Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta tafi, fatima tabita tana fadin "ummi ai gdanku za ni Allah ne yataimaka bamuyi sabani ba. Ummi tajuyo suka hada ido ,kallon datake mata yana dagawa fatima hankali, tawuce dasauri tabar gun, ta tsaya sororo tabi ummin da kallo. Dr. khalifa ya iso gabanta yace "fatima don Allah ki tsaya ki saurareni, zuciyata tana matukar so da kaunar ki don Allah ki tausaya min. A fusace tace "ai kai ba abin tausayi bane, babu wani dalilin dazaisa a tausaya maka, tunda kaima ba ka tausayin mai sonka, tun yaushe ummi take fama da ciwon sonka a zuciyarta amma ka ki kadubeta kake walakanta ta sbda kawai tana sonka ? Yazuba mata ido yana murmushi wai shi yarinya kamar fatima ke wa tsiwa haka, son da yake mata ya yi tasiri da isarsa ta namiji ba zai yi komi a kanta ba, a iya rayuwarsa bai taba samun kansa a yanayi irin wannan ba. Tayi tafiyarta tabarshi a gun yana binta da kallo, gumi yana yanko masa har ta bace sannan yashiga motarsa yaja zuwa gdansu. Baiyi tunanin nan gdan na su fati za tazo ba sai yaganta za tashiga yayi murmushi kawai ,tafizge kanta tashiga ckin gda tayi sa'a mama ta fita anguwa sai 'yan aikin gdan suna hidimomin su, ta iske ummi a daki tana hada kayanta . Ta amsa sallamar fatin ba tare da ta kalleta ba, fatima tazauna a bakin gado muryarta a kasa kasa takira sunan ta, ta waiwayo tace,"na'am fati. Tace "ummi meye laifina akan wannan al'amarin lokaci daya za kijuya min baya ki tsane ni ? shin ni na budi baki nace ina son khalifa ? ko zuwa nayi sashensa naja ra'ayinsa don yasoni ? Ummi tayi mata wani lalataccen kallo tace "ke ki kama kanki, kin san dai ban tare ki dawata magana ba akan khalifa, don haka ba na bukatar kiyi ta nemana dawasu maganganu. Fatima tadaga murya tace "wlh ummi ko kusa bakiyi min adalci ba, na yi zaton a gun ki zan fara samu shaidar wani da namiji va zai taba samun masauki a zuciyata ba, ko ina son khalifa ko babu maganar musbahu a kaina ba zan taba ba, dr. khalifa fuska ba sbda na san waye shi a gunki, ballantana kwanaki suka rage a daura min aure, hakanan ba na son shi ba na ra'ayin shi to meye na damuwa, don Allah ummi kada kidauki alhaki na kada ki watsa mana zumunci ki kwantar da hankalinki insha Allahu ta hanya ta za ki iya mallakar dr. khalifa in dai Allah ya kaddara mijinki ne zan yi amfani da damar dana samu a kansa in ja ra'ayinsa gareki amma fa sai in na samu hadin kanki. Ummi tayi dif tan juya maganganun fatima wadanda sukan saurin fisgar hankalinta tadawo natsuwarta, idanunta da zafin kishi yasa suka rufe suka bude domin ta fara jiyo kamshin nasara a maganganun fatima. Ta taso tadawo kusa da fatin tazauna muryarta a hankali tace "kiyi hakuri fatima a cikin gaba daya al'amura na ba na wasa da dr. khalifa sbda soyayyar danake mishi, ban taba jin za a wayi gari watarana inji ba na san na budi ido in ganki ba sai ranar da dr. khalifa yabudi baki yace min "ke ce mace daya dayake so ya aura a duk fadin duniyar nan, a wannan lokacin ji nayi na tsaneki fatima duk da na san ba laifinki bane ba ke kika sa yasoki ba amma wannan baiyi tasirin daya Hana