Sa'adda kika kubutar da wadansu biladama daga cikin kejina.
Ki sani cewa, wannan karon idan kika sake aikata hakan ba azaba zan miki ba, zan murder miki wuya ne ki mutu, sannan na dafaki, na cinye namankk domin na huce takaici. Kinji abinda na fada ko bakijiba?
Jikin hirama na karkarwa tace, na ji baya ninka ya abbana.
Nan take suka dunguma su hudun suka nufi gida. Sai da sukayi tafiyar saa hudu, sannan suka iso gidan nasu, wanda ke can sama bisa wani dogon tsauni da ake wa lakabi da hulasul maut.
Ba komai ne yasa ake kiran wannan tsauni da suna hulasul maut ba, face tsananin tsawon sa da fadinsa, domin tua ninka tsaunin dajin mashaarul kais sau uku.
Wani abin alajabi da ya faru shine, a cikin rabin saa maridi zurkas da iyalansa suka gama hawa kan tsaunin suka shige cikin wani katon gida, wanda aka ginashi da zallan itatuwa. Da shigarsu cikin gidan, sai zurkas ya ajiye wannan keji a kasa gefe daya da yake duhu ya soma sai maziba ta kunna fitilun da ke gidan ya haska ke gaba daya.
Su hudun suka zo suka zauna bisa wadansu kujeru domin su huta, dama tun kafin su tafi maziba ta tanadi abinci da ruwan shansu. Man take suka ci suka sha sannan aka shiga tattaunawa akan yadda za a cinye wadannan bakin biladama da aljanu da aka tsinto tamkar dami a kala.
Zurkas ne ya fara magana, ya dubi maziba yace, yake matata Yanzu yaya kike zamu farada wannan naman da muka sami. Shin biladaman zamu farka cinyewa, ko kuwa aljanu? Kinga dai aljanu ne masu yawa zamu iya yin kwana uku muna cinsu, idan muka rabasu gida uku, su kuwa biladama su ukune rak, ko ni kadai aka bar min su kwadayi zasu tayar min.
Kafin maziba ta budi baki ta bada amsa, sai Hirama ta tari numfashinta tace, ai kuwa a fara yi mana dabge da wadannan aljanu kowa yaci ya more, kusan munci nama sosai, inyaso bayan kwana ukun ku dafa biladama kuci abinkj ku uku ku raba dai dai tunda dai ni bana ci.
Koda jin haka, sai zurkas yace, gafara can shashasha, ya za ai mu fara cin nama mara dadi, sannan muzo muci mai dadin da ga baya?
Maziba tace, A'a maigida yarinya fa tana da gaskiya. Ai idan muka fara cin mai dadin, to daga baya muna fara cin mara dadin sai muji ya gunduremu. Shawararta ya kamata mu dauka.
Zurkas yayi tsaki cikin alamun rashin jin dadi yace, to ai shikenan tunda kema kin yarda da hakan.
Duk wannan hira da ake tsakanin zurkas da iyalansa ashe Lafirat tana ji, domin tuni ta dade da farfadowa daga dogon suman da tayi. Koda taji shirin da akayi a Kansu, sai hankalinta ya dugunzuma ta fara kokarin amfani da karfin sihirinta domin ta bude kejin su fita, amma sai sihirin yaki yayi tasiri. Lafirat taci gaba da kokarin tashinsu Uzaifat daga baccin amma sai ta ga sun ki motsawa tamkar sun zama gawa. Al'amarin da ya mutukar kara dugunzuma hankalinta kenan, ta tabbatar da cewa suna cikin mugun yanayi.
A wannan rana dai har dare ya raba sosai Lafirat batayi bacci ba saboda tsananin tsoro, fargaba da tunani, kuma har a sannan babu wanda ya farka daga bacci daga cikjn su Uzaifat basu san ma halin da ake cikiba.
Ita kadai ce a cikin tashin hankali. A wannan lokaci ne nadama tazowa Lafirat, tace Kash! Ina ma na karbi addinin musulunci tuntuni, da yanzu na nemi taimako a wajen ubangijin musulunci ya tserar da mu daga cikin wannan mugun hali. Kawai sai wata zuciyar tace da ita, to ai karbar addinin musulunci ba wani abu bane face ki biya Kalmar shahada.
