Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba tare da saninka ba,abu na farko shine rashin sanar dakai koyan yakina wanda na barshi sirri saboda wadansu dalilai,abu na biyu kuma shine huldar kasuwancin dana kulla da wadansu manyan sarakai da manyan attajirai na duniya,ina mai tabbatar maka da cewa a nahiyar nan tamu kaf bababu wata bafatakiya data kaini arziki da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano cewa fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa ga kasashen dake yakar juna kuma bani da bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman wadanda dole saida su za'a iya budewa komai jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa ban tara dukiya domin komai ba sai domin na kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin wulakantani ko cutar dani da sauran talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya kare kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen gari nasa a gina mini fada ta musamman inda zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da mahaifiya da sauran masoyana har izuwa karshen rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa jawabinta,sai mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar nami ba'a taba samun mai basira da hangen nesa kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba cikin kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai kowa yasan wannan dukiya da kuma inda take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku bisa wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da wanda ya dace ya zama ya gajeni daga cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan gidan sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka warware wannan matsalar ba tunda da akwai alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin hakan? Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki zauna tare dani in yaso ki tura amintattun yaranki su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin haka,sai sarki Sharkuf ya mike tsaye yayi tafitaku uku,yana mai juya mata baya,sannan yace yake 'yata kiyi sani cewa ni fa yanzu girma ya fara kamani tunda yanzu shekaruna sunkai sittin da takwas a duniya bana son naga kina yin nisa dani tunda kullum lokacina karewa yake,kuma har yanzu akwai sirrikana da dama wadanda baki sansu ba,asali ma dan'uwanki Yarima Lahaman ya fiki saninsu saboda ya girmeki sosai kuma na jashi a jikina daga kuruciyarsa kawo izuwa girmana kafin na fahimci cewar shi azzalumine wanda baya kishin talakawansa na gujeshi.Lokacin da Sarki Sharkuf yazo nan a zancensa sai hawaye ya subuto masa gimbiya Malika ta sake dafe hannun sarki akan cinyarta ta dubeshi tace,ya kai abbana kamar yadda bakasan rabuwa dani daidadi da rana daya haka nima na kasance,amma ina rokonka alfarmar nayi wannan tafiya domin itace tafiyata ta karshe akan harkokin kasuwancina kuma acikin tane nake so na cika wani buri nawa wanda bani da kamarsa a raina.Kayi hakuri bazan iya gaya maka wannan sirrin ba kamar yadda kaima bazaka iya gayamin hawa KARAGAR MUKIN kasar nan ba,amma zaka san nawa burin da zarar na dawo kuma nayi maka alqawain cewa bazan fi wata uku ba zan dawo.koda jin wannan batu,sai shima sarki Sharkuf hawaye ya zubo masa ya kamota ya rungumeta a kirjinsa suka dan jima a kankame da juna.Suna cikin wannan hali ne Malika taji an