Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kula da hakkin makotaka yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki dansa ba. Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi tsammanim hana khalifa fatima nake son yi. Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi nazari na sawa zuciyata hakuri. Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba daya, na bawa khalifa fatima. Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba. Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba Allah na gani xuciya b dadi . Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai kaddara matarsa bace. Tace "to malam yanzu ina musbahun? Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi ba nake ta kiranta bata shiga ba. Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta? mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda ace yarasa? haba ai abin da ciwo. Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar burinta akan dr. khalifa xancen ya kare. Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri. Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi yanzu? Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni. Yace "Subhanallahi *in sha magani? Tace "yanzu dai zan sha. Yace "zan iya zuwa in ganki? Tayi shiru, yace "ko akwai matsala? Tace "Gani nayi ba ka da lfya. Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure damuwa ta ta kai matakin data kai amma da yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin ki ba. Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo gdan kuma zan fito zaure kaganni. ***** A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa knan za a daura auran khalifa da fatima nan da kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya ,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan uwa a waya yana shaida musu batun daurin auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta. Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin al'amarinsa to karya damu da surutun mutane. Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai ba. Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki karba don kada mutane su ce ya yi son kai? A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan yafara cika da mutane maza da mata yan taya murna. Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu, Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen auran gadan gadan. Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata da abinda take so a zauna lfya, idan har muka hakura da khalifa to mata muka rako duniya, wannan dogon lokacin damuka dauka muna nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma gun malam. Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba. Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi mamakin aikin malam, ke de muje muji ta bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa miyar can yunwa nake ji. Ummi tace "ni don haushi ma ko yunwa ba ta damuna. ina mamakin son kan da ake nunawa kowa akan khalifa amma ta watsar da komi ta kanta kawai take ko kunyar idona ba ta ji. Hajiya tace "duk ki kyalesu son zuciya bacinta da sannu dukka za sugane kurensu. Ummi ta tashi tashige dakin hajiya ta tsaya a gaban madubi tana karewa kanta kallo tare da tuno siffofin fatima a idanuwanta tajinjina kai tare da ajiyar zuciya tace "ba komi. Sai bayan sallar isha'i suka isa gdan malam shima yana mamakin ganinsu a wannan lokacin ya san ba lfya. suka baje