Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min addu'a. Ta katse shi ckin damuwa tace "Don Allah kadaina batun mutuwar nan haka. Yace "kyaleni in yi fatima duk mai rai mamaci ne duk yadda muka kai ga son rayuwar duniya sai mun mutu, tuna mutuwa shi kesa mutum yayi wa kansa hisabin ayyukansa yadinga sanin cewa zai hadu da Allah kuma zai ga abinda ya aikata me kyau ko kishiyarsa. Tace "To nidai na ji don Allah mubar wannan maganar. Yayi murmushi yace "Shikenan na barta, yaci gaba da dan latlatsa mata jiki har sai da yayi nasarar kashe mata jikin gaba daya ya kasance ba ta da wani kuzari, sai yadda yayi da ita, duk zazzabin da take fama dashi sai da taneme shi tarasa sai tsabar tsananin son khalifa da shaukin sa. Ya zare jikinsa yamike yasawa kofar key yakara rufe lavulayen dakin yayi dan duhu duhu, tsoro yacika zuciyar fatima ta tsahi zaune tana rokon don Alla ya taimaketa kada yayi mata wani abin, yace "kiyi hakuri kawai fatima nima ba na son yimiki wannan abin anan gdan sai a gdanmu amma a halin yanzu zuciyata ba xa ta taba iya hakuri ba, kada kijefa nin ckin fushin Ubangiji kisa in je in aikata sabon Allah, kada kijefa kanki kema ckin fushin Allah kuma kinsan matsayin matar datake gujewa mijinta. Jikin fatima yadinga rawa ganin yadda yanufo ta gadan gadan sai kawai ta sallama zuciyarsa ta gama karaya ta tabbatar idan bata bashi hadin kai ba zaiyi ta karfin tsiya, tunda idanuwan sa sun rufe hankalinsa a tashe yake sosai. Kokarin da khalifa yayi shi ne ya saita kansa sanin cewa fatima budurwa ce wadda taba taba sanin da namiji ba, sannan yarinya ce karama in barda haka da yau fati ta yabawa aya zaki ? ta, duk ilahirin jikinta saida khalifa yabi yalashe, yajuya ta nan yajuya ta chan tading jan numfashi dakyar don kafin a kai ga bbabban al'amarin fatima ta galabaita, lokacin datafiya tai nisa yasamu nasarar rabata da budurcin ta bata san lokacin data saki wani kara mai karfi ba sbda zafi da taji ya ratsa mata har kwakwalwar kanta, tafita hayyacinta hatta numfshin ta sai da yayi daukewar yan mintuna sannan yadawo, khalifa yana sane da halin da take ciki sai daya gamsu son ransa sannan ya kyaleta. ***** A DAREN FARKO 35 Tuni zazzabin fatima yadawo jikinta yadauki zafi sosai, yayi saurin dagota yakaita bandaki yasa tawul da ruwa yadinga shafa mata a jikin sannan yace tadaure tayi wanka. fatima kuka take sosai da kyar tayi wankan, gaba daya jikinta ciwo yake mata ba karamar wahala tasha ba. Idanuwanta suka yi ja, bayan ta gama wankan tadaura zaninta tazauna jugum tayi tagumi tana tunanin wannan azabar ake sha idan an yi auran ? shin haka khalifa zai yi ta gwada mata karfi yana gana mata azaba, kai gskiya da sake. Yaturo kofar bandakin ya shigo, a tsorace tamike har abin ya bashi dariya daya fahimci tsoronsa take ji, shi kansa ya san ya ba ta wahala, ya matsa dab da ita yace "kiyi hakuri fatima kowace mace da kike gani tana rayuwa da mijinta sai da tasha wannan wahalar, ki kwantar da hankalin na lokaci daya ne daga yau ba za ki kara jin zafi haka ba. Tadinga sharar kwalla yace "Don Allah kidaina kuka in dai ba