Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Abba yace "to fatima mai jiki dai ga shi nan sai yadda Allah yayi, soyayya ce mai wahalarwa ya hdu da ita, sai dai hakuri. Mama dai shiru tayi tazuba tagumi tana ganin ikon Allah, magana in dai ta khalifa ce abba ba ya kawaici akanta, yaci gaba da fadin "fatima dubi halin da khalifan yake ciki har yanzu bai san wanda yake kansa ba, ni wlhi ban taba ganin inda akewa mutum irin son da khalifa yake miki ba, ga shi ba mu da ikon bayar dake gareshi, shin yaya za muyi da wannan tashin hankalim. Kukan fatima yafito karara tana juya kanta mama tace "Alhaji bai kamata kadinga fitowa da fatima irin wadannan maganganun ba sbda aikin gama ya gama alkalami ya bushe, hakuri dai khalifa zaiyi Allah yatashi kafadunsa. Cikin sanyin murya abba yace "ai nima ba wani abu nace ba. Fatima tace "Abba don Allah karoki babna ya janye mganar aurena da musbahu yana jin maganarka tare da girmama bukatarka, wlh nima khalifa nake so. Mama tarike hannunta tace "fatima mun san kina son khalifa Allah ne bai kaddara Khalifa mijin ki bane shiyasa duk abinda yafaru yafaru, wannan son zuciya ne karara idan har muka nacewa iyayanki da rokon su bawa khalifa ke,sbda shima musbahun yana sonki ba ya son yarasaki, idan mukayi amfani da wata dama da muke da ita muka rinjayi iyayanki suka ba khalifa auranki bamuyi amfani da hadisin manzon Allah dayake cewa imanin dayanmu ba ya cika har sai ya kasnce mun so wa yan uwammu abinda muke so wa kanmu, sannan na biyu mutane za su zagemu don a zahiri munyi rashin adalci mu mun san iyayanki basu hana mu auranki dan kiyayya ba sai dan girman alkawarin dasuka wa musbahu. Fatima takara rikicewa da kuka tana kallon dr. khalifa take cewa wallahi mama ba na son musbahu, khalifa nake so, ba ina fadin hakan bane don a gabanku ne ina son shi ne kawai don shi ne ra'ayina na amsa wa iyayena auran musbahu a lokacin da ban san meye so ba, yanu na fahimci inda rayuwa ta dosa don Allah mama kutaimaka ku fahimtar da iyayena kada su dauran auran da ba na so xan iya shiga ko wani hali idan ban auri khalifa ba. Aka yi tsit dakin kukan fatima kadai ke tahi, ummi kallon iyayan khalifa da fati kawai take tana girgiza kai ta ji dadi da hawayenta basu zuba ba domin ta gaji da kuka lokacin kuka ya wuce a gunta illa neman mafita, son kai ba musbahu kadai ake naman yi mawa ba har ita gara ma musbahun da yake so ake kwace masa matr ana ta nanata yadda za ayi dashi ita kuwa ba wanda yadamu da damuwar ta idan ma mutuwa za tayi tayi ta mutu, wai fati ce ke kuka a gaban iyayan khalifa tana rokonsu ita dai tana son khalifa, takallesu gaba daya tagirgiza kai tare da cije lebe. Anty sadiya tace "mama kinga abinda nake gaya miki wai meye amfanin yin shirun da akayi alhalin an san halin da zuciyoyin yaran nan ke ciki. ya kamata ayi musu adalci, shi musbahu bai san aure nufi ne na Allah ba, a zaunar dashi a yi mas bayanin kudubi halin da khalifa ke ciki daga ganin fa katin daurin auranta yashiga wannan halin ina ga idan an wayi gari yasan an kaita gdan musbahu? Tagirgiza kai. Gaskiya mama a san abin yi kada fa azo ana nadamar da ba ta da amfani gara tun kafin lokaci yagama kurewa a yi wani abin. Abba yace "maganarki haka take sadiya tabbas a yau din nan zan bi hanyar data rage tarage don ganin ankawo karshen wannan matsalar wannan lamarin na khalifa ya fi karfin a sa ido dole a yiwani abin a kai. Kofar dakin tabude dr. mansoor yashigo tare da wata nurse a bayansa ya isa gaban gadon dr. khalifa yace "har yanzu bai farka ba. Abba yace "ai ko motsin kirki ba ya yi nifa in banda ina ganin numfashinsa da yanzu na ce khalifa ya mutu. Dr. mansoor yadaga hannun khalifa ya mayar ya ajiye, yadakko wata karamar na'ura yadaura mai akan kirji yana latsawa tare dasa wani abu a kunnansa, zuwa can yacire yajuyo yadube su gaba daya yakira sunan nurse din da ke tare dashi mai suna jamila yace "ki lura dashi sosai. Tace "ba damuwa sir. Yamaido ido ga abba yace"kuyi hakuri Alhaji insha Allahu khalifa zai samu lafiya ni yanzu xan tafi gida. Abba yace "haba dr.yaya za kace za ka tafi bayan har yanzu ko farkawa khalifa baiyi ba. Dr. mansoor yace "Alhaji kada kadarra cewa samun lfyar khalifa yana hannuna wannan hukunci ne na Allah,Allah yahore mana taimakon al'umma ta hanyar ilimi daya azurta mu dashi a bisa yardarsa muke yin komi ,nan da dan lokaci kadan likitan daya karbi aiki zai shigo yaci gaba da kula dashi, Allah shi ne me ba da lafiya, kafin dai in tafi inaso idan da hali ayi duk kokarin da za ayi a nemo abinda zai sanya khalifa farin ciki yayin daya farka ma'ana