Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi hakuri da auran khalifa ba dai fatima ba don fatima ta ci amanata ta yaudareni na gama gaya mata sirrin zuciyata da niyyar ta taimake ni tasama mini fada a zuciyar khalifa amma ina maimakon tayi min hakan ganin son da khalifa yake mata sai tayi amfani da wannan dama tabi hanyar data mallake zuciyarsa har yadinga nunawa tamkar zai mutu ne idan yarasat., duk fa fatima da khalifa sun san halin danake ciki basu tausaya min ba, jidda ko ke din nan bakisan sirrin zuciyata cikin abinda yashafi khalifa ba yadda fatima tasani, ta san ydda nake kwana ba na barci, ta san yadda nake kwana idona na zubar da hawaye, ta san yadda nake yini ba ci ba sha, duk sbda na rasa khalifa, amma fatima tashare tashiga fafutuka akanta, har sai data mallakeshi, ita kadai yake kallo, itace a gabansa, wannan shine dalilin dayasa nace yadda narasa shi itama tarasa shi. Nace "Don Allah ummi me zan gaya miki ki fuskanci cewa wannan kuskure ne babba za ki tafka ? duk wannan abubuwan da kike fada ba hujja bane wanda za tasa ki raba fati da khalifa ta wata hanyar m bllantana ta wannan mummunar hanyar, don Allah ummi kiyi hakuri. Tace "Jiddah karki bta bakinki da ace, zan iya yin hakuri da tuni na ba wa kaina hakuri. Nace 'na ji ki bi duk hanyar da za ki bi don ganin kin rabasu amma ba wannan ba. Tace "jidda kudimmu dayawa sun salwanta akan in raba fati da khalifa in ja hankalinsa sai yakasance ma kamar soyayyarta ake kara masa, babu wata hanya da za tayi tasirin rabasu sai wannan hanyar da zan bi, dole in bita kiyi hakuri kawai Nace "To naji tawace hanya xa kibi ki kashe shin ? ashe ke yar ta'addace ban bansani ba ? Tabushe da dariya tace "duk lokacin dakika samu labarin an kashe dr. khalifa, ni ummi ni na kashe shi, idan kin dawo kya ji bayanin hanyar da zan bi.... To nan ne takashe wayarta. Tun daga wannan rana ban sake samunta a waya ba, hankalina ya tashi sosai idan nayi yunkurin kiran wani sai in ji a jikina kamar ba da gaske ummi take ba ko kusa ban yarda za ta iya aikata kisan kai ba, to kada yakasance nafada ita kuma ba gaske take ba dana rasa yadda zanyi sai nayi shiru naci gaba da addu'a. Ba a dade dayin haka ba wata rana da safe wani matashi yazo gdan danake zaune a london yace sako ke tafe dashi yana son magana dani, nace "daga ina ? Yace "Daga kano, na zo miki da wani muhimmin abu amma na roki yazamo sirri a gareki. . **** Jiddah zaria,,, to ko wani sirri ne kuma wannan ??? A DAREN FARKO 37 Duk da cewa zuciyata bata kwanta da mutumin ba amma na daure nace ba kmai shigo muka zauna a falo yana duba na yamiko min wani memory card, nace "Na meye. Yace "karbi xan miki bayani. Na jima ina kallonsa sannan nace "kana tunanin zan karbi abinda ba ni da masaniya akan sa. Yayi murmushi yace "don Allah kar ki damu wannan abin ba zai taba zama abin cutarwa gareki ba face yazamo abin amfani na tabbatar ba za ki taba mantawa da zuwana ba yayin da kika fahimci muhimmancin wannan abin a gunki idan bukatar sa ta taso. Nace "to ai ni bansan daga ina kake ba, ban san meye a cikin sa ba ballantana in san dalilin daya sa ka ban shi, ka fada min mana idan kana son in karba. Yace "jidda kiyi hakuri dai ki karba wannan memorin ba wani ya shafa ba illa aminiyarki ummi. Yajefo min kan cinyata yamike tsaye yana cigaba da kallona yace "na daina lallabaki akan ki karba idan kin ga dama ki jefar dashi nidai ai na kawo miki, ina son kisani lokacin da ummi