Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yin hakan tunda mahaifina da sarki Nukaib bai mutuba ba face sai da ya karbi musulunci. Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki tace, ya kai mijina lg akayi kasan cewa sarki Nukaib ya karbi musulunci alhalin kowa ya mutu a filin yakin ba a sami wanda ya kawo labarin abinda ya faru ba?. Uwaisul karni yayi ajiyar zuciya sannan yace, yake matata hakika kinyi tambaya mai matukar mahinmmanci kuma mai Ma'ana. Ina son ki sani cewa bayan kimanin shekaru arbain da mutuwar mahaifina na tsinci wata wasika a cikin irin tufafinsa da na gada wadanda ban taba sauyawa ba. Wannan wasika na kunshe da wasiyya ce ta mahaifina a gareni. Ashe kafin ya mutu a wannan filin yaki ya sami damar rubuta wannan wasiya, domin ya kawo karshen yakin a tsakanin kasashen biyu. A cikin wasikar ne ya bukaci da nayi tallan addinin musulunci ga mutanen kasar shumbul, kuma a cikin wasikar ne yayi min bayanin dangantakarsa da sarki Nukaib bisa abotarsu a makaranta da kuma duk abinda ya faru a tsakaninsu a filin yaki. Lokacin da na gama kiranta wannan wasika sai na fashe da kuka domin bakin alkalami ya Riga da ya bushe babu abinda zan iya yi a kan al'amarin. Bazan iya tsaida yakin ba tsakanina da birnin shumbul saboda na rigaya na dauki alkawarin ci gaba da yaki ga kakana, kuma har a ranar da kakana zai mutum yana kan cinyata babu abinda yaje maimaita min face na cika alkawarin da ke tsakaninmu. Yake matata tabbas bazan taba janye wannan alkawari ba, don haka dolene naci gaba da karfafawa su uzaifat gwiwa akan wannan yaki kuma duk wanda ya sami nasarar cin birnin shumbul da yaki shinea zai gajeni. Wannan itace wasiyyatr da zan bari kuma ko a bayan raina da ita za'ayi amfani. Koda gama wannan jawabi sai uwaisul karni yayiwa shulaifa sallama ya tafi izuwa dakin muzaira domin ya bata kwananta. * * * * * * Kashe gari bayan an yi kalacin safe sarki uwaisul karni ya tura aka kirawo yarima uzaifat da yarima ukashat suka gabata gareshi. Bayan sun durkusa a gabansa sun kwashi gaisuwa sai ya dube su a nutse yace yaku 'Ya'yana ina son nayi muku nasiha guda daya kafin nayi muku bayanin yadda zaku gabatar da wannan yaki da mutanen shumbul. Nasihar da zan muku itace, duk abinda zaku yi kada kuyi gaggawa, domin ita gaggawa taba kai mutum izuwa ga nadama. Sannan kuma ku kasance masu bincike bisa duk al'amarin da yazo muku saboda bincike na iya haifar da fahimtar juna gami da samun zaman lafiya ba tare da kun aikata abin da zaizo ya dameku ba. Dan gane da batun yakin da zaku tafi, ina son kuyi shiri kowannenku ya jagoranci rundunar dakarunsa a lokacin guda ku tafi yakin inda aka saba fafatawa muda mutanen birnin shumbul a gobe. A yanzu zan yi muku kacici kacici domin fitar da rundunar da zata fara tarar abokan gaba. Koda gama fadin haka sai sarki uwaisul karni ya sanya hannunsa a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wadansu takardu dunkulallu biyu ya ajiye a gabansu yace kowannenku ya zabi takarda guda. Wanda ya dauki takardar da aka rubuta daya a cikinta dakarunsa ne zasu fara fita filin daga. Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat suka tsirawa takardun biyu idanu aka rasa wanda zai fara dauka. Sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa yace, me kuke jirane. Koda jin tsawar sai jikin su ya kama kyarma, cikin sauri uzaifat ya kai hannunsa ya dauki takardar dake gabansa sannan ukashat ya dauki dayar, sarki yace to ku warware takardun don muga abinda ke ciki. Ba tare da fargabar komai ba uzaifat yayi bisimillah ya bude tasa shi kuwa shi kuwa ukashat sai ya kama nuku nuku da kyar ya bude tasa. Sarki uwaisul karni ya karbi ta uzaifat ya duba sai ga lamba biyu a rubuce, kawai sai ya nunawa ukashat yace, to kaine zaka fara tarar abokan gaba. Nan take bakin ciki ya turnuke ukashat saboda shi a tunaninsa idan su uzaifat ne suka fara yin yakin nan da nan za a fara cin lagonsu uzaifat sai su kasa samun nasara inyaso daga baya sai su tsinci dami a kala. Yayin da sarki uwaisul karni yaga alamun damuwa karara a fuskar ukashat sai ya dubeshi yace, ya kai dana kayi sani cewa komai na duniya rabone. Babu wanda ya isa ya hanaka samun nasara a wannan yaki idan kana da rabo, haka kuma babu wanda ya isa ya sa samu idan baka da rabo. Koda sarki uwaisul karni ya zo nan a zancesa sai tari ya sarkeshi. Abu kamar wasa sai tarin yaki tsayawa, sai kuma ya fara aman jini. Nan da nan hankalin uzaifat da na ukashat ya dugunzuma suka dimauce. Cikin karaji uzaifat ya kwalawa wani hadimi kira wai shi amzabu. A guje Amazabu ya shigo cikin turakar, uzaifat ya umarci amzabu daya ruga gidan likitan sarki abu sharaz ya ki rashi yanzu yanzu. Koda jin wannan umarni sai amzabu ya sake juya wa wajen ya kama dokin ya haye ya zabureshi. Jima kadan sai ga amzabu tare da abu sharaz sun shigo cikin turakar sarki. Da shigowar su abu sharaz ya ga halin da sarki ke ciki, a wannan lokaci sarki na numfashi sama sama kuma idanunsa sun kada sunyi jawur babu kyan gani, sai shima hankalinsa ya dugunzuma nan take ya bude jakarsa ya fiddo wadansu magunguna ya hadasu a cikin kofi sannan ya durawa sarki a baki. Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI 1 part E don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARI 🩷🩷🩷**DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA DAYA 1. PART E 💕💯 NA:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 💪 🥷🥷 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Kashe gari kuwa tun da duku dukun safiya bayan any isar da sallah asuba, rundunar biyu ta DAKARUN MUSULUNCI suka yi sahu sahu a kofar fada bisa dawakai kuma cikin shigar yaki mai kwarjini da ban tsoro. Al'amarin da ya janyo hankalin jamaa kenan aka firfito daga cikin gidaje aka tari ana yi musu kabbara, don kara musu kwarin gwiwa saboda sanin cewa JIHADI za su fita. Sai da dakarun biyu suka shafe kusan rabin sa'a a tsaitsaye sannan masu jagorantarsu suka fito daga gidan sarauta. Ba wasu bane face yarima uzaifat da yarima ukashat. Koda ganin iri shigar da jaruman biyu sukayi sai gaba daya jama'ar gari suka cika da tsananin mamaki. Suka zuba musu idanu kawai a lokacin da fadar tayi tsit tamakar babu mai rai a wajen. Ba komai ne ya janyo hakan ba face ganin irin shigar da yarima ukashat yayi wadda ta saba da al'adar dakarun yakin kasar. A ka'idar wannan dakarun musulunci na wannan birni duk sa'adda za'a fita yaki kowa na sanya fararen tufafi ne ba'a taba ganin wanda sanya wani kamar ba daban, amma yau sai aka ga yarima ukashat shi kadai ya sanya jajayen tufafi. Nan fa fadar ta rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa. Uzaifat ya tafi izuwa gaban dakarunsa ya tsaya, sannan Shima ukashat ya tafi izuwa gaban tasa rundunar. Faruwar hakan ke da quya sai ga wazirin sarki uwaisul karni ya fito daga cikin fada, sauran 'yan majalisa na boye da shi. Koda juma'a suka hangosu sai filin fadar yayi tsit aka zuba musu idanu har suka zo gaban juma'a suka tsaya. Bayan waziri ya wuce gaba sai ya tsaya cak ya fuskanci alumma