Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
inda take zauneta taho gaban Uzaifat tatsaya tace, tabbas abinda uwar mayu ta fadi yanzu gaskiya ne. Uzaifat yace babu komai mu zamu ratsa ta cikin dazuzzukan biyu, kuma mu wuce a raye da izinin Allah. Uwar mayu tace, ya kai wannan gwarzon jarumi kayi sani cewa yau shekara arba'in da biyar kenan ina tare da mutane da aljanu a wanann daji ina kashesu da cinyesu. Lallai wannan aiki dana ai nata ba karamin zunubi bane don haka inaso na share zunubina da aikata aikin alkhairi saboda haka nima yanzu na sallama rayuwata bisa yi muku rakiya a cikin wannan tafiya har mu isa birnin shumbul. Idan Allah yasa kun sami nasara akansu kuma ni da ya'yana rayuwar mu, shikenan sai na cika burina. Idan kuma muka hallaka, ina fata mutuwarmu ta zamo sanadin samun rahama a wajen ubangijin musulunci. Koda jin wannan batu sai Uzaifat yaji kaunar uwar mayu ta shiga zuciyarsa, abu san Sa'adda ya rungume ta ba. ******""""******""**** Najibullah Muhammad *****""******''''""""******* Nan dai Uzaifat Abul shaja'a Lafirat da Uwar mayu da yayanta suka fice daga cikin gidan suka yi ta sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, ta kan wannan matattakala. Koda fara saukarsu sai gidan yaci gaba da rushewa yana neman zubowa kasa. Cikin hanzari suka ci gaba da saukko wa da gudu, aikuwa suna gama sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasa ta bace bat. Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka afka cikin dajin mashaarul Kais suka kama tafiya ba kakkautawa. Ai kuwa suna cikin tafiyar ne suka ga irin wadannan manyan tsuntsaye na ta shawagi a samansu, amma da zarar sunyi kasa kasa sunyi arba da Uzaifat sai suke yin sama su lulaka ba sa sake dawowa. Haka dai su Uzaifat suka ci gaba da tafiya, har tsawon kwana uku a cikin dajin mashaarul kais, duk inda dare ya riskesu, sai su yada zango zai gari ya waye, sannan suci gaba da tafiya. Da yake har yanzu Lafirat na fama da lalurar wannna rauni dake bayanta Uzaifat ne ya dinga goyata a bayansa a tsawon kwanaki ukun kuma wani iko na Allah, sai ta kamu da zazzabi mai zafi, har da kumallo, al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa kenan, musamman ma shi Uzaifat domin tattara hankalinsa yayi gaba daya akanta ya rinka jinyarta yana bata magunguna tana sha, kuma ya dinga dura mata abinci da hannunsa. Da yammacin kwana na uku ne zazzabin Lafirat yayi zafi ainun, har numfashinta ya dinga sarkewa, al'amarin da ya dimauta Uzaifat kenan, bai san Sa'adda ya fara a addu'a yana rokon Allah ya baiwa Lafirat lafiya ba. Ai kuwabai dade ba da fara addu'ar, sai Lafirat ta samu sauki, har ta bude idanunta ta dubeshi tayi masa murmushi. Nan take farin ciki ya lullune Uzaifat yaji kamar ya rungume Lafirat, amma sai ya kasa. Bisa mamaki sai Uzaifat yaga hawaye na zuba a idanun lafirat al'amarin daya mutukar bashi mamaki kenan, ya dubeta cikin karayar zuciya yace, yake Lafirat ina dalilin zubar wannan hawaye naki? A lokacin da Uzaifat yayiwa lafirat wannan tambaya babu kowa a kusa da su, domin Abul shaja'a uwar mayu da yayanta na can gefe daya. Abul shaja'a yana koya musu karatun alkur'ani. Yayin da Lafirat taji tambayar da Uzaifat yayi mata, sai tayi ajiyar numfashi sannan tace, ya kai gwarzona kayi sami cewa a rayuwata babu wani mahaluki daya taba nuna damuwa da kulawa a kaina sama da kai. Tsananin farin cikine yasa kaga ina zubar da wannan hawaye bisa ganin nuna kulawarka a gareni. Kai kuwa mai ya sa ka damu da rayuwata lhakin kasan cewa bazan iya yi muku komai ba acikin wannan tafiya? Aikina kawai shine na nuna muku hanya, to yanzu ma ga uwar mayu da yayanta ko babu ni su zasu iya nuna muku hanyar. Lokacin da Lafirat tazo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi shiru yana kallonta kawai ya rasa amsar da zai bata. Lafirat tace ya naga kayi shiru baka ce komai ba? Uzaifat yayi murmushi yace kiyi hakuri yake Lafirat domin a gaskiya yanzu bazan iya baki amsar wannan tambaya ba, amma idan lokaci yayi zan amsa tambayar, idan muna tare kuma muna raye. Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya mike tsaye ya kara gaba ya bar Lafirat a zaune tana mai binsa da kallo kawai cikin mamaki da wasu wasi. Ba komai taje wasu wasi ba, face wai shin wannan kulawar da Uzaifat ke nuna mata SO ne kk tausayi? Amsar da ta kasa baiwa kanta kenan. Yayin da Uzaifat ya baro wajen Lafirat sai yaje wajen su Abul shaja'a ya zauna yaci gaba da tayasu karatun alkurani izuwa wani lokaci. Bayan sun hatatama ne Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, Yanzu ya kakejin raunin kafarka? Abul shaja'a yace, ai na warke sumul, shin baka yadda na ke takawa ba sosai yanzu, ga shi ma na daina dogara ice. Uzaifat yayi murmushi yace, gaskiya ne amma ina neman alfarma mu kara kwana uku a nan domin ku kara samun lafiya sosai, kai da Lafirat. Koda jin haka, sai Abul shaja'a ya dubi Uzaifat cikin matukar mamaki, yace aini ma warke bana bukatar karin bata lokaci, sai dai saboda ita Lafirat din. Kuma ka tuna cewa, ita Lafirat babu wani abu da zata iya yi mana a cikin wannan tafiya face nuna mana hanya, ko babu ita Yanzu akwai uwar mayu da yayanta. Uzaifat yace nasan da hk, amma lallai nafi son sai Lafirat ta warke sumul sannan zamu rabu da ita a dajin karshe, bana son mu rabu da ita tana cikin lalura. Ka tuna cewa, ba don ita ba da tuni mun hallaka tun a baya albarka cin ta ne muka kawo izuwa matsayin da muke kai yanzu. Sa'adda Uzaifat yazo nan a zancensa, sai jikin Abul shaja'a yayi sanyi, bai kara cewa komai ba. Kamar yadda Uzaifat ya tsara haka al'amari ya kasance, wato sai da suka kara kwana uku a wannan wuri, sannan suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin zarsus. A wannan lokaci kuwa Lafirat ta warke sumul, karfin jikinta ya dawo sosai tamkar ma bata taba yin wata lalura ba. Sai da suka yi tafiyar sa'a shida sannan suka iso farkon dajin zarsus. Da zuwansu bakin dajin, sai uwar mayu da ke kan gaba ta daina kada fuka fukanta da karfi ta sauko kasa, kuma ta daga hannuna tana mai yiwa su Uzaifat nuni da su tsaya. Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka tsaya cak! Uwar mayu ta dubi gabas da yamma kudu da arewa, sannan ta shauki kamshi da hancinta, kawai sai ta juyo ta dubi su Uzaifat tace, akwai mugayen kunamai anan gabanmu kadan, don haka sai kowa yayi shirin tukararsu. Ina mai gargadinku dacewa, kada ku bi hanyar da kika ga babu sabar macizai akanta a cikin wannan daji, domin itace kadai hanyar da kunamai basa bi saboda a kaidar dajin kunaman da macizan basa faduwa a waje guda. Tunda dai yanzu banjiyo kamshi macizai ba, sai na kunamai, to mu ratse hanyar su mu bi ta macizai shine kadai hanyar da zamu it tsira daga sharrin su. Koda gama fadin haka, sai uwar mayu ta wuce gaba, yayata nabiye da ita sannan Lafirat ta bisu sai Abul shaja'a, Uzaifat ne a karshen baya. Dafara tafiyar tasu a cikin dajin na zarsus sukayi kicibus da wata katuwar sabar maciji wadda za'a iya nannade gaba dayansu a cikinta saboda girmanta. Koda ganin wannan sabar maciji, sai dukkaninsu suka cika da mamaki. Abul shaja'a ya dubi Lafirat yace, yake