Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: 1) A DAREN FArko kotun ta yi tsit, kowa ya yi jigum, ana sauraran abinda xai fito daga bakin alkalin wanda yasunkuyar da kansa yana rubuce- rubuce. Lauyoyi dasauran ma,'aikata wadanda suke da alhakin zama a kotun sbda sauraron shari'ah, kowanne yana xaune a mazauninsa daya dace dashi,haka yan kallo da iyayen yarinyar da ake gudanar da shari'ar a kanta al'amarin yan ba kowa tausayi shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikin goma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yan uwanta knan. Mai shari'ah usman muhammad yadaga kansa a hankali yadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda ake tsaida wadanda ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa. Bakar rigace a jikinta da bakin hijjabi sanye akanta, ba dankwali idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, ba ta son dago kai tadubi kowa saboda tsanar kanta datayi don haka ma da alkalin yakira sunanta bata dago kanta ba ta dai amsa cikin dashashiyar murya wadda da kyar ake iya jin abinda ake fada. Alkalin yakuma cewa "Fatima Musa" Ta amsa "Na'am" "Ke kika kashe doctr Abubakar saddik wanda akafi sani da doctr khalifa??? Fatima tayi shiru alkali yana maimaita tambayar har sau uku batayi magan ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar shiru, koda fatima da mai shari'a yake kallo ana sauraron abinda fatin xa tace amma taja bakinta tayi shiru kamar dam chan yadda Llah yahalicce ta ba ta da bakin magana. Mai shari,'a Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na tausasa harshe yace "Fatima kotu tana tuhumarki da laifin kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda ka kamaki da gawarsa shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gasjiyar al'amari da bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin abinda muka fada kuma kina iya magana. idan ke kika kashe shi kifadawa kotun sannan kifadi dalilin dayasa kika kashe shi, idan ba ke bce ba to kidanyi magana kiyi bayani. Fatima tadago kanta a karo nafarko tadubi duk jama'ar kotun suka hada ido da mahaifiyarta wadda tazuba tagumi dukda nisan dake tsakaninsu da Fati, Fati ta san kuka take wiwi tana girgiza kai, Fati tadubi mai shari'a sai kawai taj kanta yana juyawa kafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza cigaba da daukar gangar jikinta tazube a gun, nan take mai shari'a Usman M Baina yadaga shari'a zuwa uku ga watan gobe idan Allah ya kaimu. Kotu tarude da hayaniya, koke koken iyayan fati da yan uwanta ya cika kotun ga uar uwarsu a matsananciyar hali amma ba yadda xa ayi su taimaketa, sunaji suna gani wasu yan sanda mata suka daga fati aka fice da ita da gaggawa sbda numfashinta ne yake sama saa kamar zai dauke. *******×*×***********×***×******×** Yammaci ne akalla za mu iya kiran lokacin karfe biyar na yamma dawasu mintuna, ummi na zaune gefen tabarma ta hada kai da guiwa tana kuka kamar ranta xai fita, goggo Abu ne gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin damuwa kobaka sansu ba kaga halin dasuke ciki sai ka tayasu wnnan kuka dasuke, ko ba a maka bayani ba ka san damuwar daxata sa a yi irin wannan kuka ya isa a tayashi kuka. Malam musa yashigo da carbi a hannunsa yayi sallama yatsaya chan daga bakin kofa yana kallonsu tsawon mituna biyar sanan ykaraso inda suke ,Allah sarki bawan Allah mai saukin kai wanda bai dauki duniya a bakin komi ba, fuskarsa cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya ka sa magana, xuwa chan goggo Abu tagoge hawayenta cikin karfin hali tace "Malam ka dawo?? sannu daxuwa. Ya daga mata hannu yace ba na son gaisuwar ta kui tunda idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan abinda ba xai yi mana amfani ba. kokuwa wannan kukan xaiyi mana magani akan damuwar damuka samu kanmu aciki?? Goggo Abu tace "Mala to yaya xanyi tunda abinnan yfaru ummi bata daina kuka ba. na yi lallashin duniyar nan yarinyar nan ta ki daina kuka har na rasa wacce kalma xan gaya mata wanda xa yasa tayi hakuri. Malam yace "Ummi kiyi hakuri ko mu damuka haifi fatima babu abinda xa mu iya akan wannan lamarin sai dai addu'a. Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace "Shin baba shikenan daga hakuri babu abinda xa ku iya gaya min wanda xan samu sassauci a xuciyata game da halin da fatima take ciki??? Wyyo Allah kaicon rayuwata ni ummi in har xan xauna ina rayuwa a cikin tunannin fatima na kulle a kurkuku ana tuhumarta da laifin dani daku daduk duniya sun san baxata taba iya aikata shi ba. Ya ya xa ayi ace fatima xa takashe rai, kisan ma ace tarasa wanda xa takashe si mijinta? kadubi wannnan al'amari ayi wani abu akai har yaushe muna zaune fatima na cikin mummunan zargi irin wannan". Malam. musa yai xaman dirshan a wurin yace "Ummi toh yaya xamuyi? Saboda girman Allah me kike ganin xa mu iya yi kinsan indai ace muna da bakin yi din da yanxu ba wannan xancen akeyi ba. kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum na da kudi idan akace case din me xafi ne da tsanani irin wannan ba ka da tacewa, kudinka ba xa suyi amfani ba dan ba xa su sayi ran da aka kashe ba balletana kasiya domin ko da ke biyan diyya idan wani yakshe wani ba a irin wnnan yanayin ake biyan diyya ba kinsan ita shari'a sabanin hankali ce, duk yadda kaje tunaninta ta wuce nan. Kuma idan ma muna da abin yin a yanxu ba xa mu iya ba idan Fatima ba ita takashe docta Khalifa ba tai magana man a kotu, kinaji kina gani daxu a kotu ka sa magana tayi ,tayi shiru tabude bakinta tace ba ita takashe shi ba tafdi yadda abu yafaru akalla idan ma akwai abinda za a yi ai a yi tunda tayi shiru me za ace?? Yagirgiza kai cikin dan zuciya yace "Allah kadai yasan yadda wannan abu yakasance sai kuma fatima. Ummi taciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace "Shi kenan baba shikenan goggo tunda kuma kun yarda fatee ita takashe doctor sai kusa ido itama a kasheta ba tare da hakkinta ba, amma dai inaso kusani ko ku kuka haifi mutum to ba kune kuka halicceshi ba yadda kake da hakkin yayi ma biyayya haka shima yanada hakinsa akanka idan kadanne Alah subhanahu wata'ala xai tuhumeka baba. Nikam ba xan bar maganar fatee tawuce haka ba ,ba xan bari acigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, zan shiga infita ko xan rasa zanin daurawa sai na taimaki Fati Insha Allahu. Malam yace ummi ba na shakku akan abinda kika fada mun tabbatar xa ki aikata fiye da abinda kik fada akan fatima kaunar dake tsakananin ku ya wuce a fadadeta da baki, Allah kadai yasan iyakacinta, sai dai inason kisani ba wai mun yarda cewa fati itace ta aikata kisan ba, kifahimci wani abu day ummi ba mu da kudin daxamu iya daukan lauya daxai kare fati, ba ki da bukatar mugaya miki halin damuke ciki na kaka ni ka yin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin daukar lauya sannan idan ma mun dauka dawacce hujja xa mufidda fati daga wannan zargi tunda ta ki magana? wannan shi ne a dalilin dayasa muka mikawa Allah lamuranmu, idan fati ba ita takashe likita ba insha Allahu Llah xai bayyanar da gaskiyar alamari Allah xi kawo mana mafita. Ummi duk wanda na sa yashiga matsanancin hali irin wannan ya gama kwanciyar hankali kada kidauka bamu dmu da ita ba illa iyaka shi lamari irin wannan idan kaga kanka acikinsa ba ka tsananta damuwa wadda ita dama rayuwa jarravawa ce acikinta, idan Allah yajareba ka dawani alamari kagode masa kawai karokeshi yabaka