inga laifinki ba. Fatima tayi murmushi tace "ke ma ba ki da laifi ummi domin ba laifi bane don mutum ya yi kishin abinda yake so, ballantana soyayya irin ta ki ga dr. khalifa, hnkalina ya tashi don sabon danayi dake ta ina zuciyata xa tasake kin juya min baya, ummi inason ganin kin mallaki dr. khalifa don haka zn daure shi da jijiyoyin jikinsa tunda ya ce yana sona to ya kawo kansa garemu, kiyi hakuri da duk abinda za kiga yana nuna mini na so, kafin mu cimma burimmu, kuma kibashi hadin kai a duk maganar dazai miki a kaina ki nuna mai kin goyi bayansa, xai kasance yana son magana dake sbda hirata da kuke. Nan take ummi taji zuciyarta ta yi mata wasai, kaunar fatima takaru a zuciyarta, tafasa hada kayanta tabar gdan kamar yadda tayi nufin yi, bayan tafiyar fatima gda takira wayar hajiyarta tashaida mata yadda sukayi da fatima, hajiya tace "anya kuwa dagaske take ummi ? kada fa tayaudare ki, sai wahala ake awai wata manufa a zuciyarta. Hajiya tace "to ki dai yi taka tsan tsan kuma kisan yadda kikayi kika kawo mana abubuwan da malam yace a kawo wadanda suka shafi khalifan. ****** Cikin dacin rai fatima tadawo gida tana takaicin son zuciyar dr. khalifa duk da ta san ba zaiyi nasara a kanta ba amma abin yana ba ta haushi sosai, ga mamakinta sai ta iske mama da anty sadiya a gdan na su suna hira da inna ga zogala a gabansu suna ci. Ta fadada fara'arta tace "lah mama dama nan kika shigo. Tace "eh amma mun biya kasuwa kafin mushigo nan din. Inna tatashi tace "bari in tuka tuwon nan in hada miya in dawo. Mama ta ji dadin fitar inna tace " 'yammata na zo ki zauna anan kiji wata magana. Daf da ita fati tazauna tace "wannan zuwan na ki ne don gunki muka zo. Tace "ni mama. Tace "kwarai kuwa fatima ko baki kai matsayin daza muzo gunki ba. Tayi kasa da kanta tana girgiza kai, mama tace "fatima munzo da kanmu ne nan dan kidauki abinda mukazo miki dashi da mahimmanci, a wani lokacin idan za kagawa mutum abu mai muhimmanci to kadubi yanayin dazaka fada masa dan yafi kama batun da daraja. fatima na san matsayin uwa nake a gunki ckin gdan nan na san bbu abunda xan nema in rasa shi sai fa in ba ku dashi. ko da yake maganar danazo miki da ita mai nauyi ne amma duk da haka nauyinta ba zai hana in gaya miki ba, sbda na san wacece ni a gunki, ba kuma ina nufin yin amfani da wannan damar bane in tursasa ki ba a'a alfarma ce nake fatan kiyi min. Fatima dan uwanki khalifa ne ke neman alfarmar ki amince mai ya aureki sbda ke kadai ce zuciyarsa ke so, kuma ta aminta ya aura. Tunda mama tafara magana fatima tasan inda tadosa, dataji ta yi shiru tace "mama duk abinda kika fda haka yake, kuma alfarma kowace iri zan yiwa kowa a gdanku amma a wannan karon sai dai in ba ki hakuri mama abu guda daya ne zai hana in amsa wa yaya khalifa soyayyarsa itace ummi. Ummi kuma fatima ? Me ya kawo ummi ckin wannan maganar ? Fatima tagyara zama tace "mama ummi itace za tayiwa yaya khalifa shamaki dani domin kuwa ta fi karfin in auri wanda maitar so da farautar nema, ummi tana tsananin so da burin auran dr. khalifa ,da wani ido xan dubeta in na aureshi,in banda haka da a yau