Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dubeta a nutse yace, " Hakika kina da babbar hujja wadda ta sa kika rabu da mahaifinki da kuma'yar uwarki. Yake wannan kyakkyawar budurwa, yanzu una batun abokan tafiyar da kika ce kin san inda suke, amma haryanzu baki sanar da mu ba. Haka kuma baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba, kamar yadda na bukata a baya?". Lafirat tayi gyaran murya tace, "A jiya da daddare, lokacin da kuka yada zango a cikin dajin nan, mai sarkakiya har kuka kafa tantuna kuka kwanta a ciki. Dukkanin ku kunyi barci face wadanda ke tsaitsaye a wajen tantin suna gadi. Sa'adda dare ya raba ne, sarki sha'aran ya turo wadansu zakwakuran aljanu dai dai adadinku suka zo suka kwashe mutanen ku gaba daya face ku biyun nan kawai. Abin da ya hana kuma a dauke ku shine, kafin kuyi barci kai Uzaifat ka tofa addu'a a cikin tantin naku a gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama da kasa. Karfin wannan addu'a da kayi ne tasa duk aljanin da ya doshi tantunku sai yaji kamar zai babbake. Bisa dole suka hakura suka tafi suka barku a cikin tantin. Bayan aljanun sun kwashe jama'ar taku sun yi sama da su, basu zame ko ina ba sai fadar mahaifina sarki sha'aran ta birnin shumbul. Tsananin ganin munin wadannan aljanu ne yasa jama'arku suka dimauce har suka kasa yin addu'ar daza su kubuta daga hannunsu. Suna ji suna gani aka kaisu har cikin fadar aka kuma daddauresu da sarkokin tsafi, kuma aka kukkulle bakunansu yadda bazasu iya motsa harsunansu ba bare suyi addu'a. Dayawa daga cikinsu ma sun haukace, wasu sun suma saboda yin arba da wadannan aljanu. Mutum dayane daga cikin jama'ar taku ba a daureshi ba da wannan sarkar tsafi. Wannan mutum ba kuwa ba kowa bane face mai jajayen tufafi, wato dan uwanka Ukashat. Lokacin da Ukashat yaga shi kadaine ba daureshi ba sai ya cika da mamaki, kuma ya zama dan kauye ya kama kalle kalle a cikin fadar mahaifina saboda ganin irin aljannar duniyar da aka shirya a cikinta. Ba zato ba tsammanin sai Ukashat yaga sarki sha'aran da sazirat sun baiyana a gabansa suna kyalkyala masa dariya. Cikin tsoro ya kura musu idanu ya kasa yunkurin komai. Sarki sha'aran ya dubeshi yace, "Ya kai Ukashat dan sarki uwaisul karni wanda ke burin zamowa sarkin Darul Husufa, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa mu ba zamu cutar da kai ba shiyasa ma muka tura aka daukkoku tun gabannin ku iso filin daga inda zamu fafata yaki daku. Ina mai tabbatar maka sa cewa koda an fafata wannan yaki, dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba, domin munfi karfin ku nesa ba kusa ba. Sarkinkune kadai ya zame mana matsala. Yanzu gashi mahifiyarka tayi mana maganin sarkinku, ta ciyar da shi guba wacce zata zamo sanadiyyar ajalinsa. Babban sirrin da baka sani ba shine, asalin mahaifiyar ka 'yar mu ce, run tana jaririya muka shayar da ita komai na al'adarmu, amma sai muka Kaita cikin birnin ku ta taso a hannun wani aminin sarkin ku a matsayin 'yarsa. Abinda bai sani ba shine, a ranar da matarsa ta haifi 'ya mace sai muka yi masa musanya da tamu ya ci gaba sa renonta a matsayin 'yar cikinsa. Tasa 'yar kuwa sai muka kawota nan muka ci gaba da renonta ta girma a matsayin mafita 'yar uwarmu. Wannan amini na Mahaifinku ba wani bane face likita Abu sharaz, wato kakana". Sa'adda sarki sha'aran ya zo nan a jawabinsa sai Ukashat ya cika da tsananin mamaki. Koda ganin haja sai sarki sha'aran ya sake tuntsurewa da