Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daya dakarun babu wanda zai iya tarar sarki shaaran face ni. Haka kuma na yarda da sauran dakaruna a cikinsu akwai wadanda zasi iya taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Zan yi iya kokari na na ga na hallaka sarki shaaran sannan na fuskanci yar sa sazirat. Babbar matsalar mu itace ta yaya zamu iya sato yarima ukashat daga cikin sansanin yakinsu a lokacin da ba a yin yaki musamman cikin dare? Koda jin wannan tambaya sai yarima uzaifat da lafirat suka sake kallon juna a kari na biyu sukayi shiru. Lafirat tayi ajiyar zuciya tace, ni kadaice zan iya wannan aiki tunda na fiku sanin dukkan matakan tsaron da ke sansanin mutanen mu kuma zan iya amfani da makirci irin namu na mata. Amma ina bukatar kwana biyu rak nayi nazari akan wannan alamari. Sarki uwaisul karni yayi murmushi yace, na baki wannan dana amma ki sani cewa lallai a ranar kwana na nake son ki cika wannan aiki in yaso kashe gari sai kusan yadda zakuyi ku sulale ku tafi can birnin shumbul ba tare da kowa ya sani ba. Lafirat ta maida wa sarki martanin murmushi sannan ta ce, an gama ya shugabana. Kashe gari da safe bayan jamaar kowanne bangaren sun kintsa sai sarki shaaran yasa aka Busa kahon ci gaba da yaki. Nan take dakaru suka hau sahu sahu akan layi akan fuskanci juna. Mahaya layinsu da ban, mayakan kasa ma layin su daban. Bayan kowanne bangare ya gama shiri tsafi sai sarki shaaran ya zaburi dokinsa izuwa tsakiyar filin yakin ya tsaya. Koda ganin haka sai shima sarki uwaisul karni ya zaburi nasa dokin ya tunkareshi har yana shirin zare takobinsa domin a zatonsa sune zasi fara bude fagen yakin sai sarki shaaran ya dubeshi yayi masa murmushi yace, ai ba fitowa nayi ba domin mu yi yaki da kai ba. Nafitone domin kaima ka fito mu tsara yadda zaaci gaba da wannan yaki domin mu gaggauta kawo karshen yakin kuma mu kece raina a tsakanin mu. Idan har ka yarda da kanka kuma ka yarda da mayakan ka. Ina son mu fara fito na fito da mutum goma sha bibbiyu daga cikin jamaarmu su yaki juna a yau. Gobe kuma sai mu fito da mutum dari dari, jibi mutum dubu dubu. A ranar kwana ma uku mu ninka sau goma. A haka za acigana da yakin har mu karshi. Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni yayi shiru yana nazari, kawai sai yayi addua a cikin zuciyar sa yace, Allah ka bamu saa a cikin wannan sabone sako da wannan makiya namu yazo dashi kuma idan wani makircin yaki ya shirya mana kada ka bashi nasara akanmu. Koda gama wannan addua sai sarki uwaisul karni ya dubi sarki shaaran ya ce, na yarda da kaina kuma na yadda dakaruna. Nayi imani cewa ubangiji na zai bamu sa'a akanku don haka na amince da wannan tsaru da kazo dashi. Koda jin haka sai sarki shaaran ya tuntsire da dariyar mugunta irin tasu ta kafirai sannan yace, muje izuwa mahaukaci ya hau kura. *********************** Najibullah Muhammad *********************** Kawai sai ya kada linzami dokinsa ya juya da baya ya koma cikin jamaarsa. Shima sarki uwaisul karni ya koma cikin tasa rundunar. Jim kadan sai ga dakaru goma sha biyu daga kowanne bangare sun fito sun nufi tsakiyar filin yakin. Su dai wadannan dakaru goma sha bibbiyu kwararru ne masana yaki kuna abin kamar hadin baki domin kowanne bangare ya zabi dakaru mafiya sa'a a wajen yaki wadanda a tarihin yake yakensu ko rauni ba a tana ji musu ba. A bangaren mayakan sarki uwaisul karni kuwa, cikin wadannan mutane sha biyu akwau wani saurayin sadaukin