dinnan xan tabbatar miki da matsayinku a gareni mama ta hanyar amsar bukatar dr. khalifa, kiyi hakuri mama ki taimaki rayuwar ummi ki ceto zuciyarta daga halin datake ciki ta hanyar sa khalifa ya aureta, mama kin zo gdan nan ne nasan sbda ttausayn sa di kikeji da gudun fadawarsa wani hali idan bai samu yadda yake so ba, mama to kisani ummi ta fidr. khalifa kuncin zuciya don shi a cikin kwanaki kalilan yake fama da ta shi damuwar yayin da ita tadade tana fama da damuwa, akwai daran datake kwana kuka akwai ranakun da ko abinci ba ta iya ci, ,kullum ciwon rai ke damunta akan dr. khalifa, in dai akwai abin tausayi ta fannin soyayya to ummi ce, kiyi hakuri mama kituno hadisin manzon rahama (SAW) da yace imanin dayanku ba ya cika har sai ya kasance yana sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa. A DAREN FARKO 21 A cikin uwar dakin mama ita da anty sadiya ne ke zaune suna fama da magana daya dai dataki karewa, khalifa yashigo fuskarsa ba walwala yazauna kan stool yana fuskantar mama yace "gani" Tace "khalifa don Allah kayi hakuri da batun fatima ba za ta amince da batun auranka batunda dai har nataka kafata har ckin gdansu na roki alfarmarta bata amince ba, karshe ma tashiga kawo min wa'azi wai yadda naji tausayinka a matsayinka na da na har nake fafutukar ganin ka samu abun da kake bukata to itama ummi in tausaya mata in taimaketa ta aureka. Khalifa yaja dogon numfashi yace "wlh mama ni ma bansan abunda ke damuna ba, na kasa hakuri da yarinyar nan wani irin abu nake ji a cikin zuciyata kamar idan ban samu auranta ba mutuwa zanyi, ina jinjina wannan yanayi danake cki mama, a ni kaina ba na ra'ayin auran zumunci ba zan auri ummi ba, fatima kuma yanzu nafara sonta ki ci gaba da kokarin taimakona da addu'a da duk abinda za ki iya mama. Wayarsatafara ringing yatashi yafita, mama taja tsaki tadubi sadiya tace "to yanzu me za muyi, nikam ban san abinda za a zarge ni da son zuciya, ba na son in ja wa kaina zagi. Sadiya tace "kidaina damuwa mama in fa fati matar khalifa ce sai ya aureta, dole muci gaba da jan ra'ayin fatima tunda ita yakeso itace farin ckinsa. Bayan dr. khalifa yagama wayar da aka kira shi dakin ummi yanufa tana zaune tana duba wani littafi, ta amsa mai sallama cikin fara'a, yazauna gefen kujerar dake gaban madubi ya amsa gaisuwar tayi masa yace "ina fatima? Tana gdansu. Ya gyada kai "ummi" Ta amsa "na'am yaya khalifa. "Ba ki da wata hanya daza ki iya ja min ra'ayin fatima, ina sonta dayawa fa. Ba karamin namijin kokari ummi tayi ba gun shanye damuwarta da tsananin kishi? ta tace "yaya khalifa tunda dai kana son fatima zan taim*e ka kasameta, ko ba komi dai na godewa Allah dayasa kakejin irin abinda masoya keji a zuciyarsu yayin dasuka rasa masoyansu. Bata jira abinda zaice ba tamike tace "bari ma inje in zo maka da fatin. Ya bita da ido har tafita, ya ji ciwon maganar data fada masa na karshe amma babu yadda zaiyi soyayyar fatima ce taja masa, in bar da haka har ummi ce ta isa tagaya mai magana, yaja tsaki yayi tagumi. dr. bashir ne ke dada karfaf masa lallai yanemi taimakon ummi maganarta na da tasiri sosai a