Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba, idan ba ni nakashe shi ba wa zance ykashe shi? Idan nace ba ni nakashe shi ba dole inyi bayanin wanda yakashe shi to waye? sannan ni akazo aka iske da wuka a hannu haka nan bakinsa gana furta takasheni ,idan akace wa sai yace fatima.. Fati tarushe dakuka mai tayar da hankalin mai imani tace "kaicon rayuwata na yi nadamar zuwa wannan duniya ace an wayi gari a rasa wanda zai kashe Dr. khalifa sai ni ni fatima me xanyi da rayuwa.. me zan tsinta a cikinta, wane farin ciki zanyi a gaba? Don Allah kudaina yun'urin kareni kuyarda ni nakashe Dr. khalifa a kashe ni in huta da wannan ba'kin cikin rayuwata ba ta da amfani. Wannan bayanin da nayi iyakarsa zan iya fd'a ba zan ta'ba bud'ar bakina a kotu ince wani abu ba game da ranar da dr. khalifa ya bar duniya, hukunci kawai nake jira kuyi ha'kuri kuyafe min. Barristr Abbas yace "to shikenan munji ke kika kashe Dr. khalifa gaya mana meyasa kika kashe shi? Ta amsa "ni ma bansan dalilin dayasa na kashe shi ba. Ba wani laifi dayayi miki? Bai min komi ba sai alheri, ba komi tsakanina dashi sai alheri, ban sani ba ko alkairin ne yasa nayi masa sakayya da kisan kai. [5:08PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: DAREN FARKO 5 TSAKIYAR dare ne za mu iya kiran lokacin 'karfe biyu da rabi nadare, fatima na zaune kan dandayyar siminti ana muku mukun sanyi ne a lokacin amma ita ta ji'ke sharkab da gumi sakamakon matsanancin halin tashin hnkalin da gararin darayuwarta ke fuskanta. Ita kanta yadda alamuran suka faru suna matu'kar ba ta mamaki, koyause tambayar datake wa kanta itace waye yakashe Dr. khalifa? Me yayiwa wanda yakashe shi? Meyasa ba'a kashe shi ba sai a daren su nfarko A DARAN FARKO na amarcinsu aka biyo shi har cikin gida akan gadonsu aka kashe shi, tabbas duk wanda yakashe Dr. khalifa ya isa azzalumi, ita da Dr.khalifan ne baya so shi yasa aka kashe shi a sigar da duk wanda yagani zaice itace takashe shi. Ita da Dr. khalifa mesuka yiwa wani daya daidaici irin wannan dare a gunsu yakashe mata miji? Wannan itace tambayar datake wa kanta tun lokacin da aka kulleta a wannan guri, itace tmbayar da ciwon dayake mata a zuci ke barazanar sa zuciyarta tabuga ta tadda mata ajalin sbda tsananin damuwa, Allahu akbar ashe ko kwana d'aya ba za tayi a gidan miji ba, bala'i zai fad'a musu A DARANSU NA FARKO. Sai kace ana tariyo mata rayuwarta da abinda yagudana a tarihin rayuwarta gaba d'aya haka yarin'ka wanzuwa a zuciyarta da 'kwa'kwalwarta kamar shirin fim. *******************************,****** Malam haruna shi ne mahaifin malam musa wanda yakasance shi ne mahaifi ga su fatima. Asali malam Haruna bafullatanin gombe ne yawon neman karatu yakawo shi kano kasancewarsu fulani ne na jame inda yazauna a hannun wani shahararran malami mai babbar tsangaya anan kano, Allah ya yi malam haruna mutum ne mai tsananin ha'kuri da biyayya malamin nan da iyalinsa suna matu'kar jin dad'in zama dashi inda a sanadin haka ne suka d'au d'iyarsu Maryama suka ba shi auranta ita kuma tahaifa masa 'ya'ya maza har bakwai, malam musa ne autansu. Bayan rasuwan malamin, malam haruna shi yazamo magajinsa don duk acikin almajiransa