kirawo sunata,a tare suka waiga baya. SHIN WANENE WANDA YA SHIGO MUSU BATARE DA NEMAN IZINI BA? SARKI SHARKUF ZAI BAR GIMBIYA MALIKA TAYI WANNAN TAFIYAR? YARIMA LAHAMAN ZAI BATA WANNAN BAWAN? INA LABARIN BAWAN DA YARIMA LAHAMAN YA KAMO? TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA LAHAMAN WAYE ZAI GAJE KARAGAR MULKIN SARKI? MU HADU A CIKIN LITTAFI "SA MAZA GUDU" LITTAFI NA BIYU(2) DON JIN WADANNAN AMSOSHI. AMMA MENE HASASHEN KU? Suleiman zidane kd whatsapp 09064179602 SA MAZA GUDU Littafi na biyu(2) Complete book 2 Typing Suleiman zidane kd. Whatsapp 09064179602 ................ A tare suka waigo baya suka duba,sai suka ashe Lasurat ce mahaifiyar Malika.Ta tunkaro su fuskarta cike da alamun damuwa.Koda ganinta sai sarki ya mike tsaye ya taryeta yana mai rike hannayenta a lokacin da ta kurawa hannun Malika idanu.Sarki yace kwantar da hankali yake Ummul Malika,kiyi sani cewa raunin da Malika taji Karami ne kuma da wuri zata warke.Koda jin wannan batu,sai murmushi ya kubucewa Lasurat tayi doguwar ajiyar numfashi tace,to nagode da abinda ya tsaya iya haka amma yaya akayi ta sami wannan raunin alhalin nasan cewa duk inda zata je kana bata tsaro mai kyau na dakaru?Sarki Sharkuf ya numfasa yace,ni kaina nayi mamaki yadda al'amarin ya faru,amma hakan bazata sake faruwa ba.Yanzu ki tafi da ita izuwa turakarki ki lallabata ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali domin akwai alamun cewa tana cikin damuwa. Batare da wata gardama ba Lasurat ta kama hannun Gimbiya Malika tajata suka nausa izuwa can cikin gidan sarautar.Shi kuwa Sarki Sharkuf sai ya bita da kallo cikin alamun tsananin damuwa gami da tunani mai zurfi.Na take idanunsa suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa saboda tausayin da ya kama shi.Ba komai ne ya sanya masa wannan tausayi ba face a binciken da yayi a hallarar tsafinsa ya gano cewa bayan mutuwarsa sai wannan 'ya da uwa sun rabu sakamakon wata kaddara wacce basu isa su guje mata ba.Tunda farkon Yammaci Gimbiya Malika ta caba ado tayi shirin tafiya izuwa wannan Gida na Yarima Lahaman.Bayan ta hama shiri tsaf,sai hankalinta ya DUGUNZUMA bisa dalilai biyu,dalili na farko shine bata san yaya taza sulale ta fice daga gidan sarautar ba tare da wani ya ganta ba.Dalili na biyu kuma bata san ko nawa Yarima Lahaman zai siyar mata da wannan bawan nasa ba Wanda taji ta kamu da tsananin sonsa farat daya.Duk da tasan cewa komai tsadar bawan zata iya sayensa,amma tayaya zata iya fitar da kudade masu yawa daga gidan sarautar batare da sarki ya gane dukkan shirinta ba?Idan tace kogon ta na dukiya zataje ta debo kudin tafiyar mai tsawon gaske ce,ba zai yiyu ba.Bisa wannan dalili ne yasa Gimbiya Malika ta kama zarya a cikin babban falo na turakarta ta kasa zaune ko tsaye.Kuma Hankalinta ya DUGUNZUMA,taji kamar ta fashe da kuka saboda bata da wani buri da kuma 'doki wanda yafi taje ta gana da wancan bakon bawa ko don ma ta sake ganin fuskarsa,Zuciyarta ta huta da tsananin begensa da tunaninsa.Malika na cikin wannan hali ne Shugabar kuyanginta wata mace yar kimanin shekara arba'in da daya mai suna Lasmira ta shigo cikin falon tare da wadansu kuyanci guda uku,domin su gabatar da irin aiyukan da suka sabayi kullum.Koda Lasmira taga gimbiya a tsaye tana kaii kawo cikin alamun damuwa,sai ta sallami wadannan kuyangi guda uku dake tare da ita,suka