so kike nima in miki kukan ba. Wannan abin na yi miki ne don ina sonki, bai dace yazamo abun damuwa a zuciyarki ba kinga gdan nan ba mu kadai bane idan su mama suka dawo suka ga kina kuka kinsan za tadamu don Allah kiyi hakuri kidaina tunda ba kyaso ba zan ka ra yimiki ba. Ya lallabata yakara rungumeta a jikinsa yana gaya mata kalamai masu sanyi har zuciyarta ta dan lafa, tafito daga toilet din ta taras ya sauya shimfidan gadon da kansa, mutumin da ba abinda yasani a rayuwarsa sai yahuta komi yimasa ake yi. Bayan ya gama yafito lokacin ta gama sa kayanta ta haye gado har yanzu idanuwanta jawur suke, ta ki yarda su hada ido da khalifa a bisa dole ya kyaleta yakoma gefe yazuba mata ido yana murmushi, shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarsa game da ita, shi dai kam yau ya san ya kwanta da mace ya gamsu yafara sanin meye sirrin dake tare da matar aure ta sunna wadda ke da banbanci data bariki, wadda a baya suka dauka itace rayuwa ta cinyewa da burgewa, ashe duk wani sirrin kwanciyar hankali na tare da matar aure, hakika zai rike fatima dakyau domin yau kam ya san ya yi aure na birgewa da morewa, yadaga hannunsa yna ma Allah godiya daya bashi fatima. Yamike yadan shafi fuskarta ba ya son fita daga dakin amma haka yadaure yafita, hankalinsa a kwance ganin hr yanzu su mama basu dawo ba, sai dai yana fitowa yaci karo da motarsu ta shigo, a tsatsaye yayi musu sannu dazuwa ta tambaye shi jikin fatin yace da sauki yadau motarsa yabar gdan. Dakinsu fatima yafra shiga, jin zafin da jikinta yayi fiye da dazun yasata kira dr. khalifa a waya ta hau shi da fada tace "Ya naji jikin Fati da zafi haka ? Baka ba ta magani bane ? Gabansa yafadi yayi zaton ko wani abu tafahimta, ya san halin mamansa da wayo, Har allura nai mata mama zai sauka ne. Tace "wane irin xaxxabi ne wannan an auna jininta ? Yace "Ina zuwa za mu zo da Br. Bashir yanzu mu auna. Ya iske Dr. Bashir a office dinsa a asibiti ba aiki yake ba kulle kansa kawai yayi yana hutawarsa, Dr khalifa yace "Ka taso muje ka auna min jinin matata zazzabi yake damunta. Idanun Bashir a lumshe yace "Kai me kakeyi da baza ka debo jinin kataho dashi nan a auna ba, don Allah ka kyaleni barci nakeji jiya kwana nayi ba barci shi yasa naki tafiya gda don ba za subarni in yi barci ba idan naje. Dr. khalifa yace "Don Allah taso muje mama sai fada take min. Dr. bashir yatashi yana mita yadauki wasu kayai aiki suka shiga motar dr. khalifa suka danno gdan. Fatima bacci take sosai sai mama ce a kanta ko da jin yanayin fitar numfashinta ka san tanajin jiki, mama tafice tabarsu. Dr. khalifa yazauna kusa da ita yadakko hannunta yadora kan cinyarsa ya amshi sirin jin yasoka mata akan jijiya zai debi jininta tasaki kara mai karfi, yavuga kafa da karfi yace "Oh my God ka ga abinda nake gudu ko. Dr. Bashir ya amsa jinin yana harararsa, yasaka a cikin waya 'yar na'ura daya riko a hannunsa, Fatima ta tashi takama kuka. Dr. khalifa ya kara rudewa yarungumeta yana lallashinta, Dr. Bashir yace "Ka ga idan ba za ka saketa muyi aikin da zamuyi ba zan yi tafiyata, haba mutun sai nacin