tayi miki wayatace za ta kashe dr. khalifa ina zaune duk wani bu da kuka fada yana ckin wannan memory daga bisani za kiga wasu muhimman abubuwa da xai miki amfani a ciki, in kuma har yanzu baki gamsu ba za ki iya jefar dashi. Yana gama fadar haka ya kama hanya zai fice, na dauki memodin jikina na rawa nabishi ina rokon yadawo yagaya min sunansa kuma yayi min karin bayani don ba karamin rikitani yayi ba. Yace "Babu wani bayani dazan kara miki, jin sunana kuma ba ya da amfani gareki a yanxu tunda dai kikaji nafadi haka kin san wannan memorin yanada amfani gareki, kiyi hattara ki kiyaye kada ki bude shi sai bukatar hakan ta taso. Iya abinda yafada min knan yafice yabarni tsaye da memory card a hannuna jikina na rawa. Jidda tayi shiru. Kowa ma a kotun shiru yayi ana kallonta, masu rubutu na yi masu nazari na yi. fatima na tsaye kyam inda aka tsaida ta ko motsi ba ta yi ba, kallon dakowa yake wa jidda itama shi take mata. Ummi kuwa da kai tsaye ita abin yake shafa tana zaune tadaura kanta bisa cinyarta itama dai bata motsa ba, mutanan da basu sn ita abin yashafa ba basu kalleta ba iyayan marigayi dr. khalifa da iyayan fatima fatima da wadanda suka san itace umin da ake nufi sun dawo da kallonsu kanta, ina zaton shi ne dalilin daya sa ta sunkuyar da kanta bata dago ba, to ama dayake hankalin mutane na kan jidda da mahukunta suna son jin yadda al'amarin ya kaya sai basu motsa da wani abu ba suka fuskanci jiddah don jin yadda za ta kasance cikin wannan al'amari mai ban mamaki, aka ba ma jidda umarnin taci gaba bayyana labarin datake bayyanawa, tadora da fadin. Bayan tfiyar wannan mutumin nazauna shiru ina tunanin al'amarin nayi shawarar in bude wnnan memory a wautata in ga meye a cikinsa, haka kawai sai naji tsoro ya kamani, kamar wadda akayi wa dabaibayi nakasa budewa kuma nakasa bayyanawa kowa al'amarin, nayi masa ajiya mai kyau har zuwa lokacin danaji gabaki daya na kasa samun natsuwa idan nakwanta bacci sai bacci ya gagareni, in kuwa nasamu barcin zan yi ta fama ne da mafarkai masu ban tsoro, dole tasa nabaro london ina ckin karatu na nadawo, a ranar dana dawo din nasamu lbrin an kashe dr. khalifa lamarin daya tayar mini da hankali sosai, nana da nan natuno hirar da mukayi da ummi a waya wanda tun daga wannan rana ban sake samun ummi a waya ba sannan itama bata sake kirana ba, a wannan lokacin ne nadakko wannan menoryn nabude naga abinda ya kunsa. Jidda takara tausasa lafuzanta cike da ladabi tace "ya mai shari'a wannan memorin shi ne shaidata dukka abinda nafada yana ciki. Mai shari'a yabada umarnin akawo na'urorin dazasu haskawa dukkan jama'ar da ke gun abin da ke cikin memorin, nan da nan aka kawo jama'a suka baza idanuwa cike da mamaki, har lokacin ummi bata daga kanta ba kuma babu wanda yayi mata magana. Abinda allon talabijn din yafara nunawa shine ummi ce tsaye a wani guri ita kadai, ta sha ado tayi kyau dayawa ,wani matashi yabullo ta bayanta yace "ummi gani na zo. Ta waiwayo tadubeshi tana murmushi tace "sannu dazuwa yaya. Yayi murmushin shima yace "yauwa ummi ya akai naga fuskar ki ckin damuwa ? Daga gani wani abu yana damun zuciyarki, gaya mim ko meye zan taimake ki in dai zan iya. Tayi murmushi tace "na san za ka taimakeni yaya shi yasa na fiddo maka damuwata, duk da cewa magana ce nazo maka da ita mai tsananin nauyi. Yabushe da dariya yace "kada nauyinta yadameki maganar dakika iya dauka nikuma sai ta gagreni ? Dubeni da kyau fa ummi. Ta jinjina