Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cika umarnin kaba.Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa tuni Lahaman ya zabga masa wawan naushi a ciki.Take wani gudan jini ya furzo waje daga bakinsa ya baje a kasa matacce ko shurawa baiyiba.A sannanne Yarima Lahaman ya takarkare ya kwarara wani uban ihu.Ihun nasa ya cika gidan da wajen gidan gaba daya.Kuma ya firgita duk wani abu mai rai dake kusa domin kuwa tsuntsaye ma tashi suka rinkayi suna sauya sheka babu shiri.Yana gama wannan ihu ne ya fashe da kukan bakin ciki yana mai cewa saboda mene na kasa cika buri na akan makiya na?Shin nayiwa abin bautarmu wani laifi ne?Idan har ubangijin namu yadaina jibantar lamari na nima daga yau nadaina bauta masa.Haka dai Yarima Lahaman ya kama sambatu da surutai irin wadanda basu da ma'ana da kan gado har yagaji likis ya fadi kasa ya kama barci.Sai dauke shi akai aka shigar dashi cikin wani dakin shakatawarsa aka kwantar dashi. SA MAZA GUDU Littafi na uku(3) Part B Kamar yadda Gimbiya Malika ta tsara haka al'amarin ya kasance wato Sadauki Aryan ya sami nasarar kaisu sarki Hilairu can gidan gonarta kuma sun isa,aka baiwa jama'ar sarki Hilairu masauki mai kyau,gami da abinci mai daraja.Dayake da yawansu suturunsu sun yayyage kuma sunyi bakin kirin kamar almajirai,sai aka kaisu kewaye sukayii wanka,sannan aka kawo musu sababbun suturu masu kyau aka basu,suka sanya sai gashi sun tsinci kansu a cikin farin ciki mara misaltuwa,sukaji tamkar a cikin tsohon birninsu suke,bambancin kawai shine basa tare da sauran 'yan'uwansu,wasunsu kuma sun rasa iyayensu,wasu yan'uwa wasu mataye,yayye da kanne,hakanne ya tuno musu da rashin da sukayi suka kama kuka.Shi kuwa sarki Hilairu da aka kai shi dakin da Gimbiya Malika ke hutawa yaga irin daular da aka shirya a cikinsa kuma har da kuyangi guda hudu kyawawa masu yi masa hidima,sai ya fashe da kukan bakin ciki saboda tunowa da yayi da daularsa da aka rushe da kuma matarsa marigayiya.Bayan yayi wanka an kawo masa abinci na alfarma ya kimtsa cikinsa sai yaje ya kwanta yana kallon wani kyakkyawan tsuntsu dake cikin keji a rataye.Nan take zuciyar Sarki Hilairu ta tafi izuwa duniyar soyayya ya runtse idanuwansa.Take ya tsinci kansa acikin wani kayataccen lambu cike da furannin kyawawa gami da kayan marmari iri iri,ya tsinki inibi kenan zai kai bakinsa sai ya hango Gimbiya Malika ta nufo gareshi a cikin ado na kasaita,fuskarta cike da annuri tana tayi masa murmushi,wani haske ya baibaye jikinta gaba daya.Koda ya hangota saishi ma ya nufeta yanamai bude hannayensa,itama sai ta bude hannayenta suna shirin su rungume juna kenan sai yaji ana kwankwasa masa kofar daki.Sarki Hilairu yayi firgigit kamar wanda ya farka daga bacci ya dubi bakin kofar shigowa a fusace saboda bai so aka yanke masa wannan tunani ba mai kama da mafarki,kawai sai yaga ashe sadauki Aryan ne ya shigo.Cikin hanzari Sarki Hilairu ya sake fuskarsa ya sauko daga kan gadon ya taho wajen Aryan.Shi kuwa Aryan sai ya sake dukawa a gabansa a karo na biyu yace,ya shugabana mun gama cika umarnin Gimbiya don haka yanzu a cikin wannan dare zamu koma gareta domin mu sanar da ita halin da ake ciki.Koda jin wannan batu sai Sarki Hilairu ya sunkuya ya kama kafadun Sadauki Aryan ya tashe shi tsaye sannan ya dubeshi cikin murmushi yace,idan ka isa wajen Gimbiya ka gaya mata cewa ina godiya a gareta mara adadi,domin kuwa bani da abinda zan iya saka mata dashi ba face fatan alheri ga rayuwarta da kuma fatan Allah yasa ta zamo mai gadon mahaifinta.Ya kai wannan jarumi ma'abocin adalci yanzu haka idan ka tafi ka barmu a wannan kauyen cikin wannan gidan gonar baka zaton cewa mutanen Yarima Lahaman zasu iya sake kawo mana wani harin ba?Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Aryan yayi murmushi yace,ya kai wannan sarki ma'abocin kyawu da kwarjini ka kwantar da hankalinka,ka sani cewa kazo tudun tsira domin kuwa wannan kauye yana karkashin tsaron amintattun dakarun sarki guda dubu dari biyar.Komai yawan runduna ta mayaka kafin su shigo garin nan su cishi da yaki tuni labari ya iske mu a can babban birni mun kawo muku dauki.Kuma ko Yarima Lahaman yazo nan da kansa baza a barshi ya shigo ba saboda fiye da shekaru goma baya sarki ya haramta masa zuwa wannan kauye bisa sharadi mai tsauri.Koda sadauki Aryan yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki Hilairu ya kwanta.Nan take dai ya sake yi masa godiya sukayi sallama.Ba tare da bata wani lokaci ba sadauki Aryan ya kwashi dakarunsa suka fice daga cikin gidan gonar suka tasamma birnin Madinatul Zauwara. Gimbiya Malika ta farka daga barci sakamakon tsamin jikinta datake fama dashi na gumurzun yakin da tayi da dakarun sumame a jiya da daddare.Koda ta bude idanunta taga yadda rana ta kwalle sai ta kurma ihu saboda sanin cewa tayi laifin makara izuwa fada.Cikin hanzari ta kwalawa kuyanginta kira suka shigo cikin turakar da gudu suka dauketa suka shigar da ita cikin kewaye suka tsala mata wanka.Kafin a gama wankan kuyanga Lasmira ta kawo mata abincin kalacinta ta ajiye akan tebur kusa da gadonta na barci.A tsaitsaye Malika ta yiwa abincin loma uku sannan ta fice da gudu ta nufi fada.Kuyanginta sama dasu arba'in suna take mata baya.Suna ruke da doguwar rigar dake jikinta wacce ke fama sharar kasa,mai siffar bindin dawisu.Wasu daga cikin kuyangin kuwa wucewa sukayi gaban Gimbiya suna watsa wani irin fure mai kamshi kuma mai launin shudi kalar rigar jikinta tana takesu da kafafunta.A haka suka iso cikon fadar,da shigar Gimbiya Malika sai sarki Sharkuf ya mike tsaye cikin murna ya taryeta cikin murna,fuskarsa cike da annuri ya taryeta.A wannan lokaci Yarima Lahaman na zaune a can gefe daya cikin yan majalisa ya murtuke fuskarsa tamkar wanda aka aiko wa da sakon mutuwa.Koda sarki Sharkif ya rungume Gimbiya Malika sai ta hada ido da Yarima Lahaman,maimakon ita ma ta daure fuska sai tayi masa murmushin mugunta mai nuna alamun ta sami nasara akansa.Al'amarin daya kara fusata Yarima Lahaman kenan bai san sa'adda ya matse hannun kujerar da yake zaune a kaiba,abinka da al'amarin Sadauki take hannun kujerar ya ruburbushe duk da cewa anyi tane da katako mai kwari.Karar karyewar kujerarce ta janyo hankalin yan majalisar dake zaune kusa dashi,suka kama kallonsa suna kallon kujerar.Kuwa sai ya kama yake yana nunawa kamar tsautsayine ya janyo karyewar kujerar.Nan take fadar ya rude da shewa bisa ganin shigowar Gimbiya Malika maroka suka kama yi mata kirari a lokacin da sarki Sharkuf ya kama hannunta ya jata izuwa can inda karagar mulkinsa take domin su zauna tare a waje daya,yayin daya rage saura baifi taku biyar ba su isa kan karagar sai Malika ta janye hannunta daga cikin na sarki ta dubeshi tace,Ina mai neman alfarma ka barni naje na zauna a kusa da yan uwana yayanka a yau rana daya jal.Koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya turnuke sarki Sharkuf domin bai taba jin Malika ta ambaci kalmar yan uwanta ba,sai a yau,hatta ragowar yayyanta maza su bakwai babu ruwanta da su kamar yadda suma babu ruwansu da ita.Asalima dukkaninsu sun tsaneta kamar yadda suka tsani mutuwarsu,saboda ganin yadda uban nasu ya fifita ta akansu kuma yake nuna mata tsananin SO DA KAUNA.Cikin fara'a Sarki Sharkuf ya dubi Gimbiya Malika yace,nayi miki alfarma jeki ki zauna a cikin yan uwanki kamar yadda kika bukata.Koda jin haka sai Malika ta nufi inda su Yarima Lahaman ke zaune fuskarta cike da murmushi.Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan cikin fadar domin bata taba zuwa cikin yan uwanta ta zauna ba.Kai tsaye Malika taje ta zauna akan kujerar dake daf data Yarima Lahaman suka hada idanu a karo ba biyu sai ta sake yi masa murmushi,sannan ta dubi ragowar yan uwanta maza su bakwai dake zaune a gefensu suma tayi musu murmushi a karo na farko a rayuwar zamantakewarta dasu.Take su duka hankalinsu ya DUGUNZUMA,kuma tsoro ya shigesu,suka fara tunanin ko wata mugunta Gimbiya Malika take shirin yi musu shi yasa ta kusancesu a wannan rana.Ba tare da bata lokaci ba aka fara zartar da harkokin fada kamar yadda aka saba.Fadawa daManyan yan majalisa suka fara fitowa gaban sarki suna kwasar gaisuwa dogarai na amsa musu.Ana cikin wannan hali ne Malika ta dubi Lahaman ta budi baki cikin karamar murya kamar mai rada tace dashi,na sayi bayi a wajenka kuma na biyaka kudinka,saboda me ka aiko a kashe su?Ka sani cewa ka tsokano tsuliyar dodon daya shekara a kwance yana barci,kuma ka haifar da yakin da bashi da karshe face dayanmu yakai dan uwansa kushewa.Jibi zan bar kasan nan domin gabatar da tafiyar dana sabayi a duk karshen shekara,idan ka isa ka debo dukkan dakarunka da kake takama dasu ka tareni a daji muyi yakin karshe domin mu warware kiyayyar dake tsakaninmu ta tsawon shekaru.Idan kuma baza ka iyaba to ka bazama a cikin duniya domin kayi sabon shiri na nemo makaman yakata,ka sani har abada tsakanina da makiya babu gudu babu ja da baya,yau zan gaya maka sirrin da ban taba gaya maka ba,ka waccan karagar Mulkin da mahaifinmu ke zaune a kanta,ko gawarka bazata hau kai ba ballan tana kai,nice zan hau kan waccan karagar kuma kanaji kana gani da ranka da lafiyarka.Tun kafin Gimbiya Malika ta gama wannan jawabi nata fuskar Yarima Lahaman ta kama gatsinewa saboda tsananin fushi fa kiyayya kai har saida ma ya dunkule hannayensa biyu da nufin ya gabza mata naushi amma daya tuna cewa a cikin zuciyarsa kar yayi haka,sai ya cigaba da kallonta kawai har ta gama suruntunta ta mike tsaye tabar wajen ta tafi izuwa wajen sarki tayi masa rada a kunne sannan ta fice daga cikin fadar gaba daya. Da kwanaki biyu suka cika ranar tafiyar Malika tazo lokacin da tazo yin bankwana da iyayanta Sarki Sharkuf da Sulaira sai suka rungumeta suka fashe da kuka. SA MAZA GUDU Littafi na uku(3) Part C Al'amarin daya karya zuciyar Malika kenan ta janye jikinta daga cikin nasu ta dubesu a alokacin da hawaye ke kwarara bisa kumatunta tace,saboda me kuke yin kukan rabuwa dani,alhalin ba wannan ne karo na farko dana fara yin wannan tafiya ba,ban taba ganin kunyi kuka ba idan nazo yi muk sallama sai a wannan karon,shin ko zaku iya gaya mini dalili?Koda jin wannan tambaya sai mahaifiyar Malika ta sunkui da kanta kas,ta kasa cewa komai.Shi Kuwa sarki Sharkuf sai ya kama kafadun Malika ya ruke a lokacin da hawaye ya subuto masa ya dubeta yace,yake yata ki sani cewa bokana wanda na aminta dashi ainun wanda duk abinda ya fada mini sai ya faru a gaske,shine ya sanar dani cewa