soyayya tamkar akanka aka fara aure. Ya maida idonsa ga fati yace "Ke fatima karfafa jikinki ba na son shagwaba tashi kiyi tafiya in gani. Fatima takara narkewa a jikin mijinta cike da shagwaba tace "Ni kafata ciwo take ba zan iya tashi ba. Dr. bashir yafiddo ido yace "Ai ko dole kitashi idan baki mike ba ya ya zan fahimci ciwonki. Khalifa yace "Ni fa ba na son iskanci duk ciwon da za kagani za kagani a jikinta ba za ka wahalar min da mata ba ko don ciwon ba a jikinka yake ba.. Dr. Bashir yace "Allah ta tashi kaine kake kara shagwaba yarinyar nan. Khalifa ya lallaba fatima ta tashi tafara tafiya da kyar takai bango tadawo za ta zauna, Dr. Bashir yace "a'a bai isa ba cigaba da tfya. Khalifa yafusata yace "Kada Allah yasa kadubata in dai sai ta cigaba da wahalar tfya kana gani fa dakyar take tafiya. Bashir yayi murmushi yace "Abbakar kaine ka haifarwa da fatima wannan ciwon. Yaja tsaki "To ina ruwanka kai dai kayi aikin ka mana ni ban son sa ido. ***** An yanke shawarar sai an kai fatima gdan wanda yahada da yini da party guda biyu amma a ranar da za akaita da yamma za ayi kamu hade da walima, ta dai ji sauki sai abinda ba a rasa ba, tun a safiyar yau lahadi tadawo gdansu, a gdan dan hausa aka shirya za ayi kamun, ango da abokanansa ma za su halarci gun domin za ayi kamun ango daga karfe hudu zuwa biyar xa ayi komi a gama, dan haka karfe uku da rabi na yamma aka fara daukar mutane zuwa gdan dan hausan, mawakan zamani na ta cashewa ana wasa ango da amarya da iyayansu mama da abba da inna ma sun halarci gun malam ne yace va zai je ba. Yau shigar ango da amarya ta kasnce dark da light brown, shi shadda ita less, abin ba a magana kyau an yi shi sai wanda yagani duk wanda yake gun ya yabawa haduwar ango da amarya sbda sunyi kyau na daukar ma'ana ayau an ga abinda ake kira matching, kalandar da aka raba a gun ta ja hankulan mutane da yawa domin anyi hoton ne a wani irin yana yi me ban sha'awa wanda yake tabbatar wa da jama'a tsananin so da kaunar dake tsakanin ango da amaryarsa. Lokacin da mawaki yanemi fitowar ango da amarya filin rawa don su taka rudewa gun yayi domin cewa yayi zai ga wanda zai riga wani mikewa tsakanin ango da amarya. Fatima tayi wuf tariga dr. khalifa mikewa, gaba daya aka shiga tafa mata, mawaki yace "kyautar fatima tafarko ce sannan ta dr. khalifa tunda ta rigashi mikewa. Lokacin dasuka iso filin rawan, iyayansu da abokai da dangi aka dinga yi musu ruwan kudi har ya kasance babu abunda kake gani a gun sai sabbin kudi suna tashi sama da kasa. Karfe biyar da rabi akayi kamun amarya karfe shida kuma akayi kamun sngo, shida da rabi aka rufe taro da addu"oi na musanmman daga manyan kuma shaharrarun malamai, bakwai saura kwata aka tashi. Karfe takwas aka shiga wata liyafar inda malamai mata suka yiwa ango da amarya fadakarwa ta awa daya kachal yadda za su zauna da junan su, karfe taran dare aka dauki amarya zuwa dakin ta bayan iyaye da yan uwa da abokan arziki sun yi mata nasihar zaman lfya tare da addu'ar Allah yasanya wa aurensu alheri tare da albarka. Duk inda amarya tagifta sai kamahi mai dadi da