Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokacin da xan iya zama in miki maganganu makamantar wannan ba sbda kallon ki nake kamar kanwar damuka fito ciki daya. Shi yasa nayi ta jinjinawa yadda zaman aure zai kasance tsakanina dake. To amma a safiyar yau abokina mansur yasauya min tunani akanki ya ce dani 'tunda aure bai haramta tsakanin ka da fatima ba ba yadda za ai kunya tahana muku nishadantar da zuciyarku ta hanyar soyayya, shi aure dakuke gani ba bu abinda yake rike shi yazauna lfya sai soyayya. Ya jawo abinci yakama ci yana cewa "fatima har na rasa dawata kalma zanyi amfani a bakina kan yiwa Allah godiya daya azurtani da mace kamarki, fatima in sonki wlh don Allah ni ma ki ce kina so na inji dad'i. Bai aune sai kawai yaga ta tashi ta faki idonsa ta fice daga dakin a guje ya kyslkyale da darya har da tafa hannu yace Allahu akbar, fati manya shi abinda yake ba shi mamaki shi ne wai an wayi gari shi da fatima sun zamo masoya soyayya kuma irin ta aure. Tabbas Allah ya amshi ran mahaifinsa ya zamo maraya sai dai shi maraya ne wanda yai rashin mahaifa amma ba wanda yarasa iyaye ba, a rayuwa iyaye suna da daya wa mahaifa ne kwara d'aya kachal, shi kam Allah yai masa baiwa da iyaye nagari yagirgiza kai yana murmushi. ****************wannan page goron jumma'a ne gareku ba ki d'aya,,,, daga jiddan nan dai 'yar mutan A DAREN FARKO 9 karfe goma da minti hamsin hajiya saudat ta faka motarta a kofar gdansu ummi, ta sha ado da wata galleliyar shadda maroon colour, ta yi kyau kasancewar su kam Allah ya hore musu kyau da son gayu. ita mijinta ba wani mai wadatar zuciya bane sosai kusan itace mai kudin don yar kasuwa ce, daga kasar dubai ake kawo mata kayan sa wa na mata, koyaushe gdan ta cike yake da mata business takeyi ko ta ina. Ita kam Alhaji muhammad ne asalin ba ta jari amma duk da haka ba sa gani. Taahigo uwar dakin hajiya hauwa tana kwance kan gado ummi na kwance gefenta zancen khalifan dai suke, saude tace "kitashi mana tun yanzu kifara shirya kayanki don da kaina yau zan kaiki gdan alhaji muhammadu chan za ki zauna ni zan xan gaya masa cewa tunda Allah yayiwa mahaifinku rasuwa ya zama dole a tallafa yaya hauwa a gun rikonku, na san dai idonsa da kunya ba zaice ba za ki zauna mai a gda ba sannan ita hajiya maijidda na san za tai farin cikin xaman ki a gdanta, don za ta ga cewa haka zaisa tasamu fada a gunmu ke Kuma idan kinje ba cewa akayi kisaki jiki kina bacci ba, yakin neman zuciyar khalifa za kiyi ko ta halin kaka sannan ki dage dun kyautatawa uwarsa, yin haka ne zai sa in yadawo daga germany ko bai sonki da kansa ita za takalli kyautatawar da kike mata ta tursasa shi ya aureki, kin san son uwa shi ne son d'a, Hajiya hauwa tace "wannan shi ne hanya mafi dacewa. Zuciyar ummi fari kal san da tagama sanya kayanta suka nufi gdansu khalifa, . A bisa hanya hajiya sauda atana ta wassafa mata yadda za tai amfani da damarta duk san da take dashi don jan hnkalinsa. Ummi jin ta kawai tana dura mata a zuciyarta, daga alhajin har hajiya maijidda sun nuna jin dadin zaman ummi a gdan daman fada ne ba na so