Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta samu tarbiyya me kyau. Mama tace "uhm sadiya mutum ba a shaidarsa mace tana da wani irin hali yayin da da namiji yadaga hankali a kanta yana sonta dayawa shike nan tasamu damar yi mai yadda taga dama maimakon tayi amfani da wannan damar gun rikeshi da kyau sai tadinga murza kambunta yadda taso. Sadiya tace "mama ki yarda da Allah ki yarda shi ne me komi, addu'ar da kikewa khalifa ke da abbansa ba zai taba faduwa a kasa ba, insha Allahu bbu abunda zai faru da aurensu sai alheri, kidauki fatima kamar "yar dakika haifa sai Allah yakalli kyakyawan niyyarki yatsare khalifa daga dukkan wanda zai masa abin da zai gusar da hankalinsa, idan kaji tsrom Allah ka kyautatawa 'ya'yan wasu Alkah zai dubi na ka zuri'ar ko ba ka da rai. mama tace "Hakane anty sadiya ina kaunar fatima dayawa nima yanayin soyayyar da khalifa ke nuna mata ne yayi yawa ni na rasa me yakeji a zuciyarsa game Da ita, in dai akan fatima ne to fa zuciyarsa ba ta da sukuni, zai iya hakuri akn komi banda ita. Duk su mama na wannan tattaunawar ne dai dai lokacin da fatima tagama wanka tafito daga toilet daga ita sai dauri kirji sai ko dan tawul din data yafa a kafadarta bata san khalifa na dakin ba, ganin shi kawai tayi tsaye jikin madubi ya kuma zuba mata wadannan fitinannun idon na sa masu tsananin kyau da laushi, tatsaya sororo tana kallonsa kamshin dayaji yana tashi a jikinta yaji kamar ana fizgarsa zuwa jiki? ta, lamarin dayayi sanadiyar daya kasa rike kansa sai da ya isa gabanta yaja hannayenta biyu yahadata gam da jikinsa yasa harshensa yana lasar lebbenta, gaba daya jikin su yadauki rawa ita tsoro takeyi kada wani yashigo ya iskesu a haka yayin da shikuma jikinsa na rawa ne sbda wata fitinanniyar shawa data jefa shi a cikin yanayin da bai taba shiga ba a rayuwarsa, yakama kunnuwanta yana gaya mata kalaman dashi kansa bai san yana fada ba, har sai da fati taji tsigar jikinta na tashi tasa hannu tarufe mai baki. Kwatsam ummi taturo kofar dakin tashigo, khalifa yasaki fati yajuyo yayi wa ummin wani irin kallo yafice, ta ajiye abin cin data zubo musu kamar ba abinda tagani tashiga jan fatin da hira nan kuwa zuciyarta kamar za ta tarwatse sbda wani azababben kishi da taji ya tokare mata kirji, sama sama fatima ke iya magana, hira ta ki yiwuwa domin hankalin fatiman ba ya tare da ummin, Dr. Khalifa angonta ne kawai a gabanta shi take muradin kasancewa tarea dashi. ***** Tunda sassafe wasu yayyan innarsu fatima suka iso gdan duk da ba yau ne za a kai amaryar ba sai sati ya zagayo amma za su dafa abinci sbda 'yan'uwa maza daza su zo domin auran. Yaya kubura tace "Ina amaryar ne? Inna tace "Tana gdansu angon amma yanzu za tazo. Gaba daya suka rike baki sukece "wani irin tsarin banza da wofi ne haka? Yaya kubura ce tafi sauran fusata tace "Ni na taba jin irin wannan? yaya za ayi ace amarya na gdansu ango? Ke ba kya tsoron ace kwadayi ne yasa ta tattare a gdansu angon? Yaya rabi tace "ke kike wannan xancan kubra tun yaushe ake cewa kwadayi ne yasa ciki sati daya aka fasa bawa musbahu aure aka bawa khalifa don kawai babanaa yanada farcan susa, to ballantana yanzu ace tan gdan wai acan ma takwana, in barda zuvarwa kai daraja meye wannan? Inna tace "Ai ba wani abu yasa taje ba sbda kunshi ne da gyaran gashi. Yaya kubra tace "duk wani gyara ita batasan inda za taje ayi mata ba sai ta tafi yawon tallan kanta a gdan surukan, To Allah dai ya sawwake amma gskiya kidinga lura