yi bukatata ta biya sai nayi. Ya kamata ka mika domin bazaku taba samun nasara ba.
Koda jin haka sai uzaifat ya daga takobinsa sama yace, tsakanina da makiya Allah babu gudu kuma babu ja dabaya.
Nima bazaniya kashe ka ba amma zan iya illataka.
Kuma da izinin Allah sai na kamaka da hannuna na damkaka ga mahaifinmu anyi maka hukunci dai dai da binda ka aikata.
Gama fadin hakan ke dawuya sai uzaifat ya afkawa ukashat suma suka kacame da azababbane yaki ya zamana cewa suka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da zafin nama da bajinta.
Kai da gani babu tambaya ka san cewa sadukantaka ce ta hadi da takwarar ta kuma kowanne na ji dan kansa.
Shikuwa sarki shaaran sai yaki saukowa daga kan cikinsa ya dubi uwar mayu da hirama a fusace ya daka musu tsawa yace, tur da wannan aiki da kuka aikata.
Ke uwar mayu hakika kin bani kunya kuma kimin bani mamaki yadda kananan yara sauya miki raayi cikin kankanin lokaci.
Ki tuna cewa shekara da shekaru kina zaune lafiya da yayanki a cikin gidanki ba a taba kashe miki kiwa ba, yau gashi an wayi gari kin rasa gaba dayan yayanki face guda daya JAL wanda ke goye a bayanki.
Yanzu wacce tina kika samu bisa karbar wannan addini na musulunci face kin rasa gidan ki mai kama da aljannar duniya kuma kin rasa yayanki, ina Zakije ki cigaba da rayuwa ma dadi a duniya.
Uwar mayu tayi murmuahi tace gaba dayan duniyar na ta ubangijin musulunci ce, don haka duk inda yaso zanje nayi rayuwata domin shine zai bani tsaro da kariya.
Babbar ribar dana samu bisa karbar addinin musulunci itace, na gane gakiya na saki karya.
Na fahimci cewa tsafi karya ne kuma zalunci haramune.
Abu ma biyu shine, na sani cewa idan na mutu anan duniya ubangijin musulunci zai kasheni nan gaba a Wata rayuwar daban, kuma zai yi min sakayya da gidan aljanna, idan har na bishi na kiyaye cikinsa.
Kaifa wane tanadi ne da a ban rayuwa ta nan duniya?
Kodajin wannan batu sai sarki shaaran ya bushe da dariyar mugunta yace, kece kika yi imani da wannan batu amma ni banyi ba kuma tabbas zan nuna miki kuskurenki kuma zan ga ta yadda ubangijin naku zai iya tserar daku daga masifata.
Shaaran ya dubi hirama yace, ke kuma kinyi babban gori ga rayuwar ki tunda har kika guji iyayenki kika jefa su cikin matsanaicin bakin ciki na har abada.
Koda jin haka sai hirama tayi murmushi tace, ai ba nice na fara yin abin gori ba yarka ce ta lafirat tafara tunda ta gujeka kuma ta tsaneka harma bata da burin da yafi ta kashe ka da hannunta, shin akwai abin da yafi wannan abin kunya da takaici.
Saadda sarki shaaran yaji wannan batu sai jikinsa ya kama tsuma zuciyarsa ta kufula. Cikin tsananin shammata ya daka tsalle sama daga kan dokinsa tamkar daga cikin baka aka cillashi.
Ya na a saman ya zare takobinsa ya kawai hirama mummunan sara a wuya da nufin ya filke nata kai.
Cikin tsananin zafin nama uwar mayu ta sure hirama daga inda taje tsaye, takobin sarki shaaran ta sari iska.
Uwar mayu ta ajiye hirama a bayanta ta ce da ita duk gumurzun da za'ayi kada ki sake ki ce zakiyi gaba da gaba da sarki shaaran.
Ban hanaki taimako na ba wajen yakarsa, amma dai kiyi taka tsantsan, nima zan tunkareahine da taimakon ubangijina, amma bani da karfin da zan iya tunkararsa.
Nan take uwar mayu ta daga kanta sama tace, ya ubangijin komai da kiwa ka sani cewa ni mai raunice akan sarki shaaran saboda haka ina mai neman taimakon ka da saarka akan wannan azzalumi mai sabonka a doronkasa.
