarki uwaisul karni yaje ya zauna a gefen shimfida da ukasha ke kwance da ruf da ciki. Aji kuwa ukasha sai ya mike zaune da kyar cikin matukar karfin hali suka rungume juna kuma suka fashe da kukan farin ciki a lokacin guda. A sannane likitan dake duba ukasha tare da wasu dakaru biyu da ke cikin tantin suka fita suka barsu su biyu kadai. Tsawon lokaci sarki da ukasha suna manne da juna. Daga can sai sarki fuskanci juna yace, ya kai Abbana kayi sani cewa da zarar na sami lafiya da kwarin jikina zan ci gaba da tayaku yaki da wadannan abokan gaba namu. Yanzu ina dan uwana uzaifa? Sarki yace, ai tuni dan uwanka ya tafi izuwa birnin shumbul shi kadai domin ya ceto rayuwar jama'ar mu da aka tsare a kurkuku da kuna rayuwar Luhaira da sarki sha'aran ya tsareta a gidan gona. Koda jin wanann batu sai hankalin ukasha ya dugunzuma yace, ai kuwa bai kamata ka barshi ya tafi shi kadai ba domin masifun da zai tarar ba kadan bane abune mawuyaci ya tsira da rayuwarsa har ya sami nasara. Ina so ka sani cewa a yanzu haka sarki sha'aran da yar sa sazirat sun tafi izuwa can birninmu domin au cimu da yaki kuma su sato mahaifiyata daga kurkuku da kasa aka tsareta. Babu mamaki yanzu haka wanann bukata tasu ta biya. Ni kam yanzu bani da sauran kwanciya hankali face na bi dan uwana izuwa birnin shumbul domin na san halin sa yake ciki, idan har ya na raye sai na taimaka masa bisa aikin da yaje yi, idan kuma na iske sun hallaka shi na rantse da darajar ubangijn ubangijn musulunci sai na Karar da mutanen birnin gaba daya na baje birnin ya zama kasa yadda har abada ba za'a sake tunowa dashi ba. Saadda ukasha yazo nan a zancensa sai sarki uwaisul karni yayi murmushi yace, ya kai dana ka sani cewa babu yadda za'ayi au sarki sha'aran su iya shiga cikin birninmu har su cimu da yaki muddin ba a tone wanann sirrin ba dake Kar kashin katangun mu hudu. Dama kai kadai ne zaka taimaka musu su cimma wannan nasara kuma gashi yanzu kaima ka gane gaskiya ka gaujesu. Dan gane da al'amarin dan uwanka zasi jiya da daddare an nuna mini halin da yake ciki ya hadu da wani jarumin musulmin aljani wanda yake taimakon sa kuma sun shiga cikin birnin shumbul har sun musuluntar da wani hadimin sarki sha'aran wanda yayi musu jagora izuwa gidan kurkukun birnin. Sun yi yaki sun sha wahala kuma suna kan wahala domin har yanzu basu damar shiga cikin kurkukun ba bare su isa inda aka tsare jama'a mu su kubutar da su. Tabbas an nuna mini cewa suna cikin mawuyacin hali. Kai yanzu gashi baka da lafiya dole ne ka yi jinyar jikinka ta tsahon kwana uku wanann karbi bayan dan uwanka ka kai masa dauki. Ni kuma a ghobe zan yi shiri na koma can gida domin naga halin da mutane na ke ciki. Duk da cewa ina da yakinin cewa birnin bazai shigu ba ai hankalina ba zai kwanta ba har sai naje na iskesu lafiya. Lallai a gobe da safe bayan na gama musuluntar da jama'ar nan da suka yi imami da addinin mu zan tafi. Wai shin yanzu kana da labarinka lafirat yar sarki sha'aran wacce ta baiwa dan uwanka hadin kai wajen ganin an kawar da mahaifinta. Koda An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 21 of 21