barci mai gaske, sannan kuma wata sarka ta tsafi ta kanannade jikinta gaba daya.
Cikin sauri sarki shaaran ya kira sunan wani aljani waishi muruzul kurbaz.
Kawai sai kasa ta stage aljanin ya Faso ta ciki ya baiyana a gaban shaaran yana mai sujjuda a gareshi.
Girman aljani muruzul Kurabz ya kai a cure giwaye goma a wajen guda sannan ya na da fuka fukai goma sha hudu manya manya a jikinsa.
Baiyanar aljani muruzul kurbaz ke da wuya sai ga sazirat ta shigo cikim tantin.
Koda taga yar uwarta Lafirat kwance a gefe daya, kuma a daure cikin sarka sai ta cika da tsananin Farin ciki ita da mahaifinta.
Sarki shaaran ya dubi aljani muruzul kurbaz yace maza ka daukemu ni da yata sazirat ka kaimu can kusa da kofar birnin Darul husuf domin mi cisu da yaki kuma mu sato muzaira.
Koda jin wannan umarni sai aljani muruzul kurbaz ya risina cikin biyaiyya yace, an gama ya shugabana.
Nan take ya rankwafa sarki shaaran da sazirat suka hau kansa suka zauna. Kawai sai ya bude fuka fukansa y luluka izuwa can kololuwar samaniya ya bace bat, a cikin gajimare.
Sarki shaaran da sazirat na kyalkyala dariyar Farin ciki.
Abinda basu sani ba shine, ukashat bai tafi can birnin Darul Husuf ba domin tono layun nan guda hudu.
Yanzu haka yana can a tsare a hannunsu sarki uwaisul karni.
Kuma wannan wasila bashi ya rubutata ba uzaifat ne domin kawai yaja hankalinsu su zata cewa ukashat na kan cikinsa.
A halin yanzu tini uzaifat ya tunkari birnin shumbul domin yaje ya kubutar da rayuwar jamaar su da a tsare a kurkuku da kuma rayuwar Luhaira yar likita abu sharhaz.
A dai-dai Nan littafi na uku ya kare, marubucin ya ce mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI na hudu don Jin yadda zata kaya tsakanin Uzaifat a birnin Shumbul..
Najibullah Muhammad with Umar Farooq ke cewa ku huta lafiya ✍️✍️👆👆👆
**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA HUDU 4 ✅
PART A 👌
MARUBUCI :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing:- Umar Farouq Zango
Posting:- Najibullahi Muhammad 🥷🥷
Marubucin ya ci gaba da bada labari kamar haka :-
* * * * * *
Tafe yake akan doki yana ta keta daji, ba tare da fargabar komai ba tamkar a cikin gidansa yake rangadi.
Gashi dai daji ne mai yawan sarkakiya da yawan duhuwa amma shi gogan naka ko kadan babu alamar tsoro a tare da shi.
In ka dauke dai daikun kukan tsuntsaye masu shawagi a sama da kuma wadanda ke saman bishiya gami sa kukan manyan dabbobin daji ababan tsoro wanda ke ta amsa kuwwa daga nesa babu wani sauti da ake ji a cikin dajin.
Haka dai yarima uzaifat ya ci gaba da tafiya a cikin wannan daji ba waige ba sassautawa har tsawon sa'a uku ba tare da ya hadu da wani mugun abu ba. Babu abinda ya sa shi Farin ciki face ganin yadda dokinsa ke ta tafiya ba tare da ya nuna alamar gajiyawa ba.
Shi dai wannan doki wanda uzaifat ke tafe akansa ya kasance fari sol gwanin ban shaawa kuma kosasshe babu tabi ko daya a jikinsa.
Dokin yana jin karfi a jikinsa tamkar idan aka daura masa keken doki komai girmansa zai iya jansa shi kadai.
Babu abinda zai burge mutum face irin yanayin tafiyar dokin cikin sassarfa da tafiyar kasaita tamkar dan sarki.
Idan kuwa yana gudu shi kansa uzaifat ji yake kamar ba akan kasa suke ba a sararin samaniya ake tafiya saboda tsananin gudun dokin domin idan ya daga kafafunsa na gaba duk inda ya diresu sai kaga tazararsu da kafafunsa na baya ya kai zirai goma.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai uzaifat ya hangi dandazon wadansu bakaken birirrika jibga jibga a gabansa wadanda adadinsu ya kai dubu uku. Tun daga nesa uzaifat ya fara jan linzamin dokinsa yama rage masa karfin gudu.