nayi a samu matsala in ba haka ba in ba haka ba idan hauwa da duk yaranta sukace za su zauna a gdan nn, rikesu xan iya insha Allahu. Daki guda aka warewa ummi a gdansu khalifa kusa da na mama, akwai gado da dressing mirror da toilet acikin dakin, tun a ranar da taje gdan aka gama wannan mama maijidda tace da ita '"gdan nan gdanku ne kin sani ki dauki kanki fiye da yadda kike rayuwa a gdan iyayanki, duk abinda kkeso akwai su idan ma babu kada kigawa kowa kigaya min in har da kudi za a siye shi zan saya miki ummi. Batazo gdan nan dan cutar da khalifa ko iyayansa ba dan haka za ta nemi soyayyar khalifa a bisa hanya ta gaskiya da tsakani ga Allah. Ta tashi tabude kofar sakamakon kwankwasawar dataji ana yi, daya daaga ckin yan matan dake aiki ne tace da ita, "Mama ta ce in zo in ce miki an gama sanya abinci a tebur kifito kici. Ummi tace "ki ce ina zuwa. Har yar aikin ta tafi ta kirata tace "meye aikinki agdan nan? Tace wanke wanke wani lokaci ina yin girki. Ta jinjina kai tace "wa ye yakedafa abincin da yaya khalifa yake ci? Tace"yana da kyankyami bai yarda da abincin mu ba shi da abbansa mama ke dafa musu abinci sai dai mu tayasu shirya tebur kawai Tace "yanzu ya dawo? Tace "eh yana falon dasuke cin abinci shi da iyayansa. Cikin zumudi ummi takoma daki gaban katon madubi ta tsaya tana kallon surar jikinta, daga sama har kasa tana tmbayar kanta shin tana da tagomashin da zata iya jan hnkalin namiji kamar khalifa? Tafito falo cikin yauki khslifa yana zaune kusa da abansa kan kujerar zaman mutum uku sanye yake da bakar kot, da wandonsu. Zahiri da badini khalifa ya yi kyau ba na wasa ba kamar yadda yake kyau a idon kowacce mace ballantana ummi data mutu acikin soyayyarsa. Ta gaidasu gaba daya, kallo daya shi ma khalifan yayi mata yamaida kansa ga jaridar da yake dubawa kafarsa daya tana kan daya, mama ce tace dashi khalifa ga kanwar ka nan ummi ta dawo gdan nan da zama. A nan ne yadan ajiye jaridar akan cinyarsa yakalli ummi suka hada ido yayi mata murmushi takaitacce yamaida ganinsa ga mama yace "ya yi dai dai hakan kinga kin samu mai tayaki zama. Tsigar jikin ummi yadinga tashi sakamakon murmushin khalifa da ta gani kuma ita yayiwa murmushin. Karfe taran dare khalifa yatashi yawuce dakinsa ya kara yin wanka yasauya zuwa blue din jeans da farar t shirt yazuba wani mai tsadar takalmi ga farin gilash dan siriri ya manna ya fesa turare yadawo falon da iyayansa ke zaune yarusuna daf da abbansa yace"abba ba ni aron makullin motarka za ni unguwa in dawo. Ba musu yazaro key din ya damka masa yakalli mama yace "mom sai na dawo. Ta sha kunu sosai tace ina za ka a wannan daren? Yadubi agogo yace "mom wani abokina zan duba a asibiti da asubahi za a tafi dashi egypt. Tarasa abinda za tace sai kallo tabisa dashi har yafice kamar yadda itama ummi ta lalace kan kallon sa. Tabdijam ashe jan aiki ne a gabanta ********** Khalifa bai dawo ba sai biyu da rabi na dare, yana shiga dakinsa yafada bisa gado bacci yai awon gaba dashi . Da sassafe ummi tariga kowa tashi agdan tayi wanka tatsala ado za tashiga kitchen sa'ar da tayi ita