Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
munyi laifi ? ko yanzu da zance zanyi aure sai ka ji bala'i na tashi nakan rasa su mata wane iri ne. Dr. khalifa yabushe da dariya yace "na san duk yunwa ce tasaka wannan surutun ai kai da sauki ma tunda ka iya shiga kitchen ka sarrafa abincinka kaci ni ko tea ba na iya dafawa. Dr.hafiz yace "to ai kuwa ka koya mata ba su da tabbas surutu da soyayya a waje suka iya idan an shigo gdan sai a hankali musamman idan an fara ajiye yara, bara in dafa indomie kaina har ciwo yake sbda yunwa. Bayan ya gama dafa indomie din suka mike a kasa suna ci yace "mutumina wai wace babbar magana ce ? Yace "ina fatan ka gane fatima" Dr. hafiz yace "ba zan kasa fahimtarta da wai ba domin na fahimci zuciyarka ta amsheta da gaggawa. Yace "kwarai ba ka yi fahimtar kuskure ba, kallo daya nayiwa yarinyar naji zuciyata ta aminta tazamo mata ta. Dr. hafiz yace "to ai bbu matsala yarinyar datake rayuwa a cikin gdan ku na yi farin cikin han. Dr. khalifa yace "kai dakata saura sati biyu bikinta. Dr. hafiz yace "to ba sai a lalubo wata ba abinda ga matan nan dayawa dakansu suke cewa ma suna so. Dr. khalifa yace "kai likita mata suna suka tara, duk yawan dasukayi irin su fatima daban suke, a iya budewai idona da yawace yawace na ban taba ganin mace mai kyaun fati ; a ba, tare da kyaun fuska ,dubi yadda tsarin halittar jikinta yake,habawa wannan ai itace mace mutumi na. Dr. hafiz yayi dariya sosai yace "kai wani irin kayatarwa fatima tayi maka, ne karude haka ? Haba likita kada kabari fatima taji za ta rainaka ka ga yarinya ce karama ko ka mance kana cewa ba ka son karanar yarinya ? Dr. khalifa yace "kai tafi chan wannan lokacin ya wuce ba zan iya hakura da yarinyar nan ba. Dr. hafiz yabata rai yace "kai Abbakar muyi magana ta gaskiya yarinyar daya rage saura sati biyu bikinta yya za ayi kace kana sonta ? ko a shari'ance ba kyau nema cikin nema ,kayi hakuri kawai mace in dai mace kake bukata za kasamu wadda tafi fatima kyau sai dai in fa fatima kake nema. Dr khalifa yadan marairaice yace "haba dr. hafizu yaya za ayi ka sanyayar min da jiki ? bayan ka san ban taba nuna maka wata diya mace dana damu da ita ba ballantana har in nuna damuwata akan sonauranta, tunda nagaya maka ai ka san dagaske nake ya kamata kataimake ni da shawarar dazan samu mafita ba kasace min guiwa ba. Dr. hafiz yace "to ai ni banga hanyar mafitar bane Abbakar, sati biyu fa yarage biki sai kuma muce muna so ? wannan ai son kai ne da zuciya, kuma kasani son kai da zuciya ba dabi'a ce ta mutan arxiki ba. Dr. khalifa yace "knan so kake kace min sai dai inyi hakuri da fatima ? Yace "Don Allah kayi wannan hakurin sai Allah yabaka wacce tafita.... Dr. khalifa yace "kai hafiz daina min wannan maganar da wuya in za tayiwu bakasan menake ji bane game da wannan yarinyar, ban taba sanin haka so yake ba. ****** Tun a wannan rana mama tafara shirya amarya fatima da kayan gyaran jiki na mata suka tunkari lamarin dagaske, batasan rikicin da dr. khalifa ke ciki game da matsananciyar soyayyar fatima da ta damki zuciyarsa ba, a wannan daren yakasa sukuni yakwana yana tunanin tawace hanya zai samarwa kansa mafita. Abin da dai yasawa kansa shi ne ko ta wani hanya zai mallaki fatima babu yadda za ayi yayi sakacin dazai rasa ta, bai san haka ciwon so yake ba sai yau. A gdan fatima takwana suna tattauna yadda biki zai kasance, abinda fati take jaddadawa ummi shi ne "ta sani khalifa sbda ba ya da tausayi, tace "ni kam ummi