juriyar cin wannan jarbawa dayayi maka domin ba wanda ya isa yakaucewa jarabawar Ubangiji . kiyi hakuri ummi. Ta jinjina kai yace "Na hakura baba, na hakura dakuka na hawaye, tunda ba ka son ganin hawayen saidai ba xan iya hakuri da fati ba ko da nima xan shiga halin datake ciki, ko nima xan rasa raina, idan ba halin daukar lauya ai muna da halin daukar akwai guraren da ake taimako a samu agaji su taimako ne a gabansu kawai a gabansu ba kudi ba, su ake kira gatan mara gata" Goggo tace"Allah shi ne gatan mara gata shi xai xama gatanmu, Ummi kiyi hakuri" Tayi murmushin karfin hali tace goggo nakanyi mamakin masu cewa inyi hakuri akan maganar fati, wa yace banyi hakuri ba? Tabbas na yi hakuri domin na hakura daduk wani farin ciki Insha Allahu akan nemawa fatee hKkinta sai inda karfina yakare ko da hakan shi xai kasance abinda xan aikata nakarshe a rayuwata". *********************************** Suna a wani dan daki mara girma Ummi da Barrister Nuruddin ,aka bude kofar dakin wani kakkauran dan sanda ne a gaba fuskarsa ba fara'a, fati na biye dashi a baya kamar kamar koyaushe bakar rigar nan ce ajikinta da bakar hijabi kai ba dankwali ta rame sossai ta yi duhu idanuwan nan kamar gauta saboda jan dasukayi, hannayenta biyu cikin ankwa, wani dan sanda a bayanta saidai shi fuskarsa akwai sassaucin ra'ayi. Fati tadubi ummi tayi murmushi cikin dasasshiyar muryarta tace "Ummi ku ne? Dan sandan yace "mintunanku ba su dayawa ku gaggauta yin abinda yakawoku dan kar kuyi asarar lokacinku". Ummi tagirgiza kai hawaye wasu na bin wasu ta ta so tadafa kafadar fatima tace "sannu Fati da izinin Allah zai kawo mana mafita a cikin alamarin nan, mun shiga tashin hankli da dmuwa akan halin dkike cki fati inajin ciwon damuwarki kamar xuciyata xa ta buga sbda tashin hnkali. WNnan shine barrister Nuraddin Mustapha,na daukeshi ne dan yazamo lauyan dazai kare ki a kotu. Fati inaso kibamu hadin kai duk tambayoyin daxai miki ki bashi amsa sannan idan anje kotu a zama nagaba kibude baki kiyi magana. Fatima tayi murmushi hade da hawaye tace "Ummi bansan dawani kalamai zanyi amfani gun gode miki ba ,komi nafada ba zai wdatar dxuciyata ba hai inji cewa na nuna miki godiyata kan soyayyar da kikemin dakuma kokarinda kike don ganin kin ceci ryuwata daga wahala. Saidai inaso kifahimci wani abu duk yadda kaso yankewa mutum wahala idan Allai bai kaddara lokacin yankewar wannan wahala ta sa ta yi ba ba za ka iya yanke masa ba. na godewa Allah daya kaddara min shiga wannan hali ina fatan wannan jarabawar da Allah yayimin tazamo kaffara agareni, ummi inaso kisani ban tsananta bakin ciki akan halin danake ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako dayaushe za aga idanuwana na yi inayinsu ne sbda tausayin iyayena daku yan uwana a Bisa halin dxaku shiga ba bakin cikin halin dana tsinci kaina a cikinsa, dkuma uwa uba rashin mijina wanda xuciyata ba ta da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan damuwar ba zanyi kuka ba inhar akan halin danake cikibne. Zaman danake ummi ina jiran ranar da za ayanke min hukuncin kisa ne inbi mijina. idan har akwai taimakon danake da bukata daga gareku ayanxu shi ne ku taimaka ayanke min hukunci inhuta wannan damuwar kuma kuhuta domin idan an kasheni kun daina ganina dole watarana kuhaura idan ko ina raye haka xa kuyi taxama cikin damuwa. Wannan shi ne dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don ba ni da abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince ba ni nakashe doctor ba, idan nace ba ni nakashe shi ba in neman kariya knan wadda e nufin inci gaba da rayuwa alhali ni kaina banga amfanin rayuwata a duniya ba. Umi kiyi hakuri kiba iyayena daduk yan uwana hakan kirokar