Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har sai da zazzabi da ciwon kai suka rufeta.. ***** Wai shin masu karatu kutambayeni ina musbahu yashiga mana? ku biyoni kuji. Lokacin da musbahu ya tabbatar ya rasa fatima sai ya kaddara a ransa cewa dama ba matarsa bace, . Musbahu gdan kawun sa malam habibu yafara zuwa ya sanar dashi abinda yafaru, kawun ya ji b dadi a ransa amma ba yadda za ayi in dai mutum mai hankali ne da adalci babu yadda za ayi yayi wani zargi akan malam da inna don sun rike musbahu tsakani da Allah, Allah ne bai kaddara fati rabonsa bace. Musbahu ya shaidawa malam cewa zai tafi garin bauchi gun yayar mahaifiyarsa ne sbda yana so yayi nisa da kano a dalilin ba ya so yaga daurin auren fatima. Karfe biyar da rabi na yamma yashiga gdan goggo mairo dake ckin garin bauchi tayi mamakin ganinsa tace "ango na amarya kaine tafe? Yace "Gwoggo ina wuni mun sameku lfya. Tace "lfya kalau yashi kaje dakin au sagiru yana nan yana barci kayi wanka kayi sallan xan aiko ma da abinci idan kaci sai kazo mu gaisa sosai. Sagiru kusan sa'an musbahu ne shi ne dan goggo na biyar ya biyo mata biyu maza biyu,. Tun a ranar yafara devewa musbahu kewar damuwar dayake fama da ita, sbda mutum ne me ban dariya, da alheri ga son mutane. Musbahu ya bayyana masa abin da yarabo shi da kano, sun tausaya mai sosai ganin damuwar dayake cki yasa nan take goggo tace ga diyarta nan hafsa in dai yana son ta ta ba shi, musbahu yayi dan jim bai ce komi ba, goggo tace "ko bata yi maka bane in dai ba ka son ta babu dole. Yace "ba haka bane goggo ina tunanin yadda malam yace ya bani fatima tace ta amince sai da na saki jiki da ita nabata amanar soyayya ta sannan tace ba ta so na, dr khalifa take so shi ne ra'ayinta nikuma ra'ayin iyayanta, nayi mata uzuri cewa ba ita ta zabeni ba niyyar biyayya ga iyaye tayi . Gwoggo mairo tayi murmushi irin nasu na manya tace "musbahu duk wannan abinda yafaru kaddara ne Allah ya hukunta cewa ba matarka bace, idan xa ka lura duka kwana nawa yarafe a daura maku aure khalifan ya bayyana, da ace matarka ce ba zai bayyana ba ko ya bayyana kuma ba zaiyi tasiri a zuciyarta takalle shi da sunan so ba. Ba wai ina gaya ma hakan ne don kaso hafsa ba, in kana raayin hafsa ga ta nan in ba ka ra'ayi kayi zamanka har Allah ya baka wadda kake so. Musbahu yakara dukar da kai yace "wallahi goggo hafsa tafi karfin namiji yaki ta, in ta amince dani ma ta yi min alfarma domin ta girmi ajina. Goggo tace "karka sake fadar haka kaje gareta ku daidaita kanku, Allah yatabbatar mana da alheri. A cikin sati biyu musbahu da hafsa suka fahimci juna, yasameta yarinya mai sauki da son mutane kamar mahaifiyarta, ga ladabi da biyayya, kowa ya yi farin ckin wannan al'amari a dangin su, nan da nan aka tsaida magana babansu hafsa yace zai ba musbahu aron gda su zauna kafin su koma kano, ba wani kudi musbahu yakashe ba illa iya abinda yayo sai da goggo tai masa fada cewa daya suke dashi da hafsa a gdan nan. Bayan wata guda aka daura aure sukayi biki sosai suka kashe kudi, musbahu har mamakin gatan da suka nuna masa yake, aka gama biki lfya aka kai amarya dakinta, a ranar da zai shiga dakin ne yadinga tunanin abubuwan daya tanada zaiwa fatima a ranar da aka kai masa ita, ashe ba matarsa bace yanzu haka tana chan da angonta ta ma manta dashi shikuwa yana fama da ita a zuciyarsa. Sai da yadinga addu"a Allah yataimake shi yarabashi da tunanin fatima kada ya cutar da hafsa sbda ya lura hafsat ta yi dammarar zaman aure dagaske tare