dariya yace, Ai na san za kayi matukar mamaki bisa jin wannan labari, amma duk abinda nake so ka fahimta shine, abokin gaba yana iya bata shekara da shekaru wajen neman hanyar da zaibi yaga ya samu nasara akan abokin gabarsa. Ya kai wannan dan sarki kasani cewa na dade ina aika dakarun aljanu domin suje su baje birninku, amma ba dayansu da yake dawowa a raye. Lokacin da nayi bincike sai na gano cewa akwai wasu layu da aka binne a Kar kashin katangun da suka kewaye birnin ku guda hudu, tunda aka kafa ganuwar wannan birin wadannan layun suke, a cikin bincikena an tabbatar min da cewa indai ina so naci birninku da yaki har nasamu basarar shiga cikin birnin to dole ne sai an tone wadannan layu, sau shida ina tura dakarun aljanu domin su tone wadannan layu shima duk wa'yanda suka tafi basa dawowa. Daga baya sai na sake shiga halarar tsafi ta kwana bakwai, a sannan na gano cewa ba wanda ya isa ya tone wadannan layu face tsatson gidan sarautar birnin, Ma'ana sai jinin sarautar birnin. Tunda na fahimci haka na dukufa wajen ganin ya za'ayi na samu nasara samun tsatson jinin gidan sarautar, ina cikin bincike na ne aka nuna min fitowarku yaki zuwa filin daga inda aka saba gwabza yaki tsakanin mu. Nayi amfani da wannan dama bayan kunya da zango a cikin wancan daji nasa zakwakuran dakarun aljanuna suka je suka deboku. Kasani ya kai yarima na dade ina jiran irin wannan dama amma bansameta ba sai yanzu. Tabbas indai ka yadda muka hada hannu ka hada kai damu muka ci birninku da yaki kuma muka samu nasarar kashe Mahaifinku da dan uwanka to tabbas duk abinda ke cikin fadar nan ya hallata a gareka. Abu na biyu da ban fada maka shine duk wannan abinda ke faruwa da sanin mahaifiyar ka domin muna tura wasu aljanu suna sanar da ita ilimin tsafi a sirrance ba tare ya kowa ya sani ba, haka kuma mu muka tsara mata yadda zata kawo mana karshen sarkinku, kuma muka umarceta da lallai idan lokacin fita yaki yayi ta sa ka kasa jajayen tufafi. Kuma mun mata alkawari indai burinmu ya cika to kaine zaka zama sarkin darul husuf. Koda ji wannan batu sai Ukashat ya dubi sarki sha'aran yace, "Yanzu ina labarin 'yar likita abu sharaz koda jin wannan tambaya sai sarki ya dubi Ukashat yace, " Yar likita abu sharaz tana gidan gonata a cikin tsaro babu wanda ya isa yaje inda take face ni. Abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka ka kall daular nan duk takace duk abinda kake so kayi amfani dashi, ga kyawawan kuyangi da 'yan mata duk wanda kakeso ka kwanta da ita zata baka hadinkai ko da kuwa 'yata ce Sazirat. Koda jin wannan batu sai Ukashat ya daga kai ya dubi irin daular dake cikin fadar da irin kayan alatun dake cikinta, sannan ya daga kai ya dubi sazirat kawai sai ya duma wawa akan kayan abinci da abinsha da aka ajiye a gefen fadar a kan tebur, daga bisani kuma ya farwa sazirat suka aikata lalata. Wannan shine abinda ya faru ga dan uwanka sa abokan tafiyarku. Koda Lafirat tazo nan a zancenta sai hawayen takaici ya zubowa Uzaifat yace, yanzu kina nufin dan uwana ya gujemu ya hada kai da kafirai makiya Allah akan kawai ya gaji karagar mulki, kuma ya yadda ya aikata zina kuma yasha giya a matsayin sa na dan sarkin musulmi me mulkin babbar kasa. Tabbas sharrin zuciya yafi fa haka, to yanzu munji bayanin inda abokan tafiyarmu suke, amma kuma haryanzu baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba. Koda Lafirat taji wannan tambaya sai tace, ai nafada muku bukatata da kuma dalilin da