A dai dai wannan lokacine sarki shaaran ya juyo ya sake fuskantar su cikin murmushi kuma ya kara rike takobinsa da hannu Baiyi yace, na gaisheki uwar mayu.
Tabbas kina da zafin nama, domin ban tana kai hari ba an tsallake sai wannan karon. Yanzu zan yakeku da dukan karfina da dukka dabarata sai na ga ta yadda zaku kubuta.
Kafin uwar mayu ta budi baki tace wani abu sai sarki shaaran ya sake afka musu ya rinka kai musu sara da suka cikin zafin nama da karfin. Uwar mayu ta wanzu ta mai karewa da hannayenta.
Duk saadda takobin sarki shaaran ta hadu da hannun nata sai kaji kamar karfe da karfe ne suka hadi, har tartsatsin wutane ke tashi.
Alamarin da ya mutukar baiwa sarki shaaran mamaki kenan domin ya san cewa babu wani abu da zai sara da wannan takobi bai rabe biyu ba ko da kuwa karfe ne ko dutse.
*********************
Najibullah Muhammad 🥷🥷
************************
Haka kuma ya san cewa a halin yanzu gaba daya sihirin tsafin uwar mayu ya karye tunda ta karbi addinin musulunci yaya akayi yanzu takobinsa ta kasa yi mata illa.
Haka dai suka ci gaba da gumurzu su sazirat da nasu sarki shaaran.
Kura ta turnuke sararin samaniya.
Karafkiyar karafa ta cika dodon kunne su kuwa sauran dakarun sarki shaaran suna sama kan tsauni sunyi cirko cirko suna more kallo kawai, kuma sun giwa filin yakin kawanya dayansu baiyi yunkurin sauko wa kasa ba.
Sazirat da lafirat sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna kaiwa junansu sara da suka, dayansu bai sami nasarar komai ba.
Koda ganin haka sai sazirat ta fara amfani da karfin sihirinta ta rinka watsa mata kibiyoyim tsafi masu da wuta.
Amma duk abinda ya doshi lafirat sai ka ga ya narke ya zama ruwa.
Ita kanta sazirat sai abin ya bata mamaki domin a saninta lafirat bata da karfin sihirin da zata iya kare kanta daga wadannan miganyen makamai.
Abinda bata sani ba shine, karfin addua ne yaje aiki.
Haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon wata rabin saar ya zamana cewa duk takubbansu sun dakushe, Shima sarki shaaran sai tsafaffiyar takobin nasa ta karye.
Cikin fushi yayi wurgi da takobin tasa.
Uzaifat da ukashat ma nasu takubban duk sun kakkarye sukayi watsi dasu. Nanfa akayi cirko cirko ana kallon juna.
Daga can sai sarki shaaran ya koma kusa da ukashat da sazirat ya tsaya.
A wannan lokaci Abul shajaa ne da sarkin yaki ne kadai ya rage suna fafatawa har ma kowannesu yayi nasarar yankar jikin dan uwansa.
Shidai Abul shajaa a kirjinsa aka sareshi wajen ya dare jini na zuba.
Amma saboda juriya sai yayi sauri ya daure kirjin da rawaninsa ya gyara tsayuwa.
Shikuwa sarkin yaki a cinyarsa aka dankara masa saran.
Shima wajen yayi rami sosai jini na shatata amma sai yayi sauri ya yage rigarsa ya daure cinyar tamu ya tsaya yana dingishi cikin juriya da bajinta.
Kawai sai suka sake kacamewa da sanin artabu. Ya zamana cewa wannan karon yaki suke mai ban tsoro domin kowa iya karfinsa yake yi. Kuma suna neman rayuwar junane.
Har ukashat ya yunkura zai kai masa dauki sai sarki shaaran ya tareshi yace, ai abin kunyane mutum biyu su rufarwa mutu daya shiyasa ma na hana dakaruna tayamu wannan yaki.
Yanzu mu zuba ido muga waye zai nasara namune ko nasu. Bayan an kashe daya daga cikinsu sai kuma mu gwanda yar kashi tsakanin mu da abokan gwaminmu, tunda makami da tsafi yaki yayi tasiri.
Tabbas yanzu ne na gane sai munyi da gaske zamu iya samun nasara akan wadannan mutane domin sihirinsu yana da matukar karfi.
