Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lahira. Ni na san bbu namijin dazanso bayan kai, Anisa.... Iya abinda takardar takunsa knan, har gumi yaji yana keto masa sbda tsabar tausayin anisa, yadinga jin wani iri a ransa yana tunanin rayuwar dasukeyi wadda ba ta da wani amfani a garesu, idan suna gaban iyayansu sai su dinga nunawa su na kirki ne amma a bayan idon iyayan na su suna aikata abinda suka ga dama. Shin tsakanin iyaye da Allah wa ya fi dacewa aji tsoro, in har suna boyewa iyayansu halin dasuke cki ne don suna tsoronsu, Allah daya halicci mutum shi yafi dacewa a ji tsoro, kuma Allah yana kallon mutum a ko wani hali yake. Wannan nasiha da khalifa yaiwa kansa yasa yaji nan take komi ya fice mai daga rai ya tsani yan matan dayake tare dasu na holewa, yana bukatar yazamo natsatsen mutum wanda yake biyayya ga Allah da manzonsa, takaicin abubuwa da dama suka kamashi har yaji kyamar kansa da kansa yakeji, yamike jikinsa ba kwari yafito daga dakin yadawo dakinsa, ya isje shu bby har yanzu baccinta take cike da nishadi da kwanciyar hankali, yasa hannu yagirgizata dakarfi tabude ido tana fadin "bacci ke damuna,yace " ba na iya juriyar yunwa. Tace "ina yar aikin gdan nan? Yace "ba ta nan. Ba abinda shukra tatsana irin girki amma da yake khalifa ne haka tadaure tadafa ruwan tea da dankali da plantain, ba wani kwarewa tayi da girkin ba yunwa ce tasa kawai yaci. ***** A DAREN FARKO 17 Tun daga wannan lokaci rayuwar khalifa ta sauya gaba daya yadaina sauraror kowacce mace har da ita kanta shuu babyn, hatta fAisal ya watsar dashi sbda ya yi ya yi yaja hankalinsa don shima yadawo hanya tagari faisal ya yi masa wani irin kallo shekeke yace "kai kiwa meya sameka da za kace mudaina rayuwarmu, tajin dadi mu takura kanmu, ko mafarki kayi ka mutu an sa ka a wuta? Khalifa yace "ko kusa banyi wani mafarki ba na dai yi wa kaina fada ne dan na fuskanci gaskiya, na ga yakamata inja hankalinka kaima damu daina wannan rayuwar kafin ranar nadama tazo mana. ko wata amsar kirkifaisal bai ka ra bashi ba yamike yavarshi a gurin,hakan yasa khalifa ya janye jikinsa yakoma rayuwarsa shi kadai, yanemi masu dafa masa abinci da gyaran gida bai zuwa ko ina sai makaranta inya dawo yakan kulle kansa a dakinsa yayi ta nazarin abinda yake karantawa ko karatun alkur'ani mai girma wanda a baya ko bude shi ba ya yi sbda shagalta da rayuwa da ya ya mata dayayi, sai yake jin dadin rayuwarsa a haka hatta hotunan sa da nambobinsa ya goge, yayi ta karfafar zuciyarsa tare da neman gafarar Allah yana rokon Allah yataimake shi yaraba shi da wannan rayuwa. A haka a haka har Allah yataimake shi yakammala karatunsa yakawo shi inda ya fito da kyakyawan sakamako zuwa babban likitan mata a lkacin ya dada kasaita irin mazan nan ne da dole idan aka kallesu a kara sbda cikar zatinsu, kwarjini da ilimi, 'yammata sun yi sunyi suja ra'ayinsa kowacce tana fatan yasota amma ya ki bada kai, matar aurance har yanzu baiga wadda yagamsu yaji ta yi masa zai zauna da ita a matsayin matar aure ba, amma dai mace ta holewa ya yi alkawarin insha Allahu ya daina. Kafin ranar dawowarsa gida nigeria ya yi ta neman yadda za ayi yaga anisa ya rasata haka a kano bai san a ina zai ganta ba, yana yawan jin tausayin ta tare da yimata addu'a duk sanda yatuna ta. Tunda ya daura damarar tahowa gida damuwarsa itace yarinyar nan ummi ya san ta yi girma yanzu sosai ta kara wayo a baya ma ta iya budar baki tace tana son shi ballantana yanzu, bayan shi ba wani sakar mata fuska yakeyi