kuna jan mutuncin ku irin wannan abu ne ke sawa a dinga wa mutum gori daganan mutumci yazuve. " Inna dai tana jinsu bata sake cewa komi ba, itama kanta ba a son ranta fati takwana gdan su Khalifa ba mutumcin mama ne yasa ba ta iya musu da ita, sun nuna suna son fati daywa, hakanan fatima tasauya ra'ayin ta gaba daya akan Khalifa. Wuraren karfe takwas da rabi su fati suka shigo tare da ummi, tun kafin matar da aka dauka musamman dan tayi mata kwalliya tazo fati har ta fara daukar ido abin gwanin ban sha'awa, kowa yakalleta sai ya kara, fuskarta dai ce ta dan kumbura sakamakon rashin barcin da bata samu ta yi sosai ba a daren jiya, tsabar tunanin khalifa da kaunarsa da asuba ne bayan sun idar da salla tazauna jugum tayi tagumi. Ummi tajanye hannun na ta tace "haba matar yayana tunanin yayan ke damunki? Tayi mata wani irin kallo tadauke kai bata ce komi ba, ummi tayi murmushi tace "Ba kiyi laifi ba dan kin kasa sukuni akan dr. khalifa, ni na san tabaki yake yana dandana miki zuma a baki, shiyasa hnklinki ke tashi dayawa, fatima ba ki da laifi don kin damu da yaya Khalifa, bai dandana wa mace irin wannan zumar ba ta rikice akansa ballantana ke da yake nuna miki so irin haka har yana hada jikinsa da naki'. ***** Karfe goma sha dayan safiyar lahadi daruruwar alummar musulmi suka shaidi daurin auran Dr. Abubakar Saddiki Muhammad da Fatima Musa, daurin auran daya samu halartar manya manyan mutane tun daga kan manyan yan kasuwa da sunan su yayi fice a fadin kasar nan zuwa manyan yan siyasa da kusoshin gwamnati da jiga jigan malaman da ake ji dasu a jihar mu ta kano, hatta bangaran sarauta sun halarci daurin auran ballantana likitoci da abin yazama nasu maganin a kwabe su, maroka suka rinka yayata sunan ango da amarya da iyayansu yayin da gdajan rediyoyi ke ta bayyana yadda abubuwan ke gudana, sai shiga ake ana fita da nau'ikan abubuwan ci da na sha na alfarma daga gidansu dr. khalifa da gdansu inna. Angon ya sha ado ya yi kyau daya wuce misali, abin sai wanda yagani shadda ce mai tsadar gaske fara kal riga da wando da babbar riga sai akayi aikin babbar riga da blue din zare, hula kansa ma ya kasance fara da blue takalminsa blue, a ckin gda amarya fatima irin shigar ango aka mata fari da blue, ba a iya tantance wa yafi kyau tsakanin angon da amaryar kowanne ba baya bane ko ina masu hoto ne da bidiyo ke daukar ango da abokanansa sannan suka shigo gda tare don gaida iyayan amarya.. Gdansu fatima ma cike yake da mata anata rangada guda d sanya albarka, fatima ta zamo matar dr. khalifa rana ba ta karya sai dai uwar diya taji kunya, farar tukunya mai fidda farin tuwo, kirari iri iri maroka suke tayi musamman a gdansu khalifa inda anan ne ake facaka da kudi kamar ba nemansu ake ba. Abba yadinga kyautar muhimman abubuwa yana fadin "ai wannan rana ce ta farin ciki garesu ranar auran dansu daya. To fa. Ina su hajiya hauwa da hajiya saude kannan abba iyayan ummi? wadanda duk wani burinsu a wannan rana bai wuce ace da diyarsu ummi aka daura auran ba, amma hakan bai yiwu ba, khalifa da iyayansa basu damu da damuwar kowa ba sai ta su. Da farko basuyi niyyar zuwa gdan ba a yau daga bisani saude tace gara suje karshe a zo anayi damu ai idan baka iya kama barawo ba kai sai ya kamaka. Ba za ka iya shaida bacin ran dake tare dasu ba amma zuciyarsu fal bakin cki da takaici, da isowarsu a safiyar abba yaraba musu sabbin kudi rafa rafa yace suyi liki, duk da haka ransu ba dadi tunanin su shi ne da da ummi aka