sanyaya zuciya ke tashi. ***** Wannan shi ne asalin labarin masu karatu sai kuyi jimirin biyoni kuji yadda aka kaya, an dai kashe Dr. khalifa a DARANSU NA FARKO da aka kai fatima, shin waye ya kashe Dr. khalifa ? shin ina labarin musbahu ku biyoni. ***** Karfe shida daidai na yammacin Alhamis jirgin da ya taso daga Lagos yadire Jidda a airport din Malam Aminu Kano dake birnin kano, tana rataye da jakarta ta hannu, tashiga motar gdansu da aka zo daukar ta, tana shiga gdansu aka rude da murnar ga jiddah ga jiddah, ta zauna a falom mahaifiyarta suka gisa tare da tambaye tambayen 'yan'uwa da abokan arziki. Ummansu tace "ke dai jiddah idan kika sawa ranki abu sai kinyi shi har yaushe kikaje london din da za kice sai kin zo hutu ? Tace "wallahi umma nima banyi niyyar zuwan ba haka kawai a wannan satin naji gaba daya hankalina ya tashi da zaman london din ga mafarkai ina tayi marasa dadi nayi nayi in jure na kasa kwana biyun da suka wuce ko barci bana yi sosai. Umma tace "To Allah yasa alheri, Allah yarabamu da muagun ji da mugun gani. Tace "Amin, ina Abba ? " Tace "Ya fita amma tunda yamma tayi yana hanyar dawowa. Tace "Bari in yi sallah in je gdan su Ummi wai tana shigowa kuwa na san rashin kirkita. Umma tagirgiza kai tace "Wayyo Allah ai ummi gaba daya ba ta ckin natsuwarta hankalin kowa a tashe yake sakamakon wani abin tausayi daya faru. A firgice jiddah tace "Mr ye umma ? ko shiyasa idan namata waya ba ta shiga a kwana biyun nan ? Tace "ai idan kikaga ummi sai kin tausaya mata sbda firgicin data shiga ai na yi zaton ta gaya miki a waya ma ? Jiddah tace "wai me yafaru ne umma ? Umma taja dogon numfashi tace "Uhum ai jidda a ranar aka kashe Dr. khalifa da Fatima ,yanzu haaka zancen danake miki fatima na kulle ana tuhumarta da laifin kashe Dr. khalifa. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Jiddah ke maimaitawa jikinta na rawa tabugi kirji tace "Mama an kashe khalifa ? Ta amsa cikin tausayi. '"An kashe Khalifa jiddah kuma fatima tana cikin mummunan zargi don ita da kanta ta amsawa kotu cewa ita ta kashe shi. Jiddah ta girgiza kai ta mike tsaye tace "Fatima ba za ta kase Dr. khalifa ba, ko da ace ba ta son shi ba ta da dalilin kashe shi akwai wadda na sani wadda ke da dalilin kashe shi kuma shi ta kashe shin ni ce zan fasa kwan, nasan waye yakashe Dr. khalifa. Alhamdulillahi. Masu karatu a yi hakuri ayi jimirin biyoni a littafi na hudu kuma na karshe don jin ya zata kasance, waye yakashe Dr. Khalifa ? A DAREN FARKO 36 NI na san wanda yakashe Dr. khalifa da dalilin dayasa aka kashe dr. khalifa.Jiddah taci gaba da tayar da maganar wanda yasa mahaifiyar ta ta cikin tashin hankali, ta zaro idanuwanta gaba daya cikin kaduwa take kallon jiddah tace "Ke 'yar nan kin san abinda ki ke fada kuwa ? Na sani Ummah, "kin sani jiddah ? "Eh na sani mana umma, idan babu rami babu abunda ke kawo batun rami, wannn maganar da idan mutum yadauketa ya san abinda yataka, haka kawai baxai fada ba sai yana da hujjah hujjar ma mai karfi. Umma ta jinjina kai har yanzu fuskarta a razane tace "Jiddah ki yiwa Allah da Annabinsa kada ki