a cikin nutsuwa sannan yayi sallama iri ta addinin musulunci. Cikin hadin baki gaba daya gaba daya jama'ar gari suka amsa sallamar sannan yayi gyaran murya yace, yaku 'yan uwana musulmi kuyi sani cewa ni wakili ne na sarkinmu mai girma sarki uwaisul karni, kuma na tsaya ne a gaban ku domin na isar da sakonsa a gareku bisa kasan cewar ba zai iya fitowa ba a yau ya fuskanceku sakamakon 'yar lalurar rashin lafiya data riskeshi a jiya. Koda jin wannan batu sai fadar ta sake rudewa da hayaniya, masu salati nayi masu yin addu'o'i nayi. Wasu kuwa sai hankalisu ya dugunzuma. Bakomaine ya haddasa hakan ba face mamaki da kima fargaba, domin a tarihin rayuwar sarki tun da ya hau kan mulki bai taba yin tashi lafiyar da ta hanashi fitowa ba sai yau. Koda waziri yaga fadar ta rude sai ya daga hannunsa sama, take kuwa juma'a suka yi shiru kamar mutuwa ta gifta waziri taci gaba da bayani yana maicewa. Yaku 'yan uwana musulmi, kuyi sani cewa babu wani abu dauwamamme face Allah da kansa, kuma ciwo ba shine ajali ba. Kada ku tayar da hankalin ku bisa lalurar data samu sarkinmu mai adalci, domin babu mai yaye masa face ubangijin daya dora masa. Abinda ya kamacemu shine muci gaba da yi masa addu'a akan Allah ya yaye masa wannan lalura. Koda gama fadin haka sai fadar ta rude da amin!! Nan take waziri yace a karantawa sarki falaki da nasi da ayatul kuriyyu. Aka rufe da sirril fatiha. Cikin hadin baki kuwa aka kammala wannan addu'a. In da mutum na kusa sa'adda ake wannan addu'a sai gaba daya tsigar jikin sa ta tashi saboda jin dadin sautin addu'ar a bakin jama'a wacce ta cika dodon kunne, kuma ta sanyaya zukata. Koda mutum kafirine in dai ya jiyo wannan sauti sai zuciyarsa ta karaya. Bayan am idar da wannan addu'a sai waziri yavi gaba da jawabi yana mai cewa. Yaku jama'ar wannan birni, kuyi sani cewa sarki yace a sanar daku ana bukatar gudunmawar ku ta addu'a bisa wannan yaki wanda 'ya'yansa zasu jagoranta izuwa birnin shumbul. Kamar yadda kuka sani shekara da shekaru muna fafata yaki da wadannan mutanen kasar shumbul amma bamu taba samun nasara akansu ba, suma haka. To fa a wannan karon anyi shiri na musamman wanda ake sa ran cewa lallai za a sami nasara akan abokan gaba, don haka ana bukatar jajircewar gudunmawarku ta addu'a daga yanzu har zuwa lokacin da za a dawo daga wannan yaki. Wannan shine iyakar sakon da sarki ya bayar a shaida muku. Idan akwai wani mai korafi yayi bayani. Idan kuma babu yanzu mu yi bankwana da mayakanmu domin su kama hanya izuwa filin daga. Koda waziri yazo nan a zancensa sai yayi shiri ya kurawa jama'ar gari idanu ko zai ji wanda zai zo da korafi. Tsawon 'yan dakiku fadar ta sake yin tsit. Daga can sai wani Dattijo mai yawan shekaru ya dogara sandarsa a hankali yana mai rantsowa ta tsakiyar jama'a ya ido gaban waziri ya tsaya sannan yayi sallama irin ta addinin musulunci ya ce, ya kai wazirin sarkinmu, kayi sami cewa mi dai a garin nan Allah yayi baiwar kwana domin a halin yanzu bana tsammanin cewa akwai mai yawn shekaru na, domin da wayona aka haigi kakan sarki na ukj. A iya taso wata a wannan birni namu mai albarka ban taba ganin bakon al'amari ba irin na yau. Wannan bakon al'amari kuwa ba komai bane face irin shigar tufafin da yarima ukashat yayi a yau. A iya sanina tun daga kafa wannan birni kawo I yau duk sa'adda za'a fita yaki kowa fararen tufafi yake saw a jikinsa, ba'a taba ganin wani ya sanya sabanin haka ba, shin ko yarima zai iya yi mana bayanin da yasa yazo da wannan sabone tsari a yau? Yayin da