daura auran nan ai sun more irin wannan dukiya haka. Bayan gama daurin auren suka kebe a ckin wani daki, saude tadubi hauwa tace "ke wadannan mutanen ba na wasa bane sun fi mu shiri. Hauwa tace "Yo ba kiji abin da malam yace jiya ba? yace ai uban fatima ne yahada wani gagarumin asiri ya dabaibaye zuciyar khalifa yadda b ya son kowacce mce si yarsa fatima shiyasa muke tayin aiki aikin ya ki kama khalifa, yace. a wani lokacin yana so ya so ummi sai asirin yayi tasiri a zuciyarsa yakasa katabus yaji kamar ba ya da iko a kansa sai son fatima. Hajiya saude tace "Haba ko da naji ni nasan arina wai an saci zanin mahaukaciya, wannan aikin da malam keyi ba zai tashi a banza ba da mugun abinda da sukayi, duk mu mun manta uban fati malami ne sai da yayiwa khalifa asiri duk iyayan ya gama dasu anma ba komi jiya da dare na je na kaiwa malam kudin bajimin sa dayace a kawo za a zubar da jini yace musa ido za muyi kallo dakansu sai sun gane kurensu kowa yaci tuwo damu miya yasha. A DAREN FARKO 33 Mama tana iya kokarin ta akan bawa su hajiya hauwa 'yanci a gdan dan dai kada ayi korafin amma bata tsira ba duk inda tayi binta suke da harara suna kwafa. Karfe hudun yamma angwaye da wasu daga ckin mutane aka fara daukan mutane zuwa inda akayi gagarumar walima maza zalla, ana kiran slar magriba aka tashi kowa yana farin ciki da sanya alheri. Karfe tara da rabi na daren dr. khalifa ya fito daga wanka a dakinsa abokansa biyun nan Dr. Bashir da Dr. Hafiz su biyu suka rage bayan kowa ya watse,yafada bisa gado yana mai da numfashi da kyar. Dr. Bashir yadubeahi yana dariya yace "Ango na amarya, amaryar ka ta yi kyau yau abin har ba a magana sai dai kwalelen ango, ko ganinta yanzu ba damar yi. Dr.khalifa yace "Ba komi ai komi lokaci gareshi rana ita yau iyanzu babu wanda zai mini shamaki tsakanina da ita zamu kwana a daki daya sai yadda naga dama da ita. Kafiz yace "Oho dai ba haka aka so ba wai kanin miji ya fi miji kyau, ko in je in dauko maka ita? Dr. khalifa yace 'Rufa mini asiri dazun nan mama takirani dakinta tana gaya mini idan taji na je gdansu fatima sai ta batan rai don Allah kaji wani danyan hukunci mutum da matarsa. Dr. Baahir yace "Ai ta yi ma haka ne don ta san halinka, a gdan iyayan na ta ma sai kabita ka matseta kai ba kunyar mutane kake ji ba. Yace "kai ba a irin gdansu fati ake wannan ba ka san akwai inda ake barin halak don kunya. Dr. Hafiz yace "To kai ka san kunya ne Abbakar? ko dayake yanzu ka sauya kamar ba kai ba, son fatima ya sauya ka dayawa kamar bakaji tashan 'yN mata ba, tunda kadaura idonka akan fatima kadaina tunanin 'yammatan ka, tun wasunsu na damuwa suna damun mu har sun hakura. Yace "Kai ni ai babu sauran wata diya mace a zuciyata tunda na mallaki gimbiyar mata fatima ta rufe kofa gaba daya. **** Da gari ya waye mama tazo da kanta taroki inna da malam akan a bata fatima akwai shirin da za ayi mata, a zuciyoyinsu basu ji dadin haka ba har ita kanta fatiman sbda ta san dr. khalifa matsamata zai yi a gidan amma mama tafi karfin komi garesu, iyayan khalifa suna da kimar da za su iya yi musu komi surutun mutane ne yake damun su fassarar nan ta kwadayi ita take damin inna komi akayi idanuwan mutane na kai kuma sai sun yi magana. Bayan tafiyar mama abinda inna da malam ke tattaunawa knan, Fatima na dakinsu na yara a kwance tana fama da barcin gajiya ita kanta ta san a yanzu ta canja, ta baza kunnuwa tana addu'ar Allah yasa kada malam ya amince da komawarta sai dai kash sai ji