Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su cutar dani ba tare dama naga wanda ya cutar dani din ba.Tunda gani a cikin turmutsun mutane da babu adadi haka dai na ci gaba da tafiya har na samu da kyar na iso gidan sarautar,ina isowa bakin kofar na kunna kai ciki,daga sannan ne naga dakarun sarki sun fara bani kariya suna hana kowa zuwa kusa dani ko ya rabeni face attajirin gasar daya zabeni a matsayin jaruminsa wanda ake kira da suna Abu Salif. Abu Salif ya kasance matashin mutum dan kimanin shekaru talatin zuwa arba'in,ya kasance gajeren mutum kamar wada amma kuma fuskarsa nada kwarjini,Abu Salif na ganina sai ya taho gareni da sauri cikin farin ciki ya rungumeni sannan ya kama hannuna muka cigaba da tafiya inda ya dubeni yace,yakai jarumina kayi sani cewa da zarar an baka wannan kambun gasa shike nan nida kai mun gama yin arziki,yayanmu da jikokinmu ma har abada bazasuyi talauci ba,sa'adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace,ai duk abinda zaka samu sakamakon cacar da ka shiga naka ne kai kadai saboda aini a addininmu caca haramunce don haka bana cin kudin caca.Koda jin haka sai Abu Salif ya dubeni cikin alamun tsananin mamaki yace,wane irin addini ne haka?Hibairu yace ni ma'abocin addinin musulunci ne.Ko da jin haka sai attajiri Abu Salif ya tsaya cak a inda yake idanunsa suka zazzaro kuma jikinsa ya kama kyarma ya dubeni cikin alamun tsananin tsoro yace,kada ka kuskura ka baiyana addininka a garin nan domin an tsani musulunci da musulmai fiye da komai,mutane zasu iya yi maka rajamu a kashe ka a banza.koda jin haka saina dubi Attajiri Abu Salif nayi murmushi nace,zan kasance a cikin tsananin farinciki idan har kuka kasheni a lokacin dana jaddada kalmar Allah a gareku saboda nasan cewa na sami kyakkyawar cikawa domin Aljanna ce mako mata a wajen ubangijina.Ina gama fadin haka saina cigaba da tafiyata cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tamkar babu wani abu daya taba damuna a rayuwata.Har muka iso tsakiyar gidan sarautar jikin Abu Salif bai daina tsuma ba saboda tsananin tsoro.Muna isowa na fara yin arba da jarumi sa maza gudu a tsaye a tsakiyar filin shi kadai a cikin gagarumar shigar yaki,nima sai na nufi inda yake naje na tsaya daf dashi,muna kallon juna sai yayi mini wani irin murmushi wanda na kasa gane ko na mugunta ne, ko kuma na farinciki,ina daga kaina sama sai na hango sarki zaldasi tare da gimbiya Lasmin zaune a can sama bisa wani gini mai tudu bisa kujeru na alfarma tare da fadawansa da manyan sarakunan nahiyar da kuma manyan baki.Ina hada idanu da Lasmin sai naga ta kura mini idanu cikin murmushi mai taushin gaske wanda ke dauke da alamonin tambaya.Nan take na maida nata da martanin murmushin,saboda dadin dataji bata san sa'adda ta wage baki ba tana dariya.Koda sarki Zaldasi ya lura da ita sai ya murtuke fuskarsa ya daka mata harara.Gaba daya gidan sarautar a cike yake da mutane babu masakar tsinke har kan katanga mutane ne a zazzaune sun zuba idanu suga wanda zai zama zakaran gasa.Acan gefe daya kuma sabbabin alkalan gasa ne kimanin su saba'in a zaune rike da alkalami da takarda na rubutu.Koda na tsaya a tsakiya filin sai na risina na gaida sarki sannan na gaisar da sauran jama'ar gari,ai kuwa sai filin ya rude da shewa