Har Lafirat ta yumkura zata budi baki ta karanta Kalmar shahada, sai taji wata irin iska mai sanyi ta bugeta takaita kas. Nan take ita ma ta kama barcin dole. Ashe maridi zurkas ne ya buso mata wannan iska kawai sai ya dubeta ya tuntsire da dariyar mugunta yace, wane ke ki ce zaki katse min shirin? Ai tabbas sai mun cinye ku da dai dai kamar yadda muka tsara.
Kashe gari kuwa da sassafe, maridi zurkas ya bude kejin ya debo yayan uwar mayu guda dari biyar ya daddatsa su kamar yadda ake gididdiba nama a mahauta, sannan ya zuba su duka a cikin wat katuwar tukunya K hau dafasu.
Sai da aka shafe sa'a ukucur ana dafa nama ya zamana cewa, yayi luguf luguf sannan maziba ta raba nama izuwa kashi hudu kowa aka bashi nasa rabon.
Koda aka bawa hirama nata rabin, sai ta karba ta mike tsaye ta koma can cikin dakin ta zauna ta faraci.
Tana cikin cin abincin sau idanunta suka ciko da kwalla ta farazubar da hawaye. Ba komai ne yasa hirama zubar da hawaye ba, face tsananin tausayi da takaici.
Nan take zuciyar hirama ta kama tafarfasa kamar zata kone , kawai sai ta aiyana a ranta cewa, komai rintsi da tsanani, kuma koda zata rasa rayuwarta sai taceci wadannan halittu aje cikin wannan keji a daren yau, lallai bazata bari a sake cinye daya daga cikinsu ba.
Alhamdulillahi nan muka kawo karshen wanann littafi na DAKARUN MUSULUNCI littafi na biyu Insha allahu ba da dadewa ba zaku jimu da cigaba a cikin littafi na uku.
Muna fatan Kun ji dadin wannan littafin.
Umar Muhammad zango &
Najibullah Muhammad ke maku fatan Alkhair✍️✍️🙏🙏♥️
**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA 3
PART A
NA:Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing Umar Farouq Zango.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷
Idan zaku iya tunawa a littafi na biyu marubucin ya tsaya a inda hirama take tunanin yadda zata iya fitar da su Uzaifat da uwar mayu da sauran yayanta daga cikin kejin da Maridi zurkas ya sa su. To Insha Allahu zamuji yadda zata kasance a cikin littafi na uku, ku biyoni muje.
Marubucin yaci gaba da cewa
Lokacin da Hirama ta aiyana a ranta cewa komai rintsi sa tsanani sai ta kubutar da rayuwar su lafirat sai gaba daya taji wannan abinci ya fita daga ranta don haka sai ta sa kamarta ta ture kwanon gaba daya har ya bingire.
Tsam! Ta koma shimfidar ta ta kwanta tayi lami tana mai rufe idanunta tamkar barci take yi. A dai dai lokacine dan uwanta Hiram ya shigo cikin dakin.
Koda ya ga hirama ta zubar da nata abincin ko rabinsa bata cinye ba, sai ya kama kyalkyala mata dariya.
Nan take ya dauki ragowar naman ya cinye yana cewa, yarinya kin bar lagwada ta wuceki. Mu kam bazamu bar wannan dadi ba. Lallai zamu kwana biyu muna walima.
Gama fadin hakan ke da wuya sai shima Hiram ya koma kan shimfidar sa ya kishinguda.
Ba dade da kwamciya ba kuwa shima barci ya kwasheshi.
Hirama dake kwance a can gefe daya tayi lami duk tana kallon sa kawai tana ta sake saken zuciya da kuma tunani da fargaba sun cika mata rai.
Abinda ya fara fadowa ran hirama a rai shine ta yaya zata iya ceton rayuwar su lafirat alhalin zurkas da maziba na nan.
Kai bama su na ko dan uwanta Hiram ba zai barta ba.
Wata zuciyar tace da ita, to me zai hana ki bari sai dare ya raba sunyi bacci sannan ki sadada Kije ki bude kejin da aka zuba wadannan biladama da aljanu ki kubutar da rayuwar su ina taso ki bisu ku tafi tare kema ki hakura da rayuwa da iyayenki da yan uwanki har abada.