wannan yar sarki shu kuwa wannan maciji mai wannan saba wane irin girma ne da shi haka? Lafirat tayi murmushi tace ai girmansa ya wuce misali, da kamantawa sai abinda idanun ya gani. Na taba ji mahaifina yace, a duniya kaf irin wannan macijin guda uku ne rak, yanzu daya na can karshen bangon duniya, bangaren kudu. Dayan kuma a bayan birnin sin yake a cikin wani teku, baya fitowa saman tekun sai bayan kowace shekara goma, don ya shaki numfashi kawai. Ina jiye mana yin arba da wannan maciji domin karfin damtsen dana sihir ba zai kwacemu ba. Gama fadin hakan ke dawuya sai suka fara jiyo wani irin numfashi mai karfin gaske tamkar an yanka shanu dubu a lokaci guda suna kakarin mutuwa. Sannan suka rinka jiyo wani irin huci yana buso musu. Al'amarin da ya matukar razana su kenan, uwar mayu ce tafara juyawa da baya kamat zata ruga da gudu suma yayanta sai suka a da baya, haka ma Lafirat da Abul shaja'a. Uzaifat ne kawai bai firgita ba, kuma ko gezau Baiyi ba. Kawai sai ya zare takobinsa ya ci gaba da tafiya ya durfafi inda wannan huci ke fitowa. Nan dazuka rasa wanda zai bi bayan Uzaifat, duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko suna kallon juna. Daga can sai Lafirat tayi kundunbala ta bi bayan Uzaifat. Koda ganin haka, sai Abul shaja'a ya bita, sannan ne uwar mayu da yayanta suka biyosu. Sai dai Uzaifat yayi yar doguwar tafiya sannan ya tsaya yayi gurus bisa abin mamakin da ya gani a gabanku. Ba wani abu ya gani ba face wani narkeken maciji wanda tsawon sa da kaurinsa ya wuce kamu dari biyu. A wannan lokaci macijin ya hadiye wata narkekiyar kunama wacce girmanta yakai na babbar giwa. Kawai macijin yayi lamo a kasa ko kyakkyawan motsi baya iya wa saboda hadiyar da ya fara. Uzaifat ya tsaya cak! Yana kallon ikon Allah. Jim kadan sai ga Lafirat ta iso wajen, sannan Abul shaja'a da su uwar mayu. Da isowar uwar mayu ta ga saura kadan macijin ya gama hadiye kunamar, sai ta dakawa su Uzaifat tsawa tace, maza ku ruga da gudu mu bar wajen nan kafin ya gama hadiye wannan kunamar dan kanmu zai juyo ya yi loma daya damu. Dajin haka sai Lafirat, Abul shaja'a da yayan uwar mayu suka falfala da gudun kara gaba. Shikuwa Uzaifat sai ya daka tsalle ya hau kan jelar macijin ya fara tafiya a kansa tamkar ya hau kan katon tsauni. Sannan ya waigo ya dubi uwar mayu yace, idan ba zaki iya tsaya wa ba, ki kallo abinda zai faru ba kuma kiyi takanki. Koda jin haka sai uwar mayu ta dan ruga gaba kadan ta buya a cikin wata yar duhuwa tana leken a abinda zai faru. Uzaifat ya ci gaba da tafiya akan macijin har ya iso tsakiyar kansa. A dai dai wannan lokacine macijin ya gama hadiye wannan katuwar kunama, kuma a sannane Uzaifat ya daga takobinsa ya cakata a tsakiyar kan macijin. Kawai sai yaji kamar akan dutse ya cakata takobin, take ta karye gida biyu, macijin ya yunkura ya girgiza kansa yayi cilli da uzaifat tabayansa can gefe daya tamkar yafado daga kan dutse mai tsawon gaske. Kafin Uzaifat ya yunkura ya mike tsaye tuni macijin ya juyo da kansa baya ya kawo masa cafka baki bude zai hadiye shi. Cikin matukar zafin nama Uzaifat ya goce yana mai mirgina jikinsa gefe guda macijin ya hadiyi iska. Uzaifat ya mike tsaye da sauri ya falfala da gudu, aikuwa sai macijin ya sako kansa ya biyoshi suka kasa tsere. Babu abinda zai mamaki face tazarar da DAKARUN MUSULUNCI Littafi na BIYU PART F ( LAST Na: Abdul Aziz Sani Madakin Gini Typing Umar Farouq Zango Posting: Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 Cikin tsananin mamaki su Abul shaja'a suka karaso gaban su Uzaifat suka