abu uku.
Abu ma farko dolene muyi abinda zai dauke musu hankali anan dajin sannan mu sulale basu sani ba mu tafi izuwa birninsu koda kuwa mu ukun nanne Jal domin mu kadai zamu iya cin garin da yaki.
Abu na biyu dole ne mu sati yata gimbiya lafirat daa sansanin su domin idan har tana tare dasu zata iya musu jagora izuwa can birninmu suje su kubutar da rayuwar dakarun nan nasu wadanda muka tsare da kuma luhaira yar likita abu sharhaz a cikin gidan gonata inda aka killaceta tsawon shekara da shekaru.
Kun sani cewa bani da wani buri wanda yafi na tara da wannan yarinya luhaira amma ba zan taba samun damar hakan na sai bayan kunci birnin Darul husuf da yaki mun Kawar da musulunci mun shimfida kafirci da addininmu na tsafi.
Lokacin da sarki shaaran yazo nana a zancensa sai hankalin ukashat da sazirat ya dugunzuma ainun. Ukashat ya dubi sarki shaaran cikin damuwa yace, ya kai wannan babban sarki yanzu ta ya ya kake ganin zamu iya sato lafirat da daga cikin wancan sansanin na su uzaifat? Tayaya kake ganin zamu sulale mu tafi izuwa can birnin Darul husuf ba tare da su sarki uwaisul karni sun sani ba? Wane abune na uku wanda dolene muyi shi idan har munason musami wannan nasara akan abokan gabanmu? Domin baka baiyana mana shi ba. Saadda sarki shaaran yaji wadannan tambayoyi sai ya bushe da mahaukaciyar dariya harda bingirewa kasa tamkar nazai daina ba. Daga can sai ya tsuke bakinsa ya hade fuska yace, dangane da abu na uku wanda ban baiyan muku shiba, abune wanda bakune zaku aikatashi ba. Ba komai bane wannan abu face sato muzaira matar sarki uwaisul karni mahaifiyarka wadda yanzu haka antsareta a kurkuku sakamakon yunkurin kashe sarki uwaisul karni da tayi.
Dole ne mu satota kafin ma ka tono wadannan layu guda gudu domin itace kadai zata iya sanar dani abinda zanyi na iya hallaka sarki uwaisul karni a filin yaki.
Lallai ni da kaina zam sulale naje birnin Darul Husuf na sato muzaura.
Yanzu sai ku sake nutsuwa kiji bayanin da zan ya muku akan yadda zaku sami nasarar yin abubuwan biyu.
Na farko wato sato lafirat da tafiya izuwa birnin Darul husuf wanda a rana daya zamuyi su.
Dafarko a gobe idan gari ya waye zamu fito filin yaki na bukaci da aci gaba da yaki, amma ta hanyar zabar gwanayen sadaukanmu da nasu guda goma shabibbiyu su kara.
A gobe kuma sai a zabi mutum dari dari. A jibi kuma sai a zabi mutum dari biyar biyar. A rana ta gudu kuma mutum dubu dubu muyi yarjejeniya akan cewa haka zaaci gaba da yakin har mu karar dasu ko su sukarar da mu.
***********************
Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷
************************
A wannan rana ta uku da za'ayi yakin mutum dari biyar daya daga cikinmu zai yi bad kama ya shiga yakin yadda ba zaa ganeshi ba.
Abinda nake bukata kawai shine ya yi iya kokarinsa ya sato gawar daya daga cikin abokam gabar ya kawo ta sansanin mu a boye ba tare da wani ya ganshi ba.
Tufafin badakaren muke so zamuyi amfani da shi idan dare yayi.
Wannan tufafi shi daya daga cikinku zai sanya a cikin daren yaje har sansanin nasu ya sato gimbiya lafirat ta kowanne hali ta hanyar amfani da dukan hikimarsa domin tsafi bazaiyo tasiri ba a cikin wannan alamari.
Idan har aka sami wannan nasara to a daren zan kirawo wani aljanina wanda zai daukemu yayi sama damu ya keta tacikin samaniya ba tare da makiya sun ganmu ba ya kaimu hat can kusa da kofar birnin Darul husuf.