da biyayya, ckin ikon Allah yataimake shi yasamu natsuwa a zuciyarsa yamaida hankali sosai gun kyautatawa matarsa sukayi zamansu lfya kowa yana sha'awar auran na su. A DAREN FARKO 40 Kusan watanni shida knan da rasuwan dr. khalifa an dan samu cgaba a rayuwar fatima sbda ta fara rage damuwa har ta shiga wataislamiyya nakusa dasu da akeyi alhamis da juma'a, ta kuma fara tunanin komawa makaranta a halin yanzu ba ta da aminiyar da ta wuce jidda koda yaushe suna tare itama jiddan bata koma london din ba ta dawo da karatu? ta BUK tana karanta mass comm. kasancewarsu tare da jidda ya taumaka kwarai gun debewa fatima kewa sai dai har yanzu idan tatuno dr. khalifa takan yi kuka mai tsanani sbda soyayyar da take masa tayi mata yawa a zuci, shi yasa yau da jidda tazo mata da wata magana sai da taji kanta yana mata tsawa. Ta zubawa jidda iso kawai tana nazarin fuskarta bata katseta ba sai da taji tayi shiru sannan tamike zaune tace "jidda maimaita abinda kika gaya min yanzu. Jidda tabata rai tace "kina nufin baki ji abinda na gaya miki ba? "Na ji ina so in kara ji ne. Jidda tace "cewa nayi yayana usman ya aikoni in mika mai kokon bararsa gareki da fatan za ki amsa mai bukatarsa. Fatima tayi ajiyar zuciya tace "ni kam jidda na yi mamaki danaji wannan maganar a bakin ki, na yi zaton ko yaushe ke nake gaya wa cewa babu wani namijin da zan iya sawa a zuciyata in haka ne kuwa bai dace ki zo min da batun wani namiji ba. Jiddah tace "Fatima kin san dai ba zai yiwu ki zauna babu aure ba don dr. khalifa ya rasu dole sai dai kiyi hakuri ki amshi kaddarar da Allah ya hukunta miki yarda da kaddara shi ne cikar imanin musulmi mumini. Ko kusa fatima ba ta jin dadin hirar don haka tace "To na ji ba ni lokaci zanyi tunani. Ganin yadda fuskar jidda ta nuna rashin jin dadin maganar tasa tace "kiyi hakuri jidda ba cewa nayi ba na son dan'uwanki ba wlh zuciyata ce ke cikin matsanancin hali har yanzu karfin hali nake ni nasan abinda nake ji game da ciwon kisan da akayi wa khllifa, ,na kasa sabawa da wannan damuwar, duk namijin danace xan aura a yanxu na cutar dashi domin ba zan ba shi kulawar data dace in bashi ba, wannan shi ne dalilin dayasa na fidda batun aure a zuciya ta, zan yi zamana haka har lokacin da Allah zai karvi rayuwata nima. **** To a bisa wannan ra'ayin fatima take tafiya da gaske ba ta son wani namijin yasake shiga rayuwarta, ba ta son sake soyayya dakowa sbda wahalar datake sha, amma ina yadda kasan kofa aka bude ma maza nasu sota, wasu su kan biyo tagun malam ganin bbu fuska ta fuskar fatima, wasu ma ta gun tsohon surukinta Alhaji muhammadu mahaifin dr. khalifa kasancewar zumuncin su ya dada karfi, Abban yana da tacewa a cikin rayuwar fatima, ya maida ita kamar diyar sa dan ma dai ba t son zuwa gdan ne a dalilin yawan kukan da take,. Bayan dawowar ta daga islamiyya yau ta idar da sallar azahar inna ta shaida mata cewa mama ta aiko nemanta, nan da nan rant yabci, to kawai tace tamike tayi wanka tasa wata doguwar riga ta shadda tasa dogon hijjabi fuskarta ba fara'a tashiga gdan su mama ta tsaya a harabar gdan tana kallon dakin dr. khalifa, har yanzu bbu abunda aka taba a ciki? sa har motocin sa suna nan cikin tamfal ta jima tsaye a vun daga bisani tagoge hawayen daya gangaro mata tawuce cki tasamu mama a cikin dakinta tana kwance bisa gado da carbi a hannunta tana ja. Ganin fatima yasa tamike cke da fara'a tace "sannu da zuwa diyata. A sanyaye tazaun a kasa ta gayar da ita, mama ta zuba mat ido tace "fatima kullum