Shi kansa dokin sai da ya firgita ya fara turjiya yana son ya koma da baya amma sai uzaifat ya masa dole yana dada dannashi gaba.
Lokacin da dandazon bakaken birirrikan suka ga uzaifat ya tunkaro inda suke kai tsaye ba tare da fargabar komai ba sai suka cika da mamaki domin sama da shekaru talatin baya duk halittar data shigo cikin dajin indai tayi arba da su sai ta firgita komai karfina da girmanta.
Uzaifat ya ci gaba da tunkarar birirrikan harya zaman cewa tsakanina da su bai wucekamu arbain ba amma bau razana ba kuma bai yi wani yunkurin zare makami ba kwai gabansa yake kallo.
Dokinsa ne kawai yake yar tirjiya da haniniya alamar ya firgita amma saboda babu yadda zaiyi dole ya ke ci gaba da tunkarar birirrikan.
Koda yazo daf da su sai suka dare suka bashi hanya a tsakiya.
Koda ganin haka sai uzaifat ya sha jinin jikinsa yayi zargin lallai zasu iya shirya masa wani mugun tuggu.
Birirrikan suka tsaya cak, kamar gumaka babu abinda yake motsi a jikinsu face idanuwansu da suka zuba akan uzaifat suna lura da dukkanin motsinsa.
Kawai sai uzaifat ya dora hannunsa guda akan kotar takobinsa yaci gaba da kallon birirrikan da wutsiyar idanunsa jira yake kawai yaga dayansu ya yayi wani yunkuri ya zare takobinsa ya kare kansa.
Uzaifat yaci gaba da kutsawa ta tsakiyar birirrikan har ya iso tsakiyar su ashe lambo suka masa suna son suyi masa rubdugu su dada masa wawa kowa ya yagi rabonsa.
Yana zuwa tsakiyar birirrikan sai gaba dayansu suka dako tsalle a sama zasu yanyameshi shi da dokinsa su yayyagasu.
Cikin zafin nama uzaifat ya zulle ya daka tsalle ya shallakesu, dayansu bai sami damar lakutar jikinsa ba suka dasawa dokinsa wawa.
Kaico! Idan mutum ya ga yadda birirrikan suka yi kaca kaca da dokin sai ya zub da hawaye idan mai tausayi ne domin nan take suka yagalgalashi suka yi filla filla da sassan jikinsa tamkar a mahauta aka gididdibashi.
Shikuwa uzaifat a sama yayi alkafira ya dira can gefe daya bisa kafafunsa.
Koda ya ga yadda birirrikan suka yiwa dokinsa sai ya fusata ainun bai san saadda ya kwalla kabbara ba ya falfala da azababben gudu izuwa kan birirrikan.
Tun kafin ya isa kansu suma suka rugo gareahi aka runguntsume da azababben yake.
Nan fa birirrikan suka rinka kai masa sara da suka da faratan hannayensu.
Shikuwa ya wanzu yana mai karewa da maida martani.
Shi kadai ya zame musu alakakai domin an rasa wanda zai taba jikinsa shima kuma ya kasa taba jikinsu domin duk saadda ya kai musu jari sai yaga sun kare da hannayensu yaji tamkar karfe ya sara har tartsatsin wuta ne ke tashi.
Sai da aka shafe lokaci mai dan tsawo ana wannan gumurzu sannan uzaifat ya gane cewa a hannu ne kadai basa jin sara da suka don haka suka ki yarda ya taba sauran jikinsu.
Su kansu birirrikan sunyi mamakin irin juriyar uzaifat da nacinsa to amma sun fuskanci cewa na da wani lokaci zai iya gajiya su sami lagonsa.
Shi kansa uzaifat ya fahimci hakan saboda haka sai hankalinsa ya dugunzuma yafara tunanin mafita domin idan ya bari aka kai wannan lokacin tasa ta kare.
Nan dai uzaifat ya nemi dabara ya rasa tamkar an kulle masa kwakwalwar sa.
Haka aka ci gaba da wannan gumurzu har tsawon rabin sa'a a sannane uzaifat ya fara gajiya.
Koda ganin ba'a sai babban cikin birirrikan ya shammaceshi ya mangareshi da hannunsa a fuska ya kife kasa saboda karfin mangarin sai da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa.