A cikin daren zamu afkawa mutanen birnin mu cisu da yaki da karfin tsiya mu kafa gwamantain mu.
Su kuwa su sarki uwaisul suna nan filin yaki suna jira gari ya waye a ci gaba da yaki basu san tabargazara da muka tafka musu ba.
Yanzu a cikinku wane zai iya samo mana gawar badakaren abokan gaba kuma ya sati lafirat?
Koda jin wannan tambaya sai gardama tasarke tsakanin sazirat da ukashat kowannensu na cewa shine zai iya wannan aiki cikin nasara ba tare d an sami kuskure ba.
Koda ganin haka sai sarki shaaran ya shiga tsakanin suka yi shiru sannan ya dubi sazirat yace, ke mecece hujjarki ta ganin cewa lallai zaki fi ukashat samun nasara yin wannan aiki?
Sazirat ta yi gyaran murya tac, ya kai abbana kasani cewa ni ya mace ce saboda haka mata sunfi maza iya makirci da iya shirya tuggu.
Koda jin haka sai sarki shaaran yayi murmushi yace, naji taki hikimar. Kai kuma fa?
Ukashat yayi gyaran murya yace, ya shugabana ni babbar hujjata itace ni na fito ne daba cikin wadannan mutane don haka ni nafi sanin dukkan dakarunsu na tsaro kuma ni ne nasan dukkan sirrin su na dana tarkon kama abokan gaba. A takai ce dai da dan gari akanci gari.
Koda jin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariya tace, Tabbasa nafi samun nutsuwa d naka jawabi don haka kaine zaka yi wannan aiki nan da cikar kwana uku.
* * * * * *
A can tantin sarki uwaisul karni kuwa, kamar yadda sarki shaaran ya zauna ya gana da sazirat da ukashat haka Shima sarki uwaisul karni ya zauna tare da uzaifat da lafirat domin su tattauna danagane da yadda zasu bullowa wannan yaki domin basu san manufar sarki shaaran bisa dalilin tsayar da yakin ba, kuma idan gari ya waye basu san abinda zai zo dashi ba.
Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat da lafirat yace, yanzu ku a tunanin ku da kuma hangen nesanku me kuka fahimta dan gane da tsayar da wannan yaki da sarki shaaran yayi ya gudu shida jamaarsa izuwa bakin wannan kogi, kuma me kuke tunanin zai iya shiryawa anan gaba wanda zai iya cutar damu?
Yayin da uzaifat sukaji wannan tambaya sai duk suka kara nutsuwa suka yi shiru.
Daga can sau lafirat tanumfasa tadubi sarki uwaisul karni cikin niyaiyya tace, ya shugabana ni a ganina mahaifina ya janye wannan yaki ne domin ya ga alamar cewa basu da nasara akanmu kuma abin da nake hange shine zai iya kokarin kawo mana farmakin sumame a cikin dare don haka dole ne kasa dakarunka su kara karfin tsaro a wannan sansanin namu ya zamana cewa ko yaushe a cikin shirin yaki muke. Kuma ko yaya muka ji wani motsi mu kai hari wajen babu sassauci.
Ya yinda sarki uwaisul karni yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, tabbas kinyi tunani mai kyau, kuma lallai zamu yi amfani da wannan shawara taki.
Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat yace, kai kuma fa me kayi tunani akan wannan alamari kafin nima ubangijina ya nusar da ni bisa abinda yazo a cikin mafarkina?
Koda jin wannan tambaya sai uzaifat yayi ajiyar zuciya sannan yace, ya kai abbana ni a tunanina da hangena lallai ruwa baya tsami banza.
Tabbas masu iya magana sunce shi yaki dan zambane don haka lallai akwai wata yaudara da sarki shaaran ke kakarin shirya mana a cikin wannan yaki.
Abu ne mawuyaci ya kawo mana harin sumame a cikin dare tunda muna dag da juna ido na kallon ido.
Ku dubi sansanin su ko ina a haska ke yake da fitilun itatuwa haka muma namu don haka babu wani bangare da zai yi wani yunkuri ba tare da daya bangaren ya gani ba.
Idan harzai shirya wata dabarako wani tuggu dole sai idan a lokacin da aka ci gaba da yaki.
