Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shiga ta jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata samini azamar das zan kara dagewa don fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa kaga idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika cikin alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi masarautar garin.. SA MAZA GUDU Littafi na uku(3) Part D Haka dai su Malika sukayi ta tafiya suna masu ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon kwana goma sha shida sannan suka iso Birnin Misra.A cikin wannan tafiya sun sha haduwa da 'yan fashi mugayen aljanu da mugayen dabbobin daji amma dukansu farat daya suke yi musu,sannan gimbiya Malika ta rike wasiyar mahaifinta bata taba kulasu wasu yan fashi ba sai sai in sun kula su,suna kula su kuwa saidai su gama dasu su bar gawarwakin a yashe a wajen su kara gaba.Da shigowar su Gimbiya Malika cikin birnin Misra sai suka iske garin ya cika makil fiye da koyaushe a duk lokutan da suke zuwa a baya.Fatake,bokaye da yan kasuwa iri iri da kuma masu fataucin bayi sun cika garin.Al'amarin daya baiwa su Gimbiya Malika Mamaki kenan har suka kasa hakuri.nan take sadauki Aryan yaga wani almajiri a zaune a gefen hanya rike da dan 'ko'kon yana bara.Shidai wannan almajiri ya kasance saurayi mai kirar sadaukai,amma kuma kafarsa guda ta hagu da hannunsa na hagu duk a shanye suke ko sarrafasu baya iyawa.Aryan ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare guda daya a lokacin daya tsaida dokinsa daf da almajirin ya jefo masa wannan dinare a cikin kokon sannan ya dubeshi yace,ba sadaka na baka ba,labari nake nema,mene dalilin wannan cikowa mai yawa a cikin wannan birni?Koda jin wannan tambya sai almajirin yayi murmushi yace,da wannan dan kudin kake son kaji babban labari sai sunyi kadan.Koda jin haka sai Aryan yayi murmushi ya sake zura hannu cikin aljihunsa ya dauko dinare guda ya jefa cikin kokon yace,yanzu fah?Almajirin yace da saura domin kuwa labarin da zan baka zai amfaneku a matsayinku na manyan jarumai daga babbar kasa.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sadauki Aryan yace,A cikin ransa anya kuwa wannan almajiri ba boka bane,yaya akayi yasan cewa mu jarumai ne daga babbar kasa,kuma menene zai amfane mu akan labarin da zai bamu.Koda gama wannan zancen zucin sai Aryan ya sake fidda dinare uku ya sauko daga kan dokinsa yazo ya tsuguna a gaban almajirin ya zuba masa dinaren a cikin kokonsa ya zama guda biyar sannan ya dafa kafadarsa yace,Abokina bani labari me yake faruwa a cikin wannan gari?Almajirin ya sanya hannunsa mai kyan cikin kokon ya kwashi dinaren ya zuba su a cikin aljihunsa na wando sannan ya dubi Aryan cikin nutsuwa yace,Ai sarkin garin nan ne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya don haka jarumai da yawan gaske sunzo daga manynan kasashe,sarakuna sun zo,kuma attajirai yan caca sun taru domin baje kolunsu a goben da safe a gidan sarauta.Duk wanda ya lashe wannan gasa za'a bashi zabin abubuwa guda uku ya dauki daya ko dai ya auri yar sarki kokuma a bashi dinare da rakuma dubu ko a bashi mulkin babbar jaha daga cikin jahohin kasar nan.Koda jin wannan