Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
an gama ya shugabana.Nan take ya juya ya fice daga cikin fadar jim kadan saiga wani badakare tare da Jarumi Sa Maza Gudu sun shigo cikin Fadar. Zan dakata anan. SA MAZA GUDU!!! Littafi Na Bakwai (7) Part B. Saiga wani Badakare tare da Sa Maza Gudu sun shigo cikin fadar.Da shigowarsu sai sarki Zaldasi ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar farin ciki ya tarbi sa maza gudu tamkar wanda yaga dan uwansa na jini har yana rungume shi sannan ya kama shi yaje ya zaunar dashi bisa wata kujera suka fuskanci juna.Nan take wata kuyanga ta kawo musu tambula na ruwan inibi a kan faranti gami da kofunan zinare guda biyu,bayan kuyangae ta zuba musu ruwan inibin sun dan kurba sai sarki zaldasi ya daga hannunsa na dama sama yana mai nuni da cewa a fita a basu wuri.Nan take kuwa kowa ya fice daga cikin fadar hatta dakaru na musamman masu tsaron lafiyar sarki.Saida Fadar tayi tsit tamkar babu mutum mai numfashi a cikinta sannan sarki ya dubi Sa Maza Gudu cikin nutsuwa yace yakai GWARZON wannan KARNI wace shawara ce kazo mini da Ita.Tabbas idanunka sunayi mini nuni da cewar akwai magana mai muhimmanci a cikin zuciyarka.Sa'adda Sa Maza Gudu yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi cikin murmushi sannan ya risina cikin murmushi yace ya shugaba na ina mai tabbatar maka da cewa baby wanda yasan tuggu da sirrin Hibairu sama dani mun dade muna gaba ni dashi kowannenmu nason ganin bayan dan uwansa.Ka sani cewa Hibairu bera ne mai mugun wayo wanda kyanwa dubu ba zasu iya kamoshi ba.Inason ka amince mini nayi muku jagora a lokacin da za'a fita farautarsa.Bukata ta biyu itace inason da zarar an kamo Hibairu kawai kasa a gaggauta yi masa kisan Gillah a bainar jama'a kuma a tabbatar mini da nasarata ta lashe wannan gasar jarumtaka kuma a daura aurena da gimbiya.Koda jin wannan batu sai sarki ya bushe da dariya sannan ya kama hannun Sa Maza Gudu suka mike tsaye tare ya dubeshi yace ka kwantar da hankalinka yakai Angon Gimbiya Lasmin,komai zai tafi daidai kamar yadda kake bukata,yanzu a hangenka menene kake ganin zai kawo mana matsala akan ganin bayan Jarumi Hibairu?Koda jin wannan tambaya sai Sa Maza Gudu yayi ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace abu daya ne zai kawo mana cikas kuma ba komai bane ba face karya zuciyar jama'ar gari akan bada imani ga addinin Hibairu.Maganar gaskiya itace furuvin da Hibairu yayi akan nasarar daya samu wajen kashe zaki nurul maut ta fara tasiri a cikin zukatun talakawa a yanzu haka na sami labarin cewa tsirarun mutane sun fara bayar da imani ga addinin Musulunci suna karbarsa a sirrance.Koda Sa Maza gudu yazo nan a jawabinsa sai hankalin sarki Zaldasi ya dugunzuma kuma ransa ya baci ainun fiye da koyaushe.Koda Sa Maza Gudu yaga yadda fuskar Sarki da jikinsa suka sauya yanayi nan take saiya dubeshi cikin murmushi yace kwantar da hankalinka ya shugabana ai magance wannan matsala abu ne mai sauki kawai ai kasa a kafa doka kuma ayi binciken duk wanda aka kama da laifin karbar addinin Hibairu to kisa ne hukuncinsa hakan zata sa duk mai sha'awar karbar addinin ma ya fasa kuma cikin kankanin lokaci wannan addini zai shafe a wannan birni naka mai albarka,dama nahiyar gaba daya.Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Zaldasi ya kwanta ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dafa kafadar sa maza gudu yace tabbas inda ka kasance daya daga cikin mutanen kasata da ayau dinnan zan maisheka wazirina ko kuma babban bafade mai bani shawara akan harkokin mulki,yanzu na umarceka dakaje ka fara shiri na farautar Hibairu da zamu fita yau da asuba.Ina mai yi maka albishir da cewa da zarar ka auri Gimbiya zaka zamo daya daga cikin manyan attajiran duniya.Koda jin wannan batu sai jarumi sa maza gudu ya kyalkyale da dariyar farin ciki ya zube kasa gaban sarki Zaldasi yayi godiya sannan ya mike da sauri yayiwa sarki sallama ya juya ya fice daga cikin fadar.Shi kuma sarki Zaldasi saiya bishi da kallo kawai yana yin murmushi na samun nutsuwa da kwanciyar hankali. *Lokacin da Gimbiya Lasmin ta ruga izuwa cikin daji bisa doki tana mai tsala azababben gudu saita rinka kwalawa Jarumi Hibairu Kira tana waige waige da dube dube alhalin bata san a inda zata ganshi ba.Shi kasan dokin nata bai san inda ya dosa ba kawai yana gudu ne bisa umarninta da kuma duk inda ta kada shi.Saida suka shafe kusan sa'a gudu da rabi sunata ratsa dajin da gudu amma ko alamun Hibairu Lasmin bata gani ba har ya zamana cewa muryarta ta fara dashewa saboda yawan kiransa,dokinta kuma ya kamayin sassarfa kamar zai fadi.Koda ganin haka sai zuciyar Lasmin ta karaya kuma hankalinta ya dugunzuma ainun bata san sa'adda taja linzamin dokin taba ta tsaya cak sannan ta sauko daga kan dokin ta zauna akan wani dutse ta fashe da kukan bakin ciki,ba komai bane ya sata wannan kuka ba face tunanin cewa itafa yanzu tana cikin TSAKA MAI WUYA domin GABA TSINI ne a gareta Baya Kuma SIYAKI.Abu na farko yanzu shine ta gudo ta baro iyayenta da daular da take ciki ta biyo jarumi Hibairu kuma gashi bata ganshi ba wata kila ma baya cikin yanki kasar gaba daya.Nan take Lasmin ta yanke shawarar cewa ba zata taba komawa baya ba koda kuwa bata ga Jarumi Hibairu ba gwara ta cigaba da nausawa cikin daji koda kuwa zata rasa rayuwarta.Ba komai ne yasa ta yanke wannan hukunci ba face ta gamsu cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya,kuma tasan cewa indai tana zaune tare da sarki Zaldasi babu yadda za'ayi ta iya karbar Addinin Hibairu.Gmbiya Lasmin na zaune a cikin wannan hali tana ta zubar da hawaye sai kawai taji an kirawo sunanta daga baya,a firgice ta waigo baya,koda tau arba da wanda yayi kiranta sai ta mike tsaye zumbur ta ruga gareshi cikin tsananin farin ciki.Ba wani abu bane ba face Jarumi Hibairu tsaye shi kadai rike da takobi yana kallon..... SA MAZA GUDU!!! Littafi Na Bakwai (7) Part C. HIBAIRU TSAYE SHI KADAI RIKE DA TAKOBI yana kallon gabas da yamma,kudu da arewa saboda zargin ko tana tare da dakarun sarki a bayanta.Yayin da Lasmin ta iso dag da Jarumi Hibairu sai ta bude hannayenta da nufin ta rungume shi,Hibairu yaja da baya yana mai kauce mata ta rungumi iska sannan ya dubeta cikin alamun rashin yadda yace saboda me kika biyoni izuwa cikin wannan daji?Koda jin wannan tambaya sai Lasmin ta dubi Hibairu cikin mamaki tace saboda me zakayi min wannan tambaya alhalin kasan amsarta.A takaice dai inason na karbi addininka kuma bani da wata hanya da zan iya karbar tasa face nazo wajenka.Hibairu ya gyada kai cikin alamun rashin yarda yace yanzu ta yaya kike ganin zan aminta dake na gamsu da cewar zakiyi watsi da mahaifinki ki zabe ni,shin yanzu zaki iyayi mini rantsuwa da girman iyayenki cewa ba hada baki akayi dake ba domin a cutar dani?Koda jin wannan batu sai gimbiya Lasmin tayi murmushi tace na rantse da darajar uwata da ubana