Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kofar gida da zata iya shanye tsawonsa kuma duk inda zai kwanta yayi barci sai yafi kamu sabain a tsawo da fadi,to wai shin ma wane irin adadin abinci da abin sha ne zai ishe shi a kullum?Allah da iko yake kuma shike yin halittarsa yadda yaso abinda Hibairu ya fadi kenan a cikin ransa,kawai bawai Hibairu daya kasance GWARZON SADAUKI ba,gaba dayan yan kallon saida suka firgita bisa ganin sadauki Ramzan saboda girmansa da kwarjininsa ya wuce a misalta sai abinda idanuwa suka gani.Mata da yara kuwa basa iya hada ido dashi tsawon dakika goma ba tare da sun kauda kai ba,saidai kaga suna rufe idanunsu saboda gudun haduwa da mugun mafarki.Masu bincike da hasashe na wannan lokaci sun tabbatar da cewa a duk fadin duniya babu wani narkeken kati mai Girma Da Nauyin Sadauki Ramzan.Lokacin da Sadauki Ramzan yazo daf da Jarumi Hibairu sukayi kallon kallo sai hantar cikin Gimbiya Zuhura ta kada,tsoro ya baibaye zuciyarta taji kamar tace da mahaifinta ya dakatar da wannan gasa,amma saboda kada kimarta ta zube a gane cewa yau ta kamu da son 'da namiji sai ta basar.Gimbiya Malika na tsaye a cikin jaruman gasa ta zuba ido ta ga yadda wanann GUMURZU zai kasnace tsakanin Hibairu daya sami galaba akanta da kuma Ramzan,sai akwai taga wanann bakon Jarumi ma'abocin kyau da kwarjini wanda yayiwa sadauki Aryan magan dazu yazo kusa da ita ya tsaya suna hada idanu sai yayi mata murmushi yace,yanzun nan zakiga yadda za'a gama da wanda ya kaiki kasa farat daya.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Malika ta dubi bakon jarumin cikin alamun tsananin mamaki tace,wanene kai kuma menene tabbacinka cewar sadauki Ramzan zai sami nasara akan Jarumi Hibairu?Koda jin wannan tambaya sai Jarumin yayi murmushi yace,sunana Jarumi Alkas dan'uwa ga Sarki Hilaur wanda kika ceto rayuwarsa data jama'arsa daga hannun dan uwanki Yarima Lahaman.Anayi mini lakabi da SA MAZA GUDU.Nayi bincike a cikin hallarar tsafina naga duk irin cin mutuncin da dan'uwanki yayiwa dan'uwana da yadda ya baje garinmu ya kone shi,nayi niyar naje na baje birninku na Madinatul Zauwara na yiawa YARIMA LAHAMAN KISAN GILLA amma saina fasa saboda na gano cewa dan'uwana ya kamu da tsananin sonki kuma bai kamata na cutar da wadda ta taimakeshi ba,bisa wannan dalili ne na biyoku izuwa wannan birnin domin na ramawa kura aniyarta.Ina nufin saka miki da abinda kika yiwa dan'uwana sannan na rabaku domin aure bazai taba yiyuwa ba a tsakaninku.Koda jin wannan batu sai hankalin Gimbiya Malika ya dugunzuma ainun take idanunta suka ciko da kwalla tace saboda me ka fadi haka?Sa Maza Gudu yace bazan iya gaya miki dalili a yanzu har sai na kashe babban makiyina a duniya.Cikin kaduwa Malika ta dubeshi tace,wannan babban makiyin naka?Sa Maza gudu yace gasi can zai fafata da Sadauki Ramzan,saboda shi na shiga wannan gasa,nima inada yakinin cewa Sadauki Ramzan zai iya kashe Hibairu amma idan har bai kashe shi ba to nine zan kashe shi,sau bakwai muna fafata kazamin yaki nidashi amma ragas mukeyi tamkar kowannenmu zai mutu,tsafi baya tasiri a kansa kuma karfin damtsensa da iya yakinsa kawai zata dore ni a kansa.Kada ki sanar da dan'uwana kin ganni anan sai bayan na kammala wannan gasa in ba haka ba kuwa duk farin cikinki da burinki na rayuwa da alkawarin da kika daukarwa dan'uwana zai rushe.Koda gama fadin hakan sai Jarumi Sa Maza Gudu ya bace bat da karfin sihirinsa na tsafiya daga kusa da Malika tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Gimbiya Malika kenan ta rasa abinda yake mata dadi a duniya.A can tsakiyar filin gasar kuwa da akayi kallon kallo tsakanin Jarumi Hibairu da Sadauki Ramzan na yan dakiku