wannan rabuwa da zamuyi dake a yanzu itace ta karshe a gareni,ma'ana ba zaki dawo ki riskeni a rayeba.Koda jin wannan batu sai Malika ta firgita ainun idanunta suka zazzaro kuma hawaye ya sake zubo mata sannan ta sake rungume sarki Sharkuf ta kankameshi a jikinta tana mai fashewa da matsanancin kuka.Itama mahaifiyartata saita rungumesu sannan Malika ta janye jikinta daga nasu ta sake fuskantar sarki tace,ai kuwa in har bazan dawo na riske ka raye ba banga amfanin yin wannan tafiya tawaba,tunda kafin na dawo Yarima Lahaman ya hau kan karagar ka,ka sanicewa idan har ya hau kan wannan karaga talaka sun shiga uku,kuma mulkin zalunci da murdiya za'a ciga da gudanarwa a cikin wannan kasa tamu mai albarka,duk kokarin dakayi na ganin an sami zaman lafiya da yalwar arziki a kasar nan tsawon shekaru ya zama na banza kenan.Koda gimbiya Malika tazo nan a zancenta sai Sarki Sharkuf ya tari numfashinta yace,kwantar da hankalinki yake yata,kiyi sani cewa kamar yadda zaki bar gari yanzu bayan kwana biyu da tafiyarki shima Yarima Lahaman zaiyi shiri ya tafi neman karin Horon yaki gami da ilmin tsafi.Kuma ba zai dawo ba sai bayan cikar watanni shida,kinga ke nan saima kin riga shi dawowa da tazarar wata uku.Bokana bai sanar dani anihin sauran kwanakina a duniya ba,zan iya kaiwa wannan lokaci na dawowarki wata kila kuma bazan kaiba.A cikin binciken da bokana yayi zaki sami gagarumar daukaka a cikin wannan tafi taki,kuma zaki hadu da wani mutum mai darajar gaske wanda shine sanadin daukakar taki,amma kada ki kuskura kice zaki yaki wannan mutum saboda zaku banbanta a addini da ra'ayi.Ki bishi a hankali kuma ki lallaba shi ki sami karin Ilmin yaki a wajensa,zaki kiyi yake yake tare dashi kuma zaki shaku dashi ainun,amma kada ki kuskura ki kamu da sonsa ko kuma ki karbi addininsa.Sai kinyi hakanne kadai zaki iya dawowa gida ki iya fuskantar dan'uwanki Yarima Lahaman domin a sannan shima ya zamo gagarumin sadauki kuma gawurtaccen matsafi abin tsoro a duniya.A sannan ne zakuyi gasar hawa karagata ta mulki a samin wanda zai gadona a cikinku.Lallai saikin kiyaye wadannan dokoki dana zaiyana miki a yanzu sannan zaki iya samun nasara akan dan'uwanki.Koda sarki Sharkuf yazo nan a zancensa sai Gimbiya Malika ta sake rungumeshi ta fashe da kuka.A cikin zuciyarta kuma tana tunanin tayi masa maganar Dan'uwan sarki Hilairu wato SA MAZA GUDU,tana jin tsoro don kada ya tambayeta a inda ta san wannan sunan har ta jawo ya gano abinda take na sirri.Nan dai ta juya ta nufi dokinta da nufin ta hau su nausa sai taji muryar Mahaifinta yana mai cewa,yake 'yata kiyi sani cewa a wannan fita da zaki yi lallai kiyi kokarin kiyaye irin mayakan dazakiyi yaki dasu.Domin a cikin wannan tafiya taku zaki iya haduwa da GUGUWAR ANNOBA wacce batada magani,Ruwa mai tafiya da duk abinda yasha masa gaba,lallai ki kula sosai domin SA MAZA GUDU yana bisa cikin wannan nahiya mai albarka.Koda jin haka sai ta waigo ta dubi mahaifinta a nutse tace,ya Abbana shin waye wannan wanda ban taba jin sunansa ba,alhalin naga a cikin batunka kana kuranta jarumtakarsa.Koda Sarki Sharkuf yaji wannan tambaya sai yace,Labarin Sa Maza gudu yana da tsayi,saidai kawai na sanar dake cewa babbar masifa ce shi a cikin duniya MURUCIN KAN DUTSE ne shi bai fito ba saida ya shirya.Asalinsa an haife shi a cikin wannan nahiyar saidai bai rayu a wannan nahiya ba,yake 'yata kiyi sani cewa shi wannan jarumi bai kasance azzalumi akan wanda bai masa laifi ba,amma ya kasance azzalumu akan