Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tunanin ckin yammatansa wa zai kira tadebe masa kewa, yanajin wani iri ne a ransa zaman anisa a gdan ya taimaka masa amma hakanan yake jin tausayinta ba zai iya maidata abokiyar debe masa kewa ba yayin da kudirin datake dashi a kansa ba zai yiwu ba. Yakoma cikin daki yafidda kayan jikinsa yabar gajeran wando kawai yahaye gado sai kuma ummi tafado masa yayi murmushi yakira laila daya daga cikin yammatan na sa, wayarta a kashe, yaja tsaki yakashe wayar ya kama barci. ********* Posting a yan kwanakin nan sai hakuri a dalilin muna ta hidimar biki, duk yadda aka gani a hakura da hakan. A DAREN FARKO 14 GIDAN ainihin iyayan ummi yau hajiya saude tayi ma tsinke ta iske hajiya hauwan tana shirin fita tace "yanzu kuwa nake shirin kiranki a waya inji ko kina gida in biyo ki min rakiya. Saude tace "ai zuwa nyi inji labarin inda aka kwana da batun ummi da khalifa, wai shin har yanzu babu wani labari? Hauwa tace "uhm wani labari ne ban da na takaici saude? wannan yaron zai wahala mu cimma nasara kansa yana da jin kan tsiya. Saude tace "shi din banza, ke fa yadda uwarsa taraba mu da dan uwanmu haka za mu rabata da danta, ba za mu samu wannan damar ba har sai khalifa ya auri ummi. Hauwa tace "to tana can dai tana faman bautar girki a gdan idan yadawo ma san abin yi, yanzu kam sai hakuri tunda ba ya nan. Saude tace '"duk da haka bai dace muyi kasa a guiwa ba da safe ake kama fara idan mukayi sakaci wankin hula yakaimu dare bazamu samu yadda muke so ba. Hauwa tazauna gefen gado tace "to me za muyi yanzu? Tace "gun boka za muyi duk abinda yadace a yi a ja ra'ayin khalifa ga ummi idan ma ta kama muhana shi zaman jamus din gaba daya yadawo ya aureta ba matsala. Zuciyar hajiya hauwa ta karfafa sosai tace, "wannan shawara ce mai kyau tashi mune. A daidai wannan lokacin babbar aminiyar ummi wato jiddah tana wurin ummi ta je yimata sallama don lokacin tafiyarta london karatu ya yi. Suna zaune dakin ummi su biyu fatima tashigo sanye da doguwar rika baka after dress ta yi mata kyau sosai, malam musbahu ne yasayo mata da sukaje kaduna da malam, suka gaisa da jiddah. Ummi tace "kinyi kyau mutuniyar bari in yi miki hoto ,Allah yasa dai angon ya ganki na san zai yaba wannan kwalliyar. Tayi wal da ido tace "shi ne ma ya aiko ni da kwan zabi yace in kawowa hajiya sunje kauye da malam sukayo tsaraba, bari ma inje yana jira na anjima zan dawo insha Allahu. Ummi tace "muje kitchen in ba ki wani lemo dana hada hirar taku za tafi armashi idan kunayi kuna sha.. Fati tace "kai antina kina shagwaba mu dayawa. Tace "haka yadace. Bayan tafiyar fati tadawo daki gun jiddah tace "Allah ya sani ina matukar son yarinyar nan fatima sbda kyaunta da halayenta masu kyau. jiddah tace "ai na ga alama za a iya dawo da ita gidan nan idan tafiya tayi tafiya. Tace "ai da za ta dawo din ai da na ji dadi mama da abba ba su da matsalar komi gdansu gdan jama'a ne suna son suga mutane suna ta zuwa gdan nan. Ta ce "ai hakan yana da kyau shin kuna waya da khalifa? Tarike baki tace "wane ni? Tunda yatafi suke waya da iyayansa bai taba tambayata ba, gaskiyar magana jiddah ina ci gaba da zama a gdan nan ne dan inajin dadin zaman gdan a dalilin kirkin mama da abba amma ba na jin zan samu khalifa ya fi karfina. Jiddah tace "ni abinda yake hada ni dake saurin karaya har yanzu dasauran batu, idan da rai da rabo idan kikayi hakuri watarana za ki cimma nasara akan khalifa, kidaure kici gaba da zama a gdan nan a matsayin mai yakin