ba ballantana ace shi kwata kwata ba ya da ra'ayin auran zumunci kuma ko yana dashi ma ummi bata cikin lissafinsa, cikin hikima yatambayi mamansa a waya ko an yiwa ummi aure, tace ai bata fidda da mijin ba ma ba ta sauraron kowa tun da tayi candy abban k7ma ya ce ya dace ta fidda mijin aure tunda mutane dayawa suna nunawa suna sonta in ya so taci gabada karatun a gdanta sai tace wai wanda takeso din ya yi doguwar tafiya idan yadawo za ta gabatar dashi. Wannan yafadarwa dr. khalifa gaba ya tabbatar yarinyar nan in baiyi da gaske ba zata zame masa matsala, har ranar dawowar tasa tunanin da yake fama dashi a xuciyarsa knan, yarinyar tashiga ran mamansa za a iya cewa sai ya aureta ko da yake bai da matsala da abbansa, maganar mamansa kuma da karfi a kansa baya son bata mata rai. ***** Karfe sha biyun rana fatima tagama shiryawa cikin wata blue din batik mai haske riga da zani ne amma kai kace siket ne sbda yadda kayan suka zauna a jikinta suka yi mata kyau abin har ba a magana, ita da kanta ta yi sha'awar kanta sbda kayan sun mata kyau, telan dayayi dinkin ya gwanance a fagen tsarawa mata dinki, ta jima tana gyara gashinta ya dau kyalli ta tsara daurin dankwalin sosai yadda yadace da adonta tazuba fashion da mayafin da suka dace da kayan, ummi ce ta bukaci taraka ta gdansu yau wato gdan iyayanta, fati bata fiye son xuwa gdansu ummi ba sbda jininsu bai haduwa da hajiyarsu ummin ba tare da ta san abinda tayiwa hajiyar ba, tana cin darajar diyarta ummi ne kawai sbda a halin yanzu ummi tanad\ matsayi lamba daya a zuciyar fatima ba ta da na biyu kowacce irin alfarma fatima za ta iya yi akan ummi. Innar tana zaune a kofar dakinta tace "inna sai mun dawo. Tace "adawo lafiya a gaida su. Tayi sallama a kofar dakin malam musbahu yadago yadubeta sai yayi saurin bude idonsa gaba daya yace "kai fatima wacce irin kwalliya ce wannan? kin ga yadda kikayi kyau kuwa? Ta lumshe kyawawan idanuwanta tana murmushi tace "ka manta na gaya maka za muje gdansu ummi. Yace "fatima gskiya in banda ummi na da matsayi mai girma a gareni ba zan iya barinki fita cikin wannan kwalliyar ba ban taba ganin ranar dakikayi kyau a ido irin wannan rana ba, fatima ina fatan Allah ya mallaka min ke. Tace "malam ai ya mallaka ma saura kadan yarage komi lokaci ne. Ganin zai tsaida ita da maganganu na santin kyaun datayi yasa tawayance tafice tabarshi yana hadiyar yawu kamar yabi ta yayi ta kallonta yau kyaun datayi masa daban ne. Bayan sun gaisa da mama tawuce dakin ummi ta iske ta tana shiryawa tace "mutuniyar kin hadu kayan nan sun yi miki kyau bana wasa ba. Fatima tace "kai wai ke ba kya gajiya da yaba kyau na ne? kullum sai kin cena yi kyau. Tayi dariya tace "to ai yabon gwani ya zama dole kinyi kyaun ne ba na gajiya da kallonki fatima, don Allah idan kinyi aure kada kidaina kwalliya kina matukar yin kyau da kwalliya dukda cewa idan ma bakiyi kwalliyar ba kyau kike yi ke kam Allah ya yi miki baiwa da yawa fatima. Tace "don Allah kiyi sauri mutafi kadda yamma tayi ba kya gajiya da surutu. A cikin mota suna tafiya ummi tana tuki fatima tana gefenta suna hira, tace "duk inda muka wuce fa sai an kalleki fatima ina kallon wani dazun da danja ta tsayar damu sajra kadan yabuga wa wani sbda kallonki, kidinga sa nikab kidaina daukar hankalin mutane. Ta dubeta tace "su sukaga za su iya ni bance wani yakalleni ba duk wanda wani abu yasame shi a dalilin kallona to shi yadauki alhakin kansa, muyi wata hirar. Tace "yawwa ai kuwa yau zan miki gagurumin albishir. Fatima