Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da babbar aminiyarta kuma makotansu wato jidda khalifa yashigo tare da sallama fuskarsa a tsuke yake amsa musu gaisuwa yace "ina hajiya? " Jiddah tace "tana gaisawa da ba'ki a sit room d‹in baba. Yace "to idan ta fito kice mama ta ce maganar sa'kon nan zatayi mata waya yanzu dai bai samu ba ni sauri nake ba zan iya jira tafito ba. Bai saurari abinda za suce ba ya fice su ma basuyimagana ba ya ga toh dasuka hada baki suka fada lokaci guda. Bayan Fitarsa jiddah tadubi umi tana murmushi tace "Oh ni tunda nake ban taba ganin mutum mai jin kai da isa irin yaya khalifa ba ko dan yana ganin ya had'u ne. Ummi tayi ajiyar zuciya tace "lallai kam ba abinda yake sashi ta'kama wanda yawuce haduwarsa sai kuma dukiyar mahaifinsa wadda yake takama da ita kina ganin duk tsadar mota khalifa zai hauta da zarar an shigo da mota sabuwar yayi 'kasar nan komi tsadarta abbabnsa zai siya masa ya hau, kuma dan wani karin jin kai da alfahari ma ba zai yawo a mota d'aya ba sai ya jera motoci goma yana tsakiya tare da abokansa yana homa daga bisani ne surutu yayi yawa a dangi da abokan abbansa ya tsawatar masa a kan yadaina fita da motoci da yawa haka shi ne yanzu yake fita da motoci biyu ko uku. Jiddah tace "duk abinda yayi ya yi daidai don ya isa yayin, ni kam yaya khalifa yana matukar burgeni ina mai ba ki shawara ummi in har za ki iya shiga zuciyarsa kada kibari ya subuce miki. Ummi tayi ajiyar zuciya tace "jiddah kin san dai yaya khalifa kuma kinsan yadda rayuwarsa take, nima kinsan gwargwadon wayewata da fahimtarki da rayuwa kina ganin zan iya shiga xuciyarsa ina nufin kina ganin ina da nagartr da zai so ni? Jiddah tace ummi kina da kyau kuma kina da wayewa, meye zai gagareki idan kika bar wannan damar tawuce miki za kiyi nadama. Ummi ta jima tana nazari kanta na 'kasa tace kada kijefa min damuwa a zuciyata kan abinda samuwarsa gareni zaiyi wahala. Jiddah tace "idan kika sa wa zuciyarki damuwa akan samuwar khalifa gareki to lallai wahala zai zame miki, yayin da idan kika sa wa zuciyarki abu ne mai sauki mai sauki ne kada kidamu da jin kan yaya khalifa ko haduwarsa da takamarsa kina da hanyar da za ki iya mallakar zuciyarsa cikin sauki mata irinmu da ba mu da alaka ta jini tsakaninmu shi ne zai mana wahalar samuwa ke kuwa uwa daya uba daya iyayanku suke gdanku gdansu ne haka gdansu gdanku ne, kitashi tsaye ki mallaki miji na fita kunya mijin da za a iya shiga dashi ko ina a kalleku bayan kyau ga dukiya ga uwa uba ilimi ba jiya kikace min zai tafi germany karatun likita ba? Cikin sanyin murya ummi tace "jiddah na yi mamakin wannan magana ta ki sai jace kin shiga zuciyata, wlh jiddah tun kafin in mallaki hankalin kaina insan waye namiji insan menene so nake matukar so da sha'awar yaya khalifa duk sanda na ganshi nadinga kwatantashi a matsayin mijina abinda yas nakasa kusantar kaina gareshi sbda miskilancinsa kina gani ko gaisawa akayi sama sama yake amsawa, ban taba gaida khalifa ya yi min murmushi ba al'amarin har tsoro yake ba ni, amma khalifa shi ne nakema son dana tabbTar babu wani d'a namiji da zanwa ko da rabin son danake