neman zuciyar masoyinki idan kika ci gaba da kyautata masa zai iya auranki musamman dayake kin shiga zuciyar iyayansa duka biyun. Tace "toh Allah yasa inafa cigaba da addu'a na san bbu abinda yafi karfin Allah. Jiddah ta mike da niyyar tafiya ta ce "ina takaici da zanyi wannan tafiyar ni kadai ba tare da ke ba soyayyar khalifa ta nisanta ki da kowa. Suka fito suna ci gaba da tattauna maganar shawarar da bata wuce abinda yashafi khalifa ba daga karshe ummi tace "jiddah soyayyar khalifa tayi min yawa a zuciyata abin har tsoro yake ba ni ,ina ta kokarin ganin na fidda shi a zuciyata don in huta amma abin ya ki yiwuwa, ina jiyewa kaina abinda zan iya aikatawa akan kowa idan narasa shi, idan na rasa khalifa bai auri wata macen ba nasan zan iya hakura abu daya ne ba zan taba iya hakura akaiba shi ne khalifa ya auri wata macen, ina nufin idan zai zauna haka ba na ganin mace a tare dashi shike nan. Jiddah taja tsaki tace "ni wannan shirmen na ki ne ba na so, wadannan maganganu? ba za subaki khalif ko su hanaki shi ba. Tace "ni fa ki sani haka jidda ina gaya miki ne dan ki san abunda ke ckin zuciyata wannan shi ne abin tsoron. Bayan tafiyar jiddah gdansu fatima tanufa ta iskesu ita da musbahu a zaure suna hira, wani yaro yashigo da sallamarsa yace "wai wani a waje ya ce don Allah wadda tashigo yanzu tazo. Ta tsuke fuska tace "kai tafi kace ba za tazo ba. Malam musbahu yace "haba ummi bai dace kiyi haka ba mu maza ba ma son muga anawa yan uwanmu haka. Fatima tace "malam ko kaje mana kaji me ke tafe dashi. Kafin malam yadawo suka shige cikin gida innarsu fati ta je unguwa a tsakar ida suka zauna kan tabarma, fati ta bata rai tace "ummi duk abinda nayi kina bata rai akan banyi daidai ba meyasa ke nake ganin ba kya iya sauraron duk masu kaunarki? shin ke abunda kikeyi daidai ne? ko kuma dan komi ke ce kika iya;? Malam musbahu yashigo cike da fara'arsa yana fadin "don Allah ummi kizo kugaisa da mutumin nan na san shi mutumin kirki ne sosai. Tace "don Allah malam kasallame shi yatafi kace an yi min miji kun taba ganin na saurari wani? Yayi dan jim sannan yace "to ba zan matsa miki ba amma zan shawarce shi akan yanemi shawra a gun abbanku. Bayan fitarsa fatima ta ci gaba dayi mata kallon tuhuma ranta a bace take fadin "baki ba ni amsar tambaya ta ba. Ummi tayi murmushi tace "fati knan kin more mijinki ma ya mori mace duk abinda kikayi kyau yake maki batan ran ma da kikayi yanzu bakiga yadda kika kara kyau da haduwa ba. Fatima takara fusata tace "ni ba wannan na tambayeki ba dole sai kin ba ni amsa ta gaskiya bisa tambayar dana yi miki idan kuma ba haka ba nima na daina yin abinda ki ke umarta ta. Ummi tana dariya tace "idan kin kwantar da hankalinki ko baki bata rai ba zan fada miki komai. Ta mike zaune suna fuskantar juna tace "fatima a cikin rayuwa bbu abinda ba ya samun mutum wani yasamu yadda yakeso wani akasin haka, wanifarkonsa yana ckin jin dadi karshensa wahala, yayin da wani zai taso ne cikin wahala karshensa yasamu jin dadi, fatima ni kam bbu wanda zanso a rayuwata bayan mutum daya da zuciyata ke muradi. Waye wannan? Na san ko baki san khalifa a ido ba hotunan da kike gani a gdansu zai sa ki shaida shi idan kin gan shi a fili, khalifa shi ne mutumin da zuciyata ta rataya da soyayyarsa, wannan shi ne dalilin dayasa ba na kula kowa dalilina shi ne duk wanda na kula bata mai lkaci zanyi domin zuciyata ba za ta so shi ba, me ye amfanin in yaudari mutum in nuna amincewa na gare shi alhali zuciyata tana tare da son wani, in