kara ramewa kke kina duhu kullum b ki da kuzari da walwala wai shin haka raywa zata tfi, tunda fa ba mu muka halicci kammu ba ba mu da iko kuwa da kammu dole ne muyi hakuri da abinda Allah ya jarrabe mu. Tadinga sharar kwalla tana fadin "wallahi mama ban san yadda zanyi in daina damuwa b, damuwa ta min yawa ji nake kamar nim mutuwa zanyi. Mama tace "mutuwa lokaci gareta fatima idan kwana yakare kowa zai mutu, kidaure kidin ga sakin ranki kina walwala kuma ya zama wajibi a cikin masu sonki ki fidda guda daya ki aura, samun abokin rayuwa zai rae miki damuwa. Tadago tdubi mama tace "aure fa kikace mama, har da ke a masu cewa in yi aure kema ba ky kishin khalifa? Mama tayi murmushin karfin hali tace "Allah sarki fatima to idan nayi kishin khalifa ya zanyi, zan iya dawo dashi duniya? Ta girgiza kai. Mama taci gaba da fadin "A daran jiya Barrister Nuraddeen ya zo gdan nan gun alhaji yana son ya tambayar masa malamko zai ashi auranki, abba yace in tambayar masa ke in kin amince ba ya da matsala da barriater nura sbda ya san iyayansa, da rayuwarsa gaba daya ba bukatr sai anyi wani vincike a kansa. Kanta yakara mata nauyi zuciyarta takara kuntata tarasa abinda za tacewa mama da abba sunfi karfin komi a gareta, ga jidda na naci akan yayanta usman itama jiddah ta fi karfin ta wofantar da maganarta sbda sadaukar daranta da tayi don ganin ta ceci rayuwarta. Mama tace "kina da damar da zkije kiyi tunani, idan har mce takasance mai hankali to kada tabi ta kyale kyalen duniya gun zabar miji tazabi nagari kawai, ko dayake zabi yana gun Allah idan mutum ya dogara da Allah sai ya zaba masa miji na gari wanda zai rike shi tsakani da Allah. ***** Fatima tadawo gda cke da tunani a ranta abi? da ta lura dashi shi ne zabar mijin aure ya zamo dole in ba haka ba ba za a kyaleta ba, kuma abin takaici suna bullowa ne ta hanyar dasuke da kima a gunta. Ta bayyanawa innarta yadda sukayi da mama dakuma maganar usman yayan jidda. Inna tace "fatima matukar kina son kwanciyar hankalin mu to ya zama wajibi ki fidda miji ki aure mu ma mun gaji da surutun da akeyimana a dangi da mutanan unguwa. Fatima tamike tashige daki takira jidda a waya bayan sun gaisa tace "ki turo min Usman in gan shi. Jidda tace "sai yau kikaga damar bshi izini yazo. Haushi yasa fati kshe wayarta tana tsaki. Bayan sallar isha'i jiddah takirata tace Usman yna bisa hanya,. wanka tayi ta murza mai tashiga atamfa super ta tsaya tana kallon kanta wai yau itace za tayi zance. wayarta ta kama ringn tadaga a sanyaye tayi mai sallama, Allah yasa da fatima nake magana, Abinda yce mata knan. Ta amsa "Ni ce. Yace "to nima ni ne usman ina jiranki a kofar gda tunda yau an min izinin zuwa..Tsaye ta iske shi jikin motarsa yana danna handst, gabanta yafadi hasken fitila ya haske mata shi tun daga sama har kasa, kananan kaya ne a jikinsa, za suyi tsawo daya da dr. khalifa, sajensa ya kayatar da fuskarsa in barda haka ba za a kirashi maikyaun fuska ba. Ya amsa sullamar da tayi masa ckin fara'a yace "Gimbiya fatima kn wahalar dani da yawa, da kin san yadda nake fama da tunaninki a zuciyata da kin tausaya min baki min wannan jan ran ba. Itadai batsan abinda za tace masa ba tayi shiru kanta a kasa, yaci gaba "fatima ina fama da matsananciyar soyayyarki a zuciyata don Allah ki ba ni hadin kai ina bukatar ki ckin rayuwata, ina da damuwa mai yawa. Tayi wal da ido a lokacin ne suka hada iso tace "ban fahimci abinda kake nufi ba. Ya gyara tsayuwarsa yace "fatima na san kinsan uwa daya uba