Koda birirrikan suka ga uzaifat yaje kasa sai suka yi caa! Akansa zasu yi masa rubdugu kamar yadda suka yiwa dokinsa.
Bazato ba tsammani sai sukaji uzaifat ya kwalla kabbara da karfi a karo na biyu amma wannan lokacin sai ya kara da kirawo sunayen Allah tsarkaka yana mai neman taimakonsa. Ai kuwa nan take yaji wani irin gagaruim karfi ya shigeshi.
Tamkar sifirn haka yayi wata irin tasowa yayi fanka da kafafunsa a tsakiyar birirrikan ya tarwatsa su kuma ya hausu da sara cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance. Sai gashi yana gididdibasu.
Nan fa jini ya rinka feshi daga jikinsu yana malama a kasa amma abinda ya firgita uzaifat shine duk sa irin wannan mugun sara da yake musu basa faduwa kasa saboda bakin naci da Taurin rai, a hakan suka ci gaba da kai masa mun anan hare hare har suka fara yi masa rauni sai dai duk da hakan su. Kasa kai shi kasa domin shia ya nuna juriya da naci.
Da kyar uzaiuya shammaci wani daga cikinsu ya fille masa kai. Nan take birin ya kife kasa matacce.
Cikin razana gaba daya birirrikan suka ja da baya domin a sanin su tunda sarki shaaran ya kawosu wannan dajin su dubu uku dayansu bai taba mutuwa ba sai yau.
Kai asalima kaifi da tsini basa tasiri a jikinsu amma yau gashi mutum daya JAL yazo ya sassareau jini ya zuba a jikinsu har ma ya kashe dayansu.
Tsawon shekaru talaitun da zaman su a cikin dajin sun fafata da mayaka fatale da sauran ayarin mutane masu gifta wa masu yawan gaske suna yi musu kisan gilla ba taba samu wanda ya taba yiwa dayansu koda rauni ba.
Sai da aka shafe dakika dari da sittin ana wannan kallon kallo tsakanin birirrikan da uzaifat a wannan kari na biyu.
Su suna tunanin yadda zasu iya hallaka shi farat daya shi kuma yana tunanin yadda zai iya ci gaba da fille musu kawuna domin ya karar da su da wuri don kada su ci gaba da yi masa raunika har fa kai cewa biri ya fara dibarsa sakamakon jini da ke zuba a jikinsa.
A yanzu haka rauni hudune a jikinsa. Daya a tsakiyar kirjinsaaka yanke shi da kaifin farce wajen ya dare tamkar da takobi aka yankeshi, jini na diga.
Daya raunin gadon bayansa ne, daya a cinyarsa ta hagu, daya kuma a damtsen hannunsa na dama wanda ke rike da takobi.
Hakika in ba don uzaifat ya kasance na mijin kwarai ba mai tsananin juriya da tuno ya fadi kasa ya kasa ci gaba da yakin.
Shi kansa ya san cewa ba dabararsa bace ko hikimarsa ce ta kwaceshi face taimakon Allah.
Koda gama baiyana hakan sai ya ci gaba da yin addua a cikin zuciya sa yana neman Karin taimakon Allah.
Bayan birirrikan sun yi masa wannan kallo na tsawon yan dakiku sai shugaban su yayi wata irin kururwa mai ban tsoro ya doki kirjinsa da hannayensa biyu sannan ya rugo da tsiya cikin mugun nufi izuwa kan uzaifat su kuwa sauran birirrikan suka tsaya cak suna jira suga abinda zai faru.
Koda birin ya iso daf da uzaifat sai ya kai masa wawar cafka da hannu daya. Uzaifat ya sunkuya hannun birin ya cafki iska kawai sai uzaifat ya cafko hannun yasa takobinsa ya tsinike shi daga jikin kafadar birin.
Birin ya kwalla ihu ya durkushe kasa a lokacin da jini ya rinka bulbulowa da ga cikin kafadar birin tamkar idaniyar ruwa ta balle.
Maimakon uzaifat yayi jifa da hannun birin sai ya rike shi a matsayin garkuwa. Koda birirrikan sukaga abinda ya faru ga babban su sai suka yi kukan kura suka sake afkawa uzaifat gaba dayansu.
Nan fa aka sake ruguntsumewa da sabon yaki tamkar sannan aka fara. Uzaifat ya dinga kar harnisu da hannun birin kuma yana mai da martani da takobinsa.