bazan taba yarda a hada baki dani ba a cutar dakai,ina mai tabbatar maka da cewa ni kadai na shigo cikin dajin nan kuma ba tare da kowa yasan fitowa ta ba,to amma babu mamaki daga baya a gane cewa na gudo a turo dakaru su biyo sawuna.Ina mai shawartarka damu gaggauta barin nan kan hanya tunda komai zai iya faruwa kuma a ko yaushe.Koda jin wannan batu sai Jarumi Hibairu yayi shiru yana tunani da nazari a lokacin da ransa ya baci ya dubi Lasmin a fusace yace zuwanki gareni yanzu bazai haifar mini da komai ba face dakushewar dukkan shirina na ganin na sami nasarar yada addinina a cikin kasarku amma kuma zai iya zama alheri akan hakan,kibar dokinki anan ki biyoni a baya muje inda zamu cigaba da tattaunawa a cikin nutsuwa.Koda gama fadin hakan sai Jarumi Hibairu ya juya ya nufi cikin wani surkuki mai duhuwa wata hanya ce wacce kamar bata bullewa,ba tare da fargabar komai ba kuwa Gimbiya Lasmin tabi bayan Jarumi Hibairu da sauri suka kutsa izuwa cikin wannan surkuki suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa a wajen ba.Lasmin ta cigaba da bin Hibairu a baya suna ta keta kwazazzabai da duhuwoyi har tsawon dan lokaci,kwatsam sai ta hango wani wawakeken rami a gabansu mai tsananin fadi gami da zurfi.Acan gabansu kuma wani katon KOGON DUTSE ne saboda tsananin zurfin wannan ramin idan mutum ya leka kasansa bai isa ya iya hango karshensa ba.Koda Lasmin tayi arba da wannan rami da kuma kogon dutsen saita firgita ainun kuma ta kamu da tsananin mamaki,ba komai ne ya firgitata ba kuma ya bata mamaki ba face ta taba jin labarin wannan rami da wannan kogon dutse a wajen mahaifinta sarki Zaldasi inda ya sanar da itace cewa fiye da shekaru sittin baya babu wani mahaluki daya isa yazo kusa da wannan rami ko kogon dutsen walau MUTUM KO ALJAN,dabba ko tsuntsu face ya zamana gawa.Nan take manyan bokaye na nahiyar sun tabbatar da cewa wani gagarumin Sihiri ne a wajen wanda aka kasa gano yanayinsa da asalinsa,wasu daga cikin bokayen sunce aishi wannan kogon dutse asalinsa gida ne na wani mashahurin boka don haka kafin ya mutu ne ya sihirce wajen saboda wata dukiya mai tsananin yawa daya boye.Abinda yafi daurewa gimbiya Lasmin kai shine yaya akayi Hibairu yazo wannan wuri wanda ya gagari kowa tsawon shekaru sittin dasu ka gabata?Da isowar Hibairu da Lasmin bakin wannan katon rami sai jikin Lasmin ya kama karkarwa saboda tsananin tsoro,koda ganin haka sai Jarumi Hibairu ya dubeta cikin murmushi yace kwantar da hankalinki ya gimbiya idan har zuciyarki tayi imani da ubangijina to kisa aranki cewa babu abinda zai sameki abinda nake so dake kawai shine ki rintse idanuwanki.Ba tare da wata fargabar komai ba sai Lasmin ta rufe idanuwanta faruwar hakan keda wuya sai Jarumi Hibairu ya kama gefen cunar rigarta ya rike sannan ya karanta wata addu'a ta musamman nanfa Allah ya nuna ikon nasa domin Hibairu na gama karanta addu'ar sai suka bace bat daga inda suke basu baiyana a ko ina ba sai bakin wannan kogon dutse.Koda Gimbiya Lasmin ta bude idanuwanta ta gansu tsaye a bakin kofar shiga wannan kogon dutse sai gaba dayan tsigar jikinta ta tashi saboda tsananin mamaki,nan take taji son Allah da tsoronsa sun kara kwarara a cikin zuciyarta don haka bata san sa'adda ta kurawa Hibairu idanu ba Tana Murmushi tace tabbas tsarki ya tabbata ga ubangijin Musulunci lallai inason ka gaggauta shigar dani cikin wannan addinin naka mai daraja.