gwanar iya girki ce da kwalliya ta yi cos din wadannan abubuwa guda biyu a gun hajiyarta. Mama tafito wurin karfe bakwai d rabi tana shirin hadawa abban kayan tea sbda fitar da zaiyi dawuri, sai taji kamshin girki ya game dakin. tashiga kitchen suka hada ido da ummi tarike baki tana murmushi tace 'oh sannu da himma ummi irin wannan kamshi hka? Ummi tatsuguna tana murmushi tagaida tace "ummi ke za kidinga girki a gdan nan, girki ba zai hanaki bacci ba a lkcn da kowa ke hutawa ko yan aikin nan a yanxu haka suna chan suna bacci idan ba abban ne zai fita da wuri ba sai karfe gomaake gama abinci sannan aci. Ummi tace "mama ai daga wannan rana dana dawo gdan nan da zama insha Allahu ruwan shayi ba za ki sake dafawa da kanki ba sai fa in ba na nan, kuma yau ma na tashi da wuri ne jin abban ya ce zai fita dawuri. Mama tagyada kai tace "ya yi kyau lallai na san za ku shirya da yayanki khalifa don yana son abinci mai dadi. Gabanta yadan fadi tayi murmushi kawai. A kwanaki shida da ummi tayi a gdan kafin tafiyarsa germany sai da tayi kokarin da khalifa yake kulata a kalla yana amsa mata gaisuwa cikin fara'a har yakan ja ta da magana a wasu lokutan. Ranar laraba da asuba ta kama tafiyar khalifa germany a daran talata bai shigo ba sai sha biyun dare yan can wurin abokansa da yamatansa da sunan sallama. Mama tana zaune a dakinta ita kadai bayan ta idar da sallar shafa'i da wutiri da casbi a hannunta, ummi tashigo da food flask a hannunta tatsuguna gaban mama tace "mama yaya khalifa ya ce amala yau yakeso da miyar kubewa ya ce a gama da wuri, na yi masa tun magriba ga shi har yanzu bai dawo ba. Mama tace "na yi zaton ma kinyi bacci dama tun dazu kina falo jiran khalifa? lallai baki san gararin khalifa ba, idan yaga dama in yazo yaci idan baiga dama ba cikinsa. Tace "mama ko dai injira in ya ce bazai iya ci va ya yi sanyi in dafa mai wani abun. Mama tace "habadae sai kace kin zamo baiwarsa, tashi ki mayar da abincin falo kitafi ki kwanta. Ummi tadawo da flask falo maimakon taje takwanta sai ta zauna tayi tagumi a daidai wannan lokaci shi khalifa na daki tare da ramcy a yau ta kare mai gida taviyo shi har gdan ubansa, kamar yadda tasha gaya masa ta ce "duk abinda zai faru in dai a kaina ne ta dauka ba gudu ba ja da baya. Khalifa ya rasa yadda zaiyi da ramcy yau ta rikice msa yini guda yayi a gidanta tun safe har dare bata barshi ya motsa ba amma da dare yayi bai san yaya akayi ba har ta biyo shi a motarta ba, sbda shi kansa a yau ckin natsuwa yake sbda alhinin rabuwa da gda ba wasa bane tun safe jikinsa yake a sanyaye dan hka yinin dayayi a gdanta ma ba abinda ya iya aikatawa sai kwanciya tana kallonsa kawai. Sa'ar da yayi shi ne lokacin da zata biyo shi ta yi shigar mutumci ta sa dogon hijjabi mai hannu har kasa yana shiga da motarsa itama tasa tata motar mai gadi zai mata hayaniya kasancewar dare yayi kuma bai taba ganin motar a gdan ba khalifa yace yakyaleta bakuwarsa ce. Suna shiga daki yarufe ta da bala'i yace "ni za ki walakanta haka? baki san uwata da ubana suna gdannan ba? me kike son a daukeni dakika biyoni, toh