na wannan lkcin ba wanda yakaishi sha'kuwa dashi, ga kaifin basira yaci gaba da jagorantar tsangayar kuma shi yari'ke iyalan malam har zuwa shima lokacin da Allah (SWT) ya kar'bi ransa sai d'ansa malam musa yagajeshi a lokacin ma bai dade da auran fari ba inda matarsa zainab tafito itama daga zuri'ar tsohon malamin marigYi malam Yakubu, an ce na ji dad'i shi ne gari ba na saba ba. Malam musa yayi kyakyawan gadon hali na hakuri datsananin juriya irin na mahaifinsa, mutum ne mai matukar saukin kaida sanin yakamata, hka itama matarsa zainabu bbu abinda yadameta da zafafawa kanta game da rayuwar duniya. Suna zaman su lfya a dan karamin gidan da yake haya kusa da makarantarsu basu dogara da kowa ba sai Allah mutane ne dako kadan va su da kwadayi, mutanan unguwar sunajin dadin zama dasu sosai ana zaune lfya. Aliyu shi ne d'a na farko da goggo Abu tafara haifawa malam sai mai sunan malam Yakub suna cewa dashi malam, sai rukayya sai fati sai mai sunan malam Haruna suna cemasa baban gida sai muhammadu nazifi sai nuraddeen ba su da wadata da dukiya rayuwa ce tarufin asiri amma akwai wadatar zuci da son juna, rayuwarsu tana yawan ba wa mutane sha'awa yadda suke kamun kak da tarbiyya da girmama jama'a da 'ya'yan gidan masha Allahu hka suke amma ba kamar fatima, itace tafi fad'a kowa d'auko halayyar mahaifinsu kamar yadda tafi kowa kama sak da mahaifinsu don hkane tafi kowa kyau a gidan. kaf zuri'ar marigayi malam haruna kyawawan gaske ne har kwatance ake dashi a garin sbda kyaunsu ga uwa uba farin jini dukda cewa ba masu kud'i bane ba su da komi sai rufin asirin Allah. Tun fati tana 'yar mitsitsiyarta ake mata shaidar hkuri dasau'kin kai duk inda fatima tashiga sai an yaba halayyarta, balletana biyayya ga iyaye wad'anda takeji kamar tayi musu numfashi don tsananin so da 'kauna ko kuma takwanta sudinga bi ta kan ruwan cikinta don biyayya. Hka a makaranta malamanta ke ji da ita bayan maida hankali akan karatu da gudun fitina ga biyayya da tsafta. Fatima kyakyawar gaske ce daga ganinta ka ga bafulatana sak zai wahala mutum yagaji da kallonta sbda Allah ya yi mata baiwar kyau mai tsayawa a zuci. Bayan auran yayarta rukayya da shekara biyu wata rana da daddare malam musa yana zaune kan tabarmarsa goggo Abu tana gefe itama kan tata tabarmar yayin da fatima ke zaune kusa da su tana yi masa firfita. Yace "zainabu yaya batun d'an gidan rukayya ya warware ko? Ta ce "Alhamdulillah jiki kam dasau'ki yau danaje na iske shi yanata wasa da yara. Yace "Masha Allah, sannan yagyara zama yadubi fatima yace "fati yaya batun haddarki ta jiya kin haddace" Tace "na haddace har d'azun na ba da a gaban malam musbahu ya dad'a min wani. Yayi murmushi yace "Alhamdulillah yana daga cikin ni'imar da Allah yake yiwa mutane shi ne yabasu 'ya'ya na gari salihai wad'anda zasu zamo farin ciki a gareka, fatima ina matu'kar alfahari dake sbda kinada hankali da biyayya ban ta'ba shakku akan biyayyar da kike mana ba wannan shi ne dalilin dayasa kai tsaye ko shawara banyi dake ba na daukeki nabawa malam musbahu auranki sbda na fahimci halayyarku ta zo d'aya. Shi ma mutum ne da Allah yahore masa ha'kuri dasanin yakamata tunda nake dashi bai