duk wanda ya taboshi,baya ragawa kowa face kaifin takobi ta shiga tsakaninsu.Don haka ina mai miki gargadi akan ki kiyaye shiga sabgar duk wanda bai shiga harkarkiba,kada kiyi yaki da kowa sai in har shi ya neme ki da yaki.Wannan kadai idan ki kiyaye zaki fita daga ukubar SA MAZA GUDU,da wannan nake miki bankwana. Nan Gimbiya Malika ta juya cike da tunani a cikin ranta ta haye dokinta Sadauki Aryan ya jera tare da ita,Dakaru dubu uku da kuyangi arba'in suka rufa musu baya,suka fice daga cikin gidan sarautar.Tun Sarki da Mahaifiyar Malika na hangosu har suka bace musu da gani.Nan take sarki ya kama hannun matarsa suka juya suka koma cikin gidan sarautar rungume da juna suna zubar da zazzafan hawaye na bakin cikin rabuwa da gimbiya Malika.Da fitowar su Gimbiya Malika daga cikin Birnin Madinatul Zauwara sai ta dubi Sadauki Aryan tace,gidan gonata zamu fara zuwa domin na gana da su sarki Hilairu sannan nasan abinda ya kamata nayi dasu.Koda jin haka sai Aryan ya baiwa sauran dakarun umarni,kowa ya kada linzamin dokinsa aka nufi hanyar da zata je wannan kauye inda gidan gonar gimbiya Malika take.Tafiyar 'yan Sa'o'i kadan sukayi suka iso kauyen,tun daga nesa masu gadin kofar garin suka hango tutar mulki ta birnin Madinatul Zauwa suka busa algaita alamar cewa gimbiya Malika ta iso.Nan da na jama'ar kauyen suka rinka tururuwa suna fitowa taryar gimbiya Malika cikin mutukar farin ciki saboda kaunar dasu ke yi mata.Dakarun kauyen kuwa sukayi sahu biyu suna mika gaisuwa,maroka da mawaka suka kama yiwa gimbiya Malika jinjina da kirari,kai hatta kananan yara da tsofaffi,matasa samari da 'yan mata fitowa suke daga cikin gidajensu a guje suna zuwa bakin hanya suna mika gaisuwarsu.Bawai a wannan kauye bane kadai ake yiwa gimbiya Malika irin wannan tarba ba,duk garin da taje a cikin kasar haka ake bikin murnar zuwanta,kuma ayita kawo mata kyaututtuka iri iri.Ita kuwa Gimbiya Malika duk garin da taje sai ta bincika taji matsalar data damesu tayi musu maganinta,idan ta fara yiwa mutane kyautar kudi kuwa har sai anga a bin ya wuce na hankali sannan kuyangi suke janyeta daga wajen.Ko kadan Gimbiya Malika bata kyamar Talakawa kuma bata gudunsu.Har ziyarar gidaje takeyi cikin dare a sirrance tana ganin matsalolinsu tana magance musu.Kananan yara kuwa da matsa kamar sa hadiyeta saboda kaunar dasukeyi mata.Wannan dalili ne yasa a cikin gaba dayan 'ya'yan sarki Sharkuf a kasar Madinatul Zauwara Gimbiya Malika tafi farin jini kuma kowa ita yake so tagaji sarki saboda tana da irin adalcinsa da jin kansa.Saida Gimbiya Malika ta batwa wajen Sa'a uku a cikin garin tana karbar gaisuwar jama'a da kyaututtuka kansu sami damar isa gonarta.Da yake dama ansan da zuwanta tuni gaba dayan ma'aikatan gidan gonar da dakaru masu tsaro da kuma su sarki Hilairu da jama'arsa sun fito sun jera layi a cikin harabar gidan gonar domin yi mata barka da zuwa.Koda Gimbiya Malika ta shigo cikin harabar gidan gonar jama'a suka fara miko gaisuwa da jinjina sai ta hango sarki Hilairu tare da jama'arsa sun zube kasa suna gaisheta,cikin hanzali Malika ta tsaida dokinta ta sauko kasa sannan taje wajen Hilairu ta kama kafadunsa a karon farko kenan da ta taba jikin wani 'da namiji inba mahaifinta ba da kuma "dan uwanta Azzalumi Yarima Lahaman wanda shima a lokacin dasuke gumurzun yaki ta tabashi.Bayan Malika ta tayar da Hilairu tsaye sai ta dubeshi ciki alamun damuwa tace,Haba yakai wannan sarki mai daraja,shin ka manta ne cewa kai ma sarki ne?Koda