Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels **DAKARUN MUSULUNCI** Na:- ABDUL AZIZI SANI MADAKIN GINI Typing:- UMAR FAROUQ ZANGO Posting Najibullahi Muhammad 🥷🥷 Marubucin ya fara da... A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude, anyi wan shararren sarkin musulunci wanda ya shekara dari da sittin akan karagar mulki, ana kiransa da suna Uwaisul Karni. Har tsufa ya riski sarki uwaisul karni matansa biyu kacal, kuma 'ya'yansa biyu dukkansu mazane kuma sa'annin juna. Ana kiran wadannan 'yaya nasa da UKASHAT da UZAIFAT. Mahaifiyar Ukashat itace uwar gida. Ukashat da Uzaifat sun taso da tarin ilimi, hankali da sanin yakamata, sannan kuma kowannesu ya kasance sadauki kuma Barde dodon maza a filin yaki, wanda har ta kai cewa an kasa banbance wanda yafi wani karfi da jarumta a tsakanin su. Ya yin da tsufa ya riski sarki uwaisul Karni sai matansa shulaifa da muzaira suka fara kisha akan kowacce tafi son danta ya gaji sarki. A dalilin haka ne suka dukufa wajen ziyartar malamai domin bukatarsu ta biya. * * * * * * A can nesa da birnin Darul husuf, wato birnin sarki uwaisul karni, akwai wata babbar kasa ta kafirai wacce ta gagari uwaisul karni, domin sau tara yana yaki da su amma sai dai ayi KARE JINI BIRI JINI. Sunan kasar SHUMBUL, kuma sunan sarkin su SHARAN IBINI NUKAIB. Lokacin da sarki uwaisul karni ya fahimci cewa ukashat da uzaifat sun tada hankalin su akan su gajeshi saboda kowanne ya dauki zugar mahaifiyarsa sai ya kirasu yace dasu. "Ya ku 'ya'yana kiyi sani cewa bani da wani buri wanda yafi naga naci birnin shumbul da yaki kafin cikar ajalina, bisa wannan dalili ne na umarceku da kije kowanneku ya shirya DAKARUN MUSULUNCI nasa mataimakansa wadanda basa yin aiki da alfasha basa shan giya, basa yin zina, wadanda basu taba sabon Allah ubangijin Muslinci ba, kowannenku ya taro nasa mataimakan, duk wanda ya sami nasarar wannan yaki akan kasar shumbul daga cikinku shi zai gajeni". Koda jin wannan batu sai uzaifat da ukashat sukayi murna, suka yi farin ciki da jin wannan batu. Domin lokacin yayi da zasu nunawa duniya cewa musulunci ba kanwar lasa bane. Anan suka yi alkawarin lallai sai sun cikawa mahaifinsu burinsa. Nana take kowannensu ya fara shirye shirye, suna masu shirya dakarun yaki kuma DAKARUN MUSULUNCI. Dama kuma sarki uwaisul karni ya basu izinin kowannesu ya tara Dakaru dudu dari uku kadai. Ukashat ne ya fara hada tasa rundunar inda yayi Saudi ya zabe dukkan in manyan Dakarun kasar wadanda ake takama dasu a fagen fama, wato wadanda suka fi jarumta, juriya da jajircewa. Lokacin da ukashat ke zabo wadannan zaratan dakaru bai yi la'akari da bayanin mahaifinsu ba na cewa lallai su zabo daga masu kwatanta gaskiya da tsoron Allah. In dai kawai ya fahimci cewa mutum Barde ne kawai sai ya zabeshi. A lokacin da uzaifat yazo zai zabi nasa dakarun sai ya ga Ashe ukashat yayi masa shigar sauri, ya kwashe manyan baraden kasar. Hatta sarkin yakin kasar kuwa salhaddeen ayubi. Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan, har yaji gwuiwarsa tayi sanyi, amma duk dahaka bai fasa zabo nasa dakarun ba wadanda basu kasance zakwakurai ba, amma kuma suna da karfin imani gami da tsoron Allah. Ya fitar da shugaba a cikinsu wanda babu kamarsa a jarumta ana kiransa da suna Abuk shaja'a. Bayan uzaifat ya gama hada wadannan runduna wadda Abul shaja'a ke jagoranta sai suka fara fita bayan gari kullum suna bawa Kansu horon yaki domin su tabbatar da cewa anyi kyakkyawan shiri kafin zuwan ranar da zasu fara fita sutari abokan gaba. A can bangaren dakarun ukashat kuwa, ko sau daya basu taba tunanin su fita yin horo ba saboda sun yarda da Kansu, sun san cewa ko daga barci suka tashi zasu iya tarar yaki. A ranar da su uzaifat suka cika kwana bakwai suna bawa Kansu horon yakan ne labari ya riski su ukashat. Al'amarin daya basu dariya kenan. Ukashat ya dubi sarkin yaki salahuddeen ayubi cikin murmushi yace, "ya kai dirkar Darul husuf kaji cewa su uzaifat sun dukufa wajen baiwa Kansu horon yaki har tsawon kwana bakwai kenan yau. An ya kuwa ba ma kai musu ziyarar ba zato ba, domin mu auna iyakar kokarinsu da namu. Ka san fa ance dan hakin da ka raina shike tsone maka ido. Kada fa muyi sakaki su bamu mamaki, wato su sami nasarar wannan yaki da za'ayi da mutanen birnin shumbul". Koda jin wannan batu sai sarkin yaki salahuddeen ayubi ya bushe da dariya yace, 'Ranka ya dade in banda abinka yaya gara zatayi da zago? Shin ka manta da yawan mayakan birnin shumbul ne da Kuma yawan zakwakuran dakarunsu ne, ai duk irin horon da su Abul shaja'a zasu samu ba zasu taba samun nasara ba a Kansu. Mu kanmu sai munyi da gaske, munyi tunanin sabbin dabarun da yakamata muyi amfani da su. Ka sani cewa a cikin mayakan birnin shumbul akwai wani gawurtaccen barde daya fara fitowa a yaki a shekara uku baya. Wannan barden shi nafi shakka fiye da kowa, kuma babu yadda za'ayi mu sami nasara akan mutanen shumbul face mun gama da bareden". Ya yin da ukashat yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace, "Mene ne sunan barden, kuma ya za'ayi na shaidashi idan muka fita yakinin? Inaso ka barni da shi, ina tabbatar maka da cewa ni zan kashe shi komai karfin jarumtar sa". Dajin wannan batu sai salahuddeen ayubi yai dariya yace, Ya kai yarima ukashat ka sani cewa sau uku ina tarar wannan barde fa muna yin ragas, ban taba samun nasara akansa ba, Shima haka. Tayaya kake tsammanin cewa kai zaka iya da shi?. Ukashat yayi murmushi yace, ina da tabbacin cewa zan iya samun nasara akanka, ka ga kenan idan har zan samu nasara akanka lallai zan sami a kansa. Na fuskanci cewa saboda bamu taba fita yaki ba ni da uzaifat shi yasa ba a san iyakar jarumatarmu ba, sai iya wadda aka ga mun nuna anan gida. Idan kana da shakkar abin da na fada yanzu mu jarraba fidda raini yanzu ni da kai. Sa'adda sarkin yaki salahuddeen ayubi yaji haka, sai ransa ya baci, zuciyar sa ta kama tafarfasa yace a ransa, Yanzu wannan karamin taron ukashat da ya girma a gabana shine yaje gamin cewa zai iya karo dani? Lallai kuwa yau zan nuna masa cewa bakin Rijiya ba wajen wasan yaro bane. Koda gama aiyana hakan aransa sai ya zare takobinsa ya sauko daga kan dokinsa a fusace ya nufi ukashat. Abinda ya daurewa sauran dakarun kai shine, ukashat bai zare tasa takobin ba bare ma ya sauko daga dokinsa, kawai sai ya ci gaba da zamansa yana mai sauraron isowar salahuddeen. Ai kuwa salahuddeen na