juya da baya suka fice daga cikin falon.Lasmira ta karasa gaban Malika ta dubeta tace,Ya shugabata menene ya dameki haka harzaki kasa zama ko tsayuwa?Koda jin wannan tambayar,sai Malika ta koma kan kujera ta zauna tayi shiru kamar baza tace komai ba,tana mai kurawa Lasmira idanu.Daga can sai tayi gyaran murya ta dubi Lasmira cikin nutsuwa tace,yake Lasmira kiyi sani cewa na yarda dake kuma nasan zaki iya rufe sirrina tunda tun ina yarinya karama kike aiki a karkashin Mahaifiya,kuma ban taba jinta tayi korafi akankin yi mata wani laifi ba,bisa wannan dalili yanzu zan sanar dake abinda ke damuna akan amana kuma ina son ki bani shawarar abinda zanyi na sami mafita.Nan take Gimbiya Malika ta zaiyanawa Lasmira duk bukatunta.Koda jin wannan bayanin nata,saiLasmirata kyalkyale ta dariya.Al'amarin daya bawa Malika haushi da mamaki kenan tace,mene kuma abin dariya a cikin wannan Al'amarin?Lasmira tace,ai gani nayi ga magani a gonar yaro amma bai sanshi ba,ai warware wannan matsala taki abu nemai sauki tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai.Abinda nake so dake kawai shine kibi duk irin umarnin dana baki,in kikayi haka dake da duk adadin kudin da kike bukata zaku isa kofar gidan Yarima na can bayan gari a asirrance kuma zaki dawo a asirrance batare da kowa ya sani ba.Ko jin wannan batu,sai farincik ya lullube Malika ta dubi Lasmira cikin zumudi tace,Fadi duk irin abida kike so nayi.Lasmira tayi murmushi tace,yanzu dai da farko ina son ki bani Dinare dubu goma kacal wanda zanje na aiwatar da wadansu ayyuka a cikin gidan nan dasu,zan dawo nan da kafin cikar rabin sa"a.Batare da gardamar komai ba kuwa sai Malika ta shiga cikin kuryar turakarta ta debo dinare dubu goma a cikin jakar kudi ta mikawa Lasmira.Lasmira na karbar wannan kudi sai ta boyesu acikin rigarta sannan ta juya ta fice daga cikin turarkar.Lasmira bata zame ko ina ba sai can kofar dakin shugaban dakarun dake tsaron gidan sarautar,wani barden jarumi wanda ake kira da suna Mahutur bin Kauzif.Da isarta sai ta kwankwasa kofar dakin sau biyu kacal,faruwar hakan ke da wuya sai Muhutur yayi magana daga ciki yace,to Lasmira shugabar yan cuwacuwar gidan nan yau kuma dame aka zo mini don nasan cewa unguwa bata jewar banza.Lasmira tace ai sai ka fito waje kaji abinda nazo dashi.Muhutur yace ai zaifi kyau ki shigo daga ciki komai zaifi sirri.Idan kuma matarka tazo ta ganmu fa sai ta zata amanarta zanci kuma ka sani cewa kawata ce ko?Haka ne to bari na kimtsa gani nan fitowa.Jin kadan saiga Muhutur ya fito yana goge bakinsa ga dukkan alamun abinci ya gama ci.Maimakon Lasmira ta bude baki tace wani abu,sai ta dauko kudin Dinare dubu uku ta mika masa.Cikin kaduwa da Mamaki Muhutur ya karbi kudin yana mai jinjina su akan tafin hannunsa,sannan yayi waige waige da dube dube yai sauri ya Soka kudin a cikin aljihun wandonsa ya dubeta yace,wannan kuma fa na menene?shin wani abu za'a siyowa Gimbiya a boye?Lasmira tace a'a itace da kanta take son ta fita daga cikin gidan sarautar nan tare da dukiya mai yawa saboda taje ta siyo wani bawa a can gidan Yarima dake bayan gari,kuma komai ana sin ayi shine a asirrance ba tare da sarki ya sani ba. Koda Lasmira tazo nan a zancenta,sai hankalin Badakare Muhutur ya DUGUNZUMA ainun ya rasa abinda ke masa dadi domin yasan cewa hadarin dake cikin wannan aikiyana da yawa saboda ko