Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan karbeta na zama na ni ke sarrafata a duniya,ba don komai ba sai domin nayi maganin manyan azzalumai irinku.Yanzu dai gani ni kadaice na zo babu wani badakare ko guda daya daya rakoni don bani tsaro.Idan ka gadama ka turo min gaba daya dakarun naka su tare mini hanya kafin na isa cikin gari suce zasu kwaci wannan dukiya da wadannan bayin dana siya wajenka.Na rantse da gemun Mahaifinmu dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba.Idan kuma kana ganin cewa kai ne da kanka zaka tareni to ina jiranka ai KAR TA SAN KAR ce kuma shege ka fasa.Koda Malika tazo nan a jawabinta sai ta dubi su sarki Hilairu tace,wuce gaba mu tafi izuwa inda zan ajiye ku.Cikin tsananin farin ciki su sarki Hilairu suka wuce gaba sannan Malika ta hau kan keken shanu Zarhus ya tuka suka bi bayan su Hilairu.Dama tunda Gimbiya Malika ta fara bayaninta ga Yarima Lahaman sai jikinsa ya kama tsuma,idanunsa suka kada sukayi jawur ya kamu da tsananin bakin ciki kuma ya rinka ji kamar ya zare takobinsa yaje ya afka mata da yaki,amma sai ya daure ya hakura sa'adda ta fadi kalma mai zafi da muni a gareshi sai dakarunsa su yunkuro zasu afka mata,amma sai ya dannesu,saboda yasan cewa AJALIN su zasu gaiyata kuma shi kansa bazai iya karesu ba da komai.Har Saida Malika tayi nisa da barin kofar wannan gidan nasa har ya daina hangosu ita da dukan bayin data siya a hannunsa,sannan ya takarkare ya kwarar uban ihu mai tsananin ban tsoro sannan kuma ya durkushe kasa bisa guiwowinsa ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki.Adaidai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tafka walkiya da tsawo amma saboda tsananin bakin ciki sai Yarima Lahaman yaki tashi ya shiga cikin wannan gida nasa.Aikuwa take aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya,koda ganin yadda ruwa yake dukan Yarima Lahaman kuma gashi ruwa ne mai karfin gaske dauke da iska,sai daya daga cikin wannan dakarun nasa ya matsa daf dashi yace,ya shugabana zaifi kyau ka tashi daga cikin ruwan nan domin zai iya cutar da lafiyar...Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa tuni Yarima Lahaman ya shammaceshi cikin bakin ZAFIN NAMA ya zare takobinsa ya share masa makogwaro,kawai sai gani akayi jini yayi feshi daga cikin wuyan badakaren sannan ya fadi matacce.A sannanne Yarima Lahaman ya mike tsaye ya goge jinin dake jikin takobinsa akan gawar badakaren sannan ya mayar da takobin cikin kufe ya daga kansa sama yayi KURURUWA mai razanarwa tamkar zaki yayi GUNJI a dawa.Nan take duk wani abu mai rai dake kusa ya dimauce,hatta ragowar dakarunsa dake tsaye a wajen da wanda ke cikin gidan saida suka firgice suka rikirkice suna neman su cika wandonsu da iska,amma sabida tsoro sai suka kasa guduwa izuwa ko ina.A sannanne Yarima Lahaman yayi rantsuwa da darajar uwarsa yace,daga yau Malika baza ta sake yi masa wulakanci ba,kuma komai dadewa sai ya kasheta da hannayensa ya huce takaicinta,koda samun nasarar yin hakan na nufin mutuwar duk wani abu mai rai dake cikin kasar nan.Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya shige izuwa cikin wannan gida nasa. Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da suka yi dan nisa ga barin gidan Yarima Lahaman tare dasu sarki Hilairu itana bisa keken shanun su kuma suna tafiya a kasa bisa kafafunsu kuma taga hadari ya gangamo an fara walkiya,sai ta bayar da umarni aka rugu cikin wani kogon dutse domin a fake.Ai kuwa suna gama shiga cikin kogon dutsen nan ruwan saman ya tsuge,nan fa kowannansu maza da mata ya sami wuri ya zauna,aikuwa aka fara ruwan saman mai dauke da iska mai sanyi ya addabi kowa.Koda ganin haka sai Malika tayi amfani da karfin sihirinta na tsafi ta kunna wutar jin dumi har guda uku.Daya sai gaba dayan matan suka kewayeta dayar kuma sai mazan suka kewayeta,ya zamana cewa saura wutar guda daya babu kowa a gabanta,shi kansa Zarhus tuni ya zaro bargo a cikin keken shanunsa ya kwanta ya lullube jikinsa gaba daya.Nan fa ya rage saura Gimbiya Malika da sarki Hilairu a tsaye a can gefe daban daban suna kallon juna,kuma suna kallon wannan wuta guda daya data rage wacce babu kowa a gabanta,kamar hadin baki sai duk su biyun suka taho izuwa gaban wutar a lokaci guda suka zauna suna jin dumin kuma suna fuskantar juna.Tsawon 'yan dakiku dayansu bece uffan ba kawunansu na sunkuye suna kallon kasa.Kawai sai suka dago kai a tare kuma kowannasu ya bude baki da nufin yace wani abu,koda muryoyinsu suka sarke a lokaci guda sai suka kyalkyale da dariya saboda mamakin yadda al'amarin ya kasance haka.A sannane Gimbiya Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murmushi mai taushi tace,ya kawai wannan saurayi Ma'abocin kyau da kwarjini waye kai kuma yaya akayi ka tsinci kanka a cikin wannan rayuwa ta bauta?Kasani cewa a karon farko dana ganka jikina ya bani cewa ka fito daga babban gida kuma asalinka baka kasance bawa ba.Koda Malika tazo nan a zancenta sai taga hawaye a zubowa sarki Hilairu,al'amarin daya karya zuciyar kenan taji ta kara kamuwa da tsananin tausayinsa.Ta dubi Sarki Hilairu cike da tsananin tausayi tace,yakai wannan sarki me yasa kake zubar da hawayenka alhalin ka tsira daga hannun dan uwana kuma kasan cewa bazan taba cutar dakai ba,kayi sani cewar bana kubutar dakai bane don cutarwa,na kubuto daku ne domin tsirar daku daga cikin kangin da dan uwana zai saka ku a ciki.Koda Sarki Hilairu yaji wannan gada Gimbiya Malika,saiya girgiza kai ya saka hannu wansa ya share hawayensa ya dubeta duba na tsanake sannan yace,yake wannan gimbiya kiyi sani cewa ba ina kuka bane don shiga halin dana kasance a ciki ba,kuma banajin shakkar komai daga gareki na tabbata kin kasance mace mai tausayin na kasa dake.Wannan kuka da kikaga inayi inayinsa ne kawai don rasa matata danayi sannan kuma ina mutukar tausaya miki dake da mahaifinki da kuma sauran al"ummar wannan birni gaba daya.Koda dayazo nan adaidai zancensa sai Gimbiya Malika ta dago kai a cikin kidima ta dubeshi domin batasan wane irin tausayi ne Hilairu yake musu ba alhalin sun kasance basu da wata lalura data addabesu,babu fari bare wata cuta data kunno kai cikin kasarsu.Don haka cikin azama ta dubeshi tace,yakai wannan sarki sanar dani dalilin dayasa kake jin tausayinmu,meya faru haka da har ka kasance cikin tausaya mana alhalin da idanuwankan kaga ni babu rashin ci da sha a cikin birninmu sannan babu wata rashin lafiya uwa uba kasarmu tana dauke da mayakan da a kaf nahiyar nan ba a isa a zo aga bayansu ba.Tana zuwa nan a zancenta sai Hilairu ya tareta dacewa,ko kina