Koda gama fadin haka sai sarki shaaran yayi shiru ya zuba ido akan gumurzun da su Abul shajaa suke.
Filin yakin yayi tsit bakajin komai face ihun Abul shajaa da na sarki yaki da kuma karar haduwar takubbansu.
Nan fa suka ci gaba da mugun artabu ya zamana cewa karfi yazo daya suka ci gaba da yiwa junan su muggan raunika.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda yanayin yakin nasu yake kasancewa. Da zarar daya yasamu nasarar yankan daya sai kaga dayan ma ya samu.
Nan da nan jikinsu yai kaca kaca da raunika, jini ya rinka zuba a jikinsu.
Tun suna tsaye sai da suka durkusa kasa suna ci gaba da saran juna. A karshe sai kowannensu ya cakawa kowa takobi a ciki. Takubbansu suka faso ta bayan su.
Sarkin yaki ya tsandara uban ihu ya fara kakarin mutuwa. Shikuwa Abul shajaa sai ya fara Kalmar shahada.
Cikin gudu uzaifat ya ruga ya dora Abul shajaa akan cinyarsa.
A hannunsa ya karasa cikawa ya rasu.
Nan take hawaye ya zubowa uzaifat ya rungume gawar Abul shajaa a kirjinsa.
A wannan lokaci ne shima sarki shaaran ya rugo fa gudu izuwa wajen sarkin yakinsa ya kankameshi yana girgizashi amma sai ya ga ko motsi bayayi. Harshensa ya zazzago kasa, idanunsa suka Kafe.
Koda ganin haka sai sarki shaaran ya takarkare ya kwada uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ihun nasa ya cika dajin gaba daura yana mai amsa kuwwa.
Nan take uzaifat ya dauke Abul shajaa ya koma can da baya ya ajiyeshi sannan ya dawo ya tsaya kusa da lafirat.
Shima sarki shaaran sai ya dauke gawar sarkin yaki ya kaita can gefe daya ya ajiyeta sannan ya dawo filin daga ya kanannade rigar hannunsa sannan ya cire dukan sauran makaman dake jikinsa ya watsar dasu gefe daya, kawai sai ya dunkule hannunsa biyu ya dagasu sama ya fuskanci uwar mayu da hirama yace, yanzu sai kuzo mu fidda raini ko.
Koda uwar mayu da hirama suka ga yadda kwanjin sarki shaaran ya kumbura kuma suka ga kirare jikinsa, suka ga duk jijiyoyin jikinsa sun kumbura, sai suka razana, jikinsu yayi sanyi zuciyar su ta karaya domin sun tabbatar da cewa ruwa ba saan kwando bane.
Shima ukashat sai ya dunkule hannunsa ya fuskanci uzaifat.
Sazirat ma ta dunkule nata hannun ta fuskanci lafirat.
Sarki shaaran ya dubi uzaifat yace, yanzu ne zami yakin gakiya da gakiya.
Na rantse da girman karagata dayanku ba zai tsira da rayuwar sa ba.
Gama fadin hakan ke da wuya sai shima sarki shaaran ya ruga kan uwar mayu da hirama ya rufesu da duka.
Naushin farko da yayiwa uwar mayu a fuska sai da gudan jini yayi fitar burgu daga bakinta, idanunta suka lumshe taga taurarin wuya. Tayi baya taga taga ta baje a kasa.
Ita kuwa hirama da kafa sarki shaaran ya nausheta a ciki, sai da tayi tsalle sama da baya ta fado kasa tana aman jini ta baki da hanci.
Kafin uwar mayu ta mike tsaye sai sarki shaaran ya ruga inda hirama ke kwance ya cafi wuyanta ya daga ta sama da hannu daya ya shaketa.
Nan da nan idanunta suka yi lubu lubu suka kada sukayi jawur, kafafunta suka kama wutsil wutsil.
A wannan lokaci uzaifat da ukashat suna mugun gumurzu suna ta naushin juna da bugun juna,duk sun hadawa junan su jini da majina.
Wani lokacin ma sai kaga sun kacame da kokawa sun rukunkume juna.
Wani lokacin kaga sun fadi kasa suna birgima wannan ya danne wancan wancan ya danne wannan, sukayi busu busu da kasa.