kai. Yaci gaba da fadin "ummi tun lokacin dana ganki zuciyata take bala'in son ki, kina ta shareni kin ki ba ni hadin kai, kin sha walakantani a gaban yarana ina kyaleki, kowa na mamakin yadda naki tsayawa in dauki kwakwaran mataki akan ki, na san ke da kankikin san kina yaudarar kanki ne kina ganin kamar kinfi karfi na ne shiyasa ban dauki mataki akan ki ba, ba haka bane ummi da ace na yi niyyar rabaki da rayuwarki gaba daya da yanzu na gama dake, da ace na yi niyyar dauke ki in boye da yanzu na yi, amma dayake duk ba wannan manufar ce a zuciyata ba na sa miki ido duk dacewa kullum kwanar duniya azabtuwa nake da soyayyarki, Allah ne yasa min sonki a zuciyata ba tare da manufar komi ba face in aure ki, ban taba sha'awar auran diya mace ba sai ke, tun daga ran da na ganki sai naji kawai ina sha'awar ace na gina gda na ajiye matar aure nima ta haifa mini 'ya'ya yadda maza keyi sai gashi ban samu hadin kanki ba. Aka hasko fuskar ummi tayi murmushi tace "ba komi ka kwantar da hankalin ka yaya lokaci ya yi da za kasamu hadin kaina yadda kake bukata. Yace "Za ki aureni ummi ? Ta amsa "zan aureka in dai kai min wani aiki shi ne sharadin aurena da kai. Yace "wani irin aiki ne wanann ummi gaya min shi komi wahalar shi zanyi in dai zai sa ki aureni, aurenki shi ne cikar burin rayuwata a duniya, ba ni da bukatar komi domin na mallaki dukiya, mace sai wadda na zaba in yi amfani da ita, ke kadai ki ka tsaya mina zuciyata ba na son bata miki rai na fi son in aureki in zauna dake a matsayin mata ta, yanayi ne daban taba fuskanta ba a rayuwa ta. Unmi tace "wannan damuwa ta ka ta zo karshe in dai kayi min abinda nakeso zan mallaka ma kaina a matsayin matar aure. Yace "To fada min meye wannan aikin ko zan rasa raina zan miki. Tayi murmushi tace "Akwai wani mutum mai suna Abakar ana cemasa dr. khalifa. Shi nake so kawai ka kashe mini in dai khalifa yabar duniya kazo a daura mana aure. Yavushe da dariya mai karfi yace "shi knan ko da wanda za akashe bayan shi ? Ta Girgiza kai "shi kadai ne ba na son gani a duniya. Yace "an gama yaushe kike son a kashe shi ? Tace "A DARANSU NA FARKO da amaryarsa kuma ina so a kashe shi ne ta sigar da za ayi zaton ita amaryar ta sa ce takashe shi, in dai kayi min haka ka biya dukiyar auran ummi. Yasake bushewa da dariya yace "in dai kisan kaine ko ta wacce hanya mun iya ta sai dai in bamu sa kammu ba. To daga wannan shafin sai aka hasko dakin da aka kai fatima, fuskar ummi ce ta bayyana yaya na binta a baya tabude mai murfin kwaba yashiga. Sai kuma aka hasko ummi t shiga daya murfin kwabar ta rufe. A wani shafin kuma an hasko fuskar dr. khalifa ne ya bude kofar kwaban da yaya ke ciki, sai ga yayan ya fito tsulum ya tsaya gaban dr. khalifa cikin zafin nama yadamke masa baki ya hantsila shi kan gado yasa filo yadanne bakinsa. Sai aka hasko fuskar ummi ta fito ta maida murfin kwaba ta rufe ta hau kan gadon da karamar wuka a hannunta ta nunawa dr. khalifa daf da kunnansa takai bakinta tace "Ni ce ajalin ka. An hasko fuskar khalifa yanata wutsil wutsil bashi da damar magana. Sai kuma aka hasko yaya ya amshi wukar hannun ummi ya chakawa dr. khalifa sau biyu, sai suka fice daga dakin suka rufe kofar shi da ummi. Bayan wannan, Sai akaga fuskar yaya a zaune kan kujera unmi na gefensa yace "Aiki dai ya kammala kuma ya yi kyau ummi ya batun aurammu ? Ummi ta harareshi tace "wai kai meyasa ba ka da hankali. Yaya yazaro ido "Ni ne ba ni da hankali ummi ? Tace "To ina kaga hankali. Yayi murmushi yace "Ni kuwa nake da hankali. Ta girgiza kai tace "babu rashin hankalin daya wuce kace kai dinnan kanada hankali kai daman ka yarda zan aureka ? Ya kura mata ido yace "ummi ni kikawa haka ? kin san waye ni kuwa ? ki guje shiga cikin hadari. Tamike tsaye tace "shi yasa nace ba ka da hankali kamar ni in rasa wa zan aura sai dan ta'adda, ko ka manta kai dan ta'adda ne, ka gaggauta fiddani daga zuciyarka domin bazaka taba samuna ba. Yayan yamike tsaye yanuna ta da yatsa yace "kin yi babban kuskure ummi sai kinyi da na sani da kika mini domin baki yaudareni ba illa kanki. Ta kyalkyale da dariya tace "yaya ba zan yi da na sani ba har abada domin ka mini aikina dr. khalifa dai ya mutu kuma ba zai dawo ba buri na knan yadda na rasa shi kowa ma yarasa ka ga zancan nadama ma gareni bai taso ba, in kuma za ka kashe shi ne to bismilla. Yace "Ba zan kashe ki ba sbda na yi alkawarin ba zan kashe ki ba ummi amma xan ba ki mamaki daman jikina ya ba ni za ki yi min wannan butulcin shi yasa na shiryawa hakan, kin z hannu ummi. Daga wannan ranar ba za ki kara yaudarar wani a duniya ba, idan ma kin ci gaba da rayuwa ni daman nawa ta kare. Iya abinda memorin ya kunsa knan TV tayi dif kamar yadda kotun tayi shiru kamar ba kowa duk da yadda tacika makil da mutane, abin mamaki har yanzu kan ummi na kasa bata dago ba. Bayan wani dan lokaci mai shari'a yadago kansa bayan ya ajiye biron da yake rubutu yace. "Kotu ta gamsu da bayanan da jidda tazo dashi tare da hujjojin dakowa yagani a zahiri, don haka ba tareda bata lokaci ba nan take wannan kotu ta sallami fatima kuma ta bada umarnin a kawo ummi da wanda yakashe khalifa, shari'a ta dawo kansu wannan yakawo karshen zargin da akewa fatima na kisan mjinta Dr. Abubakar Saddiku a bisa kwararan hujjoji na shari'a. A DAREN FARKO 38 Karfe takwas na dare agogo ya nuna, malam musa mahaifin su fatima na zaune kan tabarma da rediyo gefensa yana jin shirin iya ruwa fidda kai da akeyi gdan rediyon kano. Inna tafito daga dakinta tazauna dab da shi tce "malam ni fa lamarin nan na fatima ya dameni. Yarage sautin rediyon idanunsa na kanta yana mata kallon rashin fahimta yace "me kuma yafru ? Tace "ka ga yau satin ta biyu da fitowa daga kurkukun nan amma har yanzu ta ki daina kuka idan an tmbayeta sai tace wai babu komi, ni abin nata har ya fara ba ni tsoro. Malam yace "kira min ita. Ta kwalawa fatima kira tafito a sanyaye ta tsuguna a gefe yace "Haba fatima wannan kukan da kike yana nuna cewa tamkar ba ki ki yarda da kaddara bane shi duk abinda Allah ya hukuntawa bawansa va makawa sai ya faru, godiya ya kamata muyi wa Allah daya takaita mana al'amarin ya tsaya a haka, addu'ar da muke yi ce tayi tasiri da karshen al'amarin yazo, ko meye na tsananta damuwa, tunda kika fito daga kurkuku kike kuka kin ki cin abinci isashe, kin ki magana kin daina barci isashe to yaya kike son mi miki ? Fatima tayi ta yi tahadiyi kukan dake makale a idanunta ta kasa ta dora kanta a guiwarta hawaye suka dinga ambaliya a fuskarta, tace "kuyi hakuri baba wallahi ina jin ciwon damuwarku sakamakon damuwar da nake ciki wadda tayi sanadin damuwarku ban san yadda zanyi indaina kuka ba tabbas da na daina amma ba yadda zanyi nima ban san lokacin da nake kukan ba, zuciyata ce ba za ta iya jurewa abubuwan dasuka faru ba, ina cikin bakin ciki da damuwar abinda ummi tayi min nakasa sabawa da damuwar rashin khalifa, ummi bata yi min adalci ba da tasa