waziri yaji wannan tambaya daga bakin Dattijo sai ya gyara murya yace, to masu iya magana sunce waka a bakin mai ita tafi dadi, saboda haka yanzu zan bukaci yarima ukashat da ya fito gaban jama'a ya kare kansa in da hali domin ni kaina ban san hujjar sa ta sanya jajayen tufafi ba a yau. Kafin waziri ya gama rufe bakinsa tuni ukashat ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban jama'ar ya tsaya yana mai murmushi ba da fargabar komai ba. Nan take ukashat yayi sallama jama'a suka amsa masa, sannan yace. Yaku 'yan uwana musulmai, da farko dai ina son kusani cewa a har kullum ana son musulmi yayi aiki da kyakkyawar niyya. Al'ada bata gaban farilla ko sunana. Sanya fararen tufafi yayin fita yaki a wannan birnin namu al'ada ce ta iyaye da kakanninmu ba wai farilla bace a cikin addinin Allah, don haka sabanin haka baya nufin an kauce hanya ko an sabi Allah. Ina son kowa ya fahimat cewa na bambanta suttura ta da ta sauran abokan tafi yane domin kawai na darsa shakku a cikin zuciyar abokan gaba kuma na firgitasu suyi tunanin wani abun Daban wanda zai iya kawo musu nakasu a cikin wannan yaki. Wata kila yin hakan yazamo sanadin samun nasara akansu. Abu na biyu da nake son jama'a su fahimta shine, mahaifinmu ya tura mu wanann yaki ne akan babban hujja guda daya. Wanna hujja itace, ya raba mayakanmu izuwa kaso biyu, naso na farko na Karkashin jagorancin dan uwana uzaifat, daya kason kuwa a Kar kashin nawa jagorancin yake. Za'a fara wannan yaki ne da tawa rundunar sannan daga baya rundunar dan uwana su kafsa da abokan gaba. Duk wanda rndunarsa ta samu nasara shine zaigaji karagar sarki. Shin ba kwa tunanin cewa wannan gasa wadda sarki ya shirya mana bata dace ba? Shin ba kwa ganin cewa akwai son zuciya a cikinta? Koda jin wannan batu sai fadar ta rude da hayaniya, al'amarin da ya dugunzuma hankalin 'yan majalisar sarki kenan ga dayansu suka ware gefe guda suka tattauna. Daga bisani sai waziri yace shi kenan an yarda yarima ukashat ya tafi wannan yaki a cikin shigarsa ta jajayen tufafi. Ba tare da bata lokaci ba aka buga tambarin yaki dukkanin dakaru suka yi bankwana da iyalinsu wasu na kwalla, wasu kuma na yiwa dakarun murna akan zasu tafi neman shahada. Daga nan sai dukkanin dakarun suka hau dawakansu. A lokacin ne shulaifa ta zo gaban yarima uzaifat domin suyi sallamar karshe. Ta dubeshi cikin yanayin damuwa tace, ya kai dana kada ka mance da nasihata a gareka bisa abubuwa uku nan da nace ka kiyaye su. Abu na farko shine, gaskiya, sai amana, sai cika alkawari. Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke ummina ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zan kiyaye bisa wadannan abubuwa uku, ni dai bukatata a wajenki kawai itace ki tayani da addu'a. Koda jin haka sai idanun shulaifa suka ciko da kwalla tafara zubar da hawaye, al'amarin daya dugunzuma hankalin uzaifat kenan ya dubeta cikin matsanaiciyar damuwa yace ina dalilin zubar wannan hawaye naki ya ummina Shulaifa ta share hawayenta sannna tace, ya kai dana kayi sani cewa dolene nayi kuka domin ina cikin tsaka mai wuya. Katuna halin da mahaifinka ke ciki yana kwance cikin jinya babu tabbacin zai tashi, kai kuma gashi yanzu zaka tafi jihadi ba lallai bane ka dawo ba, kaga kenan zan iya zama bazawara kuma mara da, idan na rasaku duk ku biyun. Sa'adda shulaifa tazo nan a zancenta sai tausayinta ya kama yarima uzaifat har shima ya kama hawaye, kawai sai ya sauka daga kan dokinsa suka rungume juna. Tsawon 'yan dakiku suna Jade sannan ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace. Yake ummina ina son ki kasance mai yin tawakkali bisa kaddara, ki tuna cewa RAI DA MUTUWA duk na Allah ne, kuma Allah baya barin wani domin wani. Idan sarki na da sauran shnaruwa a duniya dole ne ya tashi daga wannan cuta. Ni kan takaicina daya ne da ya hanamj ganawa da shi. Yanzu gashi zan tafi wannan yaki ba tare da nayi masa bankwana ba wata kila kuma shikenan har abada ba zamu sake ganin fuskar juna ba. Yayin da uzaifat yazo nan a zancensa sai itama shulaifa ta kamu da tsananin tausayinsa ta rungumeshi tana kuka shima yana kuka kamar ba zai daina ba. * * * * * * A can bangaren yarima ukashat da mahaifiyar sa muzaira kuwa, lokacin da suka zo yin bankwana ko kadan babu alamar wata damuwa a tare da fuskokinsu face Farin ciki. Kalma daya muzaira ta dubi ukashat tace dashi. Nasara na garemu ya dana. Ukashat yayi murmushi yace, Tabbas maganar ki dutse ce. Gama fadin hakan ke da wuya sai sukaji an sake buga tambarin tafiya. Nan take uzaifat ya sako mahaifiyar sa ya kama dokinsa ya hate. Dam ukashat da dakarunsa ne akan gaba don haka sai suka wuce izuwa kofar fita daga cikin birnin, sannan uzaifat da nasa dakarun suka take musu baya a lokacin da jama'ar gari da 'yan majalisar sarki suka busu da kallo har aka daina hangosu, sannan waziri ya sallama kowa fada ta watse ya zamana cewa babu kowa a wajen face mutum biyu rak. Ba wasu bane face muzaira da shulaifa. Koda suka dubi juna sai muzaira tayi murmushin mugunta a gareta sannna ta taho daf da ita ta tsaya suka kurawa juna idanu. Muzaira tace, to babban abokiyar gabata kiyi sani cewa lokaci yayi da zan dauki fansa akanki da mijinmu. Ina tabbatar miki da cewa nan da kwana bakwai rak sarki zai mutu, domin ba zai tsufa daga sharrin gubar dana bashi ya ci ba. Wannan yaki da 'ya'yan mu suka tafi ina tabbatar miki da cewa sanki ba zai dawo a raye ba, dana ne zai dawo cikin koshin lafiya, kuma kafin ya dawo sarki ya mutu, kin ga kenan dana ya zama sarki, Darul Husuf ta zama tamu. Idan babu sarki babu uzaifat ta ya ya zakiji dadin rayuwa da mu? Lallai a sannane zaki ga wulakanci da tozarci irin wanda baki taba gani ba a rayuwarki. Ko magen gidan sarautarmu sai ta fiki jin daraja. Lokacin da muzaira tazo nan a zancenta sai kawai raga shulaifa ta dubeta tayi murmushi tace, ka jahila wadda bata san fari da baki ba! Shin kin matane cewa RAI DA MUTUWA duk a hannun Allah suke? Ina mai tabbatar miki da cewar gubar da ki kabawa sarki yaci bata isa ta kasheshi ba face idan kwanan sa ya kare. Haka kuma duk irin gumun da za'ayi a filin yaki bai zama dole dana ya hallaka ba, zai iya tsira da rayuwar sa tinda Allah ne mai kashe wa da rayawa ba mutum mai najasa ba. Furucin karshe da zan miki shine, kiji tsoran karshen rayuwarki, domin duk wanda ya shika sharri dole ya girbi sharri. Koda gama fadin haka sai shulaifa ta juya ta nufi gidan sarautar tabar muzaira a tsaye tana kyalkyala dariya, domin ta tabbatar da cewa babu abinda zai han hakant ya cimma ruwa. Wannan shine abinda ya faru a birnin Darul Husuf bayan yarima uzaifat da yarima ukashat sun tafi yaki tare da DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu. ***** **** ***** Najibullah Muhammad 🥷🥷 ******* ***** ********* DAKARUN MUSULUNCI LITTAFI NA 1 MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Lokacin da rundunar DAKARUN MUSULUNCI rukuni biyu ta dau hanya sai suka wanzu suna ta tafiya ba tare da sassauci ba har sai da rana ta fadi. Babu abinda ke tsai dasu face sallah da cin abincin