taba aikata min wani abu na assha ba, sai dai ajizanci irin na d'an adam wanda yake kai mutum ga kuskure. Amma dukda hka ina neman yardarki, idan kin yarda ba wani abune mai girma agareni ba don ina da ya'kini da kwanciyar hnkali akan hakan, idan kuma kin ce baki yarda ba ma'ana ba kya son shi ina mai yimiki rantsuwa da girman Allah ba zan damu ba na san Allah ne bai 'kaddara musbahu mijinki bane shi yasa kika'ki amincewa dashi. Fatima kanta na 'kasa ta shiga shararar 'kwalla batace komi ba, malam yace "fatima kada wannan magana tad'aga miki hnkali balletana tajefa zuciyarki cikin damuwa. Cikin shashe'kar kuka fati tace "dole indamu baba ban ta'ba tunanin akwai watarana dazakayi tunanin zan bijirewa umarninka ba, har inada abinda zanyi wanda zaisa inyi gaban kaina ba tare da umarninka ba. Wlh idan har akwai watarana wadda za tazo in bijirewa umarninku ba na fata tarismeni ina numfashi a duniyar nan gara in mutu da in ganta sbda haka baba ba na bukatar ka kara neman yardata a bisa wani bu wanda kake nufin zartarwa a kaina. Na amsa malam musbahu hannu biyu biyu kuma zan yi masa biyayya bakin iyawa ta. Malam musa yagirgiza kai yace "Allah yayi miki albarka fatima, Ubangiji Allah yasa kigama da duniya lfya, biyayyar dakikayi mana Allah yasa 'ya'yan dazaki haifa suyi miki wadda tafita, dukda haka ina mai tabbatar miki dacewa hakkinki ne in nemi amincewarki akan auranki da malam musbahu kamar yadda nayi miki bayani a baya ba wai dan ina shakkun amincewarki a gareni ba sai dan in ba ki hakknki a matsayina na mahaifinki. Yadda nake miki wannan magana haka na zaunar da musbahu nace dashi musbahu yau fiye da shekarar ka goma a hannuna tun lkcin dakazo da sassafe kana kuka kana ce min in taimakeka inje in ba wa kawunka hakuri matarsa ta yi maka sharri zai dake ka natambayeka abinda kayi mata kace min cewa tyi dashi na yi mata sata, malam musa yace "fatima a lokacin ne nasa musbahu a gaba har gidan kawunsa wanda yake bayan wannan layin na mu, kasancewarsa maraya, mahaifiyarsa ta rasu tun yana yayayye, yayin da mahaifinsa yarasu bayan shekara d'aya tsakani wannan shi ne dalilin dayasa kanin mahaifinsa yadaukeshi yabawa matarsa wadda ita kuma tadauki tsanar duniya ta dora masa, take wahalar da rayuwarsa. Abunda yasa musbahu yazo guna shi ne "lokaci lokaci kawun na sa yana zuwa dashi nan don daukar karatu da magriba kuma ya san akwai fahimtar juna tsakani na da kawunsa. Lokacin damukaje gdan nayi sallama da kawun yafito yana ganina tare da musbahu ya hau fada ko gaisawa bai bari munyi ba inda yake shiga ba nan yake fita ba, dakyar nasa yayi shiru nace "Alhaji Habibu ba haka ake lamarin duniya ba, idan mace tagaya maka magana saika bincika kafin ka dauki mataki, sha'anin mata idan akace ba su suka haifi d'a ba sai a hnkali ballantana d'an dayake maraya. Albaji habibu yace "duk abinda yagaya maka karya ne don ya ji Kawai ana cewa maraya ne duk abinda aka ajiye a gidan nan saiya sace yasiyar sannan idan nayi masa magana sai ytafi yana hadani da muatane ana cewa muna cutar dashi alhali shi maraya ne don ba mu muka haife shi ba. Ina dalilin wannan, haka kawai an ba ni ajiyar kudade masu yawa yabi dare ya bi rana har