isowa sai ya kai masa wawan sara a wuya. Cikin mutukar zafin nama ukashat ya sunkuya takobin ta sari iska. Kafin salahuddeen ya sake kai wani saran tuni ukashat yayi tsalle sama daga kan dokinsa tamkar an janyeshi da kugiya kawai sai ya jerawa salahuddeen duka da kafa a kirji sau uku yana a Daman kamar tsuntsu. Duk da cewa salahuddeen murjejen kato ne mai kirar sadaukantaka sai da yayi baya taga taga zai fadi, amma saboda taurin rai da zuciya sai da yadage ya tsaya cak a waje guda. A sannane fa gaba daya dakarun suka kaure da kabbara bisa mamaki ganin jarumtar da ukashat yayi. Shi kansa salahuddeen yayi mamaki, duk da cewa ya sha ganin yadda ukashat da uzaifat ke dafawa maza gumba a hannu a cikin gari, amma da yake suna shakkarsa sai yayi tsammanin cewa ba zasu iya karawa da shi ba. Abinda bai sani ba shine kawai suna girmama shine a matsayin sa na sarkin yaji kuma basa san su kunya tashi. Ukashat ya diro kasa a bayan salahuddeen ya zare tasa takobin suka fara zagaya juna ana kallon kallo tamkar zaki da zaki zasu fafata. Kawai sai suka kacame da azababben yaji suna masu kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta masu jikin karfe saboda sauri. Nan fa dakaru suka zuba ido suna kallon ikon Allah suna alajabi, domin a tarihin sadaukantakar salahuddeen ba a taba samun mutumin da ya fafata da shi ba tsawon dakika Dari da tamanin ba tare da ya kishi kasa ba, sai wannan bakon barde na birnin shambul, amma yanzu gashi ukashat na neman gagararsa. Abu dai kamar wasa sai gashi an sake shafe rabin sa'a ana fafatawa amma duk a tsawon lokacin ko sai daya salahuddeen bai samu damar yankar jikin ukashat ba ko sukarsa. Alamarin da ya kara fusatashi kenan ya kara kaimi. Yayin da ukashat yaga haka sai yayi wata irin alkafira da baya baya ya nisanta da salahuddeen ya tsaya daga nesa kadan fuskarsa cike da murmushi yace, ya kai sarkin yaki kayi sani cewa na baka dama har tsawon sama da rabin sa'a baka iya cutat dani ba, to yanzu ganinan nisa kanka nima zan yi amfani da tawa damar. Mu hadu a DAKARUN MUSULUNCI na daya 1 part B don Jin CIGABAN WANNAN KASAITACCEN KUMA GAGARUMIN LABARI 🩷🩷🩷🩷 Najibullah Muhammad 😃**DAKARUN MUSULUNCI** Littafi na daya (1) Part B MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI. TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO Posting: Najibullahi Muhammad 🥷🥷 Marubucin ya cigaba da cewa... Kafin sarkin salahuddeen yayi wani yunkuri tuni ukashat ya daka tsalle ya dira a gabansa kamar dau koshi akayi aka ajiye. Banga ya shiga kaiwa salahuddeen mummunan sara da suka. Tsakanin karfin harin yasa salahuddeen ya kasa maida martani, sai kawai yaci gaba da kare kai. A duk sa'adda ukashat ya samu damar cutar da salahuddeen sai yaji cutar dashi dan yayi dariya kawai. A haka suka cigaba da artabu har ukashat ya kaishi kasa kuma ya huge takobin sa ta fadi kasa ya tsirashi da tasa. kawai sai sauran dakarun suka rude da kabbara suna yiwa ukashat jinjina cikin matukar alajabi. Ukashat ya juyawa salahuddeen baya ya tafi izuwa dokinsa ya kama ya hau, sannan ya juyo ya dubeshi yace, ku biyoni a baya mutafi izuwa bayan gari inda su uzaifat ke baiwa Kansu horo. Gama fadin hakan ke da wuya sai ukashat ya