masa bayanin komi. Unmi ta marairaice tace "Don Allah malam kataimakeni xan rayu ckin bakin ciki mai tsanani idan narasa dr. khalifa dole in yi kishin fatima domin ta san sirrina ta san abinda ke ckin zuciyata, ko zan hakura dr. khalifa yarayu da wata diya mace ba dai fatima ba, na amince in rasa shi amma kada wata ta mallake shi. Malam yabushe da dariya yaja ra'ayinsu ya fara zane zane yana bajewa lokaci mai tsawo suna kallonsa sannan yadago kai ya dubesu yace "haba ko da naji ai uwar Khalifa ce tashiga malamai aka tsare mata jikin khalifa don kada wata macen tasamu damar asirce shi ta rabata da shi, tunda tasan yammata za su so shi da yawa ita kanta fatiman don soyayyar da yake mata ta ra'ayin kansa ce shi yasa duk ayyukan da muke jifansa dasu ba su tasiri akansa, to amma ba komi akwai aljanin da zamu hada shi da shi sai yayi tasiri a kansu shi da fatiman kuna zaune za kuga ya tsaneta hankalinsa ya dawo kan ummin, amma sai an sayi sa babba wanda za a yanka shi a yi aikin a kan sa aiki irin wannan karfi gareshi sai an yi yanka. Ganin sun yi jim yasa yaci gaba dayi musu dadin baki tare da kwadaitar dasu amfanin aikin idan an yi, yace "wa kukaga ya ji dadi ba tare da ya sha wahala ba, duk wadannan abubuwan tarihi za su zama idan Khalifa yazo hannu sai ya baku tausayi ku dai ku daure. Suka dawo gida suna tattauna yadda za su nemo kudin sa, sun yi ammana aikin malam zaici, ummi tace "Hajiya dole ne in saki jiki wurin gudanar da al'amarin bikin nan xan nuna kamar bbu wani avu a zuciyata xa ayi komi dani, amfanin hakan shi ne dan in samu kudin da za muyi amfani dasu. Hajiya tace "Lallai kin zo da dabara, idan har kika nunawa khalifa cewa kina son auran sa da fatima komi za musamu a jikinsa da abbansa, kin ga knan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya. A DAREN FARKO 31 Ana ya gove daurin auren fatima da khalifa wasikar musbahu ta iske mallam inda yake shaida masa cewa kada su daga hankalinsu a dalilin rashin ganinsa ya kauracewa gdan ne don ya samar da zaman lfya da walwala yayin bikin fatima, a cikin wasikar yace. "Malam idan naci gaba da zama kana ganin damuwata za ku dinga jin zafin fatima yayin da ni kuma zuciyata ba za ta taba yi min dadi ba in dai yakasance kuna jin ahushin fatima a sbda ni da ace da ace zan iya shanye damuwata da zan dawo amma hakan hakan ba zai yiwu gareni ba, zuciyata ba ta da wannan karfin. Baba da inna ina rokon ku yi hakuri don Allah ku dauki wannan al'amarin a matsayin kaddara kada kuyi fushi da fatima, fushinku matsala ce babba ga rayuwarta ina nan ina ta mata fatan alheri, insha Allahu da zarar an gama bikin an kaita gdanta zan dawo. Sun ji tausayin al'amarin kwarai da gaske sai dai ba yadda za suyi al'amarin kaddarar nan dai da kowa ke fada itace dole ayi hakuri a karbeta, surutun da ake gudu shi ake tayi a cikin unguwa da dangi, kwadayi kwadayin abin duniya shi ake tafada musamman lokacin da sanarwar daurin auran ta cika gari ta hanyar kafafan yada labarai dake arewacin kasar nan ba ma nan kano kadai ba tare da sanarwar za ayi gagarumar wlima bayan daurin auren da yamma amma na maza zalla,tuni aka cikawa malam gdansa da nau'ikan kayan abinci na alfarma wanda za ayi amfani dasu a gun bikin, hatta nama kala kala aka kawo, kayan da amarya za tasa lokacin biki mama da anty sadiya suka tsara mata su gun kwararrun telolinsu dake tsara musu dinki, kaya ne msu tsadar gaske haka dinkunan sun sha kudi amma fa sunyi kyau sun