abinda xan gaya miki shi ne na barki kin shigo nan dakinnan ne don kar inyi hayaniya dake a waje wanda bai san abinda ake ciki ma ba yasani, ki tashi kikoma inda kika fito... Sai tayi wuf takamoshi tarungumeshi kam kam tana masa kiss, wannan ne dalilin dayasa khalifa ba ya hada ramcy da wata dan wata hanya ta kan shawo kan namiji ta sani komi fushin da yayi kuwa, tace "khalifa me na rasa ne? meye mahaifina bazai iya mallaka min ba a rayuwa? sai kai kai ne kadai mahaifina bai da ikon yamallaka min sbda kudi bazai siye ka ba to yaya zanyi da raina khalifa? Jikin khalifa yayi sanyi kwarai da gaske bai taba tausayin wata diya mace irin yau ba, musamman yadda take me kuka da hawaye. Dai dai wannan lokaci ummi ta gaji da zama a falo tana takaicin ace khalifa bai ci wannan abincin ba yadda tzauna ta tsara shi hakan yasa ta kasa juriyar tafiya ta kwanta ta zuba abincin ta jera a plate tanufi dakinsa tunaninta shi ne tabar masa a dakin nasa tunda tana da makullin dakin shi da kansa yabata sbda yanajin dadin yadda take gyara masa komi a dakin a tsaftace. Tana isa kofar dakin tasa makulli ta bude, abinda tagani yasa gabanta mugun fadi, yaya khalifa rungumeda mce tana sanye da hijjabinta, bayan Runguma ba wani mummunan abu da ummi tagani amma duk da haka sai da abincin hannunta yasubuce ya tarwatse a gun takoma ckin gida da gudu tana haki, wani abin takaicin tahadu da mama a falo za ta sashen abba. Gaban mama yafadi tatsare ummi da tambaya, hnklin ummi yatashi tarasa abinda za tace wani karya za tawa mama, mama tawuce tabarta jiki na tsuma. Khalifa ture ramcy yayi yace shkan hnklinki ya kwanta kin tona min asiria gdan mu ko? Za tayi magana yadaka mata tsawa yace, "kawai kifita idan kikaci gaba da tsayuwa anan komi zai iya faruwa dake tunda asirina ya tonu ba na fargabar komi dn haka kama gabanki. ******** Karfwme dayan dare tayi khalifa ya kasa runtsawa, ganin da umi tai masa rungume da mace ya tayar mai da hnkli matuka bai san wani irin kallo yarinyar za ta ci Gaba da yi masa ba a yadda take ba shi girma shknan ta daina ganinsa da kima bayan wannan za ta iya gayawa mama daga nan maman za ta iyasa wa ai masa aure da diyar da maman ke son ya aura itace 'yar aminiyarta mai suna ummi. Yamike cikin tsananin mutuwar jiki cikin sanda ya kwankwasa dakin ummi a hnkli ya san dai da wahala su abba su ji. ummi tamike ckin tsoro tace waye? A hankali yace ni ne khalifa, dasauri tamike ko kayan bacci yau bata sa ba, kayan jikinta ne hijjabin datayi sallah, ta tsaya jikin bango tana kallonsa, cikin kakkausar murya ta jaruman maza yatsare ta da idanunsa. A wannn lokaci hnkalin ummi yai matukar tashi yace "ummi Murya na rawa ta amsa yace me ya kaiki dakina dazun? Tace abinci kawai naje kai maka na ga ka jima baka dawo ba ni kuma ba na so yakasance baka ci abinci ba sbda tun azahar na shiga kitchen nahda maka shi. Ya danna mata harra kamar zai shaketa yace 'damaa a dakina nasaba cin abincin? Sai dai na zo ne dan in gargadeki dan kisani kada wani yaji kinga wata mace a dakina. Idan kuma naji ko da wasa wani ya furta ta ko shakka babu