min su gafara kowa yayi hkuri yamanta dani ba na bukatar taimakon kowa agareku sai addu'a, na gode kwarai dagaske kada kisake wahalär dakanki gun dauko min lauya....... Ummi takatseta cikin huci tace "Fatima kin amince kidauki laifin daba na ki ba, kin amince kikashe kanki,? wayake kin taimako kin amince kijawa dukkan zuri'arki abin fadi? kina zaton wannan ba zai zama mugun aibi ga zuriarki ba? wanda xaija adinga aibata muku zuri'a mata surasa mazajen aure? Kina zaton idan ankashe ki wani zai sake zama lafiya acikin iyayenki da yan uwanki? To kisauya tunani lauya tunda kince ba kya so na janye shi, amma ko shakka babu kuskure ne babba wanda xa kitafka idan har kikayi ikirarin kece kika kashe docto khalifa alhalin ba ke kika kashe shi ba. Fatima tace toh idn ni nakashe shi fa ummi? Ummi tayi murmushin takaici tace ba ke ce kika kashe docta ba, dankuwa ba ki da dalilin kasheshi, kina fadin hakanne kawai dan kin gaji da duniya ba kyason rayuwa a halin da kinason ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba ranki da gangar jikinki". Dan sanda yace "Lokaci ya yi" Ummi tace kayi hkuri ina fada mata abinda xai amfaneta ne. Yace ba shi da amfani gareta da saita karba kidaina wahalar da kanki. Ya tisa keyar fatee, kallon data waiwayo tayiwa ummin tawuce shiya sa tsigar jikin ummi tashiga tashi tazube a kasa tarika kanta da hannu bibbiyu. Shi kansa barrister nura jikinsa ya yi sanyi, ya jima xaune agun yana kallon ummi daga can yadan ja numfashi yace "Tashi mutafi ummi tun anan na tabbatar yarinyar nan fati ba ita takashe docta ba dukda Cewa ta ki amincewa daduk wani taimako daxa abata ta rufe duk wata kofa takariya daxa a ba ta, bawani abune kuma yasatayi hakan ba ta yi ne kawai sbda bakin ckin dake damun xuciyarta wanda yake tafarfasa xuciyarta yasa rayuwa tafita a zuciyarta. Hakan yasa taki mgana a kotu sannan taki yarda da taimakon da za a ba ta, ba komi Llah yana tare damasu gaskiya, sannan ba ya goyon bayan zalinchi, indai ba ta da hakki dasannu xa kiga hukuncin da Allah xaiyi. " Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun. [5:07PM, 7/13/2017] ‪+234 706 196 7803‬: A DAREN FARKO 2 dasauri yagoge hawayen dake zuba a idonsa jin sallamar matarsa, goggo Abuwa tazauna sharaf a gabansa jikinta na rawa ta ajiye flask d'in abincin datazo kawo masa, yadda jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un malam kuka kake? Yayi d'an murmushi yace "haba dai kuka ba kuka nake ba Zainabu. " Tace "Dom Allah karkace haka malam bayan na gani da idona kana kukan kuma na ji shasshe'kar kuka, malam idan kayi kuka akan wannan al'amari mu kuma yaya za muyi da ranmu? Kai kake nuna mana muyi ha'kuri bisa fushi dayin Allah me zai sa kai kayi. " Malam musa yace "Zainabu al'amarin nan yana matu'kar bani mamaki da d'aure min kai, ya ya za ayi fati ta iya kashe mutum? idan munce ba ita takashe shi ba wa ne yakashe shi? alhalin da Ita sai shi a gidan d'akin a rufe da sakata taciki. Meyasa fati takashe Dr. khalifa me yayi mata? Meye iyayen khalifa basu yimana ba? shi kansa khalifan meye bai yi mana ba? Ace fati tarasa tukuicin dazata saawa wad'an nan bayin Allah saida wannan mummunan aikin? " Goggo Abu tace "malam ka yarda fati ita takashe Dr. khalifa? Yace "to zainabu idn a ita bace waye? daga ita sai shi a d'aki yashiga yarufe 'kofa shi zai kashe kansa ne zainabu? " Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani tajinjina kai tace "ko shakka bbu acikin wannan al'amari akwai rikitar da 'kwa'kwalwa sannan duk wanda yayi wannan aikin wanda yasan sirrin gidan ne, tabbas fati ba ita takashe dr. khalifa ba don ba ta da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi ba ta da 'karfin halin dazata