dace da amaryar, kayan lefene suka ce sai an gama hidimar daurin aure ango da amaryar za su tafi da kanta za ta xabi irin kayan da take so da kanta. Anty sadiya ta hurawa mama wuta akan lallai su za su gyara amarya tun daga kan fatarta da abubuwan da ake sha masu kawo ni'ima ga amarya, mama tarike baki tace "sadiya wannan ai na su ne na iyayanta da yan uwanta ina dangin miji ina gyaran amarya. Sadiya tace "Tabdijam ai kuwa mama anan ne ma yadace ki yi gyaran da hujja, me yasa kikayi mata a baya lokacin da za ta auri musbahu, kika gyara don dan wani ma ballantana na mu, ai ajiye kunya za muyi mi tattalin farin cikin danmu zamanin duhun kai ya wuce ina innarta za ta iya irin wannan abub tana fama da kunya. Mama tayi dogon tunani taga gaskiyar fa sadiya barin kashi a ciki bai maganin yunwa, musamman yadda taga khalifa yana cike da tsananin farin cikin auran daya samu ko kawaici bai iya yi. Lokacin da ummi ta iso gdan da safe tashaida mata cewr tana son tadan yi dabarar da dan ja hankalin fatima tadawo gdan nan tazauna a yau, duk abinda aka fada akan fati sai ummi ta ji tsigar jikinta ya tashi, sai dai bata bari a fahimci damuwarta ta saki ranta sosai, a wannan lokacin ma fadada fara'arta tayi tace "Ba damuwa mama ai ke ce uwar amarya uwar ango mu kuma mune kirjin biki. Bayan sun gama cin abinci tanifi gdansu fatiman ta iske su ita da ango dr. khalifa a soron gdan suna hira, tarike baki tana murmushi tace "to ai dai aski ya zo gaban goshi yaya khalifa meye na mannewa anan? Ni na dauka ma ka fita. Ya bata rai yana harararta yace "ke wai ni abokin wasanki ne xan dauki mataki akanki idan baki shiga taitayinki ba. Tace "a'a yi hakuri kamaida wukar ni dai katayamu murna Allah yasa rakiya tayi nisa. Suka bushe da dariya gaba daya ita da fatiman tawuce cikin gida tana fadin "Bari mugaisa da inna kafin kugama. Khalifa ya matso kusa da fatima yana dan rausayar da kai fuskarsa dauke da murmushi yace "Wallahi fatima har na rasa wacce hanya zan nuna miki soyayya duk abin da nayi miki don in tabbatar maki da soyayya sai in ga ya yi kadan matsayinki ya wuce nan. Ta kwantar da kanta a jikin bango tana kallonsa, shadda ce a jikinsa ruwan kwai, iya guiwa rigar ta tsaya masa ta dan matse me jiki, fuskar nan fes fes tamkar kullum kyau ake kara masa, bbu wani da namiji da fatima take tsayawa tamasa kallon kurilla sai jan gwarzanta Abbubakar saddik, sbda ahi take kallo taji sanyi a ranta, duk damuwar datake ciki in dai za taga khalifa sai taji sanyi a ranta kuma sai taji lallai ta gamsu ta ga da namiji cikakke wanda in dai ka kalleshi ka san ka ga da namiji. Khalifa yaci gaba da fadin "Fatima Allah ne yayi ke rabona ce shi yasa nadawo gida a dai dai wanna lkacin, godiya nakewa Allah daya ba ni ke, domin da na rasaki ban san halin dazan samu kaina ba fatima. Wani irin kallo take masa tana dan lumshe ido tana budewa tare da marairaice fuskarta domin za tayi kuka, lamarin daya dagawa dr. khalifa hankali sosai yakasa rike kansa yakara matsowa daf da jikinta yakai bakinsa kunanta yace "Don Allah fatima zo mu shiga dakin nan in dan ji dumin jikinki zuciyata za ta fashe yanzu. Tayi wal da ido ta waiwaya gaba da baya ba kowa. Ko me yasa bata iya musu da dr. Khalifa tana sane dacewa bukatarsa gareta bata dace ba amma ba za ta iya kaucewa abin da yake so ba, sai kawai tabishi suka shiga dakin musbahu wanda yake zauran gdan, dasauri ya rungumota sannan yayi ajiyar zuciya mai karfi yayi mata kiss, ya