na san ke kika fada, saiki saurari matakin dazan dauka wanda ba zai taba yimiki dadi ba. Sannan maganar soyayya tsakani na dake bbu, ni ba sa'anki bane, idan naji kince da mama ko abba ko wani cewa kina sona xa kisha mamakin matakin dazan dauka akanki, idan wannan ce gulmar da kika dakko kikazo gdan nan da ita sbda ni to kikoma don ba xa kiyi nasara ba, yaja tsaki cikin hushi yafice daga dakin. ******* Tabdijam su duka biyun bbu wanda yayi bacci a wannan dare, abinda yadaga hnkalin kowa daban kowa tunaninsa daban. Bayan fitar khalifa ummi tatashi ckin tashin hnkali tayi kuka kamar ranta zai fita tadubi agogo karfe biyu da minti ashirin bata ga nisan dare ba takitra mahaifiyr ta a wannan dare tana kuka wayar a kashe, hajiya sauda itama a kashe, takira babbar aminiyarta jiddh bata kashe waya ba, jiddah tadauka a figice tana fadin "inalillahi wa inna ilaihir raji'un. tadaga wayar abinda tace shi ne "ummi waye yamutu? Musanman kukan dataji ummin na rusawa kamar ranta zai fita, tace ni ce na mutu jiddah mesa kuka ban kwarin guiwar in so wanda ba zai so ni ba? Jiddah tayi ajiyar zuciya tace "ummi yau kwananki nawa a gdansu khalifa? Tace "shidda. Ta j tsaki tace "gaya min abinda yasa kika kira kanki matacciya gashi kina raye. Cikin sanyin murya ummi tabayyanawa jidda abubuwan dasuka fru a wannan daren, jiddah tace "kin ban kunya da hushi ummi kuma kin kashe kanki a wurin khalifa. jiddah tace "ummi ita nasara tare suj tafiya da hakuri, tunda khalifa tafiya zaiyi abu daya yarage miki shi ne kiyi kokarin yin abinda zai matukar ba shi tausayi tyadda idan yaje jamus abin zai tsaya masa a rai, . Khalifa na sanye da bakar kot ya tsuke sosai fuskar nan ba fara'a ya sha kunu, mama tana dakinta ko fita batayi ba, ummi ta bishi dasauri ta tsaya daga baya a langabar da kanta a jikin bango tana kallon khalifa yana taku dai dai. Lokacin dazai shiga motar ne ya waiwayo sai karaf kuwa suka hada ido da ummi, sai yayi cak yana kallonta bai shiga motar bazuciyarsa tashiga harba wa, ganin haka sai ummi tadaga hannu sama da nufin tana masa addu'a kuma tashiga yi masa bai bai da hannu tashiga ckin gda da gudu. Khalifa yafada mota abbansa na kusa dashi direbansu yahaya yaja motar zuciyar khalifa ba dadi abubuwa da dama suka cunkushe masa a zuciya. Tausayin ummi suka kamashi har suka isa filin jirgin saman malam Aminu kano hannunsa biyu tallafe a kumatunsa, abubuwa da dama suka tsaya mai a rai, abokansa da yammatansa ba wanda bai nunawa tsananin damuwa ba ama ba wanda yatsaya mai a rai irin ummi. Ya kwana yanajin zafinta a ransa a tunaninsa ma yarinya karama dako secondary bata gama ba tatsaya gaban namiji tace tana sonsa. Lokacin dazai shiga jirgi yarike hannun mahaifinsa yace "abba kayi min addu'a zan bar kasar nan cike da kewarku zuciyata ba dadi. Abban yarufe me baki yace "a duk lkcin da mutum zaiyi tfya abinda yake tsirga mishi shi ne abinda yafaru lkcn rabuwarku. Kamar yau danazo maka rakiya insha Allah kamar yau xanzo taryarka in dai muna raye. Kazauna da kowa lfya kaji tsoron Allah gun muamularka da mutane sannan kariki gskiya