Nan fa ya rinka gididdibasu yana yi musu illah domin wuyansu ya rinka datsewa, sai dai kaga kan biri yai sama ko kuna ya cire ya fado kasa. Haka dai uzaifat ya ci gaba da kashe birirrikan yana yi musu muguwar barnar ba sassauci babu alamar gajiya. Ba wani abune ya bashi wannan nasara ba face albarkacin wannan adduar da yaje ta karanta wa a cikin zuciyar sa.
Koda aka dan sake jimawa sai ya zamana cewa uzaifat ya kashe kusan birirrika dubu daya da dari takwas.
Yayin da birirrikan suka ga wannan muguwar barnar da uzaifat yayi musu suka tabbatar da cewa da Sannu zai karar dasu duka sai suka fara kokarin guduwa.
Har wasunsu na daka tsalae sama suna hayewa kan bishiyoyi.
Koda ganin haka sai uzaifat ya rinka kure musu gudu yana rafkewa har wadanda suka rinka hawa bishiyu kuwa, sai dak kaga uzaifat yana hawa kan bishiyoyin tamkar shima dan birin ne.
Haka yaci gaba da kashe birirrikan aman bai karar dasu ba sai bayan sa'a uku da rabi a sannane ya yanke jiki ya fadi kasa sakamakon jinin da ya zubar mai yawa a jikinsa da Kuna tsananin gajiya.
Lokacin da uzaifat ya farfado sai ya ga wani tsohon mutum tsugunne a gabansa yana mai kura masa ido.
Shi dai wannan tsohon mutum gaba dayan gemunsa da gashin kansa fari kal babu rats in baki ko guda daya. Kai ganin sa kasan cewa ya manyanta ainun.
Koda uzaifat yayi arba da tsohon sai ya firgita ya mike zaune zumbur ya ja da baya.
Tsohon yayi murmushi a gareahi yace, kwantar da hankalinka yakai uzaifat ibin uwaisul karni. Ka sani cewa ni ba mai cutarwa bane a gareka.
Cikin rashin yadda da alamun tsoro uzaifat ya dubi tsohon yace, wanene kai kuma yaya akayi kasanni?
Tsohon yai murmushi yace, ni ba mutum bane, sunana HURAISUL MARWAS. Na kasance babban da na sarkin musulmin aljani na birnin FARISA.
Ya kai uzaifat kayi sani cewa na dade ina yaso a duniya domin tabbatar da jihadi bisa tafarkin wannan addini namu na musulunci.
Na sha wahalar gaske a wadan su wiraren da dama wani lokacin ma kamar zan rasa raina amma ban taba da baya ba ko razana akan sharrin kafirai saboda nasan cewa koda na rasa rayu wata bani da asara tunda shahada na samu.
Ina so ka sani cewa ina da cikakken tarihi akan wannan birnin na shumbul da kake son ka shiga yanzu kuma akwai mugayen tarkuna da sarki shaaran ya shirya domin ku.
Tabbasa na san abinda kai baka sani ba kuma ina tabbatar maka da cewa idan ba ka sami taimakon Allah ba babu yadda za'ayi ka iya shiga cikin birnin shumbul har ka ceto rayuwar yan uwanka wadanda aka tsaresu a kurkuku da kuma rayuwar luhaira.
Hadarin da ke cikin gidan sarautar sarki shaaran ya wuce yadda duk kake tsammani.
Mu hadu a part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar Hikayar ✍️✍️✍️♥️🥰**DAKARUN MUSULUNCI**
Littafi Na Hudu 4
Part B ✅✅
Marubuci :- Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing:- Umar Farouq Zango
Posting:. Najibullahi Muhammad 🥷🥷
GORON JUMA'A 🤝🤝❤️❤️❤️
Saadda aljani Huraisul Marwas kurbaz yazo nan a zancensa sai uzaifat ya sake dubansa cikin alamun rashin yadda a karo na biyu yace, naji duk abinda ka ce, amma yanzu yaya za'ayi na gamsu cewa kai musulmi ne dan uwana ba yaudarata kake yi ba domin ka cutar da ni?
Koda jin wannan tambaya sai aljani Hiraisul Marwas yai Kalmar shahada yace, wannan ta isa hujja a gareka, shin ka gamsu dani yanzu?