da labarin SA MAZA GUDU?Gimbiya Malika tayi shiru tana tunani a cikin ranta ta girgiza kai alamar batada labarinsa.Sarki Hilairu yace,dakina da labarin SA MAZA GUDU dana sanar dake dalilin dayasa nake tausaya muku,amma idan kin koma cikin gidan sarauta ki tambayi mahaifinki wanene SA MAZA GUDU,in har ya sanar dake kadan daga cikin labarinsa ni kuma zan sanar dake dalilin da yasa nake tausayinku nake jin kanku badon komai ba sai don kyautatawa dakika yimin.Gimbiya Malika takara zuba masa idanu tana mamakin maganganunsa gareta tace,yakai wannan sarki ina bukatar ka sanar dani ko kadan daga ciki kafin naje ga mahaifina na tambaye shi wanene SA MAZA GUDU,inason kafara sanar dani ko yaya ne sannan ka sanar dani dalilin dayasa kake tausaya mana.Kodajin haka sai sarki Hilairu ya daga kai yace zan sanar dake kadan daga cikin alakarmu dashi,amma labarinsa sai idan kinje kin tambayi mahaifinki ya karasa miki sani akansa.Dajin haka sai takara gyara zama tana mai sauraronsa shi kuma ya ciga da cewa............. SA MAZA GUDU Littafi na biyu(2) Part D Dajin haka sai ta kara gyara zama tana mai sauraronsa shi kuma ya ci gaba da cewa: SA MAZA GUDU guguwa ce wadda batada abin tarewa a duk sa'ilin data nufo kasa ko nahiya,bata tsawaita,sannan masiface babba a cikin rayuwar duk wani mai rai dake doron duniya,ba'a fatansa ba'a kuma marmarin ganinsa.Duhu ne shi mai mamaye duk wani haske,masiface shi mai tattare da dukkanin masifa yake wannan Gimbiya,ki sani cewa wannan runduna ta SA MAZA GUDU bata da kula kan duk abinda ta sako shi a gaba,tana da ta'adi ga duk wanda ta fuskanta bata barinsa sai taga ta bata cikin kasarsa da jini,tayi masa ado da naman sassan bil'adama.Ina son ki sani cewa wannan sadauki da ake kira SA MAZA GUDU dan uwa ne a gareni wanda muka fito ciki daya,kuma a duniya bashi da wanda yake so sama dani don haka yabar ni akan mulkin kasar mu ya fita duniya.Zan cigaba da baki labarinsa a lokacin da kika samu saninsa daga mahaifinki.Sannan kuma ya cigaba da sanar da ita yadda Yarima Lahaman ya kashe masa matarsa a daren farkon amarcinsu bayan yayi mata fyade,wacce ta kasance tana tsananin kama da ita.Da yadda Yarima Lahaman tare da dakarunsa suka yita kashe mutane a birninsa suka kwashe dukiyoyinsu suka kone gidajensu kuma suka maishe dasu bayinsu.Koda Sarki Hilairu ya gama baiwa Gimbiya Malika wannan labari sai taji ta kamu da tsananin tausayinsa dana jama'ar sa fiye da koyaushe kuma taji sonsa ya karu ninki baninkin a cikin ranta don haka bata san sa'adda hawaye ya zubo mata ba,ta dubi Sarki Hilairu ta kwashe nata labarin ta zaiyana masa har duk irin kiyayyar dake tsakaninta da dan'uwanta Yarima Lahaman,da irin GWAGWARMAYAR data sha a rayuwa domin ta kare kanta daga sharrin Lahaman da kuma kokarin kawo rugujewar dukkan mugun nufinsa a nahiyar gaba daya.Daga karshe sai ta dube shi tace,yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ban siyeka ba a matsayin bawa na,na saye kune domin kubutar daku daga sharrin dan uwana Yarima Lahaman saboda nasan cewa sai ya tarwatsaku ya siyar daku ga mutanen daza su rarrabaku izuwa sassan duniya yanda har abada da yawanku bazasu sake ganin juna ba.Nayi muku alkawari indai ina raye kuma ina da koshin lafiya saina taimaka muku kun fita daga wannan nahiyar