da amana ba za ka tabe ba kuma ba za kayi asara ba insha Allahu Duk dauriyar xuciya irin na namiji khalifa sai da yashiga jirgi yana goge hawaye abbansa yabishi da kallo yana murmushi A DAREN FARKO 10 Ummi tagyara zama tare da jan dogon numfashi tace "jiddah khalifa ya tafi ba tare da na amfana da zaman da nayi a cikin gdansu ba, face bacin rai da mugun gani da idanuwa na suka gani. Jiddah tabata rai tana yimata wani irin kallo tace "wai me yasa kika fiye gaggawa ne ummi, anya za ki rinka cimma nasara a kan abubuwa, idan kika dubi tsarin khalifa gaba daya da yadda kike ba abu ne mai sauki ba mallakar zuciyarsa sai anyi da gasken gaske. Ummi tace "to in banda abinki jiddah tawace hanya zan samu nasara idan nayi hakuri, kada kimanta fa shekaru hudu khalifa zaiyi a germany kafin yadawo kasar nan, yana chan Ina nan zan iya jan hankalinsa jiddah, dole xuciyata takaraya, ke bari in gaya miki wani abu daya da ban yi zaton zan gayawa wani ba, ina cikin gdan nan fa ina kokarin jan hankalinsa na ganshi da mace rungume a jikinsa a dakinsa, idan zan iya jan ra'ayinsa zai kawo mace gdan nan ina cikinsa? Jidda ta ja dogon tsaki tace "daman kina tsammanin ko khalifa a karan kansa yake sonki za ki rabashi da yammata ne, namiji irin khalifa ko baice yana son 'yanmata, za su yi tabinshi tun bai kula ba watarana sai ya kula, don hakama shawarar da zan ba ki itace idan kinyi nasarar mallakar khalifa to ki sanya hakuri mai yawa a zuciyarki akan 'yanmatan da za suyi ta bibiyar khalifa don ba namijin mace daya bane. Ummi tajinjina kai tace "tabdijam hakika zan girgiza kowa a kan khalifa ba zan hada miji da wata ba, ba zan yi tarayya da wata macen a dakin khalifa ba. Jiddah takyalkyale da dariya tace "ummi manya har khalifan ya zo hannu da za ki wannan cika bakin. Ta lumshe ido tace "kuma fa hakane maganar dakika fada ne naji kamar har na mallake shi na ji tsananin takaicin hadashi da wata da zanyi a sunan kishiya . ************* Malam musbahu yana cigaba da karfafa zuciyarsa ga kaunar fatima tare da tattalin farin cikinta sai dai ba ya samun hadin kanta sbda tsananin kunyarta, ba ta iya sakewa dashi hakan yasa tadaina sakewa a gidan duk abinda take idan yashigo sai taji kamar za ta nutse a kasa don kunya hakan na takura shi shima don ya fi son tasaki ranta auyi soyayyar da za su fahinci juna kafin lokacin auransu. Ranar laraba da safe inna ta tursasawa fatima kaiwa musbahu abincinsa a kokarin innar na ganin sun shaku ta fuskar soyayya kamar yadda tafahimci basu sake da junansu ba, fatima ba ta son shiga dakin musbahu sbda maganar soyayya da yake mata na daga mata hankali alhali bata saba ba. ********** Lafiya kalau khalifa yasauka a kasar germany inda zai zaman karatun likita ,har yanzu damuwar daya taho da ita daga nigeria yana makale a ransa ga kewar iyayansa tamkar bai taba tafiya ba sai a wannan lokacin, yana shirin shiga motar dazata kaishi masaukinsa kamar daga sama yaji an rike mai hannu, yajuyo dasauri yazu bawa yarinyar ido, Anisa? Yafada cikin shakku dan ba shi da tabbacin ko daidai yafada sunan. Tayi murmushi tace "amma na ji dadi daka iya kiyaye sunana. Yace "nikam mamaki nayi dana ganki a kasar nan yaushe kikazo? Tace "sai mun zauna zan ba ka labari yanzu muje naga masukinka ko za ka fara zuwa ganin na wa masaukin? Yace "ah ba komi inga waya ba sai mun tafi ba. ta langabe kai tace "kada ka sanyaya min jiki bayan na yi farin cikin ganinka kayi murnar ganina. Yace "hakika na yi farin cikin ganinki domin ina bukatar abokin debe kewa a wannan kasa da nazo. Tace"to kayi hakuri mutafi mana. Yace "to muje. Sashensa daban a gdan da zai zauna, falo guda daya da bedroom ba dai wani girma bane amma akwai kayatarwa, kitchen kamar na mace sbda tsaruwar da yayi shi kansa saida yayi sha'awar ace yanada matar aure wadda za tarika dafa masa abinci irin na mamansa, wadda yayi mugun sabo dashi, a zaman da yayi da mamansa bai da matsalar komi ta fuskar abinci duk abinda yakeso shi ake masa, duk yawonsa da gararinsa bai iya cin kowani abinci sai a gdansu sbda shi mutum ne mai kyama da kuma son cin abinci mai dadi duk dadin abinci bai iya ci sai a gdansu ko a halin yanzu yunwa sosai a cikinsa bai san yadda zai yi ba tunda bai iya girki ba ko ruwan tea bai iya dafawa ba, hakan yasa tunda ya zube akan gado bai kara motsawa ba dan ko takalmansa anisa ce tazare masa. Tana zaune daf dashi tace "khalifa bayan gajiya kana tre da damuwa kataimaka kagaya min. Ya lumshe ido yace "Anisa ba za ki iya magance min matsalata ba shi yasa nace kar ki biyoni, ba za ki ga walwala ta ba a wannan lokacin. Ta marairaice kamar za tai kuka tace "dan Allah kafada min Abbakar. Yace "Anisa yunwa nakeji kuma ba za ki iya dafa min irin abincin dazai gamsar dani ba. Ta bushe da dariya tace "Abbakar idan yau ban dafa maka abincin daya gamsar dakai ba to mata na rako duniya, kuma har yanzu bakasan wacece ni anisa ba, ko ka san cewa sbda na ji labarin kana matukar son abinci mai dadi na shiga fafutukan koyon girki ko ta ina? Ya fiddo ido yna kallonta, tamike tace banga tazama ba kafin kagama nazarin maganata bara in dafa ma abincin. Ido yabita dashi har ta fice yamaida idonsa kan rufin dakin. A wani party suka fara haduwa wanda wasu dalibai suka shiga sbda nishadi, a lkcn bata dade dafara xuwa mkarantar ba, tana zaune tare da kawarta nafisa, suna hira wasu samari suka tskoanesu har nafisa za tayi magana anisa tahanata tace "kyalesu dan mu kulasu ne zo mu bar gun. Za suci gaba da binsu shi kuma khalifa yana kallonsu ya aika a gaya wa wadannan samarin su shiga hankalinsu su kyale su anisa ko yasa a musu tsirara a gun, samarin wanda sakon yafito daga gareshi yasa sukayi nasu gurin, ya aika akira mai anisa. Mamaki yakamata jin ance wai wani ne yake kiransu kamar wasu 'ya'yansa taduvi dan aiken tace "kaje kace a za mu zo ba. .. Nafisa tayi saurin rufe mata baki tace kinsan waye Abbakar muhammad? zo muje kawai. Anisa tace "to me zai mana da har zai ce muzo? Idan wani abu yakeso garemu mai zai hana shi yazo da kansa? kai je kace bazamu zo ba. Dan aiken khalifa yace "idan kika kara furta kalma mara dadi akan maigidana zanje in gaya mai idan kuwa nagaya mai daga wannan rana kin