tsaya suna kallon gawar wannan narkeke maciji. Uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, tayaya ka sami nasara kashe wannan macijin? Koda ji wannan tambaya, sai Uzaifat ya nuna Lafirat da hannusa yace, ba nine na kashe wannan maciji ba, ga wadda takasheshi, kuma ina badon ita ba da tuni nima wannna macinjn ya hallakani. Itace ta kawo min agajjn gaggawa. Dan jin haka, sai Abul shaja'a, uwar mayu da yayanta suka sake cika da mamaki, suka kura mata idanu. uzaifat yayi murmushi yace, mamakin me kukeyi? Ai dama dujk tafimu jarumataka, kawai dai don ta sami rauni ne a jikinta saboda haka daga yanzu sau u daina tunanin cewa bata da amfani a cikin wannan tafiya tunda gashi tayi abinda ya gagareni. Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yayi murmushi yace, kaima ba gagararka yayiba, shaafa kayi baka nemi taimakon ubangijinka ba, wanda ya halicceka, kuma ya halicci wannan macinj da Lafirat ta kashe. Koda jin wannan batu, sai Uzaifat yayi murmushi yace, amma fa kaima ka shaafa da neman taimakon Allah domin bai kamata ka gudu kabarni ba a lokacin da nake artabu da wannan maciji. Abul shaja'a ya sunkui da kansa kasa cikin alamun kunya. Yace kayi gaskiya ya shugabana. Ina fatan zaka yafeni domin na yi babban laifi. Nan dai suka zauna gaba dayansu a bakin wannan kofi suka huta, a nan suka kwana sai da gari ya waye sannan suka muke suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin huzurhas inda tsafaffen maridi ke zaune tare da matarsa da yayansa guda biyu. Tafiya sannu sannu kwana nesa, sai da suka cika kwanaki goma sha bakwai daga ranar da suka fara tafiya sannan suka iso dajin huzurul has. Da isowar farkon dajin, sai uwar mayu ta daga hannuna tana mai nuni da cewa a tsaya dama itace akan gaba. Ba tare da gardamar komai ba kuwa kowa yabi umarnin ta aka tsaitsaya. Uwar mayu ta kalli gabasa da yamma kudu da arewa ta shaki numfashi, so tayi ajiyar zuciya, kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya dubeta yace, ya ke yar uwata yaya kika yi shiru baki ce damu komaiba? Uwar mayu ta sake yin ajiyar zuciya sannan tace, ya kai wannan dan sarki kayi sank cewa, wannan daji da zamu shiga shine mafi hadari daga cikin dazuzzukan uku daomjn a cikinsa ne tsafaffen maridi yake, wanda ake kira da suna zurkas. Maridi zurkas ya kasance narkeken katon da bazai kwatantu ba da baki, sannan yanada masifaffen karfi na Allah ya isa domin komai kwarin dutse idan ya nausheshi da hannu sai ya dagwargwaje. Kaifin ko tsinin basa tasiri a jikinsa. Zurkas na da karfin sihirin da idan ya bace babu bokan da zai iya ganinsa. Komai yawan rundunar mayaka shi kadai yana iya tarwatsa su. Shi ma shekararsa hamsin kenan a cikin wannan daji na huzurul has, tunda ya baiyana ya hana shiga da fita. Duk mahalukin da tsautsayi ya kawoshi walau mutum ko aljan ya zama gawa kenan. Lokacin da uwar mayu ta zo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke yar uwata ki yi sani cewa, babu wani abintsoro da zai figitani a cikin wannan tafiya, domin koyaushe ina sa ran cewa ubangiji zai fitar da ni daga cikin kowane hali. Shin ki manta ne cewa baya ma kin figitamu da labarin dazuzzukan da muka ratsa kafin mu shigesu, amma sai ga shi mun shige ta cikinsu, kuma sha gumurzu tamkar na zamu Kai labari ba. Uwar mayu tace, tabbas zancenka dutsena, kuma ina alfahari da irin wadannan makamai nan, domin suna karamin kwarin gwiwa gami da Karin tsoron ubangijin musulunci da dadin imani a gareshi. Gama fadin hakan ke da wuya, sai uwar mayu ta wuce gaba, sannna yayanta suka bita baya. Abul