na rasa yadda zanyi da takaicin dana ke ji a raina game da yaya khalifa, ko ganinsa ba na son yi sbda kawai ya nuna ba ya sonki. Ummi tayi murmushi tace 'to yaya zanyi na zubawa sarautar Allah ido na zubawa dr. khalifa ido, na tabbaatarwa raina ko ban samu dr. khalifa ba to zan tabbatar wata diya mace bata same shi ba, idan narasa shi sai dai kowa ma yarasa . Fatima tace "kina nufin za ki hanashi aurene ? yaya mutumin da ka kaasa jawo ra'ayinsa yasoka za kasawa ranka cewa za ka iya hana shi aure ? Ummi ta girgiza kai "ba aure xan hana shi ba ban isa in hanashi aure ba ni dai na ce sai dai kowa yarasa . Riga da zani na atamfar egyptian ce a jikin fatima tana tsaye ita kadai a kitchen tana suyar kosai, kawai ganin mutum tayi a kusa da ita yana fadin "fatima aiki ake yi ne ? A firgice tawaiwayo tadubi dr. khalifa yana sanye da doguwar riga fara kal kamshi mai dadin gaske yana tashi a jikinsa, ta matsa gefe ganin yadda yatsaya daf da ita kamar zai taba ta, yayi murmushi yace "ya kike matsawa haka kamar kinga wani dodo ? zo ki kwashe kada yakone. Ta katsa motsawa sai gabanta ke faduwa a lkacin ummi tashigo tana fadin "fatima kin gama ? Ganin wanda ke tsaye a kitchen din yasata tsayuwa turus tana kallonsa shi da fatima, ganin ummi yasa yatsuke fuska yafice daga kitchen din ummi takwashe kosai tana fadin "yau kuma meya kawo doctor kitchen din nan ko wani abu yake nema ? Kokarin da fatima tayi shine na daidita muryarta don kada ummi tazargi wani abu a ranta tace "ni ma gani nayi ya shigo. Kallon da ummin tayi mata shi ne yasa tafahimci kuskuren ta a bisa abinda tafada, to sai dai kuma batasan abinda za tafada din ba in ba hakan tafada ba, jikinta yakara sanyi sosai ganin ummi bata sake magana ba, takwashe kosan tace tadakko kunun gyadan dasuka dama zuwa falo. Bayan sun gama shirya tebur din ne tadubeta tace "ki je kigayawa doctor an gama shirya tebur kada yai sanyi yakasa ci. Cikin dacin rai fati tace "ni ce ma zan fadi mai ? kin taba ganin na nufi hanyar dakinsa. Ummi ta tabe baki tace "ai ba abin zafi bane gani nayi ya fi son yi miki magana fiye dani amma kar ki damu bari ni inje in gaya mai. Fatima taja tsaki tawuce daki, yayin da ummi tanufi dakin dr. khalifa ta kwankwasa yace "waye ? Tace "ni ce ummi. Ga mamakinta sai yace "shigo" Ta bude jikinta ba karfi yana kwance bisa gado yanuna wata kujera yace "zauna in miki tambaya. Ummi na son kallon fuskar dr. khalifa yana yawan burgeta nan da nan taji hawaye ya taru i donta tayi kasa da kanta, yana sane da halin datake shiga idan tana kusa dashi yashare domin shi ma din a halin yanzu abin tausayi ne duk yadda take son sbi ya fita son fatima kuma ya fita shiga hadari domin kuwa gab yake da yayi babbar asarar rasa fatima. Ke ummmi gaya min dangantakar ki da fatima". Abin da yace da ita knan lamarin dayasa tadago cikin sauri zuciyarta na bugawa sosai tace "ban gane ba yaya khalifa. yamike zaune bai ce komi ba, tunanin da yake kai komo a zuciyarsa shi ne shawarar da dr. bashir yaba shi duk a daren jiya lokacin daya same shi a waya yabashi labarin halin daya ke ciki yace "Bash don Allah kada ka kashe min guiwa ba zan iya hakuri da fatima ba ni kadai nasan halin da zuciyata ke ciki. Dr. bashir yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba. Khalifa yce "ya ya naji ka yi shiru. Bashir yayi ajiyar zuciya yace "Abbakar ta yaya xa a maido wannan aure a kanka bayan sati biyu yarage kace ayi mata aure. Yayi tsaki yace "amma dai ni ne nafada maka