yaya aka sami akasi ya rasa aikinsa kenan .Don haka sai ya murtuke fuskarsa kuma ya murza gashin bakinsa yace,kai ungo kudinki bazan yi wannan aiki ba,hadarin dake cikinsa yafi abinda kika bani.Koda jin haka,sai Lasmira ta sake saka hannunta cikin aljihunta ta dauko wani damin kudin Dinare dubu uku ta wurga masa tace,ga wadansu dinare dubu ukun kaga ke nan inka hada dana farko sun zama dinare dubu shida daidai albashinka na shekara biyu kenan,shin ka amince yanzu zakayi wannan aiki?Koda jin wannan tambaya,sai jikin Muhutur ya kama kyarma ya rasa hukuncin da zai yankewa kansa,saida yayi duru duru yayi gaba yayi baya sannan ya juyo ya fuskanci Lasmira yace,to ina kudin dakarun dake aiki a yau?kinsan cewa suma sai na raba musu wani abun sannan zasu ki duba duk abinda za'a wuce dashi.Koda jin haka sai Lasmira ta zura hannu cikin aljihun rigarta ta dauko wani kullin kudi na dinare dubu ta mikawa Muhutur tace,wannan dinare dubu ne nasan ya isa ka raba musu,wane lokaci za'a fito da Gimbiya da dukiyarta?Muhutur yayi shiru yana tunani sannan yace,ai yau talata ce kuma duk ranar talata da yammaci ne sakalaiya Sarki ke kwanciya domin ya huta ba zai sake fitowa waje ba sai gobe da safe don haka a daidai wannan lokaci za'a fito da Gimbiya.Lasmira tayi murmushin farin ciki ta juya da baya da gudu taje ta sanar da Gimbiya Malika duk abinda ya faru tsakaninta da shugaban dakaru Muhutur.Sannan sai ta dauko wani shudin magani a cikin wata yar karamar kwalba ta mikawa Malika tace,ungo wannan kisha makurwa biyu kacal,batare da gardamar komai ba ko tsoron wani abu sai kawai Malika ta karbi ruwan maganin ta cire murfin kwalbar tasa a bakinta tasha makurwa biyun kamar yadda aka umarce ta.Bayan kamar dakika ashirin da faruwar hakan sai Malika ta fara jin jiri,ta kama tangadi daga tsaya sannan ta tafi luu.. zata fadi,amma sai Lasmira ta tafa hannunta sau uku,saiga wadansu hadiman gidan su Gimbiya Malikan guda uku karti sun shigo,dayansu dauke da wata doguwar akwatin katako.Da zuwansu sai suka ajiye akwatin suka bude shi saiga matattun beraye,kyankyasai da sauran kananan kwari masu addabar mutane a gidan.Kawai sai suka daga abinda ke dauke da wadannan kwari daga cikin akwatin sai ga katon fiki a kasan akwatin aka saka gimbiya Malika a ciki sannan suka dauko katakon dake dauke da matattun kwarin suka dora a saman Gimbiya Malika ya zauna darama.Komai kallon kurilla,mutum bai isa ya iya ganewa cewa akwai wani abu a kasan akwatin,saidai ayi tunanin cewa akwatin cike take da wadannan kwari babu komai a kasanta.Bayan an rufe Malika a cikin wannan akwati sai kuma wannan hadimai uku suka shiga can cikin kuryar turakar gimbiya suka rinka fito sa irin akwatunan har guda arba'in,ashe kowacce a kasanta lu'u lu'u aka zuba dunkim a samanta kuma aka zuba matattun kwarin.Akwatuna guda arba'in da daya aka loda su a kan keken shanu aka tunkari kofar fita daga cikin gidan sarautar.Saida aka wuce ta cikin kofofi tara,kuma duk kofar da akazo ko tsayar da keken shanun ba'ayi,da an hango su daga nesa sai a bude musu kofa tun kafin ma su iso.Saida kawai su wuce.Haka dai direban keken shanun ya cigaba da wucewa har ya iso kofar karshe,har masu gadin sun janyo kofar sun bude masa zai fita kenan,sai sukaji an daka mus tsawa,a firgice direban keken shanun tare da dukkan masu gadin kofar kimanin su dari suka waiga suka