lafiya kun koma izuwa kasarku ta haihuwa kun sake gina birninku kunci gana da rayuwarku kamar yadda kuka saba.Duk abinda kuke bukata na kudi zan taimaka muku dashi,kuyi sani cewa yau saura kwana uku kacal nayi shiri na bar kasar nan saboda haka kuma saiku zauna cikin shiri domin tare zamu bar kasar nan.Lokacin da Malika tazo nan a jawabinta sai farin ciki ya lullube sarki Hilairu da dukkan jama'arsa.Suka kama yi mata godiya da jinjina suna shewa daga can sai sarki Hilairu ya dubeta cikin alamun damuwa da fargaba yace,yake wannan yar Sarki mai adalci yanzu bakya tunanin cewa wannan dan uwa naki bazai shirya tuggun da zai raba mu dake ba ba,bare har kin sami damar taimakonmu?Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Malika tayi murmushi sannan tace,idan har kaga wani tsautsayi ya sameku to tabbas nima ya sameni,idan har kayi imani cewa ni mai kaunace a gareku ba mai cutarwa ba to tabbas zaku tsira da mutuncinku,rayuwarku daafiyarku.Abinda nake bukata daku kawai shine kuyi duk irin umarnin dana baku,kada ku kuskura kuyi wani abu daban bisa yin kanku face bisa izinina da umarnina.Koda Gimbiya Malika tazo daidai nan a zancenta sai suka ji an dauke ruwan saman dake ta tafkawa yayi dif tamkar ba ayiba har wasu daga cikin jama'ar sarki Hilairu sun yunkura zasu fita daga cikin kogon dutsen sai Malika ta daka musu tsawa tace,ku koma ku zauna ashe bana gaya muku cewa kada kuyi komai ba sai bisa umarnina.Koda jin haka sai kowa ya koma inda yake ya zauna suka shiga taitayinsu,Malika ta mike tsaye tsam ta fito waje daga cikin kogon dutsen,tana fitowa saita tsaya cak ta kasa kunnuwanta sosai tana sauraran duk wani sauti dake cikin dajin kuma ta dubi gabas da yamma,kudu da arewa kawai sai taji a jikinta cewar akwai sauyin yanayi a cikin dajin wanda bata gamsu dashi ba,don haka sai kawai tayi nuni da hannunta izuwa kofar wannan kogon dutsen wanda su sarki Hilairu ke ciki.Nan take wata irin yanar tsafi mai kauri ta lullube kofar yadda babu wani abi da zai iya ratsawa ta cikinta.Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai taji takun sawaye da yawa a saman kan duwatsu ana gudu alamar cewa akwai mutane da yawa kewaye da wannan kogon dutse,kwatsam saitaji hucin kibiya ta taho da gudu zata soketa a kirji,cikin ZAFIN NAMA tasa hannunta ta cafe kibiyar kuma ta cillata izuwa saitin inda aka harbota kawai sai tajiyo ihun kato,saiga wanda kibiyar ta caka ya sallamo daga can saman dutsen dake gabanta ya fado kasa tim a gabanta ya zama gawa alokacin da jini ke kulbulowa daga cikin kirjinsa sakamon kibiyar data cake masa da hannunta tayi masa KAIKAYI KOMA KAN MASHEKIYA.Faruwar hakan keda wuya saiga dakarun sumame a cikin shigar bakaken tufafi kuma sun rufe fuskokinsu su da yawa suka baiyana akan duwatsun a saman Malika kuma dukkaninsu sun dana kibiya akan bakansu sun saitota.Ba tare da wata alama ta fargaba ba ko tsoro sai Gimbiya Malika ta gyara tsayuwarta tana kallonsu kawai.Nan take shugaban dakarun sumamen ya daga hannunsa sama yama mai bayar da umarnin a sakar mata harbi,aikuwa sai gaba dayan dakarun sumamen suka harbowa Malika kibiyoyin,nanfa suka ga abin Al'ajabi saboda duk kibiyar data durfafeta take take ruburbushewa tazama gari.Koda ganin abinda ya faru sai shugaban dakarun ya zare takobinsa