gaske mai suna aba Huraira. Aba Huraira ya kasance kyakkyawan saurayi maabocin hidimar addini kuma yana da tarin ilimi na alkurani da sauran litattafai na addini. Shekarunsa gaba daya ba zasi fi ashirin da uku ba. Ya kasance makusancin sarki uwaisul karni domin kusan kullum ko yaushe suna tare dare da rana basa rabuwa face idan lokacin bacci yayi. A kullum aba Huraira ne ke kuka da shimfidar sarki uwaisul karni ya aminta dashi ainun yana matukar kaunarsa shima haka. A takai ce dai sun shaki da juna. Tun aba Huraira yana shekara goma sha daya yakewa sarki uwaisul karni wannan hidima ta kuka da shimfidarsa kuma tun a sannan aba Huraira ya taso da tsananin Farin jini a wajen yan matan birninsu amma har ya cika saurayi bai taba yin soyayya ba kuma bai yi tunanin yin Aure ba. Bisa wannan daliline wata rana sarki uwaisul karni ya kirawo shi suka kadaita a cikin turakarsa ya dubeshi yace, ya kai babban masoyina aba Huraira kayi sani cewa Allah ya yi maka gagarumar baiwa guda biyu. Ka kasance kyakkyawan saurayi kuma sadauki abin kwarance domin a duk fadin garin nan babu gaba da kai face yaya na uzaifat da ukashat. Abu ma biyu Allah ya baka tarin ilimi mai yawan gaske tun shekarunka basu kai haka ba. Me zai hana kayi aure da wuri ko Allah ya sa ka haifa mana wadansu yayaye irinka? Saadda aba Huraira yaji wannan batu na sarki sai ya sunkui da kansa kas cikin alamun kunya yana yake yace, ya shugabana kaine mafi sanina a duk fadin wannan gari namu. Ni maraya ne kuma tun ina da shekara bakwai a duniya suka mutu a wani yaki da akayi da mutanen birnin shumbul. Tun daga sannan nadawo hannunka ma zamo uwata d ubana. Bani da wani abokin shawara sama da kai. Ya shugabana wallahi ban isa ma zabawa kaina matar aure ba kuna duk zabin da ka bani shi zan karba. Koda jin haka sai hankalin sarki ya dugunzuma yace, haba ya kai aba Huraira kayi sani cewa kowacce zuciya akwai abinda yakan kawatu a cikinta. Blallai bane zabina yayi maka dadi ba. Dajin haka sai aba Huraira ya numfasa yace, ai kuwa har abada ni bazan iya yiwa kaina wannan zabi ba domin tutuni na dauki wannan alkawari a zuciyata cewar babu abinda zan gudanar da shi na rayuwata face bisa kan umarninka. Ya shugabana na sani cewa Allah ya baka baiwa ta ganin alamura da zasi faru a gaba cikin mafarkinka saboda haka kayi mini istihara bisa wannan alamari duk abinda da Allah ya nuna maka a kaina a cikin mafarkin ka zartar dashi a gareni amma ina rokonka alfarma guda daya. Lallai kadaka ka sanar dani abinda ka gani a cikin mafarkinka har sai ranarda alamarin ya faru. Kod jin wannan batu sai jikin sarki uwaisul karni yayi sanyi domin bai sao faruwar hakan ba don gudun kafata hango abinda bashi yaje son gani ba, amma sai ya yi ajiyar zuciya yace, to shikenan ya kai babban masoyina Allah ya za'a mana alherinsa. Aba Huraira yace, amin Sannan suka ci gaba hira har dare ya raba sosai. Koda aba Huraira yaga sarki uwaisul karni ya fara gyan gyadi daga zaune sai yayi masa sallama ya tafi izuwa nasa dakin. Fitarsa ke dawuya sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye yayi alwala sannan yazo ya gabatar da nafila rakaa biyu. Bayan yayi sallama sai yadaga hannayenasa sama ya roki Allah yana maicewa, Allah ka nuna min matar da aba Huraira zai aura a cikin baccina kuna ka nuna mini dukkan abubuwan alheri da kishiyarsa masu kusantar jamaata da birninmu gaba daya. Koda gama wanna addua sai sarki uwaisul karni ya kwanta. Kwanciyarsa ke wuya