Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dai fatana a yi mana addu'a. Tace "addu'a kam dare da rana bata yankewa daga bakinmu, Allah yai muku albarka, Allah yara ba ku da duniya lafiya,Allah yaraba ku da sharrin makiya da mahassada. Khalifa yadinga fadin "amin amin inna ngd. Yana son magana ya kasa bayyana wa inna abi? dake tafe dashi ya dan jima zaune shiru daga bisani yayi mata ama yafice daga gdan. Malam misbahu yavishi da kallo zuciyarsa ckin matsanancin kishi da kunci, me khalifa da fatima ke nufi dashi ? saura kwana takwas kachal yarage a daura musu aure amma yana jan fatima a mota yana fita da ita a mota, ba Khalifa ne abin mamaki ba fatin ce, kowa ya san ta da kyawawan dabi "u ya za ayi akan khalifa tasauya lokaci daya haka ? Yatuna yadda sukayi da ummin dazu a gdansu Khalifa lkcn da yayi ta rokon ta da Allah tafdi masa abinda tasani game da mu'amalar fati da Khalifa ,ya hadata da girman Allah akan kada taboye masa gskiar abinda tsani. Ummi dakyar ta iya rike kanta a lokacin itama ta kanta take ji ta fi musbahu shiga tashin hankali, jin cewa wai dr. khalifa da fati sun fita a mota ina za su ? meye dalilin fitar ta su ? da wace manufa fati tabishi ? shin ta bi shi ne dan taci gaba da jan ra'ayinsa akan yaso ita ummin ko Khalifa ya ja ra'ayin fatin ne ta fara son shi ? abubuwa da dama suka dawo mata game da yanayin jikin Fatima dake sanyi a duk lkcn da suka kebeda Khalifa idanuwan ta sukan yi jawur me yakawo. haka, itama lallai tana bukatar wadannan tambayoyin da gaggawa. Wannan tunanin ne yahana ummi magana ga musbhu ya tsareta da ido hnkalinsa a tashe yana ckin fargaba, da. kyar ta iya bude baki tace mishi "kayi hakuri fatin tadawo zanji ta bakinta. Kina nufin baki san komj ba ? Kadafa ki manta na hadaki ne da girman Allah. Tace "ban ce maka ban sani ba kayi hakuri akwai wasu bayanai danake son tattarawa xan gaya ma gskiyar dana sani amma ba yanzu ba. Dakuar ummi ta lallabashi yahakura yatafi, tunda yadawo gida yakasa zaune yakasa tsaye, tunaninsa me fati da khalifa suka fita yi a mota? kuma fatin tana ganin shi a tsaye ko kunyarsa bataji ba suka wuce meye hadin ta da khalifa? har zaiyi wa inna maganar yaga bai dace ba, shi ne fa tun da yafito waje yazauna bai iya tashi ba har su fati suka dawo, ganin dukiyar da ake shiga da ita gdan yakara rudewa, ga fati ta wuce ko sannu batayi masa ba yadinga fadin "Lahaula wala kuwwata illa billahil azim. Babu tunanin da bai yi ba a wannan lokacin hnkalin sa ya tashi sosai. A DAREN FARKO 24 A rikice ummi tashiga gdansu tazube a gaban hajiyarta hauwa tana shaida mata cewa ga dukkan alamu fatima za ta ba wa khalifa hadin kai, ra'ayinta ya fara karkata gare shi. Hajiya tace "to ai dama ke ce kika yarda da ita, fatima karya take tace za taki khalifa akan wannan musbahun, wa yaki dadi? ballantana daula irin ta gdansu khalifa ga shi dan gata, ke ce baki da wayo yaudararki kawai take tana gaya miki cewa za ta taimake ki yasoki, soyayyarsu suke yi, dan kada kijuya mata baya ne take miki haka, kinga dai ke ce kika wayar wa da fati kai amma tafi ki wayon, iya zaman duniya da mutanan ckinta. Ummi ta jinjina kai tare da cije lebe tace "Amma lallai fatima ta tafka babban kuskure idan har ya tabbata yaudara ta tayi bata yaudareni ba kanta ta yaudara, do min kuwa sai na nuna mata cewa duk wanda yariga ka bacci sai ya rigaka tashi ba zan barta ta mallaki khalifa ba, domin ban cancan ci yaudara a gun fatima ba. Hajiya tace "to ki dai san abin yi bai dace wannan wahalar damuke sha yatashi a banza ba. Tace "karku damu in dai ban samu khalifa ba to na hakura dashi to bbu wacce za tasame shi ko zan rasa raina na amince akan khalifa. Ta fiddowa hajiya guzurin kayan data yi musu itama tace abban khalifa ya aiko mata da kudin don haka suka yiwa gdan malam tsinke da tsakiyar rana. Hajiya ta jadadda masa cewa ayi wa khalifa aikin da uwarsa ma bata isa dashi ba sai ummi, tace "malam muna so mu mallake shi shi da dukiyar tasa gaba daya data uban. Malam yayi dariya yace "ai kar ku damu tunda kuka kawo wadannan abubuwan ai an gama. ku sa ido za kuga yadda khalifa zai zamo a hannunku. **** Kwance take laga laga tana cike da tsananin shaukin jikin dr. khalifa da son jin muryarsa,komi na ta ya suaya fatima ta tsinci kanta a wani irin sabon yanayi na bukatar rayuwa,tunda take rayuwa a duniya bata taba jin abinda taji yau ba game da Khalifa,, kamshin sa har yanzu yana tare da jikinta, kyakyawar surarsa tadinga gani a idonta, ta hasko mijin da za ta aura rana ita yau musbahu, nan take taji ta tsane shi, daman bata taba jin tana son shi ba biyayya biyayya ce kawai. Lallai a yau ta fuskanci meye so, don kuwa ta samu kanta cikin irin yanayin da ummi ke bayyana mata tana shiga a kan soyayyar khalifa. khalifa kam ya isa miji abin so da burgewa . Tamike zaune tazuba tagumi shin yaya za tayi da musbahu da ummi, ko shakka ba ta yi a halin yanzu tana son Khalifa kuma shi za ta aura, musbahu da ummi fa? mutane ne masu kima da daraja a idonta me za tace dasu? Duk bata san inna ta dade tsaye a kanta ba sai data yi mata tsawa tadago da sauri ta dubeta, a fusace inna ta tsare ta da ido tace "tunanin uban wa kike tun dazu nake tsaye akan ki ina magana? Fati tayi shiru takasa magana, inna ta jinjina kai tace "tabdijam amma kina da jan aiki fatima, da can wani namiji bai ja ra'ayinki ba sai yanzu, yau din nan fa za a fara rabon goron bikinki, to karkace kunnuwanki da kyau kiji idan ma son khalifa kike to kishiga taitayinki, kisan abinda kike, kinsan dai mu ba kwadayayyu bane duk abinda iyayan khalifa suka mana mun gode ba za muce bamu gode ba amma dai ba rokonsu mukayi ba ba za mu kai kammu inda Allah bai kai mu ba, dan mu tsira da mutumcin mu, ni kaina na gamsu duk abubuwan da iyayan Khalifa ke mana sunyi ne don Allah to amma mutanan dake gefenmu kallon kwadayi suke mana, kin ga dai su suka ja mu a jiki amma yanzu da zarar an ji wata magana ta fito fassarar kwadayin nan za a yi mana, sbda haka kisan abinda kike kada ki soma daukar dabi'ar da ba ta ki ba ki sa wa ranki wahala, kitsaya a matsayin da Allah ya ajiye ki sai ki zauna lafiya. Bayan fitar inna, fati tayi shiru tana tunanin maganganun inna, wadanda akan hanya da gaskiya suke, sai dai kash zuciyarta ta kamu da soyayya farat daya hankalin ta da tunanin ta sun dawo kan Khalifa, tana jin sa a ko ina a jikinta. **** Ummi da hajiyarta da hajiya saude sun dawo gida zuciyarsu cike da tabbacin abinda malam yagaya musu zai auku har tadinga jin kamar ma ta mallaki khalifan ne, sai fatima ce dai a ranta ita ke daga mata hankali. Takira jiddah a waya ta gaya mata abinda ke cigaba da faruwa. Jiddah tace "ummi in tambayeki mana" Tace "Allah yasa na sani. Tace "wai shin dama a baya khalifa bai taba wata budurwa ba sai fatima? mesa za ki daga hankalin ki haka akan fatima? bayan kina sane da cewa duk inda yake "yammata natare dashi. Ummi tace "ke jiddah tsaya kiji duk wata 