take sauran yaran nasa sukayi koyi dashi suka dako tsalle kasa suna masu dira bisa kafafunsu suka rutsa ta da makamansu alhalin ko tsinke babu a hannunta da sunan makami wanda zata kare kanta.Lokaci guda suka afka mata gaba dayansu da nufin suyi mata rubdugu su daddatsa sassan jikinta.Cikin wani bakin zafin nama Malika tayi wani irin katantanwa a kasa ta buge kafafun dakarun sumamen dake gabanta duk suka zube kasa.Kuma ta taso sama kamar an harbota tayi fanka da kafafunta akan fuskokin dakarun sumamen dake samanta ta tarwatsa su da karfin tsiya kuma tayi wuf ta cafe takobin daya daga cikinsu.Kafin ta duro kasa ta hausu da SARA DA SUKA,nanfa wurin ya hargitse aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI yazama cewa duk inda Malika tasa gabanta saidai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe gona.Nanfa ihun mazaje ya cika dodon kunne jini ya rinka feshi da fantsama,karafkiyar karafa ta cika dodon kunne yazama cewa yawan dakarun sumamen yazama na banza amma saboda suna da bakin naci da kuma taurin rai sai gashi indai ba kawunansu Malika ta sara ba bata samun nasara.Aka cigaba da gumurzu sannan kuma sai suka rinka rugowa da gudu izuwa kofar wannan kogon dutse domin su shiga ciki su hallaka su sarki Hilairu,amma duk wanda ya sari wannan yana mai kauri wacce ta lullube kofar kogon sai yaji kamar dutse ya sara domin kuwa tarwatsin wutane ke tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma takobin nasu ke dakushewa.Saida aka shafe sama da sa'a hudu ana yin wannan masiffafen yakin tsakanin Gimbiya Malika da wadannan dakarun sumamen yazama cewa ita bata karar dasu ba,su kuma sun kasa koda lakutar jikinta kuma sun kasa shiga cikin wannan kogon dutsen.Koda shugaban dakarun ya lura da cewa Gimbiya Malika tayi musu mummunar barna don ta kashe masa yara sama da guda dubu daya,sai yayi sauri ya zaro wani karamin kaho ya busa,take gaba dayan dakarun nasa suka dira akan saman duwatsu sukabar Malika a tsaye ita kadai jini na diga a jikin takobinta,kawai sai shugaban dakarun ya diro kasa kusa da ita suka fara kallon kallo.Shidai wannan shugaban dakarun sumamen ya kasance narkeken kato mai kira irinta mutanen farko domin tsayinsa ya ninka na gimbiya Malika sau biyu kuma ya kasance kakkaura mai fadin kirji gami da lafta kaftan hannaye.Koda ya tsaya a gaban Malika sai ta zama yar kankanuwa tamkar an ajiye dan tsako a gaban shirwa,duk dacewar Malika ta yarda da kanta tasan cewa ita jaruma ce ta kwarai saida ta dan razana ta dan ja da baya.Nan take shugaban dakarun ya kama rigarsa da hannu ya tsarge ta daga sama har kasa,yayi wurgi da ita saiga damatsan sa da kwanjinsa sun baiyana kai kace duwatsu aka cuccura aka lika masa ajikin nasa ga kuma tarin jijiyoyi sun tashi sunyi burdin burdin kai da gani kasan cewa dole ne a sami gagarumin karfi a tare dashi.Kawai sai ya zare wadansu tagwayen adduna daga jikin guibin cinyoyinsa dama da hagu.Addunan sun kasance masu fadi da tsananin kaifi.Shugaban dakarun ya gyara tsayuwa yana mai bude hannayensa alamar cewa a shirye yake a fara kafsawa.Koda ganin haka sai itama Malika tayi wuf ta suri wata takobi dake kasa wato ta hada gud biyu hannunta ta gyara tsayuwarta tana mai fuskantarsa.Bayan sunyi kallon kallo na tsawo