a lokacin da filin gasar ya rude da shewa gami da ihu da jinjina.Makada da mawaka kuwa kowannensu na wasa wanda yake so,kawai sai akaji an buga gangar fara gumurzu,take jaruman suka ja da baya a tare sukayi taku bakwai bakwai sannan suka tsaya suka daya takubbansu sama suka sake rike garkuwoyinsu sannan suka ruga da gudu izuwa kan juna suna suna ruri da kururuwa kai kace a tsakiyar miliyiyon mayaka zasu kafsa. Nima ganin sun tawo zasu afkawa juna suna ihu da kururuwa yasa na dannan okay ban sani ba na tsaya domin kallo. Maybe innaga comments da like anjima Da dare na cigaba.Amma banda tabbaci. SA MAZA GUDU Littafi na Hudu (4) Part B Kai kace a tsakiyar milyoyin mayaka zasu kafsa.Cikin bakin zafin nama Ramzan ya kawowa Hibairu sara a wuya da nufin ya cire masa kai,Hibairu ya sunkuya takobinsa ta sari iska a lokacin dashi ma ya kaiwa Ramzan sara a kafadarsa shima sai ya kare da garkuwarsa ya zamana cewa kowannensu yayi gaba ba tare da ya sami wata nasara ba.Nanfa yan kallo suka rude da shewa.A fusace jaruman biyu suka waigo ba tare da jiran komai ba suka sake rugowa da gudu izuwa kan junansu suna haduwa suka kacame da azababben yaki,bisa mamaki sai akaga Jarumi Hibairu na iya kare dukkan sara da sukan Ramzan.Kuma yana iya maida martani alhalin ansan cewa babu wani jarumi da yake iya tare harin Ramzan.Ai kuwa sai jama'a suka dada kaurewa da shewa,aka shiga yiwa Hibairu jinjina da tafi ana ambaton sunansa,al'amarin daya kara fusata sadauki Ramzan kenan ya kara fusata kuma ya dada zage damtse iya karfinsa yana kaiwa Hibairu munanen hare hare.Saida suka shafe sa'a daya da rabi sunayin wannan bakin gumurzu ba tare da dayansu ya samu nasarar koda lakutar jikin dan'uwansa ba,koda gimbiya Zuhura taga haka sai ta kamu da tsananin farinciki,hankalinta ya kwanta sosai saboda murna bata san sa'adda ta yiwa Hibairu jinjina ba har ta kira sunansa cikin jinjina.Koda sarkin Misra ya lura da halin da yarsa take ciki sai ya kamu da tsananin mamaki saboda wannan ne karo na farko dayaga an sami jarumin daya burgeta har tayi masa jinjina alhalin duk shekara akeyin wannan gasa kuma ta halacci gasar a kallah sai bakwai.Nan take sai yaji wani irin farin ciki ya shigeshi domin ga dukkan alamun ta sami mijin data zaba a matsayin abokin rayuwarta.Lokacin da jarumi Hibairu da sadauki Ramzan suka ga har takubbansu sun fara dakushewa saboda tsabar gogar juna amma babu wata nasara sai kowannensu ya fusata ya yarda takobinsa sannan suka yi cirko cirko suna kallon juna kamar zakaru suna haki saboda tsananin gajiya.Daga can kuma sai suka rugo da gudu izuwa kan juna da nufin su kacame da bugu da naushi amma sai Ramzan ya shammaci Hibairu ya danki kugunsa da hannayensa biyu ya matse shi.Hibairu ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin dayaji tamkar kasusuwan bayan nasa zasu karye,amma sai yayi wuf ya kama hannayen Ramzan da nasa hannayen biyu ya fara kokarin banbare su daga jikinsa.Wohoho!nan fa karfi ya fara halinsa domin saigashi kuwa yana neman ya cire hannayen Ramzan daga kugun nasa.Ramzan ya dage iya karfinsa wajen ganin Hibairu bai cire nasa hannayen ba,sai gashi kowannensu ya kasa idda nufinsa,ma'ana Ramzan ya kasa ci gaba da matse gadon bayan Hibairu,shima Hibairu ya kasa banbare hannayen Ramzan.A tarihin gumurzun Ramzan bai taba yiwa wani jarumi irin wannan kamu ba ya tsira da rayuwarsa domin na take yake rugurguza kasusuwan bayansa yayi jifa da gawarsa amma sai gashi ya kasa gamawa da Hibairu.Koda Hibairu ya fahimci cewar idan fa baiyi da gaske ba Ramzan zai sake samun damar matse masa Gadon baya,sai shima ya shammace shi ya buga masa tsakiyar kansa a kan fuskarsa,babu shiri Ramzan ya saki Hibairu