jin wannan tambaya sai Hilairu yayi murmushi cikin yake yace,tabbas a da ni sarki ne,amma a yanzu na kasance bawa na yar sarki tunda siyo ni akayi daga hannun wani.Koda jin wanna batu sai tausayin Hilairu ya kama kowa a wajen musamman ita kanta GimbiyaMalikan,kawai sai ta sake dubansa ta girgiza kai tace,ai ni ban fanso ka ba domin ka zama bawana ba,sai domin na 'yantaka tare da dukkan jama'rka,yanzu mu karasa cikin dakin shakatawa ta saboda ina da magana mai muhimmanci dakai.Koda jin wannan batu sai Farin ciki ya lullube gaba dayan mutane sarki Hilairu bisa jin cewa an 'yanta su,nan fa suka kama tsalle da murna suna yiwa gimbiya Malika Godiya.Bayan Malika ta zauna ta huta tareda da Sadauki Aryan a cikin dakinta na hutun.An kawo musu abinci da abin sha na alfarma sun ci sun gyatse,sai ta tura aka kirawo Hilairu.Da shigowarsa cikin dakin sai Malika ta dubi Aryan tayi masa inkiya ya tashi ya basu wuri.Nan take Aryan ya mike ya fice daga cikin dakin zuciyarsa cike da kishi domin a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da yaga wani 'da namiji ya kusanci Gimbiya Malika.Fitar Aryan ke da wuya sai Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murna tayi masa izinin ya zauna akan kujerar da take fuskantar tata sannan ta dubeshi tace,yakai wanna sarki,kayi sani cewa tun daga ranar danaji labarinka bisa mugun abinda dan'uwana Yarima Lahaman yayi maka a birninka naji na kamu da tsananin tausayinka,babu wani abu dazaisa zuciyarka tayi sanyi face na mayar da kai da jama'arka izuwa kasarku ka koma kan kragarka ta mulki.Kuma na taimaka maka da kudi a sake gina birnin a kawata shi ainun tunda an kone gidajenku,kayi sani cewa na dauki alkawarin yin hakan acikin zuciyata tuntuni,amma a halin yanzu bani da ikon cika wannan alkawari saboda ina kan hanyata ne ta zuwa manyan kasashen duniya guda uku domin gabar da harkokina na kasuwanci kamar yadda na saba a duk karshen shekara.Shin zaku bini ne izuwa wannan tafiya kuyi min rakiya idan na gama sabgata na dawo gida sai mu sake shiri mu tafi?Lokacin da Gimbiya Malika tazo nan a zancenta sai Sarki Hilairu yayi ajiyar numfashi yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiki daga can sai ya dago kai ya dubeta yace,yake wannan yar sarki kiyi sani cewa zamana a nan ko a can birnina acikin daula da kwanciyar hankali bazasu taba dawo min da abinda na rasa ba,na sani cewa kina da labarin matata wacce dan'uwanki yayi mata fyade kuma ya kasheta a gaban idanuna wacce take tsananin kama dake tamkar an tsaga kara.To kiyi sani cewa dawowar wannan masoyita tawa shine kadai zai yaye mini damuwata da bakin cikin zuciyata.Koda sarki Hilairu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa ya fashe da kuka,nan take Malika taji da kamu da tsananin tausayinsa fiye da koyaushe har ta budi baki zatace dashi a shirye take ta maye masa gurbin matarsa sai ta kasa,Ta sunkui da kanta kasa tayi sauri ta goge hawayenta don kada ya gani.Saida taga ya nutsuwa ya daina kuka sannan ta dubeshi tace,yanzu mene zabinka? zaka bini ne ko zaka zauna anan din?Koda jin wannan tambaya sai Sarki Hilairu ya dago kai ya dubi Malika yace,na zabi na biki tare da jama'ta.Dajin Haka sai farin ciki ya lullubeta,Gimbiya Malika nan take ta sallame shi ya tafi izuwa can wajen mutanensa.Ita kuma sai ta shiga can cikin kuryar dakin ta kwanta akan gado domin tayi barci amma sai barcin ya gagara sakamakon tunanin al'amura biyu da suka fado mata.Al'amari na farko shine tunowa da