duba inda sautun tsawar ya fito saboda sun dauki murya.Ba muryar wani bace face ta sarki Sharkuf yana tahowa daga cikin gidan sarautar bangaren da turakarsa take.Sarki Sharkuf ya kara so garesu fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri,ya dubi direban keken shanun ya sake daka masa tsawa a karo na biyu yace,ya kai Zarhus yau kuma wace irin sharace za'a fitar da ita da wannan yammaci sakaliya haka?Koda jin wannan tambaya,sai jikin Zarhus ya kama tsuma ya sauko daga kan keken shanun ya zube a kasa gaba Sarki tamkar zai masa sujjada,sannan ya bude baki cikin rawar murya yace,Ya shugabana sharace ta matattun kwari kuma tayi yawa ne shi yasa kafin mu gama kwasheta lokacin ya kure mana.Koda jin wannan batu,sai Sarki Sharkuf ya sake bata rai yace,ban yarda ba a bude akwatunan gaba dayansu na gani.Dajin haka sai dakaru suka rugo izuwa kan keken shanun suka kama bude akwatunan sarki Sharkuf yazo kan akwatin farko wacce a karkashinta ne Gimbiya Malika ke kwance tana fama sharar barci kamar gawa.Koda sarki Sharkuf yaga matattun beraye da kunamai da kyankyasai har sun fara doyi sai yayi sauri ya toshe hancinsa.Har ya yunkura zai duna cikin ta biyu sai ya dawo da baya ya daga kwagirinsa da nufin ya lumata cikin akwatin farko domin ya jiyo karshen zurfinta,kawai sai yaji an kwala masa kira,yana waigawa baya yaga ashe shugaban tsaro na gidan ne ya tawo da gudu yana sassarfa da tuntube kamar wanda zai fadi yana cewa,ka gafarceni ya shugabana nayi kusjure da baka riskeni ba anan bakin kofa.Koda jin wannan batu,sai sarki Sharkuf ya basa luma kwagirinsa a cikin akwatin ya juyo ya fuskanci Badakare Muhutur yana mai kyalkyala dariya yace haba yakai Muhuru ai bazaka tabayin laifi ba a wajena saboda yau shekara arba'in da biyar kenan kana aikinka na tabbatar da tsaro,ba'a taba kama da laifi ba,wata almundahana ko rashin gaskiya ba.Shin ka caje wadannan akwatunan guda arba'in da daya na shara ka tabbatar cewa sharace zalla a ciki ba'a boye wani abu ba?Muhutur ya gyada kai yace,na caje su gaba daya ya shugabana,babu wani abu a ciki sabanin wanda ka gani.Koda jin haka sai Sarki Sharkuf ya saki ransa,hankalinsa ya kwanta,ya kyalkyale da dariya sannan ya dafa kafadar Muhutur yace,na yarda dakai dari bisa dari nasan cewa ba zaka taba cin amana taba,kuma bazaka taba yarda ayi wani abu ba wanda zai cutar dani koya cutar da wani nawa.Koda gama fadin haka sai Sarki Sharkuf ya dubi Zarhus yace ko kayan laifi ka dauko a yaudai ka sha.Zarhus ya risina yayi godiya sannan ya sake hawa kan keken shanun ya saki linzami ya fice daga cikin gidan sarautar.Sarki Sharkuf ya bishi da kallo kawai a lokacin da Muhutur yaji idanunsa sun ciko da kwalla kamar ya fashe da kuka,saboda yasan cewa tabbas yasha cin amanar sarki ana shigowa gidan da abubuwan da basu dace ba ko kuma a fitar da wasu. Tafiyar rabin sa'a kacal direba Zarhus yayi ya iso kofar gidan yarima Lahaman dake bayan gari.Da isowarsa sai shugaban masu gadin gidan ya dubeshi ya daka masa tsawa yace,kai kuma wane irin wawa ne da zaka kawo shara nan gidan?Waye ya baka umarnin yin hakan?To kayi sauri ka bace daga nan tun kafin Yarima ya fito ya ganka yasa takobi ya sareka.Maimakon Zarhus yace wani abu sai kawai ya sauko daga kan keken shanun ya bude wannan akwatin ta farko.Yana budewa saiga Gimbiya Malika kwance a ciki tamkar gawa bayan ya dauke