gami da tafi aka rinka yi mini jinjima.A wannan lokacin hayaniyar mutane ta cika gaba gidan sarautar daya,kowa yana fadin albarkacin bakinsa ne dangane da wannan gasa da akayi,wasu ma musu sukeyi akan cewa babu yadda za'ayi a iya tantance gaskiyar wanda ya lashe wannan gasa tsakanin Jarimi Hibairu da Jarumi Alkas,wasu kuma jimami sukeyi akan rashin da'akayi na dumbin rayuka.Anan cikin wannan hali ne sarki Zaldasi ya mike ya daga hannunsa sama.Nantake fadar tayi tsit tamkar babu mutane a cikinta sannan yayi gyaran murya yace,yanzu zamu saurari bayani daga bakin wadannan manyan zaratan jaruman gasa guda biyu wadanda su kadai ne suka tsira da rayuwarsu a cikin dajin Sairul sakamakon yin arba da zaki nurul maut,kuma sune kadai suka fafata dashi har suka sami nasarar kashe shi.A cikin bayanin kowannensu numa son ya fadi shaidar da zata tabbatar da cewa shine ya kashe wannan zaki.Bayan mun gama saurarin bayaninsu ne alkalan gasa zasuyi amfani da hankali da kuma hikima wajen tantance mai gaskiya,sannan abashi ladansa na gasar kamar yadda nayi alkawari,ma'ana zan baiwa zakaran wannan gasa auren 'yata gimbiya Lasmin.Zan raba kasata biyu na bashi rabi ya mulka kuma zan bashi dukiya mai tsananin yawan da har bayan sa ma bazasuyi talauci ba.Koda jin wannan batu sai fadar ta rude da shewa gami da tafi,makada da mawaka suka kama shagalinsu.Saida sarki Zaldasi ya koma kan kujerarsa ya zauna sannan aka sake yin tsit,a sannanne shugaban alkalan gasar ya dubi sa maza gudu yace,kai ne zaka fara yin bayani,sannan jarumi Hibairu yayi nasa.Ba tare da bata wani lokaci ba Sa Maza Gudu yace gyara tsayuwarsa kuma yayi gyaran murya yana mai fuskantar miliyoyin jama'ar dake cikin fadar ya bude baki yace,kamar yadda aka gani a zahiri mun kai mu dubu dari shida da doriya muka shiga cikin dajin Sairul domin kashe zaki nurul maut,amma mu biyu ne kacal muka dawo a raye,ina mai tabbatar muku da cewa munga bala'i da masifa irin wacce babu makamanciyarta a cikin wannan duniya,lokacin da mukayi arba da zaki nurul maut,kuma nan take zaki nurul maut ya rikide ya zama wani irin mugun jan haske ya rinka burma gadon bayan mutane da kirazansu suna zubewa kasa mattatu,wadanda dama sukayi yunkurin guduwa ma sai ya rinka binsu yana farkewa.Nida Jarumi Hibairu ne kadai zaki nurul maut ya kasa kusanta farat daya saboda karfin sihirin tsafin dake jikinmu.Saida zaki nurul maut ya gama kashe gaba dayan jama'ar dake tare damu sannan ya juyo ya fuskancemu nan take dan'uwana Hibairu ya firgoce ya ruga izuwa bayan wani dutse ya buya,ni kuwa sai na tsaya na fuskanci nurul maut a lokacin da zuciyata ta kekashe ga barin jin tsoron komai.Koda Sa Maza Gudu yazo nan a zancensa sai nayi murmushi kuma na kamu da mamakin yadda ya tsala karya haka ba tare dayaji kunyata ba.Sa Maza gudu yacigaba da cewa na take na zare takobina na afkawa zaki nurul maut suka ruguntsume da azababben yaki saida muka kwana muka yini muna wannan yaki nida zaki nurul maut sannan na samu da kyar da sidin goshi da kuma karfin damtse dana sihirin tsafina na tsargeshi da takobina na rabashi gida biyu,bayan yayi mini raunika da yawa ajikina.Koda Jarumi Hibairu yaga na sami wannan nasara sai ya rugo da gudu cikin shammace ya suri rabin jikin zaki nurul maut ya dubeni ya kyalkyale