sakarwa dokinsa linzami ya sukwaneshi da gudu ya bar harabar gidan sarautar. Cikin alamun kunya da matukar takaici sarkin yaki salahuddeen ya mike tsaye ya hadu kan nasa dokin a lokacin da kwallar takaici ta ciko idanunsa, amma kuma da yaga sauran dakaru sun tsaitsaya a bayansa sai daya hau dokinsa yayi gaba sannan suka take masa baya sai yaji dadi a ransa, domin ya fahinci cewar haryazu yana da sauran kina da martaba a idanunsu duk da cewa yarima ukashat ya kaskantar dashi a gabansu. Sarkin yaki salahuddeen da sauran dakaru suka zaburi dawakansu a guje har suka cimma ukashat, ha zamana cewa ukashat da salahuddeen sun kusan hada kafada. A sannane ukashat ya dubi salahuddeen yace Ka gafarceni ya dirkar darul husuf, kayi sani cewa bani da niyyar kaskantar da kai akan idanun kowa. Koda jin wannan batu sai salahuddeen yaji zuciyarsa tayi sanyi ya maida masa martanin murmushin sannan yace, ya shugabana ai kome kamin bazai taba zama laifi ba, domin kaine sarkin gobe. Fatana shine idan har bukata ta biya nazamo makusanci a gareka. Sa'adda ukashat yaji haka sai ya bushe da dariya daga can kuma sai ya hade fuska yace, idan har Ka taimaka min wannan runduna tamu ta ci birnin shumbul da yaki nayi maka alkawarin kaine zaka zama wazirina yayin da na zama sarkin darul husuf. Koda jina haka sai salahuddeen ya cika da tsananin Farin ciki, ya kara bakinsa daf da na yarima yace ukashat yace, ai kuwa koda zan kace hanya saina kace muddin bukatar mu zata biya, saboda haka ka Kwantar da hankalika komai rintsi da tsanani kaine zaka hau karagar sarki, ba dai uzaifat ba sai dai idan bana numfashi a doron kasa. Dajin haka sai shima ukashat ya cika da murna suka ci gaba da hira cikin nishadi har suka iso bayan gari inda su yarima uzaifat suka yada sansani suka kafa tantuna. Da zuwa kuwa sai suka iske uzaifat tare da dakarunsa yana tsaye a tsakiyarsu sunyi masa da'ira yana koya musu yadda ake sarrafa takobi a tsakiyar abokan gaba, harma yana umartar wasu daga cikinsu da su afka masa. Da zarar sun afka masa sai su ga ya tarwatsasu nan da nan. Suna cikin wannan hali ne kawai sai suka hango Karar dawakan su ukashat daga nesa kadan don haka sai suka tsaya suna jiran isowarsu don su ga ko su waye. In ba don ma sunga cewa daga cikin gari suka fito ba da sai suyi tsammanin ko abokan gabane suka kawo musu farmakin sumame. Lokacin da su ukashat suka karaso aka ga juna sai mamaki ya kama uzaifat ya dubi ukashat yace, lale marhabun da dan uwa rabin jiki. Shin kunzo ne ku bamu gudunmawa bisa kokarin da mukeyi?. Ukashat ya kada kai alamar cewa ba wannan ce ta kawo su ba, sannan yace munzone muyi leken asirinku mu saci irin salon halin da kuka tanada. Koda gama fadin haka sai mamaki ya kama uzaifat da jama'arsa, domin sun san cewa basu fi su ukashat iya yaki ba, asalima ko tafin hannunsu basu kai ba. Ukashat da jama'arsa suka bushe da dariya, al'amarin da ya Sosa zuciyar uzaifat kenan, amma sai ya dubi ukashat yace, ya kai dan uwana ina son kubar wajen nan kau da jama'arka ku kyalemu muyi abinda ke gabanmu mu da ku kiwa tasa ta fishsheshi. Ukashat ya gyada kai yana mai yin murmushin mugunta yace, Bazai yiwu muzo har nan kuma mu tafi a banza ba . munzone