tace "Allah sarki ai kuwa ni bani da wani labari da nake son ji mai faranta rai daya wuce in ga khalifa ya dawo ya amince da batun auranki da shi, wlh a wannan rana bansan farin ckin dazanyi ba, bansan yadda zan fassara wannan rana ba, gskiya anty ummi ina kaunar khalifa ne sbda son da kike mishi., duk da cewa na tsane shi tawani fannin sbda ba ya da tausayi. Ummi tayi dariya tace"ummi misali idan ke ce wani namijin yazo yana miki irin son danake wa khalifa za ki tausaya mai kiyarda da auran ko da ba kya sonsa ? Fatima tace "ummi ni mutum ce da ba na son ganin musulmi dan uwana a cikin damuwa in dai har na san yana zubda hawaye akan ciwon so na irin yadda kike zubda hawaye akan son khalifa zan tausaya mishi. Ummi ta girgiza kai "to albishirinki soyayya ba haka take ba. Tayi saurin katseta da fadin "ko ma yaya take ummi, khalifa ba shi da kirki, ba shi da tausayi, ya kamata mutum yaso mai sonsa, ya kamata mutum yakasance mai tausayi, nikam ba zan taba yiwa khalifa uzuri ba, duk da haka don Allah ina rokon idan khalifa yadawo kasar nan...... " Ummi tayi fakin a kofar gdansu tace "ki kwantar da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe khalifa zai dawo kasar nan. Tadafe kirji tare da fiddo ido tace "don Allah dagaske kike ? Tace "kada kiyi shakkar hakan kizuba ido gobe za kiga dr. khalifa. Ita kantaa ummi bataji dadin samun hajiya saude a gdan ba sbda a fili suke nuna ba sa son fatima, yayin da ita kuwa ta tsani mutum ya nuna mata ba ya son fatima, tana matukar kaunar fatima a ranta. Fatima tatsuguna har kasa tagayar dasu su ka amsa kowacce fuska ba fara'a suka ja baki suka tsuke, wayar fatima tafara ringing tamike tayi sauri tafita ganin sunan malam musbahu, nan da nan hajiya saude tazubawa ummi harara tace "wai me kike nufi da yawo da wannan kodaddiyar yarinyar, duk inda za ki sai da ita za ki, sai da ita za kizo gdan nan ma kin dauko ta kina nufin duk abinda xa mu tattauna akai sai dai muyi a gabanta knan ba mu da wani sirri sai ta ji ? Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ba ma wannan ne abin haushin ba saude sai yadda ummi take bata rai idan munce muna son magana da ita wai lallai sai duk abinda za a fada a fada a gaban fatima. Bayan ita fatimar idan sun tashi na su sirrin da ta ta uwar tafiya take gdansu suyi maganarsu ba a gaban ummin ba. Hajiya saude tace "ai ummi ba ta da wayo na rasa wacce irin soyayya takewa fatima kamar wadda ta asirceta, ga ta dai a haka kamar wata mai wayo nan kuwa ba komi a ranta sai wauta, mu da mukeso mu mallaki khalifa ta jawo wannan mai kama da aljanu ta jawota gdan kullum a gdan take yini idan yadawo ba kya jin ba zai ce fatima yake so ba ? Ummi tace "hajiya ya ya za ayi khalifa yace yana son fatima bayan an kusa bikinta, kwanaki kadan suka rage akaita gdan mijinta. Hajiya tace "wohoho ummi sai yaushe za ki fahimci halayyar mutane ne kidinga taka tsan tsan dasu, ki guji sharrin wanda kika taimaka wa, lokacin daka tausaya wa mutum kadakko shi daga rana kayi masa gata kadawo dashi inuwa bbu wanda zai tura cikin rana sai kai. Kin ga dai ke ce kika wayar da fatima da iya kwalliya da komi hatta magana ke kika koya mata amma babu wanda fatima za ta fara yiwa illah sai ke, tabbas idan bakiyi taka tsan tsan ba sai kin ce na gaya miki. A DAREN FARKO 18 Ummi takwana tana jujjuya maganganun su mahaifiyarta tana musanta duk abunda suka fada, ita kam ta yarda da fatima dari bisa dari bazata cutar da ita ba ta tattara duk maganganun na su ta watsar, ta fuskanci