'ya mace dake tare dashi ita ke nace masa bai damu dasu ba fatima kuwa shi yake sonta, tarihin rayuwarsa ba macen daya ke nunawa zai shiga kowani irin hali a k anta sai fatima, wannan al'amari yana matukar daga min hankali da ba ni tsoro jiddah. Jiddah tace "kai wani irin soyayya ce wannan? ko da yake fatin da khalifa duka ababen so ne, hakika ba abin mamaki bane dan namiji ya shiga kowani irin hali akan fatima, wannan yarinyar Allah ya hore mata kyau me shiga zuci, sannan khalifa Allah ya hore masa kyau na daukar hankali, fatima za ta iya kamuwa da son khalifa haka Khalifa zai iya kamuwa da son fatima fiye da duk yadda kike kwatantawa, amma shawar da zan ba ki itace kiyi hakuri kiyi hakuri idan Allahyakaddara fatima matar khalifa ce kiyi hakuri kiyi hakuri Allah yabaki wanda za kifi so fiye da son da kikewa dr. Khalifa. Tace "jiddah idan nahakura ya ya zanyi da son danake wa dr. khalifa? Tace "ummi tun a fari ni ce na sa ki a hanyar ki so khalifa, amma hakan bai hana a yanzu in ba ki shawarar kiyi hakuri da Khalifa ba sbda maslahar zuciyarki, ummi yanada kyau kisani duk abinda Allah bai kaddara makasamunshi ba ba za kataba samun na sa ba har abada sbda Allah ya kaddara ba rabonka bane, kitsaya akan wannan don ki zauna lfya. Ko kusa shawarar jiddah bata samu karbuwa a zuciyar ummi ba, domin abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ji take har gwamma ta sallamawa wata khalifa in da za ta iya yin hakan akan ta sallamawa fati. Su hajiya ma sun tsaya tsayin daka akan sai ummi ta mallaki dr. Khalifa ko da yake su dukiyarsa kadai suke kwadayi. Dab da sallar magriba ummi ta iso gdansu khalifa, ta iske shi suna alwala tare da dr.bashir ,ta tsaya suka gaisa abin mamaki fara'a ce karara a fuskar khalifa yana fadin "yawwa kanwata daman ina son ganinki, bari in dawo daga masallaci. Ta shige gida cike da zargi iri iri a zuciyafmrta, musamman ganin yadda fatima tadaina neman ta ko da a waya ne, tabdijam ckin dakin mama tafara shiga ta iske ta ta tayar da sallah ita dayake ba sallar za tayi bata watsar da jakarta da mayafinta tazauna gefen gado tayi tagumi. Mama ta idar da sallah tazuba mata ido tace "sai yanzu ? Ta sauko kasa suka gaisa tace "mama yaushe rabon fatima da gdan nan ? Tayi murmushi tace "ai fatima ta dauke kafarta daga gdan nan ne sbda mun zamo surukanta. Tace "kamar yaya mama ? Tace "uhm kina nufin baki san meke faruwa ba ? Tace "mama idan ma na sani ina bukatar karin bayani daga gareki. Mama tace "ummin hankalina a tashe yake domin abbanku ya goyi bayan son zuciyar da khalifa yazo dashi karara bayan ya san hakan bai cancanta ba. Bakin ummi na rawa tace "mama kina nufin abba ya goya ma khalifa baya ya auri fatima. Tace "wannan shi ne damuwata. ina tsoron kallon da mutane za suyi mana musamman kasancewar musbahu talaka khalifa me kudi abin da kowa zai ce shi ne anyi amfani da dukiya gun dannewa musbahu hakki don ba shi da dukiya, ya kamata abba ya takawa Khalifa burki yanunamasa jan ido tunda ba shi za ya daurawa kansa auran ba, dole yahakura amma ya ce ba xai hana shi yin abinda ba ya so ba ina jiyewa khalifa rayuwar da abba yasa shi bai san bbu ba bai san yanemi abu yarasa ba sai dai duk abinda yanema sai ya samu, wace irin rayuwa ce wannan ? idan khalifa bi san rayuwa ba yanzu sai yaushe zai sani ? Cikin nauyin baki da takaici ummi tace "mama to ke kin amince ? Ta amsa "to yaya zanyi ummi ? ina da ikon yiwa abba musu akan wani abu daya tsara akan