dai ba yaudarar mutum zanyi ba to gwara in kyaleshi bbu wanda zan mallakawa zuciyata bayan shi, bbu wani da namiji da zai samu farin ciki a tare dani sai shi domin shi ne nake da kwarin guiwa dazan farantawa zuciya ko ina so ko ba na so sbda karfin kaunar danake masa ba mai misaltuwa bace, son danake masa ba zai bari in yi abinda zan bata masa rai ba, wannan shi ne dalilin dayasa nake ta burin ace shi na aura don in samarwa kaina farin ciki da kwanciyar hnkali a auran, kuma insamu tsira a gaban Allah idan nayi mai biyayya, fatima ina zaton wannan shi ne dalilin dayasa ake ba ma'aurata daman zabar wadanda suke so yayin neman aure, wanda zuciyar mutum ta aminta tana so shi take iya bi. Fatima tace "toh ummi an yi maganar auranku ne da khalifan kan tafiyarsa ? Tayi murmushi "fatima in banda khalifan iyayansa ma basu san ina masa wannan son ba, ya gargade ni akan kar in sanar da iyayansa ballantana a matsa masa kan ya aureni, khalifa ba ya so na ni ce dai zuciyata ba ta iya hakuri dashi. Fatima ta girgiza kai"anya kuwa za ki ce kai tsaye bai son ki ummi ? shin meye abin ki a tare dake, ko halayyarki ta arziki ta sa mutum yaso ki. Tace "Allah sarki fatima ke ce kime ganin haka, ai ita soyayya ba ruwanta da kirki ko rashinta, idan kana son mutum to kana sonsa idan ba ka so kuma ba za ka so shin ba koda ya fi kowa kirki. Fatima tace "to yanzu meye abinyi ummi ni bar na ji na tsani khalifan sbda rashin tausayin daya nuna miki, bai dace ka watsawa wanda yake sonka kasa a ido ba ya dace yatausaya miki, ni kam ina bakin cikin wannan damuwa ta ki inama inada halin taimakonki wlh da sai inda karfina yakare. Ummi tace "fatima idan kika biyewa damuwata za kiyi tazama cikin damuwa ne domin kuwa damuwa ba ta kare mini don lokacin dana fara son khalifa nake kuka nake zama a cikin damuwar da har sai da nasaba da ita, inata kokarin raba kaina da soyayyarsa don in huta amma ko yaushe soyayyarsa karuwa take a zuciyata abin ko sauki ba ya yi, tunda har aka kai wannan lokacin khalifa bai waiwayeni ba ba zai tausaya min ta fuskar soyayya ba kuma dagaske yake bai sona, ban isa in tursasawa khalifa ya aureni ba dole knan in hakura da auransa, amma ba zan iya hakuri dashi ba, ba zan auri ko wanne namijj ba ba zan hakura da khalifa ba. ******** Khalifa ya fara karatu mai zafi a kasar germany cike da zuciya mai karfi da cikawa mahaifinsa burinsa na ganin ya zamo cikakken likita dan yataimaki al"umman musulmai, Anisa tana tre dashi a gdansa ta zamo tamkar kukunsa itace abincinsa na safe da yamma a bisa ka'idarsa na cin abinci guda biyu kamar yadda ya tsarawa kansa, ko kusa Anisa batayi niyyan zaman gdan khalifa ba illa soyayya data rinjayi zuciyarta wadda ba ta barinta tayi tasiri a tare dashi, duk abinda yace mata dashi take amfani, yana matukar gamsuwa da nau'ikan abincin da take shirya masa kuma yana yaba mata tare da nuna mata jin dadinsa, lamarin dayayi mata dabaibayi knan take jin cewa data sabawa dr. khalifa gara ita ta matsawa kanta, babbar abin mamakin shi ne duk irin yadda ake neman soyayar mace ga da namiji zuciyar anisa ta gama nisan kiwo a ckin son khalifa amma a takure take da zaman gdan na sa sbda bbu abunda yake hadata dashi sai hirar duniya ba batun soyayya, idan gari yawaye tagama masa abin karyawa zai fita zuwa makaranta itama za taje ta ta, idan tadawo sai tayi abincin yamma, in dare yayi zai shirya ya dau ado yafice yawon zaga gari yayin dazai barta a gida kamar wata yar jiran gdansa, sai ya gama gararin ta zai dawo yabarta