Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba tare dayace komi ba, wuri d'aya suka zauna mutane suna mamaki sosai yadda suke ganin iyayan wanda aka kashe da iyayan wacce ake zargin ta yi kisan. wannan abu yana matu'kar baiwa mutane mamaki haka zakaga jama'a na kallonsu, yai d'in ne ma dai hajiya maijidda tasauya fuska sama sama suka gaisa ba wani magana dasukayi fuska tamau ko da aka shigo da fatima ma ko kallon inda take batayi ba. ummi kamar ta fi su kansu fati shiga tashin hankali ta rame ta lalace . Fati na shigowa kotu da ummi suka fara ido sannan tadubi iyayanta dasauri tad'auke idonta xuwa 'kasa tashin hnkali datake ganin iyayanta a ciki ko wannan ma ya ishi mutum tashin hnkli da ba'kin ciki ina amfanin rayuwarta. Yau kam duk abinda zai faru sai dai yafaru lallai sai ta kawo 'karshen wannan zaman kotu. Bayan da akayi abubuwan daya dace ayi aka zauna mai karanta 'kara yakaranto, tuhumar da akewa fati na ta kashe mijinta a ranar da aka d'aura musu aure a daren farko. Mai shari'a Usman Muhammad Bamaina yace "fatima musa kinji tuhumar da ake miki a karo na biyu? " Ta gyad'a kai tace na ji ya mai shari'a, yau kowa na jin muryarta sosai, kuma kowa ya ji dad'in yadda tayi mgana har alamun natsuwa a fuskar iyayanta da 'yan uwanta musamman ummi wadda har tsima jikinta yake a ranta tana fad'in yawea fati gara ki yiwa kanki adalci da iyayanki damu masoyanki.Mai shari'a yace "fatima musa me za ki iya Fad'awa kotu akan haka? ma'ana kin amince ke kika kashe mijinki Dr. khalifa.? Kai tsaye fati taware muryarta tace "Eh ni na kashe shi ya mai shari'a. [5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO 3 Gabad'aya kotu tarud'e da sallalami kowa na fad'in albarkacin bakinsa ,iyayan fati dasu kansu surukan suka rud'e, ummi kuwa hannu tad'ora aka tana fad'in "wayyo Allah na wayyo fati meyasa kikace ke kika kashe Dr. khalifa bayan ba ke kika kashe shi ba. Mai shari'a yayi tsawa akayi tsit sai dai kukan 'yan uwan fati da ba ya 'karewa, ita kuwa fatin yau tana tsaye 'kyam ko gezau gadukkan alamu zuciyarta ta fara soyewa, idanuwan amma ba kuka take ba zafin zuciya ne, ba ta son takalli iyayanta taga mummunan tashin hnkalin dasu ke ciki, dama chan ita mutum ce mai tsananin tausayin mutane balletana iyayenta. Mai shari'a yace "fatima kotu tanason kiyi mata bayanin dalilin dayasa kika kashe mijinki a daren tarewarku. Fati tace "ban san dalilindayasa kika kashe mijinki a daran tarewarku". Fati tace "bansa n dalilin dayasa nakashe shi ba, ba abinda nao na zai iya furtawa a kan haka ya mai shari'a ina ro'kon wannan kotu mai alfarma Data taimaka min tayanke min hukuncin kisa a yau in bar duniyar nan inhuta, ba na son bugawar da zuciyata keyi yazamo sanadin mutuwata na fi son a yanke min hukunci dai dai da laifi na. Tanumfasa tana kallon al'kalin daga bisani tad'auke idanunta daga kansa zuwa kan jama'ar dake kotun, gaba d'ayansu su ma ita suke kallo kowanne da abinda zuciyarsa ke sa'kamasa game da ita. Tayi shashe'kar ajiyar zuciya tace "iyayena da 'yan uwana da dukkan masoya na ina ro'konku don girman Allah kuyafe min wannan yanayi dana sa ku nadamuwa sannan kuyi min addu'a rayuwa ta fita daga