ya fado kasa a lokacin dayaga taurain wuya akan fuskarsa,kuma hancinsa ya kama yoyon jini yaji wani irin zugi da radadi ya shigeshi.Koda Ramzan ya shafa hancinsa yaga jini sai ya fusata ainun ya dunkule hannayensa ya afkawa Hibairu suka kama naushi da bugun juna sai gashi kowannensu na shanye dukan abokin gwaminsa.Nanda nan suka hadawa juna jini da majina,tun suna tsaye sai da suka durkushe kasa suka jigata ainun suna layi ya zamana cewa da kyar ma suke iya kaiwa junansu bugu.A na cikin hakan Ramzan ya sake shammatar Hibairu ya tallafo wuyansa ya dagashi sama ya fyadashi a kasa,kafin Hibairu ya wattsake ya iya mikewa tsaye tuni Ramzan ya turmusheshi ya zauna dirshen akan ruwan cikinsa sai gashi Hibairu ya fara kakarin kumallo saboda tsananin nauyin Ramzan.Koda Ramzan yaga ya sami wanann nasara sai ya fara kyalkyalewa da dariyar mugunta da farinciki,su kuwa yan kallo masu kaunar jarumi Hibairu sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka saddakar da cewa shike nan an gama da Jarumi Hibairu,ma'ana tasa ta kare.Bazai iya ture Ramzan daga kansa ba saidai ya mutu a haka,tuni a wannan lokaci Gimbiya Zuhura ta fara zubar da hawaye saboda bakin cikin ganin halin da Hibairu ya shiga.Adaidai wannan lokaci ne hankalin Jarumi Hibairu yakai izuwa kan fuskar Gimbiya Zuhura,koda yaga ta kura masa idanu har tana zubar da hawaye saboda son sa da tausayinsa sai yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi,bai san sa'adda ya kwalla kabbara ba a cikin zuciyarsa,kawai sai gani akayi yasa hannayensa biyu ya tunkude Ramzan daga kansa,Ramzan ya fadi can gefe daya cikin dungure.Abinka da mai nauyi kafin Ramzan ya yunkura ya mike tsaye har ya juyo tuni Hibairu ya shiga tsakanin kafafunsa kawai sai gani akayi Hibairu ya suri Ramzan yai sama dashi tamkar kiyashi yayi dokon giwa,take Hibairu ya kwala Ramzan da kasa.Ramzan ya kurma uban ihu domin ji yayi tamkar anzare lakarsa gaba daya,take ya baje a kasa ya kasa mikewa ma zaune har izuwa tsawon dakiku koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewar jama'a aka kama yiwa Hibairu jinjina da tafi,shi kuwan Ramzan sai daukeshi akayi daga tsakaiyar fili saboda ya kasa mikewa tsaye.Jarumi Alkas wato SA MAZA GUDU dake cikin jaruman gasar saiya cika da tsananin mamaki saboda bai taba zaton cewa Hibairu zai sami nasara ba akan Sadauki Ramzan,Bayan an dauke Sadauki Ramzan da kamar tsawon dakika ashirin sai alkalin gasa ya sake fitowa tsakiyar fikin ya dubi jama'a yace,yanzu zamuyi wasa na karshe a wannan rana,a zagayen farko Jarumin dazai kara da gwarzonmu na yau shine Jarumi Alkas daga wata kasa dake kudancin wannan birnin namu na Misra.Koda Sa Maza Gudu yaji an ambaci sunansa saiyayi sauri ya dauko hular karfe ya sanya a kansa don kada a shaida shi dama ba kowane ya sanshi ba a fuska,an dai fi sanin sunansa domin ya shahara a ko ina cikin nahiyar.Batare da bata lokaci ba jarumi Sa Maza Gudu ya fito cikin tsakiyar filin,koda Jama'a suka ganshi shima yanada sura irin ta Jarumi Hibairu wato siffa irin ta Sadaukai kuma tsawonsu da kaurin jikinsu ya kusan zuwa iri daya sak sao aka rude da shewa.Hakika dan'uwa rabin jikine duka dacewa Alkas ya rufe fuskarsa da hular karfe saida Sarki Hilairu ya shaida shi wato ya gane cewa lallai wannan dan'uwansa ne Alkas wanda mutane keyiwa Lakabi Da Sa Maza Gudu.Nan take Hilairu ya kamu da tsananin farin ciki amma dayaga cewa zai fafata da wannan bakon Jarumi wato Jarumi Hibairu sai hankalinsa ya dugunzuma abu na farko daya fadowa Hilairu a rai shine me yasa Alkas bai nemeshi ba sun hadu tun kafin a fara wannan gasa,ko kuwa baisan cewa yana nan a cikin birnin Misra ba?Ai kuwa Alkas yana da karfin Sihirin