dakina ya sace, to ba zan iya ba yan sanda zansa sukama shi su kulle in huta ko kuma in kai shi gidan kangararrun yara ka ga na huta. Na dubeshi tsam sai da yagama fadace fadacensa nace"to ni kam ba zan bari kakai musbahu gidan kangararrun yara ba tunda shi ba kangararre bane, idan kai ba za ka iya rikon shi ba dan kawai ba kai kahaife shi ba ni zan iya, sai dai ina son kadinga Tunawa wannan yaron maraya ne kuma maraya ne a gareka, idan kaci amanarshi Allah ya tambayeka kamar yadda yazo acikin hadisin ma'aiki(SAW) ,sai ya tambayi kowa akan abinda yaba shi kiwo, maigida mai kiwo ne Allah sai ya tambaye shi akan iyalansa ya yatafiyar dasu.......... Ya katseni cikin hushi yace "Ni bance kayi min wa'azi ba tunda nan ba makaranta bace, ka ce za ka iya rike musbahu, ka ga gashinan kuje kukarata idan yagwada maka mugun halin sa za ka koreshi ne, da kai ka kama da sannu zan ganku a rana. " Nace "Insha Allahu ba za kaganmu a rana ba, kai ne dai za kayi nadamar abinda kayi masa, da sannu za kaga sakayyar da Allah zaiyi masa kuma da sannu za kagani watarana zai zama abin taimako gareka da iyalin na ka ma wadanda kuka hada kai dasu kuka walakantashi. A lokacin kawun musbahu yashiga dakin da musbahu yake kwana a zaure yadinga watso masa kayansa yana masifa a haka nataya shi mu*a kwaso kayan, wannan shi ne dalilin zaman muśbahu a gidan nan lokaci lokaci dangin iyayansa na uwa dana uba sukanzo guna suna yi mini godiya shi ma yana ziyartarsu. malam musa yaci gaba dacewa fatima lkcn dana gama tunasar da musbahu wannan lbri kansa na kasa nakara da fadin "musbahu lkci ya yi dazakayi aure shekararka ashirin da bakwai a duniya, kana bukatar ajiye iyali tunda kke baka taba cemin ga wata mace dakakeso ba sbda kunya dakake da ita da kawaici. Musbahu ka rayu kana hidima gareni vakin iyawarka, allah kadai yasan kaunar danake maka, wannan shiyasa nadauki diyata mafi soyuwa a zuciyata nabaka ita dan tazamo matarka uwar yayanka. Yayi saurin fadin fTima yana me dafe kirji da fiddo idb stories A DAREN FARKO 7 A babban falon alhaji aka sauki iyalan malam, falon da ba kamarsa a gdan duk wani kasaitaccan bakon da zai gana dashi a gidan nan yake sauke shi, aka kawo musu abubuwan ci dana sha na alfarma. Alhaji da hajiya maijidda suka fito aka gaisa, malam yagabatar dasu ga iyalansa aka shiga yi musu godiya mai yawa, alhaji hace "malam kwarai dagaske na ji dadi matuka da zuwanku gidan nan, sbda dama wannan gda ne na mutane ba mu da 'ya'ya in banda d'a guda d'aya da Allah yabamu amma idan kashigo koyaushe za ka iske mutane da yawa a gdan ko da yaushe muna godewa Allah kalar jama'a kam ba wadda ba ma gani a wannan gida sai dai a gefe guda banji dadin wannan zuwa na ku ba da sunan godiya don banga abinda nayi ba, wlh da ace malam za ka baiwa 'dana khalifa auran 'yarka da na yi murna duk dan kusan d'aya muke da kuwannan dukiyar da Allah yabani ba ta gabana ballantana har in ga wai na fi wani. Malam yayi shiru yana tunanin maganganun Alhaji muhammadu, shi kam vai taba burin kai diyarsa irin gida na aljahi muhammadu ba hakan yasa hnkalinsa yatashi sosai jikinsa yayi sanyi. Bayan sun dawo gida suna zaune a tsakar gida da da daddare