tayi malam din na cewa ta tafin kawai. Amma dai kija mata kunne tasan abinda takeyi, kuma tasan kanta. Ya sa kai yafita. Inna ta kwala mata kira ta fito ckin rashin kuzari kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki tazauna daf da ita, tace "To malam dai ya amince da zan ki a gdansu khalifa, jan kunne da zanyi miki shi ne ke diya macece ki san darajar kanki idan har kina son ki samawa kanki kima a gun khalifa na san yadda kike biyewa al'amarin khalifa sbda son da kike masa, to kisani namiji sai ana taka tsan tsan da al'amuransa dole mace Tayiwa mijinta biyayya domin aljannarta. na karkashin kafarsa amma kada ki zake karki ja wa kanki abin fadi. Jin tayi shiru yasa fatima a sanyaye tace "Inna don Allah kibarni anan nima ba na son zama a gdan nasu. Tace "to yaya za muyi kin san ko a yanzu khalifa ya fimu iko dake in dai aure ke sa ayi iko da mace tunda an daura kasancewar ba a kaiki gdansa ba ba zai hana dokar Allah aiki a kanki ba a cikin hakkokinsa da Allah ya jarabta akanki, kai mace daki ba shi ne sharafin biyayyar aure ba shaidu da sadaki sune aure in dai an yi su ya zama dole mace tayiwa mijinta biyayya ko a ina take kuwa kinga in dai haka ne dole mu amince da zuwanki gdansu khalifa. Fatima taji zuciyarta ta karaya bata ankara ba kawai sai jin hawaye na xubo mata, ,ita kanta bata san kukan metake ba batasan ma'anar kukan na ta ba. Inna tayi murmushi tace "To meye na kuka, khalifa zabinki ne fatima kin manta yadda kika dinga kuka kina rokon a bashi ke? Duk abinda khalifa yazo dashi dole kiyi biyayya domin aure kikayi na soyyaya na zabin ranki da zuciyarki,ban taba zaton xan ga hawayenki ba bayan kin zamo matar khalifa fatima, ki share hawayenki ki mike kafafuwanki kiyi walwala kin auri wanda kike so. Fatima tayi jugum ta san magana ce irin ta gugaz zana inna take gaya mata akan abinda tayi akan musbahu ,taci gaba da kuka sosai ,taci gaba da kuka sosai inna ta tashi tashiga hidimomin gabanta tana fadin "Ai sai kiyi. Fatima ta koma ckin daki ta kwanta bata san abi? da ya daga mata hankali ba hawayanta suka ki tsayawa, ummi ce ta yaya lavulan dakin da sallama tayi turus tan kallonta tace "Kukan amarci kike tun yanzu fati ko wani abu aka miki? Babu Babu amsar da za ta iya ba ummi don ita kanta bata san kukan da take ba. Ummi tace "to koma dai meye kisaki kukan tashi kiyi hakuri kiyi wanka ki shirya tafiya za muyi ango yana jiranki za mu fara fita hada kayan sayan baki kafin na lefe shi khalifan ma ya so ace Dubai za aje a hado har kayan dakinki mama ta ce babu inda zai tafi dake ba tare da an kaiki gdanki ba. Fatima dai ba ta son magana ta tashi tayi wankan, ummi tagama shirya mata kayan ta, suka yi sallama da inna suka nufi gdan mama, dogon hijabi da nikab tasa suna shiga harabar gdan fati tayi sauri tashige ciki don kar su hadu da khalifa ta zauna a falo a kunyace tagaishe da abba da mama ko kanta ba ta iya dagawa. Sai mama ke mata dariya tace "in har wannan kunyar za ki sawa ranki za kiyi ta wahalar da kanki ke kawai ni dai ba suruka na dauke ki ba a matsayin diyata kike har yanzu, tashi ki wuce daki idan kin huta akwai girke girke na abokan mijinki. Da zarar an kra dr. khalifa mijinta sai taji wani iri a jikinta, tana jinjina alamarin kamar a mafarki ,duk yadda ta so shi a ranta take tsananin son tadinga ganinsa a ko yaushe sbda burgetan da yake yau tsoron ganinsa take, fatanta kada yashiga gdan suhadu, tayi sa'a kuwa har magriba tayi bai shiga ba tuni suka gama