matattun kwarin dake samanta.Cikin kaduwa da mutukar firgici masu gadin gidan sukayi kamar su ruga izuwa cikin gidan amma sai suka fasa sakamakon ganin Malika zaune a cikin akwatin tamkar gawa ta faso kabari.Ashe dama can kuyanga Lasmira ta auna iya tsawon lokacin da Malika zatayi barcin kuma ta farka adaidai lokacin da Zarhus ya iso kofar gidan Yarima Lahaman.Shiyasa tace da ita tasha wannan maganin barcin makurwa biyu.Koda Malika ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin keken shanu,ga akwatuna arba'in a bayanta kuma gata a kofar gidan Yarima Lahaman,sai farin ciki ya lullubeta ta sako kasa daga kan keken shanun sannan ta dubi shugaban masu gadin ta daka masa tsawa tace zakaje ka gayawa ubangidan naka cewa gani na iso ko aa?Kodajin haka sai badakaren ya juya da sauri ya fada cikin gidan. Acan cikin gidan kuwa sarki Hilairu tare da ragowar jama'arsa bayi mutum dari na zaune sunyi jugum jugum suna tunanin halin da suka tsinci kansu ta rayuwar kunci,damuwa dakuma wahala.A yau dinma tun safe da aka basu abinci ba'a sake basu ba.Gashi har rana ta fadi magariba ta doso kal.Dukkanninsu jikinsu yayi sanyi lagwab tamkar jikakkun tsumokara musamman matan cikinsu wadanda dole ne mutum ya kamu da tausayinsu Idan ya kallesu saboda su masu rauni ne basu da juriya irinta maza. Kwatsam sai ga.... Suleiman zidane kd . Kwatsam sai ga Yarima Lahaman ya shigo cikin dakin dakarunsa na take masa baya fuskarsa a murtuke babu alamar annuri.Kai tsaye Lahaman ya durfafi inda sarki Hilairu ke zaune ya dube shi yace,ya kai wannan sarki naga alama cewa kai mutum ne mai sa'a domin gashi ina shirin na siyar dakai gobe ga manyan attajiran da zan sami babbar riba,amma sai gashi 'yar uwata tazo yanzu domin ta siyeka.To ka sani cewa karkon kifi zakayi domin babu wani abu da ya taba shigowa hannuna kuma ya kubuta.Nayi maka alkawarin ko ka subuce mini yanzu nan,ba da dadewa ba saika dawo hannuna,kuma saina siyar dakai ga inda za'a tafi daku izuwa wani bangaren na duniya mai nisan gaske inda ko duriyarka ba za'a sake jiba.Koda gama fadin hakan,sai Yarima Lahaman ya fice daga cikin dakin tare da dakarunsa masu take masa baya suka nufi can wajen gidan.Gimbiya Malika na tsaye kusa da keken shanunta mai dauke da akwatunan kudi saiga yarima Lahaman ya fito daga cikin gidan.Koda yaga Malika a gaban keken shanu mai daukar akwatunan sharar gidan sarauta saiya bushe da dariya yace,yanzu yar sarki ce guda a cikin kekn daukan shara,to yanzu ina kudin da zaki siyi bawan?Koda jin wannan tambaya,sai Malika ta turbune fuskarta tace,a ina ka taba ganin anyi cinikin kifi a ruwa,muje ka nuna min abinda nazo siya na ganshi a raye cikin koshin lafiya sannan muyi cinikin ba biya.Koda jin haka,sai Yarima Lahaman yayi murmushi yace,Tabbas kina da wayo da dabara ki biyo ni a baya muje kiga muradinki.Yana gama fadin hakan sai ya juya ya shige cikin gidan.Kawai sai Malika ta dubi dakarun dake kofar gidan tace,ba baku ajiyar keken shanuna da direbansa,idan na fito na iske wani abu ya taba lafiyarsu abaka cin rayuwarku.Tana gama fadin hakan sai tabi bayan Yarima Lahaman da sauri har suka iso dakin dasu Sarki Hilairu ke ciki.Da zuwansu aka bude musu kofa suna shiga sai Sarki Hilairu da Gimbiya suka hada Idanu take yaji zuciyarsa ta buga da karfi karo na biyu na haduwarsu.Ita kuwa Malika ji tayi gaba dayan tsigar