kara furta wannan maganar ballantana wani yajita kija bakinki ki shiru. Jiddah tai murmushi tace "Ummah na yi zaton za kitambayeni inda nasan wannan maganar me cike da gagarumin sirri ba wai ki dinga rokar kada in fada ba, yaya lallai in boye wannan maganar ko kuma kiyi shakkar inda naji ta. Umma ta girgiza kai tace "Jiddah tsoron hadarin dake cikin maganar ne ya firgitani yasa narude ni din ma dakike fadawa tsoro nakeji ballantana idan magana tafasu kowa yaji, kin san irin wannan maganar gagurama ce kuma ni banyi shakka don na ce kina da masaniya akan kisan khalifa ba sbda bazai yiwu kifadi hakan ba face lallai kin sani, mamaki na shi ne a ina kika sani ke da ba ki a kasar, to amma tsoron danaji yasa maganar mamaki ta kau a zuciyata nake roko ki rufawa kanki asiri ki rufa mana. Da zarar kin furta wannan maganar za a shiga tuhumar mu. Jiddah tace "Umma yaya za ayi ina ganin gskiya kiri kiri a rufeta, yanzu sai kisa ido a kashe Fatima ? Alhali ba ita takashe khalifa ba dole in bayyana wanda yakashe khalifa yau din nan, tamike tsaye. "Umma ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same mu sai alheri insha Allahu, itama umman mikewa tsaye tayi tace "ta ina zan kwantar da hankalina jiddah ? ai hankali ya bar kwanciya in dai kika fasa wannan maganar ni dama na sani ban fadi miki ba. Tace "Ummah ko baki gaya min ba zanji ke dai ki tamin addu'ar neman kariyar Allah ahine me kowa da komi, tarike hannunta lokacin data yi hanyar fita tace "jiddah kar dai kijefa kanki ckin hadari, takatse ta umma bazaki tambaye ni wanda yakashe dr. khalifa da dalilin kashe shi ba sai rayuwa ta kike neman karewa to bari kiji, "Kariya tana gun Allah ban taba tunanin zan dawo nigeria a wannan lokaci ba haka kawai ina zaune hankali na naji ya tashi, Allah ya dawo dani ne don yatoni asirin wadanda sukayi wannan kisan . Allah ya dawo dani ne don ya kubutar da Fatima kinga kuwa ba ni da dalilin dazai sa in rufe bakina don in kare rayuwata, jin an yi kiran sallar magriba yasa jiddah tafita tana fadin "ina zuwa ummah. Hankalin ummah yatashi sosai zuciyarta tashiga harbawa, kar fa yarinyar nan tajawo mana fitina ya kamata in sanar da babanta halin da ake ciki, wannan maganar me hadari wa zai sa kansa a ciki don wauta ? Tana cikin wannan tunanin babansu jiddah yashigo tare da babban yayansu Alhaji Nazifi, tace "Yawwa Alhaji gara da Allah yaka wo ka jiddah dai ta dawo mana da fitina tana neman jefamu ckin zargi. Yace "me ya faru daga dawowarta ? Ta bayyana masa duk abubuwan dasuka tattauna da jiddah, hankalinsa shima yatashi, Nazifi har ya fi abban na su fusata yace "kin ga yarinya mara hankali ? wa yagaya mata ana irin wannan ? Alhaji yce "Dakata, tanada dalilin fadin hakan, ta gaya miki ? Umma tace "Yo Alhaji ni da hankali na yatashi ina na tsaya tmbayarta wanda take nufi ya yi kisan. Yace "yanzu tana ina ? Tace "ta fita nasan dai ba za tawuce gdansu dr. khalifan ba ko gdansu fatima. Yadubi Nazifi yace "maza nemo mini ita a waya, zo muje masallaci mudawo, Alhaji Nazifi yayi kwafa xuciyarsa cike da haushi nomban jiddah tana dagawa yace "Ke fitinanniya munji maganar dakika zo da ita sai ki zo kiyi mana bayani. Bai jira jin abinda za tace ba yakashe wayar. Suka yi alwala suka nufi masallaci. itama umma alwalar tayi tai sallah zuciyarta cike da fargaba sai a yanzu take son jin hujjar da jiddah ta taka take furta cewa ta san wanda yakashe dr. khalifa. **** A harabar gdansu ummi, jiddah ke tsaya tana neman wata waya kiran yayanta yashigo, don haka tafasa shiga gdan tadawo da baya zuwa gdansu kafin baban na ta sudawo daga masallaci itama tayi ta ta sallar. Kannanta duka suna falon da abokiyar zaman umanta hajiya zainab da suke cewa Anti, Abba da Nazifi suka shigo har gara fuskar Abban tana nunawa zai karbi maganar da fahi ; ta. Nazifi kuwa gallawa jiddah harara yake kamar ya shaketa yahuta, ya tsani ana zaune lafiya a tado da ftina. Jiddah na zaune gaban abbansu ta lankwashe kafafu kanta na kasa tana mai bayanin daya daurewa kowa kai, babu wanda yakatse ta sai da tayi shiru. Nazifi yaja tsaki yace "kai jiddah ni duk da haka inain wannan abubuwan dakika fada bai isa ya zamo hujja akan wannan gagarumin magana ba,. Shari'a fa sabanin hankali ce kuma ita an yi mata lakani da mace mai ciki ba a san abinda za ta haifa ba, sannan hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba barawo sai ya kamaka, eh abubuwan da kika fada mana ya isa a dubesu a yi nazari amma ba zai isa gamsashiyar hujjar da za a tunkari kotu da ita ba kai tsaye sai an yi dogon bincike da taka tsan tsan sbda kotu ba gun wasa bane. wannan maganar saita jefamu a wahala. Umma tayi farat tace "yawwa alhaji abinda nake son ka kalla knan mutum yana ckin zaman sa lfya bai dace yadauko ma kansa abinda zai zama fitina gunsa ba, wannan magana ce me sarkakiya. Jiddah tace "ki kwantar da hankalinki insha Allahu Allah zai fitar damu ni dai addu'arku nake nema, ina ji a jikina wani nauyi ne ya hau kaina wanda ya zamo dole in yi magana a cikin wannan lamarin idan nazauna inajin tsoro za ayi kwaba. Gaba daya suka yi shiru kowanne zuciyarsa bata gamsu da abunda jiddah ke niyyar yi ba a son ransu abba ya hana amma ga mamakin su sai ga abban na cewa "Allah ya taimake ki jiddah, Allah ya tsareki. Dama kowa ya san fatima ba ita tayi kisan nan ba fatima ba za takashe khalifa ba. ***** Daga wanna rana rayuwar Jiddah ta kasance a boye babu wanda yasan tana kano sai 'yan gdansu har zuwa ranar da kotu za tazauna don yanke huku ? cin karshe tunda dai wadda ake zargi ta amsawa kotu karara cewa ita tayi kisan. A ranar fatima fuskarta ba tashin hankali sosai idanuwan ta ba hawaye sai dai jawur dasuka yi. Yau kotun ta cika makil, 'uyan'uwan fatiman har wadanda basu taba halartar kotun ba yau sai da suka zo. Ummi na zaune kusa dasu inna kamar yadda tasaba kanta na kasa. Fatima na tsaye kan minbarin amsa kara bayan mai karanto kara ya karanto. Kafin kowa yace komi sai akaji barrister abbas ya tashi ya nemi izinin magana. Alkalin yace "yana da damar yin hakan, yayi godiya sannan yashaidawa kotu cewa yau ya zo da babbar hujjar da zata gamsar da kowa cewa ba fatima ce tayi wannan kisan ba, aka bashi izinin yagabatar