aikata wannan mummunan aikin, saboda zuciyarta tanada sau'ki akan al'amura, Allah kad'ai yasan yadda al'amarin nan yakasance. " Cikin sanyin murya malam yace "Zainabu nima abinda yake damuna knan kowa ma haka yake fad'a su kansu iyayan khalifa haka suke cewa basu yarda fati takashe shi ba, to amma meyasa ba za tayi magana akotu ba idan akaci gaba da tafiya a wannan hali za asamu mafita ? Tunda ba ita bace tayi magana mana " Goggo tace "wannan shi ne abinda yadamu kowa ma ba kai kad'ai ba malam. " ************************************ Kasancewar mahaifin marigayi Dr. khalifa babban mutum,d'aya daga cikin masu fad'a aji a cikin gwamnatin garin yabasu damar ganin fatima cikin isashen lokaci batare da tsayawar 'yan sanda ba, ko kuma ankwa. Alhaji Muhammadu Nazif mahaifin marigayi Dr. khalifa da hajiya maijidda mahaifiyarsa suna zaune a wani babban d'aki da aka 'kawata da kujeru, Malam musa da goggi suna zaune gefensu sai babban wansu fatima dakuma ummi da Barrister Nuraddeen, fatima na tsakiyarsu kanta a 'kasa ba kuka takeba su d'in ne baki d'ayansu ke sharar 'kwalla sakamakon matsanancin tausayi da bayanin datake furtawa yabasu Alhaji muhammad yace "Fatima abinda nakeso kigane shi ne dukkanmu nan mun san ba ke kika kashe Dr. khalifa ba sbda kamar wanda zaiyi kisan kai ya fita daban, ko da auren dole akai maki dashi ba za ki iya kashe shi ba balletana anyi auran nan ne da amincewarki, ke yarinya ce mai biyayya ga iyayenki, wadda kike zaune dakowa lfya kowa na yabon kyawawan halayenki tayaya za ayi Muyarda kin kashe Dr. khalifa. Ki bud'e bakinki fatima nan ba kotu bane mu ba lauyoyi bane mu iyayenki né duk duniya ba wanda kike dashi wadanda suka fimu idan rufin asiri ne ba rufin asirin dayafi na Allah, ba wanda zai rufa miki asiri bayan mu, kigaya mana saurin lamari waya kashe Dr khalifa ?? Falon yayi tsit kamar ba kowa sai 'karar A. C ko motsi fati batayi ba ballantana tabasu amsa, malam yace "fati dame muke magana kigaya mana yadda akayi idanma ke kika kashe khalifa ya ya za muyi dake ? khalifa dai ya mutu kuma ba zai dawo ba, fad'a mana gaskiya shi yafi dacewa, kullum hankalinmu a tashe yake fati ba mu da sukuni idan mun kwanta don muyi bacci bacci ba ya yiwuwa, abinci ba ya ciyuwa, muna cikin matsananciyar damuwa ,bansan dawani ido zan kalli iyayan khalifa ba, bansan da wanne ido zan cigaba da kallon 'yan uwansa ba damutanan unguwa, ba wani abu ne ma ba fatima shirun dakikayi har yau baka fad'i Wata magana wadda za a kama ba akan maganar nan kin mana adalci, dukkan 'yan uwansa da masoyanki kowa yana cikin damuwa. " "Ni na kashe shi baba. " Akayi tsit kowa yazuba mata ido, maijidda kallonta kawai take ta yi tagumi d'ansu da suke mutuwar so khalifa ta sake rushewa da kuka, Goggo Abu tace "shikenan tunda kince ke kika kashe shi to lallai ne kidaina wahalar da mutane idan anje kotu kifad'i dalilin dayasa kika kashe shi, kin san ba wai kice ke kika kashe shi kiyi shiru ba dole ne kifad'i abinda yasa kika kashe shi. Ummi tari'ke hannun goggo tazaunar da ita tace "goggo me mye amfaninki yi hushi da fati alhalin kowa anan ya san takura matan da akayi da maganar nan yasa tace Ita takashe shin to haka idan ma akaje kotun aka takura Mata abin da za tace knan 'karshe idan tace ita takashe shin dole tayi shiru tunda ba ta da dalilin dazata fad'a wanda yasa takashe shi. " Goggo tace "shikenan ummi haka za muyi tazama cikin damuwa tunda ba ita takashe shi ba idan anje kotu ta fad'i Iya abinda tasani mana. " Fatima tana kuka tace "kiyi ha'kuri goggi ba'kin cikin damuwar danasa ku ya fi damuna fiye dakowa sai dai ba yadda zanyi, goggo ba zan iya cewa ba ni nakashe Dr. khalifa ba sbda gaba d'aya bayanan sun tabbatar dacewa