daya mu*e da jidda,na yi aurena shekaru biyu da suka wuce a nan kano matsalar da na samu itace matata farida batasan me ake kira aure ba, ina nufin duk wasu hakkokin miji da suka rataya wuyan mace farida bata san su ba ko kuma ta sansu ba za ta sauke bane sbda dalilin da ita tasani... AYYAH KUYI HAKURI RUBUTUN SUNYI DAMEJI BA NA IYA GANI... Abinda ke faruwa a gdan usman ba ya yiwa kowa dadi a danginsu sbda fitinar matarsa tayi yawa, ko dayake tun kfin auran an sha gaya msa gdan dayake neman aure ba gdan tarbiyya bane, mahaifiyar su farida sai abin da tace da babansu yake yi, kuma a haka ta trbiyyantar da diyanta mata, usman yawatsar sbda soyayya dayasa ransa . Hjiyr su farida tan da tsananin son abun duniya, son da farida ke ma usman ne yasa ta amince za ta ba shi , yayin da dabi'un gdan ke damun iyayan usman, babansa ya ce ba zaiyi aure ba sai ya samu aiki ,bayan ya samu aikin akayi bikin inda babansu yabashi gdan dasuke cki a zoo road. Da farkon auran an mori soyayya, a cikin wata na uku kachal da auran usman yafara fuskantr matsala da farida dayawa tatatara mai kawayenbanza a gda, ko da yaushe gdansa cike da "yammata wani lokacin har da zawarawa da matn aure irinta wadanda suka fi karfin mazajen su, sai yawon gdajen kawaye, abin takaici wasu yammatan har da samarinsu ke zuwa daukarsu a taya su hira a shiga har falonsa, girke girken abinci, abin takaici ba zai zo yasamu gdan sa ba baki ba sai dai yashige daki yazauna. Yayi kokarin yim hakuri ya kasa yashiga nunawa farida rashin dacewar abinda take, ranar da ya fara mata maganar fiddo da ido tayi tace "ina ruwanka dasu man? kadubi fa yadda suke girmama ka amma kace su daina zuwa, ni kadai zan dinga zama a gdannan ga unguwa shiru,ni ban saba zaman kadaici ba a gdan mu sai dai kayi hakuri. Daga nan tashiga yin allurar hana daukar ciki ba da sanin sa ba, tadaina zama a gdan tadaina mishi abinci sai randa taga daama, ya yi ya yi ya saita ta ta ki, shi dalilin daysa yafara tunanin aure don yasamu sauki tawani bangran, lokacin daya furt a gdansu kowa yai murna sbda tausaya masa da halin dayke cki, sai dai abin fargabr wace mace zai aura su zauna lfya da farida a yadda ba ta da kunyar nan ta raina kowa. Shima din bai san wa zai aura ba ya maida hankalinsa ga addu'a, kwatsam ydor idonsa akan fatima lokaci guda yaji wani salon soyayar da bai taba jin ta ba., a gdansu ya ganta wataran t zo gun jidda, byan tfyarta ykira jidda yasha kunu yana tmbyrt shin fatima ta tsaida mijin aure ne, tayi dan jim tace "yaya sonta kake? Yace "son ta nake ko ba za ta amince min ba. Tace"ko ban sani ba amma dai ina fargabar hakan zan sanar da ita. Fatima tashiga zuciyar usman kwarai dagaske yashiga addu'ar Allah ya mallaka mai zuciyarta don yna hangen maslaha a tare da aurenta, Allah yataimakeshi aikin dayake fafutukar nema Abuja yasamu a wannan satin, fatan sa idan fati ta amince yatafi da ita su zauna. chan yabar farida takarata a kano. Yabar fatima a gdansu zuciyarta ba wani kwantawa yayi da auran usman ba, ta kwanta tana tunanin yaya za tayi knan. washegari da yamma barrister nuraddin kuma yazo da tasa bukatar datafi na usman zafi, lamarin dayasa taji kamar tayi ta kuka sbda damuwa. Yace "fatima ina fatan sakona ya zo gareki, Allah ya jarrabi zuciata da tsananin soyayyarki da bukata mai zafi a kan auranki ina fatan zan samu hadin kanki. Kwarjinin barrister yahanata hada ido dashi hasalima batasan abinda za tace masa. Tadai cije tadaure tace Allah ya tabbatar mana da alheri. Ya