raina minti d'aya ba na son in 'ka ra yi a duniya na fi son inbi mijina. " Tayi shiru kamar yadda kotun ma tayi tsit kai ka ce ba kowa a kotun, al'kali yana 'yan rubuce rubucensa, haka a 'bangaran lauyoyi wasu suna rubutu wasu shiru kawai sukayi suna kallon fatima. Taci gaba da fad'in "ya mai shari'a a karo na biyu ina ro'on a taimaka a yanke min hukunci daidai da laifina na amsa laifina ni ce nakashe mijina". Wani daga cikin lauyoyi yami'ke yanemi izinin magana daga gun mai shari'a yace kanada daman magana. Yayi godiya yadubi fatima yace "sunana barrister Abbas Mukhtar inason kare wadda ake 'kara sbda na fahimci ba ita tai kisan ba ina nufin fatima musa ba ita takashe mijinta Dr. khalifa ba ina ro'on wannan kotu mai adalci data ba ni damar yin cikakken bincike a kan wannan al'amari, kuma inason a ba ni damar dazan yiwa fatima tambayoyi akan abinda ake tuhumarta dashi. " Mai shari'a yace "kanada damar yin haka. Yayi dariya yana d'an murmushi ya'kara maida fuskarsa ga fatima wadda itama shi take kallo fuskarta a tsuke, yace "malama fatima musa 'karfe nawa aka kaiki gidan mijin kuma a wace rana ce. " Fatima tayi shiru kamar ba da ita ake magana ba, Barrister Abbas ya'kara maimaita tambayar tare da ro'kon kotu data tursasa fati tayi magana". Mai shari'a yayi hakan amma Fatima cewa tayi "nagode da kake burin taimakona a bisa halin danake ciki, sai dai inason kayi ha'kuri gaskiyar magana ba zan iya ba ka amsa ko d'aya ba a bisa tambayar dakake min sbda ba so nake in ku'buta daga halin danake ciki ba, wanda yake bu'katar lauya shi yakeson yatsira nagaya muku ba na bu'katar rayuwa dan Allah kuyafe ni. Mai shari'a Usman muhammad Bamaina yadubi wani dogon d'an sanda dake tsaye gefe yace "Za a gwada 'kwa'kwalwar fatima don mu tabbatar da mai hankali muke shari'a, idan munyi zama na gaba za mu ji sakamakon sannan mud'ora a inda muka tsaya. Daganan aka d'aga 'karar zuwa mako biyu idan Allah yanuna mana,amma kotun ta ba wa 'bangaran lauyoyi guda biyu damar suyi duk binciken su akan yadda al'amarin yakasance don ba da kariya dawadda ake zargi. Yau ma kamar wancan karon kotun ta tashi da hayaniya kowa na fad'in albarkacin bakinsa akan kafiyar da fati tayi a shari'ar mamakin da take bawa yawancin mutane shi ne tayaya za ayi mutum yace shi ya fidda rai kwata kwata da rayuwa mutuwa yake muradi, wasu suna ganin wannan ya isa kowa ma ya amince ba ita tayi kisan ba, yayin dawasu ke ganin dan ace ba ita bace shi yasa tasallama tami'ka wuya, idan ba ita bace waye? Gida su biyu kachal ba kowa d'aki a kulle su biyu in har ance ba fati takashe Dr. khalifa ba to sai dai ace shi yakashe kansa, hatta hajiya Maijidda mahaifiyar marigayin dayawa daga 'yan uwansu abinda suke gani knan wannan kukan da take abinda suka d'auke shi kukan munafinci ne kawai. A harabar kotun kafin sutafi gaida malam musa ya tsaida barrister Abbas yana masa godiya a bisa 'ko'karinsa nakare 'yarsa, barrister yayi murmushi yace, "Ba komai kada kadamu baba na yi wannan ne domin Allah da tsananin tausayin da fatima ke ba ni tun randa aka fara tsaida ita a gaban shari'a na tabbatar ba Ita tayi wannan kisan ba, duk wanda yakashe Dr. khalifa na gida