saura sati biyu ayi bikin ko ? ka ga ba na bukatar kasanar dani shawara dai nanemeka bashir. Yace "to shi me rai ba ya rasa motsi, hanya daya ce wata kila idan munbi za mu iya dacewa. "Fadi inji" Bashir yace "ta hanyar ummi da mama ne kawai za mu iya yin nasarar jan hankalin fatima idan da rabo sai ayi nasara. Ummi tace Bashir ? Ya amsa "ita nace dalilin dayasa nace ita kuwa inada labarin cewa fatima ba ta da kawa aminiya abokiyar shakuwar data wuce ummi, ummi na iya sauya ra'ayi da tunanin fatima sbda yarda da amincin dake tsakaninsu, yayin da mma ke da girma a idon ummi ba ta iya musa maganar mama. Dr. khalifa yajinjina labarin a ransa yace "hakane Bashir to amma fa kada ka manta ba wanda ummi ke so sai ni, ban amince da auranta ba ta yaya za ayi ta amince da wannan batu ? Ba ka ganin za tayi amfani da wannan damar gun lalata min al'amarina da fatin ? Bashir yace "to ai daman ba kai tsaye za kagaya matan ba sai ka bi tawasu hanyoyin na hikima wanda zaisa ta fahimci kana sassauta zuciyarka akanta,ma'ana kadinga sakar mata fuska kuna hira kuma karara kanuna mata cewa kana bukatar ta taimaka maka akan fatima za kayi mata duk abinda take so, idan kayi mata za ta amince tunda tana sonka ba ta son damuwarka, sannan ita kuma mama ka marairaice mata sosai kanuna mata ba za ka iya rayuwa ba fati ba, so so ne amma son kai ya fi da sannu za ta tausaya maka tagoya ma baya. Dr. khalifa yakashe wayar kansa a daure tamau yana jinjina yadda zai iya jan hankalin ummi har ta taimaka masa, bayan magana ma ba yi mata yake ba, ya kwana yana tunanin abin ga dumbin ciwon so na karuwa a zuciyarsa har yana jin ina ma zai iya fidda son fati daga ransa ya huta, amma ina duk yanayin dazai shiga in dai zai mallaki fatin dole yajure tunda mallakar ta shi ne kadai kwanciyar hankalinsa da farin cikin rayuwarsa, amma fa yana takaicin hakan bai damu da lallaba mama ba ya san tana sonsa da tausayinsa, ummin ce dai matsalarsa kuma ya amince ta hanyar ummi zai iya cimma nasara.. Wannan shi ne dalilin dayasa da gari yawaye yanufi kitchen ya san ummin ce ke dafa abincin safe a gdan ga mamakinsa sai yaga gimbiyar ce a kicin din... Yakatse tunaninsa anan yadawo da ganinsa ga ummi wadda tayi tagumi tana goge hawayenta wadanda tayi kokarin tsaida su suka ki tsayuwa takyalesu suyi ta zubar lokacin su ne. Ummi" Muryar dr. khalifa ya ratso kunnanta da sassan jikinta tadago kai suka kalli juna tace "Na'am". Ina son ki yi min wani taimako daya za ki iya ? Idan bai fi karfina ba insha Allahu zanyi maka, fada min inji" Ummi "inason kawarki fatima. Inason in aureta za ki iya taimaka min ki ja min ra'ayinta a fasa ba musbahu auranta a bani ? Wai shin mafarki ne wannan ko gaske ? Dr. khalifa datake tsananin so ne yake gaya mata da bakinsa cewar fatima aminiyarta yake so ya aura har yana neman ta taimakeshi. wane irin raini khalifa yake mata, wani irin cin fuska ne wannan ? Hawayen idanuwan ummin suka kara ballewa tashiga kuka kamar ranta zai fita, Dr. khalifa yace "ummi idan ba za ki iya taimako n ba kitashi ki ban guri. Tace "ya ya khalifa ba ka da tausayi kuma baka san darajar soyayya ba, baka san ciwon so ba, da ka san zafi da dacin rai dake cikin ciwon so da baka nufeni da wannan maganar ba, ka san yadda nake ji a zuciyata kuwa ? tamike tsaye idanunta tazuba kansa wadanda suka kada jawur tana huci tace "khalifa na sani ba ka so na, ba zan yi maka dole kaso ni ba, kuma ba zan taba bin wata hanya don kaso ni ba,, ni kam ina sonka