a falo yashige dakinsa, anan take kwana, wani lokacin tanaji zaiyi ta hira da yammatansa taci kukanta tagaji tahakura, idan tayi yunkurin barin gdan sai taga wata dai sabuwar damuwa ce za ta hada kanta da ita idan ba ta ganinsa. Yau ta tashi da kasala zuciyarta bbu dadi tahada abincin safen kamar yadda tasaba tashiga falon fuskarta bbu walwala, dr. khalifa na zaune teburin cin abinci bai fara cin abincin ba magana yake a waya tazauna tana mai kallo, a kullum shi me kyau ne amma kyaun dayayi yau na daban ne, wani irin abu taji ya kara turnike mata zuciya, idanuwanta suka kada jajur tazauna kan kujera taci gaba da kallonsa yanata hirarsa a waya cike da nishadi abubuwan dayake fada suka cigaba dasa zuciyarta a wani yanayi tadinga jin cewa meye amfani zamanta a gdan khalifa kullum ranta na baci, bata san inda tadosa ba, ya kamata tayiwa kanta fada. Bayan ya kashe wayar ya kawo ganinsa gareta yace "ya akai sister an tashi lfya ko,? Wani irin kallo tayi masa wanda bai taba gani ba tare da ita yataso zuwa gabanta yatsaya hannayensa zube ckin aljihun wandonsa yana kayataccen murmushin nan na sa mai kayatar da zuciyarta amma yau takaici ne yakara rufeta, hawaye suka taru a idonta tai sauri tashige daki. Khalifa yatsaya shiru yana kallon kofar dakin nata cike da mamakinta, ko dayake bai kamata hakan yazamo abun mamaki ba gareshi don yanada tabbacin son da Anisa ke masa ne yasa tayi shahadar zama a gdansa tare da sadaukar da kanta gun hidimar dafa abinci da gyara mai gida, hatta gadonsa ita ke gyarawa za tawanke mai toilet tagyara mai kayan sawar sa da komi na sa, in banda ya dage akan bai so tai masa wanki da gugar kayansa da tuni ita ke wankewa don har ta fara ya yi mata jan ido yace ba zai yiwu ba ayyuka za suyi mata yawa, ita ba lada zai biyata ba ballantana yadinga biyanta kudi ,damuwarsa itace bai san dawani ido zai dubeta ba ranar data gaji ta bayyana mai batun soyayya da bakinta tare da bukatar aure, alherinta yanada yawa a gareshi. Bai jima da fara zuwa makaranta ba yasamu aboki guda daya mai suna Faisal wanda yafito daga gda Nigeria jihar kaduna, Faisal tantirin matashi ne mai budaddan ido yadda khalifa ke da farin jinin yammata haka faisal yayi fice a wannan fannin, sa'ar da akayi shine faisal na da kokarin karatu, wannan shi ne dalilin dayasa khalifa yaji dadin abota dashi bayan haka faisal ba bako bane a kasar germany ya saba zuwa kuma yanada yammata da yawa, tun da suka fara abota khali:a yasaki ransa sosai ko yaushe suna tare sai lokacin barci suke rabuwa anan fa 'yammata suka fara kawo kansu ga khalifa, son karatu dayake yasa bai son su shiga jikinsa sosai don kada su shagaltar dashi. A yammacin jiya bayan sun kammala da makaranta wata budurwar khalifa mai suna shukura dasuke cewa 'shu baby'ta nace akan sai ta biyoshi gdansa yau dai ta tayashi kwana tace in kuma bai sonta yafito yagaya mata, yace "nikam ba na bukatar kwananki a gidana kiyi hakuri. Tace "ni na rasa dalilin dayasa kake min haka ko dai matar aure gareka a gdan. Faisal ya ja tsaki yace "ke ce kika kwallafa ranki kan wannan wahallaln ina mamakin dabi'unka khalifa har yaushe kanada matsayi irin wannan a rayuwa za ka takura kanka. Khalifa yace "faisal na fi shu baby bukatar ta a gidana ina kaucewa hakan ne sbda Anisa. "Anisa ? Faisal yafadi ckin mamaki. Ya amsa mai da fadin "Anisa mana, anisa ta cancanta in kaucewa abinda zai bata mata rai tana hidima dani sosai. Faisal yace "ka ga tunda ba ka iya debe kewar rayuwa da ita kasallameta daga gdan mana