Abinda nake so damu shine, da zarar an ci gaba da yaki lallai mu sa ido akan abokan gaba kuma ta kowanne hali kada mu bari mutum daya cikinsu ya shigo cikin wannan sansanin namu kuma duk yadda zamuyi lallaine mu yi kokarin kwato yarima ukashat daga hannunsu ta kowanne hali a matsayin fursunan yakin mu domin shine kadai ya san sirrin birninmu kuma shine kadai zai iya shiga birnin ya cutar da jamaarmu ko kuma Ya tono wadannan layu daga karkashin katangun birnin namu.
Abu na uku da ya kamata muyi shine, lallai da zarar an fara ci gana da wannan yaki mu sami wani daga cikinmu wanda zai sulale ba tare da anganshi ba ya tafi can birnin shumbul yaje har inda aka boye mutanen mu da inda aka boye luhaira yar likita abu sharaz yaceto rayuwar su.
Ina ganin idan muka sami nasarar aikata haka bukatarmu zata biya kuna zamu sami cikakkiyar nasara akan abokan gaba.
Saadda uzaifat yazo dai dai nan a jawabinsa sai sarki uwaisul karni ya jinjina kai yayi shiru yana nazarin alamarin har izuwa lokaci mai dan tsawo.
Daga can kuma sai yai ajiyar zuciya yace, ya kai dana hakika ka zo da shawara mafi kyau.
To amma yanzu tsakanin kai da lafirat wanene zai iya izuwa can sansanin shumbul ya ceto rayuwar jamaaramu a cikin nasara ba tare da an sami matsala ba.
Kuma wane ne zai tayamu tabbatar da tsaro a wannan sansanin yaki namu?
Koda jin wannan tambaya sai uzaifat da lafirat suka dubi juna sukayi shiru.
Daga can sai uzaifat yace, ni ina ganin cewa dole sai da dan gari akanci gari.
Lallai lafirat ce ya kamata ta tafi birninsu ta ceto mana rayuwar jamaarmu da ta luhaira tunda ta san a inda suke kuma ta san duk irin matakan tsaron dake wajen.
Ni kuwa sai na tsaya anan filin yaki na tabbatar da tsaro kuma na tayamu yaki har Allah ya baku nasara akan abokan gaba.
Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lafirat ya dugunzuma tace, ai idan akayi haka ni burina bazai cika ba na ganin cewa na kashe mahaifina da yar uwata da hannuna tunda wata kula bana nan za'ayi yakin.
Ku tuna cewa nayi alkawarin ba zan karbi addininku ba har sai na ga na cika wannan buri nawa. Shin bakwason na karbi addinin naku ne?
Saadda sarki uwaisul karni da uzaifat sukaji wannan tambaya sai jikinsu yayi sanyi, suka sunkui da kawunanzu kas suka yi shiru basu ce kala ba.
Daga can sai sarki uwaisul karni ya dago kai ya dubi lafirat yace, ya ke yata hakika kinyi babban ganganci da kika daukarwa kanki wannan alkawari mai nauyi kuna mai wuyar cikawa tunda ako yaushe zaki iya rasa rayuwar ki.
Kinga kuwa idan har kika mutu baki karbi addininmu ba kin mutu kafira baki da rabo gobe kiyama.
Ni a yanzu tawa shawarar kuma bisa hangena ke da uzaifat zaku tafi izuwa can birnin shumbul domin a hangena ke kadai ba zaki iya wannan aiki ba na ceto rayuwar jamaarmu da ta luhaira saboda babu wani abu da kike takama dashi sama da tsagwaron iyakar karfin dantsenki da sihirin tsafi.
Na tabbata mahaifinki ya fiki karfin sihiri don haka ba zaki iya datea hijaban da ya sanya ba na bayar da tsaro da a wuraren da ya boye jamaarmu shi kuwa uzaifat zai iya keta hijaban da karfin addua kinga kenan kuna bukatar juna ku biyun tunda ke kin san wuraren da zaaje, shi kuma zai iya shigo ko ina.
A gaba daya dakarun babu wanda zai iya tarar sarki shaaran face ni.
Haka kuma na yarda da sauran dakaruna a cikinsu akwai wadanda zasi iya taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Zan yi iya kokari na na ga na hallaka sarki shaaran sannan na fuskanci yar sa sazirat.