A bangaren sazirat da lafirat ma kuwa irin abinda ke faruwa da su uzaifat suma shi sukeyi, wato karfi yazo daya sun ragargazar juna, fuskokinsu duk sun kumbura saboda tsabar naushin juna, kuma kowaccensu jikinta yayi tsami har suma sun fara kokawa a kasa.
Lokacin da uwar mayu ta dawo cikin haiyacinta ta mike tsaye zumbur ta hango sarki shaaran rike da wuyan hirama ya shaketa tamau har kumfar wuya ta fara fita daga cikin bakinta.
Sai ta sake mikewa tsaye ta ruga kansa ta rufeshi da duka da dukan karfita.
Ai tamkar yarone ke dukansa ko juyowa baiyi ba ya kalleta, kawai sai yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta, kuma ya dada shake wuyan hirama da karfi, ya zamana cewa hirama da kyar take iya motsa kafarta guda, ta wuce mutuwa sai dai ace suma suma.
Koda uwar mayu taga haka sai ta daga hannayenta sama ta kwala kabbara da karfin tsiya tana mai neman taimakon Allah, kawai sai ta karci bayan sarki shaaran da faratanta. Take wajen ya dare gida takwas jini yayi tsartuwa.
Sarki shaaran ya kwala ihu ya dimauce.
Bai san saadda ya saki hirama ta fadi kasa ba.
Shima sai tsugunna kasa bisa gwiwoyinsa ya rintse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi.
Nan take wannan rauni na bayansa ya fara warkewa da kansa da kadan kadan, daga ya na sama raunin na bacewa tamkar bai taba wanzuba a wajen.
Cikin hanzari uwar mayu ta ruga da gudu izuwa inda hirama ke kwance ta fara yi mata firfita da hannayenta domin ta farfado daga dogon suman da tayi.
Kafin sarki shaaran ya mike tsaye daga inda yake durkushe ya sake kawo musu wani harin.
Ai kuwa a dai dai wannan lokacin da saunin sarki shaaran ya gama bacewa ne hirama ta farfado daga sogon suman da tayi.
Cikin zafin nama uwar mayu ta sunkuceta ta goya a bayanta ta daureta tamau da jelar jikinta sannan ta juya ta fuskanci sarki shaaran a lokacin da ya mike tsaye ya juya suka dubi juna.
Kawai sai sarki shaaran ya rugo da gudu izuwa kan uwar mayu cikin mugun mufi.
Kafin uwar mayu ta budi baki tayi wata addua ka ta nemi taimakon Allah sai kawai ta ga sarki shaaran ya baiyana a gabanta tsulum kawai sai ya sa hannunsa UA gabza mata nashi a fuska.
Saboda karfin naushin sai da ta yi katantanwa sau uku a tsaye sannan ta sukale kasa a sume. Hirama ta subuce daga bayanta itama ta baje a kasa.
Sarki shaaran ya sunkuyo da nufin ya kama kan uwar mayu da na hirama ya murde, kawai sai ya juyo ihun dakarunsa dake saman tsaunin.
Nan take yaga ana jeho dakarun nasa daga kan dawakansu suna gangarowa kasan tsaunin.
Wasunsu da kibiyoyi ake harbosu, wasu kuwa sai dai kaga an fille kawunansu.
Nan da nan saman tsaunin ya kacame da azababben yaki.
Ba wani bane yake wannan barnar ba face sarki uwaisul karni da dakarunsa na yaki wadanda suma adadinsu ya kai miliyan uku da dubu dari bakwai.
Da karfin tsiya sarki uwaisul karni ya tarwatsa dakarun sarki shaaran dake gabanta yana ragargazarsu har ya iso karshe tsaunin ya leka kasa.
Nan take yayi arba da sarki shaaran, suka kalli juna sannan taga yayansa uzaifat da ukashat suna ta tumurmusar juna.
Kuma ya hango lafirat da sazirat suna kwamarzuwa.
Kana ya hango gawar Abul shajaa a can gefe daya a kwance.
Koda ganin wannan alamari sai sarki uwaisul karni ya fusata ainun, zuciyar sa ta kama tafarfasa kamar zata kone.
Sai mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI 3 part D Don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma kayatacciyar Hikayar ✍️✍️🙏**DAKARUN MUSULUNCI**
LITTAFI NA 3
PART D✍️✍️
NA;ABDUL'AZIZ
SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷🥷
Bai san saadda yayi kundunbala ba ya dako tsalle daga saman tsaunin ya duro izuwa kasansa yana mai kwala kabbara duk da cewa nisan kasan tsaunin ya kai zirai arbain.