ne wanda yasan sirrin gidan insha Allahu da izinin Allah zamu gano ko waye,sai dai inason kataimaka min fatima tadinga ba da amsa a kotu sannan xanje inganta kutaima ka min tayimin cikakken bayani duka tambayoyin da zan mata dan insan yadda zan 'bullowa al'amarin. Malam yace "To ni na rasa me yasa fati take tsuke bakinta komi sai tace ba za ta iya fad'a ba sbda rayuwar ta fita Daga ranta. Barrister yayi murmushi yace "bako mi tsananin damuwa ne yasa take fad'in haka, matsayinku na iyayenta ku yadace kulalla'bata tafad'i yadda akayi. Malam yayi masa godiya mai yawa bayan tafiyarsu malam d'in barrister na xaune a motarsa shi kad'ai yana nazarin alamuran fatima tausayin ta har ya yi masa yawa a zuci.,daurewa kawai yau yayi ya zo kotun tun a wancan zaman da akayi hankalinsa yatashi sosai gameda al'amarin yarinyar, tun lkcn abinda yake d'aga masa hnkali matsalar d'aya matsalar kowama ita ce shirun da fati tayi tana neman mutuwa ido rufe ta 'ki ba da had'in kai ballantana a samu mafita. ********************************************* A hankali ummi tafito daga motar tabi bayan mama zuwa cikin gida, kowanne zuciya ba dad'i , a falo suka zauna gaba d'aya yayin da ita ta dawo dabaya zuwa ainihin d'akin Dr. khalifa na gidan har yanzu mukullan d'akin yana hannunta ita kad'ai take bud'ewa tashiga tunda ga lokacin daya mutu zuwa yanzu, komi na nan yadda yake wani irin 'kamshi mai dad'in gaske yana tashi a d'akin, gaba d'aya kayansa nasawa suna jere a cikin wardrobe gwanin ban sha'awa manyan hotunansa da akayi enlargement d'insu guda biyu na gefe da gefe na gadon ya yi kyau ba na wasa ba. Tazauna a gefen gadon tanasa hannu tad'auki hoton tarungume kam kam idanunta a rufe hawaye wasu na bin wasu zuwa chan ta ajiye tashiga bud'e durowowin jikin madubin hotunan bikinsa da fatima ne birjik musamman ma gun lunching da dinner dayawa yarungume fatin ne 'kam 'kam a 'kirjinsa wasu kuma tare da abokanansa maza da mata. Kan cinyar ummi yaji'ke dahawaye kamar ruwa aka zuba mta a cinya tun ranar da aka kashe Dr. khalifa take kuka amma bata ta'ba kuka irin na wannan rana ba, har sai dataji numfashinta kamar zai d'auke. Ba za ta ta'ba mantawa da abinda yagya mata ba a yammacin lahadin daza akai fatima gdansa wanda kuma a wannan rana ce aka kashe shi bai sake kwana a gidan duniya ba. Yana tsaye a harabar gdansu tare da manyan abokansa biyu wad'ana baida aminai kamar su. Manyan likitoci Dr. Hafiz Bala Muhammad da Dr. Mustapha Abubakar kura, yana tsakiyarsu suna hira, sai ita ummi tafito daga cikin gida tana ganinsu tahau yimusu hoto a wayarta, Dr khalifa yaharareta yace "wai meyasa kike daraina mutane ne ummi ni kikewa hoto? Sai Dr. Mustapha yace "kaima kanada saurin hushi khalifa ko wacce rana idan an maka abu za ka 'bata rai banda wannan rana wadda tazamo ta auranka da matar dataza mo allura cikin ruwa kaine kaxamo mai rabon daka zu'kota. " Dr. khalifa yarausayar dakai yana murmushi tare da lumshe ido yace "ka fad'i gskiya Dr. Mustapha tabbas ni ne na cafko wannan allurar data zamo tamai rabo ce, a daidai lokacin dana fidda rai da ita sai najita kawai a hannuna ,tabbas wannan rana ta dace tazamo ta farin cikina, ranar