Koda aiyana haka sai zuciyar hirama ta buga da karfi sosai sakamakon tunowa da yanayin yadda kofar kejin take.
Ita dai kofar kejin ko tabbata kayi sao tayi kara, saurin Karar ya cika codon kunne don haka duk irin bacci da zurkas da maziba ke yi da zarar an taba kofar wannna keji sai sun farka.
Hirama ta tuna cewa shi kansa dan uwanta Hiram ba karamin matsala bane a gareta domin idan dare yayi ana rufe kofar wannan daki da suje kwance kuma ko yaya ta mike tace zata je ta bude kofar dakin sai tai motsinta da zarar yaji motsin kuwa sai ya tina mata asiri.
Lokacin da Hirama tazo nan a tunaninta sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, nan fa ta sake afkawa cikin sabon kogin tunani.
Bayan ta jima tana tunani sai hawaye ya sake zubo mata sakamakon mugun nufin da ya fado mata arai wanda shine kadai mafitarta idan har tanaso ta cimma wannan buri nata na kubutar da rayuwar su Uzaifat.
Ha dare ya fara rabawa hirama idanunta a bushe suke bata rintsa ba kuma zuciyarta sai faman sake sake take.
Tana cikin wannan hali ne Zurkas da maziba suka shigo cikin dakin suna magana sai tayi sauri ta ruf da ciki kuma ta rufe idanunta tayi kamar ta dade da yin bacci har da Jan dogon munshari kamar yadda dan uwanta Hiram ke yi.
Dama zurkas ne akan gaba rike da fitilar. Maziba na biye da shi.
Kai tsaye zurkas yaje kan Hirama ya tsaya ya dallare fuskar ta da fitila domin ya tabbatar da baccin take ko kuwa lamo tayi.
Bisa mamaki sai yaga idanunta basu motsa ba kuma gashi tana Jan dogon munshari.
Kawai sai yayi murmushi ya dubi maziba yace, nifa ban yarda da wannan yar taki ba domin gani nake zata iya haintarmu a ko yaushe tayi mana nasarar wannan da muka damu.
Kodajin wannan batu sai Maziba ta bushe da dariya ta dubeshi tace, Haba mai gida ta yaya Maziba zata iya kubutar da wadannan fursunoni namu ba tare da muji motsinta ba.
Kai kafin ma ta bude kofar wannan daki nasu ta fita na tabbata dan uwanta Hiram yaji motsinta. Ka san kuwa yana jin motsinta zai tona mata asiri.
Kai koda ma baiji motsinta ba tayaya zata iya bude kofar wannan keji ba tare da mu muji motsinta ba.
Na rantse da darajar auren mu idan kuwa tayi wannan ganganci ni da kaina zan yi mata kisan gilla sannan na dafeta tayi luguf mu cinye namanta don mu huce takaici.
Zurkas yace, Haba ai idan kika kasheta farat daya Mun yi mata adalci ma.
Ai tana ji tana gani da ranta zamu daurewa tamau sannan mu dinga yankar sassan jikin ta da kadan kadan muna cinyewa har akai munzalin da zata mutu a haka.
Yanzu dai sai kj zo mu koma can dakin mu mu fara cin naman.
Ni anya ma kuwa yau zanyi barci saboda murnar wannan garabasa da muka samu?
Maziba ta bushe da dariya tace ai yau batun bacci ma babu shi kwana zamuyi muna rakashewa ni da Kai.
Irin soyayya da muka yi tun a daren farkon auren mu sai mun maimaitata a yau.
Koda jin wannan batu sai zurya maziba ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya kama hannunta suka fice daga cikin dakin.
Sun fita sai zurkas ya rufe kofar dakin yasa wani katon kwado ta waje ya datse kofar.
Cikin mamaki maziba ta dubeshi tace, saboda me zaka rufe yaran nan ta waje.
Zurkas yace, nifa hankalina bai kwanta da wannan yarinya Hirama ba gani nake a koda yaushe zata iya haintarmu, gwara dai mu dauki kwakkwaran mataki akan ta.
Maziba tayi murmushi tace, kaima kana da gaskiya domin kuwa riga kafi yafi magani.
NAn take zurkas da maziba suka tafi izuwa nasu dakin suka Zauna suka hau cin naman su shan ruwan giya.