hada abinci mai rai da lfya suka shirya kan tebur tashige daki tayi wanka tasa doguwar rigar shadda koriya takara gyara gashinta tayi sallar isha'i tana shirin hawa gado takwanta aka turo kofar cikin tattausar muryar nan tasa yayi mata sallama. Khalifa ne.. A figice tadago idonta taxuba masa yana ckin wata lafiyayyar shadda brown me haske an mata aiki da dark brown din zare irin dinkin tazarcen nan, kamshin turaransa yadinga ratsa mata zuciya, ya fidda gilashinsa ya baibayeta da fitinannun idonsa ba walwala sosai a tare dashi yace "Fatima. Duk kokarin da tayi na tsayuwa ta kasa svda rawar da kafafunta suka shiga yi, ta durkusa a gun tadafa gado. Ya kara kirn sunanta a karo na biyu a nan ne ta amsa, yace "Tun karfe nawa kikazo gdan nan? Muryarta na rawa tace "sha biyu. Yace "Amma ba ki san hanyar dakina ba ballantana ki zo ki gaisheni. Gabanta yafadi tadago ido a tsorace tana dubanshi abinda ta gani a cikin kwayar idonsa yasa tayi saurin maida kanta ksa, yace "kin yi daidai knan? A hankali tace "kayi hakuri. Yayi saurin katseta yace "Ba zan yi hakurin ba. Tabude baki cike da mamaki tana kallonsa abin ya ba shi dariya ya iso gabanta ya kamo hannunta yamikar da ita tsaye, kai tsaye yahadata da jikinsa ya matseta yadda ba za ta iya motsi ba, ya cusa bakinsa ckin nata yadinga tsotson lebbanta ckin wani irin salo na gwanancewa a harkar sarrafa mace har jikinsa yafara rawa yafara manta a ina yake. Kwatsam yaji mama na kwalawa fatin kira daga falo dasauri yasake ta yafito falon, mama tayi mai wani irin kallo fuskarta a tsuke tace "Daman kana ciki? Yayai dan murmushi yana sosa keya yace "Yanzu na shiga. Ta harare shi tace "To me ka shiga yi? Yace "A'a gani nai dai ban ga fatin a falo ba shi ne na bita ciki. Mama taja tsaki tace "ka ji dashi dai ina fatiman. Yace "Kayanta take swa, ya wuce tebur yana bude buden kayan abincin yace "mama asa su fatima su kawo mana dakina muna da yawa. Tace "kai kafita daga idona khalifa babu abunda zai kawo fatima dakinka kuma idan baka saurara dashiga dakinsu ba zanyi maganin ka. a zuciyarsa yace "a baya ma na taba fatima ballantana yanzu, ai zancan ace kada in taba ta ma bai taso ba, mutum da halak malak. Unmi ce ta taya shi kai abinci tana zolayarsa yana dariya, ummi tana mamakin yadda khalifa yazamo mai mata walwala akan fatima ya dawo kamar ba shi ba, mutumin da murmushi ma a baya tsada yake masa, shi ne yanzu ake hira dashi yana dariya, in dai kana son ganin walwalar khalifa yi masa zancan fatima, wannan lamari yana taima zuciyar ummi tare da gigita ta, abinda ta tabbatarwa ranta shi ne na raba zuciyar Dr. khalifa da son fatima sai dai mutuwa idan ransa yabar jikinsa amma ba dai wani boka ko malam ba. A DAREN FARKO 34 Abokansa suka tsare su dtambayar ina amarya tunda an ce tana gdan dole suna son ganinta, khalifa ya marairaice fuska yace "to ya zanyi !? Mama ta yi ruwa ta yi tsaki ta ce fatima ba za tazo dakin nan ba, ni ban taba ganin irin wannan tsarin ba mutum da matarsa a dauki ido a dora mai ko kallon fatima nayi mama sai ta hau fada na rasa dalili bata san jin zuciyata nake kamar za tafashe ba idan tana hanani ganin mata ta. " Wani a cikinsu mai suna Nura yace "Ai mama tayi min daidai sanin halinka ne yasa tayi ma haka,idan aka kyaleka za ka iya kwana da fatima a dakin nan da safe kuma kayi mirsisi kana kallon idon mutane. Khalifa yakara fusata yace "Kai da Allah kar ka dada batan rai haramun ne dan na kwana da matata. Dr. Bashir yabushe da