da zarar ya bude idonsa yakasance ya ga wani abu dazai faranta masa rai, wannan zai taimaka gun sanya natsuwa a zuciyarsa. Abba ya waiwayo yadubi fatima sannan yamaida kallonsa ga likitan yace dashi "ka ga wannan yarinyar? Dr. mansoor yadubi fatima dake tsugune gefe tana sharar kwallah abba yace "to itace yarinyar da khalifa ke so kuma iace silar fadawarsa cikin wannan halin. Dr. mansoor yace "Alhaji kana nufin itace fatima. Dasauri Abba yace "itace kuwa likita ina kasan sunanta? Yace "a jiya da kuka kawo khalifa lokacin da numfashinsa yafara dawowa bayan salatin Annabi da yayi sunanta muka ji yana ambata tun daga nan muka kaddara cewa a dalilin mace yafada ckin wannan damuwar, to tunda ga ta meye abin tashin hankali ba sai a bashi auran na ta ba kowa yahuta. Abba yayi murmushin takaici yana girgiza kai yace "Likita wannan yarinyar tafi karfin khalifa, kudi ba sa sayan mutum da ace kudi na sayan mutum ko nawa fatima takai sai na siyawa khalifa dan in rabashi da wannan damuwar dayake fama da ita, saura kwanaki biyu kachal awa 48 fatima tazama matar wani ban san halin da khalifa zai shiga ba, Inalillahi wa inna ilaihir raji'un. Dr. mansoor ya jinjina kai yace "gaskiyar magana abba tunda halin da khalifa yashiga ya kai haka to kanemi iyayan yarinyar nan ku daidaita magana su zo suga halin da danka yake ciki su taimaka kowa yataimaki wani Allah zai taimake shi, kada kabari wani ya auri fatima alhali khalifa na ckin wannan halin. Akayi shiru gaba daya har Dr. mansoor yafita bbu wanda yasake magana. A DAREN FARKO 29 Karfe daya daidai Abba yace zaije gida yayi wanka yayi sallah yadawo. Mama ta biyo shi har mota tana rokon yadaure yaci abinci. Ya dubeta da jajayen idon sa yace "cikin nawa ne bbu dadi tun dazun nake jin zuciyata na tashi kamar zan yi amai ga kaina na juyawa. Tace "kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka komai na Allah ne, duk wadannan abubuwan dake fruwa idan Allah ya yi fatima matar khalifa ce zai aureta, za kaga yadda Allah zai juya al"'amarinsa daga damuwa izuwa farin ciki, babu abinda ya gagari Allah shi ne me yadda yaso a lokacin daya so, yayin da duk damuwar da za ayi da duk halin da za a shiga idan Allah bai kaddara matarsa bace sai dai mutari muyi hakuri muyi fatan alkhairi. Abban yadora kansa a kujerar da yake kai idonsa na kallon sama ,sun samu shiru daga bisani yace "Hakane sai na dawo. yaja motar ita kuma tadawo ciki. Tace "Fatima ku ci abinci kutafi gida ku huta don Allah ki daina yawaita wannan kukan ba zai yi mana maganin komi ba sai addu'a da hakuri. Cikin shashekar kukan tace "ni kam mama a idanuwa na ba za su taba daina zubar da hawaye ba sbda tashin hankalin da take ciki. Mama tace "kiyi hakuri fatima kada ki ja abin da za ki bata da iyayanki bayan a baya kuna zaune lfya kullum inna tana yabon halayyarki, iyaye suna da kima sosai a gun dansu in dai da yana son a gama da duniya lfya to yabi iyayansa, na tabbatar ba za su so ace ba ayi auranki da musbahu ba sbda shi ne xabinsu, hakan ba yana nufin suna kin khalifa ba, idan muka ce iyayanki ba sa son khalifa ba muyi musu adalci ba tundamuna sane da yadda al'amuran suke. Fatima duk da cewa ni na haifi khalifa na fi kowa jin ciwon da tashin hankali halin nan dayake ciki, idan a son raina ne izuwa yanzu yakasance kina dakin khalifa a matsayin matarsa sbda son da yake miki kowa ya san bashi dawani farin ciki wanda yawuce ya mallae ki, yanayi ne wanda kowa yasan khalifa bai taba samun kansa a ciki ba, ai wannan dalilin ne yasa kowa yake tabbatar da son da yake miki na gskiya tun yana fada da baki har gashi yau a gadon asibiti bai san waye a kansa ba, to amma duk da haka ba zan rufe ido a kan abinda ba ma gskiya da adalci ba na hakura na zubawa sarautar Allah ido idan Allah ya yi khalifa zai rayi zai tashi, ni dai na san rayuwa cike take da jarabbawa iri iri, komi lokaci gare shi duk yadda tsanani ya tsananta insha Allahu akwai sauki da zai biyo bayansa, a ckin alkur'ani mai girma ma Allah (SWT) yana fadin, dukkan tsanani suna tare da sauki. A wannan lokacin fatima dora kanta tayi bisa cinyar mama tana kuka har sai da hawayenta suka jikawa mama zaninta, lamarin dayasa itama mama takama sharar da kwallah duk kokarin data dinga yi gun hadiye hawayenta tun safe abin ya ci tura, wannan karon kuka take sosai, sai anty sadiya da ummi ke basu hakuri. Mutmryar khalifa tasa suka mike gaba daya a rude suna kallonsa, idonsa yabude yana fadin "Lahaula wala kuwwata illa billahil azim. Gaba daya suka iso kanaa suna masa sannu. Bai fahimci a inda yake b kansa a rude yake don haka yamaida