dazan sadaukar da komi na wa sbda Fatima. " Ummi tay murmushi tace "shiyasa nima nake maka hoto domin ka yi min kyawun daban ta'ba ganin ka yi shi ba a duniya dukda cewa kai d'in me kyau ne kullum kyau kake da ado. " Dr. Hafiz Bala yace "har bayan hoto yanada kyau ma yayi miki kyauta ta musamman ummi." Dr. khalifa yayi murmushi yace "ko shakka babu a wannan rana ina cikin farin cikin daban ta'ba samun kaina a cikin shi ba, sai dai kasan tun safiya gabana ke fad'uwa bansan dalili ba wannan yayi sanadin dayasa tun ruwan shayi danasha rabin cup d'azun bayan d'aurin aure ban iyacin komi a bakina ba. Ummi tayi wal da ido tace "fad'uwar gaba kuma Dr. a irin wannan rana? ni dai na san ko kusa bakayi kama da wanda mace za ta ba wa tsoro ba ballantana ince firgita kayi sbda fatima. Dr. Mustapha ya bugi kafad'arsa yace "wa wannan? ni tunda ake ma gwargwadon bud'ewar idanuna ban ta'ba ganin namijinda yayiwaa mata farin sani irinsa ba, farin ciki ne yayi masa yawa sbda soyayyarshi yasa ma gabansa yake fad'uwa....... " Tunanin ummi yakatse a nan lokacin da mama taturo 'kofar d'akin tatsaya tana kallon ummi kukan datake yabata tsoro ta'karaso dasauri ta kamata takwashe hotunan dasuka ji'ke da hawaye ta mayar, takamo hannunta tafito da ita tarufo d'akin takar'be makullin tace "daga yau ko 'kofar d'akin nan ba na so kisake zuwa, haka kada ki 'kara zuwa kotu ba xa muyi biyu babu ba, mun rasa Dr.khalifa muna cikin ba'kin ciki mai tsanani kema damuwa na neman xama ajalinki to B xai yiwu ba. Cikin kuka ummi tace "Don Allah mama kada kiharamta mini shiga d'akin likita, yin hakan ne kad'ai zaisa zuciyata ta sassauta daga damuwar danake ciki, na rasa d'an uwana ga aminiyata na cikin matsancin zargi na bi duk hanyoyin daya kamata inbi don ganin fatima ta ba lauyoyi had'in kai ta 'ki burinta akasheta meyasa ba zanyi kuka ba mama? mama tayi tsaki tace "ina mamakin yadda ke Da Alhaji kuka d'auki damuwar duniya kuka d'orawa kanku akan fatima shin dakuke cewa batace komi ba me za tace, fatima ba ta da abin cewal shiyasa tai shiru, ko a hankalce kun san 'karyane ace akwai. mutumin da ake tuhuma irin hka ya'ki amsar taimako daga lauyoyi don kawai yana burin mutuwa. kinta'ba ganin wanda yazauna yana jiran mutuwarsa kuma yana maraba da ita, saidai fa in ta zo a kar'beta don ba yadda za ayi da ita. Ummi tasaki hannun mama tazubla mlatla ido muryarta a dashe tace "mama shin kina nufin kin amince fati za ta iya kashe likita? Mama tayi murmushi tace "ummi ummi kiji tsoron duk wanda kika taimakawa. Akoda yaushe idan za ki taimakawa mutum to kitaimake shi kai tsaye don Allah ba wai don zai saka maki da alherin dakika yimasa ba, shi dama mutum bbu abinda yake cika cikinsa sai 'kasa shi. mai butulcewa mahaliccinsa ne ma ballantana ace wani gama garin mutumin don hka ba abin mamaki bane ga mutumin daka d'auko shi daga rana kadawo dashi inuwa shi kuma yaturaka ranar,a cikin mutane mutumin dayake salihi ko mai shiru shiru irin fatima mutane ba sa zarginsa da mugun abu sbda yanayinsa amma Allha (SWT)daya halicci zuciya shi yasan abinda ke cikinsa. Ummi tayi shiru na lokaci mai tsawo daga bisani tace "Mama kina nufin kin amince