masa, tabbas a wannan rana kin fama min inda ke min 'kai'kayi a da na kwantarwa da zuciyata soyayyarsa dake raina amma yau kin tayar min da ita insha Allahu sai inda karfina yakare xan nemi soyayyar yaya khalifa bakin raina zanyi duk abinda zan iya don ganin na mallake shi ba zanyi sakaci wata d'iya mace tarabani dashi ba ko ta halin 'ka'ka. Tami'ke a hankalin ta tsaya gaban madubin dake bango tana kallon kanta tun daga sama har kasa, doguwar rigace a jikinta wadda tafito da zahirin suffar jikinta, gashin kanta ya sauka har gadon bayanta, kamar yadda take doguwa mai kyau siffa tana daga cikin abinda yake dauker hankalin maza tare da ummi shi ne gogewar fatarta, ba fara bace 'kal 'kal amma tana da haske sosai, fuskarta tanada daukar hankalin mai kallonta, sannan tana da daukar dressing in dai za tasa kaya sai sun amsheta sbda ba zai yiwu tasa kayan dabasu dace da kalar jikinta ba, haka duk d'inkin dazatayi sai ta tabbatar zaiyi mata kyau sbda ita Allah ya yi ta da iya zabar kaya dan shi kanshi telanta daban ne shi yake mata tsala tsalan dinkuna nagani, duk kayan daza tasa sai an tabbatar an yi matching dan a birge ai kuwa tana birgewar, ko a salon iya tsara magana aka tsaya musamman ummi za tatafi da imanin mutum yatsaya yasaki baki yana kallonta yadda za kaga tana tsara xance daya bayan daya mai shiga cikin wannan ne yasa takeda mutane a gida da makaranta, hatta malamansu sun santa kan tsananin iyayinta da son gayu duk kudin da hajiyarta tasamu akan sayawa ummi sutura mai tsada da kayan kwalliya suke tafiya kowanne kya sai an hada mai mayafi, takalmi da fashion don ace dai an yi kyau. Ummi tana matukar jin kanta ba kowani d'a namiji take kulawa ba duk da dumbin masoyan dake nuna mata zahirin kauna ba wani d'a namiji daya taba burgeta sai yaya khalifa. ************** Jidda ce kawai ta 'kud da 'kud kuma aminiya ga ummi tun suna yara ba ajin kansu kasancewar katanga ce kadai taraba gdansu kafin rasuwar mahaifin ummi baida abokin shawara kamar aminin daya wuce babansu jiddah shi ne dalilin dayasa zumuncin na su yakara kwari, duka makarantun dasuke zuwa guda uku a kowacce rana duka ajinsu daya kullum tare suke wuni babu abinda yake rabasu sai bacci, kullum shawararsu daya banbancinsu shi ne jiddah ta fi ummi tanada tsiwa da jin kai da raina mutane, yayin da jiddah ke da girmama mutane da gudun zuciya. Iyayan jiddah hamshakan masu kudi ne su biyu suka haifa daga ita sai yayanta Habibullah wanda yake kasar england karatu, itama jira suke takammala secondary su fidda ita kasar waje tayi karatun ta na jami'a dukda cewa ta ce babu inda za taje sai fa in za a hadasu da aminiyarta ummi, lokacin data fadi haka mominta ta yi murmushi ne tace "jiddah manya, jiddah aminiyar ummi, idan har ummi da iyayanta sun amince za ta outside karatu mai zai hana dady dinta yabiya mata insha Allahu indai kinga ummi baku tafi tare da ita ba ,ita ko iyayanta suka ce ba za ta ba. Cikin tsananin farin ciki jiddah tashigo gdansu ummi dagudu ta isketa cikin dakin hajiya tana kwance bisa gado tana karatun littafin hausa tafisge littafin ta watsar tace "Albishirinki. Ummi ta lumshe ido tace "kina burgeni jiddah sbda koyaushe ina ganin ki cikin nishadi da wahala mutum ya fahimci wata damuwa a zuciyarki. Tace 'hakane ummi ban cika sa wani abu a azuciyata ba ballantana yadameni ina daukar raywa da sauki dan kada in dami zuciyata zuwa nayi in gaya miki insha Allahu idan mun gama secondary tae za mu tafi outside karatu. Ummi tayi shiru batace komi ba fuskarta ko walwala babu ballantana tanunawa jiddah ta ji dadin maganarta, itama jiddar gimtse far'arta ayi tace "ummi yaya ni dana taho da batu mai dadi gareki ina mai gaggawar yi miki albishir sai inga fuskarki ta ahiga damuwa kamar wadda tazo miki da labarin tashin hankali ? Ummi tayi doguwar ajiyar zuciya tace "jiddah ba wai farin cikine banyi ba ba yadda za ayi ayiwa mutum albishir irin wannan yakasa farin ciki sai dai inason kiyi hakuri jiddah na gode kwarai da gaske da kaunar dakike min wadda tasa har kike jin ba za ki iya tafiya wani gari kiyi rayuwa babu ni ba, iyayanki suka amince miki akwai haka tare Dacewa kudi za su kashe ba na wasa ba, babu inda za ayi haka sai in akwai kauna mai yawa kuma kauna wadda take ta gaskiya sbda Allah to sai dai inda gizo ke sakar shi ne jiddah kiyi hakuri, zuciyata ta yi nisan kiwo a cikin soyayyar yaya khalifa, ba zai yiwu bayan kammala secondaru din mu in bar kasar nan zuwa wata kasa ba ba tare da na san matsayina a zuciyarsa ba. Ba tare dani ba duka hanyar da ta dace nabi don in nemi soyayyarsa ba don in nemawa kaina masauki na din din din a zuciyarsa. Tagyara zama har yanzu idanuwanta na kallon jiddah taci gaba da fadin "jiddah zuciyata tana yiwa yaya khalifa wani irin so wanda ban taba tunanin akwai irin son a duniya ba, ba zan iya bayyana miki irin yadda nake jin ciwon sonsa a zuciyata ba. Kullum dashi nake kwana in tashi kullum soyyayarsa karuwa take a zuciyata ban kuma samu mafita ba akan yadda zan bullowa lamarin har gashi tafiyarsa germany ta matso. Tun a yanxu ban samu mafita ba inaga in yatafi tafiyar dazata dauke shi shekaru hudu. Ina matukar tausayawa rayuwata jiddah ban san halin da zuciyata za takasnce ba yayin dana rasa yaya khalifa.... . Jiddah takamo hannunta cikin tausaya wa tace "ki kwantar da hankalinki ummi in dai yaya khalifa mijinki ne da izinin Allah za ki aure shi, in har baki auri khalifa ba to Allah ne bai kaddara aure ba ba za ayi ba, shi ne amfanin daukar rayuwa dasauki. Ummi hakika na san yaya khalifa miji ne abin so gakowacce irin d'iya mace kowa cece ita kuwa, ko ni kaina din nan abinda yasa nake nesanta kaina daga burgewar da yake min na san ya yi min nisa ne ba zan same shi ba, ke din ma bansan za ki tsanantawa zuciyarki matsananciyar soyayyarsa har tashafi duk rayuwarki ba, da tun farko ban zungure ki da maganarsa ba, ko dacewa kina sonsa daman chan a baya tun kafin in tuntubeki da maganar amma tuntubar danyi miki ita tajefa ki a wannan damuwar. Ummi ina mai ba ki shawara ta gaskiya akan ki dauki rayuwa dasauki duk abinda kika zafafa shi zafi zaiyi gareki Kuma ba wanda zai dagawa hnkli sai ke din. Ki cigaba da fafutuka akan neman soyayyar yaya khalifa har kiga kin aure shi amma dan Allah kada kibari damuwa ta lalata miki