gu? fatima kada yadamu da abinda zaiji yagani domin duk abinda kake neman nasara a kansa sai ka yi hakuri, ba abi? da yatsana irin raini, Allah yasa ba alhakin 'yammatan daya wahalar ke bibiyarsa ba. Yana ckin wannan tunanin fatima da unmi suka shigo dakin idanunsa akan fatima yaji wani irin sanyi a ransa kamar yatashi yarungumeta nan take yakara sallamawa al'amari ummi a gun fatima, bai dada tabatar da haka ba sai da fatin tarusuna ta gayar dashi tace "ga ni yaya khalifa. Ummi tace "yawwa nikam na gama aikina, ke fatima kinsan dai yaya khalifa yayanmu ne. Ta gyada kai tace "na gane anty ummi. Bayan fitar ummi, dr. khalifa yakamo hannun fatima ya mikar da ita tsaye ya kura mata kyawawan idanuwansa masu laushi da daukar hankali, nan take yafara jefa mata wani bakon al'amari a zuciyarta, nan da nan tayi kasa dakanta tana jan numfashi dakyar, lamarin dayasa takasa cigaba da tsayawa ta janye hannunta ta zauna, yazauna daf da ita yace "haba fatima dago idonki kidube ni mana, wai meye aibuna da ba kya son kallona? Ta maraice murya tace "don Allah yaya khalifa kaji tausayin ummi ka amsa soyayyarta tana sonka dayawa, kayi hakurin fiddani daga zuciyarka, an riga an ba da ni kwanaki kadan suke rage nazamo matar wani.... Yasa hannu yatoshe mata baki yace "in kina son in a; hi batunki dago ki kalli kwayan idanuna. Ba ta son kallon idonsa sbda idon na sa daban yake dana sauran maza, amma bukatarta datake son tabiya yasa dole tawatsar da abinda takeji tawarware idonta ta dubeshi, ya lumshe ido yana mata kyakyawan murmushi, tamaida kanta kasa yace "fatima idan fa kina son in yi miki yadda kike so sai dai kiyi ta kallona har sai na ce kidaina. Tun fatima na zamewa kallon na sa har tafara rikicewa domin wani irin yanayi tafara ji a jikinta wanda bata taba jinsa ba, yakara matsowa daf da ita yasa hannayensa biyu yadafa kafadarta, "wlh ina sonki fatima inajin kihar ckin jijiyoyin jikina don Allah fati kada kibari kirasa ni kada kibari in rasaki, fati duk wanda yayi ceton rai... Yakasa cigaba da maganar sakamakon wasu siraran hawaye dasuka shiga zubo masa, lamarin dayasa fati tarude tana fadin "meye abin kuka khalifa ? Yace "ke ce bakiga abin kuka ba. Yasaketa yamike, tamike itama tatsaya a gabansa takasa magana, sun jima a haka daga bisani yafice daga dakin yana cigaba da sharar hawayensa, yawuce mama a falo yafita, gabanta na faduwa sbda ta ga yanayin daya fito nan take tsoro ya mamaye zuciyarta. A cikin dakin fatima sororo a tsaye tana tunanin khalifa, karo nafarko dataji tausayinsa ya kamata, ta yaya za tayi da wannan al'amarin, abinda yatsaya mata a rai shi ne hawayen khalifa da kyakyawan murmushinsa,dr.khalifa ya zamo namijin farko dataji lallai tanason taji ta a jikinsa sbda burgetan da yyi. Ta kwanta bisa gado tayi luf, a lokacin ne ummi tashigo dakin da zumudin jin yadda sukai ganin kwanciyar da fatima tayi da yanayin jikinta yasa gabanta yafadi sosai. Ko dai khalifa ya fara wa fati tasiri a zuciya, a sanyaye tzauna daf da ita muryarta cikin wani irin yanayi tace "fati yaya akayi naga kin zama wani iri. Fati tayi firgigit tamike zaune