akashe fatima akan kisan likita? " Tace "ummi ba ni da masaniyar abinda shari'ar za tahaifar, sbda ita shari'a macece da ciki ba wanda yasan abinda za tahaifa sai Allah mudai mun mi'ka kukanmu ga Allah yabayyanar da gaskiya. " Tayi gaba tabar ummi tana binta da ido jikinta yayi sanyi 'kalau, da'kyar tad'aga 'kafa tabita cikin gida. . . [5:08PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO 4 maganganu sunyi yawa a kan abubuwan dasuke faruwa a kotu, wasu sun fara yarda tunda tace takashe Dr. khalifa yayin dawasu har yanzu suna ganin ba'kin cikine yahanata magana dukda cewa su d'inma suana gnin fati ba ta da hujjar da za tasa taja bakinta tayi shiru ta 'ki cewa komi. Kwana biyu a zauna kotu malam musa da mahaifiyarsu fatima da da ummi da Barrister Abbas suka isketa a inda take tsare abisa alfarmar dom mahaifin marigayi Alhaji muhammad amma fa akwai sa idon 'yan sanda guda biyu. Fatima tarusuna tagaida mahaifinta ciwon rai ya'kara damunta sakamakon ramewar dataga ya dad'a yi ya fita hayyacinsa kaida gani ka san yana cikin matsananciyar damuwa da takaici, sannan tagaisa dasu ummi da barrister. Malam yace "fatima. Ta amsa 'na'am baba. Yace "fatima wannan shi ne zuwa na 'karshe dazanyi gunki akan in ro'ki kiyi bayani a kotu idan kinga dama kiyi magana fati idan baki ga dama ba kicigaba dayin shiru tunda kinfi 'bukatar mucigaba dazama cikin tashin hnkali darashin sanin abin yi. A yau na zo ne ba dan in ro'ke ki kiba lauyoyi da al'kali amsar duk tmbayar dsuka bu'kata agunki ba zuwa nayi in ba ki umurni a matsayina na mahaifinki idan ya cancanta kiyi min biyayya kiyi fatima idan kuma ban isa ba kici gabadayin shiru kamar yadda kika saba. Fatima tace "baba idan nayi bayanin zai sauya 'kaddara ne? ko kuwa bayanin na wa zai dawo da rayuwar Dr. khalifa izuwa gidan duniya, baba idan ni ce nakshe Dr. khalifa idan ma ba ni bace Allah SWT ya san haka tunda shi yake ganinmu a lokacin damuke kulle mu biyu acikin d'aki ni da Dr. khalifa, ni dai abinda nakeso ayi amfani dashi shi ne tunda naji na gani na amince ni ce nakashe shi na yi i'kirari da bakina a yi min hukunci dai dai da laifina shiknan shari'a sai a gaban Allah (SWT) wannan itace rana daza a tsage gskia ranar dakowa zaiyi bayanin abinda ya aikata da ga'bo'binsa bama da bakinsa ba kuma itace dawwamammiyar rayuwa wadda va za ta'kare ba har abada. Don Allah baba kayi ha'kuri kada kayi fushi dani akan hka bbu abinda bakina zai iya furtawa a lamarin kisan nan. Ummi tace "fati mahaifanki sun kasance suna masu alfahari dake a bisa biyayya da kike musu, baki ta'ba yin musu dasu ba, ba'a ta'ba samun wata rana da suka baki umurni kika sa'ba ba, meyasa a wannan karon za kisa'ba musu? Ba ki da hujjar dazakice rayuwarki ta zo 'karshe fati, ko kuma dan kina jiran mutuwa shiyasa kike ganin biyayya ga iyayankinya va ta da amfani? To bari in tunatar dake wani abu guda d'aya ance akwai mutumin dazai ta aikin alheri wanda yake share masa hanyar tafiya aljannan sai 'karshen rayuwarsa tazo sai kawai ya aikata wani abu wanda zai kaishi wuta sai ya shiga wuta. Yayin dawani zaita aikata aikin dazai kai shi wuta gab da mutuwarsa siya aikata abinda zai kaishi aljannan