kadauki yaron gda wanda za ya dinga maka duk hidimar da Anisa ke maka tunda ba kudin dazaka biya karasa ba, yaya za ayi kazauna kana shakkar sakewa a gdan ka sbda Anisa, gskiya kasauya tunani. Tausayin anisa yakeji sosai a ransa shi kansa yana bukatar mai debe me kewa a gidan ba zai yiwu yadinga kwana shi kadai a gado ba bayan yanada ikon yin hakan. Yayi ajiyar zuciya yamike da niyyar yaci abincinsa yabar gdan, sai yakasa yanufi dakin data shiga yabude tana kwance rub da ciki bisa gado tana kuka, yahaye gadon yakwanta kusa da ita yana shafa bayanta da fuskar ta cikin muryar nan tasa mai taushi da kayatar da zuciya yace da ita "bansan dalilin wannan kukan naki ba Anisa in dai ina da matsayi a gunki na hadaki da Allah ki bayyana min damuwarki. Tabude idonta zuciyarta a karaye tace "Abbakar ba za ka iya min maganin damuwata ba da za ka iya da bamu kawo wannan lokacin cikin wannan yanayi ba. Yace 'haba anisa Allah musuru gareni da zan san damuwarki har in magance miki ita alhali baki sanar dani damuwar ta ki ba. Tamike zaune tana goge hawayen dasuka cigaba da zubo mata tace "Abbakar meye dalilin zamana a gdan nan? Ya amsa "kauna. Me yasa kace kauna? Ya amsa "Na san babu abinda zaisa ka zauna da mutumin da ba ka kauna, dan haka kaunar da kike min ce tasa kika zauna tare dani. Bayan wannan za ka iya rantse min da Allah akan cewa bakasan wani abu a zuciyata ba game da kai. Yace "to in banda abinki anisa akwai wanda yasan abinda ke cikin zuciya bayan Allah? Ya matso jikinta sosai yakamata yarungume yayi mata kiss yace "kidaina sawa zuciyarki komi game dani kidaina bari ranki yana baci duk abinda kike bukata zan miki. Ya yi hakan ne dan yahanata fadin abinda yasan tana daf da fadinsa, yashga shashafa mata bayanta da cinyoyinta nan da nan jikinta yayi sanyi tadinga jin wani irin abu na yi mata yawo a jiki, so ya yiso a zuciyarta kallon kyakyawar fuskar khalifa ya hanata ta hanashi aiwatar da abinda yake mata alhali nasihohin mominta na ta kai kawo a zuciyarta, zuwa can khalifa yadinga fidda numfashi dasauri dasauri yana cakudata yadda yaso, abin yafara ba ta tsoro tayi kokarin janye jikinta daga na sa yayi wuf yakamota yana fadin "kar ki gujeni a wannan lokacin ke ce kika ja ra'ayina ba zan iya hakura dake ba ki daure kibani hadin kai zan maki maki duk abinda kikeso. Ya kwantar da ita bisa gado yadanneta da faffadan kirjinsa yarufe ta ruf yana mata kiss, gabadaya hankalinta ya tashi sosai sai jikinta yake rawa, a haka dai khalifa yasan ta diya mace yayi mamakin yadda yasanta a matsayin sabuwar budurwa wadda bata taba sanin da namiji ba, dama "yammata suna kaiwa wannan lokacin da budurcin su? A DAREN FARKO 15 yamike yayi wanka yafito falo cike da nishadi yaci abincinsa bai koma dakin ba yafita abin da yasawa ransa shi ne ashe yanada abar hutawa a gda tun farko yaki ba ta kai . Anisa tayi kuka tayi kuka har taba uku lada, zazabi da ciwon kai suka rufeta takasa tashi, takira number ramat tace "ke ni fa ba zanzo gdan wannan abin jin kan tsiyar ba ke dai da kike mayen sonsa kikaga za ki iya zaman gidansa sai kiyi tayi, ni dai ina ba ki shawarar kidauke ranki akan khalifa ba za ki iya mallakarsa ba ke ko kin mallake shi wahala za kisha dan namiji ne me garari da tsada. Anisa ta jefar da wayar taci gaba da kuka sam dawani ido zata dubi mominta ko da ta san cewa ba za tasan abinda yafaru ba abin takaici ne ace ta karya alkawarin datayi wa momin ta ta na cewa za ta rike mutuncin kanta, shin ina makomarta a gun khalifa, shin meye