zainabu tace "malam ai kuwa a dazu rukayya take ce min tunda alhaji yanemi aure a gdan nan mai zai hana abashi fatima. Sai ya bata rai yace "shi yasa hnkali na yatashi lokacin da alhaji yafurta wannan magana a gabanku, sbda ku mata ne karamin tunani gareku, tunanin ku ba ya wuce karan hancinku, ko da yaushe kyale kyale na duniya kan dauki hankalinku ku aikata abinda zuciyoyin ku suka raya muku sai daga baya azo ana nadama sbda haka ba na son wannan magana daga yau, shi yasa ko amsa ban ba wa alhaji ba lokacin da ya fada, ba na ra'ayin diyata tayi auran dukiya, idan alhaji ya kasance mutumin kirki mai taimakon talakawa sai akace muku shi dan na sa da sauran danginsu haka suke? da zaran mun dauki fatima mun ba su shikenan kowa ma cewa zaiyi kwadayi yakaimu ba za ace su suka nemi auran ba cewa za ayi ni ne nanemi khalifa ya auri fatima duk gorin da akanmu da duk walakancin da akayi mata mu muka jawo. Goggo Abu tace "kuma hakane fa malam bbu wanda yayi wannan tunanin acikinmu kowa kirkin Alhajin yake kallo. ************ Tun daga wannan lokacin aminci mai karfi da zumunci yashiga tsakanin mutanan da iyalansa da alhaji da hajiya maijidda a lokacin nan shi khalifa yana kasar germany inda yake karatunsa na likita. Alhaji bai da abokin shawara sai malam haka hajiya maijidda ta dauki goggo Abu kamar yar uwarta tajini, dukda cewa alhaji muhammadu bai ka ra nuna wa malam yana son yabawa dansa khalifa auran 'yarsa fatima ba tun daga wannan lomacin hankalin malam bai kwanta ba ba wai don yana kin alhajin ba, malam yana matukar kaunar alhaji har cikin zuciyarsa kamar yadda shi ma alhajin yake nuna masa kauna ta tsakani da Allah, auran fati ne kawai ba ya son yabawa khalifa sbda abinda zai je yazo. Bayan shi kansa alhajin akwai mutane wadanda suke da kima a idon malam suna nuna sha'awarsu akan malam yaba 'ya'yansu auran fatima sbda kamun kai na yarinyar da uwa uba kyawun halittarta bai taba furtawa wani ya ba shi ba, sai dai yayi dariya kawai yace aure nufi ne na Ubangiji. A ranar da alhaji yazo wurin malam da daddare bayan sun gama karatu da addu"o i yace dashi "malam idan Allah ya nuna mana rana itayau khalifa zai dawo daga kasar germany. Gaban malam yafadi amma bai bari alhaji ya fahimci fargabar da zuciyarsa ke ciki ba, ya fadada fara'arsa yace "masha Allah ya kammala karatun knan. Alhaji yace "kwarai kuwa karatu ya kammala lfya don ya samu cikakkiyar takardarsa ta shaida ya kammala karatun sa a matsayin cikakken likitan mata. Malam yace "mun godewa Allah, Allah yasa anyi a sa'a kuma Allah yadawo dashi lfya. " ***************** Shi kansa malam baisan dalilin dayasa hankalinsa yatashi sosai da maganar dawowar Dr. khalifa ba, tun da alhaji yashaida masa zancen dawowar yashiga damuwa sosai ko goggo Abu bai gayawa ba, shi kadai yake tunani a ransa karshen tunaninsa shi ne ba abinda yadace yayi wanda yawuce yaba auran fatima kafin dawowar Dr. khalifa ko da alhaji ya tada maganar idan yagaya mai ya bada ita shikenan an huta. Wannan ahi ne dalilin dayasa yadauki fati yaba amintaccan almajirinsa kuma d'ansa wanda yayarda dashi fiye dakowa,a 'ko'karinsa na ganin iyalansa sun zauna lfya a gidajan mazajansu, tun ranar