sai bacci ya daukesbi bai farkawa a sai daf da asuba. Yana farkawa kuwa ya tashi yaje yayi alwala ya tafi masallaci aka yi sallah da tare da shi. Bayan an idar da sallar ne ana cikin yin addua sai sarki uwaisul karni ya tuno da mafarkin da yayi a jiya daddare. Nan take alamarin mafarkin gaba daya ya dunga zuwar masa a cikin ransa tamkar a sannane yake mafarkin. Kawai sai aka ga hawaye ba zubowa sarki uwaisul karni daki daki kuma ya kasa daina zubar da hawayen. Alamarin da ya dugunzuma hankalin Lima da sauran jamaar dake masallacin kenan. Lima ya kasa hakuri ya dubi sarki uwaisul karni yace, ya shugabana me ya faru gareka kake ta faman zubar da hawaye haka?. Koda jin wannan tambaya sai sarki uwaisul karni ya sunkui da kansa kas yace, babu komai Liman. Kawai sai ya mike tsaye ya fita daa masallacin ya nufi gida. Daga wannan rana sai sarki uwaisul karni ya kwana bakwai yana kuka dare da rana kuma a tsawon bakwai bai sake yarda sun hada idanu da aba Huraira ba. Duk saadda aba Huraira yazo wajen sa sai ya sunkui da kansa kas ya dauki alkurani ya ta karatu har sai shi kansa aba Huraira ya tashi ya tafi don kansa sannan sai sarki uwana karni ya ci gaba da kuka abinsa. Shi kansa aba Huraira da ya ga sauyin yanayi a tare da sarki uwaisul karni a gareahi sai hankalinsa ya dugunzuma to amma da yaga sarki uwaisul karni ya saki ransa bayan kwana bakwai sunci gaba da hulda kamar yadda suka saba sai hankalinsa ya kwanta bai kara jin wata damuwa ba a ransa. Tun daga wannan lokaci kawo izuwa wannan rana da aba Huraira ya fito wannan yaki a cikin mutane gona sha biyu da aka zabo sarki uwaisul karni bai baiwa aba Huraira labarin wannan mafarkin da yayi ba akansa kuma shima bai tambayeshi ba. Lokacin da aba Huraira ya gyara damararsa kuna ya zare takobinsa cikin kuzari da yarda da akai sai yazo zai gifta ta gaban sarki uwaisul karni. Koda suka hada idanu sai sarki uwaisul karni yayi sauri ya sunkui da kansa kasa bai yarda ya dago sun hada idanu ba har aba Huraira ya isa tsakiyar filin yakin tare da sauran yan uwansa mutum sha daya. Bayan dakarun kafirai mutum sha biyu sun fuskanci DAKARUN MUSULUNCI sha biyu ana shirin Busa kaho don basu umarnin fara yaki, sai aba Huraira ya juyo da fuskarsa baya ya dubi inda sarki uwaisul karni ke tsaye sai kuwa suka hada idanu. Nan take sarki uwaisul karni ya ga kwalla a idanunsa amma kuma yana yi masa murmushi da wani irin kallo mai nuna alamun bankwana. Alamarin da ya mutukar baiwa sarki uwaisul karni mamaki kenan kuna ya karya masa zuciya bai san saadda hawaye y subuto masa ba har aba Huraira ya ga hawayen. A dai dai wannan lokaci ne aka busa kahon fara yaki, mayakan guda ashirin da gudu suka kacame kowa ya zabi abokin gwaminsa aka soma kwabsa azababben yaki, kura ta turnuke filin yakinn, karar karafliyar karafa ta da tartsatsin wutana tashi. Maza suka soma cakuduwa da kirazan damakansu na bangazar juna. Sai da aka shafe sa'a uku cur ana wannan gumurzu ya zamana cewa mutum ashirin da buyi duk sunyi ragas saura mutum biyu kacal suna fafatawa. Wadannan mutane biyu ba wadansu bane face aba Huraira da wani babban hadimin sarki shaaran wanda Shima a shekaru ba zai fi aba Huraira ba kuma ya kasance kyakkyawan saurayi mai kirar sadaukai ana kiransa da suna salhaf. Kamar yadda aba Huraira ya shaku da sarki uwaisul karni haka shima salhaf ya shaki da sarki shaaran harm shakuwar taci wacce ke tsakanin tasu aba Huraira da sarki uwaisul karni domin duk duniya