khalifa ? Ummi tajinjina kai a zuciyarta tace "gaba dayanku kunyi kuskure wato cikinku babu wanda yadamu da damuwata sai damuwar danku ? Hakika son zuciyarku da kanku ya zame muku damuwa daman ance son zuciya bacin ta. Tabude baki za tayi magana wayarta tafara ringing, khalifa ne tadaga yace da ita "taho mana da abinci mana dakina. Ta tambayi mama abincin na su tace yana kan tebur. Wani iri ummi take jin zuciyarta kamar ba ita ba, tadauki abincin tanufi dakin na sa, bayan ta zauna Khalifa yace "ina kawar ta ki ? Tace "fatima. Yace "eh. Tace "ai ina zaton a halin yanzu ka fini sanin inda take tunda ka fi ni kusa da ita. Yace "um um ummi ba haka bane kina da matsayi babba a gun fatima koyaushe tana maganarki da kokarin ganin ta nema miki mafitar da za ta haifar maki da kwanciyar hankali,kada wani abu yarufe miki zuciya ki zargeta da abinda bai dace ki zarge ta dashi ba. Gaba daya taji takaici da bakin ciki sun kara rufeta maganganun sa kara mata damuwa suke, meye amfanin abunda yake fada mata kan ftima, tamike da niyyar tafita yakira sunanta yace "zauna. Takoma ta zauna tana kallon sa yace "ummi ya zamo dole in miki godiya domin kin taimaka min akan fatima, zuciyarta ta karkata a gareni ta amince ta amshi soyayya ta duk da cewa wasu abubuwan suna firgitata wadanda sune suka hanata sakin ranta sosai tabani hadin kan daya dace, ina miki godiya ne ummi sbda kin taka muhimmiyar rawa akan hakan. Tayi masa wani irin kallo cike da mamakin abinda yake gaya mata, ba ta son tayi kuka sbda lokacin kuka ya wuce gareta, ta dade tana kuka akan khalifa lokaci ya yi da za ta daina kuka, don da ace kukan zai mata maganin damuwarta da ya yi abinda yadace da ita shi ne tanema wa kanta mafita kawai ko ta wani hali, tadubi khalifa tace "a takaice daikwalliya ta biya kudin sabulu fatima ta amince da soyayyar ka ko ? Ya amsa "eh hakane abu guda daya zuwa biyu ne damuwarta ke da musbahu tana jinjina yadda za ku kalleta, shiyasa nakiraki yanzu dan in roke ki kinunawa fatima ba komi kuma kisaki ranki sosai da ita kamar yadda kuke rayuwa a baya, yin hakan ne kawai zaisa ta kwantar da hankalinta tabani hadin kan danake bukata. Kai khalifa da wauta yake. Abinda ummi ke fadi a ranta knan ko da yake gani yake ya fi karfin komi tabbas khalifa ya rainata, shi yasa ko wani irin danyar magana sai ya tareta da ita to kuwa za ta shayar dashi mamaki daga shi har fatima da iyayansa masu son zuciya. A fili kuma dubansa tayi tace "karka damu zanyi yadda kace. Yayi murmushi yace "nagode ummi zan miki kyauta mai ban mamaki". A DAREN FARKO 25 Tsakiyar dare ummi ta kasa barci tana tuna abubuwa iri iri ta saka wancan ta kwance, tun tana ganin auran fati da khalifa ba mi yiwuwa bane har nesa tafara matsowa kusa, abinda ya faru da karfe goman daren yau ne yatabbatar mata da haka. Wato ta zo za ta shiga dakin mama ta tsinkayi muryar mama da anty sadiya suna hira da daga murya soai, anty sadiyance take fadin "to wai mama idan Allah ne yakaddara fatima matar khalifa ce fa ? kin san dai babu wanda ya isa ya shirya wannan al'amarin sai Allah ko ? tunda ita kanta yarinyar ta amince to meye na damuwa ? kin san babu yadda za a yi abba ya sauya ra'ayinsa, kada ki jawo abin da zai zamo na rigima. Mama tace "haba sadiya yanzu ko a hankalce wannan ya yi dai dai, da kunyar son da ummi ke masa zanji ko da malam musbhu. Anty sadiya tace "duk ki kwantar da hankalinki ki kaddara cewa Allah ne yakaddara faruwar hakan ki toshe