batu sai Sadauki Aryan ya kamu da farin ciki nan take ya aiyana a ransa cewa lallai zai shiga wannan gasa,amma ba don kawai a bashi wannan dukiya ta dinare ba.Rakuma gudu dubu saboda in ya koma gida yayi amfani da ita wajen cika wani babban buri nasa wanda ya gagare shi cikawa tsawan shekaru.Kawai sai Aryan ya dubi wannan Almajiri yace Abokina meye sunanka? Almajirin yace Sunana Hibairu bin Usman.Koda jin haka sai Aryan ya mikawa almajiri Hibairu hannunsa na dama shima ya bashi nasa hannun suka gaisa.Aryan yace,ina fatan zamu hadu gobe a fada muyi kallon wanna gasa tare.Hibairu yayi murmushi yace,tabbasa zamu hadu,koda gama fadin haka sai Aryan ya mike da sauri yaje ya hau dokinsa ya zabure shi da sauri domin ya riski su Gimbiya Malika saboda sun bashi tazara mai dan yawa.Da isar Aryan wajen gimbiya Malika sai ta dubeshi cikin murmushi tace,me ka tsaya yi a wajen wancan almajirin?Aryan ya maidawa Malika martanin murmushin cikin biyayya yace,na tambaye shi dalilin wannan cikowa mai yawa a garin nan shine ya labarta mini cewa Sarkin garinne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Malika ta dubi Aryan tace,da zarar mun sauka a masaukinmu kaje ka nemi sarkin kasuwa ka gaya masa cewa nima ina son na shiga wannan gasa don haka yaje ya biya mini kudin shiga gasar tun kafin na yazo gareshi muyi lissafin kudaden.Koda jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka kama sadauki Aryan ya dubi Malika cikin alamun tsananin dimuwa yace,Haba ya shugabata ai girmanki da darajarki tafi gaban shiga wannan gasa,saidai ki barmu mu wakilceki kada ki manta cewa gaba dayan manyan sarakuna kina hulda dasu kuma babu wanda ya san cewa kina da wannan jarumtaka bai kamata ki tonawa kanki sirri ba.Koda jin wannan batu sai gimbiya Malika tayi murmushi tace,idan kida ya sauya dole ne rawa ta sauya.Ya kai Aryan ka sani cewa ni yanzu tun dana baro gida neman yadda zan kare kasata daga shirin abokan gaba na daina daukar kaina a matsayin yar sarki,wannan gasa da zan shiga ta jaruman duniya zata taimaka mini na kara sanin iyakar jarumtakata da iya yakina.Kuma zata samini azamar das zan kara dagewa don fuskantar babban aikin dake gabana.Abinda nake so da kai shine kaima ka shiga wannan gasa kaga idan kayi nasara koda ni banyu ba shike nan daukaka dai tana hannunmu.Koda jin wannan batu sai sadauki Aryan ya sake duban Malika cikin alamun tsananin damuwa da mamaki yace,Haba ya shugabata ta yaya zan iya lashe gasar jarumtaka alhalin kina cikinta kuma na tabbatar da cewar kin fini karfin damtse da iya yaki?Koda jin wannan tambaya sai Malika ta yi murmushi tace,yakai Aryan ka sani cewa karfin damtse da iya yaki basu ne kadai ke sawa a sami nasara ba akwai sa'a da rabo.Koda gama fadin hakan sai Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi masarautar garin [5/20, 9:00 AM] princeauwal3156: SA MAZA GUDU Littafi na Uku(3) Part E Koda gama fadin hakan sai Malika ta karawa dokinta kaimi tayi gaba ta nufi masarautar garin,sauran tawagar suka bita da sauri a lokacin da sadauki Aryan ya bita da kallo kawai yana tunanin wannan kama da ta gaya masa ta karshe,ya tabbatar da cewa shifa a rayuwarsa sa'a da rabo