saketa yace "to zo ki shiga gida. Mamaki yasa ta tsaya galala tana kallonsa, yakama dariya yace "ai dama ba wani abu mai yawa zan miki ba soyayya ce ta yi mini yawa, shi yasa idan idan ina gabanki bana iya jurewa, ki yi hakuri daga gobe idan Allah yakaimu na zamo mijinki za ki ga abubuwa da dama a tare dani, kada kidamu soyayya ce wadda za takasance abar alfahari gareki, sai kinyi tsammanin kin fi kowace mace sa'a a duniya, zan tabbatar miki ina sonki, zan baki kaina kiyi yadda kika ga dama dani fatana dai kiji tsoron Allah, kiyi min adalci kada kiyi amfani da wannan damar ki wahal dani, kiyi hakuri mu zauna lfya shi ne kadai abinda zai sa in samu farin ckin rayuwata. Babu abinda fati ke iya ce masa sai kallo da ido, abubuwan datake ji game dashi a zuciyarta ya fi karfin ta iya fda masa da baki sai dai tabarwa zuciyarta, ita dai ta san tana son dr. khalifa kuma in dai haka soyayya take hakika masoya suna fama da wahala, meye wahala? wahalar ciwon so daban ba kamar kowacce wahala bace, in da wahalar take shi ne in dai mutum bai ga wannan masoyin na sa ba to zuciyarsa na cikin fitina da garari. Yarike hannunta kam kam yayi mata kiss, sannan ya saketa ya fice, ita kuma tashiga gida ta iske ummi da inna suna hira. A cikin daki ummi tadubi fatima tarike kugu tana murmushi tace "amarsu ta ango in ji ko dai dr. khalifa ya fara latsa jikin ki ne.? Tafiddo ido tace "Ban son sharri ummi. Itama ta tsareta da na ta idon tace "ke fatima kada ki mayar dani yarinya karama mana daga lokacin da soyayya ta tsumu a zuciyar mace budurwa mai tashen kuruciya irinki har takai namiji ya fata tabata sai ta sauya. Duk da kyau da ki ke dashi a baya amma yanzu kina da bambamci, idan ke baki san yanayin jikinki ya sauya ba ni na san ya sauya. Fatima taja doguwar ajiyar zuciya ta zauna gefe tana kallon immi, takasa magana. Ummi ta kyalkyale da dariya tana tafa hannuwa tace "Daman akwai lokacin da za ki iya soyayya ? Tadan yi murmushi tace "Anty ummi ai dr. khalifan ne ya isa a so shi ya hadu. Ummi taji wani dam a jikinta da zuciyarta kamar za ta shaki wuyar fatima tace "tashi ki shirya fita zanyi a yi miki gyaran jiki mun dai makara jibi a cigaba. A kofar gdansu dr. khalifa, fatima ta kafe akan ba za tashiga ba ita kunya take ji, ummi tace "ki rufa wa kanki asiri idan mama taji kin ki shiga fushi za tayi dake, idan ma kin sa wa zuciyarki surukuta da kunyar mama to wahala za ki ba kanki tunda kin san ita wayayyar mace ce bbu ruwanta da irin wadannan abubuwan. A harabar gdan suka ci karo da mama ta yowa baki rakiya, bata amsa gaisuwar fatima ba sai harararta datayi tace ke kin dauke kafarki daga gdan nan wai ke suruka ko ? Fatima ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta gayar da baki, tawuce ckin gda da sauri jin mama tana fadama bakinta cewa wannan ce amaryar khalifa. Ai kuwa suka fara fadin "kai msha Allahu wannan yarinya da kyau take ya more mace ga kyau ga kuruciya. Daya daga ckin bakin tace "to ai ta fishi morewa a wannan zamanin samun namiji irin da na khalifa sai an tona kinga kuwa mu za muyi yanga va mu za a yiwa yanga ba, tunda duk inda danmu yake rububinsa ake. Bayan sun tafi mama tadawo ckin gida ta samesu a falo tare da anty sadiya ,tace "yawwa "yammata a zo a dafa ma abba abinci saura yan mintuna kadan bakinsa su iso. A ? ty sadia tace "mama munada abubuwa da yawa da za muyi fa lokaci zai kure mana. Tace "ai komi za ayi dole a tsaya a yiwa mai gidana abinci in