tsafi donhaka dole ne yayi bincike ya gane inda yake kuma yaga duk irin cin zarafin da Yarima Lahaman yayi a birninsu.Sarki Hilairu na cikin wannan tunani ne yaji an buga gangar fara gumurzu.Nan take alkalin gasa ya jefawa Jarumi Hibairu wata sabuwar takobin ya cafe sakamakon cewa waccan takobin tasa ta dakushe.Kafin Hilairu ya gama gyara tsayuwarsa tuni Alkas ya durfafo shi amma takobinsa a kas,saida yazo daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan yace,yakai tsohon abokin gaba,ya gashi mun hadu a inda babu wani abu dazai raba mu face mutuwa,lallai a yau saidai ni ko kai wani ya kashe wani,domin mu kawo karshen wannan kiyayya,idan kana da wasiya ta karshe ga yan'uwanka ko danginka ka hanzarta sanar dani lallai zan isar da ita.Koda Alkas yazo nan a jawabinsa sai Jarumi Hibairu ya kyalkyale da dariya sannan yace,ai ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare,sau ashirin da daya muna fafata kazamin yaki tsananin ni dakai a cikin garuruwa da dazuzzuka daban dabam amma baka taba samun nasara ba a kaina,nima kuma ban taba samun nasara ba a kanka,yanzu kai a tunaninka saboda mun hadu a wannan gasa ta jarumta shine kake ganin cewa ka sami damar da zaka iya kasheni?To ka sani sai an gwada sannan a kan sanin na kwarai don haka ga fili ga mai doki dan halak ka fasa.Koda gama fadin hakan sai jarumi Hibairu ya dan ja da baya kadan ya gyara tsayuwarsa yana mai buda hannayensa,shima Alkas sai ya gyara tsayuwarsa ya buda hannayensa suka kurawa juna idanu.Lokaci guda sai suka rugo da gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da azababben yaki wanda ya baiwa kowa mamak kuma yasa hankalin kowa ya dugunzuma ainun.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin irin tsananin jarumtakar dasu Hibairu keyi ta ban al'ajabi.Cikin bakin zafin nama suka rinka kaiwa junansu sara da suka ba kakkautawa tamkar jikinsu bana jini da tsoka bane.Wani lokacin saidai aga suna tashi sama suna shawagi akan juna tamkar tsuntsaye masu fukafukai,saida suka shafe kusan sa'a guda suna wannan bakin artabu sannan da kyar da sidin goshio kowannensu ya sami nasarar yankar dan'uwansa.Shidai Hibairu ya sami nasarar yankar Alkas a kan damtsen hannunsa na dama ne wanda ke rike da takobi shi kuma akan kafadar Hibairu ta hagu ya yanke shi.Duk da cewa kowannensu saida inda aka yankeshi ya dare jini yayi tsartuwa amma ko gezau basuyi ba,kuma basuyi kokarin daure raunikan nasu ba don tsaida jini,kawai sai suka gyara tsayuwars suka sake rugowa da gudu isuka kacame da sabon masifaffen yaki,ya zamana cewa wannan karon sun hada da kaiwa junansu naushi da bugu,saigashi kowannensu na iya shanye dukan gami da maida martani,abudai kamar wasa suka sake shafe wata rabin sa'a suna gumurzu.Nanfa yan kallo suka gane cewa tabbas karfinsu yazo daya,su kuwa attajiran gasar dasuka zabi Alkas a matsayin gwaninsu kuma suka zuba kudi mai dumbin yawa hankalinsu ne ya dugunzuma ainun saboda basu da tabbacin cewa shine zai lashe gasa.Al'amarin Gimbiya Zuhura kuwa tun daga lokacin dataga Alkas ya yiwa Hibairu rauni a kafadarsa jini na zuba sai ta dimauce hankalinta ya tashi ta rasa abinda ke mata dadi,domin jitayi kamar ta roki mahaifinta yasa a gaggauta tsayar da yakin amma sai ta dake.Tun Hibairu da Alkas nayin wannan gumurzu da kwarinsu da karfinsu har saida suka sare suka durkushe kasa cikin matukar galabaita,kowan nensu ma bai san sa'adda takobinsa ta subuce ba daga hannunsa suka kacame da kokawa.Adaidai wannan lokacine aka buga gangar dakatar da gasa don haka sai Alkalan gasar suka rugo da gudu izuwa cikin filin suka raba Alkas da Hibairu,aka janyesu izuwa inda likitoci zasuyi musu magani,shi kuma babban Alkali