yasa na ceci rayuwrku tun a cikin labarin da na baku ni da 'yar uwata. Bukatar kuwa itace ina so ku taimaka min na samu damar da zan iya hallaka mahaifina wato sarki sha'aran da kuma yar uwata sazirat, domin a binciken da nayi dole sai na hada kai da ku domin samun wannan nasara na cika burina. Sa'adda Uzaifat ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya yace damu dake duk bukatar mu irin daya ce bambancin dake tsakani kawai shine, ke kina sone ki kashe sarki da Sazirat don sun aikata wancan aikin, mukuma muna so ne muyi jihadi mu kafa turar musulunci a kasar. Abinda nake so dake shine zamu taimaka miki amma bisa sharadi guda daya, sharadin shine zaki mana rakiya izuwa kurkukun birninku inda aka kai abokan tafiyamu domin na ceto rayuwarsu, kuma na dauko 'yar likita Abu sharaz a cikin wannan gidan gona inda aka tsareta, inyaso sai mu koma can kasarmu domin muyi sabon shirin yaki. Kuma naje na ga halin mahaifina ke ciki, yana rayene ko ya mutu?. Koda jin wannan batu sai Lafirat ta kwalla ihu mai razanarwa, sannan tace, ai kazo min da abinda yafi karfina. Idan har na bika izuwa cikin birnin mu tabbas hallaka zanyi, burina bazai cika ba, domin ban gama shirye shiryena ba na tunkarar ubana da 'yar uwata, A kalla ina bukatar wata uku nan gaba kafin na kammala shirina. Shawarata agareku itace, ku koma da baya zuwa birninku kuje ku sanar da jama'ar ku abin da ya faru, domin kuyi gagarumin shiri kafin su sarki Sha'aran su iso birninku don yakar ku. Nima zan kawo gudunmawata idan yakin ya taso. Koda jin haka sai Uzaifat ya dubi Lafirat a cikin fushi yace, yake wannan basadaukiya kiyi sani cewa ni bazan koma da bayaba, ba tare da na kaiwa 'yan uwana dauki ba! Da dai na koma na tare da cikakken labarin su ba gwara na sara rayuwata. Idan har ba zaki iya yi mana jagora ba izuwa birnin shumbul to ki samu a hanya, in kuma ba haka ba sai dai mu ma mu warware alkawarinmu na baki had in kai. Yayin da Lafirat taji haka, sai hankalinta ya dugunzuma, tarasa abinda ke mata dadi a duniya, don haka sai ta kasa zaune ko tsaye. Tayi ta kai kawo a cikin fadar tana tunani. Najibullah Muhammad 🥷🥷🥷 Sai da ta dade a cikin wannan hali sannan tazo daf da Uzaifat ta tsaya tace, shikenan, na yarda zan yi muku rakiya. Amma zan tsaya a dajin karshe wanda daga shi sai birninmu. Zan yi jiranku anan tsawon kwana uku, idan kun sami nasara kun fito a raye sai mu rankaya mu dawo tare. Idan kuwa kwana uku ya cika ban ga dawowarki ba na san cewa kun hallaka sai na dawo izuwa nan gidana. Shin kun yarda da wannan sharadi? Kafin Uzaifat yace wani abu, sai Abul shaja'a yace, kwarai kuwa, mun yarda da hakan. Lafirat ta dubi Uzaifat tace, Daga bakin ka nake son naji wannan amsa. Uzaifat yayi murmushi yace, abinda Abul shaja'a ya fada shine a raina. Koda jin haka sai lafirat tace, tunda hakane yanzu yanzu zamu yi shirin wannan tafiya, domin idan muka yi sanyi lokaci zai shammacemu harsu sarki sha'aran su kammala nasu shirin su tafi izuwa birnin ku su ciku da yaki. Tabbas wannan aiki dake gabanku ba karami bane sai Kunyi mutukar zage damtse. Kuma ina tabbatar muku da cewa komai zai iya faruwa, walau kuyi nasara ko kuma ku hallaka. Uzaifat yace, tabbas mun san da haka. Ai matsoraci ba shi zama gwani, kuma da wata masifar gwara wani bala'in. Ina son ki sani cewa dukkan mai tsoron abokan gaba har abada ba zai taba samun nasara akansu ba. Ni nayi imani cewa akan gaskiya muke, don haka ubangiji bazai bari