idnuwanta a waje tana kallon ummi tace "an samu nasara domin kuwa ya fara amsa min zai min duk abinda nake bukata. Ummi tayi ajiyar zuciya "fatima lallai idan kika ceci zuciyata daga halin da take ciki kin yi taimako. Tadafa kafadarta tace "ba komai kidaina yawan damuwa. ****** Tsakiyar dare ummi takira jidda dake londn ta fayyace mata abubuwan dake faruwa, jiddah tace "Dr. khalifa na son fatim Tace "kwarai kuwa jiddah soyayya kuma ba gama garin soyayya ba original one, domin kuwa tunda yadora idonsa a kanta gaba daya ya rikice ya rasa sukuni, kin san dai yadda khalifa ba ya sakar min fuska ko ? To a halin yanzu sbda in masa kamfen a gun fatima za kiyi mamakin yadda yake ja na a jiki ko kunyata ba ya ji. Jidda tayi ajiyar zuciya tace "anya kuwa umi ko dai dr. khalifa tsammani yake son wasa kike masa. Tace "haba jiddah wani irin wasa kuma, da dai ace mun saba wasa ni dashi to zaiyi tunanin haka, mutumin da bai min ko kallon arziki za kiyi mamakin yadda yasauya akan son fatima abin har tsoro yake ba ni jiddh. Ta jinjina kai tace "to yanzu wani mataki kika dauka akansu ? ko kin hakura dashi ? In hakura jiddah ? Tabdijam ai idan kika ga na hakura da khalifa to numfashin karshe nayi a duniya, ma'ana rayuwata ta kare amma idan ba haka ba matukar ina numfashi ba zan hakura da doctor ba. Jiddah tace "to ummi ta wce hanyar za ki mallakeshi bayan kin san ko da akewa maza auran dole a wani lokaci ba za ayiwa dr. khalifa ba. Tunda kinfi kowa sanin cewa mahaifinsa yana fifita shi akan komi yana kara akan komi banda khalifa. Ummi tace "eh nima bance za ayi mai auran dole ba kawai dai ba zan bar ma wata shi ba. Jiddah tace "ko da fatiman ta ki ta aura ? Tace "wannan ne abinda yafi daga min hankali ban so yakasance dr. khalifa fatima yake so ba sbda kaunar da nakewa fatima ba na son wani abu na bacin rai ya sameta, in da nake dan samun natsuwar zucia shi ne fatima ba son dr. khalifa rtake va, bayan kasancewar saura kwanaki kadan a daura auranta, fatima tanada burin biyayya ga iyayanta shi yasa bata kula kowanne da namiji, wannan yanuna kwanciyar hankali. A DAREN FARKO 22 Gaban abban yafadi ras yayi wa dr. khalifa wani irin kallo yace "ai an kusan bikinta da musbahu. Yace "na sani abba ai aaure nufi ne na Allah idan matata ce sai kaga.... Ya katse shi yace "kai khalifa wannan abu ne da ba xai yiwu ba nima na so auranka da fatima domin yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata,to amma ta ina xanje in ce a fasa ba musbahu aure a ba ka, gskiya sai dai kayi hakuri Allah yabaka wata. To shima khalifan ya san abun da nauyi soyayyar dayake mata ne yasa yarufe idonsa yakeso ya mallaketa kota wani hali, bai ka ra cewa ko ; i ba, abba ya bishi da ido jikinsa gaba daya yai sanyi ba ya son dan na sa yanemi wani abu yarasa a rayuwarsa. Nan da nan yanayin abba ya sauya ganin damuwar da ke tare da khalifa, yamike yashiga dakin mama, tamike dasauri daga kwanciyar da tayi tace "daman ka fito Alhaji ? Fuskarsa ba walwala yace "na fito, khalifa ne yazo min da maganar data dagan hankali. Mama tace "uhm Allah yasa ba maganar fatima yakawo maka ba",. Ya