take kaishi ga nasara bisa duk abinda ya a gabansa amma ba wai jarumtakarsa bace da iya yakinsa.Kamar yadda gimbiya Malika ta shirya haka al'amarin ya kasance wato suna sauka a masaukinsu,sai sadauki Aryan ya tafi izuwa gidan sarkin kasuwa ya isar da sakon Gimbiya Malika.Koda sarkin kasuwa yaji cewar gimbiya Malika zata shiga cikin wannan gasa sai mamaki da tsoro suka kamashi yayi kamar yaki zuwa ya biya musu kudin shiga gasar saboda tsoron kada wani abu ya sami Gimbiya Malika Sarki Sharkuf ya turo a kamashi,amma da ya tuna cewa sadauki Aryuan babban badakaren tane kuma amintaccenta,lallai da yawunta yake magana kuma idan yaki bin umarninta zata iya kwace duk harkokin kasuwancinta dake hannunsa.Sai ya mike tsaye zumbur ya kama hannun Aryan yaja shi suka tafi izuwa fada.Da zuwansu sarkin kasuwa ya biya dinare dubu dari sannan ya bayar da sunan Gimbiya Malika da Sadauki Aryan a matsayin jaruman da zasu shiga gasar.Su kansu masu rubuta sunan sai da suka dago kai suna yiwa sarkin kasuwa kallon mahaukaci sabon kamu,amma da suka fuskanci cewa a cikin hayyacinsa yake lafiyarsa kalau sai suka kamu da tsananin mamaki.Kashe gari da duku dukun safiya fadar birnin misra ya cika ta batse da jama'a ya zamana cewa duk inda mutum ya hanga babu abinda zai gani face kawunan bil'adama fululu babu matsakar tsinke duk wani sarki mai isa gami da koshin lafiya ya halarci wannan taro haka ma dukkan bokaye da hamshakan attajirai sun zo,masana tarihi da masu bincike a wannan rana saida suka tabbatar da cewa ba'a taba kashe makudan kudade ba a duk tarukan da kayi a duniya sama dana wannan rana.Attajiran caca kuwa saida suka kure taskar kudadensu suka fito dasu gaba daya saboda basu taba yin cacar data kai wannan daraja ba.Duk wanda ya cinye gasar ya san cewa idan aka lissafa attajiran duniya sai ya sami shiga a cikin mutane goma.Saida kowa ya gama hallara a cikin filin gasar sannan aka ji an buga gangar sarauta alamar cewa ga sarkin Misra nan ya fito zai shigo filin gasar.Nan fa kowa ya mike tsaye don girmamawa a wannan lokaci gimbiya Malika da sadauki Aryan suna cikin jaruman gasa a tsakiyar filin sunyi shigar kayan yaki kuma gimbiya Malika ta rufe fuskarta da hular karfe.Nan take sai ga Sarkin Misra tare da 'yarsa Gimbiya Zuhura sun shigo cikin filin gasar.Yaune ranar farko da mutane suka fara ganin fuskar gimbiya Zuhura saboda bata taba fitowa daga gidan sarautar ba tunda aka haifeta.Koda mutane suka yi arba da Gimbiya Zuhura suka ga irin tsananin kyawun da Allah ya bata sai suka dimauce suka kama surutai da sambatu,da yawa daga cikin matasan dake wajen kuka suka kama yi saboda nadamar rashin shiga wanna gasa ta jarumtaka ko don suyo suna ace sun taba neman auren wanna 'yar sarki.Hatta Gimbiya Malika wacce take ganin kamar babu mace mai kyanta a gaba daya wannan fili saida ta raina kanta ta gamsu a cikin zuciyarta cewa ita mummuna ce akan gimbiya Zuhura.Tun da sadauki Aryan ya shigo cikin wannan filin gasar yake ta ware idanu yana kalle kalle da waige waige ko zaiga Almajiri Hibairu a cikin yan kallo amma ko mai kama dashi bai iya ganiba.Koda Aryan ya juya ya fara kallon 'yan uwansa jaruman gasar sai zuciyarsa ta buga da karfi ya kamu da tsananin mamaki.