Uzaifat ya gyada kai yace, na gamsu.
Huraisul Marwas yace, yanzu sai ka tashi mi ci gaba da tafiya domin mu isa da wuri dag da faruwar rana.
Koda jin haka sai uzaifat ya dubi huraisul Marwas cikon mamaki yace, menene zai sa mu bata lokaci mai tsawo haka ahalin kai aljanine zaka iya kaimu can a cikin kankanin lokaci.
Huraisul Marwas ya sake yin murmushi a karo na biyu yace, da kafafun mu zami wannan tafiya kuma abinda nake so da kai shine, ka yi iya kokarinka ka kare kanka daga sharrin duk abinda zai tunkaromu kuma duk irin halin da zaka tsinci kanka a ciki kada ka manta da Allah.
Ni dai bazan yi maka dakin komai ba sai dai nayi kokarin kare kaina kuma na nemi taimakon ubangiji, kaima haka za kayi mini. Wannan yana daga cikin dokar tafiyar da zamuyi ni da kai.
Doka ta biyu itace, duk abinda na ga za kayi komai kyau ko mara kyau ba zan hanaka ba kaima kuma bazaka hanani ba.
Doka ta uku wacce itace ta karshe, in dai muka yi gaba to fa babu komawa da baya koda kuwa mun tabbatar da cewa hallaka ce a gabanmu har sai mun si nasara abinda kazo yi cikin wannan birnin na shumbul.
Saadda aljani huraisul Marwas ya zo nan a zancensa sai uzaifat ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi yace, to yanzu menene amfanin yin wannan tafiya ni da kai tunda babu taimakekeniya a tsakanin mu?
Ni kawai ka kama hanyara nima na kama tawa kowa tasa ta fissheshi.
Koda gama fadin haka sai uzaifat ya mike tsaye ya karkade kurar jikinsa ya fara tafiya, a sannane raunikan jikinsa suka far yi masa radadi da zugi, ba shiri ya zauna a kasa dirhshan ya juya ya hada ido da huraisul Marwas kawai sai ya ga ya yi masa murmushi.
Uzaifat ya sunkui da kansa kas sanna ya kwanto da wata yar karamar haka a bayansa ya budeta ya fiddo garin magani ya shafa akan raunin nasa da ke kan kirjinsa, ya sake shafawa a cinyarsa da damtsen hannunsa.
Nan fa ya fara kokarin shafa maganin akan raunin dake gadon bayansa amma sai ya kasa domin hannun nasa yaki kaiwa baya.
Har ya dubi huraisul Marwas da nufin ya budi baki yace dashi ya taimaka masa ya tuna cewa akwai doka ta kin taimakon juna a tsakanin su, saiya kau da kai ga barin kallonsa, kawai sai ya daga kansa sama yace, ya Allah ka warkarmin da wannan ciwo dake gadon bayana da wuri wuri idan har jihadin nan da ma fito dominka ne.
Koda gama fadin hakan sai ya mike tsaye yaci gana da tafiya. Take huraisul Marwas ya bishi a baya suka nasa cikin daji.
Tun da suka fara tafiyar uzaifat yaji ko kadan baya jin zugi da radadin ciwan dake bayansa tamkar ma bai taba jin raunin ba.
Alamarin da ya mutukar bashi mamaki kenan domin sauran raunikan dake jikin nasa basu kai girman na gadon bayansa ba aman sun isheshi da ciwo har ji yake kamar bazai iya ci gaba da tafiyar ba domin ba karamin karfin hali yake ba.
Sai da suka shafe tafiyar rabin sa'a dai dai basu sake faduwa da wani mugun abu ba.
Kwatsam sai suka hangi rundunar wadan su mayaka kimanin su dubu arbain bisa wadansu irin manyan dawakai masu matukar kwarjini da ban tsoro irin wadanda bil'adama bai taba gani ba. Girman kowanne doki guda ya kai na giwa.
Abin mamaki shine, mahayan dake kan dawakan sun fi dawakan girma, tsawo da muni domin ba mutane bane, wadansu irin dodannine mara sa kyan gani kuma dukkanin su suna rike da mugayen makami iri iri, wani makamin ma ko a tarihi mutum bai taba jin labarinsa ba.
Lokaci guda dodannin suka wangame bakunansu mai kama da burmammiyar ganga suka yi gurnani mai kama da na gwaggon biri. Ba ma uzaifat ba shi kansa aljani huraisul Marwas sai da ya razana sakamakon jin wannan gurnani ya dan ja da baya.