da hujjarsa. Wata kofa ce tabude jidda ce tafito, lamarin dayasa kallo yakoma kanta ana shirin ganin abinda zai faru, itama fatiman kallon jidda kawai takeyi cike da mamakin lamarin kamar yadda fuskar kowa a kotun yanuna ckin wadanda suka san jidda, kowa ma knan ballantana babbar aminiyarta ummi. Barrister abbas ya gabatar wa da kotu jidda da kuma rokon kotu tabawa jidda daman gabatar da bayanin datake dauke dashi, ake ce duk za a iya yin hakan. Bayan jiddah ta yi sallama tafara da fadin "Ina gdan da nake zaune birnin london wani yamaci naji wayata na ringi ? g ina dakkowa naga nomban babbar aminiya ta ummi, hakan yasa nadaga dasauri muka gaisa na tambayeta labarin gida da rayuwa. Tace "komi lfya jiddah, sai dai ni ina cikin matsanancin tashin hankli wanda yasa rayuwat ma gaba daya ta fita daga raina. Nace "Subhanallahi me ke damunki kike fadin haka ummi. Tace "eh to jidda a iya saninki dai kin san tun tasowa ta ma'ana lkacin da na mallaki hankalin kaina babu abinda yake barazana da duk wani farin ciki na rayuwata wanda yawuce dr. khalifa ko ? Na amsa mata "eh na sani ummi. Tace "To dr. khalifa shi ne matsala ta ko kin san cewa zancen auransa da fatima ya tabbata. Nace "to kiyi hakuri mana ummi, ni dai na san duk abinda ke faruwa Allah ne yahukunta hakan zai faru sai dai kiyi hakuri domin kuwa lamari na Ubangiji yadda yakaddara haka zai faru, cikar imanin musulmi yadda da kaddara cikin abinda yayiwa mutum dadi ko akasin haka. Ummi taja dogon numfashi tace "Jidda kina nufin in hakura da dr. khalifa ? duk lokacin dana bata ina jiran dawowarsa daga grmany ya tashi a bansa knan. Nace "Bai tashi a banza ba idan har za kiyi aiki da shawarar dazan ba ki, abinda nake so kigane shi ne idan zuciyar mutum tadamu da son wani abu kuma bai samu ba yadan gana ga Allah yayi hakuri, yakaddara cewa Allah ne bai kaddara abin nan da rabonsa bane to Allah zai dubi niyyarsa ya musanya masa abin nan da wanda yafishi, don a lokuta da dama mukan so abunda ba alheri bane garemu, abinda nakeso inkaiki gareshi ummi shi ne ki kaddara dr. khalifa ba rabonki bane a bisa abinda Allah ne yakaddara ba wani ba, domin wani ko wata bai isa ya kwace maka abinda Allah yakaddara rabonka bane, in dai kin yarda da haka to saikiyi hakuri na san abinda ciwo amma in kin daure kin yi hakuri don Allah, zai miki maganin damuwar ki, ance idan so cuta ne hakuri magani ne. Ummi taja dogon numfashi tace "jidda hakika shawararki itace akan hanya anma wannan hanyar binta ba zai yiwu ba idan nabita mutuwa zanyi. Nace 'Haba ummi ya ya za ace wanda yabi hanyar gskiya yamutu. Tace "jiddah ba zan taba iya hakuri da dr. khalifa ba idan kuwa nace zan hakura dashi to mutuwa zanyi. Nace "To ni dai kuma ban san abinda zan ce miki ba ummi ba ni da abinda zance sai dai kiyi &akuri. Tace "Ba zan yi hakur ba jiddah na yarda na rasa dr. khalifa amma yadda na rasa shi sai dai kowacce mace tarasa shi, babu macen da za ta moreshi. Na ce "ummi me kike nufi da fadin haka ? Kai tsaye tace "Kashe shi zanyi. A nan ne jidda tayi shiru. Yayinda jama'ar kotu suka rude da hayaniya ana fadin "Lahaula" wasu na salati, sai da aka tsawatar sannan kowa yai shiru. Mai shari'a ya dubi jiddah yace "kotu ta ji abinda kikace, akwai karin bayani ko shi knan hujjar ta ki ? sannan kuma akwai shaidar da za ki tabbatarwa da kotu cewa kunyi wannan magana da wadda kika kira ummi. Ta gyda kai tace "Ina da kwakwarar hujjah ya mai shari'a. Cikin rudani na tambayi ummi "kashe shi za kiyi ? Tace "Abinda kunnanki yagaya miki shi nake nufi tare da kara tabbatar miki da hakan kar ki dauka da wasa nake...... Na katseta nace "ummi an taba irin wannan maganar da wasa ? Tace "Yawwa gara da baki wahal da kanki gun shakkar abinda nafada ba. Nayi ajiyar zuciya nace "ummi meye dalilin da yasa za ki furta wannan maganar mai tada hankali ? Tayi dariya tace "na gaya miki idan har na rasa khalifa to sai dai kowa yarasa shi har iyayensa da kowa nas. Nace "amma lallai yau ummi na tabbatar ba ki da hankali kuma ba ki da tunani. Tace "in dai akan son dr. khalifa ne ba damuwa duk abinda za ki kirani kinyi dai dai. Idanuwana a makance suke babu abunda zan hango illa abunda nasa gaba zan aiwatar wanda shi nake ganin zai bani mafita, haka kunnuwana a toshe suke ba zan iya sauraron kowani nasiha ko gaskiya ba da ace zan vi hanyar gskiya wannan hanyr da kika nuna mini ba zan kauce mata ba tunda hanya ce ta hakikanin gskiya. Na marairaice murya "ummi bakin ki ne ke furta wannan kalma na ta'addanci ki ji tsoron Allah kidaina fada ni har kin sa tsoro ya kamani. Tabushe da dariya tace "kidaina damuwa jiddah babu wanda nataba fadawa wannan maganar sai ke, kuma na gaya miki ne sbda ke din sirrina ce babu maganar da ba zan iya gaya miki ba duk nauyinta kuwa. Nace "meye amfanin gaya min din tunda na ba k8 shawara kin ki dauka, har da bakinki kince abinda nafada gaskiya ne kiyi wa Allah ummi kiyi hakuri da dr. khalifa kada soyayyarsa tasa ki haukace, don ni na fara zargin kin samu tabin kwakwalwa ne, lfya kalau kike ba za kidinga furta wannan mummunan lafazin ba. Tace "Lafiya ce ta sani furta wa kuwa jidda zan kuma aikata. Na ce "to meye laifin khalifa don bai so ki ba, ana soyayya dole ? ke yanzu za a tursasa ki son wanda ba kya ra'ayinsa ? Tace "Nima bance miki dr. khalifa ya aikata min wani laifi ba, zan kashe shi ne don kowa yarasa shi sbda sun nuna min rashin tausayi shi da iyayansa sun san ina son khalifa amma lokacin daya dawo daga germany ya rikice akan cewa fatima yake so sai suka watsar da komi ba sa kallon kowa sai dansu suka fifita bukatar sa akan ta kowa aka bashi fatima sbda gata ana bukatar farin ckinsa, idan har khalifa zai kasance ckin fari ciki to basu damu da kowa ba da komi ba wannan ne dalilin dayasa zan kashe shi kowa yarasa. Nace "kai lallai ummi kin cika mara hankali, to na ji za ki kashe shi ba kya tsoron kema kar a kashe kin ? kinsan fa hukuncin wanda yai kisa kashe shi akeyi ko bakisan da haka ba. Dariya sosai tayi tace "na sani mana jidda ai ni mutuwa hutu ce gareni da akan rashin khalifa, ke bari in gaya miki wani abu matukar ina cikin duniyar nan ba zan bar khalifa yarayu da wata diya mace ba ne ko zan

Chapter 16 of 19