Babbar matsalar mu itace ta yaya zamu iya sato yarima ukashat daga cikin sansanin yakinsu a lokacin da ba a yin yaki musamman cikin dare?
Koda jin wannan tambaya sai yarima uzaifat da lafirat suka sake kallon juna a kari na biyu sukayi shiru. Lafirat tayi ajiyar zuciya tace, ni kadaice zan iya wannan aiki tunda na fiku sanin dukkan matakan tsaron da ke sansanin mutanen mu kuma zan iya amfani da makirci irin namu na mata.
Amma ina bukatar kwana biyu rak nayi nazari akan wannan alamari.
Sarki uwaisul karni yayi murmushi yace, na baki wannan dana amma ki sani cewa lallai a ranar kwana na nake son ki cika wannan aiki in yaso kashe gari sai kusan yadda zakuyi ku sulale ku tafi can birnin shumbul ba tare da kowa ya sani ba.
Lafirat ta maida wa sarki martanin murmushi sannan ta ce, an gama ya shugabana.
Kashe gari da safe bayan jamaar kowanne bangaren sun kintsa sai sarki shaaran yasa aka Busa kahon ci gaba da yaki.
Nan take dakaru suka hau sahu sahu akan layi akan fuskanci juna. Mahaya layinsu da ban, mayakan kasa ma layin su daban.
Bayan kowanne bangare ya gama shiri tsafi sai sarki shaaran ya zaburi dokinsa izuwa tsakiyar filin yakin ya tsaya.
Koda ganin haka sai shima sarki uwaisul karni ya zaburi nasa dokin ya tunkareshi har yana shirin zare takobinsa domin a zatonsa sune zasi fara bude fagen yakin sai sarki shaaran ya dubeshi yayi masa murmushi yace, ai ba fitowa nayi ba domin mu yi yaki da kai ba.
Nafitone domin kaima ka fito mu tsara yadda zaaci gaba da wannan yaki domin mu gaggauta kawo karshen yakin kuma mu kece raina a tsakanin mu.
Idan har ka yarda da kanka kuma ka yarda da mayakan ka. Ina son mu fara fito na fito da mutum goma sha bibbiyu daga cikin jamaarmu su yaki juna a yau.
Gobe kuma sai mu fito da mutum dari dari, jibi mutum dubu dubu. A ranar kwana ma uku mu ninka sau goma.
A haka za acigana da yakin har mu karshi.
Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni yayi shiru yana nazari, kawai sai yayi addua a cikin zuciyar sa yace, Allah ka bamu saa a cikin wannan sabone sako da wannan makiya namu yazo dashi kuma idan wani makircin yaki ya shirya mana kada ka bashi nasara akanmu.
Koda gama wannan addua sai sarki uwaisul karni ya dubi sarki shaaran ya ce, na yarda da kaina kuma na yadda dakaruna.
Nayi imani cewa ubangiji na zai bamu sa'a akanku don haka na amince da wannan tsaru da kazo dashi.
Koda jin haka sai sarki shaaran ya tuntsire da dariya**DAKARUN MUSULUNCI*
Littafi Na 3
Part E ♥️✍️
NA: Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing Umar Farouq Zango
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
A wannan rana ta uku da za'ayi yakin mutum dari biyar daya daga cikinmu zai yi bad kama ya shiga yakin yadda ba zaa ganeshi ba.
Abinda nake bukata kawai shine ya yi iya kokarinsa ya sato gawar daya daga cikin abokam gabar ya kawo ta sansanin mu a boye ba tare da wani ya ganshi ba.
Tufafin badakaren muke so zamuyi amfani da shi idan dare yayi.
Wannan tufafi shi daya daga cikinku zai sanya a cikin daren yaje har sansanin nasu ya sato gimbiya lafirat ta kowanne hali ta hanyar amfani da dukan hikimarsa domin tsafi bazaiyo tasiri ba a cikin wannan alamari.
Idan har aka sami wannan nasara to a daren zan kirawo wani aljanina wanda zai daukemu yayi sama damu ya keta tacikin samaniya ba tare da makiya sun ganmu ba ya kaimu hat can kusa da kofar birnin Darul husuf.