domin a bambance tsakanin Yaya da tsakuwa, asan wadanda ya kamata a tura yaki ba sai an tsaya bata lokack ba. Ciki. Fushi uzaifat ya dakawa ukashat tsawa yace, wannan ai zancen banza kakeyi, domin kuwa ba haka Abbanmu ya shirya ba. Cewa yayi ni da kai kowa yashirya dakarun sa daban, kuma dukkaninmu zamune wannan yaki bai zaba ba. Ukashat yayi dariya sannan yace wannan gaskiyane haka abbanmu ya tsara amma kuma nima yanzu nazo da nawa tsarin kuma dole haka za'ayi. Koda gama fadin hakan sai ukashat ya dubi su sarkin yaki salahuddeen yace, ku afka musu ku maishesu nakasassu yadda bazasu iya fita yaki ba. Koda jina wannan umarni sai su salahuddeen suka zare makamnsu da nufin au afkawa su uzaifat, amma sai uzaifat yayi wuf ya sha gabansu yace, ku fara gamawa dani kafin su. Da jin haka sai su salahuddeen suka dan ja baya domin sun san cewa abune mai hadarin gaske idan dayansu ya kuskura ya taba lafiyar yarima uzaifat. Ukashat ya dafawa su salahuddeen tsawa ya ce, me kuke jirane da shi? Ku afka masa kawai, umarnina ne ba umarnin kowa ba. Cikin sanyin jiki da alamar karayar zuciya sarkin yaki salahuddeen ya dubi ukashat yace, ya shugabana kai ma ka san cewa duk wanda ya taba yarima daga cikinmu zai fuskanci fushin sarki. Ina ganin cewa zai fi kyau muhakura da wannan shiri mu koma cikin gari. Koda jin wannan furuci sai ukashat ya fusata, ya zare takobinsa ya nufi uzaifat gadan gadan yana mai cewa ni bari na nuna muku misali kuga zahiri, don ku san cewa babu wargi a cikin lamarina. Lokacin da uzaifat yaga dan uwansa ukashat ya taho kansa rike da takobi tsirara cikin mugun nufi sai shima ya zare tasa takobin ya tare shi a lokacin da gaba daya dakarun dake wajen suka nutsu suka tattare hankalinsu kowa a akan su. Yan uwa biyun na haduwa suka kaure da azababben artabu, ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka ciki zafin, juriya da bajinta. Wohoho! Idan sadaukantaka ta hadu da takwararta dole ne idanu su more kallo. Lokacin da wannan gumurzu ya dan yi nisa sai hankalin gaba daya dakarun dake wajen ya dugunzuma ainun, domin tsananin ya kai tsanani, ga dukkan alamu ba za a gama lafiya ba ba tare da an salwantar da rayuwar daya ba. Domin yadda suke kaiwa juna gari tamkar kafiri da musulmi sun hadu, kowannensu bil hakki yaje fadan kuma a fusace suna kokarin ganin bayan juna. Koda aka kara shafe rabin sa'a ana wannan fafatawa sai sukaja da baya a lokaci guda suka ba da tazarar taku biyar biyar, sannan suka rugo ga juna cikin mugun nufi. Tun kafin su hadu hankalin kowa dake wajen ya kara dugunzuma, domin an san cewa in dai aka hadu karon ba zaiyi kyauba. Koda ya rage saura taku daya su hadu sai suka daka tsalle suka yi sama a lokaci guda suka kaiwa juna sara da takobi. Kowa sai ya sami nasara suka yanki damatsan hannayensu, jikinsu ya dare jini ya zuba suka rikito kasa suna masu dage raunikan. Amma saboda juriya da jarumataka basu nuna wata gazawa ba, sai kawai suka sake yunkurawa suka ruva ga juna. Cikin zafin nama sarkin yaki salahuddeen ya daka tsalle ya dira a tsakiyarsu, bai bari sun hadu ba. Cikin fushi ukashat ya dakawa salahuddeen tsawa yace, saboda me zaka katse mana wannan fadan?. Salahuddeen ya risina yace ka