dakiku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna a tare suka kacame da azababben yaki. Zidane Wohoho idan jarumta ta hadu da jarumta kuma gwaninta tayi karo da takwaranta tofa dan kallo ya shigo tashin hankali bare wata halitta mai rai data ra'bi kusa da inda ake gumurzun.Koda Malika da shugaban dakarun suka fara kawai junansu sara da suka cikin zafin nama,juriya da bajinta sai nan da nan suka tashi hankalin bishiyoyin da dukkan duwatsun dake wajen domin kakkaryewa da farfashewa suka kamayi,sakamakon masifar kaifin addunan shugaban dakarun da kuma nauyin saransu.Nan fa tarwatsin wuta da hayaki ya cika wajen ya addabi sauran dakarun sumamen dake sama bisa duwatsu suna kallon wannan bakin artabu.Nanfa Malika ta gane cewa ta gamu da gamonta domin bata taba jin mutum mai nauyin sara da iya yaki ba kamar wannan shugaban dakarun face mahaifinta sarki Sharkuf.Duk sa'adda ya kawo mata sara ta kare da takubban hannayenta biyu saita durkushe kasa bisa guiwarta guda ko duka biyun ma saboda nauyin saransa.Badan ma tana da mutukar zafin nama ba gami da juriya da naci da tuni ya zargeta gida biyu.Duk da haka wani lokacin yana samin nasarar gabza mata naushi ko bugu da hannu da kafa ta kife kasa amma sai tayi wuf ta mike tsaye su cigaba da fafatawa.Lokacin da Malika ta fahimci cewa idan fa suka cigaba da gumurzu a wannan yanayi zai sami nasarar galabaitar da ita,idan kuwa ta galabaita take zai hallakata,nan take ranta ya baci ta tuna cewa wadannan dakarun sumame Yarima Lahaman ne ya turosu domin su hallakata kuma su hallaka su sarki Hilairu,idan kuwa hakan ta faru karshen adalci da zamam lafiya yazo karshe a nahiyar gaba daya tunda dai shi ma Sarki Sharkuf girma ya kama shi,a kodayaushe ajali zai iya riskarsa ya zama cewa babu wanda zai iya takawa Lahaman birki.Koda gama aiyana hakan a cikin ranta sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata kone nan taje taji wani irin gagarumin karfi ya shigeta don haka sai ta faki numfashin shugaban dakarun ta daka tsalle sama a lokacin da ya kawo mata wani mummuna suka da adda tagoce a saman ta gabza masa wasa naushi a fuska da dukkan karfinta.Take hakorinsa guda daya daga cikin bakinsa yayi fitar burgo gami da feshin jini saboda karfin naushin sai gashi ya ya fadi kasa dukda girman nasa.A lokacin dayaji jiri ya kwashe shi,kafin ya mike tsaye tuni Malika ta dako tsalle sama ta dira akan kirjinsa kuma ta soka masa takobi guda a cikin bakinsa.Aikuwa sai takobin ta bullo ta keyarsa ta cake cikin kasa jini na bulbulowa.Koda sauran dakarun sumamen suka ga abinda ya faru ga shugabansu sai suka firgice suka tarwatse izuwa cikin jejin da gudu domin su tsira da rayukansu.Ita kuwa Malika sai ta bingire kasa daga kan gawar shugaban dakarun ta kama haki har tana furzar da gudan jini daga cikin bakin nata saboda tasabar lugudan naushin da tasha,saida ta huta sosai sannan ta iya mikewa tsaye taje tayi nuni da hannunta izuwa ga wannan yana data lullube kofar kogon dutsen.Take yanar ta bace bat Malika ta kunna kai cikin kogon dutsen tana tafe tana layi da tangadi kamar zata fadi kasa ga jini na yoyo a hancinta.Koda su sarki Hilairu hangota taho garesu a cikin wannan hali sai suka firgice,Sarki Hilairu bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur ya rugu gareta,kafin ya isa