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya mamaye jarumi Hibairu yace kwantar da hankalinki yake gimbiya yanzu dai mu fara shiga cikin wannan gida mu zauna domin mu tattauna cikin nutsuwa sannan na shigar dake cikin addinin nawa.Koda gama fadin hakan sai Hibairu ya kunna kai izuwa cikin wannan tsohon kogon dutse mai dimbin tarihi gami da matukar kwarjini da ban tsoro.Da shigowarsu cikin farkon kogon sai gimbiya Lasmin ta kamu da tsananin mamaki domin ta tsinci kanta ne a cikin wani tafkeken gida wanda aka gina shi da zallan dutsen zinare kuma aka kawata shi da kayan alatu na lu'u lu'u.Kai da ganin wannan gida kasan cewa an shirya aljannar duniya.Babban abinda yafi daurewa Gimbiya Lasmin kai shine duk da cewa fiye da shekaru dari da daya babu wani mahaluki daya kara shigowa gidan amma ko ina fes fes yake babu inda mutum zaiga koda digon kura.Dakarun yaki kuwa na Aljanu gami da borori da kuyangi duka na aljanu gasunan a ko ina cikin gidan amma dukkaninsu sun kame sun zama gumaka tamkar ruhi bai taba shiga shiga cikin gangar jikinsu ba,Duk da cewa Gimbiya Lasmin na biye da Jarumi Hibairu a baya daf da daf saida jikinta ya kama tsuma saboda tsananin razanar da tayi bisa ganin siffofin Aljanun dake cikin wannan gida domin bata san sa'adda tayi wuf ya kamo hannun Hibairu ba ta damkeshi da kyau.Koda Hibairu ya fahimci cewa lallai a tsorace take ainun saiya juyo ya dubeta cikin murmushi yace kwantar da hankalinki Gimbiya Muddin kina tare dani babu wata halitta data isa ta matso a cikin gidan nan har ta iya cutar dake ko kuwa har yanzu baki gama yin imani bane da addinin nawa?Lokacin da gimbiya Lasmin taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace ko kadan bani da wani shakku a cikin zuciyata akan wannan addinin naka kuma na yarda dasi dari bisa dari.Haka dai Jarumi Hibairu da Lasmin suka cigaba da ratsa fadoji,harabobi da dakuna barkatai na cikin wannan gida har saida suka isa karshen gidan inda sukazo wani bangare wanda shine mafi kyau a gidan.Shidai wannan bangare shine asalin turakar bokan daya kirkiri gidan,a cikin wani babban falo kasaitacce suka tsinci kansu wanda aka zuba masa wadansu irin manyan kujeru na alfarma masu taushin gaske,ga yayan itatuwa wato kayan marmari na lambu gasu nan birjik bisa farantai nunannu kala kala tamkar a sannan aka tsinkosu daga cikin itatuwansu.Al'amarin da yayi matukar daurewa Gimbiya Lasmin kai kenan ta sake razana har tsigar jikinta gaba daya ta tashi jikinta gaba daya ya dume da wani irin mugun sanyi mai tabbatar da tsoronta.Koda jarumi Hibairu yaji hannu Lasmin ya dume da mugun sanyi nan take kuma ya cigaba da karkarwa saiya juyo gareta da sauri ya ruke hannayenta biyu yace maza ki maimaita abinda zan fada yanzu.Nan yake Hibairu ya karanta kalmar shahada koda Lasmin ta biya Kalmar sai taji wata irin nutsuwa ta shigeta kuma take dukkanin tsoronta ya yaye tamkar bata taba yinsa ba,saida Hibairu ya fahimci hakan sai shima ya kamu da farin ciki kuma yai sauri ya saki hannayenta a lokacin da suka zauna a kan wata doguwar kujera tare suka kallo junansu cikin MURMUSHI.A sannan ne Hibairu ya kawo gwauron numfashi ya ajiye yace yake gimbiya yanzu kin zama cikakkiyar yar uwata musulma don haka babu wani abu mai rai daya isa ya sake tsorataki a cikin wannan gida.Ki sani cewa a farkon shigowata cikin wannan gida duk aljanun nan da kika gani a kame kamar gumaka da ruhi a jikinsu kuma nasha gumurzun yaki dasu bisa dole sukayi MUBAYA'A a gareni