dada bata rai yace "af daman kinsan da zancen baki fada min ba ? Mama tace "to Alhaji idan na fada maka me za kayi !? abinda zai yiwu ahi ake, ta yaya khalifa zai samu auran fatima idan kuwa ba zai samu ba meye amfanin tattauna maganar. Alhaji yazauna gefen gado yana fadin "to haka za mubarshi a ckin damuwa hajiya ? gaskiya ba zai yiwu ba. Mamaki yakama mama ganin yadda abba ke neman rufe ido kiri kiri yayi son kai, tace "alhaji gskiya sai dai hakuri domin ni da kaina naroki yarinyar tanuna min gskiya ba zai yiwu ba,ni abinda ke hadani da Khalifa shi ne idan yakallafa ransa kan son abu ba zai iya hakura yabi abin a hankali ba, sai dai ydga hankalinsa yadaga wa wani hankali. Abba yace "ba dole yadaga hankali ba, in bai gaya mana damuwarsa ba wa zai gayawa, kin san zafin soyayya kuwa ? Tace "hakane ban sani basai ka nema mai auran nasan dai sai da amincewar yarinyar da iyayanta za ayi ko ? Abba yace "Gaskiya ba zan bar yaron ckin damuwa ba, dole in bi duk hanyar dazan bi don ganin na samar mai dafarin ciki a rayuwarsa. Yajuya yafita yayin da mama tabishi da kallo cike da takaicin yadda abba ba ya son nunwa Khalifa yadda rayuwa take. **** Fatima ce zaune a runfar innarta ta yi tagumi ta kasa cin abincin dake gabanta, innar tana dakin malam, sauran kannanta duk sun tafi makaranta, musbahu yashigo da sallamarsa, tadaga ido ckin ladabi ta amsa muryarta a sanyaye tace "ina kwana. Idanuwan daya kafa mata yasa tayi kasada kanta yazauna kusa da ita yace, "fatima a kwana biyun nan kin sauya kamar ba ki da lfya sai ramewa kike ko dai fargabar auran ne ? Ya fada yana dan murmushi a kokarinsa na kwantar mata da hankali, itama murmushin tayi tace "lafiya kalau. Yajawo abincin gabanta yafara ci yana fadin "kai abincin nan yayi dadi da yawa na san ke kikayi. Bata ce komi ba, yaci gaba "gaskiya fatima Allah ya yi miki baiwa da yawa shi yasa zuciyata ke kara sonki don Allah nima ki soni kuma kidinga tausaya min wahala zan sha idan nasamu sauyi daga gareki. Anan ma shiru tayi masa don bata san abinda za tace dashi ba, wani iri takeji a jikinta ko kallonsa ba ta iya yi, yace "ftima don Allah kiyi min magana ko zanji dadi mana kin san ina sonki. Fatima bansan abinda zai same ni ba hakanan nake jin zuciyata tana cik e da fargaba idan nakwanta bacci kuma sai in ta mafarkai barkatai marasa dadi wanda yafi daga min hankali shi ne wanda nayi yau da asuba wai wani ya kwace min ke ta karfin tsiya, shi ne jikina duk yakara sanyi. Ga mamakin ta sai taji hawaye ya taru a idonta, tatashi dasauri tashige daki tace dashi "ina zuwa . Misbahu yabita da kallo har yagaji dazama yatashi bata dawo ba bai san meke faruw aba baiyi tunanin binta ckin dakin ba yafice daga gdan. Itama inna data shigo dakin kallon mamaki tabita dashi ganin yadda take saharar kwalla tace "lfya fatima? Tace "ba komi inna Ba komi kike kuka? Takasa magana domin itama batasan dalilin kukan na ta ba ballantana ta bayyanawa inna, inna ta jima a tsaye tana kallonta daga bisani tadaga kai tafita . Wayar fatima tafara ringing tadauko ta bakuwar lamba ce, tadaga tare da sallama, daga can bangaran