shaja'a ne ke biye musu, sannan Uzaifat da Lafirat suka jera tare. Abu kamar wasa sai da suka shafe sa'a tara suna tafiya a cikin dajin huzurul has basu hadu da wani mugun abu ba, face kanan kwari da daidaikun tsuntsaye masu shawagi a sararin samaniya. Al'amarin da ya daurewa su uwar mayu kai kenan suka cika da mamaki, domin ta taba ni a bakin sarki shaaran cewa duk halkitar da ta shiga cikin dajin huzurul has ba zata yi sa'a ba a raye, amma ga shi su yanzu sunyi sa'a tara cif abin da ya samesu. A dai dai wannan lokaci ne rana ke daf sa faduwa, kuna dukkaninsu akwai alamun gajiya a tare sa su. Koda Uzaifat ya lura da hakan sai banga can gabansu ya hango wani wuri mai cike da bishiyoyin masu yawan rassa sannan ga ciyayi masu taushi a wajen tamkar kilishi aka shimfida. Cikin farin ciki Uzaifat ya bada umarni a karasa wannan wuri a yada zango. A guje suka karasa wajen gaba dayansu. Da zuwa sai Abul shaja'a ya kwance a kansa. Ita ma Lafirat ta fiddo wata babbar fatar damisa ta shimfida, ta dubi Uzaifat cikin murmushi mai nuna tsantsar kauna ta ce, zo ka shingida anan ya gwarzona, ina son mu yi yar hira. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Uzaifat yaje ya zauna akan farar damisar itama Lafirat sai ta zauna daf dashi a lokacin da uwar mayu da yayanta suka baje akan ciyawar mai taushi a gefe guda suna hutawa. Lafirat ta dubi Uzaifat tace, ba ni labarin yadda ake bikin aure a aladarku da addininku. Koda jin wannan tambaya sai Uzaifat ya kyalkyale da dariya, yace ke kuwa saboda me kikayi mini wannan tambaya? Lafirat tace, saboda ina son na sami ilimi ne akan al'amarin kafin ya tabbata a kaina, domin a halin yanzu shine burina na biyu a duniya. Fatana na farko shine, na kashe ubana da yar uwata sazirat da hannuna bisa mugun aikin da suka aikata, kuma na dakatar da dukkan barna da suke shukawa a doron kasa. Fatana na biyu shine, na ha na karbi addinina, kuma na zamo abokiyar rayuwarka Koda lafirat tazo nan a zancenta sai Uzaifat ya tari numfashinta yace, Haba ai sai Yanzu nagane dalilin da yasa kika ki karbar addinina da wuri. Ina tabbatar miki da cewa, zamu iya samun nasarar hallaka mahaifinki da yar uwar ki ba tare da kinyi amfani da karfin sihiri ba. Ki tuna cewa, duk sihirin da kike takama sa shi mahaifinki ya fiki, to taya kike tsammanin cewa zaki iya hallakashi? Lokacin da Lafirat taji wannan batu sai zuciyarta ta karaya, tayi shiru ba tace komai ba, tsawon yan dakiku daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Uzaifat tace, mahaifina ya taba gaya mini cewa hr abada babu abin da zai iya hallakashi face sihiri. Nayi imani da wannan furuci na mahaifina, shi yasa na sa a raina cewa bazan iya hallakashi ba face da karfin sihiri. Uzaifat yayi dariya yace, amma dai kin yarda cewa, karfin ubangijin musulunci ya tafi kowane karfi ko? Lafirat tace kwarai kuwa domin na ga zahiri da idanuna, ni ganauce ba jiyauba. To tunda haka ne ina mai baki shawara da ki karbi addinin musulunci tun gabanin dama ta wuceki, domin rayuwa bata da tabbas, in mune yau ba mune gobe ba. Ko yanzu idan kika mutu kin mutu ne a matsayin mafita, kuna Allah bazaiyi miki uzuri ba. Lafirat ta gyada kai tace, tabbas maganarka gaskiya ce, kuma na karbi wannan shawara taka, ina fatan nayi amfani da ita cikin gaggawa. Koda gama fadin hak, sai Lafirat ta bude salkarta ta kama shan ruwa. Gama shan ruwan ke fa wuya ta dubi Uzaifat, sai ta ga Ashe har ya fara bacci. Kawai sai tayi dariya ta mike tsaye tsam ta koma can gefe daya tayi wat shimfidar dabam ita ma ta kwanta. Kafin cikar sa'a daya