mu tabe ba, domin har kullum gaskiya na akan karya. Lafirat tace, na yarda da kai dari bisa dari, kuma tabbas na ga alama cewa ba zaka yi wasa da nasihar da mahaifiyarka ta baka ba. Wato ka kiyaye abu uku: gaskiya, amana da alkawari. Nima ina baka shawara akan ka rikesu da kyau, domin su ne kadai abubuwan da zasu ceceka a cikin birnin shumbul har ku sami nasarar ceto rayuwar 'yan uwanku. Kuma ku sami nasara sato yarima ukashat da Luhaira. Cikin tsananin mamaki Uzaifat ya dubi lafirat yace, yaya akayi kika san da nasihar da mahaifiyata ta bani? Lafirat tayi murmushi tace, kada ka damu zan sanar da kai anan gaba. Koda hama fadin haka sai ta mike tsaye daga kan karaga ta bada umarnin a shirya musu guzurin tafiya. Ba tare da wani bata lokaci ba aka shirya musu isashshen guzuri, sannan aka kawowa Uzaifat da Abul shaja'a dawakai guda biyu kosassu ababan sha awa suka hau a kofar gidan gaban wannan farin katon dutse. Ita kuwa lafirat sai ta shafi dutsen dai dai inda dokin nan nata ya raba, sai ga dokin nata ya sake fitowa ta cikin dutsen tamkar haifoshi akayi. Dokin ya daga kafafun sa biyu ma gaba a gaban lafirat yayi haniniya, sannan ya sauke su kasa ya na mai sunkui da kai al'amarin cewa yana gaisuwa da biyayya a gareta. Al'amarin da ya mutukar baiwa su Uzaifat da Abul shaja'a mamaki kenan. Amma da suka tuna cewa aikin tsafine, sai sukayi murmushi kawai. Nan take Lafirat ta kama wannan dokin nata ta hau tayi gaba. Su Uzaifat suka bita a baya. Sun fara wannna tafiya ne da duku dukun safiya, amma tun da suka fara tafiyar babu wanda yace uffan kamar kurame, har rana ta take. Koda Uzaifat ya fuskanci lokacin gabatar da sallar azahar yayi, sai yayi gyaran murya. Kamar Lafirat ta san bukatarsa, sai kawai Tana linzamin dokinta ta tsaya cak, suma suka tsaya, sannan ta waigo ta dubesu tace, Lokacin yin ibadarku yayine? Uzaifat yace, kwarai kuwa. Lafirat tace, ai Shikenan, faduwa tazo dai dai da zama, sai mu yi amfani da hoge daya mu jefo tsuntsaye guda da dutse daya. Maana kuyi ibadarku, kuma muci abinci, sannan muci gaba da tafiya. Gama fadin hakan ke da wuya sai lafirat ta sauka daga kan dokinta ta daureshi a jikin wata bishiya, sannan tayi shimfida a gefe daya ta kwanta don ta huta karkashin wannan inuwar bishiyar da ta daure dokin nata. Uzaifat da Abul shaja'a kuwa sai suka matsa gaba kadan suka yi alwala, sannan suka shimfida wani buzu suka yi sallar su. Abin ka da gajiyayye, lokacin da Lafirat ta kishingida akan shimfidarta don ta dan huta, sai nan da nan barci ya saceta bata sani ba. Bayan su Uzaifat sun idar da sallah sun fara addu'a sai suka rinka jiyo motsi kadan kadan acikin duhun ciyayi. Da farko sai suka yi zaton ko kananan dabbobin dajin ne suke sartu a wajen, amma da suka ji motsin na karuwa ko ta ina, kuma yana kara matsarsu, sai duk suka mike tsaye suka zare takubbansu suka kama kallon gabas da yamma kudu da arewa. Ba zato ba tsammani sai suka ga wadansu irin manya manyan birirrika ba adadi sun yi musu kawanya. Tunda su Uzaifat suka zo duniya basu taba ganin birirrika masu girma, kwarjini da ban tsoro irin su ba. Su dai wadannan birirrika suna da tsawo da kauri, kuma gasu bakake sidik, haka kuna munana na kyan gani. A tsaye suke tafiya da kafafunsu tamkar mutane, sai dai dukkaninsu sun rankwafa sunyi doro. Kowannesu na rike da katon sungumin ice mai girma fa nauyi, wand inda za a ajiye shi a kasa karfi goma majiya karfi ba zasu iya dagashi sama ba. Koda ganin