Da suka cika cikinsu sai zurkas ya dauko wata katuwar ganga tasa ya kama koda, ita kuwa maziba ta dinga tika rawa a gabansa suna ta kyalkyala dariya cikin farin ciki da annusuhuwa.
Da yaje dare ya raba sosai sai dajin gaba daya ya dinga amsa kuwwar dariyarsu da wannan koda.
Al'amarin Hirama kuwa, duk irin Hirar ta wakana tsakanin zurkas da maziba taji don haka bata san Sa'adda ta fashe da kukan takaici ba. Babu abinda ya bakntamata rai face yadda taji iyayen ta suna cewa zasuyi mata kisan gilla muddin tayi yunkurin tserar da rayuwar wadannan fursunoni.
Bayan hirama ta dade tana tunani da kuka sai dabara ta fado mata akan yadda zata fita daga cikin dakinsu ba tare da dan uwanta Hiram yaji motsinta ba.
Nan taje ta aiyana a ranta cewa lallai a cikin wannan dare zata fita kuma ta yanke don dukkanin kauna tsakaninta da iyayenta don haka yanzu wannan fita da zatayi ta sallama ranta ne ko tayi nasara ko akasin haka, amma babu gudu kuma babu ja da baya.
Ba tare da bata lokaci ba hirama ta mike tsaye tsam cikin sanda da lambo ta bude wata katuwar bakar akwatinta wadda take ajiye tarkacen ta a ciki ta fiddo wat yar karamar kwalba mai dauke da wani Jan gari a ciki.
Hirama ta bude kwalbar ta zazzaga garin kadan akan tafin hannunta.
Kawai sai taje kan hiram ta sa bakinta ta hurawa garin iska ya vade fuskar Hiram.
Faruwar hakan ke da wuya sai Hiram yaja dogon numfashi, bisa dalilin shakar wannan hodar gari sannan yaci gaba da bacci mai nauyi.
Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube hirama ta juya tanufi bakin kofar dakin nasu tasa hannunta ta zare sakatu biyu ta janyo kofar da nufin ta bude, sai taji kofar ta ko budewa.
Al'amarin da ya mutukar girgiza ta kenan kuma ya bata tsoro ta fahimci cewar an kulle kofar ta waje.
Nan fa hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ta shiga sabon tunani bisa neman mafita.
Tana cikin haka ne dabara biyu ta fado mata ta kama bangon dakin ta hau tana tafiya akansa kamar kadangaruwa har ta USA inda rufin dakin yaje wanda aka yishi da itatuwa da manyan ganyayen bishiya mai fadi.
Kawai sai ta sa hannunta ta zare itatuwa shida a hankali, sai ga wawakekiyar hanya a saman rufin daki.
Kawai sai ta zuro kanta cikin hanyar ta dubi gabas da yamma kudu da arewa bata ga kowa ba.
A wannan lokaci tana iya hango zurkas da maziba daga can nesa suna ta sharholoyarsu ta kida da rawa.
Cikin sanda hirama ta hau kan rufin saman dakin tana tafiya da ruf fa ciki har ta biyo saman katangar dakin ta sauko kasa tamkar kadangaruwa.
Tana dira kasa ta ruga bayanta wata bishiyar ta labe ta ci gaba da hangen iyayenta a wannan lokaci ne jikinta ya kama Bari saboda tsananin tsoro da fargaba saboda tasan cewa ko yaya asirinta ya tonu tata ta kare kam.
A rayuwar Hirama babu abinda jikinta baya so irin sanyi, kuma gashi a wannan lokaci ana wata irin iska mai sanyin gaske.
Nan da nan jikinta ya kama bari, bakinta ya kama rawa har hakoranta na sama suka gogi na kasa.
Karar haduwar hakoran nata ne ya baiyana a fili kuma a kunnuwan zurkas da maziba don haka sai suka tsaya cak! Ga barin kida da rawar suka kura idanuwansu suna kallon kowacce kusurwa.
Ita kuwa Hirama sai tayi sauri ta datse bakinta ta rukeshi GAM da hannunta a lokacin da taji tsoro ya kara dabaibayeta fiye da kowanne lokaci.
A wannan lokaci inda wani abu kanka ni zai dungureta ta baya zata iya sakin fitsari saboda tsananin razana.