aka kashe khalifa na san tana sonsa amma ita tanuna min ta hakura dashi ta gaya min cewa idan bai aureta ba kashe zhi za tayi da..... Malam ya katseta yace "Fatima khalifa ya rsu kuma ba zai taba dawowa ba har abada, tunda aka halicci duniya bbu wanda yataba dawowa bayan ya mutu haka khalifa ma ba zai dawoba, kin g kuwa idan hakane babu amfanin aci gaba da tattaunawa da maganar, zai fi kyau miyi hakuri, wannan al'amarin daya faru mu barshi a matsayin kaddara, Dr. khalifa babu abunda za muyi masa illa addu'a, Allah yaji kansa yakai rahama kabarin sa, kuka da zaman damuwa ba zai sa yadawo ba kuma ba zai goge abin da ummi tayi ba, da ace zai goge ko yadawo mana da khalifa da sai ai tayi, kiyi hakuri Allah yabaki wani mijin. ***** Tun a lokacin da kotu tagama yanke hukunci ummi tafadi bata kara sanin inda kanta yake ba, a bisa dole aka kaita asibiti tun tana numfashi har ya kaance ba ta iya numfashi da kanta sai da taimakon oxygen. Kowa sai Allah wadai abinda ta aikata akeyi tare da mamai mai tsanani, abinda yafi zama abin mamaki shi ne yadda ummi ta tayar da hankalin ta bayan mutuwar khalifa, ta fi kowa nuna damuwarta akan mutuwar ta sa, tunda aka binne dr. khalifa ummi take kuka ta rasa sukuni, kullum ckin zirga zirgar masu taimakon ta don fidda fatima daga zargi tare da binciko wanda yayi wa khalifa kisan gilla, abin mamaki wai itace ummul haba isin kisan, wannan shi ne a na zatom wuta a makera sai ga ta a msaka. Hakika fatima ta ba ma kowa mamaki ta bar ma mutane abin tattaunawa kowa na fadin albarkacin bakinsa ciki dai har da iyayan ita kanta ummin ballantana wadanda suka haifi khalifa, mama ita ke tare da ummi kullum tun kashe dr. khalifa har yau ita tafi kowa sanin damuwar da ummi ke ciki da irin kukan da takeyi a lokuta da dama ita maman ce ke lallashin ummi amma ckin wani irin yanayi ya bayyana cewa ummi ce ta kashe wanda take kokawa mutuwarsa kukan da batayi ba a lokacin da mahaifin ta yarasu, abin tambayar anan shi ne shin me yasa ummi take kukan mutuwar khalifa ? bayan ita takashe shi, sbda bata son rayuwarsa a doron kasa a bisa gurguwar hujja wai don ta rasa shi kowa ma sai dai yarasa idan akace don ta yaudari mutane take wannan kuka tana zargin daman asirin ta zai tonu ne, kokuma ta yi abin ne don ya dameta, shiyasa take kokawa kanta don ta san ta yi babban kuskure da ganganci a rayuwarta. To koma dai meye Allah kadai yasan dalilin kukan ummi bayan kisan datasa aka yiwa dr. khalifa da kanta. Ga ta nan dai a bisa gadon asibiti batasan inda kanta yake ba, karkashin kulawan jami'an tsaro, likitoci sun bada sakamakon binciken dasukayi akan ummi cewa damuwa tasa tashiga wannan halin, akwai yiwuwar tadawo normal akwai yiwuwar tarasa ranta, sbda tsananin damuwar datake ciki yayi yawa. Mahaifiyarta hajiya hauwa ce me jinyarta, hankalinta a tashe sosai yake sbda yadda ake yayata labarin a kafafen yada labarai na jihar har da makota, tayi kuka ta yi kuka har ta ba uku lada, ba a barin kowa ganin ummi sai dai tasa ummin a gaba tana kuka, tunda aka kawo ummi bata taba farkawa ba, numfashinta yahau ya sauka sai dai wani lokacin tana motsawa kamar za ta farka sai kuma tacigaba da barcin da in barda ana ganin numfashinta sai kace ta mutu ,kunyar mutane yasa hajiya hauwa ba ta iya fita ko ina batasan yadda za ayi ta iya hada ido da iyayan khalifa ba, dansu kwaya daya ummi ta yi sanadiyar barinsa duniya sbda wani hujjarta mara tushe ballantana makama. Tuni dai yan