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin almajiri Hibairu a cikin shigar yaki kuma a tsaye daram cikin koshin lafiya babu tauyewar hannu ko kafa.Suna hada ido sai Hibairu yayi masa murmushi kuma ya dago masa hannu,cikin alamun takaici Aryan ya ciza yatsa yace,lallai wancan almajirin ya raina mini hankali,ashe ba nakasasshe bane amma na dauki kudina mai yawa na bashi sadaka,ai kuwa sai ya biya ni kudina,kuma Allah yasa mu hadu dashi a cikin wannan gasa dukan tsiya zanyi masa nayi masa lilis amaimakon kudi na daya ci.Aryan yana cikin yin wannan tunani ne yaji alkalin gasa yayi gyaran murya a lokacin da filin gasar yayi tsit kamar mutuwa ta gifta.Kawai sai Alkalin gasar yace,Jaruman gasa na farko sune Gimbiya Malika daga Birnin Madinatul Zauwara zata kara da Jarumi Hibairu daga Birnin Nurul Islam.Koda jin haka sai mamaki ya turnuke sadauki Aryan kuma ransa ya baci bisa jin cewar wai wannan makaskancin jarumi kuma almajiri shine zai fafata da gimbiyarsa.Su kuwa 'yan kallo da sauran manyan mutanen dake filin gasar zazzaro idanu sukayi saboda bisa jin cewa Gimbiya Malika 'yar sarki Sharkuf ta shiga wannan gasa.Nan take Jarumi Hibairu da Gimbiya Malika suka fito tsakiyar filin gasar suka fuskanci jina kowannansu na rike da takobi da garkuwa,kawai sai ji sukayi an buga gangar fara gumurzu.Dukaninsu sai suka rugo da gudu kan juna suka runguntsume da azababben yaki mai mutukar ban al'ajabi da ban tsoro. WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN GASAR JARUMTAKA TSAKANIN JARUMI HIBAIRU DA GIMBIYA MALIKA? WANE IRIN GAGARUMIN KARFIN DAMTSE DANA SIHIRIN TSAFI YARIMA LAHAMAN ZAI SAMU KUMA IDAN YA HADU DA MALIKA ME ZAI FARU? SHIN MALIKA DA SARKI HILAIRU ZASU KARBI SOYAYYAR JUNA?YAUSHE NE GIMBIYA MALIKA ZATA CIKA ALKAWARINTA TA MAYAR DA SARKI HILAIRU KASARSA YA KOMA KAN KARAGARSA KUMA A GYARA BIRNINSA? TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA LAHAMAN WAYE ZAI HAU KAN KARAGAR BIRNIN MADINATUL ZAUWARA YA KASANCE YA GAJI GIDAN SARAUTAR? MU HADU A WANNAN LITTAFI SA MAZA GUDU LITTAFI NA HUDU DON JIN YADDA ZATA KAYA.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT SA MAZA GUDU Littafi na Hudu (4) Part A Lokacin da Gimbiya Malika da Jarumi Hibairu suka ruguntsume da azababben yaki sai gaba daya jama'ar dake cikin filin gasar suka kamu da tsananin mamaki da al'ajabi saboda basu taba ganin gumurzu irin saba.Gaba daya sauran jaruman gasar ma saida suka tsorata da ganin wadannan jaruman biyu,domin basu taba ganin mutanen da suka iya sarrafa takobi ba,kuma suna yaki ne da matukar zafin nama na gaban kwatance tamkar jikinsu bana jini da tsoka bane.Da farko saida suka shafe kusan rabinsa'a suna kaiwa junansu sara da suka kowannensu na iya karewa gami da maida martani amma Jarumi Hibairu yafi Malika iya yaki,zafin nama da iya sarrafa takobi.Domin wata irin gagarumar jarumtaka da bajinta ya rinka yi yana shawagi a samanta kamar tsuntsu,kuma ya zamana cewa da kyar take iya kare saransa.Tun tana iya karewar ma da kyar har ya zamana cewa ta fara durkushewa kasa saboda gajiya,kawai sai gani akayi Hibairu ya buge takobin Malika