kunnuwanki daga duk wani surutun mutane idan kika biyewa mutane babu wani abun alherin dazaki kulla a rayuwarki, ki kyaleshi ya aureta Allah yasa haka shi yafi alheri itama kuma ummi Allah yabata wani haka shima musbahun. Abin da ummi taji mama tafada ne takara tsinkewa da al'amarin cewa tayi "sadiya ni ma na fi son Khalifa ya auri fatima fiye da kowacce mace, sbda tarbiyyarta da nagartarta, na san inaha Allahu za yi alfahari da auranta, Allah yasa haka shi yafi alheri. Anty sadiya tace "to Alhajin ya yiwa mahaifin fatiman magana ? ni na fi son ayi komi a gama hankalin kowa yakwanta. Mama tace "eh da magribar dazu ya ce idan yafita masallaci zaiyi wa malam maganar zan tambaye shi in ji yadda sukayi, na san dai da wahala in za su ki. A hankali ummi taja jikinta tadawo dakinta zuciyarta na azalzala mata tamkar za tafashe, tabude wayarta ta binciko wani kyakyawan hoton khalifa data faki idonsa ta dauke shi bai sani ba tadauke shi a falo, yana sanye da kananan kaya dasuka matukar karbar jikinsa, murmushin da yayi ya dada kayatar da kyaun hoton. wata rana tazauna tazubawa hoto ido, fatima ta iso kanta bata sani ba, ta jima tsaye tana kallonta ganin bata motsa ba fatima tazare wayar tana fadin "wa ki ke kallo haka ? Ummi tamike takwanta bisa gado tana dariya tace "wa kika san zan kalla in banda sahibi na. Fatima tadubi hoton tace "yayi kyau kam amma zan ba ki shawara. Tace "tame fa yar kawata ? Tace "ummi ina matukar jin tausayinki game da al'amarin khalifa, kina sonsa da yawa kada ki ja wa kanki wahala yayin da so ya tsananta a zuciyarki don Allah ki dinga bi a hankali yadda za ki iya daukar duk abun da zai faru me dadi ko akasin haka. Murmushi ummi tayi tace "hakane fatima amma za ki iya fada min dalilin dayasa kika min wannan nasihar ? Tace "ba wani abu ne yasa nace haka ba illa la'akari da yanayin khalifa anya wannan zai tsaya kan mace guda daya ? idan ma bai ce yana so ba sai ance ana son shi, wata rana idan bai amince ba watarana zai amince amfanin shawarar dana ba ki itace idan kin bi komi a hankali sai komi yazo miki da sauki. Ummi tace "fatima wai don Allah kina ganin zan samu dr khalifa. Tace "ummi wannan lamari ne na Allah babu w ? da ya isa ya yanke hukunci sai shi, za ki iya samun sa za ki iya rasa shi, ba komi mutum yake nema yasamu ba Ummi ta rausayar da kai tana dan murmushi tace "fatima don Allah idan ke ce xa kiyi hakuri da khalifa akan soyayyar danake masa ? Fatima tayi dariya sosai tace "ummi kin ganni nan wallahi har yanzu ban san meye so ba. Ummi tafiddo ido "fati wace irin magana ce kike haka ? meye matsayin musbahu a gunki knan idan dai baki san meye so ba. ? Fati ta tabe baki tace "musbahu zabin iyayena na, ba na fatan ganin ranar da zan sabawa umurnin su, shi yasa na tallafe shi hannu bibbiyu kuma na yi damarar rike shi da kyau in dai batun so za ayi to ban san me akeyi idan ana son mutum ba. Ummi tace 'Don Allah dr. khalifa ya taba birgeki ? Tayi mata wani irin kallo tace "ni dai na yarda har zuciyata khalifa ya isa namijin da za a so shi, ko da nace bn san so ba, na san cikakken namijin kuma na san namijin dazan kalla in ce ya hadu, shi yasa ba ni ganin laifinki don kina damuwa da khalifa face ina jan hankalinki don ki dauki komi dasauki... Ummi ta buga kwafa, lallai ba abin mamaki bane don fatima ta amince ta amshi soyayyar khalifa, sai dai ita tana tausaya mata don ba karamin kuskure tayi ba. A DAREN FARKO 26 Ba karamin tashin hankali inna