sanda sun sami nasarar chafke matashin nan me suna yaya wanda ya tabbatar shi yakashe dr. khalifa da hannunsa a bisa umarnin ummi, bai wahalar da shari'a ba ya amsa laifin sa har yayi magana da yan jaridu cewa ai dama kawo kansa hukuma ne kawai bai yi ba amma zaman jiran kamu yake tunda shi da kansa ya bayyanawa duniya ta yadda al'amarin yakasance kuma yabari aka ga fuskarsa to ai ya yi talla da laifinsa knan. A gdansu khalifa abin ya zamo tamkar na jajantawa yadda jama'a suka dinga ta zuwa bayan 'yan jaridu dake zuwa neman labari, Abba na iya magana da 'yan jarida ita kam mama wannan al'amari ya dawo mata da mutuwar khalifa sabo fil a zuciyarta, tayi kuka ta yi kuka kukan da bata taba irinsa ba a rayuwarta, jama'a na bata hakuri tana fadin, "ku kyaleni in yi kuka abin kukan ne ya sa mun, ummi ta cuci kanta me yasa ta hau dokin zuciya. Wasa wasa lamarin mama tadaina barci tsabar takaici ne fal a zuciyarta, dan na su kwara daya shi ne don masifa sai da aka salwantar. Wannan daran ma zama tayi daram a dakin abba tazuba tagumi tana kallonsa yana barci ita kuwa ta kasa tayi juyi ta yi juyin shiru, ta gaji ta tashi tazauna hawaye wani na bin wani, tadunga tuno yadda al'amrin yakasance bayanmutuwar khalifa. A DAREN FARKO 39 UMMI takan zauna tana kuka kamar ranta zai fita, watarana mama ta isketa a zau? e a harabar gdan tana sana'ar ta ta, mama tace "ummi ya ya kika fito nan kina kuka? kowa yana kallonki duk kukan na ki ya wuce ckin gida sai kinzo waje. Ummi tace "mama wai ba ni da dalilin kuka ne? duk wanda yashigo gdan nan abin mamaki ne don ya ganni ina kuka? Wallahi mama tun daga ranar da aka sa khalifa a kabari har yau har nima in mutu ba zan daina kuka ba. Mama tace "haba ummi a matsayimmu na musulmi dole mu dogara ga Allah a bisa kaddarar da Allah yadora mana, ni ce fa na haifi khalifa wa ya fini sanin ciwon sa? a cikina ya rayu nayi nakudarsa na raine shi, bbu wanda zai nuna min son khalifa tunda na hakura na karbi kaddara ya dace kema kiyi hakuri. Ummi tadago jajayen idanunta tadubi mama tace "na san da haka mama amma kin san wani abu daya, kuna kukan rashin khalifa ne don ku kuka haife shi nikuwa kukan danake daban ne da zan iya bayyana miki wani gagarumin sirrin dake zuciyata da daga yau na san ba za ki kara cewa indaina kuka ba mama. A wan? lokacin da ummi ta fadwa mama wannan magana babu abunda tasa a ranta face sirrin da ummi ke nufi bai wuce na soyayyar da take wa khalifa ba. Abba dake ta barci yamike zaune kamar an tashe shi ya zubawa mama ido yace "maijidda wanan tunanin zai ci gaba da hanaki barci a kowane dare idan har ba za kiyi hakuri ba. Mama tafashe da kuka tace "Alhaji ta yaya tunani da damuwa za su fita daga xuciyata, wane irin bakin ciki ne wannan? Yace "kiyi hakuri Allah ne yakaddara kwanan khalifa ya kare shiyasa suka samu nasarar kashe shi, kuma da sukayi hakan meye meye ribar da suka samu banda faduwa, tunda aka kai khalifa kabari ummi bata sake samun natsuwa ba babu abunda yaja mata hakan face hakki, haka shima wanda tasa yayi kisan hakki ne yasa ya tonawa kansa asiri da kansa. To kinga lah za muyi wa godiya muyiwa khalifa addu'a . ***** Jiddah ce tadaga labulen dakin inna tare da sallama, inna ta fadada fara'arta tace "maijidda ke ce tafe da yamman nan, daga ina? zauna ga kujera nan. Bayan sun gaisa tace ina fati;a? Inna tace "Tana daki shiga. Ganin fati a kwance yasa tabata rai tace "wai don Allah fatima sai yaushe za ki kwantar