tunani ki dogara ga Allah sai komi yazo miki dasauki. Ummi bata kara cewa da jiddah komi ba har aka fara kiraye kirayen sallan magriba tayi mata sallama takoma gdansu, dakyar tatashi tayi sallah taci gaba da zama a daki kan daddumar datayi sallah tana jan carbi tayi tagumi idanunta sunyi jawur. Hajiya hauwa taahigo dakin ta sha adon ta kamar yadda tasaba kai bakace ita ta ajiye manyan samari irin su hassan ba, mace ce mai son gayu shi yasa ummi ke samun daurin gindin gayu da kece raini a gunta. Tayi sororo tana kallon diyar tata tace "ummi wai lafiya kike kuwa kwana biyun nan kin sauya ko ba ki da lfya ne? Ummi tadago ido zuciyarta ba dadi tace "hajiya zauna kiji wata magana. Dasauri tazauna ummi tace "hajiya barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, yau zan fayyace miki damuwata dan kisamo min mafita a cikinta, hajiya zuciyata ta kamu da tsananin son yaya khalifa inaso kigaya min hanyar dazanbi yasoni. Hajiya tadafe kirji tare da fiddo ido tace "ummi kinsan maganar dakike fada kuwa? a duniya kirsa wanda za ki so sai khalifa? Kara gaya mini ko dai ba khalifan dana sani ba kika ce kina so? Ummi tamatso kusa dai tadora kanta akan cinyarta tace "hajiya babu wani khalifa dazan yi magana akansa wanda yawuce na mu ba zan iya raba zuciyata da son sa ba kuma ba na bakin ciki da son da zuciyata ke masa insha Allahu ba xanyi nadama ba mafita ce ban sani ba ita nakeso kisanar dani hajiyta. ************ Maganarta tadamu hajiya hauwa yau dai ba ta son mahaifiyar khalifa haka shi kansa khalifan ba kaunarsa take ba, a daran takira kanwarta hajiya sauda wadda ita ke binta ko gaisawa bata bari sunyi ba tace "saude tashin hankali ne ya saman a daran nan. Hajiya saude tace "har gabana ya fad'i "meya faru yaya hauwa? Tace "wai ummi tarasa wanda takeso sai wannan yaron mai shegen girman kan tsiya wanda ko kallo mutane basi ishe shi ba. Hajiya sauda tace "wai waye ne ?duk kin rikitani. Hajiya hauwa taja dogon numfashi cikin takaici tace "waye in banda khalifa. Hajiya sauda tace "to sai me dan ummi ta ce duk duniya babu wanda takeso sai khalifa, kada kibani kunya mana yaya hauwa kamar ba ke ba ko in ce kamar ba mu ba? Hajiya hauwa tace "uhm saude dole hankalina yatashi kina kallo fa yadda rayuwar yaron nan yake, ko kallo mutane basu ishe shi ba, gaisuwa da yake mana ma dan ya zama dole ne a gareshi, in banda haka khalifa bamu isa yagaidamu ba ni kam ba khalifa da uwarsa na tsanesu ba zan taba kaunarsu ba shiyasa da ummi tabudi baki tace min ba ta da gwani wanda yawuce khalifa hankali na yayi mugun tashi nayi gaggawar kiranki a waya dan musan abin yi. Hajiya sauda tayi murmushi tace "Allah sarki yaya hauwa ni ko da kika gaya min maganar nan sai naji zuciyata ta yi 'kal 'kal, na jima banji maganar data faranta min rai irin wannan ba. Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ke da Allah ana ga yaki ke kina ga kura me za muyi khalifa, yarinyarn nan ummi duk dan abinda na samu a gun kayan kwalliya suke tafiya don dai musamu gallelen alhajin birni mu darje amma ta lalace kan khalifa, wannan sangartaccen yaron da bai san yafita neman na sa ba sai dai dukiyar ubansa dasuks jiku a ciki shi da uwarsa. Hajiya hauwa tace, "to sai me idan khalifa bai nnemi na sa ba sai na ubansa? dama me muke nema ne? burin mu dama aibai wuce musamu wani ba ko d'an wani, to bamu samu wanda yake wanin ba ai a karan kansa sai dan wani to dawani da d'an wani in dai za mu shaki dukiya ai mu burinmu ya cika. Hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "to in banda abinki saude taya za mu iya mallakar wannan yaron mai masifar girman kan tsiya, zancan danake miki fa a satin dazai kama idan Allah ya kaimu zai tafi germany karatu sai ya yi shekaru hudu zai dawo, na ji uban abban hajiya yana gayawa jummai wai so yake yazama cikakken likitan mata, don haka karatu yakeso yayi a germany mai zurfi. wlh saude idan kinji kudin da muhammadu yakashe akan wannan tafiyar na khalifa sai kin rike baki sai hankalina ya kasa karba inda zai zauna ma tsawon wannan shekarun hudun da aka zuba akan su ya ishe irin mu mumore mun gama arziki a duniya dai. Wai amma jummai maimakon tai mashi fada yarage kashe kudi haka akan khalifa sai fadi take ya yi daidsi. Hajiya saude tayi murmushi tace "to ko anan za kisan lallai auran ummi da khalifa shi zaisa mu mallake dukiyar alhaji muhammadu cikin sauki kinsan ana cewa daka haifa gwamna gwara kahaifi matar gwamna saita kawo maka gwamna har gida sai ka shekara kana yawan neman ganin gwamna ma baka ganshi ba amma idan kabi takan matarsa lokaci guda sai kaganshi ba tare da ka samu matsala ba sbda ita mace mace ce daban take, yanzu idan muka bi duk hanyar data dace gun cusa ummi a zuciyar khalifa shikenan mun mallaki khalifa, idan muka mallaki khalifa sai yadda mukayi dashi ko uwarsa bata isa tayi yadda takeso ba sai mu din dai. Da ba a so muci arzikin slhaji muhammadu kinga munci dan bakin ciki sai dai yamutu. Kuma anan ne za mu fanshe haushin da mukeji na hajiya maijidda uwar khalifa, tana ji tana gani za mu aurawa khalifa ummi za mu mallake shi 'kaf shi da dukiyar uban na sa tunda dama alhaji muhammad ba shi da tunani sai khalifa, idan ummi ta auri khalifa shi kuma zai kasance ba shi da tunani sai na ummi sai yadda mukayi dashi da dukiyar ta shi, hajiya maijidda tazama yar kallo yadda tamaida mu yan kallo mu da dukiyar dan uwanmu ba mu da iko akanta muna gefe sai abinda aka sammana me zai hana muyi farin ciki akan soyaygar da ummi ke wa khalifa, wannan itace hanya daya tilo da burinmu zai cika kuma za mu nunawa maijidda ita ba komi bace hancin gauta ce bata isa komi a miya ba. Hajiya hauwa tace "tabdijam amma fa kinyi tunani saude shi yasa ake cewa mai shawara ba ya aikin banza, tabbas gaskiya kika fada sai dai abinda nake jinjinawa shi ne tayaya za mu mallaki khalifa kidinga tuna masifar jin kansa fa. Hajiya saude tace "kash yaya hauwa ni kunya nakeji kamarki wannan maganar kalaman nuna karaya da gazawa suna fitowa daga bakinki, khalifan banza khalifan wofi har meye shi, wa yayi ma ballantana yafi wani ko za murasa zanin daurawa sai mun mallaki khalifa, sai mun shiga ko ina zamu shiga dan mu tura ummi gdan khalifa, matakin farko dazamu fara dauka shi ne ummi za takoma gdansu khalifa dazama, hikimar yin hakan shi