daya shiga gdan alhaji yatabbatar wannan rayuwar ta fi 'karfin fatima ba za ta iya ba me zaisa yada'u d'iyarsa yakaita inda za tashiga wani hali rayuwar da mutum ya sabayi ita yake iyawa,idan yaje inda aka fi 'karfinsa wahala zai sha. ***************'Karfe bakwai daidai na yammacin litinin jirgin IRS yasauka dasu Dr. Abubakar Assadiq wanda aka fi sani da Dr. khalifa a filin jirgin saman Malam Aminu kano dake nan kano wanda yad'aukesu daga filin jirgin saman murtala muhammadu dake birnin ikko jihar lagos, bayan da jirgin da jirgin daya d'akkosu daga jamus ya ajiye su da asubahin wannan rana. Dr. khalifa dogon matashi ne kyakyawan gaske irin mazan nan da ko wace mace ke burin mallaka ba wai don shi da mahaifan sa sun mallaki abun duniya ba sai dan haduwarsa na gwarzon namiji wanda ya isa a kalleshi a san cewa shi d'a namiji ne abin kwatance acikin mazaje. Yana da madaidaiciyar 'kiba wacce tadace da tsawonsa ma'ana 'kibar da tsawon basuyi masa yawan dazasu sa shi muni ba. Babu inda yabar mahaifinsa alhaji muhammadu a kyau kamanninsu d'aya har tafiyarshi dai bambamcin halayyar abbansa mutum ne mai matukar kirki da sau'ki kai da son mutane yayin da Dr. khalifa yakasance miskili tun yana yaro bai da son magana sai dai 'kar'karfar mutum ne kuma gwarzo wanda ba shi da tsoro ko kad'an. Dr. khalifa ya taso cikin gata da kulawar iyaye bai san wani abu wai shi babu ba duk abinda yakeso shi akeyi masa, hakan ne yasa yagirma cikin izza da isa da raina mutane, sai dai yana raina wanda yashiga harkarsa ne, idan baka kalli inda yake ba ba ruwansa dakai, kuma bai ta'ba damuwa da yawan alherin dayake yi wa mutane ba idan ma Allah yayi mutum yana da rabo idan kazo neman abu gun abbansa sai yabaka abinda yafi wanda abban zai ba ka ma'ana dai shi kyautar sa taganin dama ce kuma sa'a ce. Bayan ya kammala karatun sa na secondary yafara karatu anan jami'ar bayero dake kano. Inda Allah yataimake shi shine dukda gatan da yakeda shi na iyayansa bai wasa da karatu kamar yadda sauran 'ya'yan gatan ke shagwaba suyin karatu sbda iyayansu suna da dukiya. Dr. khalifa tun yana nursery yake da kaifin basira wannan yasa yake da farin jini a gun malamansa har izuwa jami'a inda anan ne yazamo kamar jinjiri wata sha kallo sbda farin jinin dayake dashi, bayan dai tsabar kyau da iya dressing da Allah yahore masa. Kaifin basirarsa yana burge kowa sannan ga 'barnar dukiya dayake wa abokai maza da mata,shi yasa duk inda Dr. khalifa yake sai ka ga mutane ana wata irin shafta mai dad'i. A cikin Bayero 'yan matan dasuka shiga mawuyacin hali akan son Dr. khalifa Allah kadai yasan yawansu yayin dashi bai san suna yi ba, wasu suna ganin sbda dukiyar ubansa ne suke sinsa, kasancewarsa dan gata ahi kad'ai suka mallaka duk wannan tarin dukiyar da Allah yaba mahaifinsa shi ne mai mallakarta to kuma shi akwai 'ya'yan manyan masu kudi suna matkar sonsa, su ba abinda suke nema dashi sai shi kansa, shi mutum ne mai saurin d'aukar hankalin d'iya mace sbda Allah ya ba shi surar da mata keso wadda take burge su. Sai dai kash babu soyayya acikin ra'ayin Dr. khalifa, babi wata d'iya mace daya taba kallo yace yana ao da bakinsa wadanda suke nuna masa soyayyarsu