na gasar sai ya tsaya a tsakiyar filin ya fuskanci jama'a yace,a halin yanzu Jarumi Hibairu na birnin Nurul Islam ya sami nasarar shiga zagayen wasa na biyu.Gimbiya Malika da Jarumi Alkas kuwa suna da sauran wasanni biyu kafin su shigo zagayen na biyu don haka a tafi hutu saida yamma za'a dawo inda za'a fitar da jarumai biyu wadanda zasu kara dasu Gimbiya Malika.Yadda za'a fitar da jaruman biyu kuwa shine za'a hada gaba dayan sauran jaruman gasar su yaki juna,wanda duk yaje kasa ya fita daga gasar har sai an sami gwanaye biyun da basu fadi kasa ba sune zasu kara da Malika da Alkas.Koda Yan kallo da attajiran gasa sukaji wannan batu sai suka rude da shewa suka kamu da matukar farinciki,sarkin Misra da 'yarsa Gimbiya Zuhura ne suka fara mikewa tsaye suka fice daga filin Zuhura nata waigen kofar inda aka shiga dasu Jarumi Hibairu,suka tafi izuwa gidan sarautar,sannan taro ya watse kowa ya kama gabansa.Jama'a suka tafi suna ta fadin albarkacin bakinsu. Nima ganin su Gimbiya Zuhura,Jaruman Gasa da sauran jama'ar gari sun tafi Hutu yasa nima na tafi Hutu. SA MAZA GUDU Littafi na Hudu (4) Part C Kowa ya kama gabansa,Jama'a suka tafi suna ta fadin albarkacin bakinsu. Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da ta isa masaukinta ta shiga cikin turakarta sai ta zauna tayi tagumi kuma ta fada cikin kogin tunani mai zurfi,tana cikin wannan hali ne sarki Hilairu ya shigo cikin turakar yana mai yin gyaran murya,kamar wacce ta farka daga barci haka ta dago kai ta dubeshi cikin firgici.Koda taga shine sai tayi ajiyar numfashi gami da murmushi sannan ta nuna masa wata kujdera tana mai yi masa nuni daya zauna,cikin nutsuwa yake ya zauna akan kujerar wacce ke fuskantarta sannan ya dubeta a cikin nutsuwa yace,yake Gimbiya Malika wane irin tunani kikeyi ne haka mai zurfi?Shin kinga abin mamaki ne a cikin wannan gasar jarumtaka da kika shiga?Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Malika tayi ajiyar zuciya sannan tace,tabbas abinda ka fada gaskiya ne,tabbas wannan bakon jarumi wato Hibairu ina ganin kamar shine bakon jarumin da mahaifina ya bani labarin cewa zan hadu dashi kuma ya umarceni dana yi masa biyayya ya koya mini yaki domin na kare kaina daga sharrin dan'uwana Yarima Lahaman anan gaba,shi kuma wancan daya jarumin dayai gumurzu dashi shine....Kawai sai Malika tayi shiru taki karasa abinda take son fadi.Cikin mamaki da zakewa sarki Hilairu yace ki gaya mini mana wanene shi,ni kaina na fara zargin nasan shi,duk da cewa ya rufe fuskarsa a cikin hular karfe kuma ya rufe jikinsa duka da sutura ina ji a jikina kamar na sanshi.Wanene shi,me kika sani akansa,waishin ma me yasa ba'a baiyana garin daya fito ba?Sa'adda Malika taji wadannan tambayoyi daga bakin sarki Hilairu sai tayi sauri ta juya masa baya don kada ya fahimci cewar lallai akwai abinda take boye masa sannan tace,ina kyautata zaton shine shugaban wata runduna ta mayakan taimako.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sarki Hilairu ya zagayo kusa da ita suka sake fuskantar juna sannan yace,wace runduna ce ta mayakan taimako?Malika tace ai wata runduna ce mai yaki da zalunci,ita dai wannan runduna tana shiga ko ina a wannan nahiya cikin dazuzzuka ta kawar da yanfashi sannan kuma tana kai agajin gaggawa ga garuruwan da suke fama da annoba ta fari ko cututtuka,bayanga haka kuma duk inda suka ji labarin sarki azzalumi suna zuwa su saukeshi daga kan karagarsa da karfin tsiya,su nada waninsa mai adalci.Koda jin wannan batu sai Sarki Hilairu ya gyada kai yace,indai haka ne kuwa wannan jarumi bazai kasa sanin dan'uwan ba wanda ake kira da Alkas mai lakabi da SA MAZA GUDU saboda ra'ayinsu yazo iri daya,Shi Alkas ma