amfanin zuwanta germany ne? **** Bayan tafiyar jiddah london karatu abunda su hajiya sude suka maida kai shi ne yawon gdajen malamai da bokaye wai su burinsu khalifa yaso ummi ko ta halin kaka, mafi yawan malamai na bayyana musu cewa khalifa fitinannen yaro ne mai jarabar kwadayin mace amma bbu batun aure ko kadan a zuciyarsa, haka shi mutum ne da ba ya son raini da ace yanada sausaucin ra'ayi zai iya kula ummi da sunan soyayya tunda da sha'awa mai zafi amma a bisa la'akari da yadda yanayinsa yake bazai iya baiwa ummi fuskar soyyaya ba dan gudun kada tarai na shi tunda yana ganin ta ne a karamar kanwarsa, malamin daya fara shaida musu wannan batu ya tabbatar musu da cewa wannan shi ne hakikanin ra'ayin dr. khalifa wanda yake tafiya akai, hajiya hauwa tace,"to malam ba za a iya tankwasa zuciyarsa yasota ba ko ya ki ko ya so, malam mahaifin yaron nan dan uwanmu ne matarsa ta asirce shi bai jin maganar kowa sai tata duk wannan uwar dukiyar daya tara idan bbu shi ita da khalifa za su mallaketa. Malam yayi murmushi yace "akwai hanyar hakan amma ba zai yiwu ba har sai ya dawo kasar nan dazama sbda za muyi amfani da kasar daya taka ne muyi masa aikin da mukewa lakani da bita zai zai, zaita bin ummi sai yadda tayi dashi, anan ne suka dan yi murmushi hnkalinsu yafara kwanciya. "Yace suyi hakuri nasara sai a hankali da hakuri ake samunta ba da gaggawa ba,. **** Fatima da jiddah daga can london din ke damun ummi akan tadinga neman khalifa a waya da sunan za ta gaida shi bai dace tabar damuwa a cikin ranta haka ba, suna ba ta wannan shawarar ne saboda ganin yadda hnkalinta ke tashi musanman fatima da ke kusa da ita tana ganin yadda ummi ke kuka akan rashin khalifa tun tana boye wa har kukanta ya bayyana ita kanta mama ta fara gane damuwar da ummi take ciki, dukda cewa ba a san abinda ke damunta ba idan ta tambayeta sai tace bakomi, mama ba ta son takurawa ummi sbda tanajin dadin zama da ita. Rannan dai da fatima ta matsa mata akan sai ta kira khalifa a waya tayi murmushi tace "fati idan yabamu amsar da za ta daga mana hankali fa? da muguwar rawa ai gwamma kin tashi, fatima tagirgiza kai tace "wannan hujjar ta ki ba za tasa mi ta zama ckin damuwa ba, idan kin ce da muguwar rawa gwamma kin tashi ai kuma kar ki manta ance a rashin kira karen bebe ya bata kuma a rashin tayi akan bar arha, ummi tajawo wayarta ba tare da ta ce komi ba ganemo nomban khalifa takira ckin sa'a tashiga. Bata jima ba tana ringing yadaga cikin kasaitacciyar muryarsa yai sallama gaban ummi na faduwa tasa hands free dan fatima taji da kunnanta. Ta gayar dashi ya amsa tace "ka gane me magana yayana? Yace "na gane mana ba ummi bace. Tace "ni ce kira nayi dan mu gaisa na ga tun tfyarka kana tmbayar kowa a gdan nan amma ban da ni, bansan laifin da nai maka ba, . Yayi dan jim kamar ba zai amsa ba, daga bisani yace "ina cewa kowa lafiya? idan nace kowa lafiya kina ciki. Ta ce "shi knan nagode yaya karatu.? Ya amsa "karatu Alhamdulillahi. Za takara magana taji dif ya kashe wayar tayi murmushin takaici tace "kin ji ko? Wadannan abubuwan ne suka sa ba na son bugawa khalifa waya, ba wai dan ba na jmson jin muryarsa ba kullum farin cikina ko da a waya ne in dinga hira da khalifa ina jin muryarsa amma ba zan samu wannan hadin kan daga gareshi ba, sbda ba ya bukatar soyayya dani. Hawayen dasuka zubo mata yahana. ta cigaba da magana, hankalin fatima ya kartashi taji tsanar khalifa ya kara kamata, wai wani irin mara imani ne wannan tasa dankwalin ta tana sharewa ummi