da hankalin ki ki dinga walwala? dubi yadda kika rame kika yi duhu kullum idanuwan ki ckin zubar hawaye har sun zama jajaye fati me yai zafi haka? Fatima tamike zaune tace "jiddah duk wadannan abubuwan dakuke ganin laifina da rashin dauriya na kune baku san ina dauriya akan su ba, jiddah tun da nake rayuwa a duniya ban taba kwatanta so ba sai akan khalifa, ko da cewa a baya na yi niyyar auran musbahu na ami? ce ne sbda da darajar iyayena amma ko sau daya ban taba jin digon soyayyarsa a zuciyata ba, ni kadai nasan asarar dana tafka wadda ba za ta taba mayar da ko da kwatankwacin mijina ba ballantana fa daidai dashi . Jidda tadafa mata kafada tace "kiyi hakuri yadda Allah yabaki khalifa ya amsa abinsa haka zai musanya miki da wanda zuciyarki za taso, lamarin na ubangiji ne babu abunda zai fi karfinsa in dai bawa zai dogara dashi to ya isar masa. Fati tace "jidda har ban san kalaman da zan yi amfani dasu gun gode miki ba, kin yi namijin kokari a gareni Allah yayi miki sakayya da mafificin alherin sa na duniya da lahira. Jidda tace "fatima godiyar nan ta isa na gamsu Allah shi ne abin godiya daya nufeni da in yi hakan da bai ba ni iko ba ban isa in yi ba, yanzu wata alfarma nake son ki yi min. Fati tace "ki fada jidda ko mene zan miki in dai xan iya, kin fi karfin komi a gareni. Jidda tace "sanin hakan danayi shiyasa nazo, a safiyar yau din nan ne mahaifiyar ummi taxo tana rokona in taimaka in zo in roke ki ki je asibitin da ummi ke kwance ki dubata domin ta farfado amma tana ta kuka tana rokon a kawo mata ke da iyayan dr. khalifa za ta fada maku wata maganar, dafarko nace da hajiya babu ruwana sai nagata kama kuka tana rokon in taimaketa tace wllhi jidda nima ba laifina bane ba ni da masaniya ko ta kusa ko nesa game da abinda ummi ta aikata,. Fatima ta jinjina lamarin sosai a ranta, yanzu kam a duniya ba ta da makiyin daya wuce unmi, ji tayi kamar za ta hadiyi zuciya ta mutu sbda bakin ciki me za tayi da wadda tarabata da masoyinta, kai hakika ummi ta gama cutar ta har me za ta gaya mata. Babu yadda ta iya da jidda tana ganin kimarta da yawa don haka ya amsa mata cewa za ta, ta sanar dainna da malam suka mata izinin zuwa, dogon hijjabinta me hannu da nikab tasa ravon ta da fitowa waje tun ranar da aka sallamo ta daga kurkuku, hawaye suka dinga zuba daga idonta har suka iso asibitin., a lokacin taga mama suma suka iso su biyu jidda takira hajiyar ummi a waya tace dasu sun zo tafito tashiga dasu dakin da ummin take. Duk yadda zuciyarsu ke cike da tsanar ummi da bakin ciki sai da jikinsu yai sanyi, sakamakon yadda suka ga ummi ta yi wata muguwar rama kamar an sauya ta, ta yi baki ta fita daga hayyacinta, babu wanda yazauna sun kame ne suna kallonta. Ummi ckin rawar murya hawaye wasu na bin wasu tace "Abba, mama, fatima na gode kwarai da kuka danni zuciyarku kuka zo nan, na bukaci zuwanku ne don kuga halin danake ciki kafin Allah yakarbi rayuwata, domin ni tawa ta kare ba zan kai labari ba ba kuma so nake ku tausaya min ba don ni ba abin tausayi bace, kuyi hakuri masu karatu a littafin babu page 47-51 Kwanan ummi goma sha shida a gadon asibiti karkashin kulawar lokitoci da jami'an tsaro tarasu, bayan aman jini ta hanci da baki data yini tanayi saita dinga sai tadinga zabura tana gwara kanta da bango tana ihu, "Na cuci kaina, shi ne kadai abi? da bakinta yake furtawa har tadaina numfashi, lokacin da labarin mutuwarta yazo kunnan fatima ta yi kuka

Chapter 17 of 19