idonsa yarufe, rudewa tasa Fatima ta manta tana tare da mahaifiyar khalifa takamo hannun khalifa tana fadin "Don Allah katashi daga barcin nan ya isa haka. Kamar a mafarki yake jin muryar fatima, sai yayi saurin bude idonsa, ai kuwa fatin ce a kansa ya zuba mata ido har yanzu dai a tunanin sa rayuwar mafarki yake, yace "Fatima. Ta amsa "Na'am khalifa. Ya matse hannunta yace don Allah fatima kada ki auri wani ba ni ba mutuwa zanyi idan na rasaki, mafarki nayi wai na ga katin daurin auranki fatima bai dace ki yi min haka ba ko so ki ke in mutu? Ni kadai iyayena suka haifa, ko su ya dace ki tausaya wa. Fatima tarufe me baki tace "ka kwantar da hankalin ka insha Allahu za ka mallakeni kasan nima ina sonka. Bayan khalifa ya yi sallolin dake kansa yana zaune kan darduma fatima thada mai ruwan shayi shi kadai yace zai iya sha gaba daya jikinsa yayi sanyi kallon kowa yake kadan kadan yake iya bude idonsa, kowa yazamo dan kallo, fatima ce ke da bakin magana a gun, shayin ma ita ta matsa masa tace sai ya sha gudun kada tayi masa hushi yasa ya hakura zai sha, amma bbu abunda yake sha'awa. Kofar dakin tabude, abba da malam musa mahain fatima da musbahu da inna suka shigo. Fati tatashi zumbur daga gaban khalifa domin zaune take sosai a gaban na sa tana rokon ya daure ya dan ci abinci ko kadan ne, kunya ce takamata sosai musamman ganin kallon da iyayanta ke mata duka fuskokin su ba walwala, ballantana musbahu wanda yake jin kamar ita kanta fatin ya shaketa kowa yahuta. Bayan sun gama gaisawa da tambayar jikin khalifa, musbahu yadubi malam da Abba yace "Don Allah ku yi hakan baba a kawo karshen wannan damuwar a yau, har abada hankalina ba zai taba kwanciya ba idan ya kasance dan uwana musulmi yana ckin damuwa a dalili na kuma zan iya taimakawa gun magance masa damuwar. Musbahu yayi shiru yakasa ci gaba da fadin abin da yayi niyyar fadin sbda wani irin abu da yaji ya tokare masa kirjinsa da makwagaronsa haka bakinsa yayi masa nauyi idanuwa sun yi jawur, dakin yayi tsit kowa kallon tausayi yakewa musbahu sbda matsananciyar damuwar data bayyana a fuskar sa. Da kyar yaja dogon numfashi yaci gaba da fadin "Baba na san ina son fatima har ga Allah ina jin daci da ciwon rabuwa da ita amma ba yadda zanyi kukan ya zame mini dole sbda in da baki yakarkata nan yawu ke zuba, in ji masu iya magana, tun kafin mukawo ga wannan halin na tabbatar wa zuciyata fatima khalifa take so, na auna abubuwa dayawa na ga dai hankalinta ya karkata akai wannan ne yasa na tilasta kaina nabar masa ita, na barwa khalifa fatima don Allah baba ku ma kuyi hakuri ku ba shi ita, ku dubi yanayin dasuke ciki ku kauda tunanin komi mu kaddara haka Allah yanufa, wannan rana da aka sa za a daura mana aure da fatima a daura da khalifa ina fatan Allah yasa haka shi yafi alheri gare mu gaba daya. Mama tadaga mai hannu tace "gaskiyar magana ba za ayi haka ba musbahu, tun yaushe kake son fatima, tun yaushe aka ma alkawarin an ba ka ita, amma lokaci daya a rufe ido a yi maka kwace, wane irin kallo mutane za suyi mana knan? fassarar da kowa zai mana ita ce ta rashin adalci, khalifa ne zai yi hakuri da fatima. Musbahu yayi murmushi tare da girgiza kai yace "mu wuce wannan gun mama tunda har fatima ta amince khalifa take so shi yadace a aura mata, ita diya mace in har ana son a zauna lfya da ita a bata wanda take so. Ya kasa ci gaba da maganar sbda wani abu dayake jin yana tokare masa makoshi, kirjinsa yana mai nauyi gudun kada suga hawayansa yatashi yafice daga dakin yanufi hanyar fita daga asibitin cikin sauri yasamu wata hanya a bayan asibitin yashiga yazauna a kasa yajingina dawata katanga yahada kai da guiwa yana ajiyar zuciya, a lokacin ne yasaki hawayen da yake ta boyewa yakama kuka mai ciwo da karfi, hannunsa daya dafe da kansa, kai da ganinsa ka san yana ckin tashin hnkali mai yawa da damuwa, tabbas yau ya san ya rasa fatima ya rasa yarinyar daya ke matukar so so mai yawan gaske, yarinyar da bai taba hadata da wata diya mace ba ballantana yakalli wata da sunan so bayan ita ba, hakika ba ka sanin kana son abu sai sanda karasa shi, wannan ciwon dayake ji a ransa ya san har ya mutu ba zai barshi ba, amma wajibi yayi hakuri fatima ba ta son shi abinda yayi shi yafi masa. A DAREN FARKO 30 A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya samu bakin tattauna wata magana sai da suka dawo gida gaba daya. Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a rumfar inna tana jiran abinda za ace mata musamman ganin yadda malam musa yazauna ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da zama a yi bikin na ku a can ko? Inna tace "Ni ma haka na gani malam. fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa. Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka, misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a walakanta shi a banza ba. Malam yabude baki zai yi magana wani kanin fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa malam cewa ga abba can a waje yace yana son ganinsa. Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba suka zauna suka ka ra gaisawa. Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba, idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa. Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki yake mai son mutane da kula da hakkin makotaka yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki dansa ba. Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi tsammanim hana khalifa fatima nake son yi. Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi nazari na sawa zuciyata hakuri. Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba daya, na bawa khalifa fatima. Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba. Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba Allah na gani xuciya b dadi . Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai kaddara matarsa bace. Tace "to malam yanzu ina musbahun? Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi ba nake ta kiranta bata shiga ba. Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta? mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda ace yarasa? haba ai abin da ciwo. Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar burinta akan dr. khalifa xancen ya kare. Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri. Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi yanzu? Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni. Yace "Subhanallahi *in sha magani? Tace "yanzu dai zan sha. Yace "zan iya zuwa in ganki? Tayi shiru, yace "ko akwai matsala? Tace "Gani nayi ba ka da lfya. Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure damuwa ta ta kai matakin data kai amma da yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin ki ba. Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo gdan kuma zan fito zaure kaganni. ***** A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa knan za a daura auran khalifa da fatima nan da kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya ,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan uwa a waya yana shaida musu batun daurin auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta. Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin al'amarinsa to karya damu da surutun mutane. Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai ba. Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki karba don kada mutane su ce ya yi son kai? A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan yafara cika da mutane maza da mata yan taya murna. Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu, Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen auran gadan gadan. Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata da abinda take so a zauna lfya, idan har muka hakura da khalifa to mata muka rako duniya, wannan dogon lokacin damuka dauka muna nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma gun malam. Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba. Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi mamakin aikin malam, ke de muje muji ta bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa miyar can yunwa nake ji.A DAREN FARKO 30 A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya samu bakin tattauna wata magana sai da suka dawo gida gaba daya. Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a rumfar inna tana jiran abinda za ace mata musamman ganin yadda malam musa yazauna ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da zama a yi bikin na ku a can ko? Inna tace "Ni ma haka na gani malam. fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa. Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka, misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a walakanta shi a banza ba. Malam yabude baki zai yi magana wani kanin fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa malam cewa ga abba can a waje yace yana son ganinsa. Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba suka zauna suka ka ra gaisawa. Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba, idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa. Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki yake mai son mutane da

Chapter 13 of 19