Tsawon dakika sittin maziba da zurkas sun tsaya cak! Suna sauraro da kalle kalle basu ga komai ba kuma basu ji motsin komai ba face sautin gyare da ya cika dajin gaba daya.
Zurkas yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi maziba yace, nifa naji kamar motsin wank wani abu, bari naje na bude dakin yaran can na gani ko Hirama ce ke kokarin fitowa don ceton fursunonimu.
Koda gama fadin haka sai zurkas ya yunkura zai Mike tsaye.
Caraf! Sai maziba ta cafo hannunsa ta zaunar da shi tace, Haba maigida ai amfani hankali aiki dashi.
In banda abinka ta yaya Hirama zata iya fitowa daga cikin dakinsu alhalin muna hango kofar dakin nasu daga nan.
Ai yau anan zamu zauna mu ci gaba da hirarmu domin mu tabbatar da tsaro kuma mu Kawar da zargi har gari ya waye ko barci ba zamuyi ba.
Koda jin wannan batu sai zurkas ya bushe da dariya sannan ya rungume maziba suka kishingida a kasa ta kwanta bisa kirjinsa yana mai cewa, madallah da ke matata ma'abociyar jikina da basira.
Lallai kuwa yau ko rintsawa ba zamuyi ba, kawai mu ci gaba da hirarmu. Sa'adda hirama taji wannan batu sai hankalinta ya kara dugunzuma ainun ta tabbatar da cewa Yaufa tashi ga TSAKA MAI WUYA, domin bata isa ta sake motsawa ba daga inda take labe domin ko yaya ta motsa sai zurkas sunji motsinta tunda yanzu sun daina kisa da rawa bare wani abu ya dauke musu hankali, duk da cewa kuwa akwai yar tazara a tsakaninsu.
Haka dai hirama taci gaba da hangen su zurkas zuciyarta cike da tsoro da fargaba kuma tana ta tunanin mafita, amma babu har tsawon sa'a guda ya zamana cewa bata da sauran buri akan rayuwarta kawai sai ta rungumi kaddara ta ci gaba da jiran gari ya waye asirinta ya tonu iyayenta su hallaka ta.
Allah sarki, hakika ita hikima baiwa ce, kuma komai na duniya rabone. Shikuwa rabin kwado baya hawa sama, koda ya hau kuwa sai ya fado.
Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace mai rabon ganin badi sai ya gani.
Kwatsam! Bazata ba tsammanin sai hirama ta tuni da wannan garin hodar bacci dake cikin karamar kwalbar dake tare da ita.
Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI 3b Don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar Hikayar✍️✍️🙏👌**DAKARUN MUSULUNCI**
Littafi Na Uku 3
Part B ✍️
Na: Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing Umar Farouq Zango
Posting: Najibullah Muhammad 🥷🥷
Nana take ta dauko kwalbar ta budeta zazzaha hodar akan tafin hannunta sannan ta dauke numfashinta ta hira hodar da iskar bakinta.
Nan take hodar taji iska, kamshinta ya tafi har zuwa inda zurkas suke albarka cin iska mai karfi da take kadawa a cikin daren.
Koda zurkas da maziba suka shaku wannan hoda sai suka fara lumshe idanu suna cikin wannan hira tasu.
Basu ankara ba kuwa sai duk su biyun suka bingire suka kana bacci mai nauyi. Kafin ajima munsharinsu ya cika dajin gaba daya.
A wannan lokaci ne gagarumin farin ciki ya lullube Hirama ta fito daga inda take a labe ta ruga izuwa inda wannan keji yake ta bude kejin.
Koda ta ga fursunoni gaba dayansu a kwance suje suna ta shara baccin tsafi., sai hankalinta ya dugunzuma domin ba zata iya daukar su gaba daya ba.
Ta san dai zata iya daukar biladama guda uku amma bazata iya daukar uwar mayu da sauran yayanta ba.
Nan fa ta tsaya tana tunanin mafita nan take kuwa dabara ta fado mata ta ruga da gudu izuwa dakin mahaifinta zurkas inda yaje ajiye kayan tsafe tsafensa.
Da shigarta cikin dakin ta zubawa tarkacen tsafin idanu wadanda adadinau yafi dubu.