tayi ba lokacin da fatima da kanta ta zauna tana yi mata wani mamaki wanda yabata mamaki, kallon fatin take kamar ba ita ba, tun tana fada har ta dawo yi mata nasiha amma fati ta murje idanunta kukan da take ma yau batayi ba don tsakaninta da Allah so take inna ta amince da abinda take fada mata. Inna tayi tagumi tana kallonta tace "maimaita min abinda kika fada. Fatima tace "inna kiyi hakuri ni na san wannan magana ba za tayi muku dadi ba amma kuyi hakuri ku karbeta a matsayin abinda Allah ya kaddara mana ni daku, inna don Allah kiyi hakuri kada kuyi fushi dani nima ban taba tunanin zan bijire wa auran malam musbahu ba sai a wannan lokacin dana samu kaina a cikin yanayin da ban taba tsammaninsa a gareni ba, tayi shiru ta kasa ci gaba da magana ganin yadda inna ta tsareta da ido kamar za ta shaketa. Fuskarta a tsuke alamun fushi da zuciyarta ke ciki, jin shirun ya yi yawa inna tace "kici gaba mana tunda bakiji kunyar fara fadar wannan maganar ba ba wani dalilin dazai sa kiji kunyar karasawa. Kan fati na kasa bakinta ya mata nauyi ga maganganu na cinta ta kasa karasawa bayan ta zauna a gaban innar ne cike da azamar fada din sbda ance barin kashi a ciki bai maganin yunwa. A daran jiya ne da barci ya gagari idanuwanta ta kwana tana juyi kamar zuciyarta xa ta tsage, ta yanke shawarar idan gari ya waye za ta tari inna da maganar duk abinda zai faru yafaru, itama a halin yanzu tasan meye so ta san abinda ake nufi da ciwon so. Bayan tayi duk sallar asuba tazauna shiru tana tunanin ta yadda za tadubi tsabar idon inarta ta shaida mata cewa su yi hakuri su bata khalifa shi take so, ba wata manufa data wuce hakan amma akwai tashin hankali mai yawa a cikin al'amarin da ban tsoro, iyayanta suna matukar kaunar musbahu kamar su suka haife shi, ba sa wasa da abinda ya shafe shi, kamar yadda shima yake matukar sonsu da kula da al'amarinsu, ko da su suka haifeshi ba zai yi musu biyayyar da tafi haka ba ko da yaushe malam yashiga yafita maganarsa musbahu, duk abinda za ayi a gdan musbahu ne zai ce yayi, shi kuma ba ya kasa a guiwa gun aiwatar musu da abin da suke so ko meye shi kuwa, in dai ba wanda yasani ba ba mai cewa musbahu ba dan gdan bane, ta ina iyayanta za su amince da damuwar musbahu, damuwa kuma irin wannan. Idan fatima takalli girman son da takewa Khalifa sai ta tuna matsayin musbahu a gun iyayanta ba karamin tashin hankali bane a yanzu tace zata juyar da ra'ayin iyayanta daga auran musbahu zuwa khalifa. Tana cike da wannan rashin kwarin jiki da karayar zuciya taci gaba dakulla shawarwarin yadda za ta tunkari inna da maganar kafin ma malam yaji wanda yafi kowa son musbahu. Da gari yagama wayewa tafito tsakar gida duk sanda suka hada ido da inna sai gbanta ya fadi, lokaci lokaci takan faki idon inna tagoge kwallar dake taruwa a gefen idonta, innar ce tagaji takira ta daki tazaunar da ita tace yau sai ta gaya mata abin dake cin zuciyarta wanda yasa tadaina walwala. Ta mayar da kanta kamar bakuwa a gdan, da farko shiru fatin tayi tana sharar kwalla, inna tace "uhum ta yaro kyau take ba ta karko, babu abi ? da zai sa ki tashi a gun nan sai kin min bayanin abinda ke rufe min zuciyarki.... A kofar gdan malam musa, Alhaji muhammadu mahaifin khalifa ne zaune kan tabarma, shima malam din suna hira, musbahu yafito musu da kunun ayar da inna tahada musu yayi sanyi sosai yana ta kamshin kayan yaji, suna sha suna ci gabada hira. Abba yana son gayawa malam abin da ke tafe dashi