dan ji sanyi a ransa yayi murmushi yace "knan kin ami? ce da soyayyata fatima? Taji dam a zuciyarta ita dai ba za ta iya cewa a'a ba idah kuma tace eh ta yi karya. Bata sake cewa komi ba yawuce gaba tayi mai rakiya yace "fatima ban san abinda kika fi so ba ballantana in kawo miki ga wadannan kudin kisayi duk abinda ranki ke so. Tadubi sabbin kudin a razane tace "ina zan kai wannan kudin barrister, don Allah kabarsu ni ban bukatar komi. Yace"nima ban ce kina bukata ba na ba ki ne a matsayin kyauta kuma ba a mayar da hannun kyauta baya, na hadaki da girman Allah ba dan ni ba ki karba. Hannu biyu tsa tare da risinawa takarba tace "na gode Ubangiji Allah yasaka da alheri. Ya lumshe ido yace na ji dadin wannan addu'ar ta ki. Zai shiga motarsa knan malam yadawo daga anguwa, fatima tashige gda dasauri yayin da barrister yazube a gun yana gaida shi, da fara'a malam musa ya amsa tare da kara masa godiya akan namijin kokarin daya musu a kotu, yace ba komi sai dai ya zo ne yana son fatima kuma ya ji ta bakinta ta amince taimakon dayake son a masa shi ne a bashi ita dawuri don tfya ce a gabansa. Malam yace "ba komi yabashi kwana biyu zai neme shi. Bayan tfyar barristr malam yashiga gda da kudin daya basu masu yawa ga wanda fatima tashigo dasu, inna tace "wallahi malam nikam na kagu a aurar da fatima a huta da wadannan fitinannun. Wannan zuwan da ake wannan yazo da katuwar mota, gove ma wani yazo an dau ido an sanya mana a unguwa, ni dai tafidda wanda tafi so tsakanin lauya da usman a daura auran a kaita kowa ya huta. Malam musa yace "nima abinda nake bukata knan a yau din nan za ta gaya min wanda takeso.. Fatima na kuka tace "don Allah baba kuyi hakuri zuwa da safe zanyi istihara duk wanda Allah ya zaban min shi ne zabina nikam ba ni da zabi. Duk inda aka ce Allah angama magana gaba daya takashe musu jiki dole suka kyaleta. A DAREN FARKO 41 A wannan daren fatima *wana tayi tana kai kukanta ga Allh tana rokon yazaba mata mijin da zai fi alheri a tare da ita, da mutum biyun nan takwana a zuciyarta amma da usman ta tashi ba brriater b. Shi taji ya fi kwanciya mata a rai duk da cewa shi yana da mata amma hakan taji shi taji tafiao, don haka kai tsaye ta sanar da babanta cewa yab barrister hakuri ta tsaglyar da Usman a matsayin mijinta,suka sanya mata albarka tare da fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alheri a tare dasu. Duk yan gdansu usman fatansu ftima ta ami? ce ta auri usman sbda ba karamar damuwa bace dashi a gdansa, ba kamar jidda wadda duk tafi kowa tsanar farida ko gaisuwa ba ta hadasu har faridan ta daina zuwa komi na danginsu itama ba mai zuwa inda take dama ba haihuwa ba ta mike kafa ne tana abinda taga dama. Lokacin daya samu tabbas daga mahaifin fatima cewa an bashi ita yaturo manyanaa, hannu yadaga yana wa Allah godiya, nan da nan aka kai kudin aure aka sa ranar aure nan da sati hudu daurin aure da biki gaba daya. Ya shiryawa fatima gda da lefe mai ban mamaki, har aka kusan biki farida bata sani ba domin yanzu yawonta ya kara kaimi tunda juma'a kawai usman ke zuwa kano yakoma abuja ran lahadi, sai da yarage saura kwana uku kachal daurin aure wata kawarta nafisa tazo gdan da yamma tace da ita. 