don su tsira da rayukansu kuma shugabansu ya tabbatar mini da cewa nine bil'adama na farko daya shigo gidan bayan mutuwar ubangidansu da tsawon shekaru dari da sittin da uku,dukkanin wadannan aljanu sun tuba kuma sun karbi addinin musulunci,nine na umarce su dasu kame su zama kamar gumaka don kada ki firgice bisa ganin su a raye suna kai kawo dayin hidimarsu ta wannan gida da sula saba yi tsawon shekaru.Yanzu tunda kin zama yar uwarsu musulma ba zaki tsorata dasu ba.Kafin Hibairu ya gama rufe bakinsa tuni wadansu kyawawan kuyangi na Aljanu su uku sun shigo cikin wannan babban falo a cikin shiga ta kamala bata tsiraici ba dauke da tambula na ruwan inibi gami da abinci na alfarma irin na bil'adama sun ajiye a gaban gimbiya Lasmin kuma suka zube kasa suka gaisheta sannan suka mike suka fice daga cikin falon suka barsu su biyu rak.Nan take Hibairu ya dauki cokali da faranti ya zubawa kansa abincin sannan ya dubi Lasmin yace da ita kema ki zubawa kanki abincin nan kici cikin salama na gaya miki babu abinda zai cutar dake.Koda gama fadin hakan sai Hibairu ya juyawa Lasmin baya saboda kunya yayi bismillah a fili ya kama cin abinsa.Da ganin haka sai itama Lasmin ta zubawa kanta abincin ta kama ci bayan tayi bismillah kamar yadda taji yayi,haka dai suka cigaba da cin abincin har saida suka koshi.Ai kuwa suna kammalawa saiga wadansu sababbin kuyangi guda uku sun shigo,nan take kuyangin suka dauke kwanukan da suka ci abincin suka fice,fitarsu keda wuya sai ga wani narkeken Aljani mai surar SADAUKAI a cikin gagarumar SHIGAR YAKI ya shigo cikin falon.Daga nesa dasu kimanin tazarar taku ashirin sai wannan Aljani ya zube kasa bisa guiwarsa guda kansa a sunkuye a kas saboda biyayye ya bude baki yace ya shugabana muna da baki a kofar gidan nan.Koda jin wannan batu sai Jarumi Hibairu yayi murmushi yace su waye? Aljanin ya sake risinawa yace ai ba wasu bane face Sarkin Yakin Sarki Zaldasi tare da wadansu dakaru su dari kacal,tabbas sarki ne ya turo su suyi farautar Gimbiya su mayar da ita gida.Dukkaninsu sunyi cirko cirko a kofar gidan nan sun kasa koda motsawa gaba da taku daya saboda TSORO.Lokacin da Aljanin yazo nan a jawabinsa sai Hibairu ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan ya dubeshi yace yakai Zulfanu kaje ka baiyana kawai a gabansu kayi shiru kada kace dasu kala duk abinda kaga ya faru ka dawo ka sanar dani.Dajin wannan umarni sai Zulfanu ya risina yace an gama ya shuganana,nan take Zulfanu ya bace bat daga cikin falon tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen Ba. *A can Kofar kogon dutsen kuwa sarkin yakin Sarki Zaldasi tare da dakarunsa mutum dari ne a tsaye cirko cirko bisa dawakai suna kallon kogon kawai,bawai su dakarun ba hatta dawakansu ma kyarma sukeyi saboda tsoron wannan kogon dutse.Tun sa'dda suka iso bakin katoton ramin dake gaban kogon dutsen suka firgita ainun su da dawakan nasu har sun zabura zasu kada dawakan nasu su juya da baya sai shugabansu wato sarkin yaki ya daka musu tsawa yace shin baku da hankali ne?To kusani cewa gabanmu tsini ne baya kuma siyaki,idan muka koma gida babu gimbiya Lasmin gaba dayanmu sai sarki Zaldasi ya kashe mu saboda bamu da wata hujja wacce zamu iya nunawa ta ceci rayukanmu bisa cewar munyi iya kokarinmu wajen samo gimbiya.Kowanne nku yaga sawayen gimbiya dana bakon Jarumi Hibairu har.