ma share su yake kamar bai gane ba, a lokuta da dama har tambayar kansa yakanyi wai meye so? Ta yaya kake ganewa ka kamu da son wance? Shekarar sa hudu da kammala digiri dinsa nafarko a Bayero mahaifinsa alhaji muhammadu yace "yayi shirin tafiya germany inda yakeson yayi karatun zama cikakken likitan mata. Lokacin dayake gaya masa wannan magana suna zaune ne a falon abban na cikin gida dasafe suna breakfast tare da mamansu hajiya Maijidda. Dr. khalifa ya ajiye cup din shayi yana kallon abbansa yace "abba na ji koda yaushe fa kana gaya min bbu abinda kafi bukata wanda yawuce inzauna kusa dakai in kula maka da harkokin kasuwancinka. Abba yayi murmushi yace "ina sane da wannan khalifa sai dai hakan ba zai hana in yi abinda ydace ba, ina burin kazamo likita don in gina maka babban asibiti anan kano wanda zan sadaukar dashi sbda Allah a dinga taimakawa bayin Allah wadanda ba su dashi. Yace "abba toh kasuwancin na ka fa? ba ka son in taimaka maka akansa? Yace "kada kadamu da wannan saddik ina bukatarka a kusa dani a ko da yaushe sbda abubuwa suna mini yawa sannan yaran danake dasu ba kowane yakeda amana ba, sannan ina samun matsalar rashin masu sa ido a kan abubuwa dukda kokarin danake da ganin na basu hakkokinsu gudun samun matsala irin wannan toh amma matsalata ba za tasa in ki taimakon al'umar musulmi ba, na hakura da amfanuwar da kasuwancina zaiyi dakai kaje kayi wannan karatu don ka taimakawa al'ummar musulmi 'yan 'uwanmu. Mama tace "to amma abba kafin yatafi yanada kyau yayi aure yatafi da matar ko? Dr. khalifa tadafe 'kirji tare da fiddo ido yace "aure mama? sghekaruna duka duka ashirin da biyu ina ni ina maganar aure? don Allah karki 'kara wannan maganar mama ni tun da nake ma ban ta'ba ganin wata mace da zuciyata ta ta'ba so ba, wadda har nakejin zan iya aure. Mama ta ta'be baki tana harararsa tace "kai da Allah rufe mana baki ni za kacewa ba wata mace daka taba so, duk 'yammatan dake biyoka har gidan nan ba 'yan matanka bane? kokuwa kana zaton ba ni da masaniya kan abinda kake? Yalangabar dakai yace 'Alah mama ba budurwata ko daya aciki? su duk wacce kikaga ta zo gdan nan nemana kawata ce ina nufin abokan karatu. Abba yayi murmushi yace "to ko ma dai meye za katafi germany a haka ba tare da aure ba amma idan Allah ya dawo dakai lafiya za ka yi aure insha Allahu ka fahimta ko? Kansa na kasa bai ce komi ba shi kan baya so ko zancan aure a yi masa don ba batun soyayya a gabansa ama batun kawaye wadanda ake debe kewar rayuwa dasu ai babu wadda babu. Bayan fitar khalifa abba yabata rai yana kallon mama yace "ba na son kina matsawa yaron nan kan batun aure tunda ba shi da ra'ayi har 'kwara nawa khalifan yake da za ace dole sai ya yi aure. Mama tace "Alhaji ai kaine dai bakasan abinda ke faruwa ba, dukiyar daka sakarwa yaron nan tasa yanayin abinda duk yaga damar yi masa auren shi ne abinda yafi dacewa. Ya kara tsuke fuska yace "ni fa ba na son zargi irin wannan muci gaba da dagewa da addu'ar damuke masa insha Allahu Allah zai tsare mana shi. Tace "shikenan alhaji kuma bayan haka kana sane da maganar yarinyar nan zainab tana matukar son khalifa amma 'ki'ri'kiri yake nunawa ba ya son ta ka ki yin