saiya shiga janna. Fatima ina ro'kon ki kiyi abinda iyayanki suka bu'kata ba ki da hujjar dazaki sa'bawa umarninsu, ba ki da tabbacin kwann ki ya 'kare mutuwa zakiyi fatima. Barrister kallon fatima kawai yake yarasa yadda xaiyi da tausainta a zuciyarsa, yamatso daf da ita muryarsa 'kasa 'kasa yace "fatima 'karfe nawa aka kaiki gidan Dr. khalifa? Ta amsa 'karfe biyar da rabi Zuwa shida a wannan d'an tsakanin ba'a wuce haka ba. Gaba d'aya sai da fuskokinsu suka nuna jin dad'in had'in kan data fara badawa, barrister yace a wace rana knan fatima? Ta amsa "A ranar lahadi biyar ga watan uku" Ya gyad'a kai yana murmushi yace "fatima suwa dawaye suke cikin motar da aka kaiki? Tayi d'an jim daga bisani tayi murmushi tana kallonsu tace "ummi za ta fini snin suwaye a motar da ka kaini sbda ni fuskata a rufe take ba wanda zan iya shaidawa a lokacin sai dai tabbas na san ina tare da manyan aminai na guda biyu kamar ita ummin da d'ayar aminiyar ta wa Jiddah. Barrister yace "yawwa ko za ki iya tuna 'karfe nawa kowa yawatse acikin gidan aka barki ke d'aya lkacin dakike jiran ango kamar yadda al'adar amare take a ranar da aka kaisu d'akunan mijinsu,? Tace 'lallai kam ba zan manta ba bayan an yi sallar isha'i wuraren 'karfe takwas nadare su ummi da maijidda dawasu 'kannan mahaifiyata biyu kad'ai suka rage a gidan inda mukai sallar isha tare dasu sannan sukayi shirin tafiya suka tafi gaba d'ayansu. Barristr yace "bayan haka waye yashigo gidan kafin zuwan ango dr. khalifa? " Tajima tsit tana nazari tace "gaskiya ba wanda yashigo kuma banji motsin kowa ba ni kad'ai nazauna. Barrister yace "zaman minti nawa kikayi 'kiyasi kafin dai zuwan ango ? Tace "tace ba'ayi minti sha biyar ba naji tsayuwar motarsu shida manyan abokansa guda biyu wad'anda sukayi masa rakiya. Barrister yace "kafin dai zuwan angon ba wanda yakiraki ko da awaya ne? Tagirgiza kai ba wanda yakirani in barda shi angon Dr. khalifa. Me yace miki? "Cewa yayi inyi ha'kuri suna hanya " Ke kuma me kika ce masa? Cewa nayi to Allah yakawosu lfya. Yace "dukda haka bakiji ko da alamar motsi a gidan ba har lokacin da dr. khalifa da abokanansa suka iso. Tagirgiza kai gaskiya babu wani alamun motsin danaji saifa lokacin dasuka shigo. "Su nawa suka shigo. " Barrister yaci gaba da tambayar har yanzu idanuwansa na kanta. Tace su uku wato shi da abokan na sa guda biyu. Yace "yaya sunayensu.Ta amsa "daya sunansa Dr. Mustapha kura d'aya Kuma Dr. Hafiz. B. Muhammad. " Yace kafin auranku yaya ala'karku dasu abokan na sa? ina nufin sun amshe ki a matsayin matar abokin su ko kuwa ba sa yi dake? Fatima tace "Nikam alhmdlh Dr. khalifa da iyayansa da abokansa da yan uwansa ko sau d'aya babu wanda yata'ba nuna min wata 'kyama ko wani abu wanda zai sa ince lallai wane ba ya 'kaunata, daidai gwargwado ina samun had'in kai daga garesu to sai shi kuma abinda yake na nasani mutum yakeda masaniya akai abinda yazamo na bad'ini Allah kad'ai ke da masaniya akansa sa sai dai mubarwa Allah ikonsa". Barristr yace "to fatima za ki iya gaya mana maganar dasuka yi lokacin da za suyi sallama daku a wannan dare? Tace "eh gaba d'aya tunda sukazo nasihohin zaman lfya suke mana bayan hka sun