da dariya yace,kaga yanzu zan sami wannan kambun gasa batare danasha wahalar banza ba,domin kashe ka zanyi na dauke gawar zakin na tafi da ita.Koda naji wannan batu sai na bushe da dariua sannan na murtule fuskata na dubi Hibairu nace idan har kaga ka sami nasarar yin hakan to lallai bana numfashi a doron kasa.Nan take muka ruguntsume da azababben yaki a cikin rabin sa'amukayi mugun yaki ni da Hibairu harta kaimu gayinragas muka zube kasa sumammu,saida muka jima a kwance cikin suma sannan muka farfado.Bisa dole muka hakura da batun yakar juna muka tako da kafafunmu da kyar muka dawo sansani.Wannan shine iyakar abinda dana san ya faru a can dajin Sairul.Koda jarumi sa maza gudu yazo nan a labarinsa sai jama'a suka rude dayi masa tafi gami da jinjina,har saida alkalin gasar ya daga hannun sannan akayi tsit ya dubi Jarumi Hibairu yace kaji abinda abokin gasarka ya fada yanzu kaima saika bamu naka labarin muji domin mu tantance mai gaskiya a tsakaninku.Koda naji wannan umarni sainayi gyaran murya sannan na dubi gaba dayan miliyoyin jama'ar dake cikin gidan sarautar nace,da farko dai ina mai rantsuwa da girman darajar ubangijina abin bautata duk labarin dazan fadi yanzu zan fada ne bisa gaskiya.Idan har nayi karya a cikinsa ina rokon mahaliccina da ya kashe ni yanzu take a wannan wuri batare danayi koda taku daya ba da kafata.Koda jama'a sukaji wannan batu sai kowa ya cika da tsananin mamaki yadda Hibairu yayi wannan ganganci saboda kowa yayi imani da abinda yake bautawa a nahiyar,duk wanda akaji ya rantse da abin bautarsa na tabbatar da cewa bazaiyi karyaba.Nan take Hibairu ya kwashe labarin duk abinda ya faru a cikin dajin Sairul ya zaiyane shi gaba daya bisa gaskiya ba tare da yayi kari ko ragi ba.Daga karshe sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa yace,shin kun san waye ya bani gagarumin karfin da har na iya daga wannan zaki na makashi akan wannan dutse ya dagargake?To ba wani bane face UBANGIJIN MUSULUNCI,Tsaya kuyi tunani da hankalinku da kuma basirarku.Aduk fadin nahiyar nan gaba daya babu wanda yafi sarki Zaldasi karfin sihirin tsafi amma zaki nurul maut ya gagareshi kashewa,abinda ya gagareshi kuma shine za'ace jarumi Alkas ya iya dashi?Lallai Alkas makaryaci ne bashine ya kashe wannan zaki ba,nine na kashe shi da karfin ubangijin musulunci,ubangijin daya halicci kowa da kowa.Koda Hibairu yazo nan a zancensa sai jikin gaba dayan miliyoyin jama'ar dake wajen yayi sanyi har dukkanin alkalan gasar kuwa,domin kowa ji yayi ya gamsu da duk abinda Hibairu ya fada Sa Maza gudu kuwa saiya rude ya kama ihu yana karya ta Hibairu.Koda Sarki Zaldasi ya fahimci cewa gaba dayan jama'ar dake wajen zasu karbi addininmu na musulunci sai ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ya baiwa dakaru umarni yace su kama Hibairu su kaishi kurkuku su kulle shi saboda yazo da sabon addini.Nan take kuwa sama da dakaru dubu suka afka masa da nufin su kamashi,amma sai ya zare takobinsa ya taresu aka ruguntsume da azababben yaki. SHIN ZA'A KAMA HIBAIRU A KAISHI KURKUKUN A KULLE? WAZA'A BAWA KAMBUN WANNAN GASA TSAKANIN HIBAIRU DA SA MAZA GUDU? YAYA KARSHEN WANNAN LABARI DA HIBAIRU KE BAIWA SU SARKI KAMZAL DA GIMBIYA ZUHURA ZAI KASANCE? YAYA KARSHEN GABAR HIBAIRU DA SA MAZA GUDU ZATA