son da ba zan taba dainawa ba, abu daya nake son tabbatar maka wanda shi ne ba zan taba barwa wata kai ba sai dai kowa yarasa ni kam na ami ? ce na rasaka.... Amma ba zan hakura ba. A fusace tabude kofar tafita, yabiyota dasauri yasha gabanta ya sausauta murya yace "haba ummi kitsaya ki fuskance ni da kyau mana na yi miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso matukar na mallaki fatima. Murmushi tayi masa tace "ka yi kuskure babba doctor daka fuskance ni da wannan maganar. Ta zagaye shi tashige cikin gida. Abba da mama ne kawai a falo suna breakfast, tashige dakin dasauri dan ba ta son sukalli idonta. Ba karamin faduwar gaba fatima tayi ba ganin ummi ta shigo tana kuka, tamike tariko ta tana tambayarta lafiya ? me khalifan yayi miki ? Ta ja hannunta suka zauna tana goge mata hawaye, ummi tace "ummi babu abinda dr. khalifa yayi min fyace ya shaida min cewa yana sonki yana son in taimake shi yasamu auranki. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. fatima kefadi muryarta na rawa tace "bai san an kusan bikina bane, ke ko ba a kusan biki na ba ina ni ina shi. Wani irin abu ummi taji ya tokare mata zuciya, kirjinta yamata nauyi, kanta ma yashiga sarawa nan da nan taji jiri ya fara dibarta, tadaure tatashi tadauki hijjavinta tayi sa'a abba da mama sun shige daki tafice daga gdan taja mota sai gdan mahaifiyarta. Hajiya Hauwa na barci ummi tafada jikinta tana kuka mai tsanani, a rude hajiyar tatashi tana tambayar lafiya lafia ? Wa ye yamutu ? Tace "hajiya na ga takaina na shiga uku, wai khalifa ne yau din nan yakirani yana shaida min cewa ba macen da yake son aura sai fatima. Yana son in taimake shi yasamu hadin kan fatima. Hajiya tace "yawwa abinda nake gayan miki ya auku ko ? ai lokacin da muke gaya miki gani kike ba zai taba yiwuwa ba, bayan mu munsan faruwarsa abu ne mai sauki, idan kika kalli fatima da tsarinta mace ce da maza ke burin mallakar irinta, ta yaya khalifa yana ganinta a gdan zai hadiye maitarsa. Ummi kuka take tana karawa fargaba da takaici sun sa ta kasa samun abinda za tace yayin da hajiya ke ta fadace fadacenta inda take shiga ba nan take fita ba, takira hajiya saude a waya tace "kinga abinda muke gudu saida ya auku, taurin kan yarinyar nan zai ja mana asara. Bayan saude ta saurari abinda ke faruwa daga bakin hajiya hauwa tace "kujirani za mu yi maganinsu dukkansu wannan karon sai mun bude musu wuta duk tsawon lokacin da muka dauka ya tashi a banza knan ? wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. Ba afi minti daya ba hajiya saude tayi dirar mikiya a gdan tadubi ummi tace "kukan banza da wofi idan mutum bai aiki da shawarar na gaba dashi yana tare da nadama, gun malam za mutafi yanzun ba za mu rangantawa khalifa ba. Hajiya hauwa ta tabe baki "ba sai in za tayi abubuwan da aka ce mata ba. Tace "to kada ma tayin batayi ba ta isa tazo tana mana kuka anan ? Har suka isa gdan malam din kuka sosai ummi takeyi ita takaicin ta ace dr. khalifa yarasa wa zai so sai aminiyarta fatima, tunda su hajiya suke gaya mata abin da zai iya fruwa ganin take bazai taba yiwuwa ba ashe kuskure tayi babba, hajiya hauwa da hajiya saude ke ta tattaunawarsu kan matsalar ita kam ta sunkuyar da kanta tana tunanin yadda za takasance in har fati ta amshi soyayyar dr. khalifa koda yake abu ne da take ganin kamar zaiyi wahala sbda koyaushe fatima na tabbatar mata da cewa bbu abinda zai hana yi ma iyaynta biyayya, tanayin wannan magana ne idan wasu daga kawayensu suna