ni nakashe shi." Kuyi ha'kuri shirun danayi a kotu wannan shi ne abin da yafi damuwa na, idan nace zanyi magana bansan abinda zan fad'a ba 'karshe dai na san duk abinda shirun na wa zai haifar bai wuce a yanke min hukuncin wanda yayi kisan kai bane a kashe ni. To dama abinda nake jira knan, ni kam rayuwa ta 'kare a guna sai dai sai dai jiran lokaci ko ba'a kasheni ba ba'kin cikin halinda iyayena kuka shiga a sanadiya ta da ba'kin cikin rashin mijina shi zaisa zuciyata tabuga in mutu ba zan iya cigaba da rayuwa ba shi yasa ba na bu'katar taimako tako wani fuskar lauya don ku'butarwa idan akwai abinda nafi bu'kata bai wuce addu'a ba, wannan ba sai na ro'keku ba na san kuna yi min. Dan Allah kuyi ha'kuri kuyafe min babu abinda zan iya cewa a kotu. Aliyu yayan fati yayi mgana a karon farko tun zamansu a d"akin yace "fatima bamu amince kici gaba dayin shiru a kotu ba dole kiyi magana. " Tace "shi knan yaya zanyi magana. Alhaji muhammadu dakowa yafi sani da, abba yace "kar kice ke kika kashe shi fati". Tace "Abba idan nace ba ni nakashe shi ba waye? idan kuma akayi bincike aka gane ni d'in ce abinda ake gudu shi zai faru, kuna fad'in hakane don fa kusamar min mafita wadda za ta ba ni damar ci gaba da rayuwa a duniya, yayin da ni kuma ba na son rayuwar ta fita daga raina so nake na mutu na bar duniya yadda mijina yabarta. " Aliyu yace "Anya fati baki samu ta'bin hankali ba? " Tace "lafiya 'kalau nake yaya ".kowa yarasa abin fad'i a kayi shiru. ********************************************* ********* Da sassafiyar ranar daxa a koma kotu hajiya maijiddah da akafi sani da mama tana kwance kan faffad'an gadonta na alfarma tunani da ba'kin cikin duniya ya isheta tarasa abin dake mata dad'i, tana mutuwar son D'anta an kashe mata shi wata 'kanwarta dake tayata zama wato anty sadiya tashigo d'auke da abincin karin kumallo tazauna kusa da ita suka gaisa tace "kidaure ki sha ko da ruwan sanyi ne zama da yunwa ya fi komi illa duk abinda yafaru rubuttaccen alamari ne babu wanda ya isa yago ge shi. " Tami'ke zaune tazubawa anty sadiya ido tace "anty sadiya kina ganin haka yadace mu zubawa lamarn nan ido kullum Alhaji yana cewa fatima ba za ta kashe khalifa ba toh ni so nake agaya min wa yakashe min d'ana? Anty sadkya tace "tabbas kam fatima ba za ta iya aikata wannan mugun aiki ba abinda yake da sar'ka'kiya shi ne daga shi sai ita a d'akin to waye yashiga yakashe shi? Mama tace "ke sadiya idan ma ba ita takashe shi da hannunta ba to da had'in bakinta aka kashe shi sbda ana ganin ubansa yana da dukiya d'ansa d'aya ne ko don a mallake dukiyar ubansa za ta iya yimasa haka. Anti sadiya tace "kigafarce ni amma ban tari numfashinki ba to amma idan haka ne da had'in bakin fatima ya ya za ayi ita data kasheshi ko ta had'a baki aka kasheshi bata gudu ba har akazo aka kamata? Allah (SWT) dasu kuma mahukuntan tunda Allah yabasu basiran gano gaskiyar wannan alamari cikin hikima da izinin Allah za su gano mana wanda yakashe mana d'a jininsa ba zai tafi a banza ba. A bisa hanyarsu tazuwa kotunne cikin mota mitar da mama ke tayi wa abba kenan yayi tsit yana jinta ko tari vaiyi ba ya yi tagumi yana jan charbi. Suna shiga su malam da goggo suka shigo suka gaisa, Abba yace"malam bana jin dad'i Yadda kake kaucewa had'uwa dani tunda wannan abu yafaru. " malam yarufe fuskarsa da babbar riga dan kar abba yaga fuskarsa yace "haba alhaji me, zan ce dakai? menake dashi wanda zan gaya maka dahar zaisa intsaya in kalleka, kaico. Ina ba'kin ckin faruwar wannan alamari har ina cewa ina ma ace banzo duniya ba da dai ace 'yar cikina ta kashe d'an mutumin kirki kamar kai d'in nan Alhaji muhammadu. Abba yaja hannunsa suka wuce cikin kotu

Chapter 1 of 19