KASANCE? GIMBIYA MALIKA ITA DA DAN'UWANTA YARIMA LAHAMAN YAYA KARSHEN TASU GABAR ZATA KASANCE? Mu hadu A Littafi na gaba Sa Maza Gudu Littafi na bakwai(7)An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTSA MAZA GUDU!!! Littafi Na Bakwai:(7) Part  LOKACIN DA AKA RUGUNTSUME DA AZABABBEN YAKI TSAKANIN JARUMI HIBAIRU DA DAKARUN SARKI ZALDASI SAI HANKALIN GABA DAYAN JAMA'AR DAKE WAJEN YA DUGUNZUMA AINUN SABODA GANIN IRIN BALA'IN DA YAKE FARUWA DOMIN IHUN MAZAJE NE YA CIKA DODON KUNNEN MUTANE GAMI DA KARAFKIYAR KARAFA.Duk inda Jarumi Hibairu yasa gabansa saidai kaga sassan jikin bil'adama na shawagi a sama suna zubowa kasa a lokacin daya lazimci yin kabbara da karfi,babu abinda zai baiwa mutum mamaki fave ganin irin tsananin jarumtakar Jarumi Hibairu keyi gami da wani irin masiffan zafin nama kuma yana kai sara da suka izuwa ko wace kusurwa ma'ana gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama da kasa.Nan da nan ya zamewa dakarun alakakai suka rasa yadda zasuyi dashi,shi kansa Jarumi Hibairu yasan cewa wannan karfi da jarumtaka ya daya samu bayin kansa bane abu ne kawai daga Allah.Lokacin da bala'i yakai bala'i sai jama'a suka kama guje guke da iface iface,kafin shudewar dakiku masu yawa filin wajen ya dade babu kowa face tsirarun fadawan sarki dashi kansa Sarki Zaldasi sai kuma Sa Maza Gudu da kuma dakarun dake yakar Hibairu sai kuma Lasmin wacce ke tsaye daf da sarki Zaldasi tana kallon yakin da akeyi cikin tsananin tsoro da fargaba domin gani take yi kamar a ko yaushe dakarun sarki Zaldasi zasu iya samun galaba akan Hibairu tunda SARKIN YAWA YAFI SARKIN KARFI.Koda jarumi Hibairu yaga barnar da yakeyi ta yi yawa domin ana ta yin asarar dubunnan rayuka ne kuma shi ba burinsa kenan ba.Babban burinsa shine jama'ar kasar su fahimci ADDININ GASKIYA Kuma su karbe shi.Koda gama aiyana hakan a cikin zuciyarsa saiya budewa kansa hanya da karfin tsiya ya fice fit daga cikin dandazon dakarun kuma ya falfala da azababben gudu.Koda ganin haka sai Sarki Zaldasi yayi wuf ya zare takobinsa ya daka tsalle ya haye kan dokin yabi Hibairu a guje domin ya kure masa gudu,nanfa akaga abin al'ajabi domin wani irin gudu na ban mamaki Hibairu ya rinka yi yana tserewa dakarun da sarki tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya.Kafin kiftawar ido Hibairu ya fice daga cikin birnin gaba daya ya nausa cikin daji kuma ya bace bat tamkar ma bai taba wanzuwa ba.Duk dakarun da suka biyo shi da gudu saida suka sare suka zube kasa magashiyan suna haki kamar ransu zai fita.Shi kuma sarki Zaldasi saida ya shafe sa'a uku yana bin sawun Hibairu da gudu akan dokinsa har ya zamama cewa dokin nasa ya gaji ainun ya fadi dashi kasa.Cikin tsananin fushi sarki Zaldasi ya mike tsaye zumbur ya dada falfalawa da gudu izuwa cikin dajin yana neman Hibairu.Shima gudu yake yi na ban al'ajabi da karfin sihirinsa na tsafi amma har ya sake shafe wata sa'a uku ko alamun Hibairu bai gani ba kuma takun sawayen Hibairu sun dauke dif tamkar daukewar ruwan sama.Koda ganin haka sai Sarki Zaldashi ya tsaya cak kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa biyu yana haki kamar ransa ne zai fita.Daga can kuma saiya takarkare ya kwarara wawan ihu cikin tsananin takaici da bakin ciki.Saboda karfin wannan ihu nasa