babu mutumin da us isa ya baiwa sarki shaaran abinci ko abin sha yayi amfani da shi face salhaf. Babu wani sirri na sarki shaaran wanda salhaf bai sani ba, kuma bashi da wani abokin shawara sama dashi. Kai saboda tsananin yarda da kauna irin wacce sarki shaaran ke yiwa salhaf sai ya zamana cewa ya bashi gaba dayan sirrikan tsafinsa ba tare da lafirat da sazirat sun sani ba. Lokacin da gumurzu ya kai gumurzu tsakanin aba Huraira da salhaf ya zamana cewa karfinsu yazo daya sun kasa cutar da juna sai salhaf ya fara amfani da sihirinsa domin cutarda aba Huraira shikuwa aba Huraira sai kama karanta adduoin nema tsari don haka sai tsafin yaki tasiri a haka suka shafe sa'a guda a banza. Da kansu suka yarda takubbansu suka kacame da kokawa suka hau naushi da bugun juna. A wannan lokaci ne fa gadan ya sauya salo domin nan da nan suka hadawa junansu jini da majina kuma a sannane hankalin sarki uwaisul karni da na sarki shaaran ya dugunzuma ainun har suka kasa ci gaba da zama akan dawakansu ya zamana cewa sun sauko sun matsa daf da su aba Huraira kowanne na karawa nasa matayakin kwarin gwiwa da baki suna yi masu kirare da yi zuga. Nan ga samarin biyu suka kara kaimi wajen ragargazar juna. Har ta kaisu fmda cewa sun yiwa juna jina jina, jiri na dibarsu suna faduwa amma sai kaga sun sake mikewa sun kacame da sabon gumurzu. Wani lokacin kaga sun rukunkume juna da kokawa su fadi suna birgima su fadi nam su tashi can suka rinka birgima a kas. A wannan lokaci ne sarki shaaran d sarki uwaisul suka far kuka saboda ganin cewa kowannensu zai rasa masoyinsa, sukaji kamar su raba fadan amma da zarar sun dubi jamaarsu wadanda ke kallon gumurzun sai su kasa. Bayan aba Huraira da salhaf sun galabaitar da juna ainun har takai cewa basa iya mikewa tsaye a durkushe suke naushi da bugun juna sai kawai sarki shaaran ya zare wat wuka a jikinsa ya salhaf. Salhaf yayi sauri ya cafe wukar ta cakawa aba Huraira a tsaki DAKARUN MUSULUNCI Littafi Na Uku 3 Part F 💯👌 Marubuci Abdul Aziz Sani Madakin Gini✍️ Typing Umar Farouq Zango🤝 Posting Najibullah Muhammad 🥷🥷 Note: Ina yiwa dukkan jama'ar wannan gida masu bibiyar littatafan da muke kawowa barka da Sallah, tare da fatan kowannenmu yayi sallah lafiya Kuma cikin aminci Allah yasa haka Amin🙏 Bayan haka Ina Mai Kara Baku hakuri sakamakon dakatar da kowane posting da mukayi na kwana biyu, hakan ya faru ne a dalilin watan Ramadan Mai albarka da muka tsinci kanmu ciki, shiyasa muka zubar da gaba dayan makamanmu domin Neman yardar Allah ♥️💯🙏 Kuma Muna Fatan Allah yasa Muna daga cikin yardaddunsa, Allah Kuma ya tattara mu a cikin gidan Aljannah kusa da MUHAMMADAN RASULULLAHI SALLALAHU ALAIHI WASALLAM ♥️💯💯🙏🙏🙏 Muna yiwa kowa fatan Alkhairi. Naku har kullum wato Najibullahi Muhammad 🥷🥷🥷 Marubucin ya ci gaba da cewa:- Kawai sai aka ga salhaf ya kama kyalkyala dariyar mugunta. Ya mike tsaye da kyar yana dariyar. Bazato ba tsammani sai kuma aka ga Aba Huraira ya zare wukar daga cikinsa ya daka stalle daga inda yake durkushe tamkar biri ya dira akan salhaf kawai sai yasa wukar aka wuyansa yayi masa yankan rago. Nan take salhaf ya kife kasa matacce shima Abta Huraira ya fado kasa ya baje yana kakarin mutuwa. Lokaci guda sarki shaaran da sarki uwaisul karni suka ruga garesu kowa ya rungume nasa a kirjinsa suna matsanaicin kuka. Cikin matukar karfin hali Aba Huraira ya dubi sarki uwaisul karni yace, ya shugabana kayi sani cewa tuntuni Allah ya nuna mini a cikin mafarkina