••••••••• SA MAZA GUDU!!! Littafi Na Bakwai (7) Part D. KOWANNAN KU YAGA SAWAYEN GIMBIYA DANA BAKON JARUMI HIBAIRU HAR ZUWA BAKIN WANNAN KATON RAMI KO SHAKKA BABU SUNA NAN CIKIN WANNAN KOGON DUTSE,ina mai tabbatar muku da cewa zan iya tsallakar damu wannan katon ramin da karfin sihirin tsafina amma fa bani da tabbacin kare dayanku daga sharrin wannan kogon dutse.Lallai ku sani cewa bamu da wani zabi wanda yafi mu shiga cikin wannan kogon dutse.Koda sarkin yaki yazo nan a jawabinsa sai gaba dayan dakarun su dari suka firgita ainun,cikin kowa ya duri ruwa suka rasa abinda zasuyi.Kawai sai wani zakwakurin Barde daga cikinsu abin kwatance ya dubi Sarkin Yaki a fusace batare da wata fargaba ba yace kai sarkin yaki ka tuna cewa fiye da shekaru dari babu wani mahaluki daya jarraba shiga cikin wannan kogon dutse hatta sarki Zaldasi da kansu kuwa,sai wannan shaidanin bakon jarumi Wato Hibairu,kai ka sani cewa shigarmu cikin wannan kogon dutse daidai yake da siyar da rayukanmu.Kada ka manta cewa da yawanmu nan muna da yaya,mata da iyaye,kuma ko wasiya bamu bar musu ba muka fito wannan aiki.Shin kanaso ne mu mutu a banza a wofi kenan kuma mu bar bayanmu a cikin maraici,talauci gami da shan wahalar rayuwa,zaifi kyau mu koma ga sarki mu gaya masa cewa Hibairu da Gimbiya sun shiga cikin wannan kogon dutse kuma mun kasa shigarsa.Kaga kenan idan shi yana ganin zai iya shiga sai yazo ya jarraba.Koda wannan Barde yazo nan a zancensa sai gaba dayan sauran yan uwansa dakaru suka kama shewa suna masu cewa sun amince da wannan sharawa daya kawo,shi kuwa sarkin yaki da farko jikinsa ne yayi sanyi don haka sai yayi shiru yana tunani da nazari daga can sai ya daka musu tsawa ya dubi badakaren yace baka da hankali ashe ka manta da halin sarki kenan,to ka sani cewa idan mukaje masa da wannan labari cewa mun kasa shiga kogon dutse nan ko dai yasa a kashe mu ko kuma a yanke mana hukuncin daurin rai da rai.Shin yanzmu zamu gudu ne mubar iyalanmu saboda TSORON MUTUWA?Mafitar mu kawai itace muyi iya kokarin mu koda kuwa wasunmu zasu hallaka sauran su koma da raunika,yanzu inason kowa ya rufe idanunsa domin mu tsallake wannan rami wanda duk yayi yunkurin gudu daga cikinku ni da kaina zan kure masa gudu na kashe shi.Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki ya runtse idanunsa kuma ya bayar da umarnin kowa ma ya rufe idonsa,ba tare da gardamar komai ba kuwa gaba dayan dakarun suka rintse idanuwansu.Faruwar hakan keda wuya sai wata irin guguwa mai karfin gaske ta zagayesu kura ta turnuke wajen gaba daya dajin yayi bakin kirin yadda ko tafin hannu mutum bazai iya gani ba.Daga nan kuma sai kurar da duhun suka dauke dif tamkar daukewar ruwan sama.Koda kowa ya bude idanunsa sai suka tsici kansu da dawakansu a tsallaken wannan katon ramin tamkar mutum ne yasa yatsunsa guda biyu ya kwashe su su duka ya tsallakar dasu gefan ramin.Nanfa su duka suka cika da dumbin mamaki gami da farin ciki basu san sa'adda suka kamayin murmushi da dariyar murna ba,amma kuma sai nan take fuskokinsu suka juye izuwa tsananin tsoro,jikinsu ya kama karkarwa tamkar an tsomasu a cikin kogin kankara.Ba komai bane ya haddasa hakan face ganin Aljani Zulfanu ya baiyana tsulum a gabansu.Hannayen Zulfanu na makale cikin hammatarsa,ga tarin MAKAMAN YAKI a jikinsa sama da kala dari kuma fuskarsa a murtuke take wacce saboda tsananin muninta da kwarjininta saida gaba dayan dakarun dari suka rinka sakin fitsari a cikin wando batare dasun hakan na faruwa ba.Sarkin yaki ne kadai bai saki fitsarin ba