cewa"kyaun halittarta ya fi karfin ta auri malami almajiri irin malam musbahu wanda ba wayewa a tare dashi, to anan ne take tabbatar musudacewa "malam musbahu ya fi kowanni namiji a gunta tunda shi iyaynta suka zabar mata dole tayi iyayya gasu sbda yardar Allah take nema a cikin al'amuranta ba wai kyale kyalen duniya da abinda ke cikinta ba. Ummi tana cigaba da gasgata abubuwan da fatin ke fada ne ganin yadda bata kila kowani irin da namiji duk matsayinsa, hakan ne yasa ummi ta tabbatarwa kanta cewa ko dr. Khalifa yadawo ya ce yana son fati bazata amince da batunsa ba, sbda akidar biyayyar iyayanta data sawa zuciyarta to in dai haka ne ma me zaisa in daga hankali na ? Ta tambayi kanta in dai fatima bazata amince da dr. Khalifa ba me zaisa ta tayarwa kanta hankali, to a daidai lokacin da wannan tunanin ke tasiri a zuciyar ummi har tafara jin saukin zafin da zuciyarta tadauka sai kuma dai wani gdfen na zuciyarta yafara tunasar da ita cewa fa dr. Khalifa kyakyawan namiji ne ga ilimi ga naira, mata kuwa ba abinda suke so a gun da namiji wadanda suka wuce kyau da naira ballantana abin yahadu da ilimi da wayewa, kadan ne suke la'akari da addini da kyawawan dabi'u, fatima kam tanada banbanci da sauran matan zamani, iya zaman ta da ummi ta tabbatar za ta mata wadannan kyawawan shaidar a ko ina fatima ba ta da kwadayin abin duniya don da tanayi da dr. khalifa bai dawo yasa meta, wannan tunanin duk yake kara kuna a zuciyar ummi sunada tasiri mai karfi don ta tabbatar da hakan. Ummi na wannan dogon tunani ne kafin malam yabasu damar shigowa, hajiya suka shaida masa abinda ke tafe dasu, yajawo wani rairayi dake bayansa yafara zane zane yana tambayarsu wasu abubuwan dasuka shafi dr. khalifa da fatima da iyayanta. Malam yajinjina kai yace "hakika khalifa ba karamin so yakewa fatima ba, kai hasalima bai taba jin son wata diya mace a ransa kwatankwacin yadda yake son fatima ba, kuma ya yi dammarar auranta ko tawani hali. Wannan bayanin na malam yasa ummi tunani kamar kirjinta zai tarwatse sbda faduwar gaba, hajiya hauwa tace "to malam yanxu knan khalifa ba zai auri ummi ba, kuma kana ganin auransu da fatima mai yiwuwa ne dukda cewa an kusan bikinta ? Malam yace "to ni dai na gaya muku abinda nagano tar da khalifan ne, batun yiwuwar auransa da ummi idan kun bi abubuwan dazan tsara muku anyi an gama, fatima kuwa zan fatattaki soyayyarta ne daga zuciyarsa, amma gskiyar magana ba aiki ne mai sauki ba. Hajiya saude tace "malam indai za asamu nasara wahala mai sauki ne kuma me wucewa ne me ake bukata ? Malam ya gyara zama yace "dafarko kamar yadda nagaya maku a baya za ku kawo min kasar da khalifa ya taka, za ku kwao gashin kansa da hankicinsa da hularsa da hotonsa, za ku biya kudin fararan raguna guda uku, jajayan akuya guda uku, jajayan zakaru bakwai, sauran abubuwan kuma mu za mu samo su, kudin aiki dubu dari, ku zuba ido za kuga aiki da cikawa. Suka tsaya akan cewa bayan kwana biyu za akawo duk abinda aka bukata har kudin, suka dawo gda da shawarar yadda za asamu kudin dasuka kama har kusan dubu dari biyu, a karshe dai Alhaji muhammad mahaifin dr. khlifa aka buga wa waya suka mai karyar cewa asibiti za su yace zai aaiko musu da kudin dama sun saba dahaka duk abinda suka bukata zai musu iya ikonsa amma ba sa gani, su dai matarsa da dansa ne ba sa so dashi kansa sai dai dukiyarsa A DAREN FARKO 20 Fitar ummi yakara dagawa fatima hankali sosai takifa kanta a cinyarta tana sharar kwalla, meyasa dr.khalifa zai