dariya yace "Wannan ihu ne dai bayan hari in ka isa katafi dakin mama kayi mata wadannan fadace fadacen karshe tace sai bayan wata uku za a kaima amaryar in ga kuma yadda za kayi. Khalifa yayi dariya yace "Tabdijam ai kuwa da na basu mamaki nima in ga yadda za ayi dani. Nura yace "Uhum ka bisu dai a sannu idan kai baka ba su mamaki ba su subaka mamaki. ***** Mama tayi tsayuwar daka gun gyara amarya da abubuwan da za sukawo mata ni'ima a jikinta, ita dai burinta hankalin danta yakwanta,. Fatima ta cika ta batse ta kara wani irin kyau kyaun ma mai ban sha'awa, tayi fresh babu abinda ke damunta. Mama ta hanata fita ko ina don kar ta shiga dakin khalifa sai dai shi in ya shigo su gaisa iya fali. Ya yi fushin ya yi mitar har ya gaji ya zuba ido shi kadai yasan damuwar da yake fama ita a zuciyarsa, a ranar da fatima tayi kwana biyu a gdan ana ya jibi za a kaita gdan Dr. Khalifa aka kai kayan lefenta gdansu, lefen da aka dinga surutun karya tayi yawa, wannan ai almubazzaranci ne da dukiya kamar ba masu neman taimako da za a kashe dukiya irin wannan a lefe,? Abinda 'yan'uwan abba sukayi ta fada knan, daga bisani wannan yazamo ba abin surutu ba lokacin da aka kaisu ganin gdan dr. khalifa da fatima za su zauna wanda yake court road, da irin kayan alatun da aka dankara a gdan abin sai ya wuce ayi magana da baki sai gani da ido, duk wani abinda za a kawata gda dashi a kalla asan ya yi kyau sai da akasa a cikin wannan gda, komi ya kammala amarya kawai ake jira. Washegari ranar asabar wanda yakasance saura kwana daya akai fatima gdanta tatashi da ciwon kai abisa dole mama tace khalifa yashiga dakinsu ya dubata, shi bai ma san ba ta da lfya ba svda hushi yayi yadaina shiga harkar mama da ita kanta fatin, idan ma yashigo falon ta gayar dashi fuska a tsuke yake amsawa sbda ya gaji da jan ran da ake masa kawai don an ga ya damu. Lokacin daya shiga falon suka gaisa da mama yawuce kan tebur zai ci abinci ta dubeshi tace "Yau baka tambayi matar ta ka ba. Ya dan tabe baki kamar bai damu ba yace "Oh tana ina ne ? Tace "Tna daki ba ta da lfya. Yaji wani irin abu ya dakar masa zuciya duk da haka yashare bai bari mama ta fahi ; ci halin da zuciyarsa tashiga ba, yayi zamansa yafara tsiyaya tea a kofi yana fadin "Me ya sameta ? Ta amsa "Tashi tayi da ciwon kai da amai idan kagama kashiga kaduba ta. To kawai yace yaci gaba da cin abincinsa, da ya gama din ma maimakon yashiga dakin au fatima sai yadauki hanyar fita. Mama tace "Ba za kaduba fatiman bane ? Yace "Af har na manta. Yamurda kofar dakin tana kwance bisa gado nannade da bargo, idanuwanta a rufe, yazauna kusa da ita yayaye bargon data rufe, ya taba wuyanta zafi sosai, yace "Subhanallahi. Nan da nan yaji tsigar jikinsa ta kama tashi, yakira dr. hafiz a waya ya gaya masa irin magungunan dazai aiko masa dasu, yafita dan yadan hada mata abinda za taci sbda allurar da zai mata. Mama tace "za su fita da anty sadiya yanzu za su amso dinkunan fatima tunda ba kowa a gdan yazauna yalura da ita. Zuciyarsa tayi mai fari kal 6au ya sami dama amma sai yadan kanne yaduba agogo yace "Da fita zanyi kuwa. Tace "Kadan jira mudawo bai dace a barta gda ita daya ba sai 'yan aiki alhali ba ta da lfya. Bayan fitar su mama yahada mata shayi ba madara yazuba mata dankali shi kadai yanufi dakin, yazauna gefen gadon yajawota jikinsa yana lallabata kamar kwai yarungumeta yana bata shayi tana dan sha a hankali tace ita dai ta koshi. Wata daga cikin ma'aikatan asibitinsu dr. hafiz