kuma shine kadai ya iya hada idanu da Aljani Zulfanu suka kama kallon juna cikin harara.Tsawon yan dakiku kadan suna yin wannan kallon kallo sai sarkin yaki ya zare takobinsa ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa.Tabbas inda a filin yaki ne ya kurma wannan ihu da komai yawan abokan gabansa sai sun zube kasa a firgice kuma a nakashe.Kafin sarkin yaki ya gama kwarara wannan ihu sai akaji muryarsa ta shake nan take kuma ya kame kyam kamar gunki.Koda da dakarun suka dago da kawunansu suka dubseshi sai sukaga bakinsa ya karkace rabin jikinsa kuwa bangaren dama ya shagube ya shanye ko motsashi baya iyawa.Koda ganin abinda ya sami sarkin yaki sai dakarun dari suka sake dimauce ainun fiye da karon farko basu san sa'adda suka cure gaba dayansu a waje guda ba.Da kyar sarkin yaki ya wurkila idonsa na hagu bangaren da bai shanye ba Kenan.Nan take wannan guguwa mai karfi ta sake baiyanaa ta daukesu duka ta tsallakar dasu wannan katon ramin a sannan ne hankalinsu ya dawo jikinsu.Sarkin yaki ya dubi dakarun nasa da kyar cikin karfin hali ya bude karkataccen bakinsa yace to yanzu ne zamu iya komawa ga sarki tunda mun sami shaidar da zamu iya kare kanmu.Yana gama fadin hakan sai hawayen bakin ciki ya subuto daga cikin idanuwansa yace ni kam shike nan a haka zan karasa sauran rayuwata,na gama zama nakasasshe,babu wani magani ko sihiri da zai iya warkar dani.Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun suka kamu da tsananin tausayinsa nan dai wasunsu suka kama tayashi kuka,Batare da bata lokaci ba suka juyar da dawakansu suka nufi hanyar da zata mayar dasu izuwa cikin birnin Misra. *A can cikin wannan gida na kogon dutse kuwa bayan jarumi Hibairu ya sallami Aljani Zulfanu ya fita ya barshi da gimbiya Lasmin sai Hibairu ya dubeta yace yake Gimbiya kiyi sani cewa ban gudu daga cikin birninku ba don tsoro ba,sai domin na tsayar da salwantar da rayukan dakarun mahaifinki,burina shine jama'arku gaba daya su gane gaskiya kuma su karbeta bawai nayi ta zubar da jininsu ba,kuma guduwata izuwa nan zaisa zuciyoyin jama'arku su karaya su karaya bada gaskiya da addinin Gaskiya.Kowa ya gani da idanunsa cewa nine na lashe gasar Jarumtaka da mahaifinki ya shirya,amma saboda son zuciya irin na mahaifinki gami da kiyayyarsa akan addinina saiya take gaskiyar yace a kamani a kaini kurkuku yanzu gashi an kasa kamani na tsere musu kuma gashi ya turo dakaru su kamani sun kasa,shin kinsan me zai biyo baya idan sarkin yakinsa da dakarunsa daya turo suka koma gareshi babu ni babu ke?Koda jin wannan tambaya sai gimbiya Lasmin ta girgiza kai alamar cewa bata sani ba.Kafin na bude baki na bata amsa saiga Aljani Zulfani ya sake baiyana tsulum a gabanmu yana mai yimana alamar sallama gami da durkusawa a gaba na Kansa na sunkye cikin biyayya saiyace Ya shugaban dakarun sarki Zaldasi sun firgita ainun da gani na kuma koda sarkin yakinsu ya zare takobinsa da nufin yayi yaki dani sai na shafeshi kadan,take rabin jikinsa ya shanye da kyar ya iyayin tsafi suka gudu daga bakin kofar gidan nan.Koda jin wannan labari sai Farin ciki ya turnuke jarumi Hibairu ya dubi Aljani Zulfanu yace da kyau aikinka yayi,zamu sake zubo ido daga nan zuwa kwanaki biyu muga abinda zai biyo baya.Tashi ka tafi na sallameka.Kafin Hibairu ya gama rufe bakinsa tuni Aljani Zulfanu ya bace bat.Hibairu ya duni Gimbiya Lasmin cikin murmushi yace kiyi amfani da wannan dama ta kwanaki biyu ki koyi yadda