hawaye, tace "ki yi hakuri insha Allahu khalifa zai zamo mallakinki. Ta ina? Akwai wanda zai yiwa khalifa auren dole? idan har kuwa ba auren dole za a yi masa ba to ba zan same shi ba don baya sona, rokon dazan miki daya neduk yadda mama za tayi miki akan ki gaya mata abinda yake damuna kada kisake tasan cewa khalifa nake so. Fatima tayi mata wani irin kallo tace "matsalarki knan ummi banga ta inda za a samu mafita ba ana wannan boye boyen. A DAREN FARKO 16 .Sai da dare yayi sosai khalifa khalifa yadawo gdan tare da shu baby yau ta yi masa nacin da dole ya amincewa kwananta. agdansa, ahi kansa bai san dalilin dayake gudun kawo mace gdansa ba sbda anisa, tun daga nau'in kayan jkin shu baby za kasan lalacewar ya yi yawa, a ranta tace "tabbas yau sai na ga abunda khalifa yake tsoro, tabi bayansa zuwa ciki, anisa na kwance a bisa kujera a fali tana kallon wani film a wayarta, duk zamanta a gdan bata taba ganin khalifa ya zo da mace ba duk da ta san yana tare dasu sai fa yau, suka dubi kowa ita da shu baby kowacce tashaki wani masifaffan kishi a zuciyarta, anisa ta maida kanta tana kallonsu suka wuce dakinsa, bby tace "sbda wannan figigiyar yarinyar dama kake kin kawo ni gdanka? Yamata wani irin kallo yace "kiyi abinda ke gabanki shuu wannan kanwata ce ba na son.... Bai cigaba da maganar ba yashige toilet yayi wanka yayi alwala, bayan ya idar da sallar dake kansa yaleka falon yace "anisa wannan da kika gani abokiyar karatuna ce ki kawo mana abinci daki kuma ina so ki gaisheta. Yawan kukanta yana ba shi haushi ganin ta fara share kwalla yasa ya koma cikin daki, tunanin da anisan tayi shi ne wai ita wacece ne a gun dr. khalifa da har zai gujewa bacin ranta, tunda takawo kanta zama a gdansa dole tahakura da duk abinda za taji ko tagani, a sanyaye tamike tashirya abinci a tray tashiga dakin da sallama tatsuguna ta gaisar da baby tafita, kallon daya bita dashi yakara baiwa baby haushi taja tsaki tabude abincin taxuba a plate tafara ci, dandanon abincin ya burgeta ga takaici da kishin wadda tadafa, shima yazuba na sa yana ci yana fadin "kai aniaa ta iya girki mijin ta ya mori mace. Sun kwana suna morar junansu ta hanyoyi daban daban wadanda suka kware a kansu ko wannenau ba baya bane a wannan harkar, sun gamsu iya gamsuwa hakan yasa kowanne zuciyarsa wasai ba damuwa, khalifa na son yayi bacci sosai amma yunwa ta hana shi baccin dole yafito falo sai dai tebur wayam yaleka kicin ba abinci bbu anisa yadawo dakinta ya iske doguwar takarda mike bisa gado tun kafin yakaranta ya san abinda ta kunsa yace"shikenan shukura ta ja min asarar mai dafa min abinci da kula da gdana. Salam. Abbakar ina maka ban kwana tare da fatan allah yasa kagama karatunka lafiya ka koma gda lfya, xamana a gdanka ya kare ba tare da na gaji da ganinka ba sai dai yin haka shi yafi mana ni da kai, na gode kwarai dagaske da masuakin daka ba ni a gdanka duk da cewa hakkana bai cimma ruwa ba na samun masauki a zuciyarka wanda shi ne makasudin zuwa na wannan kasar, amma dai na godewa Allah daya ba ni ikon aikata abinda natabbatar zai wahala ka manta dani har ka koma ga mahallincinka, ina rokaonka a duk sanda katuna dani kai min addu'ar alheri. khalifa na zo wannan kasa ne dan neman soyayyarka da take ta cin zuciyata tun daga ranar da idanuna suka fara ganinka na yi suk kokarin da zan iya na ganin na ja raayinka banyi nasara ba, tun daga gda nigeria har izuwa yanzu dana tabbatar ba zan same ka ba, daga karshe ina maka fatan dukkan alherin duniya dana

Chapter 7 of 19