mata haka, ya ya za ayi yarasa wadda zai fadawa cewa ma yana sonta sai ummi wannan ba karamin cin fuska bane da walakanci, duk abinda zai sa ummi tayi hushi da ita abin ya yi yawa ko da yake ta san dole ne ummi tayi fushi da ita akan dr. khalifa, ba wanda ummi ba za ta iya juyawa ba sbda son datake masa ba kadan bane, ta gaji da kukan bakin ciki da takaici tatashi a sanyaye. zata tafi gda taci karo da mama a harabar gida tana magana da ado me musu wanki da guga, yanayin ta da mama tagani yasa tayi saurin matsowa daf da ita tace " 'yammata lafiya ? kukan me kikayi haka ? Ba kuka nayi ba wani abu ne yafada min ido. Tace "ina ummi ? Tace "ta fita ban san ina taje ba. Tace "ke ina za ki yanzun ? Tace "gida za ni yanzun xan dawo. Kamar zata hanata tafiya sai tayi tunanin bai dace ba batasan abin da za tayi ba don haka ta kyaleta tatafi tadawo falo tazauna. Dr. khalifa yashigo cikin shirin fita yazauna suka gaisa tace "ba za kaci abincin bane naga ka yi shirin fita ? Ya girgiza kai"ba zan iya cin komi ba xuciyata tana ckin damuwa bansan mafita ba a cikin halin danake ciki. Mama tayi murmushi tace "khalifa Allah (SWT) daya halicce mu cewa yayi "ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta min, to ni dai a ganina ba wani abinda zai dagawa mutum hankali akai in dai ba bautar Allahn nan ba, to ita kanta bautar Allah ba zafafa mana akai ba, Allah ba ya daurawa wata rai sai abinda za ta iya, in kuwa haka ne bbu abinda zai zamo mai tsanani a cikin wannan rayuwa ko meye shi kuwa, musanman ida mutum yana la'akari da rayuwar duniya, wadda fararriya ce kuma kararriya, duk wani abu dakasani dayake a cikin duniyar nan a dayan biyu yake, ko dai ka kare kabar shi ko shi yakare yabarka, to meye dalilin damuwa. Khalifa yayi ajiyar zuciya yace "mama na san za ki yi min shaidar hakuri da kau da kai a cikin al'amarin rayuwa idan yataso min, mama a wannan karon na samu kaina a yanayin dana kasa mallakar kaina, don na sa hakurar da zuciyata tayi hakuri da abinda take nema. Wallahi ji nake k ; ar zan mutu sbda ciwo fmda radadin da nakeji a zuciya ta. Mama tayk mai zumu da ido tana kallon fuskarsa, tabbas yanayin fuskarsa ta nuna tabbatar da abinda yake fada haka ne, tausayin sa yakamata amma tjure don kada ta dada karayar mai da zuciya tace "khalifa daman akwai abinda ba za a iya hakura dashi ba a duniyar nan ? a matsayin mu na musulmi munyi imani da cewa dukkan abinda yasa me mu haka Allah ya kaddara mana kuma ba mu da ikon kaucewa abinda Allah yakaddara mana ,kadaure kayi hakan mana. Yace "mama ba zan iya hakuri da fatima ba, don Allah ki taimake ni duk yadda za kiso alheri a gdan wanda za a ba auran fatima ba kamar a gdan nan ba. Mama ta jima kanta a kasa tarasa abinda za tace, Dr. khalifa yaci gaba da fadin "wlh mama babu abinda zan iya aiwatar wa a rayuwa ta in dai ina cikin wannan yanayin ni dai kisha min kan yarinyar nan da iyayanta ina matukar kaunarta. Tace "khalifa wace irin son zuciya kake son mu aiwatar ne ? don Allah kayi hakuri. Ya tareta dasauri yace "don Allah kada ki ba ni umurnin yin hakuri ina son fatima dayawa zan iya kowani irin hali idan ban mallaketa ba, ke za kiyi hakuri ki taimakeni ba wai ni zanyi hakuri ba waye zai iya hakuri da abinda yake so mama" Tace "ahi ke nan kabani kwana biyu zanyi tunani. Nan take mama tgano dalilin kukan da fatima ke yi knan, to kuma meye dalilin fitar ummi da safen nan ba tare da ta sanar dakowa inda za ta ba, ta kira wayar ummin a kashe takira