daina farin ciki a wannan makarantar. Ga dukkan alamu ita kawarki ta san shi ke kuwa bakuwa ce shiyasa nayi miki uzuri. Anisa takara fusata sosai za tayi magana nafisa tarufe mata baki ta ja hannunta tace zo muje. Har anisa ta dage akan ba ta zuwa sai kuma taga bara taje taga abinda wannan mai gadarar yake takama dashi tabashi mamaki. Khalifa na zaune kan kujera tare da abokansa, Anisa da Nafisa sukazo gabansu, Nafisan ce tayi musu sallama ita kuwa anisan bakinta ne yayi nauyi duk abinda nayi niyyan fada masa ya gagara sai ido data bishi da shi. Yayi murmushi yanuna musu gun zama yace "kuzauna 'yammata. Bata san sanda tazauna ba, gayen ya gaji da haduwa ya yi mata ya burgeta anya kuwa ta taba ganin matashi mai kyaun wannan a rayuwarta? Tun daga wannan rana suke gaisuwar mutunci da shi da abokansa, zuciyar Anisa ko yaushe a cike yake da kuncin son khalifa batasan yadda za ayi tasamu soyayyar ta sa ba, hatta nafisa duk yadda suke ba sa boyewa juna sirrinsu amma ta kasa gaya mata . Lokacin dataji cieon so na neman hallakata ne ta sanar da nafisa halin datake ciki, tayi dariya tace "haba sister na san halin dakike ciki boye min din da kikayi ne yasa na nuna miki ban sani ba. Tace ni dai na ji ina mafita? Anisa kai tsaye zance ba za kisamu khalifa ba, ba za ki iya mallakarsa ba sai dai in Allah ya sa ravonki ne amma sai kinyi hkuri mai nisa kafin kicin ma nasara, kada kifito kigaya mai kina sonsa saidai kici gaba da hakurin bin wasu hanyoyi dan kija ra'ayinsa. Anisa taci gaba da binciken rayuwar khalifa daki daki me yakeso da wanda bai so, har a gdansu, abinda yatsorata ta shi ne mata dayake mu'amula da su sannan ba shi da niyyar aure. Lokacin daya kammala karatunsa na Bayero duka shekararta biyu a nata karatun, anan ne hankalinta yatashi sosai ganin bbu hanyar da zata kara ganinshi kuma tashiga binciken ina yasa gaba a rayuwarsa, aiki zai fara ko ci gabada karatu, bata samu cikakken byani ba sai da aka dade tana fama da azaban ciwon sonsa a zuciyarta, tadagawa mominta hankali akan sai an maidta kasar germany ta karsa karatunta acan, momin tadube ta cike da mamaki tace "ke kuwa sbda me? Kasancewar nisa ce diya tafari a gun mahaifiyarta kamar kawa da kawa haka suke bata iya boye mata duk wani sirrin daya shafeta ko meye shi, taciro wayarta tanuna mata hoton khalifa tare da bayyana mata halin datake ciki a kansa, tace "momi tsawon shekaru biyu zuciyata ta rayu ckin azabtacciyar soyayyar har wani lokaci inaji a raina kamar mutiwa zanyi idan ban mallakeshi ba, mom ba zan iya rayuwa bbu khalifa ba ke kadai ce za ki iya min wannan taimakon. Hnklin mmin yatashi sosai ta tausaya wa Anisa, ta jima tana kallonta sannan tayi ajiyar zuciya tace, "Anisa ba zan ga laifinki ba dan kin kamu da soyayyar wanda kikeso tunda ba mutum ne yake dorawa kansa so ba kuma zan yi iya kokarin inga burinki ya cika. Zan sa abanku yashirya maki zuwa germany kiriga khalifa zuwa, zanyi ta binciken tafiyar shi da saukar shi a kasan, inaso ki kasance a filin jirgin lkcn dazai sauka domin kibashi mamaki, dan zai sauka ckin kewar

Chapter 5 of 19