akeyin bautar Allah.Koda gama fadin uakan sai Hibairu ya mike tsaye kuma ya tafa hannayensa faruwar hakan keda wuya saiga shugabar kuyangin gidan ta baiyana,wata kyakkyawar sankaceciyar budurwa a cikin wata doguwar farar riga,shugabar kuyangin ta risina a gaban Hibairu ta kwashi gaisuwa shi kuma saiya dubeta yace Ga Gimbiya nan a kaita masaukinta kuma ki koyar da ita yadda akeyin wankan tsarki,alwala da sallah kuma ki koya mata fatiha da falaki da nasi.Koda jin haka sai shugabar kuyangin ta sake risinawa ga Hibairu tace an gama ya shugabana,kawai sai ta kama hannunta da nufin ta janyeta ta tafi amma sai Gimbiya Lasmin ta noke ta dubi Hibairu cikin alamun matukar damuwa tace ta yaya wadanda ayau dinnan suka koya daga gareka zakace su koyar dani?Ka sani fa cewa nifa mutum ce kamarka su kuwa jinsi ne dabam nifa har yanzu tsoronsu nakeji kuma ban saba dasu ba.Koda jin haka sai Jarumi Hibairu yayi dariya sannan yace kamar yadda kike ganin cewa baki saba dasu ba aini ma yaune ranar farkon haduwata dasu to amma saboda karfin imani na da ubangijina sai nake jin kamar dama can sun kasance yan uwana na jini tunda sun karbi addinina,kiyi kokari ki sami irin wannan imani dana samu a cikin zuciyarki.Idan kikayi haka zaki daina jin komai a ranki dangane dasu,kuma ina mai tabbatar miki da cewa babu dayansu dazaiyi yunkurin cutar dake domin suna matukar kaunarki fiye da yadda suke son kansu saboda tuni su imaninsu ya tabbata ga ubangijin musulunci ba zasu taba cutar da dan uwansu musulmi ba.Koda jin wannan batu sai nan take gimbiya Lasmin taji kishi ya shigeta bisa jin cewa wadannan Aljanu sun fita karfin imani.Nan take ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace yanzu ta yaya kenan nima zan iya karfafa nawa imanin yafi nasu?Kafin ta iya baiwa kanta amsa tuni an janyeta an tafi da ita izuwa masaukin nata.Tafiyarsu keda wuya sai Hibairu ya mike tsaye yaje yayi alwala sannan ya jagoranci gaba dayan aljanun dake cikin wannan gida yayi musu sallar magriba a matsayin limaminsu.Tun kafin a gabatar da wannan sallah sautin murya na kiran sallar da akayi ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa kuma iska ta dauki zazzakar muryar datayi kiran sallar ta kaita har cikin birnin Misra.Koda jama'ar birnin misra suka jiyo wannan sauti wanda basu taba ji ba a rayuwarsu kuma sukaji yadda ake ambaton Allah da manzonsa a cikin kiran Sallar daga can cikin kuryar daji sai tsigar jikin kowa ta tashi suka fara jin cewa lallai akwai alamun cewa wannan addinin shine addinin gaskiya.Adaidai lokacin da sautin muryar kiran sallar ta doki kunnen sarki Zaldasi yana kwance ne akan doguwar kujera ta turakarsa don haka saiya mike zaune zumbur a firgice yayin da zuciyarsa ta kama dukan uku uku,dama kawai a kishingide yake kawai cikin tsananin bakin ciki kuma zuciyarsa na tafarfasa kamar zata kone bisa takaici da tunanin yadda al'amara suka sauya farat daya a cikin birninsa na gargajiya wanda suka gada tun iyaye da kakanni.A fusace sarki Zaldasi ya zare takobinsa saboda shi a tsammaninsa Jarumi Hibairu ne ya shigo cikin birnin yana karanta wannan kiran sallah.Koda ya fito daga cikin turakar tasa ya iso cikin harabar gidan sarautar sai yaga dakaru da hadiman gidan sun bishi da kallo cikin mamaki don haka saiya nutsu ya dubi wani babban hadimi nasa yace me ake ciki ne shin sarkin yaki bai dawo bane daga aikin dana tura shi?Saboda me kabar wannan shaidanin

Chapter 15 of 19