rana da sukeyi sau daya. Sa'adda rana ta fadi sai suka yada zango a cikin wani daji mai yawan sarkakiya, duhuwa da dogayen bishiyoyi. Shi dai wannan daji yana da mutukar kwarjini da ban tsoro, domin sai da kowa ya sha jinin jikinsa. Tabbas ba za a rasa mugayen abubuwa ba a cikin wannan daji fiye da shekaru arba'in baya fatake ma basa yarda su yada zango a bakin wannan daji, amma yau sai gashi DAKARUN MUSULUNCI sun tsaya a wannan waje. Watakila ko don sun ga yawansu ne ko kuma don sun yarda da Kansu ne? Amma a zihir dosowar magriba ce ta sa suka yada zango a wajen domin su gabatar da sallar magriba. Nan take salahuddeen da Abul shaja'a suka baiwa dakarun su umarnin a sassabe ciyayi masu tsawo, sannan a kunna fitilun itace kuma a kafa tantuna. Nan da nan kuwa aka cika wannan umarni, cikin kankanin lokaci. Bayan an tabbatar da cewa babu wani mugun abu a kusa sai aka tayarda sallar magriba. Da aka idar aka shafa addu'a sai aka shiga kokarin cin abincin dare. A wannan lokaci ne Abul shaja'a da yarima uzaifat suka shiga cikin tanti suka zauna aka kawo musu nasu abincin. Koda uzaifat yayi loma daya sai ya kasa ci gaba da cin abincin, ya sunkui da kansa kasa ya shiga tunani. Cikin alamun damuwa Abu shaja'a ya dafa kafadar uzaifat yace, ya Shugabana lafiya, tunanin me kakeyi haka? Uzaifat yayi gyaran murya yace, ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ina cikin tsananin damuwa bisa halin da na baro mahaifina a ciki na rashin lafiya, har ina jin kamar na koma da baya a sirrance na shiga har cikin turakar sa na ganshi. Koda jin haka sai Abul shaja'a yace, haba ya shugabana ai tunda sarki ya kafa dokar cewa kada dayan ku ya sake ya shiga cikin turakar sa face da izininsa ai bai kamata ka karya dokarsa ba, tunda ka kasance mai biyayya a gareshi tun daga kuruciyarka kawo izuwa girmanka. Ina son kasani cewa sarki na da babbar hujja wadda tasa ya kafa wannan doka babu mamaki idan ka karya dokar ka wargatsa masa wank shiri nasa. Sa'adda uzaifat yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla, ya ce, Wane shiri ne ga mutumin da ke kwance cikin jinyar ajali? Ya kai Abul shaja'a kayi sani cewa ban sa ran sarki zai kara kwana bakwai a duniya. Cikin mamaki Abul shaja'a ya dubi shi yace ya ya akayi kasan haka? Take hawaye ya zubowa uzaifat yace, ya kai Abul shaja'a ka sani cewa mahaifiyata tayi mafarki an ciyar da sarki guba tun data bani wannan labari sai nayi istihara aka nuna min abinda ta gani. Abinciken da nayi wajen likitoci sun tabbatar min da cewa in dai mutum yaci guba a cikin abinci abune mawuyaci ya wuce kwana bakwai a duniya. Abul shaja'a ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, sannan ya dubi uzaifat cikin matukar mamaki yace, wane ne ya baiwa sarki guba yaci. Uzaifat yace, a gaskiya bazan iya cewa komai ba sai dai mu jira izuwa lokacin da asirinsa zai tonu. Wai shin yanzu tafiyar kwana nawa zamuyi mu isa filin daga inda za'a kafsa wannan yaki tsakanin mu da mutanen birnin shumbul? Abul shaja'a yace, a Kalla sai munyi tafiyar kwana goma sha biyar sannan zamu isa. Ya kai yarima ka sani cewa karo da mayakan birnin shumbul ba karamin aiki bane, domin duk sa'adda muka gwabza yaki dasu muna shan tsananin wuya... In ba domin karfin addu'a ba zasu iya samun nasara akanmu. Tabbas a wannan karonina shakkar gamuwarmu da mutanen birnin shumbul saboda matsala biyu. Matsala ta farko itace, babu gwarzon mayakin mu wanda yafi kowa jarumataka a Darul Husuf, wato sarki da kansa. Matsala ta

Chapter 3 of 21