daga hannunta ta fadi kasa can gefe daya kuma ya tsirata da tasa takobin yana mai saita makoshinta kuma yana murmushi.Nan take filin ya rude da shewa a ka kama yiwa jarumi Hibairu tafi da jinjina.A wannan lokaci gaba dayan attajiran cacac mutum daya ne jal ya zabi Hibairu a matsayin gwaninsa don haka koda a kaga ya sami wannan nasara sai kowannensu ya kamu da tsananin mamaki gami da nadamar rashin zabarsa,gashi a dokarsu tayin wannan caca babu damar mutum ya sauya jarumi face an gama zagayen farko na gasar.A bangaren sadauki Aryan kuwa tunda yaga Hibairu Yafi Malika iya yaki da jarumtaka sai jikinsa yayi sanyi mamaki ya turnukeshi ainun,bai san sa'adda ya kama yin zancen zuci ba yana mai cewa a ransa duk yadda akayi BASAJA ne ya shiga wannan gasa ta jarumta saboda wata bukata tasa dabam,amma badon ladan daza'a biya mutum ba,wata kila so yake ya mallaki wannan zukekiyar buduwar 'yar sarki Misra wato Gimbiya Zuhura.Yana cikin wannan tunani ne yaga wani jarumin gasar ma'abocin kyau da kwarjini ainun yazo kusa dashi ya tsaya fuskarsa cike da murmushi kawai sai jarumin ya dubeshi yace,amma uwargidanka Gimbiya Malika ta bani Kunya domin yadda nake jin labarin jarumtakarta bai kamata ace lokaci kankani haka har an sami galaba a kanta ba.Koda jin wannan batu sai Sadauki Aryan ya fusata ya dubi bakon jarumin cikin alamun fushi yace,in banda abinka ai idan ana ta barawo dole ne ayi ta mabi sawu,shin bakaga irin gagarumar jarumtakar da abokin gwamin naya keyi ba ne,tunda dai kana cikin gasar ai zaka kara dashi in yaso zan gani ko kaima bazaka bamu kunyar ba.Koda jin wannan batu sai bakon Jarumin ya bushe da dariya yace,hakika ka fadi gaskiya yakai Sadauki Aryan,domin gani ya kori ji,lokaci zai bambance komai.Koda gama fadin hakan sai Jarumin ya bar inda Aryan ke tsaye ya kara matsawa gaba a lokacin da Aryan ya bishi da kallo cikin tsananin mamaki.Ba komai ne ya bashi mamaki ba face yadda akayi wannan bakon jarumi ya san sunansa,abu na biyu kuma daya lura dashi dangane da jarumin shine yana kama da sarki Hilairu mutuka.Anya kuwa wannan ba 'dan uwan sarki Hilairu bane?Kash ina ma ace bana cikin jaruman gasar nan da nan da nan zan ruga naje na kirawo sarki Hilairu yaga mai kama dashi,abu na uku daya kara daurewa sadauki Aryan kai shine wai shin me yasa tunda ya shigo cikin garin nanne abubuwa suka zuwar masa kamar almara?Da farko ya hadu da jarumi Hibairu a matsayin nakasasshe kuma almajiri amma yanzu gashi a matsayin lafiyayye sannan kuma yanzu ya hadu da wani bakon jarumin wanda ko a mafarki bai taba ganin mai kamarsa ba amma gashi yasan shi harma ya fadi sunansa dana Gimbiya Malika.Lokacin da Gimbiya Malika taga Jarumi Hibairu yasa ta durkushe kasa a gabansa har ma ya kade takobinta daga hannunta sai ta cika da tsananin mamaki kuma ranta ya baci ainun saboda in banda Mahaifinta Sarki Sharkuf babu wani jarumi daya taba samun irin wannan nasara farat daya a kanta ba.Cikin alamun tsananin fushi Gimbiya Malika ta mike tsaye zumbur tana mai gyara tsayuwarta kuma ta dunkule hannayenta biyu alamar cewa a shirye take a gwada 'yar gwanji.Koda ganin haka sai Jarumi Hibairu yayi murmushi kuma ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dubeta yace,yake wannan 'yar sarki zaifi kyau ki sallama akan cewa na lashe wannan gasa a kanki saboda bana son ko kadan na lalata wannan kyakkyawan jiki naki da naushi,kiyi duba izuwa ga masoyinki can Sarki Hilairu ya kura mana idanu,ga dukkan alamun hankalinsa a tashe yake baya son muyi wannan fafatawa.Koda Hibairu yazo nan a zancensa sai Gimbiya Malika ta cika da tsananin mamakin Hibairu ta ayyana a cikin ranta tace,anya kuwa wannan mutum ne?Ina ganin dai aljani ne ya shigo cikin mutane in ba haka ba ya za'ayi yasan ko ni wacece har ma ya san abinda ke cikin zukatanmu nida Sarki Hilairu.Ai da ganin wannan tsananin kyawin nasa ma kasan cewa ba mutum bane aljani ne.Duk da haka sai na jarraba karfin damtsena akan nasa koda kuwa zai cutar dani domin ta hakane ma zan dada ganewa idan mutum neshi.Koda gama fadin hakan sai Gimbiya Malika ta ruga izuwa kan Jarumi Hibairu,koda ya rage saura baifi taku uku ba su hadu sai ta daka tsalle masa ta kai masa mugun duka a kirjinsa.Cikin bakin zafin nama ya kaucewa dukan nata kafarta ta naushi iska,kawai sai ta wuntsila jikinta ta kawo masa wani dukan da daya kafar tata akan fuskarsa.Kawai sai ya cafi kafar tata da hannun yayi hajijiya da ita a sama tamkar yar tsana ce a hannunsa yayi kamar zai fyada ta da kasa a lokacin da hankalin kowa ya dugunzuma a filin saboda indai ya fyadata da kasa zata iya kakkaryewa koma ta rasa rayuwarta gaba daya. Tuni a wannan lokaci kowa ya mike tsaye an bude baki ana jimami kowa ya saddakar da cewa Gimbiya Malika ta mutu,ba zato ba tsammani sai akaga Jarumi Hibairu ya ajiyeta a hankali ya juya da baya yana mai daga hannayensa sama alamar cewa yayi nasara,ai kuwa sai filin gurin ya rude da shewar jama'a aka kama yi masa tafi da jinjinaCikin sanyin jiki gami da mamaki Gimbiya Malika ta mike tsaye ta koma cikin jaruman gasa ta tsaya.Ba komai ne ya bata mamaki ba face abu biyu,abu na farko shine bata taba gumurzu da jarumin data kasa taba shi ba ko kaishi kas ba face Jarumi Hilairu,abu na biyu kuma shine tayi matukar mamakin dalilin da yasa Jarumi Hibairu yaki kwalata da kasa?Shin tausayinta yaji a matsayinta na 'ya mace ko kuwa dai akwai wani dalilin dabam?Amsar da Malika ta kasa baiwa kanta kenan,a wannan filin gasa gaba daya babu wanda yafi Sarki Hilairu farin ciki bisa gani cewa ba'a yiwa Malika rauni ba,shi kuwa Sadauki Aryan hankalinsa ne ya dugunzuma ainun bisa ganin irin tsananin jarumtakar da Jarumi Hibairu wanda bai taba zaton cewa nada karfi haka.Nan take yaji zuciyarsa ta karaya a cikin wannan gasa bisa ganin yadda Gimbiya Malika ma ta wulakanta duk da tsananin jarumtakarta da kuma tunanin yana mai cewa a cikin ransa anya muwa zan iya tsianana wani abin arziki a cikin wannan gasa.A can bangaren da Sarkin Misra ke zaune tare da sauran abokansa manyan sarakai babu abinda suke tattaunawa face maganar Jarumi Hibairu saboda kasancewarsa bakon jarumin da babu wanda ya sanshi a nahiyar.Ita kuwa sarauniyar kyawawa wato Gimbiya Zuhura tun a karon farko da idanunta sukayi arba da Jarumi Hibairu sai ta kasa sukuni da nutsuwa domin nan take taji zuciyarta ta kama bugawa da