Ai kuwa kafafunsa na dira bisa kasa sai ya ruga izuwa kan sarki shaaran rike da takobinsa a sama.
Koda sarki shaaran ya hangoshi sai yayi alkafira a kasa izuwa inda ya watsar da wasu gajerun addunansa guda biyu ya suresu sannan ya tari sarki uwaisul karni suka kacame da sanin masifaffen yaki.
Sai gashi ana yaki a saman tsaunin a kasa ma anayi.
Yanzu dai gashi manyan kuraye biyu ne a kasa suke fafatawa wadanda suka kasance tsofaffin abokan gaba da suka zamana cewa KAR TA SAN KAR, kuma a shekara da shekaru kowannensu na son ganin bayan kowa amma lamarin ya taazzara.
Sarki shaaran da sarki uwaisul karni suka wanzu suna kaiwa junansu sara da suka cikin nuna kwarewa da sanin makama har tsawon sa'a daya da rabi, amma dayansu bai sami nasarar komai ba.
Sarki shaaran ya fara amfani da karfin sihirinsa domin ya hallaka sarki uwaisul karni amma sai abu ya gagara.
Haka dai suka ci gaba da artabu har wata rabin sa'ar ta sake shudewa ya zamana cewa duk sun gaji.
Da kansu suka rabu suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru.
A sannane sarki shaaran ya dubi uwaisul karni ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuska yace, ya kai abokin gabata kayi sani cewa kk yanzu rasuwa tatashi dan koli ya ci riba.
Na haddasa rashin kwanciyar hankali a gareka da jamaarka.
Na raba zumuncin dake tsakanin yayanka.
Kuma na sa dankara guda daya akan mugun TAFARKI na sabawa ubangijin ku.
Kuma ina tabbatar maka da cewa babu yadda za'ayi ku sami nasara a wannan yaki da mukeyi.
Kodai mu musami nasara akanku ko kuma ayi RAGAS.
saadda sarki shaaran yazo nan a zancensa sai sarki uwaisul karni ya yi murmushi yace,ya kai abokin gabanta kayi sami cewa zuciyata a wanke take tas babu wani takaici a cikinta bisa illar da kaimin.
Dana da ya bijire min ya hada kai da ku domin aga bayanmu yayi hakance saboda kwadayin duniya kawai domin baya son dan uwansa ya samu mulkin birnina.
Nayi sani cewa ya aikata babban laifi huda biyu na karya dokokin ubangijina.
Kuma akwai hukuncinsu da ya dace da wadannan laifuka.
Na sani cewa yanzu baka da wani buri wanda yafi kai da jamaarka kun dangana izuwa birnina har ukashat ya sami damar tono wadannan layu guda gudu da aka binne a karkashin katangunhudu na birnina.
To ina Tabbatar maka dacewa kaine abin tausayi a ganina tunda gashi yar cikinka bata d wani buri wanda yafi ta kasheka da hannunta.
Ina tabbatar maka dacewa ko yanzu ka umarci dana ukashat ya kasheni da hannunsa ba zai iya ba duk da cewa baya kaunata a zuciyar sa. Idan kuma kana musu ne to ka jarraba ka gani.
Saadda sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa ne ukashat da uzaifat suka baje a kasa suka daina gadan saboda tsananin gajiya suka kama haki da numfashi kamar tansu zai fita.
Sazirat da lafirat ma haka alamarin y kasance a garesu.
Koda ganin abinda ya faru sai sarki uwaisul karni ya daga hannunsa yana mai nuni ga jamaarsa da su janye daga filin yakin.
Nan take kuwa aka Busa kahon tsaida yaki sai dakarun suka fara guduwa daga filin yakin suna barin gawarwakin yan uwansu suka nufi can bakin wani kogin.
Har dakarun sarki uwaisul karni sun fara binsu suna rafkewa sai sarki uwaisul karni ya daka musu tsawa suka daina.
Shikuwa sarki shaaran sai yayi nuni da hannunsa izuwa ga ukashat da sazirat da kuma gawar sarkin yakinsa. Nan take suka bace daga filin yakin.