gafarceni ya shugabana, kayi sani cewa idan muka bari kuka lahanta junanku sosai fushin mahaifinku zai tabbata akanmj. Idan ka ga munbarku Kunci gaba da wannan fada sai dai idan bama numfashi a doron kasa. Sa'adda ukashat yaji wannan batu sai takaici ya Ka mashi ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, kawai sai yayi tsaki ya juya ya tafi ga adokinsa ya Kamashi ya hau ya sukqaneshi a guje. * * * * * * Da magriba yarima uzaifat ya shiga cikin gidan sarautar ya nufi bangaren mahaifiyarsa gimbiya shulaifa. Dashigarsa cikin tura karta sai ya isketa a zaune ta idar da sallah taba nafila. Cikin biyayya uzaifat ya sani wuri ya zana a gefe daya. Koda ta idar da sallah ta juyi sai tayi arba da raunin dake jikin hannun uzaifat. Nan taje hankalinta ya tashi, ta mike tsaye ta karaso gareshi ta rike kafadunsa tace, yaya akayi kajika wannan raunin? Ai wannan ma da gani saranka akayi da takobi?. Ya yin da uzaifat yaji wannan tambayar sai ya yi murmushi yace, karki damu ya ummina, wannan ba komai bane, kin san muna fita hoton yaki ni da dakaruna, to a can ne na sami wannan raunin. Shulaifa tayi ajiyar zuciya tace, Haba dana yau kwana nawa kuna fita wannan horon? Me yasa tsawon kwanankin nan bakayi wannan raunin ba sai yau? Na san irin jarumtakarka duk garin nan mutum dayane za ka kafsa dashi har ya sani nasarar yi maka rauni. Koda jin wannan batu sai jikin uzaifat yaya sanyi, ya tabbatar da cewa ta gano cewa ukashat ne yayi masa wannan rauni. Cikin alamun damuwa ya dubeta yace yake ummina kiyi sani cewa shima wanda yayi min wannan rauni nima haka nayi masa. Na rokeki dan girman Allah kibar wannan zance a tsakanin mu, domin idan maganar taje ga kunnen sarki gurina zai wargatse zai iya fasa gasar da yasa mana tsakanina da dan uwana. Sa'adda shulaifa taji haka sai itama jikinta yayi sanyi tace, shikenan na bar Maganar. Yanzu wane irin ci gaba ka samu a bangaren horon daku ke yi kai Dakarunka?. Uzaifat yace Alhamdulillahi muna samun ci gaba sosai. Yake ummina abin danake so shine, ki cigaba da yin min addu'a bisa nasara da nake nema a wannan ganin dazamu yi da birnin shumbul. Shulaifa tace, kullum a cikin yi maka addu'a nake, kuma da izinin Allah zaka sami wannan nasara, domin alherine a zuciyarka ba sharru ba. Ina tabbatar maka da cewa bazan daina yi maka addu'a ba daga yau har izuwa ranar da zaka tafi wannan yaki. Nasihata a gareka itace, ka rike abu uku, in dai kana rike da su dukabinda daka sa a gabanka zakayi nasara. Wadannan abubuwa guda uku ba komai bane face duk abinda zaka fadi ka tabbatar cewar ka fadi gaskiya, idan aka baka Amana ka riketa, kuma idan ka dauki alkawari ka tabbatar cewar ka cikashi, indai ka kiyaye wadannan abubuwan uku to tabbas makiya bazasu ga bayanka ba. Lokacin da shulaifa tazo nan a zancenta sai yarima uzaifat ya jinjina kai yace, Insha Allahu kuwa zan kiyaye wadannan abubuwa uku. Nan take yayi mata sallama ya fita daga cikin turakar. * * * * * * Al'amarin yarima ukashat kuwa, lokacin da ya shiga turakar mahaifiyarsa muzaira taga wannan rauni na hannunsa sai hankalinta ya dugunzuma, ta dubeshi tace, ya kau dana, yaya akayi ka sami wannan rauni?. Ukashat ya kashe labarin duk

Chapter 1 of 21