karfi.Lokacin dataga irin tsananin jarumtakar da Allah ya bashi kuma ta kare masa kallo taga irin kyawun fuskarsa da kyawun surar jikinsa tamkar shiyayi kansa sai taji ta kamu da matukar son sa,al'amarin dayayi matukar bata tsoro da mamaki kenan,domin ko a mafarki bata taba zaton cewa zatayi soyayya ba.Komai kyan saurayi da iya adonsa komai matsayinsa idan yazo wajen Gimbiya Zuhura da sunan soyayya sai ya wulakanta kuma ya raina kansa,har kirari ake yiwa Gimbiya Zuhura da Sa Maza Gudu.Sau dayawa idan dan sarki yazo wajenta,to ko duniya za'a bashi gaba daya bazai yarda ya sake dawowa ba saboda shi yasan irin wulakancin daya gani.A kullum Gimbiya Zuhura tana yiwa mahaifinta kuri da alwashin cewa ita fa har yanzu bata ga wani 'da namiji ba wanda ya burgeta bare ta bashi soyayya.Bayan Jarumi Hibairu ya lashe gasar jarumta akan Gimbiya Malika wacce ta koma cikin jaruman gasa ta tsaya ta barshi shi kadai a tsaye a tsakiyar filin gasar jama'a nayi masa shewa gami da jinjina,attajirin daya zabe shi a matsayin gwaninsa na caca yana tsalle da murna sai alkalin gasarya shigo cikin tsakiyar filin gasar ya tsaya.Faruwar hakan keda wuya sai filin gasar yayi tsit yamkar babu mutane a cikinsa domin a saurari abinda alkalin gasar zai fada,nan take kuwa yayi gyaran murya sannan yace,yaku jama'a kamar yadda kuka gani da idanunku a zagayen farko Jarumi mai suna Hibairu daga Birnin Nurul Islam ya lashe gasa a kan Gimbiya Malika daga Birnin Madinatul Zauwara.Bisa ka'idar wannan gasa duk Jarumin dayayi nasara a karon farko sai ya sake fafatawa da mutum biyu,idan yayi nasara to ya haye zagayen farko na wannan gasa saura zagaye biyu cakal a gabansa.Koda jama'a sukaji wannan batu sai suka rude da shewa sannan alkalin gasar ya daga hannu aka sakeyin tsit yace,yanzu Jarumi Hibairu zai kara da Jarumi na biyu wanda ake kira da Ramzan daga Birnin Sin.Koda jin wannan suna sai gaba dayan filin ya rude da shewa take da yawa daga cikin yan kallon suka fara tausayin Jarumi Hibairu don sun tabbar dacewa ajalinsa ne yazo.Shidai Jarumai Ramzan ya kasance narkeken kato mai katon ciki gashi dogo kuma gashi mai kauri da kibar gaske,masana yaki sun tabbatar da cewa karfin saransa da nauyinsa yakai nauyin giwa guda kuma takobinsa lafceciyace mai fadin gaske gami da kaifin tsiya tamkar zabira don haka duk abinda ya sara da ita ko bishiya ce kuwa sai ya rabata gida biyi komai kaurinta idan kuwa ya matse gadon bayan mutum da hannayensa biyu saidai a rinka jin karar karyewar kasusuwansa haka kuma idan ya zauna akan cikin mutum saidai aga mutum na aman jini ta hanci da baki take zai sheka barzahu.A tarihin gasar jarumtakar da akeyi a ko ina a duniya indai ya shigeta shi yake karbar Kambu.Batare da bata lokaci ba Jarumi Ramzan ya shigo cikin filin gasar yana taku dai dai karfin takun sawayen nasa ne suka haifar da karamar girgizar kasa gami da tashin kura,shi Kansa Hibairu sai daya dan tsorata da yayi arba da wannan narkeken katon domin da farko ma ya zata bishiya ce tazo gabansa saboda take ya zama dan wada a gabansa.Abind aya fara daure masa kai shine ta yaya wannan mutum yake iya rayuwa a cikin sauran al'umma? Babu wata

Chapter 9 of 19