ranar dazata fuskanto ta wato ranar dawowar mutumin da ba tasan abinda sakamakon dawowar ta sa za tahaifar mata ba, farin ciki ko bakin ciki dole a daya biyu ne don haka a wannan daren bacci ta ragagge ne duk sanda tafarka sai ta ji gabanta ya fadi. Da sassafe takira fatima a waya tace don Allah tazo, tace lafiya, tace "banjin dadin jikina ne da zuciyata inason ki zo miyi hira. Fatima tace "don Allah ki kwantar da hankalinki khalifa fa ba wani bane illa mutum kamar kowa, meye na(aga hankalin ki akansa ? Tare da fatin suka shiga kitchen lokacin dataxo gdan wuraren karfe tara na safiya, ko da yaushe mama na yabawa yadda suke tsara girki da tebur a halin yanzu fatima dai da iyayanta sun zamo yan gda sosai a gdansu mama, suna yawan yi musu alheri na kayan abinci da sutura, wani lokacin mama dakanta take zuwa gun innar su fatima suyi hira sosai tanajin dadin shawarwarin datake ba ta akan rayuwa, sun shaku dayawa haka malam da abban khalifa sun zamo aminan juna ,idan kashiga gdan za kace fatima 'yar gdan ce sbda sakewar da takeyi, ci mai kyau da sha mai kyau ga kayan ado hakan yasa fatima tayi kyau ba na wasa ba kamar a taba jikinta jini yafito ta zamo kamar irin taurarin matan nan da suke zamowa ababan kallo a duk inda suka shiga, mafi yawan mazan dasuke shige da fice a gdansu mama idan sunga fatima sukan nace suna sonta, ba ta sauraron kowa duk kudin mutum da kasaitarsa, fatima ba ta bari yashiga ranta sbda alkawarin datayiwa babanta na auran malam musbahu yana tsaye a zuciyarta, bata taba wasa da maganar iyayanta ba koyaushe farin ciki ? su shi ne ranta. Gargadin karshe dasu hajia hauwa suka yiwa ummi shi ne "ta sallami fatima daga gdansu mama kafin khalifa yadawo kasar nan in ba haka ba tai kuka dakanta, ta jiye ma kanta abinda zaisa ta tayi kuka ba iyaka, bbu maganar data kama ummi aciki face ma dariya dasuka bata, magana daya tayi musu inda tace "su kwantar da hankalinsu da ace fatima za tayi soyayya da wani da tuni ta yi kafin ma khalifa yadawo sbda mazaje dayawa masu matsayi da takama da dukkan abinda da namiji yake takama dashi sunce suna sonta bata taba sauraron wani ba, ta rike maganar iyayanta dagaske ,tunda dai fatima bata yi soyayya da wani da namiji ba ba za tayi da khalifa ba. Hajiya saude tace "haka kike gani, ke mesa kikace ba kya son kowa sai khalifa ? Tace "wannan kuma daban soyayya gamon jini ce bai zamo dole don ina son wani yakasance wance itama shi tame so, masu iya magana ma kance abincin wani gubar wani. Gaba daya ummi ta san basu gamsu da hujjojinta ba, hankalinsu a tashe yake a bayan azahar in yau sai da hajiya takirata tana tmbayarta "in ce ko fatima ba ta gdan nan, na ji ance khalifa ya iso gda nigeria yana Lagos yana shirin isowa kano. Ummi tace "hajiya itace take tayani hada mai abinci, kin san yana son abinci mai dadi. Taja tsaki takashe wayar har tarasa yada za tayi da ummi. Karfe hudu na yamma dun abubuwan ci da na sha da sukaiwa khalifa sun hada a tebur, gida ya dau kamshi an gayare mai dakinsa fes yanata kamshi, bayan fati Ta idar da sallar la'asar tazura dogon hijjabin ta da nufin tafiya gda. Ummi ta fito daga wanka tace "zan tafi idan bakon ya isa ki ce muna masa sannu da zuwa. Ummi tace "ai kuwa baki isa ba dole ki tsaya kiga khalifa ya dace kigan shi. Tace "To ai na sanshi a hoto duk wanda ke shigowa gdan nan ko bai taba ganinsa a fili ba ya san shi a hoto ko ina a gdan nan fa hotonsa ne. Tace "ai na san da hakan nace kitsaya kigan shi duk yadda yake a hoto ya fi nan. Fatima