Uzaifat da huraisul Marwas suka dubi juna suka yi ajiyar zuciya a tare, kai da gani kasan cewa duk su biyun sun firgita bisa ganin wadannan dodanni.
Huraisul Marwas yace, wadannan dodannine na masifa domin sara da suka baya tasiri a jikinsu kuma basa jin duka. Ta yaya ke nan zamu iya hallakasu mu wuce gaba?
Allah ne kadai ya sani, uzaifat ya baiwa huraisul Marwas amsa.
Nan take uzaifat ya fara kirawo sunayen Allah. Koda ya hada ido da huraisul Marwas sai ya fuskanci cewa shima adduauyake, domin yaga yana matsa bakinsa.
Abinda bai sani ba shine irin adduar da yake karantawa shima ita yake yi.
Lokaci guda duk su biyun suka ruga da gudu izuwa inda rundunar dodannin take. Kod dodannin suka hango su uzaifat sun durfafosu sai suma suka sakarwa dawakansu linzami suka sukwanesu cikin matsanaicim gudu.
Na da nan suka tayar da kura ta turnuke dajin gaba daya.
Koda kofaton dawakan nasu ya fara bugun kasa, sai kasa ta kama girgiza tamkar zata dare komai dake kanta ya rufta ciki, duwatsu suka kama girgiza, bishiyoyi kuwa suka rinka rangaji tamkar za su kakkarye, su zube kasa. Koda aka hade tsakanin dodannin da su uzaifat sai aka riguntsume da azababben yaki.
Gashi dai babu makami a hannun uzaifat da huraisul Marwas amma sai hannayensu suka zame musu makami suka kama dokin in doka tsakanin su da dodannin.
Duk saadda dodannin suka karci jikin su uzaifat da faratan hannunsu ko suka cijesu da hakoran bakunansu sai suji kamar dutse suka gwaguya.
Su kuwa su uzaifat duk dodon da suka nasa sai kaga ya baje a kasa sumamme, kuma nan take ya mace.
Cikin kankanin lokaci suka ragargaji dodannin suka bazar da sama da rabinsu. Uzaifat da aljani huraisul Marwas suka cika da tsananin mamaki bisa ganin irin gagarumin karfinda suka samu suke ta ragargazar wadannan dodanni domin bama dodannin ba hatta wadannan manyan dawakan nasu naushi daya suke yi musu su kife kasa.
Cikin abinda bai wuce sa'a daya ba suka gama ragargaje gaba dayan dodannin da kuma dawakansu ya zamana cewa babu guda daya da ya rage a tsaye.
Daga can kuma sai suka GHA gawarwakin dodannin da na dawakan nasu duk sun rugurguje sun ruburbushe sun zama.garu sannan wata irin iska mai karfi ta kwashe garin tai sama dashi ya balbalce a sararin sama.
Alamarin da ya sa su uzaifat suka gane cewa lallai wadannan dodannin da dawakan nasu duk na tsafi ne babu su azahiri.
Nan take uzaifat da aljani huraisul Marwas suka yiwa Allah godiya bisa wannan taimako da ya basu suka sami nasara akan wadannan halittun tsafi cikin kankanin lokaci.
Ba tare da bata lokaci ba su uzaifat suka ci gaba da tafiya suka durfafi birnin shumbul.
Bayan tafiyar rabin zango dai dai sai suka hango kofar birnin. A wannan lokacin yammaci ne sosai daf da gabatowar faruwar rana.
Abu na farko da ya matukar basu mamaki shine, babu kowa a kofar garin wato babu mai gadi ko guda daya sannan kofar garin a bude take wanwar ba arufe ba.
Cikin tsananin mamaki uzaifat da aljani huraisul Marwas suka tsaya suka yi cirko cirko kuma suka kallo kofar birnin sannan suka kallo kansu.
Uzaifat yace, ya kai dan uwana kayi sani cewa masu iya magana sunce, ruwa baya tsami banza.
Anya kuwa baka ganin cewa wani mugun farko ne su sarki shaaran suka shirya mana ba a cikin birnin nasu?
Ni a sanna babu yadda za'ayi ace an bar kofar gari a bude haka kawai sai dai idan akwai wani dalili kwakkwara ko kuma idan anci garin ne da yaki.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 21