gaba dayansu sun bige da bacci, saboda gajiyar da suka sha a baya. Kash! Rashin sani yafi dare duhu, hakika wannan bacci da su Uzaifat sukayi a wannan wuri shi ne babban kuskurensu. Shi dai wannan wuri da suka kwanta Ashe wajen shakatawar maridi zurkas ne da iyalansa, kuma kullum sai sun zo wajen su zauna sun huta bayan sun yini suna farauta a adaji. Har magriba ta kusa yi dayansu daga cikinsu Uzaifat bai farka ba. Kwatsam sai ga maridi zurkas tare da matarsa maziba da kuma yayansa hiram da hirama, sun durfafo wannan wuri. Tun daga nesa maziba ta kyallara ido ta hango su Uzaifat a kwance sai ta kama hannun Zurkas da hannun su hirama ta tsai dasu suka tsaya cak! Sannan tace, yau fa mun tsinci tsuntsu daga sama gasasshe. Cikin mamaki da fushi zurkas ya dubeta ya ce, wannan kuma wace irin maganar banza kikayi haka, ina gasasshen tsuntsun yake? Maziba tace, dubi can wajen hutawarmu da kyau ka gani. Wasu biladama ne kwance suna shara bacci abinsu. Zurkas yace, hana maziba shin kin fara makancewa ne? Yaya za'ayi biladama su shigo wannan daji alhalin sama da shekaru talatin suka daina ratsawa ta nan, ba ma biladama ba, hatta aljanu ma sun kauracewa dazuzzukan nan guda uku. Koda jin wannan batu sai ran maziba ya baci tace, ai idan ni ban makance ba, to kuwa tabbas kai ka makance. Ka tambaya yayanka ka ji ai su yara ne masu kuruciya suna da lafiyar idanu. Kafin zurkas ya bude baki tuni Hiram yace, ya kai abbana hakika maganar Umma gaskiya ne, akwai biladama a kwance a can wajen hutawarmu, har ma da wadansu aljanu kimanin su dubi daya da doriya. Biladama kuwa basu wuce su uku ba. Tabbas yau zamu sha romo mu more, wai yaushe rabonmu da cin naman biladama da na aljanu? Ai munfi shekara talatin. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube zurkas ya dubi maziba, Hiram da hirama yace, ku tsaya anan kada ku biyoni, sai bayan na gama kamasu. Koda gama fadin haka, sai zurkas yayi girgiza ya bace bat. Bai baiyana a ko ina ba, sai gaban su Uzaifat suna ta shara barcinsu. Nan take zurkas yayi nuni sa hannunsa a garesu sai ga su a cikin wani katon keji na bakin karfe. Zurkas ya ci gaba da kallon su Uzaifat daya bayan daya. Koda ya zo kan Uzaifat, Abul shaja'a da uwar mayu sai ya gane cewa, sun kasance maabota addinin da bai sani ba, ita kuwa Lafirat saibya gane cewa matsafiyace. Nan take ya nisa wata iska daga cikin bakinsa sai barcin Uzaifat, Abul shaja'a da na su uwar mayu ya kara nauyi, ita kuwa Lafirat sai ta farka. Koda ta gansu a cikin keji a kulle, sai ta mike zumbur a firgice a Sanna ne tayi arba da maridi zurkas. Nan take ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin da tayi domin a rayuwarta bata taba ganin halitta mai matukar kwarjini ban tsoro da muni kamarsa ba. yayinda zurkas yaga Lafirat ta suma sai ya bushe da dariyar mugunta, wadda aminta ya haifar da girgizar bishiyoyin dajin gaba daya. Nan take ya dauki kejin da yatsa daya ya juya don ya tafi, sai ga maziba da su Hiram sun rugo da gudu izuwa gareshi suna tsalle da murna, amma ita Hirama ba ta farin ciki sosai, domin a rayuwarta babu abinda taje tausayi, sama d biladama. Ko a shekarun baya idan an kama biladama an bata, Sam bata cin namansu, amma tana cin na aljanu. Lokacin da zurkas ya lura da fuskata Hirama yaga bata farin ciki da wannan garabasa da aka samu, sai ya dubeta ya data mata tsawa yace, ya ke hirama ina mai yi miki gargadi da kada ki kuskura kice zaki kubutarda daya daga cikin wadannan biladama da muka kamo. Ki tuna irin muguwar azabar da nayi miki a shekaru baya,

Chapter 10 of 21