wadannan birirrika sai jikin Abul shaja'a ya kama tsuma. Shi kuwa Uzaifat ko gezau bai yi ba, amma hankalinsa ya tashi Busa ganin tsananin yawan birirrikan, domin ya san cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi. Bayan birirrikan sun gama yi musu kawanya sai dukkaninsu suka tsaya kam basu motsa ba tamkar masu jiran umarni. Suma su Uzaifat sai suka ki yin wani yunkurin komai. Kwatsam! Sai ga shugaban birirrikan wani narkeken kato wanda duk ya fisu girma, ya ratso ta tsakiyarsu ya baiyana a gaba. Karfin takun sawayensa ne ya tashi Lafirat daga barci, kuma ya farka ne a dai dai lokacin da shugaban birirrikan ya baiyana. Koda lafirat ta kyallara ido tayi arba da birirrikan sai ta yunkura cikin mutukar zafin nama ta daka tsalle ta suri Uzaifat da Abul shaja'a da hannu dai dai tamkar shaho ya suri kaji biyu tayi sama da su tamkar tsuntsuwa. Bata dora ko ina ba sai kan dokinta. Take ta zare takobinta ta sare igiyar data daure dokin ta zabureshi da gudun tsiya, ya zamana cewa Uzaifat da Abul shaja'a na zaune a bayanta bisa dokin, wato su uku ne akan dokin. Nan fa aka kasa tsere tsakanin su da birirrikan kai kace karnuka dubu ne suka taso kyanwa daya a gaba. Duk da cewa dokin Lafirat na yi azababben gudu amma da zarar su Uzaifat sun waiga baya sai suga kamar a ko yaushe birirrikan zasu iya cimmusu, domin tazarar dake tsakanin su bata wuce namu biyar ba. Babban abinda ya daurewa su Uzaifat kai shine, irin azababben gudun da birirrikan suke mai ban alajabi. Har tashi sama suke suna bangazar bishiyoyi da duwatsu komai girmansu sai sun tarwatsa shi. Wato dai karfinsu ya wuce misalin. Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalisu Uzaifat kenan, suka tabbatar da cewa yau fa sun gamu da gamonsu. Ana cikin wannan tseren gudu ne Lafirat tace da su Uzaifat, ku gafarceni na sha'afa ban yi muku bayanin wadannan mugayen birirrika ba, ban taba tsammanin za su zo nan inda muke ba. Cikin rashin fahimta Uzaifat yace, to yanzu menene amfanin wannan tseren gudu da muke yi da su? Kina tsammanin cewa zamu iya guje musu ne? Lafirat tace, a'a ba zamu iya tsere musu ba, amma hikimata anan shine, kawai wurin da nake son mu isa inda basu da tasiri sosai, anan ne zamu iya yaki da su. Ko kadan su Uzaifat basu fahimci bayanin ba, don haka sai suka zubawa sarautar Allah idanu. Ana cikin wannan azababben tsere ne taga wasu birirrika masu nacin tsiya na neman cimmusu, don haka sai ta saki linzamin dokin nata ta juya da baya da jikinta gaba daya ya zamana cewa kirjinta da na Uzaifat sun hade. A haka ne ta ciro kwari da ga bayanta ta dana kibiyoyi biyar a lokaci guda ta damesu ta saki harbi. Sai ga kibiyoyin sun cake a idanun birirrika biyar masu nacin. Take suka zube kasa matattu. Nan fa taci gaba da zaro wasu kibiyoyin cikin mugun zafin nama tana ci gaba d harbi birirrikan. Al'amarin da ya mutukar baiwa su Uzaifat da Abul shaja'a mamaki mamaki kenan, domin basu taba ganin gwanin iya harbi ba da zafin nama kamar Lafirat. A haka ne Lafirat ta sami nasarar kashe birirrika sama da dubu, har suka dan razana suka rage kusantarsu, ya zamana cewa suna baya baya. Amma saboda naci basu daina binsu ba. Haka dai aka ci gaba da wannan tsere har aka ido bakin wani kogi. Kai tsaye Lafirat ta shiga kogin da dokinta har sai da taga ruwan ya zo iya rabin dokinta sannan ta tsai da dokin. Su kuwa birirrikan sai suka tsaya a bakin gabar wannan kogi suna gurnani da baki, dayansu bai shiga cikin