'Farida anya kuwa kin san me ke faruwa dake naga kiba ma kikeyi ba kisan tashin hankalin daya tunkaro ki ba ko? Farida tayi mata wani irin kallo na rashin fahimta tace "me kike nufi. Nafisa tabude jaka tafidda katin daurin auren usman da fatima ta dora mata a cinya ya ta ce. "Karanta anan za ki fahimci me nake nufi. Farida ta tashi zaune hannu na rawa ta dauki kati ganin sunan mijinta yasa ta gwalalo idanu tace "nafisa a ina kika samu wannan katin? Tace "a gari mana ana nan ana ta rabawa jama'a na gayyata ni nasan tunda baki mana zancan ba jiya a gdan hajiya ladidi na san baki sani ba. Gumi yadinga ketowa farida ta kasa motsi sai numfashi take fitarwa da kyar dga bisani tatashi tace "nsfisa bar masa gdansa zanyi. Nafisa tace "wannan shi ne aikin banza harara a duhu, kina zaton yanzu kina gaban usman ne, idan ma kin tafi cewa zaiyi ya huta, tashi zakiyi yanzu muje gdansu amaryar mu ci mutumcin su muyi musu kaca kaca mu firgitasu ta ydda ba xa tayi sha'awar shigo miki gida ba, shi kuwa bakin munafikin idan yadawo ki nuna ki nuna mai hauka ki ganar dashi kuransa ta yadda zai shiga taitayin sa dole a fasa auran. Farida tazauna daram a kan wannan shawarar don jin zuciyarta take kamar za ta fashe. **** A ckin motar da usman ya siyawa farida suka fito tare da nafisa, farida ce ke tukawa fuskarta a tamke kamar za ta fashe tana ci gaba da daukar shawarar nafisa har suka isa kofar gdansu fatima kasancewar nafisan ta binciko komai. Cike da isa suka shiga, sukayi sa'a fatima ce kadai a tsakar gda tana wanke wanke. Mamaki ya kamata ganin mutane sun shigo musu gda ba sallama. Farida ta nunata da yatsa tace "ke ce fatima? Tace "eh ni ce lfya. Kawai fatin bata ankara ba taji farida ta cafko mata wuyar riga da karfi ta jijjiga ta tace "ni ce farida matar usman idan ma baki sanni ba yau ki sanni ganina ya fi ji na. Inna tafito dagudu daga bandaki tana salati tace "ke yar nan lfya za ki zo har gda kiyi mana tijara? Farida tasaki fatima tanuna inna da yatsa tace "ke yi min ahiru munafuka idan kina neman kai da wannan figigiyar 'yar taki ne ki kawota gdana kusha mamaki kwadayayyu kawai. Fatima tayi tsalle itama za tadamki farida, inna tariketa tace "kyaleta fatima duniya ce suk abinda kayi za ayi maka, kishiya dai duk bala'in ta za amata gda dai sai kin shiga takashe ki jahilar banza da wofi. Nafisa tace "ai ba cewa mukayi karta shigo ba, mun fi so ma tashigo mu nuna mununa muku su waye mu shi yasa yanzu muka fara zuwa har gda mu sanar daku. Farida tace "ga ku ga gdan usman nan daidai kushigo kugani idan idan kuna tsammanin barazana muke muku. Suka fice a fusace suka shiga mota, farida ta fizga da karfi suka fita daga layin suna kyakyata dariya. Karfe ukun yamma uaman yashigo gdan a gajiye yake sosai sbda yau shi yatuko kansa, tun daga hanya yake tunanin yadda zai fuskanci farida da maganar auransa, duk abinda ake ciki, ya sha alwashin yau zai sanar da farida, tun da aka fara batun auran tunanin dayake knan bai san tashin hankali gashi ita kuma anan takware. A falo ya sameta baiyi mamakin kin amsa mai sallamar datayi ba, dan haka shima bai kalleta ba yawuce da jakarsa zuwa dakinsa yashiga wanka. Farida tashigo a zafafe zu-iyarta kamar wuta don tsabar bala'i hatta idanuwanta sunyi jawur, idanuwanta suka fara dira kan wayarsa ta dauka hoton fatima ne yafara yi mata maraba ta sha ado ta yi kysu abinta har ba a magana. Wato ma har akan screen usman yake dora hoton fatima, batayi tunanin komi ba tadaga wayar ta dokata akan tayal ta tarwatse gaba daya, daidai lokacin usman yafito wanka hankalinsa yatashi dayaga barnar da farida tai masa, ya zubawa wayarsa ido mai tsaadar gaske yarasa abinda zai ce mata sai ya tsuguna zai kwashe sim din sa, ta daddage ta hankada shi tace "wa to ma ka maidani mahaukaciya ba ka a lokacin