Wasu daga cikin kayan tsafin ma sari suke dole ta rinka tashen hancinta.
Kawai sai idanunta suka kai kan wata farar siririyar kwalba mai dauke da shurin gari a ciki.
Hirama ta kurawa kwalbar idanu nan take ta tuni da wata rana Sa'adda zurkas ke yiwa maziba bayanin amfamin wannan shurin gari, a lokacin hirama na labe a kofar dakin tana kallon su da sauraronsu basu sani ba.
Abinda hirama ta iya tunowa kawai shine, taji zurkas yana cewa.
Wannan hodar tana yin aiki casain da tara amma fa idan akayi aiki da ita bisa kuskure za'a iya asarar rayuka da duk wani abu mai tsiro daga cikin kasa a cikin dajin gaba daya.
Sa'adda Hirama ta gama wannan tunani sai kawai taje ta dauki wannan kwalbar ta fita da gudu ta koma can inda kejin yake.
Da zuwa sai ta fara dauko lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a ta sabasu a kafada tamkar ta saba gawa sannan ta busawa su uwar mayu wannan sbudin garin tsafi cikin yanayin tsoro domin duk jikinta kyarma yaje domin gani take kamar zata iya sauya musu kammani ko ta zamo sanadin ajalinasu.
Koda garin hodar ya basu akan uwar mayu da ragowar yayanta sai duk suka farka daga bacci a firgice suka yunkura zasu rafka ihu sai hirama ta zazzare musu idanu tana mai yi musu nuni da su nutsu.
Dama ita uwar mayun a nutse ta mike zaune tayi nazarin abinda ke faruwa.
Hirama ta dubi uwar mayu tace, abinda nake so daku shine, Yanzu zamuyi gudu iyakar marfinmu har tsawon sa'a shida, idan ba muyi haka ba lalli dayanmu ba zai tsira ba daga sharrin iyayena ba.
Koda gama fadin haka sai Hirama ta juya ta falfala da azababben gudu izuwa cikin daji tana dauke da Uzaifat.
Koda ganin haka sai uwar mayu da yayanta suka firfito daga cikin kejin suka yi koyi da hirama wato suma suka ZAGE DANTSE wajen yin gurin mutuwa, musamman ma da suka ga Hirama ta basu rata mai yawa wacce koda karfin tsafi ba su isa su cimmata ba.
Tun da uwar mayu tazo duniya bata taba gamin wata halitta nai karfin gudu ba kamar Hirama.
Iat ma uwar mayu ta zage damtse iya karfinta tana gudu har ta wuce dukkan yayanta da tazarar zira'i arbain amma da kyar take iya hango kurar uwar Hirama.
Kamar yadda hirama tayi bayani haja al'amarin ya kasance, wato sai da suka shafe sa'a shida suna tsala gudu amma har alfijir ya keto, rana ta fara budewa basu tsaya ba.
Uwar mayu da yayanta suna gudu suna haki kamar ransu zai fita, wani lokacin ma sai kaga yayan uwar mayu suna faduwa kasa amma saboda tsoron mutuwa sai kaga sun mike zumbur sun ci gaba da tafiya.
Lokacin da hirama ta iso karshen dajin huzurul has dai dai inda yayi iyaka da dajin cikin birnin shumbul, sai Hirama ta fadi kasa tana haki ta dauke Lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a a kasa a hankali ta zuba ido akan hanya domin ta ga isowar uwar mayu da yayanta.
Sai da ta shafe rabin sa'a a zaune tana kallon hanya amma ko alamun su bata hango ba.
Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinta kenan ta fara tunani cewa lallai iyayenta sun farka daga barcin sun biyo bayansu har sun cimma uwar mayu da yayanta.
Ba kamai ne yasa Hirama tayi wannan tunani ba ba face sanin cewa iyayenta da tsananin karfin gudu ninkin nata sau uku.
A Yanzu dai da ta iso wannan iyaka ta dajin huzurul has ta san cewa ita da su Uzaifat sun tsira daga sharrin iyayenta domin basu isa su ketara wannan iyaka ba saboda haja dokar tsafin zurkas ta shirya masa shi da matarsa maziba, amma banda yayansa.
Idan kuwa har suka yi gangancin haura iyakar nan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 21