saida aka jiyoshi a can cikin birnin nasa.Al'amarin daya firgita komai da kowa kenan har dabbobi suka kama neman inda zasu buya,tsuntsaye kuwa suka rinka tashi daga shekarsu suna sauya matsuguni.Mutane suka rinka kulle kofofi da tagogin gidajensu saboda kasar birnin ce ta kama girgiza gaba dayanta tamkar zata tsattsage duk abinda ke samanta ya rufta kasanta.Saida sarki Zaldasi ya shafe kusan rabin sa'a a tsugunne yana faman rusa kukan takaici da bakin ciki sannan ya mike tsaye ya juya da baya ya sake falfalawa da azababben gudu domin ya isa cikin garin da wuri.Da shigowar Sarki Zaldashi Cikn gari saiya rinka ganin mutane majalisa majalisa suna yin kus kus da zarar anga sarki Zaldasi sai ayi shiru a zube kasa gabansa ana kwasar gaisuwa.Koda ganin wannan al'amari sai hankalin sarki Zaldasi ya dugunzuma ainun yaji zuciyarsa ta buga da karfi,abinda zuciyarsa ta raya masa shine anya kuwa mutane basu fara yin imani da addinin Hibairu ba?Koda ya yiwa kansa wannan tambaya sai ransa ya baci nan take ya kara karfafa gudunsa nan da nan ya isa fada.Da isarsa sai yasa akayi shelar taro na gaggawa a fada.Ai kuwa kafin cikar sa'a guda fadar ta cika makil da mutanen gari har da gaba dayan fadawansa da dakarunsa.Lokacin da sarki Zaldasi ya mike tsaye ya karewa fadar kallo gaba dayanta yaga cewa hatta mata,yara,tsofaffi sun halacci wannan taro sai ransa yayi fari,amma kuma daya lura cewa akwai mutum daya jal wanda bai halacci wannan taro ba sai ransa ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa tamkar zata kone.Bayan sarki Zaldasi ya gama kallon kowa da kowa sai yayi gyaran murya yace yaku jama'ar wannan birnin mai albarka,kun sani cewa fiye da shekaru dubu a wannan kasa tamu muna tafiyar da addininmu wanda muka gada tun iyaye da kakanni ba'a tba samu wani shaidani ko wani takadari dayazo ya la'ance addininmu ba ko kuma yazo mana da wani sabon addinin daya fifita shi akan namu.Yanzu akan wane dalili zamu yarda da jarumi Hibairu ya yaudare mu da siddabarunsa yace damu wai ubangijinsa ne ya bashi sa'a da nasara har ya kashe zakin daya addabi gaba dayan jarumai.Sarakai da bokayen wannan nahiyar kada ku kuskura ku yarda a hillace ku da siddabaru ko sihiri a canja muku addini.Ina mai sanar daku cewa tunda wannan yaro yazo yaci mutuncin addinin iyayenmu da kakanninmu to ba zamu kyaleshi ba dole ne mu kamo shi a duk inda ya buya a cikin dazuzzukan dake cikin kasar nan domin muyi masa kisan Gilla.Ku sani cewa na bishi izuwa cikin daji kuma nayi amfani da dukkan karfin sihirin tsafina domin na kama shi kona hallaka shi amma abu ya faskara. °Abubakar Haleefah Physicist° Yanzu na yanke hukunci cewa zamu sake hada runduna ta zaratan mayakanmu wadanda muke takama dasu mu tafi neman jarumi Hibairu kuma da zarar mun kamo Jarumi Hibairu zamu zo dashi har nan fada muyi masa KISAN GILLAH a bainar jama'a domin ya zama abin misali ga sauran mutane irinsa masuyin mafarkin kawo mana sabon addini.Muna gamawa da wannan shaidanin yaro zamu baiwa Jaruma Sa Maza Gudu kambunsa na wannan gasar jarumtaka bisa nasarar daya samu ta kashe zaki Maut.Koda gama fadin hakan sai sarki Zaldasi ya waiga bayansa ya dubi Sarkin Yakinsa yace aje a fara shirin fita farautar da zamuyi ta Hibairu kuma a sanar da duk masana daji da