kuma ba haka ba a fasa fitar. Ummi tace "tabdijam ai kuwa mama a yadda muke ji da amaryar nan tamu yau ko tsakar dare za mukai a gdan mai gyaran jikin nan xa mu kai, mai kunshin ma daukarta za muyi mutafi da ita. Mama tace "Lallai abin naku nayi ne sai ku kira angon a waya yazo yabada kudin kunshin don kuwa bbu wanda zai biya masa kudin kunshin matarsa tunda don shi za a yin. Anty sadiya tace "Eh ko zai bayar kema sai kin bayar da wani abu mama kudin fa da yawa. Tace 'Au tausayin khalifa kukeyi ni baku tausayi na ? duk fa abubuwan nan da ake yi ko sisinsa bai kashe ba hatta walimar nan da za ayi idan allah yakaimu goben su dr. hafiz ne suka dauki nauyi da wani abokinsa da sukayi karatu a jamus, to ko nawa yabayar gun kunshi ai ba wani abu ko ? Ummi takirashi a wya tace "yaya kana ina ne ? Yace "mun fita dasu dr. bashir. Tace "To muna bukatar kudin kunshin amarya da gyaran gashinta. Yayi wani mur. ushi yace "Da kyau ummi idan har aka yiwa amaryar nan tawa adon daya birgeni ni nasan kyautar da zan miki ko nawa ne zan biya a yi mata in dai zai yi kyau. A DAREN FARKO 32 Ummi tayi dariya tace "yaya knan in dai batn kyau ne yau za mukai amaryarka in da za ka kasa gane ta sbda kyaun da za tayi. Khalifa ya kyalkyale da dariyan da bata taba jin ya yi ba yace "kia ina ja fa ummi amaryata fa me kyau ce shi yasa na zabeta a cikin dubban mata nace ita kadai zan aura sbda dogon nazari nayi a kanta tun daga lokacin da idanuwa na suka fara gani? ta. Ummi ta cije lebe tare da runtse ido har wani gumi taji yana tsiyayo mata sbda daci da ciwon maganganun da khalifa yake yaba mata, ji take kamar ruwan zafi ake watsa mata a jiki, shi yasa nan take tajike da gumi, a hankali tace "yaya khalifa wai don Allah me yasa kazabi fatima ka fifita ta akan duk wata diya mace, har kabata matsayi me girma a zuciyarka? Yace "Ummi na ji dadin wannan tambayar da kika yimin domin ina son in ji ina fadawa wanda yashafi fatima matsayin fatiman a zuciyata don yarinka karfafa mata xuciya tana sanin cewa dagaske nake. Ummi tace "to in banda abinka daman yaya khalifa ai fatima ta san kana sonta ,yanayin soyayyar dakake nuna mata ne ma yake karfafa mata zuciya take kara sonka tare da sakin zuciyarta ta yarda da son da kake mata, in ban da haka fati za ta iya sanya shakku a zuciyarta game da kai sbda yanayinka. Khalifa ya dan tsuke fuska yace "sbda me kika ce hka ummi? wannan magana ta ki ta ban mamaki don Allah yi min karin bayani. Tace "yaya khalifa a yanayin rayuwa irin na fatima dole taji tsoron sakin jiki dakai idan tana kallon yadda rayuwarka ke tafiya, kayi mata nisa nesa ba kusa ba, amma dayake kana nuna mata soyayya mai karfi ta yarda dakai ta amince akan kana mata so na gskiya, ina ganin idan haka ne ba ka da bukatar wanda zai ci gaba da nusar da fati soyyarka gareta. Khalifa yace "kuma hakane amma duk da haka ina bukatar taimakon ku fatima yarinya ce. Bayan sun yi sallama ummi ta ajiye wayar a gefe tayi tagumi, wannan soyayyar da dr. khalifa kewa fatima tana da yawa, fidda fati daga zuciyarsa abu ne mai wahalar gaske, wace hanya za tabi knan, ta ina za tasamu khalifa? Duk kudin da suke kashewa a gun malamai abin ya ci tura tamkar suna asirin karawa dr. khalifa soyayyar fatima ne, aiki ne ja a gabanta tun da ta tabbatar wa ranta ba za ta hakura tasa ido wata diya macen ta mallaki khalifa ba in dai tana raye. Tayi kwafa tamike tabi fatima da anty sadiya inda suke girkin abincin Abba. Suna ckin