cewa ba zanyi aure ba har na mutu kuma a filin yaki zan samu shahada. Naji a jikina cewa kaima abinda ka gani ke nan a cikin mafarkin ka shi yasa ka kasa sanar dani. Shin abinda na fada gaskiya ne ? Ma za ka sanar dani kafin rai yayi halinsa domin kuwa dama alkawarin dake tsakaninmu cewar baza ka sanar dani mafarkina ba sai ranar da abin da ka gani a mafarkin ya faru. Koda jin wannan batu sai sarki uwaisul karni ya sake fashewa da kuka kuma ya dada kankame Aba Huraira a kirjinsa ya ce, Ya kai masoyina tabbas zamcenka dutsene, abinda kaga ni shi na gani a cikin nawa mafarkin. Gama fadin hakan ke da wuya sai Aba Huraira ya biya Kalmar shahada ya rasu. Nan take uwaisul karni ya kasa sakin gawar Aba Huraira yayi ta kuka kamar ba zai taba dainawa ba. Shima sarki shaaran haka yaci gaba rungumar gawar salhaf ya kasa tashi har sai da kowannensu jamaar sa suka daukeshi kuma suka da dauke gawarwawkin dake filin yakin A wannan rana sai da kowa yayi bakin cikin mutuwar wadannan kyawawan samari biyu. Uzaifat da Lafirat ma sun sha kuka mai yawa. Haka ma a can bangaren sai da ukashat da sazirat suka sha faman nasu kukan. Kai gaba dayan mayakan dake wannna sansanin yaki babu wanda bai zubar da hawaye ba saboda wannan gagarumin rashi da akayi. Kashe gari da safe kuwa aka sake ta busa kawon ci gana da yaki. Sai da aka fito da mutane dari dari daga kowanne bangare kamar yadda akayi alkawari. Ba tare da bata lokaci ba aka bada umarni wadannan mayaka dari biyu suka kacame da azababben yaki. Sa'a daya akayi ana wannan gumurzu sai gashi an kashe mutum tamanin daga cikin dakarun kafirai. Mutum ashirin sun raunana ainun yadda bazasu iya moruwa ba. Watakila ma anan gaba su rasa rayuwar su. A bangaren dakarun musulunci kuwa, mutum talatin kacal aka kashe aka raunana saba'in, kuma ba Irin raunin da zai zama sanadin ajalinsu ba. Dama anyi kaida cewa sa'a daya na cika za a tsaida yakin, walau anyi nasara ko baayi nasara ba. Don haka lokaci na cika aka busa kahon tsaida yaki kowanne bangare ya rugo ya kwashe gawarwakinsa da raunatattunsa. Lokacin da sarki shaaran yaga cewa wannan yakin an fisu rinjaye, gashi kuma na jiya ragas akayi, sai ya cika da tsananin bakin ciki mara misaltuwa, don haka sai ya sake kadaita da ukashat da sazirat cikin tantinsa yace dasu, ina mai yi muku tini da cewa gobe fa itace damarmu ta karshe bisa abinda muka shirya domin samun nasara akan wannan abokan gaba. Kun sani cewa a gobe mutum dari biyar biyar zasu fafata wannan yaki, don haka lallai a cikin su ne daya daga cikinku zaiyi badda kama ya sato mana gawar abokan gana guda daya yazo da ita ba tare da kowa ya ganshi ba. Kai ukashat lallai kaine zaka yi wannan aiki. Kuma kaine zaka sa tufafin gawar kaje can sansanin abokan gaba ka sato mana gimbiya Lafirat. Koda jin wannan batu sai ukashat yayi murmushi yace, ya shugabana na ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa. Na rantse da darajar burin zuciyata sai na sai na sami nasara bisa wannan aiki a gobe kuma sai na sato Lafirat na kawota nan gabanka. Da jin wannan batu sai sarki shaaran ya cika da Farin ciki ya kama kyalkyla dariyar mugunta. Daga can kuma sai dariya ta juye izuwa kuka har da hawaye. Alamarin da ya matukar baiwa ukashat da sazirat mamaki kenan. Cikin matukar damuwa sazirat ta dubi sarki shaaran tace ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka ? Sarki shaaran yayi ajiyar zuciya, sannan ya sa hannu ya share hawayen idanunsa yace, ya