kunya ta kamashi yarasa ta ina zai faro maganar, bai yi tunanin zaiji nauyin maganar da take ta damun zuciyarsa ba, bai san me xe ce da Khalifa ba idan yakoma gda a haka har suka gama hirar yabar gurin zuwan gdansu, ai kuwa khalifa ya iske shi a falo tare da mama ta tare shi da tambayar "Abba ya kuka yi da malam din!? Ya fidda babbar rigarsa da hula ya ajiye yazauna. Khalifa naje na kasa gaya masa, ban san dalili ba naji bakina ya rasa yadda zai furta maganar khalifa me xai hana ka daure kayi hakuri komi na Allah ne. Mama tayi farat tace "yawwa abba don Allah kadinga nuna masa hakan irin wannan son kan ba shi da dadi. Khalifa ya kwantar da kan shi a jikin kujera yace "abba ni zanje dakaina in sami mala.m din in gaya masa, ni bakina ba zai ji kunyar fada ba, wannan yarinyar ba zan taba iya hakura da ita ba a rayuwata don Allah kuyi hakuri ku ci gaba da tayani addu'ar Allah yasa auran fatima alheri ne a tare dani. Yamike zai fita abba yace "kayi hakuri kar kaje zan kara yin tunanin akan al'amarin. Murmushi yayi yafice. Yana fitowa harabar gdan yakira fatima a waya yanayin dayaji muryarta ya tabbatar itama tana fama da damuwa. Bayan sun gaisayace "a ina zan ganki? "kazo gdammu kawai ina son kowa yatabbatar ina snka kuma na amince dakai. An gama gimbiyar mata. Inna da malam, zaune a tsakar gida suna hira ,khalifa yayi musu sallama, cikin fara'a sosai suka amshe shi ya tsuguna suka gaisa nan da nan kamshin turaransa ya game gdan, farar shadda ce a jikinsa sai walwali yake, yace "inna yaya naganku a duhu? Tace "khalifa ai ka san ba kullum suke kawo wutar ba? Yace "ba injin a gdan nan? Sukayi shiru, yace "idan Allah ya kaimu gobe za a kawo muku injin. Malam yace "Don Allah khalifa kudaina mana hidima haka abin ya yi yawa. Yace "haba abba meye amfanin arzikin da ba za a taimaki al'umar musulmi dashi ba, mu dai a dinga sanya mu cki? addu'a yanzu ma bukata nazo da ita gareku. Malam yace "in dai bata fi karfinmu ba insha Allahu za muyi maka kai da mahaifinka kunfi karfin komi a gdan nan. Kansa na kasa yace "baba dazun abba ya zo gdan nan da nufin isar da sakon dana turo shi dashi gunka amma ya koma yace min ya kasa gaya ma, shi ne ni nazo in fada maka kuma in roko alfarmarku. Malam musa yayi murmushi, "amma alhaji ya ba ni. mamaki yanzu har akwai abinda zai ce yaji nauyin gaya mana, ni dashi ai mun zama daya fada min khalifa ko meye in dai mallaki na ne zan maka shi. Khalifa yaji sanyi a ransa guiwarsa takara karfi yace "baba auran fatima nake son kabani. Gumi yashiga karyowa malam kansa na kasa yayi shiru yakasa magana, itama innar shirun tayi yayin da fatima ke cikin daki a zaune tana jiyosu sai gabanta ke faduwa. Zuwa can malam yadago kansa yace "ikon Allah, khalifa ban taba zaton bukatar da za kazo min da ita ba knan, ko dayake ba abin mamaki bane don ka so fatima Allah ne mai hada zukatan bayi su so juna kuma na ji dadi sosai na gode da son da kakewa fatima, amma ina ba ka hakuri na riga na ba da fatima, a inda ba zan iya karbota in ba ka ba, in banda haka wallahi zan ba ka fatima khalifa kayi hakuri insha Allahu za miyi ta maka addu'ar Allah yabaka matar datafi fatima. khalifa yayi shiru kansa na kasa lokaci lokaci yana sharar gumin da yake tsatsafo masa, gdan ma ya yi tsit kamar ba kowa a gdan, daga bisani yamike dakyar ko ina a jikinsa ya yi mai nauyi yace "to na gode baba Allah yasanya alheri. Malam yamike yabiyo khalifa kofar gda suka tsaya, malam

Chapter 11 of 19