abubuwan da mahaifinta Sarki Sharkuf ya gaya mata dangane da bakon jarumin daya bata labarin cewa zata hadu dashi a wannan fitowa da tayi.Take ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace,wai shin yaya kamanin wannan jarumi zai kasance bare da zarar ta hadu dashi ta gane shi,kuma aina ma zata hadu dashi? To yaya zan ribaci wannan jarumi har na karo horon yaki daga wajensa,alhalin mun banbanta a addini da ra'ayi?Koda Malika tazo na a tunaninta sai ta kasa baiwa kanta amsa,a sannan ne kuma tunanin dan uwanta Yarima Lahaman dana SA MAZA GUDU suka fado mata a rai.Ta shiga Tunanin yadda za'ayi Lahaman ya zama gawurtaceen jarumi kuma matsafi a cikin watannin shida kacal.Nan hankalin Malika ya DUGUNZUMA ta gane cewa lallai aikin dake gabanta ba karami bane,kuma Allah ne kadai yasan irin gwagwarmayar da zata sha da bakar wahalar daza ta fuskanta kafin ta sami nasarar zama sarauniyar birnin Madinatul Zauwara.Haka dai Malika taci gaba da wannan tunani tana so ta huta sosai domin idan sun ci gaba da tafiyar Sarki Hilairu ya bata Labarin Jarumtakar SA MAZA GUDU,da haka har barci ya saceta bata saniba.A wannan rana Sadauki Aryan ne yayi gadin Gimbiya Malika kuma bai bari sarki Hilairu ya sake shiga wajenta ba har gari ya waye.Tun da duku dukun safiya Gimbiya Malika tare da jama'arta da jama'ar sarki Hilairu sukayi shirin aka kawo mata dokinta aka dunguma gaba daya aka fice daga cikin yankin kasar Madinatul Zauwara.Koda aka iso wani wuri inda hanya ta rabu gida uku,sai aka tsaitsaya.Kawai sai Sadauki Aryan ya dubi Gimbiya Malika yace,ya shugabata yanzu wace kasa zamu fara zuwa Tsakanin Misra,Yemen da kuma Kisra.Koda jin wanna tambya sai Malika tayi shiru tana tunani kamar bazatace komai ba,daga can kuma sai ta dubi Sadauki Aryan tace,mu tunkari birnin Misra domin shine birnin da muka dade rabonmu dashi.Koda jin haka sai Aryan ya kada dokinsa ya nufi gabas take Malika da sauran jama'ar gaba daya suka rufa masa baya.Haka dai su Gimbiya Malika sukayi ta tafiya suna ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon kwanaki goma sha shida sannan suka iso birnin Misra. Part D Haka dai su Malika sukayi ta tafiya suna masu ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka har tsawon kwana goma sha shida sannan suka iso Birnin Misra.A cikin wannan tafiya sun sha haduwa da 'yan fashi mugayen aljanu da mugayen dabbobin daji amma dukansu farat daya suke yi musu,sannan gimbiya Malika ta rike wasiyar mahaifinta bata taba kulasu wasu yan fashi ba sai sai in sun kula su,suna kula su kuwa saidai su gama dasu su bar gawarwakin a yashe a wajen su kara gaba.Da shigowar su Gimbiya Malika cikin birnin Misra sai suka iske garin ya cika makil fiye da koyaushe a duk lokutan da suke zuwa a baya.Fatake,bokaye da yan kasuwa iri iri da kuma masu fataucin bayi sun cika garin.Al'amarin daya baiwa su Gimbiya Malika Mamaki kenan har suka kasa hakuri.nan take sadauki Aryan yaga wani almajiri a zaune a gefen hanya rike da dan 'ko'kon yana bara.Shidai wannan almajiri ya kasance saurayi mai kirar sadaukai,amma kuma kafarsa guda ta hagu da hannunsa na hagu duk a shanye suke ko sarrafasu baya iyawa.Aryan ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare guda daya a lokacin daya tsaida dokinsa daf da almajirin ya jefo masa wannan dinare a cikin kokon sannan ya dubeshi yace,ba sadaka na baka ba,labari nake nema,mene dalilin wannan cikowa mai yawa a cikin wannan birni?Koda jin wannan tambya sai almajirin yayi murmushi yace,da wannan dan kudin kake son kaji babban labari ai sunyi kadan.Koda jin haka sai Aryan yayi murmushi ya sake zura hannu cikin aljihunsa ya dauko dinare guda ya jefa cikin kokon yace,yanzu fah?Almajirin yace da saura domin kuwa labarin da zan baka zai amfaneku a matsayinku na manyan jarumai daga babbar kasa.