aka amsa mata "Khalifa ne. Gabanta yafadi "ko baki fahimci khalifan bane? "Na fahimta. "To ai na ji kinyi shiru. Tace!"bansan abinda zan ce bane. Yayi dariya "za kisani yanzu kuwa, so nake kizo mugaisa tun da natashi idanuwa na ke son ganinki zuciyata na azalzala min da yawa don Allah kidaure ki zo. Tace "haba khalifa meye ma'anar zuwana gareka? me ganin zai haifar maka, me yasa kke mantawa na kusa zama matar wani ne.... Ya katse ta. Don Allah kidaina gayamin wannan maganar ki daure ki zo muyi wa kanmu maslaha. Shi knan a ina zan sameka? 'Yawwa tawan ina kofar gdanmu ckin mota ta. Hijabi tasa wanda yazo har kafafunta ydda idanunta ke kode sunyi ja haka tafita bayan ta shaidawa innarta cewa za ta gun ummi.. Ta wuce musbahu a kofar gda tare da wani abokinsa mai suna Aminu, khalifa yana hangota ya bude mata kofar motar tarike kofar tana kallon sa tace "idan na shiga mota ina zamu? ko a cikin motr za muyi magana? Yace "inaso kiyi min rakiya wani wuri. ne ba nisa. Ta waiwaya tadubi musbahu ita yakafawa ido, ta dawo da idon ta kan khalifa tace "kn ganin hakan y dce? "Eh ya dace mana kowa ya sanba na satar mutane, Fatima maslaha muke nemawa kanmu ina bukata kema haka in haka ne ki shigo mutafi. Bbu abinda ummi ke kallo sai rayuwar ummi wannan ce damar da zatayi amfani dan tallafawa ummi, sai ta zuke fargabarta tshga motar tarufo. . Ta gabansu musbahu, kbalifa yawuce idon ta ckin na musbahu taji gabanta ya fadi an ya ta yi dai dai kuwa. Gdan dr. bashir yanufa da fatima, matar dr. bashi ta asheta hannu biyu zuwa falonta takawo musu abinci da shayi, dr. khalifa yahada tea yafara sha, dr bashir ya harare shi "wato haka Za kadinga son kai ko ita amaryar fa. Don Allah ku rufa min asiri ina tare da matsaloli ko yanzun ma na biyo shi ne domin in fahimtar dashi. Farida tahada mata shayin taja hannunta zuwa ckin daki tace "fatima don Allah dagaske ba kya son Khalifa? Fatima tawaro ido tace "me son na shi xai amfana min, a rayuwata bbu abin da na tsana irin in yi abu in dawo ina nadama. Farida tace 'dr khalifa yadaga hnkli akan tsananin sonki, da za ki amsa soyayyarsa xa ki mori rayuwar aure, irin su tsada garesu. Fatima tace kin san kyaun mijin daxan aura da halayansa? an masa adalci in nabarshi na auri Khalifa? aminiyata na tsananin son khalifa ya kamata in watsar da batunta in aure shi? abinda khalifa ke nunawa fa son kai ne kuma ba dabi'ar musulmin kwarai bane, ya kamata kidnga fadwa Khalifa wadannan, don ydinga sa hkuri a zuciyarsa a rayuwa ba komi mutum ke so yake samu ba. Farida tarasa abin da xa tace sbda hujjojin fati sun daure mata jijiyo tamike tadawo falo tace da Khalifa da wuya fati ta amince yahakura kawai. Khalifa yace kai ba zai yiwu ba turo min ita, ban taba neman abu na rasa ba ba xan fara akan fatima ba, fatima ba ta ckin matan da za a iya hakuri dasu. **** Tun daga ganin yanayin fuskarsa ta san ba lfya, bayan sun gaisa ta tambayeshi "yace "ummi don Allah ko kin san wani abu tsakanin ummi da khalifa? Tace "wani abu kagani? Yace "kwana biyun nan na fahimci wani abu na damunta ta ce min ba komi, daxun kuma naga ya dauketa sun fita a motarsa, na kira wayarta bata daga ba. Ummi ta fiddo ido "fatiman? yace itafa abin ne nima yabani mamaki da yawa shiyasa nakasa aurewa sai sun dawo nazo inji ta bakinki na san kin san komi. Ummi tayi shiru kanta na kasa ". Lamarin daya dada firgita musbahu gabansa yashiga faduwa yashiga rokonta da Annabinsa in ta san wani abun kada taboye masa..... A DAREN FARKO. 