shirya tebur khalifa yashigo gdan cikin sauri tare da dr. Bashir, kai tsaye suka wuce tebur din wai dama yunwa sukeji, mama ta harare su tace "ai duk yunwar ku ba za kuci wannan abincin ba. Khalifa yaduvi fatima zai yi magana mama tace "oh za kace mini matarka ce tayi ko? Yarufe baki yana dariya, fatima dai tabar dakin dasauri tanufi dakin ummi suka yi sallar azahar ummi tashigo musu da abinci suka ci a tsatsaye. Kudin da dr. khalifa yaba ummi na gyaran jikin amarya sai da suka firgita su sbda yawansu, ta yi murna sosai domin abin nema ya samu a ranta tace "ka ba da kudin da za a yaki soyayyar fati a zuciyarka da sannu za kagane kuskurenka. Mama ma tadada musu kudin tace su sayo duk abu! uwan dasuke bukata har na su ma kansu ita da anty sadiya. Da yake lamari idan nakudi ne bbu matsala suna zuwa gdan gyaran jikin aka watsar da kowa a ka dukufa akan fatima babban guri ne kamar wata ma'aikata, ayyuka sukeyi kala kala, cikin awa biyu xuwa na uku fatima ta sauya gaba daya ta dauki walwali abin ba acewa komi, anayi ana turara mata jiki da turaren wuta masu kamshi mai sanyi da shiga rai ga humra ana mulkawa. Bayan an gama da nan aka zuba mata kamshi kafa da hannu masu gyaran gashi na tsaye sunayi fatima tazamo tamkar tauraruwa a cikin taurari hatta su ummi da sadiya lalacewa sukayi gun kallon fatima sbda kyau datayi ya wuce misali, ga wani kamshi mai dadin gaske na tashi a jikinta, basu dawo gda ba sai karfe sha dayan dare, tuni angonta yadamu da son ganinta yanata kiransu a waya suna mishi dariya. Yana tsaye yana waya dawasu abokansu yan kaduna yaga shigowar motarsu, yayi saurin katse wayar yace zai kira yafito. Kafin ya iso garesu anty sadiya taja hannun fatima suka shige gida, suka turata toilet wai tayi wanka ba ta son dr. khalifa ya ganta lokaci guda yarikice. Jikin fatima kawai yake bukata, yashiga dakin mama tana zaune tana hada wata zuma da tsimi da za taba fatima. Tayi mai wani irin kallo ganin yanayin daya shigo dashi tace "kai kuwa lfya? Yace "Mama ina fatima? Tayi tsaki tace "wai kanka daya kuwa? da tsakar daren nan kake nemanta me za tayi maka? Ya dan langabar dakai yashiga in ina yarasa abinda zai cewa mama, karshe yace "wai da indomie za tadafa min. "To da basu dawo da ita nan gdan ba fa? Wa zai dafa maka? ta watso mai tambayar tana harararsa tace "to bace min da gani kaje kace ummi tadafa maka. Zaiyi magana tace "Allah idan kana matsa mata xan hanaka ganinta. Yafice zuwa falo abinda yasawa ransa shi ne ba zai iya barci ba sai ya rungumi fatima a jikinsa ko ta halin kaka. Anty sadiya tafito daga dakin dasu fatin suke za tashiga dakin mama ganin shi a tsaya yasa tace "yaya akayi boy? Ya tsareta da ido fuskarsa ba walwala yace "ina fatima? Tace "wanka take. Bai ce komai ba yasa kai dakin ummin, ta bishi da kallo tana jinjina kai tashige dakin maman tazauna kusa da ita tace "in kin gama ki ban in ba ta tasha ba za tasaki jiki tasha a gabanki ba. Mama tamika mata a sanyayae tace "kazar "yar sokoto ta kawo ma yana kitchen idan za ta iya ci ki hada ki bata wannan fitinannan yaron za a sha matsala dashi dole sai an gyara fatima, sai dai ni kam jikina ya yi sanyi wannan soyayyar da khalifa ke nunawa fatima ta yi yawa, kada fa idan sun je aun zauna tayi amfani da wannan damar tadinga juya shi kamar waina. Anty sadiya tace "don Allah mama kada ki sawa ranki irin wannan damuwar kowa da lokacinsa kuma a yanayin fatima ba za tayi haka ba yarinyar

Chapter 14 of 19