dukkan mafarautan kasar nan ban daukewa kowa wannan fita ba.Gama fadin hakan keda wuya sai Sarki Zaldasi ya sauko daga kan mumbarin da yake tsaye ya juya ya shige izuwa cikin GIDAN SARAUTA.Faruwar hakan keda wuya sai jama'a suka watse kowa ya kama gabansa,mutane suka tafi izuwa gidajensu jikinsu a sanyaye kai da gani kasan cewa mutane suna cikin shakku gani da wasi wasi bisa duk abubuwan da suka faru yau a gasar jarumtakar da akayi.Lokacin da sarki Zaldasi ya shiga cikin gidan sarautar ya isa babban falonsa saiya iske Gimbiya Lasmin zaune ita kadai bisa kujerar daya saba zama fuskar gimbiya a murtuke take ko kadan babu annuri a tare da ita sannan kuma idanunta sun ciko da kwallah.Koda ganinta a cikin wannan hali sai hankalinsa ya dugunzuma yazo daf da ita ya zauna kuma ya dubeta cikin nutsuwa fuskarsa na nuna alamun matukar damuwa yace yake yata na sani cewa ban yiwa jarumi Hibairu hukunci na adalci ba amma ki sani cewa in banyi hakan ba bazan iya tsare mutuncin addininmu ba wanda muka gada tun iyaye da kakanin.Koda jin wannan batu sai gimbiya Lasmin ta dago kai ta dubi Sarki Zaldasi ranta a bace tace na sani cewa zaka iya hana mutane karbar wannan sabon addinin na jarumi Hibairu ta hanyar tsoratar dasu ta batun azaba ko kisa amma ta yaya zaka iya goge abin al'ajabin da idanuwansu suka gani? Ta yaya zaka iya lullube rashin adalcin daka yiwa Hibairu daga kan idanu da zuciyoyin jama'a,ka sani cewa bawai kawai anan iya cikin birninka matsalar ta tsaya ba,a halin yanzu duk kasashen dake wannan nahiya tamu babu inda labarin jarumtakar Hibairu bata kai ba bisa abin al'ajabin da yayi a wannan gasa kuma na tabbatar da cewar baza'a rasa wadansu ba daga cikin sarakunan.Ina mai tabbatar maka da cewa komai yawanku da shirinku ba zamu iya kama jarumi Hibairu ba a wannan farauta tasa ta zaku fita.Koda jin wannan batu sai ran sarki Zaldasi ya baci,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fishin da yayi bai san sa'adda ya dakawa Lasmin tsawa ba mai karfin gaske wacce tasa ta firgita ainun har ta fadi kasa dirshan.Sarki Zaldasi ya matso daf da Lasmin ya sunkuyar da kansa daf da fuskarta yace kada ki fusata ni nayi miki abinda ban taba yi miki ba a rayuwata wannan shine karo na farko dana tabayi miki tsawa irin wannan akan mulkina,al'adata da addinina zan iya salwantar da komai nawa na hakura dashi.Yana gama fadin hakan saiya mike tsaye ya shige izuwa cikin dakinsa da sauri a fusace ya banko kofar da karfi karar rufewar kofar ta sake razana gimbiya Lasmin taja da baya ta zauna.Saida Gimbiya Lasmin ta shafe sama da sa'a guda a zaune tana tunani da nazarin wannan al'amarin cikin bakin ciki,hawaye na shatata bisa kumatunta,kawai saita mike ta fice daga cikin dakin da sauri sauri gudu gudu,duk inda tazo wucewa sai kaga ana darewa ana bata hanya da sauri walau kuyangi,borori da dakaru.Kai tsaye Gimbiya Lasmin ta nufi inda bargar dawakai take,koda mai kula da bargar ya hango gimbiya Lasmin ta durfafo shi saiya taho gareta da sauri ya zube kasa gabanta ya kwashi gaisuwa ya dago kai ya dubeta yace ya shugabata lafiya kuwa naga kinzo nan da kanki alhalin baki taba ba?Koda jin wannan tambaya sai Lasmin ta dubi Hadimin a fusace ta daka masa tsawa tace maza ka kamo mini kosassan doki guda kuma lafiyayye