tayi dariya tace "na san zaifi haka ummi idan za ki lura ai ban taba cewa kinyi laifi don kin wa dr. khalifa son da kike masa ba, ya cancanci a so shi dan ya hadu kowa yana son abu mai kyau, ba laifi bane don mace ta so mijinta yakasance mai kyau irin dr. khalifa sai dai bbu ,gskiya yi hakuri ba zan boye miki ba ba na farin ciki da gani ? khalifa, ina tayaki murnar dawowarsa ne kawai don shi ne farin ckin rayuwar ki ina son abinda zai faranta ranki ummi fiye da farin cikina, da ace dr. khalifa ya amince ya karbi soyayyarki da zan kasance cikin dumbin farin ciki mai yawan gaske amma duk da haka.... Ta katseta "fatima in dai dagaske kina son farin cikina tsaya dr. khalifa yazo don Allah. Fati bata sake magana ba tafidda hijjabinta tahaye gado takwanta, doguwar rigar shadda ce a jikinta ruwan powder, daga sama ta matseta yayin da tayi fadi daga kasa, babu kwalliya fuskarta gashin kanta ne dai ya sha gyara yakwanta a kafadarta ,a cikinsu babu wanda tasan khalifa ya shigo gdan. Ummi tace "don Allah fatima dako min ragowar furar dana rage a fridge. Fatima tafito a yadda take ko dankwali babu tashiga kitchen din falo tadakko furar kwatsam suka hada ido da dr. khalifa daya fito daga dakin mamansa, abbansa na biye dashi da manyan abokansa biyu dr. hafizu da dr. bashir, gaba daya taji kunya ya kamata cikin karfin halin gaske tarusuna tace "barka da isowa. Kallon da yayi mata yasa jikinta ya hau rawa ta wuce dasauri cikin dakin ummi tace "ke ai mutumin na ki sun shigo. Ummi tadafe kirji tace "don Allah ? furar da bata sha ba knan tazuba wata doguwar riga amma ita ta atamfa ce tayafa dankwalin a kanta ta fesa turare ta fito falon, tuni har sun haye tebur sun fara cin abinci. Fatima tabude dakin taleko don taga kallon da dr. khalifa zai yiwa ummi, ai kuwa fuskarsa baa fara'a yake amsa mata gaisuwa, su dr. hafiz ne masu zolayarta, shi kam gogar na ka ya yi dif abinci kawai yake durawa cikinsa. Wani irin takaici yakama fatima kamar taje tashake dr. khalifa tahuta an masa abinci ko yabawa ba zai yi ba yana walakanta wadda tayin. Wai wane irin mutum ne haka, nan da nan tayi takara tsanar sa, taja tsaki takoma kan kujera taharde . Ummi tashigo dakin harara tafara samu a idon fati tace "mi yiwa Allah ki daina son dr. khalifa ba shi da kirki. Ummi jikinta a sanyaye tazauna tayi tagumi tace "kiyi hakuri haka halayyarsa yake har in mutu ba zan daina sonsa ba, shi kadai nafara so a rayuwa rata, ba na iya hadashi da kowa ko bai aureni ba ba zan hakura dashi ba kitayani addu'a kawai. Fatima tafigi hijjabinta tace "to gaskiya ni ba zan iya ci gaba da zama a gdan nan ina ganin wanna abin haushin ba. Bata ji kiran da ummi ke mata ba tafice, sai dai abi ? takaicin dole tawuce ta falo gashi ba ta son kara ganin dr. khalifa yayin da shikuma dr. din kamar an ce yadago idonsa sai yadago karaf akan fatima za tafita, shi kansa bai fahimci muryarsa ba lokacin daya ke ce wa, "ke zo nan" Tayi dan jim, ba wata a falon lallai ta san da ita yakeyi, ya dace ta walakanta abin da ummi ke so, ranta a bace ta nufo inda suke ta tsuguna a gefe kanta na kasa tace "Ga ni . To bai san dalilin dayasa yakirata ba, ballantana yasan abinda zai gaya mata, ya samu kan shi da zuba mata ido shi dai bai san ta a gdan ba, Dr. hafiz ne yace "yammat don Allah ya sunanki ? Fatima kawai tace. Kafin wani cikin su yakara magana tamike dasauri tabar gdan. Dr. khalifa ya ajiye spoon din hannunsa yayi ajiyar zuciya yace "fatima. Kai wannan yarinya Allah ya hore mata