wani abu a kan wannan maganar dakayi inason kabani goyon baya ne don ayi auransu da zainab har kunyar mahaifiyarta nakeji yadda fa yake d'angata itama 'yar gata ce mahaifiyarta na sonta kaga...... Abban yace "Don Allah kihutar da bakinki da fad'in abinda ke kanki kinsan ba zai yiwu ba. Daman na ce miki mahaifiyar zainab ba ta son ta ne, kokuwa kin ta'ba ganin wanda yahaifi d'ansa yace ba ya so? kawai dai kud'i ake nunawa da so? kinfi kowa sanin cewa ba zan ta'ba tursasawa d'ana auran matar da ba ya ra'ayi ba don muna da dangantaka da iyayanta, kamar yadda nima ba zanso a tursasawa wata d'iya ta auri khalifa ba alhali ita ba ta so. Inaso idan khalifa yatashi aure ya auri matar dayake matukar so itama tana matukar sonsa, insha Allahu zanyiwa khalifa bikinda za a jima a garin nan ba a ga biki na d'an gata irin sa ba. Farin cikina da kwanciyar hnkalina bai wuce auran soyayya bane don hka idan khalifa yanason zainab zai aureta a lokacin daya nuna yana son aure, idan kuma ba ya sonta zai auri wadda yake so ne bbu dlilin dazaisa don tana son shi ace dole sai ya aureta, hkan na nufin ita an mata adalci shi kuma an tauye masa hakki nsa knan? Tace "shknan ya wuce. A DAREN FARKO 8 Ummi d'iya ce ga Hajiya Hauwa yayar Abba wadda take bin babbar yayarsu Hajiya jummai duk da cewa kafin tasowar ummi hajiya Hauwa ba sa shiri da mama don tana cikin masu zakewa 'yan gaba gaba a kan sai abba ya yi aure tunda ita maman ba haihuwa take ba, in banda hajiya jummai datafi karfinsu ita kuma tana matukar son mama sbda kirkinta yayin dasu hajiya hauwa gani suke duk kirkin dasu jummai ke cewa tana dashi na kissa ne da munafunci don ta mallakesu su da d'an uwan tare dacewa babu abinda alhaji muhammadu ba ya musu hatta saudiya shi yakai hauwan ita da mijinta kasancewar duk cikin 'yan uwan nata ma itace ta auri mai karamin 'karfi sai dai tsananin soyayya, kayan abinci da kudi akai akai yake musu aike dukda haka hajiya hauwa ba ta gani kawai sbda ba ta son matarsa hajiya maijidda, yan biyu hajiya hauwa tafara haifa sannan tahaifi wani namijin mai suna Abdulrasheed tahaifi wasu 'yan biyun su kuma mata ummi ce d'iyarta ta biyun 'karshe inda taci sunan mahaifiyar abbansu ake cemata ummi daga ita sai dan autansu umar. Hajiya hauwa na matukar son ummi kasancewarta mai halayya irin ta ta, tun tana yar karama take abokiyar shawara gareta ,ba laifi itama tanada kyau da d'an gwargwadon abinda yasa ake dad'a ganin kyaun ummi bai wuce yanayinta ba da kuma bkin tsiwarta tsiwar kanta tan yi mata kyau, tana burge mutane da dama. Bata fiye zuwa gdan abba ba sai ana wani sha'anin sbda ba shiri take da mama ba, tanada d'abi'ar duk wanda hajiyarsu bata shiri dashi itama baza tayi shiri dashi ba, tana biyewa ra'ayi da son zuciyar hajiyarta shi yasa ra'ayinsu ya zo d'aya. Ummi na aji hud'u na secondary Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa kuma a gun zaman makokin ne wata irin soyayya tashiga zuciyar ummi da Dr. khalifa farat d'aya a lokacin ummin shekarunta goma sha shida kacal a cikin 'yan maan ma bata ri'ka ba shi ne lokacin dasuke tasawa. Ranar da aka kwana bakwai da rasuwar suna zaune a d'akin hajiya hauwa ita

Chapter 3 of 19