ne a matsayinta tamace wadda takai mace muka dade muna koyar da ita kissa da kisisinar jan hankalin namiji tabi hanyar duk data dace tafara kafa gwamnatin ta a zuciyar khalifa kafin tafiyarsa germany a wadannan gajerun kwanakin 'kididdigaggu, ko yaya ne mu tabbatr khalifa ya bar kasar nan ne da tunanin ummi ba wai soyayyarta ba. Kafa soyayya a zuciyar wanda kwata kwata hankalinka ba ya kansa abu ne mai wahala sai a hankali, lamari ne da ba ayi masa gaggawa a cikin lamari irin wannan to ko shakka babu ba zai ci nasara ba, ana kaddara cewa mutanen dasuke cin nasarar abubuwan dasuka sa gaba na rayuwa su ne masu hakuri a dukkan lamarinsu. Sbda ita nasara kafad'a da kafad'a suke tafiya da hakuri, ballantana lamari irin wannan ba abu bane mai wahala amma fa ga mace datasan abinda take wadda takaranci halayyar d'a namiji, kada ki jinjinawa ummi jin kan khalifa har jikinta yayi sanyi, ki kashe mata guiwar taji cewa ba za ta iya ba ,ko da tanajin cewa ita d'iya mace ce da za ta iya jan hankalin d'a namiji ko waye shi, idan kika jinjina al'amarin itama girmama zaiyi a zuciyarta daga nan sai ta kasa yin komi sai asarar tashafe mu baki d'aya. Amma idan kika nuna mata ba kowane khalifa face namiji kamar kowa shikenan saita ka ra samun kwarin guiwar kokarin janyo hankalinsa har muyi nasara. Yadda za ayi takoma gdansu khalifa da zama kuwa wannan sai idan Allah ya kaimu wayewar gari gobe lfya idan nazo sai musan abin yi. *************** Ba kowa a gidan sai fatima ita kadai, sauran kannanta suna makaranta yayin da goggonsu Abu tatafi barkan haihuwa da akyi musu, ta karasa tankadan garin tuwon datake takai kitchen tashare gidan tadora ruwan tuwon sannan takoma kan tabarma tadauki wani littafi na addu'a tana dubawa maisuna Du'a'ul mustajaba. Zuwa can ta ajiye ta kwantar danta kan pillow tana tunanin auran da za ayi mata da malam musbahu nan da lokaci kadan har yanzu dai malam bai yanke lokacin da za ayi bikin ba haka zalika musbahu bai taba kiranta da sunan zancan ba, kunyarta yakeji kamar yadda ita matake bala'in jin kunyarsa, kafin malam yafurta cewa zai hada su aure, malam musbahu ba wanda yafi shiri da shi a yaran gdan sai ita, tun tana karama musbahu ya fi kaunarta fiye da kowani d'a a gidan nan duk abinda yasamu kafin yaba kowa sai ya ba ta har sai da mutane suka shiga zargin ko dai son ta yakeyi, ganin bai furta ba yasa aka watsar haka itama take bala'in kaunarsa tun lokacin da bata sani ma musbahu ba dan gdansu baneballantana data mallaki hankalin kanta tagane musbahu maraya ne yahadu da zaluncin matar kawunsa har malam ya amshi ragamar rigimar rikonsa, sai tausayinsa yasa take ka ra kaunarsa suka rike shi tamkar dan gdansu, in banda wannan lokaci da malam yake gayan mata, da ya gayawa mutanensa cewa zai ba wa malam musbahu auran diyarsa fatima sannan dayawa wasu suka san ba malam bane yahaifi musbahu ba sbda yadda malam din da ita goggo Abu din da yayansu ke matukar ji da musbahu shi ma haka yazamo dan halak agaresu ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya gun soyayya a garesu, kyautata musu tamkar su suka haife shi, koda yake ako da yaushe yana gayawa