mana addu'o i na neman zaman lfya bayan haka sukayi mana sallama suna mana barkwanci irin na abokan ango ranar siyan baki irin wannan. To daga nan sai me yafaru? Tace "saiya rakasu" Ke kuma kina ina? Ina zaune akan gado ko motsi banyi ba kamar yadda suka sameni, bayan ya rakasu saiya dawo yazauna kusa dani yana d'an zolayata. Barrister yace "dukda haka a lokacin ba wani motsi a gidan sannan shi d'inma bai nuna miki ya ji motsin wani abu ba ko kuma ke kin fahimci wata razana a fuskarsa? " Tace "gaskiya banga komi ba yana cikin nishad'i sosai yadda yakamata ango yakasance a irin wannan dare. " Daga nan fa? Sai yace dani kinga hayaniya tayi yawa a kaina ko sallar isha'i banyi ba nayi 'ko'karin inyi kafin mutaho su mustapha suka daman akan inyi sauri su garin za subari a daran. "Garin za subari? inji barrister yafad'a yanayinsa yasauya. Tace "haka dai yace daganan kuma bai 'kara fad'ar wata magana wadda tashafi wad'annan abokai na S ba yatashi yafita bansan ina yaje ba saiya dawo. Ya yi kamar minti nawa dafita kan yadawo? Tace zaiyi kamar minti goma saiya dawo yacire babbar rigar jikinsa ya Ajiye kan gado yace ya kamata inyi sallar nan dashi kuma inajin yunwa tun d'azu anti take ce min ga abinci na ka sa zama inci sda jama'a gaba d'aya na ji abincin ya fita daga raina ba na sha'awarsa sai yanzu nakejin yunwa,amman bari inyiwa mama waya tasa akawo mana abincin hatta kazar amarcinki ma tana gun mama ita tace za tagasa dakanta akwai tanadin datayi miki a ciki. Duk yayi wad'annan maganganun ne a tsaye yana murmushi tare da daddana wayarsa tahannu yakira maman bayan sun gama wayar sai ya ajiye wayar akan madubi danufin yashiga toilet sai aka kirashi yayi magana mai tsawo dawanda yakirashi d'in sannan yakashe yadubeni yace "idan mutum yana harka da jama'a sai ha'kuri, tashi kema kiyi alwala idan nayi sallar isha'i sai muyi Nafila ko bari inyi tawa a d'akina sai intaho da littafina daganan saiya fice waje Nikuma nashiga toilet na idar da alwala na fito ne na iske gawarsa akan gado. Barrister yagirgiza kai cike da tausayi yace "fatima. " Yanayin fuskarta ba d'ad'in gani sbda tamkar lamarin datake bayarwa yana fama mata wani gyambo nazuciyarta wanda yake mata tsananin zugi a zuci yake rabata da duk wani zaman lfya da walwala a zuciyarta, hatta kallon datayiwa shi barristan lokacin daya kira sunanta ya firgita shi zuciyarsa tabuga yayi mata tsai da ido don yana son taci gaba da bashi amsar tambayoyin dayake mata. Yace "fatima kin kai minti nawa a toilet d'in lokacin da kika shiga danufin yin alwala. Tace "minti kamar goma don na d'anyi wasu abubuwan kafin in gabatar da alwala. To sai kika fito inda kika ga gawar mijinki Dr. khalifa shimfid'e akan gado, haka ne? Tace "eh ina daga band'aki naji motsin bud'e 'kofa sau biyu dakuma motsin bud'e kwaba ko me zan kawo a rainadon na ji wannan motsin, d'auka zanyi shi ne tunda ba kowa a gdan a iya sanina dagani sai shi. Yace "kuma ba motsin gudu? Tace "Gaskiya banji wani motsi wanda yake tabbatar da rashin gaskiya ba ko kusa. Yace "to bakiji 'karar mijin na ki ba ko wani abu da yayi kama da haka a lokacin da za a kashe shi? Tace "nidai banji komi ba yadda nagaya