yabar gida ne saboda ya shiga duniya yayi yaki da zalunci kawai,tun ban hau kan karagar mulki ba ya bar gida kuma na tabbatar da cewa idan ya dawo yaga yadda dan'uwanki Yarima Lahaman yaci mutuncinmu ya baje birnin namu zai fusata yace zaije ya yaki kasarku.Ni ne kadai zan iya hanashi aiwatar da hakan don haka zan so ace bayan an gama wannan gasa ta jarumtaka anan birnin Misra ki barni na koma izuwa can kasata koda kuwa ba zaki iya taimaka mini da abinda zan gyara birnin ba a yanzu.Lokacin da sarki Hilairu yazo nan a zancensa sai gimbiya Malika ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace,shin ka manta ne cewa barinka kai kadai kayi tafiya mai nisa abune mai hadarin gaske tunda dan'uwana Yarima Lahaman na nan a raye kuma yana mugun bakin ciki bisa karbarka da nayi a hannunsa,ina mai tabbatar maka da cewa zai kasance a cikin farautar rayuwarka data jama'arka,ni kaina ba kyaleni zaiyi ba,zai cigaba dasa ido a kaina ya nemi hanyar da zai iya cutar dani,kafin ma yaje ya gama sabon shirin yakata,kada kayi mamakin cewa a halin yanzu ma akwai yan leken asirinsa a nan cikin birnin misra masu sa ido akanmu.Ni kawai yanzu babban abinda ya dameni shine bansan ta hanyar da zan bullowa wannan bakon jarumi ba,Hibairu ya amince ya koyar dani salon yakinsa,gashi na lura da 'yar sarkin garin nan naga cewa ta kamu da matukar sonsa farat daya,Anya kuwa nima bazan ribace shi da batun soyayya ba? Koda jin wannan tambaya sai Sarki Hilairu yaji kishi ya turnukeshi don haka sai ya dubeta cikin alamun damuwa yace,ai kuwa gwara ki sauya shawara domin babu yadda za'ayi ya so ki ya bar gimbiya Zuhura yar sarkin garin nan tunda tafi ki kyau ta fiki mulki,me zai hana ki lallaba wancan daya bakon jarumin ya baki nasa horon yakin ba tunda karfinsu yazo daya,gashi a zahiri kowa ya gani.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Malika ta girgiza kai tace,a'a ba agareshi mahaifina yace na nemi horon yaki ba,ka sani cewa abinda na gaba ya hango maka,yaro ko ya hau kan tsauni bazai iya hangoshi ba,daya jarumin sun banbanta asiffa,addini,hali da yanayi don haka ba lallai bane ba na sami nasarar abinda nake nema ba a wajen Alkas.Yanzu na gaji sosai ina bukatar na kwanta na huta,ina ganin zaifi kyau ka tafi izuwa taka turakar.Koda jin wannan batu sai sarki Hilairu ya rissina ga Malika yana mai godiya sannan ya juya ya fice daga cikin dakin zuciyarsa cike da dumbin damuwa a lokacin da itama ta bishi da kallo kawai tana mamakin yadda akayiya kusan shaida dan'uwansa SA MAZA GUDU duk da cewa ya rufe fuskarsa da jikinsa.Acan gidan sarautar sarkin misra kuwa tunda Gimbiya Zuhura ta koma gida ta shiga cikin turakarta sai ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta kasa kwanciya da tafiya,da zarar taje ta kwanta akan gadonta ta rintse idanunta domin tayi barci bata ganin komai face fuskar jarumi Hibairu.Koda taga tunaninsa da begensa ya hanata sakat kuma lallai zata iya cutuwa idan bata ganshi ba sai ta mike tsaye zumbur ta tafi izuwa turakar mahaifinta do min ta rokeshi yasa aje azo da Jarumi Hibairu.Zuhura na shiga cikin babbar turakar mahaifin nata sai ta kame kamar gunki saboda tsananin mamaki,ba komai ne ya bata mamaki ba face ganin Jarumi Hibairu tare da mahaifinta a zaune su biyu rak suna ciye ciye da shaye shaye,cikin raha da annashuwa tamkar sun san junansu da dadewa.Lokaci guda sarki Kamzal da Jarumi Hibairu suka juya suka dubeta suna ganinta suka mike tsaye a tare suka kura mata idanu saboda mamakin rashin sanin sa'adda ta shigo.Sarki Kamzal ya taho ga Zuhura da sauri ya tarbeta cikin murna yana mai ruke hannunta ya janyota izuwa inda Hibairu ke tsaye a lokacin da Hibairu yake yi mata