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sadauki Aryan yace,A cikin ransa anya kuwa wannan almajiri ba boka bane,yaya akayi yasan cewa mu jarumai ne daga babbar kasa,kuma menene zai amfane mu akan labarin da zai bamu.Koda gama wannan zancen zucin sai Aryan ya sake fidda dinare uku ya sauko daga kan dokinsa yazo ya tsuguna a gaban almajirin ya zuba masa dinaren a cikin kokonsa ya zama guda biyar sannan ya dafa kafadarsa yace,Abokina bani labari me yake faruwa a cikin wannan gari?Almajirin ya sanya hannunsa mai kyan cikin kokon ya kwashi dinaren ya zuba su a cikin aljihunsa na wando sannan ya dubi Aryan cikin nutsuwa yace,Ai sarkin garin nan ne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya don haka jarumai da yawan gaske sunzo daga manynan kasashe,sarakuna sun zo,kuma attajirai yan caca sun taru domin baje kolunsu a goben da safe a gidan sarauta.Duk wanda ya lashe wannan gasa za'a bashi zabin abubuwa guda uku ya dauki daya ko dai ya auri yar sarki kokuma a bashi dinare da rakuma dubu ko a bashi mulkin babbar jaha daga cikin jahohin kasar nan.Koda jin wannan batu sai Sadauki Aryan ya kamu da farin ciki nan take ya aiyana a ransa cewa lallai zai shiga wannan gasa,amma ba don kawai a bashi wannan dukiya ta dinare ba.Rakuma gudu dubu saboda in ya koma gida yayi amfani da ita wajen cika wani babban buri nasa wanda ya gagare shi cikawa tsawan shekaru.Kawai sai Aryan ya dubi wannan Almajiri yace Abokina meye sunanka? Almajirin yace Sunana Hibairu bin Usman.Koda jin haka sai Aryan ya mikawa almajiri Hibairu hannunsa na dama shima ya bashi nasa hannun suka gaisa.Aryan yace,ina fatan zamu hadu gobe a fada muyi kallon wanna gasa tare.Hibairu yayi murmushi yace,tabbas zamu hadu,koda gama fadin haka sai Aryan ya mike da sauri yaje ya hau dokinsa ya zabure shi da sauri domin ya riski su Gimbiya Malika saboda sun bashi tazara mai dan yawa.Da isar Aryan wajen gimbiya Malika sai ta dubeshi cikin murmushi tace,me ka tsaya yi a wajen wancan almajirin?Aryan ya maidawa Malika martanin murmushin cikin biyayya yace,na tambaye shi dalilin wannan cikowa mai yawa a garin nan shine ya labarta mini cewa Sarkin garinne ya shirya gasar jarumtaka ta duniya.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Malika ta dubi Aryan tace,da zarar mun sauka a masaukinmu kaje ka nemi sarkin kasuwa ka gaya masa cewa nima ina son na shiga wannan gasa don haka yaje ya biya mini kudin shiga gasar tun kafin na yazo gareshi muyi lissafin kudaden.Koda jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka kama sadauki Aryan ya dubi Malika cikin alamun tsananin dimuwa yace,Haba ya shugabata ai girmanki da darajarki tafi gaban shiga wannan gasa,saidai ki barmu mu wakilceki kada ki manta cewa gaba dayan manyan sarakuna kina hulda dasu kuma babu wanda ya san cewa kina da wannan jarumtaka bai kamata ki tonawa kanki sirri ba.Koda jin wannan batu sai gimbiya Malika tayi murmushi tace,idan kida ya sauya dole ne rawa ta sauya.Ya kai Aryan ka sani cewa ni yanzu tun dana baro gida neman yadda zan kare kasata daga shirin abokan gaba na daina daukar kaina a matsayin yar sarki,wannan gasa da zan

Chapter 8 of 19