kyau. Dr. bashir ya kyalkyale da dariya yace "likita knan bokan turai nan kuma kagano ance inda baki yakarkata nan yawu ke zuba. Fitowar mama takatse maganar tazauna suna hira, dr. khalifa yace "mama ina kuka samo fatima ? Tace "yarinyar nan makwabtan mu ne wanda kuka gaisa da babanta a waje dazun wanen malam musa. Ya basar da maganar kamar bai damu ba sukaci gaba da wata hirar. ***** Tun a daren masu zuwa yiwa dr. khalifa sannu dazuwa suka fara cika gdan yawanci tsoffin abokansa ne musamman na B. U. K da 'yan'uwa da abokan ckin dangi, wayoyin sa ma kashe wa yayi don yahuta, bai samu kansa ba sai sha biyun dare yahada ruwa mai zafi yai wanka yafesa turare yahaye gado, tunanin bai samu masauki a zuciyarsa ba yahau bacci sallar asuba ma sai da abbansa yatayar dashi suka nufi masallacin tare, ita kanta sallar idanunsa a rurrufe yayi ta suna dawowa yakoma wani sabon barcin. Yayin da ummi takwana ckin fargaba da kai komo a zuciyarta da tunanin tayaya za ayi dr. khalifa ya aureta ? zancen haduwa yanzu ba a magana, a tsaya bayyana tsarin kyau da Allah ya hore wa dr. khalifa bata baki ne, zuciyarta takara rudewa, sabuwar soyayyar data ninka ta bata ta karu akan ta da, ummi ta ji kanta tamkar tsawa tsawa yake mata. Da sassafe kamar yadda tasaba tashiga kitchen tafara hada abincin dr. khalifa na musamman, mama ta fita tace mata takira fatima a waya tazo tataya ta domin akwai wasu abokan dr. khalifa daza suyi breakfast tare nan da karfe takwas. An yi sa'a fati ba ta kashe waya, lokacin da ummi tabayyana mata bukatarta amsawa kawai tayi ba dan ranta ya so ba, hakanan take jin wani irin abu a zuciyarta jininta bai hadu da dr. khalifa ba, kallon da yayi mata ya firgita ta kwarai dagaske, ba ta da matsala da inna da babanta akan zuwa gdan mama, hijjabinta dogo har kasa tasaka tafito zuciyarta cike da sake saken abinda zai je ya xo. Aikin suke kowacce da abinda zuciyarta ke sakawa, karfe takwas komi yakammala a tebur suka debi na su sukayi dakin ummi. Kinga dr. khalifa ko fati ? Ummi tayi tmbayar tana kallon idon fatima wadda tagyada kai fuskarta a tsuke tace "eh na ganshi meye. " Ummi tasa gefen mayafinta tana sharar kwalla takasa cigaba da magana, zuciyar fati ta kuntata sosai yadda abincin yaki ciyuwa a gun ummi itama kasa ci tayi, tace "ummi ko zuwa zanyi in rokeshi yasoki. Tace "karki yi haka ya gargade ni akan kada in fadama cewa ina son shi, dole in kiyaye dokarsa in dai inason in zauna lfya. Fatima tace "to yanzu haka zamuyi ta zaman damuwa ? Ummi tace "damuwa ta kam ba zata gushe ba amma na ci alwashin ba zan bar dr. khalifa ba ba zan yarda in rasa shi wata tasame shi ba. Tunda ummi take irin wadannan kalaman jinta kawai fati take ta san me za ta iya ? hakuri ne yazame mata dole in batayi ba tayi tashan wahala idan so cuta ne hakuri kuma magani ne. ***** A wannan rana malam musa mahaifin su fatima yafidda bayanin cewa sati biyu rak za ayi bikin fatin da musbahu akai tagdansa, har inna tace "malam bai yi wuri ba har yaushe aka gama shiri. Yace "shi kam wannan lokaci yasanya kuma ba zai daga ba, fatima na dawowa gda malam musbahu yatare ta da zancen yana cikin farin ciki mai yawa, itama ta nuna gamsuwarta tare da fatan alheri garesu baki daya, yatambayeta abinda za tayi da kawayenta na shagalin biki tace ta fi sha'awar walima a ranar jumma'a da yamma amma dai za tayi shawara da antinta ummi. Data shiga ckin gda takira ta a waya tashaida mata, ummi tarangada guda tace "amarsu ta ango knan wannan sai mun zauna an tsara yadda