wani irin kallo wanda ta kasa gane ko na menene,shin kallo ne na so ko kuwa kyawunta ne ya firgitashi? Amsar data kasa baiwa kanta kenan,abinda ya burgeta dangane dashi shine irin shigar da yayi ta kamala kuma data dubi kan teburin da suke cin abinci sai taga babu tambulan din giya ko guda daya a gaban Hibairu face tambula na ruwan inibi,shi kuwa mahaifin nata akwai tambulan giya sama da kala uku a gabansa.Sarki Kamzal ya zaunar da Gimbuya Zuhura akan kujera ta uku dake karkashin teburin da suke cin abinci sannan shima ya zauna kuma ya dubi Jarumi Hibairu yayi masa izinin sake zama.Take Hibairu ya zauna amma saboda kunyarsa sai ya sunkui da kansa kasa bai yarda ya cigaba da kallon fuskar gimbiya Zuhura ba,shi kansa sarki Kamzal wannan halaiya ta jarumi Hibairu ta bashi mamaki kuma ta burgeshi saboda wannan ne karo na farko dayaga saurayin dayayi arba da 'yarsa bai rude ba.Nan take Sarki Kamzal ya gabatar da Zuhura a wajen Jarumi Hibairu yace,wannan itace gimbiya kuma 'ya ta guda daya jal a duniya wacce nakeso fiye da komai a duniya,duk da cewa ka ganta a filin gasa dole ne na sake gabatar da ita a gareka kuma naji dadi datazo nan yanzu ta samemu saboda akwai tambayar da nakeso ka amsa mini ita a gabanta.Tambaya ta kuwa itace,wanene kai? ma'ana inason naji tarihin rayuwarka duk da cewa naji ance ka fito ne daga birnin Nurul Islam garin nan na ma'abota addinin musulunci,addinin da ko kadan bashida farin jini a wannan nahiya gaba daya,menene dalilin dayasa ka baro kasarku harka zo ka shiga wanann gasa ta jarumtaka wacce nake shiryawa duk karshen shekara?Idan ka lashe wannan gasa me kakeso a baka?Shin zaka bukaci auren 'yata ne ko kuwa zaka karbi dukiya ne?Sa'adda sarki Kamzal yazo nan a jawabinsa sai Jarumi Hibairu ya dago kai ya dubeshi sannan ya dubi Gimbiya Zuhura cikin alamun girmamawa da kawaici sannan yace,yakai wannan sarki mai daraja ina rokon alfarmarka bari sai bayan na lashe wannan gasa sannan na fadi ladana amma ba yanzu ba.Dangane da labarina kuwa abune mai tsawo amma zanyi kokari na dan gajarce muku shi cikin yan sa'o'i.Koda Jarumi Hibairu yazo nan a zancensa sai yayi gyaran murya sannan ya yiwa Gimbiya Zuhura wani irin satar kallo yace,da farko dai... SA MAZA GUDU Littafi na Hudu (4) Part D Da farko dai kamar yadda kukaji na fito ne daga birnin Nurul Islam garin dake can kudancin birnin Kisra kuma wannan birni yana bisa wani tsibiri ne zagaye da kogi don haka sai anyi tafiyar sa'a uku kacal a cikin kwale kwale ake isa garin.Gari ne karami wanda gaba dayansa Al'ummar dake cikinsa bai wuce da dari bakwai da arba'in ba.Ina nufin mazanmu da matanmu,yaranmu da manya,kuma muna yin addinin musulunci wanda shine addinin bautar Allah Sarki Guda wanda bashi da abokin taraiya,ba a hade komai dashi,muna zaune a wannan tsibiri cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da nutsuwa da wada.Addininmu nada dokoki wadanda muke binsu sau da sau,shan giya haramunne,caca ko zina da sata duk haramunne,muna da alkawari a tsakaninmu,muna da ruke amana,kuma duka abinda zamu fada sai gaskiya,wani baya danne hakkin wani,talaka da attajiri,bawa ko ubangida duk daya ne babu wanda yafi wani face wanda yafi tsoron Allah,kewaye da wannan tsibiri namu akwai dazuzzuka masu dauke da tarin ni'ima gami da dimbin dabbobin daji iri iri,bisa wannan dalili ne ya zamana cewa bamu da wata sana'a wacce tafi farauta kuma idan muka farauto dabbobin daji muna haurawa izuwa kasashen makwabtaka muna siyar musu da fatoci da sauran sassan jikin dabbobi,kamar hauwan giwa da kasusuwa wadanda ake amfani dasu wajen yin wadansu kayan amfani na yau da kullum.Wannan sana'a tamu itace kadai hanyar kasuwancinmu kuma itace