23 Dr. khalifa yaci gaba da cusawa fatima maganganu a cikin kunnuwanta, suka dinga ratsa mata zuciya ga hgangar jikinta, lamarin daya sa ta kuma jin tsigar jiki? ta tana tashi tarabu da marsh war zuciyarta ,lokacin da dr. Khalifa ya fahimci ya yi ntasirin jan hankalinta sai ya saketa ya zaunar da ita gefen gadon yazauna a kasa. yace "fatima kiyarda in zama mijinki zan shayar dake zumar soyayya, zan dandana miki wata rayuwa wadda mafarkin ki bata taba ba ki ba, duk wani jin dadi da kwanciyar hankali da diya mace take fatan samu a gdan mijinta zan ba ki shi ba dan komi ba sai don ina sonki, ni kaina na san zuciyata tana sonki ba zanyi wasa da duka abinda yshafe ki ba. Abinda ke tafiyar da fatima shi ne son kallon fuskar Khalifa da idanuwanta ke nacin yi, idan kuma takalle shin sai taji wani irin abu nai mata yawo a cikin zuciya d jiki, ckin kasalalliyar murya tace "wai don Allah ya kakeson in yi da matsallina ? yaya xanyi da musbahu da ummi. Yaja tsaki yace '"don Alah ki ce kin amince dani kina sona za ki aureni, musbahu na san yadda zanyi dashi, unmi kuwakadaki kara min maganarta tunda nace ba na sonta ban sonta ba zan auri matar da ba na so ba. Tace" amma docter ya dace katausaya mata yadda kake son kaima. a tausaya maka yadda kake kokawa a bisa soyayyar dakake min tana wahal ma da zuciya, kowa fa yataimake wani Allah zai taimaka masa. Ya dan harare ta yana murmushi. "To na ji sarkin iya wa'azi. Takara langabe kai "to baka ce komi ba. Yace "to wai so kike in hakura dake in auri ummi ,ko kuwa in aure ku tare. Yana tsaye ne kyam a gabanta, kai wannn bawan Allah dakyau yake Allah ya yi halitta anan, ta hadiyi yawu tace"ni dai ina so ka aureta. Yace "to baki amsa ba in hakura dake ko in aureku tare ?ki je kiyi tunani ki zo min da amsa nan da gobe tashi mutafi gida. A hanyarsu ta komawa gda yatsaya a wani makeken super market yadinga zabar mata kayan kwalliya masu tsadar tsiya da burgewa sannan yajuya kan ciye ciye da na masarufi sai daya jibgesu a kujerar baya tana kallonsa. Wannan karon ma musbahu yana zaune shi kadai a kofar gidansu fatima kan benci, khalifa yayi parking, sakinbaki yayi yana kallonsu har suka fito tashige cikin gida dasauri yayin da khalifa yashiga kwasar kayan da zai iya, yakira wasu yara suka dinga deban buhunhunan shinkafa da kwalaye suna shiga dasu, duk wani abu na kurewar jin dadi a fannin ci da sha khalifa ya siye shi ba kadan ba. Inna tana tsaye a tsakar gida tana kallon ikon Allh ana ta jibge kayn tatmbayi yaran sukace khalifa ne yace a kawo. Fatima kam daki tashige, xuwa chan dr. khalifan yashigo inna takarbe shi da fara'a zuwa rumfarta "duk dawainiyar da ke damu bata isa ba si anyi wata. Yace "don Allah kar ku damu inna ni

Chapter 10 of 19