wanda zan hau yanzu.Sa'adda hadimin yaji wannan batu sai jikinsa ya kama kyarma ya dubeta cikin alamun tsoro yace ya shugabata kiyi mini rai idan na baki dokin kika hau kika fice daga cikin gidan nan sarki kashe ni zaiyi.Koda jin haka sai Lasmin tayi wuf ta zare takobin hadimin daga jikinsa ta dota kaifin takobin akan wuyansa tace yanzu saika zaba shin kana so ka mutu ne yanzu yanzu bisa kin bin umarnina ko kuwa so kake ka mutu bayan kabi umarnina bisa hukuncin sarki?Har hadimin yayi yunkurin yayi gardama sai yaji wani mugun zugi a wuyansa inda Lasmin ta dora masa kaifi,a dimauce yasa hannunsa ya shafi wuyansa ai kuwa sai yaga jini,a dimauce yaja da baya sannan ya ruga izuwa cikin bargar dawakai ya kamo wani farin ingarman doki ya daura masa siddi sannan ya kawo mata.Bisa mamaki sai kawai yaga gimbiya ta daka tsalle sama ta haye dokin ta zabure shi da gudu ta nufi hanyar fita daga cikin gidan Sarautar.Abinda ya daurewa kowa kai a gidan sarautar shine ganin gimbiya akan doki tana sarrafashi yadda take so babu wanda ya taba sanin cewa ta iya doki domin yaune karon farko da aka tava ganin ta hau doki.Nan dai Hadimin ya bita da kallo yana murmushi bai san sa'adda maganar zuciyarsa ta fito fili ba yace ai kin cece ni tunda kinyi mini rauni a kan wuyana,kin bar min shaidar da zata kubutar dani a wajen sarki.Lokacinda Gimbiya ta iso bakin kofar gidan sarautar ta isketa a rufe sai dakarun dake gadin kofar kimanin su arba'in suka taso da sauri suka sha gabanta.Sarkin kofar ya dubeta yace ranki ya dade lafiya kika fito a sukwane haka ke kadai kuma ga takobi a hannunki?Koda jin wannan tambaya sai gimbiya ta murtuke °Abubakar Haleefah Physicist° fuskarta ta dubi sarkin kofar tace gori akayi min wai ban taba yin wani abin gwaninta ba shine nake son na basu mamaki.Maza ku bude miki kofa na fita ko kuma nayi amfani da kaifin takobina a kanku,kun sani cewa duk wanda ya bata mini rai daga cikinku a bakacin aikinsa.Koda jin haka sai jikin sarki kofa ya kama rawa ba shiri ya bayar da umarni aka bude mata kofa ta fice da gudu tana mai karawa dokin nata kaimi.Sai bayan kamar sa'a guda da tafiyar Gimbiya Lasmin sannan aka farga cewar bata cikin gidan sarautar.Al'amarin daya dugunzuma hankalin mahaifiyarta kenan ta ruga da gudu izuwa turakar sarki ta sanar dashi.Koda sarki Zaldasi yaji cewar gimbiya Lasmin ta fice daga cikin gidan sarautar sai ya kamu da tsananin bakin ciki don haka bai san sa'adda ya takarkare ya kwarara uban ihu ba.Take Mahaifiyar Lasmin ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin razanar da tayi,saida kuyangi suka ruga suka dauketa izuwa cikin turakarta sunayi mata fifita.Nan take sarki yasa aka kirawo sarkin yaki yace dashi yayi sauri ya dauki dakaru dari su bazama neman gimbiya Lasmin sai bayan sunzo da ita zai yanke hukunci akan wadanda sukayi sakaki har ta fice daga cikin gidan.Lallai ku dawo kafin dare ya raba saboda da asubar fari nake son zamu fita FARAUTAR JARUMI HIBAIRU.Koda jin haka sai sarkin Yaki ya risina yace ya shugabana jarumi Sa Maza Gudu na tsaye a kofar fada yana son yayi magana da kai.Dajin haka sai sarki Zaldasi yayi murmushi yace maza kaje kasa a shigo dashi gareni kai kuma ka tafi izuwa aikin dana baka yanzu,sarki yaki ya risina yace

Chapter 14 of 19