ke yata kiyi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan kuka ba face tunowa da masoyina salhaf. Na rantse da darajar tsafi idan muka sami nasarar wannan yaki sai anyiwa sarki uwaisul karni da duk iyalansa kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani bil adama ba a duniya. Koda jin wannan batun sai ukashat yaji ransa ya baci saboda jin cewa za'ayi wa mahaifinsa kisan gilla duk da cewa ko kadan baya kaunar mahaifin nasa a cikin zuciyar sa, amma kuma sai ya danne damuwarsa a cikin ransa bai nuna na a fuskar sa. Nan dai sazirat ta shiga rarrashin sarki shaaran tana bashi baki. Shikuwa ukashat sai ya mike tsaye ya fita daga cikin tantin ya barsu su biyu. A can sansanin mayakan sarki uwaisul karni, a cikin tantinsa hankalin uzaifat dana Lafirat a tashe yake domin tun daga lokacin da aka kashe Aba Huraira sai sarki uwaisul karni yashiga cikin wani irin hali na rashin ci da sha da kuma rashin baccin dare ida rana ya zamana cewa bashi da aikin yi sao jan carbi, tunani da zubar hawaye. Da kyar da Sidin goshi uzaifat ke lallabashi yaci dabino guda biyu rak, kuma ya karbi ruwa sau daya a tsawon rana guda. Alamarin da ya jefa kowa cikin damuwa kenan saboda sanin cewa rashin yin baccin sarki uwaisul karni ba karamar ila bace akan samun nasarar yakin. Dama idan har sarki uwaisul karni zaiyi bacci, to tabbas Allah zai nuna masa duk irin kaifin abokan gaba da zasu shirya a yakin da za'ayi kashe gari. Yanzu gashi kowa yasan cewa abu ne mawuyaci sarki uwaisul karni yayi bacci a daren yau saboda alhinin masoyinsa Aba Huraira kuma gashi yakin da za'ayi gobe mai zafine tunda mutum dari biyar biyar ne. Bisa wannan daliline uwaisul da lafirat suka tafi izuwa tantin da uwar mayu da hirama suke suka zauna tare da domin suyi shawara bisa irin matakin da ya kamata su dauka a yakin da za'ayi gobe. Kafin kowa ya fara magana sai Hirama tai gyaran murya tace, ina da uzuri guda daya. Cikin mamaki uzaifat ya dubeta yace, fadi uzurinki muji yake Hirama. Hirama tayi ajiyar zuciya tace, ina mai rokon alfarma guda biyu rak a wajenku. Alfarmar ta farko itace, ina so ku shigar dani cikin wannan addini naku yanzu take. Alfarma ta biyu ina so koda bayan wannan yaki ne mu koma can dajin Huzurul Has mu yaki iyayena mu kawar da su domin indai suna nan a raye ba zasu daina cin naman mutane ba dana aljanu kuma ba zasu bari a rinka ratsa dajin ba. Saãd uzaifat da lafirat sukaji wannan batu sai suka cika da tsananin Farin ciki. Uzaifat ya dubi Hirama yace, ke kuwa menene ya janyo hankalinki har kikaji kina son ki karbi addininmu? Hirama tace, ai na ga abubuwan alajabi da yawa a cikin tafiyata da ku. Duk balain da muka shiga sai na ga mun kubuta da zarar dayanku ya nemi taimakon ubangijin musulunci. Hakance tasa na tabbatar da cewa lallai wannan addinin shine addinin gaskiya domin babu wani tsafi ko wata dabara da ta isa ta cecemu. Koda jin haka sai uzaifat yayi kabbara, nan take uwar mayu ta biyawa Hirama Kalmar shahada ta maimaita sannan suka rungume juna. Uwar mayu na cewa, tabbas yanzu kin zamo cikakkiyar yar uwar mu. Da ni dake da uzaifat mun zama tamkar jini daya. Cikin alamun matukar damuwa uwar mayu ta dubi Lafirat tace, yake wannan jaruma me yasa kema bazaki karbi addinin Allah ba yanzu take domin ki zamo cikakkiyar yar uwarmu tunda dai kin aminta dashi? Kodajin haka sai lafirat tayi murmushi ta ce, kada ki damu yake kawata tabbas nima ina daf da samun wannan

Chapter 15 of 21