wajenta ta langabe zata fadi kasa,amma sai yayi sauri ya cafota ta sume akan kirjinsa.Nan da ya dauketa a dimauce yazi ya kwantar da ita suka shiga kokarin ceto rayuwarta saboda tuni a wannan lokacin numfashinta ya dauke kuma ba komai ne ya haddasa hakan ba face mugun naushin da wannan shugaban dakaru ya jera mata akan kirjinta ba,in badon ma ta kasanace BASADAUKIYA ba da tuniya ya karya kasusuwan kirjinta,duk da haka jini ne ya kume mata daga cikin kirjin nata shi yasa tashiga wannan mugun hali.Sa'ae da akayi daga cikin matan dake wajen akwai likita.Koda likitar tayi nazarin jikin Malika ta gane cewa tasha naushi da bugu a kirjinta sai nan take tasa akaje aka tsinko mata wadansu ganyaye a cikin daji da yan dabaru aka hada murhu aka dora tukunya aka dafa ganyayen sannan bayan ruwan maganin ya dan huce sai aka durawa Malika a baki.Faruwar hakan ke da wuya sai ta farfado ta kama aman bakin gudan jini,saida ta amayar da jini mai yawa sannan ta dawo cikin haiyacinta,a sannane ta iya bude idanunta tayi arba da sarki Hilairu a zaune daf da ita idanunsa na kallonta suna zubar da hawaye saboda tausayin Halin da yaga ta shiga,suma sauran jama'ar tasa duk sun zageta sunyi jugum jugum kamar ana zaman makoki.Malika ta dubi sarki Hilairu cikin matukar karfin hali tayi masa dan guntun murmushi kuma ta budi baki da nufin yi masa magana amma saita kasa.Koda ganin haka sai wannan likitar ta dubi zarhus tace,dole ne ka hanzarta mayar da gimbiya can gidan sarauta domin likitanta ya kara taimaka mata saboda ni anan banida magungunan da ya kamata acigaba da bata.Koda jin haka sai Zarhus ya mike tsaye da sauri yaje ya janyo keken shanunsa mai dauke da akwatuna guda Arba'in da daya yazo gaban gimbiya Malika ya dubi sarki Hilairu yace,kusa Gimbiya a daya daga cikin wadannan akwatunan.Batare da wata fargabar komai ba kuwa suka kinkimeta suka sanyata a ciki tamkar sun sanya gawa domin ko motsin kirki batayi.Nan take tsoho Zarhus ya zira hannunsa a cikin aljihu ya dauko yar karamar kwalbar nan mai dauke da maganin barci wacce kuyanga Lasmira ta bata tasha,ya bude kwalbar ya diga wa gimbiya digo hudu na maganin a cikin bakinta ta hadiye.Take barci ya dauketa,koda ganin haka sai ya dauko mushen kwarin nan ya kifa akanta sannan ya dubi su Sarki Hilairu yace,ku cigaba da zama a cikin wannan kogon dutse kada dayanku ya kuskura ya fita waje nan da kamar sa'a uku gimbiya zata turo dakarunta su dauke ku izuwa inda zasu tsira.Koda gama fadin haka sai tsoho Zarhus ya zaburi keken shanunsa da gudu ya fice daga cikin kogon dutsen ya nufi hanyar dazata mayar dashi cikin birnin Madinatul Zauwara.Su kuwa su Sarki Hilairu sai hankalinsu ya DUGUNZUMA ainun saboda suna ganin cewa koda yaushe Yarima Lahaman da dakarunsa zasu iya zuwa wajen su kawo mus hari su kashe su ko su kame su. MEYE A CIKIN LABARIN JARUMI SA MAZA GUDU? WANE IRIN MASIFA ZAIZO TA ITA? SHIN SARKI SHARKUF ZAIBAR GIMBIYA MALIKA TAYI WANNAN TAFIYAR? SHIN YARIMA LAHAMAN YANA SAKE KAWOWA SU SARKI HILAIRU HARI? INA LABARIN SAURAN DAKARUN SUMAMEN DASUKA GUDU? SHIN INA SUKA TAFI? Mu hadu a cikin littafi SA MAZA GUDU littafi na uku dan jin wadannan kayatacce lbr.. Naku Suleiman zidanekd. Whatsapp 09064179602 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk

Chapter 3 of 19