kulani ko? Ya tattara ta ya watsar gefe guda yace "Ba ki da hankali wa zai saurari marar hankali, abinda zan gaya miki ki gaggawar shiga hankalinki tun kafin ki jawa kanki abinda za ki zo kina nadama. Cikin daga murya tace "awai nadamar data wuce na aurankada nayi, ka cuceni ka ci amanata ban taba zaton kana ckin munafukan maza ba sai yau... Saukar mari mai karfi tajia. kuncinta wnda ya gigi ta tafita dagudu tadauko wuka, ,ganin haka yasa ya muedeta zai amse wukar, taja wukar da karfi tazuge mai hannu, jini yafara zuba duk da haka sai da ya karve yace "ba ki da hankali farida, ba ki da hankali. **** Tafiyar su farida da nafisa gdansu fatima akayi jugum ana tunanin wannan bakon bala'i ,fatima kuka take tana fadin "inna ba zan iya da wannan masifaffiyar matar ba na fasa auran usman don Allah ki kirashi a waya yanzu ki gaya masa na fasa auran sa yazo ya amshi komi na sa yazauna da matarsa, kina ji har cewa take sai ta zamo ajalina. Inna tace "ke ba komi irin barazana ce yau kika fara jin inda akai irin wadannan abubuwan, to ki dogara ga Allah matar usman ba kowa bace akan wasu matan don duk abinda kayi wani ya ninka naka kuma anga karshensa, haka duniya tagada, duk wannan abinda tayi ta yi ne don a tsorata ace an fasa idan an fasa din taci galaba daga nan ta samu damar takawa yadda take so, ki kwantar da hankalinki addu'ar da muku da wadda kikeyi insha Allah za tabaki kariya ba abinda zai sameki sai alheri, ba na son ki gayawa kowa ma. ***** Jikin fatima yayi sanyi sosai har dare ba ta da kuzari, lokacin da usman yazo ma haka tafito masa fuskarta ba walwala sai yaji duk abin duniya ya yi masa zafi. Yace "fatima meke faruwa ne akwai damuwa a tare dake don Allah ki gaya min,. Tadago tayi mai wani irin kallo tace "dama haka matr ka take? Gabansa yafadi yace "me yafaru? Ta labarta masa duk tijarar da farida da kawarta sukayi musu, ransa yabaci yace "na ji dadi datazo har gda ta nuna muku mugun halinta, ai da farko na fara gaya mikikikace ba kya son ji, don Allah kiyi hakuri zan dauki mataki a kanta, barazaana ce kawai don ta tsorataki babu abunda ta isa tayi miki ke ba a garin ma za ki zauna ba a ina za taganki ballantana tayi miki wani abu. Ganin fatima ta ki sakin ranta hankalinsa ya dada tashi, sai kawai gani tayi ya durkusa a gurin yana bta hakuri, tace "haaba haba usman ba girmanka bane. Yaki mikewa tsaye yace ba zai tashi ba sai ta ce ta hakura, dasauri tace "na hakura na hakura. KARSHE karfe sha daya aka tabbatar musu da cewa an daura auran usman da fatima, farida tayi kasa tana birgima tare da fadin "ahikenan na shiga uku na gama yawo. Isha ta daga ta tace tashi baki shiga uku ba, fatima abin da za ayi shi ne idan usman yadawo gdan nan kinuna masa kuranki da nadamarki, ckin ruwan sanyi sai mu gasata mu korera da kissa. Gaba daya sukayi na'am da wannn shawara. Karfe goma sha biyun dare usman ya iso gdan, har zai wuce dakinsa sai dai yafasa ya murda kofar dakin farida,. Ga mamakinsa sai yaga ta saki fuskarta ta amsa mai sallama tare da mai sannu daxuwa. Usman ya saki baki galala yana kallonta cike da mamaki da farin cki a zuciyarsa. Da gari ya waye ne take tmbayarsa ina za akai amaryar bataga anyi shirin komi a gdan ba. Yace "ai abuja za mutafi da ita anjima tunda kin ga gdan nan ya yi muku kadan. tace ai ma hakan yayi daidai kaima za kafi jin dadin zaman abujan amma dai zanyi rakiya ko tunda dama ban taba zuwa ba. Yayi dan jim bai so hakan ba amma ya daure yace "shknan sai ki shirya

Chapter 18 of 19