malam cewa bai taba kaunarsa a matsayin iyayan riko ba kullum a matsayin mahifa yake daukarsu wanda ba shi da kamarsu a duk fadin duniyar nan kamr yadda yake da tabbacin suma haka suka dauke shi, rayuwa suke a gdan mai dadin gaske ga shi dai ba su da abin duniya sai rufin asirin Allah, abinda yakesa suke jin dadin rayuwa shi ne girmama junansu da kaunar juna da ake sbda Allah da tarbiyyar data ratsa duk d'an dayake na gidan ne, nisan da fatima tayi cikin tunani yasa har ruwan data d'ora bisa wuta ydinga tafsa tamanta dashi sannan mutum na tsaye a kanta bataji takunsa a lokacin daya shigo ba ballantana sallamar da yayi mata saida yatsuguna gabanta yace "fatima wani irin tunani kike haka kina yarinya karama mai kankantar shkaru haka ina ke ina wannan tunani? Kafin yagama rufe baki fatima tatashi dagudu jikinta na rawa za ta shige daki, musbahu ya mike shima yana murmushi yatare kofar dazata shiga yana murmushi yace "fati haka za mu zauna koda yaushe kina guduna kamar dodo tunda malam yace ya ba ni ke ban kara magana dake ba ko gaida ni ba kya zuwa kiyi ina dalili. kan fatima na kasa kamar za ta nutse a gun sbda kunya, tarufe fuskarta da tafukan hannayenta yace "je ki kigama tuwon kuma kada ki kona mana tuwo amma fa lallai yau ke za ki kawo mana tuwo ni da abokina mansur, idan har bazaki kawo mana da kanki ba ba na cin tuwon, idan kinyi kada ki aiko dashi zan kwana da yunwa, bai saurari abinda za tace ba yafice yabarta tsaye kamar an zare mata jijiyoyin jikinta tana kallon yadda ruwa ke tafarfasa akan wuta amma ta kasa tashi tayi talge, hankalin fati ya tashi kwarai da gaske idanunta suka cika da kwalla har ji tayi kirjinta ya yi mata nauyi numfashinta yana sama sama kamar zai dauke . Tun tasowar fatima babu wani d'a namiji daya taba cewa yana sonta ta amsa mai ballantana maganar soyayya ta had'a ta dashi shekarunta goma sha shida da haihuwa ajinta hudu a secondary, tun tana shekara sha biyar ake cewa ana sonta kasancewar ita yarinya ce da Allah yahorewa kyau ba na misali ba abin sai wanda yagani sannan tana da shiga rai yadda kasan wadda aka tsuma ta da maganin farin jini, in dai namiji zai ga fatima sai ya yi shaawar ace matarsa ce. sbda bayan kyaun ga natsuwa ko magana fati take ka san ta samu tarbiyya irin wanda duk d'a namijin arziki yake burin mallka a matsayin matar aure. Shigowar goggon ta Abu yasa tatashi dagudu tawuce 'yar rumfar kwanon dake gaba kitchen dinsu inda suke hura wuta, goggo tarike baki fatima yau me ya sameki sai yanzu ake talgen tuwo? kina sane dacewa ba na son ayi tuwon dare a gidan nan, fati bata saba karya ba don haka tai saurin kallon idanunta kadai, goggo dai ta san akwai abinda ke damunta yau abinka ga babba ballantana wanda yahaifeka, ta jima tana nazarin fuskar fatima sannan ta gyada kai tawuce daki. Har fati tagama tuwo a sanyaye jikinta yake ko magana akai mata dakyar take amsawa hatta shi kansa bakinta ya yi mata nauyi, bayan sun idar da sallar isha tana zaune kusa da goggo sanye da hijjabinta da charbi a hannun ta tana ja hawaye sai neman xubo mata sukeyi tana maida su dan kar goggon ta gane tayi mata tambayar da za ta