hajiya hauwa ita kuma tana ringing ba a daga ba, ta aje wayar a gefe tayi tagumi tunani ya sha mata kai, shin yaya za ta yi da wannan al'amari, tana bukatar shawara, ko dayake duk wata shawara ba ta wuce ta lallashi khalifa yayi hakuri ba domin wannan son zuciyar ba yiwuwa zaiyi ba. Takira sadiya kanwarta dake tayata zama a gdan a dalilin mutuwar auranta tashaida mata abinda ke faruwa. Sadiya tace "tabdijam wannan ai babbar magana ce. Tace "to sadiya nima haka nagani, na rasa ta ina zan gano mafita. Sadiya tayi murmushi tace "to amm fa mama so so ne sonkai ya fi, tun kafin khalifa ydawo kasar nan idan nakalli fatima nakanji sha'awar ina ma itace khalifan zai aura, hakan yasa ba na so ma in ji ana hirar auranta me zai hana tunda dai khalifa ya nuna wannan damuwa ta sa mu san yadda za muyi ya aureta dama ance matar mutum kabarinsa wani bai auran matar wani. mama tagirgiza kai tace "kai anty sadiya anya wannan maganar ta yi daidai kuwa ? Sadiya tace "ta yi dai dai mana mama abinda yasa nace dake haka, idan khalifa bai samu auran fatima ba ba zai maida kansa kan aure ba sannan tunda ita yakeso in ya aureta hankalinsa zai kwanta sosai, yarinya ce mai hankali da natsuwa, gskiya mama kada muyi wannan sakacin daga karshe mu zo muna nadama. Mama takwantar da kanta bisa kujera idonta na kallon silin, sadiya ma ta zo da maganar daya cancanta a duba, abin ne da nauyi dole kam tsan abin yi in banda wannan matsalar ta fi kowa son khalifa ya auri fatima sbda fatima mace ce tagari to ya ya za tayi tadubi fati tace tafasa auren musbahu ta auri khalifa ??? ****** Tunda fatima tashiga gdansu bayan gaisuwa datayi da iyayanta bata kara cewa kowa kmi ba tashiga dakin innarta takwanta tana ci gaba da hawaye. Inna ta tambayeta damuwarta tagaya mata komi tace "tabdijam abin da malam ke gudu ne yafaru kin san shi Alhaji baban khalifan ya taba cewa yana son malam yaba dansa auranki yace ya riga ya ba da ke. Fatima tace "to ai inna ko da ba a bayar dani ba bazan taba amincewa khalifa ba, sbda aduniya dai banga da namijin da ummi ke so irin sa ba, ummi ba ta da burin daya wuce mallakarsa, ta kwallafa rai a kansa tana matukar so da kaunarsa. Matsayin ummi gareni ya wuce in yi mata haka, don Allah inna kada ki saurari maganar khalifa ba shi da tausayi bai da adalci. Tace "to ina ma za ayi haka ? dole yahakura. Fatima tadinga nacin kiran ummi a waya wayar a kashe take, dole taje ta lallashi ummi, ummi ta fi komi a gareta. Bayan sallar azahar tashaidawa inna za ta gdansu ummi tace sai ta dawo, ko ganin gdansu dr. khalifa ba ta son yi ,sbda takaicin ya cuceta ya hadata da babbar aminiyarta abokiyar shawararta. Tana tsaye bakin titin kan layinsu tana neman adaidaita sahu kawai sai ganin mota tayi ta yi fakin a gabanta, bakaken gilashin da aka zuge yabata damar ganin wanda ke ckin motar. dr. khalifa ne gabanta yafadi tsmatsa dasauri tana masa wani irin kallo, yace "ina za ki ne fatima. " Tayi shiru kamar ba da ita yake ba, yace "don Allah kigaya min inda za ki in kaiki. Anan ne ta hasala tace "ina ruwanka da inda za ni, ni ba neman taimakon mota nake ba. Yakashe motar yafito yana kare mata kallo daga sama har kasa, yana murmushi a wannan lokacin ne yadada tabbatarwa kansa yana son fatima kuma ba zai iya sakacin dazai rsata ba insha Allahu wannan yarinyar matarsa ce ta sunnah. Kwatsam adaidaita sahu ta tsaya a gabansu, ummi ce tafito idanunta fes akansu bata ce komi ba tabiya dan adaidaita kudinsa tawuce za

Chapter 9 of 19