Har uzaifat ya yi yunkurin yin addua domin Allah ya baiyana su, sai sarki uwaisul karni ya hanashi ya dubi lafirat yace, tashi kuzo muje can kusa da inda su mahaifinki suka tsaya muma mu kafa namu san sanin wannan yaki bai kare ba sharar fage kawai akayi.
Ba tare da fargabar komai ba kuwa uzaifat da lafirat ta mike tsaye tazo kusa da uzaifat ta tsaya.
Sarki uwaisul karni ya kama hawa kan wannan tsaunin uzaifat da lafirat na biye dashi.
A sannane uwar mayu ta mike tsaye da kyar dama ta dade da farfado sannan taje ta dauki hirama ta sake goya ta a bayanta tabi su uzaifat.
Koda suka hau kan tsaunin gaba dayansu inda sauran dakarun yaki suke sai sarki uwaisul karni yasa aka baiwa uzaifat da lafirat dawakai suka hau.
A sannane hankalinsu ya kai kan uwar mayu da hirama.
Har uzaifat ya bude baki zai ambaci wani abu sai yaji uwar mayu ta ambaci sunan Allah kuma tayi godiya a gareshi bisa ceto rayuwar su da yayi ita da hirama daga hannun azzalumin sarki shaaran.
Kod jin haka sai sarki uwaisul karni yayi shiru baice komai ba.
Su kuwa sauran dakarun koda suka hango uwar mayu goye da hirama ta durfafo inda suke sai suka firgice suka hau dana kibiyoyi akan baka suka saitata.
Take uzaifat ya daka musu tsawa yace, akul dayanku ya harbeta domin yar uwarmu ce musulma.
Koda jin haka sai dakarun suka sauke bakansu kas suka cika da tsananin mamakin yadda wannan shirgegiyar aljanar ta karbi musulunci.
Ba tare da bata lokaci ba sarki uwaisul karni ya bada umarni a tafi can kusa da inda wannan kogin ya ke inda su sarki shaaran suka je suka tsaitsaya yace, ake a kafa tantuna. Amma a sami tazara ta a kalla zirai sabain a tsakani yadda dai suna iya hangosu suma haka.
Nan take kuwa aka bi umarni. Da izuwa aka iske tuni jamaar sarki shaaran sun gama kafa nasu tantunan.
Don haka suma dakarun sarki uwaisul karni sai suka hau aikin kafa nasu tantunan. Cikin kankanin lokaci suka kammal.
Gashi dai kowacce runduna tana hango kowanne bangare an zuba dakarun tsaro sun kewaye sansaninsu don gudun kada akawo farmakin sumame na bazato.
Lokacin da sarki shaaran ya shiga tantinsa ya zauna ya huta aka kawo masa abinci da giya yayi hanian sai ya tura aka kirawo masa ukashat da sazirat amma kafin su zo tuni yayi bincike a cikin hallarar tsafinsa.
Da shigowar ukashat da sazirat sai suka zauna a gefe daya suka fuskanceshi sukayi shiru. Sarki shaaran ya dubesu cikin nutsuwa tamkar bai sha wani abu na maye ba yace, abinda nakeso da ku shine ku saurara da kyau kiji abinda zan gaya muku domin idan kukayi kuskure guda daya a cikin aikin da zan baku yanzu shikenan dukkanin shirin mu ya ruguje babu wanda burimsa zai cika daa cikinmu.
Da farko dai ina so ku sani cewa ba wani abu bane yasa na tsaida wannan yaki ba face gano cewa idan aka ci gaba dashi bamu da nasara.
Domin sai an kasheni gaba dayanmu a wannan karon.
A yanzu haka daa cikin dakaruna mutum miliyan gudu an kashe mutum miliyan daya da dabi saura miliyan uku cif.
Ba komaine yasa suka sami wannan nasara ba face farmakin sumamen da suka kawo mana lokacin da jamaata ke bisa kan wannan tsauni ashe tuntuni suna labe a cikin dajin a kwance cikin duhuwa suna kallon mu sai bayan mun hau kan tsaunin sannan suka sadado suka afka mana.
A cikin binciken da nayi yanzu na ga duk wannan alamari a mudubin tsafina. Idan har muna son mu cisu da yaki kuma muje har can birnin Darul husuf mu karya katangarasu ya zamana cewa ki ukashat ka hau karagar mulki dole ne muyi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 21