jikinta ta tashi kuma sai kwarjinin Hilairu da tsananin kyawun fuskarsa suka dimantata tayi sauri ta dauke mazansu da matansu.Take taji ta kamu da tsananin tausayinsu don haka sai ta dubi yarima Lahaman tace ciniki ya sauya salo yanzu ba mutum saya kadai nake so ka siyar min ba,gaba dayan bayin dake cikin dakinnan nake bukata.Koda jin wannan batu,sai yarima Lahaman ya bushe da dariyar keta yace,yaya ke da bakizo da kudin siyan mutum daya ba ma amma kike tunanin siyan mutum dari?Malika tace,ai sai ka bari mu gama cinikin tukunna idan kaga na kasa biyanka kudinka shine kake da bakin magana.Lahaman yayi gyaran Murya sannan yace,shidai wannan saurayi ma'abocin kyawu da kike son ki fansa sai kin biyani kudi dinare dubu dari biyar.Su kuwa ragowar yan'uwan nasa ko wane dayansu sai kin biya dinare dubu hamsin sannan zaki mallake su.Koda jin wannan batu,sai Gimbiya Malika ta dubu Yarima Lahaman cikin alamaun fishi da bakin ciki tace,haba yakai yarima ai ko ranar kasuwar garin nan ba'a taba siyar da bawan da darajarsa takai dinari dubu biyar ba amma kai yanzu gashi kace na siyi kowane daya akan farashin dubu hamsin.Shidai wanacan saurayin ma'abocin kyau da kwarjini na yarda na siye shi a farashin da ka fada,domin darajarsa ma tafi haka,amma ina neman sassauci akan ragowar bayin.Koda jin haka sai Yarima Lahaman ya turbune fuskarsa yace,ai ba neman kai nake yi ba dasu,idan ba zaki iya siyansu ba a wannan farashin saidai ki hakura gaba daya.kuma inda kina bukatarsu sai ki biya kudinsu yanzu take sannan ki kada ki tafi dasu.Malika tayi murmushi tace,kudi ba matsalata bane yadda zan kashe su shine matsalata.muje wajen keken shanun na biyaka kudinka duka,amma lallai kasa a kwance wadan nan bayi daga cikin sarkoki su biyo mu izuwa waye.Batare da wata gardamar komai ba,yarima Lahaman yasa dakarunsa suka kwance bayin daga cikin sarkoko aka tusa keyarsu izuwa wajen gidan Sarki Hilairu ne akan gaba ana ingiza keyarsa ana kai masa bugu.Da fitowarsu kofar gidan sai aka jera bayin akan layi sahi sahu sannan Lahaman ya tsaya a gabansu dakarunsa kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin wannan tambaya sai ya sauko daga keken shanun ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka cika da tsananin mamaki yadda akayi ta mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna wannan aiki sannan suka kammala amma duk da haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da aka umarce su kuma suka rage kudade da yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya karba yana ta farin ciki da walwala sannan an saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar dayake so yana walwala batare da sun kareba.Koda Yarima Lahaman... Zidane kd.. Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido yaga wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani cewa babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk irin tsananin son da yake mata saboda ya kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin 'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunawa Yarima Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu na tara dukiya da baka da kaso daya cikin gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya a wannan zamani nice babbar dilar da babu kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna cikin shiri kwanan nan

Chapter 2 of 19