za ayi, zanso ganinki ranar wannan biki za kiyi kyau na jan magana. Fati tace "fatana aure dai Allah yasanya mai alheri da albarka ba na na so inga anyi aure anyi shagali aure na soyayya amma auren bai je ko ina ba sai kiga ya lalace ko ayi ta samin matsala a rasa laifin waye mazan ko matan ? Ummi tace "kowa na da laifi fati a tsakanin mazan da matan ko wanne akwai rawar dayake takawa gun haifar da matsaloli ckin auran da rabuwarsa, amma dake insha Allahu za kuzauna lafiya da malam musbahu domin aure ne da aka gina shi a bisa kyakyawar turba, kuma za ayi shi ne don Allah,. Bayan ummi ta kashe waya tafito falo, ganin dr. khalifa ya hakimce bisa kujera wata lafiyayyar shadda a jikinsa maroon colour dinkin da matasan zamani ke yi yayi, ya yi kyau har ya wuce misali, farin gilashin idone a fuskarsa bai damu da zaman ummi a gun ba yaci gaba da fadin "mama kinsan maganar aure tana bukatar nazari da bincike, wlh a rayuwata bbu auran dana tsana irin je ka kadawo, ayi aure ana farin ciki da zarar an je an zauna a kasa fahimtar jin dadin dake ckin zaman auren, kullum kana ckin damuwa matarka na ckim damuwa meye amfanin hakan, amma idan aka natsu za asamu kwalliya tabiya kudin sabulu sbda na sani bbu wanda ya isa yakaucewa abinda Allah ya hukunta masa. Yayi shiru anan yana nazarin fuskar mama don ya fahimci yadda tadauki maganar, batace komi ba tajuyo tadubi ummi tace "'yammata yaya akayi ne yau fatin batazo tayin hira ba ? A sanyaye tace "batazo ba waya tamin yanzu tace malam ya ce idan Allah ya kaimu nan da sati biyu za ayi bikinta. Mama tatsuke fuska tace "wani irin sati biyu kuma ? Tace "haka dai tace. Tace "to je ki kiramin fatin har yaushe akayi mata shiryen shiryen amaren. Dasauri ummi tabar gun tafada daki don tasamu damar yin kukan data ke ta hadiyewa. A falo kuwa dr. khalifa ne yaji wani irin abu ya tsirga masa a cikinsa zuciyarsa takama bugawa. Fatima Za ayiwa aure nan da sati biyu ko kuwa wata fatin ce daban, nan da nan yanayinsa yasauya gaba daya yawaiwayo tare da zare space din sa yadubi mama yace "mama wace fatin za ayiwa aure ne ? Tayi murmushi "fatima yarinyar nan dai ta makotanmu daka gani jiya. Yace "doyar malam musa ? Tace "yawwa ita kuwa. Abinda yafito daga bakinsa shi kansa ya ba shi mamaki don bai san sanda yace "Lallai da sake". ****** A DAREN FARKO 19 Mama tayi masa wani irin kallo tace "me kake nufi ? Anan ne yadan shiga natsuwarsa yace "mama wannan yarinyar nakeso na aura don gskiyar magana ita neke ganin ta dace da rayuwata da tsarina haka nan zuciyata ta aminta da soyayyar ta dari bisa dari don... Ckin zafin rai mma tadaga mai hannu tace "kai ya isa haka, saita bakinka kasan abinda kake fada, fatima an yi mata miji tsawon lokaci mai yawa kuma ba za a fasa ba shi a ba ka ba. kada kasoma sanyawa zuciyarka soyayyarta wahalar da kanka za kayi don baza kasame ta ba. Bai ce komi ba yamike yabar faol zuwa daki ? sa yakira dr. hafiz yace "kana ina ? " Yace"ina asibiti yanzu muka fito daga meeting.. Yace "to ina ka dosa ? Yace "gida za ni akwai magana ne ? Yace "kwarai kuwa magana ma babba ba karama ba. Yace "kasameni a gida mana. Mota yadauka yanufi gdan dr. hafiz da ke hotoro ya iske ya rigashi isa, yace "matar gdan fa da yaran ? Dr. hafiz yatabe baki yace "ai mata ba su da matsalar data wuce biki, sunan wai kanwa ta ce data haihu tun karfe bakwai tabar gdan nan ko abinci ba a tanadar min ba kuma yunwa nakeji sosai, yanzu sbda Allah a irin wannan tsarin idan munce, za muyi aure

Chapter 8 of 19