gagara amsawa amma ina dole tatashi daga gun tashiga dakin dasuke kwana da kannanta tazauna tana sharar kwalla, har goggo tashigo tazauna kusa da ita cikin saryin murya da tausayawa irin na d'a da mahaifi tace "fatima na san duk abinda zai dameki bai wuce maganar auranki da musbahu ba, fati kada kicutar da kanki idan ba kya son musbahu kina sane malam bazai matsamiki ba, shi ma tunda farko abinda yasa yace ya ba shi ke kai tsaye dan ya san dakake har musbahu babu wanda ba zai yi masa biyayya ba. Sannan ya yi la'akari dacewa ke da musvahu akwai kaunar juna mai karfi a tsakaninku tun kafinn ku mallaki hankalin kanku kusan ku waye ku a rayuwa. Fatima tace 'goggo inason yaya musbahu sbda ba shi da makusa da mace za ta ki shi hasalima banga abinda baba na zai bakata in ki yi masa ba, inji ina kinsa a matsayinku na iyaye na, biyayyarku a gareni wajibi ce, wannan damuwar tawa ba ta da nasaba na kin yaya musbahu sai dai ni kaina bansa abinda yashiga xuciyata ya tsunduma ni a bakuntar rayuwa a yau din nan . Goggo tayi murmushi tace "ai baki shiga bakuwar rayuwa ba fatima sai randa kika shiga gdan aure kika zamo matar aure lokacin ne za kishiga cikin bakuwar rayuwa wadda baki santa ba amma da sannu saiki zama 'yar gari har wata rana kigaya wa wasu yadda aka gaya miki, kowacce mace sai da tashiga irin wannan bakuwar rayuwar. Tashi maza ki kaiwa musbahu abinci daga yau haka za kidinga yi. Bayan goggon ma cigaba tayi da zama ta kasa tashi har sai da goggon taleko takara yimata magana sannan tafita tadauki abincin tanufi dakin musbahu dake zaure, ta yi sa'a ba kowa a dakin ta ajiye dasauri za tafita sai ga shi yafito daga toilet yace "to dawo kidana murna dodon na ki yananan, har wani rawar jiki kike za kigudu ko? Tayi murmushi tatsuguna daf da gado tarufe fuskarta da hijabi, yazauna akan kujera yace "fatima ki rufe fuskarki yadda kikeso sbda kina da abin rufewar, mace kyakyawa irinki ta isa tayi irin kowacci yanga ga kowane d'a namiji ko waye shi ballantana almajiri kamar ni. Fatima tun lokacin da baba yabudi baki yakira sunana har sau uku hankalina a tashe nadinga amsa masa sbda bansan wace magana zai gayamin ba wadda har tasa yayi min irin wannan kiran. Tun kafin yagaya min na san duk abinda zai gaya min din magana ce da muhimmancinsa ta isa. Fatima malam yabude baki yace dani "musbahu na ba ka auran fatima, wlh fati ban taba kwana a zaune ba, yadda naga rana haka naga dare hnkalina ya tashi kwarai dagaske ba dan komi ba sai dan tunanin dame zan rike mace kamar ke fatima. Ina sane dacewa mutane da dama suna tunanin inasonki ne sbda yanayin shakuwar mu tun kina karama nima ina karami to Allah yasani fatima ina matukar kaunar ki sbda haduwar jini da Allah kan hada tsakanin mutum da mutum amma Allah ya sani tun da nake ko da wasa ban taba kallonki da wata siffa ko da wata manufa ba, bayan kanwata ina kallonki ne a matsayin kanwata wadda muke ciki daya. Yana magana ne cikin yanayin tausayin kai muryarsa kasa kasa yana mata wani irin kallo, lamarin yajefata ckin sabon tashin hnkali da rudani idanunta suka kama zubar da hawaye, fatima ban taba tunanin akwai

Chapter 4 of 19