A cikin daren zamu afkawa mutanen birnin mu cisu da yaki da karfin tsiya mu kafa gwamantain mu.
Su kuwa su sarki uwaisul suna nan filin yaki suna jira gari ya waye a ci gaba da yaki basu san tabargazara da muka tafka musu ba.
Yanzu a cikinku wane zai iya samo mana gawar badakaren abokan gaba kuma ya sati lafirat?
Koda jin wannan tambaya sai gardama tasarke tsakanin sazirat da ukashat kowannensu na cewa shine zai iya wannan aiki cikin nasara ba tare d an sami kuskure ba.
Koda ganin haka sai sarki shaaran ya shiga tsakanin suka yi shiru sannan ya dubi sazirat yace, ke mecece hujjarki ta ganin cewa lallai zaki fi ukashat samun nasara yin wannan aiki?
Sazirat ta yi gyaran murya tac, ya kai abbana kasani cewa ni ya mace ce saboda haka mata sunfi maza iya makirci da iya shirya tuggu.
Koda jin haka sai sarki shaaran yayi murmushi yace, naji taki hikimar. Kai kuma fa?
Ukashat yayi gyaran murya yace, ya shugabana ni babbar hujjata itace ni na fito ne daba cikin wadannan mutane don haka ni nafi sanin dukkan dakarunsu na tsaro kuma ni ne nasan dukkan sirrin su na dana tarkon kama abokan gaba. A takai ce dai da dan gari akanci gari.
Koda jin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariya tace, Tabbasa nafi samun nutsuwa d naka jawabi don haka kaine zaka yi wannan aiki nan da cikar kwana uku.
* * * * * *
A can tantin sarki uwaisul karni kuwa, kamar yadda sarki shaaran ya zauna ya gana da sazirat da ukashat haka Shima sarki uwaisul karni ya zauna tare da uzaifat da lafirat domin su tattauna danagane da yadda zasu bullowa wannan yaki domin basu san manufar sarki shaaran bisa dalilin tsayar da yakin ba, kuma idan gari ya waye basu san abinda zai zo dashi ba.
Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat da lafirat yace, yanzu ku a tunanin ku da kuma hangen nesanku me kuka fahimta dan gane da tsayar da wannan yaki da sarki shaaran yayi ya gudu shida jamaarsa izuwa bakin wannan kogi, kuma me kuke tunanin zai iya shiryawa anan gaba wanda zai iya cutar damu?
Yayin da uzaifat sukaji wannan tambaya sai duk suka kara nutsuwa suka yi shiru.
Daga can sau lafirat tanumfasa tadubi sarki uwaisul karni cikin niyaiyya tace, ya shugabana ni a ganina mahaifina ya janye wannan yaki ne domin ya ga alamar cewa basu da nasara akanmu kuma abin da nake hange shine zai iya kokarin kawo mana farmakin sumame a cikin dare don haka dole ne kasa dakarunka su kara karfin tsaro a wannan sansanin namu ya zamana cewa ko yaushe a cikin shirin yaki muke. Kuma ko yaya muka ji wani motsi mu kai hari wajen babu sassauci.
Ya yinda sarki uwaisul karni yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, tabbas kinyi tunani mai kyau, kuma lallai zamu yi amfani da wannan shawara taki.
Sarki uwaisul karni ya dubi uzaifat yace, kai kuma fa me kayi tunani akan wannan alamari kafin nima ubangijina ya nusar da ni bisa abinda yazo a cikin mafarkina?
Koda jin wannan tambaya sai uzaifat yayi ajiyar zuciya sannan yace, ya kai abbana ni a tunanina da hangena lallai ruwa baya tsami banza.
Tabbas masu iya magana sunce shi yaki dan zambane don haka lallai akwai wata yaudara da sarki shaaran ke kakarin shirya mana a cikin wannan yaki.
Abu ne mawuyaci ya kawo mana harin sumame a cikin dare tunda muna dag da juna ido na kallon ido.
Ku dubi sansanin su ko ina a haska ke yake da fitilun itatuwa haka muma namu don haka babu wani bangare da zai yi wani yunkuri ba tare da daya bangaren ya gani ba.