hanyar cinmu da shanmu.Kuma babban arzikin kasarmu domin kasar garin namu bata yin noma.Tsakanin Birninmu na Nurul Islam da sauran kasashen dake makwabtaka damu akwai yarjejeniya ta zama lafiya gami da dokoki,yarjejeniyar itace kuma ba'a yarda muyi tallan addininmu ba ga kowa kuma ba'a yarda muyi auratayya da dan wata kasa ba,ma'ana baza'a bmu aure ba,muma bazamu bayar ba.Sama da shekaru dari da ashirin da muke zaune lafiya a cikin wannan yarjejeniya ba'a taba samun wani sabani ba saboda mutanenmu suna matukar kula da kiyayewa.Mahaifina shine Sarkin Mafarauta na birnin Nurul Islam,ana kiransa da suna Uraisu bin Hannaf.Mafarauci Uraisu ya shahara ainun ko ina a cikin kasashen dake makwabtaka damu sabida duk sa'adda akayi gasa ta farauta a kowacce kasa shike zuwa na daya.Mutum ne shi mai tsananin jarumtaka,sanin sirrin daji da kuma tsananin sa'a da rabo.A cikin wannan sana'a ta sa ne Allah yayi masa arziki sosai har ya zamana cewa a gaba daya birninmu na Nurul Islam babu attajiri kamarsa,amma ko kadan dukiyarsa bata dameshi ba,kulluma a cikin rabar da ita yake ga miski da almajirai da masu bukata,hakanne ya janyo masa matukar farin jini a wajen jama'a har ya zamana cewa ana girmamashi fiye da yadda ake girmama sarkinmu.Wannan ne dalilin daya haifar da 'yar tsana tsakaninsa da Mahaifinmu saboda gani yake kamar ma wata rana mahaifin nawa zai iya kwace masa sarautarsa,shi muwa mahaifina ko kyauta aka bashi mulkin bazai karba ba.Lokacin da arzikin mahaifina ya bunkasa ya zamana cewa ya auri mataye har uku dadin da uwata hudu kenan,ya zamana ceqa ya fara tara iyali sai yasa aka fadada gidansa akayi gini mai kyau wanda ma yafi gidan sarki kyau.Hakanne ya kara janyowa mahaifina bakin jini a wajen sarkinmu yaji ya tsaneshi sosai amma a zahiri baya nuna hassadarsa,saidai ma muna tsantsar soyayya a gareshi saboda kusan bukatun gidan sarkin mahaifina ne ke daukar nauyinsu.A wannan lokaci ina da shekara goma sha tara a duniya kuma inada kanne gosha sha biyu wadanda suka kasance kananan yara babu dan sama da shekaru goma.Nima na taso da jarumtaka,sanin sirrin daji,iya farauta gami da mutukar sa'a bisa duk abinda nasa a gabana tun banfi shekara shifa ba,mahaifina ke fita dani daji yana koya mini yadda ake farauta kuma ya koyar dani yaki don baiwa kaina tsaro daga harin yan fashi da yan sumame.Lokacin dana kai shekara tara ne na fara yin abubuwan ban al'ajabi na jarumtaka,domin komai girman dabbar daji da hadarinta ina iya tararta na kasheta kuma komai yawan yanfashi ina zame musu alakakai na kashe na kashewa masu gudu su gudu,in tarwatsa su.Birnin kisra shine birnin da yafi dukkan birane girma da daukaka gami da karfin masarauta,gaba daya sarakunan kewayen suna tsoron sarkin birnin Kisra saboda karfin mayakansa da kuma tsananin zaluncinsa.Bisa dole ma suke kai masa haraji mai tsoka don gudun kada ya yakesu,ana kiran wannan sarki da suna Zadasi bin Auzir.Babu wata hulda data taba shiga tsakanin mutanenmu na Nurul Islam da birnin Kisra,asalima babu wani dan garinmu daya taba shiga cikin birnin kisra a tsawon shekarun da birnin namu ya kafu,amma su mutanen birnin kisra suna shigowa cikin birnin Nurul Islam domin siyan fatocin dabbo da kasusuwa.Wani babban abin mamaki shine kafin sarki Zaldashi anyi sarakuna arba'in da daya a birnin kisra amma daya daga cikinsu bai taba sa ido akan birninmu na Nurul Islam ba kuma bai taba neman harajiba.Gaba daya sarakunan dake nahiyar suna mamakin wannan al'amari,mu kanmu mutanen birnin Nurul Islam muna mamakin haka tunda dai munsan cewa mutanen Kisra ba tsoronmu suke ji ba,sun fimu tarin mayaka da kayan yaki.A yawa kuwa sun ninkanamu sama da sau dubu

Chapter 10 of 19