wannan kogi ba, har shugaban nasu ya karaso. Nanfa aka tsaya ana kallon kallo tsakanin birirrikan da su Lafirat. A sannane Lafirat ta mai da kwari da bakanta baya sannan ta zare takobinta ta dubi Uzaifat tace dasu. Tofa sai ku shirya, anan ne zamu iya yin yaki da wadannan birirrika. Sirrin da yasa na jawosu nan shine, ko kadan basa son ruwa ya taba kansu, domin ko yaya ruwa ya taba kansu dimaucewa suke harma suna iya suma. Gama wannan jawabi ke da wuya sai suka ga birirrikan nan gaba dayansu sun daukko hulunan karfe sun rufe kawunansu. Al'amarin da ya mutukar razana su Lafirat kenan, har tayi ajiyar zuciya tace, shikenan tamu ta samemu, domin sai mun gajiya har wadannan birirrika sunci lagonmu. Koda jin haka sai Uzaifat ya dubeta yayi murmushi yace, kada ki damu da izinin ubangijin musulunci mu ne zamu ci lagonsu. Kafin Lafirat ta budi baki tace wani abu tuni birirrikan sun shigo cikin rugo cikin kogin. Uzaifat ne ya fara rugawa izuwa gare su yana mai kwala kabbara, ya taresu aka fara kwabsa azababben yaki. Yayin da suka yi mas **DAKARUN MUSULUNCI** LITTAFI NA 2 PART A 💯 NA- Abdul Aziz Sani Madakin Gini✍️ Typing:- Umar Farouq Zango🧑‍🍳 Posting: Najibullah Muhammad ( SARKIN YAKI 🥷🥷) MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.. A can birnin Darul Husuf kuwa, lokacin da kwanaki bakwai suka cika sai mutanen birnin suka taru a fada domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki a masa jana'iza, a wanna lokaci gidan sarautar yayi tsit ba'a jin komai face sautin iskar dake kadawa. A can kofar turakar sarki kuwa shulaifa da muzaira ne a gefe daya a tsaye yayinda sauran bayi da kuyangin gidan suma sukayi sahu sahu, kowa kansa a sunkuye, a gefe guda kuma sauran yan majalisar sarki ne suma sunyi sahu sahu kowa kansa a sunkuye. Bayan wasu wani lokaci sai kawai akaji karar bude kofar turakar sarki, sai kowa ya dago kai domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki. Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka ga sarki ya fito yana takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, bai doshi ko ina ba sai inda matansa suke, wato inda mulaifa da shulaifa ke tsaye. Yana zuwa gaban su ya tsaya sannan ya dubi muzaira yace kinyi mamakin ganina a raye ko, wannan kadan daga ikon Allah kenan, gubar da kika bani gashi bata kasheni ba. Koda gama fadin haka sai muzaira ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da sarki uwaisul karni yada matarsa muzaira ta sulale kasa sumammiya, sai ya dubi dakaru ya ce, ku dauketa ku kaita kurkuku ku kulleta. Nan take kuwa wasu dakaru biyu suka cika wannan umarni. Faruwar hakan ke da wuya, sai shulaifa ta ruga ga sarki uwaisul karni ta rungumeshi cikin farin ciki, tana mai godiya ga Allah da ya tserar da rayuwarsa. Sarki uwaisul karni ya janye jikinsa daga cikin na shulaifa, sannan ya dubi wani hadiminsa yace, kaje kayi shela a gari cewar kowa ya hallara a fada yau da yamma bayan sallar la'asar. Hadimin ya risina yace, an gama ya shugabana. Bayan anyi sallar la'asar kuwa, sai fadar ta cika ta batse da jama'a, ya zamana cewa duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan bil adama rututu, babu masak tsinke. Jim kadan da gama taruwar jama'a, sai ga sarki uwaisul karni ya fito Fes da shi yaci ado yana takawa a cikin koshin lafiya, a wannan lokaci yana sanye ne da fararen tufafi, farin rawami da farin takalmi fade, ya shafe gemunsa da sajensa da kunshi, sai kyalli suke

Chapter 5 of 21