Idan harzai shirya wata dabarako wani tuggu dole sai idan a lokacin da aka ci gaba da yaki.
Abinda nake so damu shine, da zarar an ci gaba da yaki lallai mu sa ido akan abokan gaba kuma ta kowanne hali kada mu bari mutum daya cikinsu ya shigo cikin wannan sansanin namu kuma duk yadda zamuyi lallaine mu yi kokarin kwato yarima ukashat daga hannunsu ta kowanne hali a matsayin fursunan yakin mu domin shine kadai ya san sirrin birninmu kuma shine kadai zai iya shiga birnin ya cutar da jamaarmu ko kuma Ya tono wadannan layu daga karkashin katangun birnin namu.
Abu na uku da ya kamata muyi shine, lallai da zarar an fara ci gana da wannan yaki mu sami wani daga cikinmu wanda zai sulale ba tare da anganshi ba ya tafi can birnin shumbul yaje har inda aka boye mutanen mu da inda aka boye luhaira yar likita abu sharaz yaceto rayuwar su.
Ina ganin idan muka sami nasarar aikata haka bukatarmu zata biya kuna zamu sami cikakkiyar nasara akan abokan gaba.
Saadda uzaifat yazo dai dai nan a jawabinsa sai sarki uwaisul karni ya jinjina kai yayi shiru yana nazarin alamarin har izuwa lokaci mai dan tsawo.
Daga can kuma sai yai ajiyar zuciya yace, ya kai dana hakika ka zo da shawara mafi kyau.
To amma yanzu tsakanin kai da lafirat wanene zai iya izuwa can sansanin shumbul ya ceto rayuwar jamaaramu a cikin nasara ba tare da an sami matsala ba.
Kuma wane ne zai tayamu tabbatar da tsaro a wannan sansanin yaki namu?
Koda jin wannan tambaya sai uzaifat da lafirat suka dubi juna sukayi shiru.
Daga can sai uzaifat yace, ni ina ganin cewa dole sai da dan gari akanci gari.
Lallai lafirat ce ya kamata ta tafi birninsu ta ceto mana rayuwar jamaarmu da ta luhaira tunda ta san a inda suke kuma ta san duk irin matakan tsaron dake wajen.
Ni kuwa sai na tsaya anan filin yaki na tabbatar da tsaro kuma na tayamu yaki har Allah ya baku nasara akan abokan gaba.
Koda jin wannan batu sai hankalin gimbiya lafirat ya dugunzuma tace, ai idan akayi haka ni burina bazai cika ba na ganin cewa na kashe mahaifina da yar uwata da hannuna tunda wata kula bana nan za'ayi yakin.
Ku tuna cewa nayi alkawarin ba zan karbi addininku ba har sai na ga na cika wannan buri nawa. Shin bakwason na karbi addinin naku ne?
Saadda sarki uwaisul karni da uzaifat sukaji wannan tambaya sai jikinsu yayi sanyi, suka sunkui da kawunanzu kas suka yi shiru basu ce kala ba.
Daga can sai sarki uwaisul karni ya dago kai ya dubi lafirat yace, ya ke yata hakika kinyi babban ganganci da kika daukarwa kanki wannan alkawari mai nauyi kuna mai wuyar cikawa tunda ako yaushe zaki iya rasa rayuwar ki.
Kinga kuwa idan har kika mutu baki karbi addininmu ba kin mutu kafira baki da rabo gobe kiyama.
Ni a yanzu tawa shawarar kuma bisa hangena ke da uzaifat zaku tafi izuwa can birnin shumbul domin a hangena ke kadai ba zaki iya wannan aiki ba na ceto rayuwar jamaarmu da ta luhaira saboda babu wani abu da kike takama dashi sama da tsagwaron iyakar karfin dantsenki da sihirin tsafi.
Na tabbata mahaifinki ya fiki karfin sihiri don haka ba zaki iya datea hijaban da ya sanya ba na bayar da tsaro da a wuraren da ya boye jamaarmu shi kuwa uzaifat zai iya keta hijaban da karfin addua kinga kenan kuna bukatar juna ku biyun tunda ke kin san wuraren da zaaje, shi kuma zai iya shigo ko ina.
A gaba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 21