maka naga gawarsa haka nagan shi ba wani abu da na sani bayan wannan. Yace "dame aka kashe shi? Ta amsa "wu'ka ce 'karama. kin ta'ba wu'kar? Tace "eh lokacin danafito daga band'akin hankalina yayi mugun tashi natafi dagudu nad'aga wu'kar daga cikinsa domin wu'kar tana kan cikinsa ne bayan an luma masa sai aka zareta aka d'orata akan cikin na sa nikuma danazo saina d'aga wu'kar shi ne dai dai lokacin da 'kaninsa isma'il ya 'kwan'kwasa 'kofa jin ina ihu innalillahi wa inna ilaihir raji'un saiya danno 'kofar yashigo da food flask d'in abinci a hannunsa wanda mama tabashi yakawo mana. Barristr Abbas yace "fatima lokacin dakika iso kan mijinki dr. khalifa yanada sauran rai ko ya mutu? Tace "dasauran ransa don kuwa har yana d'an juya kansa yana cewa ta kasheni ta kashe ni har lokacin dashima isma'il yashigo d'akin yana magana ganin yanayin da ya iskemu aciki yasa isma'il d'in yawatsar da abincin hannunsa ya isa kan d'an uwansa a gefe ana fad'in, ya ya wa yakashe ka, yakasa hannuwansa daidai bakin dr. khalifan yana cewa don Allag gaya min wadda takashe ka nima yanzu inkasheta. Ban san yaya akayi ba ko shi Dr. khalifan a lkcn bansan waye a kansa yake masa magana ba ne ban sani ba naji Da kunnena dai lokacin Da dr. khalifa ke cewa Fatima ta kasheni, fatima ta kasheni. Fatima tayi shiru zuciyarta na bugawa kamar lokacin abin yafaru, daga barrister har malam da ummi dashi kansa d'an sandan dake tsaye a kansu sun ji'ke sharkab da gumi sbda tsananin tausayi da tashin hnkali. Idanuwan fatima sun 'kafe ba zancan hawaye sai tsananin zugi da rad'ad'i dasuke mata 'kirjinta kuwa kamar zai 'balle dan azabar zafin da yake mata numfashi na fita da'kyar. Tunda al'amarin yafaru yau ne ta iya bud'e baki tabada labarin yadda abubuwan suka wakana. Sun jima zaune shiru tuni lokacin daya dace sufita yawuce shi kansa d'an sandan ya kasa cewa sufita hnkalinsa shima a tashe yake.. Barrister abbas tagumi kawai yayi da tambayoyi a bakinsa, bakin ya yi masa nauyi la'b'bansa sun bushe da'kyar yake iya numfashi tare dacewa, shi cikakken lauya ne Kum 'kwararre mai cin gashin kansa don tuni ya jima da 'kasaita akan aikinsa sbda matakin daya ta ka nakaratu, irin wadannan abubuwan ba bakin al'amura bane gareshi, aikinsu nako yaushe jin abubuwan tashin hnkali amma bai ta'ba fuskantar alamarin dayake tsananin d'aga hankalinsa da ba shi tausayi irin wannan ba, ya damu da mGanar 'kwarai dagaske. Kafin ma yayi mata tmbaya taci gaba da fad'in "Abinda bakinsa ke furtawa knan har yabar duniya, wato ta kasheni fatima, takasheni Fatima. Isma'il yana ihu akansa yana cewa "yaya fatima ce takashe ka? fatima ce takashe ka? bai 'kara motsi ba yaci gaba da jijjigashi ko shurawa baiyi ba, tuni jini yayi faca faca akan gadon. Wu'kar tana hannuna ina tsaye har izuwa lokacin da isma'il yasake shi yafita baice min komi ba, ban ajiye wukar ba sai lkcin da yan sanda suka shigo d'akin wani acikinsu yalulku'be hannunsa da safa yakar'bu wu'kar daga hannuna. Tayi ajiyar zuciya tace "ba wani abu dana sani bayan wannan ,bbu kowa a gidanmu lokacin da aka kashe Dr. khalifa sai mu biyu a gidan ni da shi ni kaina na shaida banji motsin kowa

Chapter 2 of 19