takawo magungunan yabata tasha yayi mata allura guda daya tana zuba shagwabarta yadda taga dama, hankalin khalifa yakara tshi zuciyarsa ta tsimu komi na jikin fatima ya bayyana a gareshi, domin wasu riga da siket ne a jikinta marasa nauyi takara zama fara kal, ko idanunsa bai iya daukewa a kanta ba, itama tana son tadinga kallonsa duk da tanajin nauyinsa, ganin ya fara shafa mata cinya da ciki yasa tadan janye jikinta ta matsa, yayi narai narai da idanuwan nan na sa yana mata wani irin kallo mai daga hankali. Yace "Haba fatima kin san matsayinki a guna bai dace ki biyewa mama kina wahalar dani ba, wai ace fatima tsakanina da ke sai gani da ido daga nesa,. Ni fa mijinki ne ina da hakki akanki ko kin manta ne ? Doguwar ajiyar zuciya tai tace "mama ce ba ta son in zo gunka nikuma ba zanyi abu ? da zai bata mata rai ba. Yace "ai dama ba cewa nayi ki bata mata rai ba, amma ya dace ace ko da daddare ne kina dan fakar idonta kizo dakina kitayani hira ki debe min kewa tunda kin san dole ina fama da damuwa a zuciyata ko ? tunda kika dawo gdan nan dazama kullum dare ba na iya barci sbda kewarki fatima, ina son ko kakane in dinga jin dumin jikinki, ko rungumarki nayi na miki kiss ai zan ji dadi a zuciyata ko ? Amma ke ba ruwanki sai ki biyewa mama ki shareni sai dai in shigo in ganki kyaunki na karuwa zuciyata tayi ta fama da kewarki ya kamata ki tausaya min Fatima. Ya kamo hannunta yakara janta jiki ? sa yarungumeta sosai yaci gaba da cewa "Wallahi fatima ina sonki son da ban taba zaton zan ma wata diya mace a duniya ba, sbda kafin ke ba zan iya tantance miki meye soyayya ba, nidai nasan ina mu'amula da mata amma ban taba damuwa dawata diya mace ba saida nafara ganinki nadin ga jin tamkar zan mutu idan ba na tare dake, duk wata natsuwa takan gushe mini idan ban ganki ba, shi yasa na rikice na gigice lokacin danaga katin daurin auranki da musbahu, Fatima idan ciwon sonki ya tsananta a zuciyata sai in dinga jin kamar ba zan yi doguwar rayuwa dake ba, fargaba takan kama mini zuciya in rasa yadda zanyi da raina, fatina dan Allah,. Yayi shiru yakasa cigaba da magana. Tausayin sa yakamata sosai taji ciwonta ya sauka gaba daya babu abinda ke gabanta sai khalifan tadinga jin wani so da shauki yana ratsa mata zuciya kamar yau ne tafara sanin khalifa, a wannan lokacin da kanta tasa hannayenta biyu tarungumi dr. khalifa kam kam a jikinta tana hawaye. Yasa harshensa yadinga lashe hawayen na ta yana fadin "fatima, fatima kukan me kikeyi. Ta tura bakinta cikin kunnuwansa tace," kukan farin ciki ne kada yadameka. Yadda tayi mai shima haka yayi mata yace "Farin ciki kala kala ne fatima don Allah fassara min yanayin farin cikin daya sa ki kuka. Tace "Babu wani farin ciki ga masoyi wanda yawuce mai sonsa ya soshi, hausawa kan ce son maso wani koshin wahala ne, idan mutum yana son wanda ba ya sonsa ya gamu da wahala idan kuwa mutum yana son wanda yake son sa yana ckin farin ciki da kwanciyar hankali, a yau ban san wanda yafini farin ciki ba shiyasa nake kuka. Khalifa yayi murmushi yace "Allah sarki ashe in dai hakane za kiyi ta kuka tunda ni yanzu nafara nuna miki so da tattali har zuwa ranar da Allah (SWT) zai karbi rayuwata. Fatima ina fatan Allah yasa in mutu in barki sbda nasan insha Allahu za kiyi tamin addu'ar neman gafarar Allah. Bayan haka ina jimantawa kaina halin da zan shiga idan na rigaki mutuwa, mutuwata sutura ce a gareni idan yakasance kin mutu fatima don Allah ki dinga yi

Chapter 15 of 19