Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT SA MAZA GUDU Littafi na biyu(2) Part A A tare suka waigo baya suka duba,sai suka ashe Lasurat ce mahaifiyar Malika.Ta tunkaro su fuskarta cike da alamun damuwa.Koda ganinta sai sarki ya mike tsaye ya taryeta yana mai rike hannayenta a lokacin da ta kurawa hannun Malika idanu.Sarki yace kwantar da hankali yake Ummul Malika,kiyi sani cewa raunin da Malika taji Karami ne kuma da wuri zata warke.Koda jin wannan batu,sai murmushi ya kubucewa Lasurat tayi doguwar ajiyar numfashi tace,to nagode da abinda ya tsaya iya haka amma yaya akayi ta sami wannan raunin alhalin nasan cewa duk inda zata je kana bata tsaro mai kyau na dakaru?Sarki Sharkuf ya numfasa yace,ni kaina nayi mamaki yadda al'amarin ya faru,amma hakan bazata sake faruwa ba.Yanzu ki tafi da ita izuwa turakarki ki lallabata ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali domin akwai alamun cewa tana cikin damuwa. Batare da wata gardama ba Lasurat ta kama hannun Gimbiya Malika tajata suka nausa izuwa can cikin gidan sarautar.Shi kuwa Sarki Sharkuf sai ya bita da kallo cikin alamun tsananin damuwa gami da tunani mai zurfi.Na take idanunsa suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa saboda tausayin da ya kama shi.Ba komai ne ya sanya masa wannan tausayi ba face a binciken da yayi a hallarar tsafinsa ya gano cewa bayan mutuwarsa sai wannan 'ya da uwa sun rabu sakamakon wata kaddara wacce basu isa su guje mata ba.Tunda farkon Yammaci Gimbiya Malika ta caba ado tayi shirin tafiya izuwa wannan Gida na Yarima Lahaman.Bayan ta hama shiri tsaf,sai hankalinta ya DUGUNZUMA bisa dalilai biyu,dalili na farko shine bata san yaya taza sulale ta fice daga gidan sarautar ba tare da wani ya ganta ba.Dalili na biyu kuma bata san ko nawa Yarima Lahaman zai siyar mata da wannan bawan nasa ba Wanda taji ta kamu da tsananin sonsa farat daya.Duk da tasan cewa komai tsadar bawan zata iya sayensa,amma tayaya zata iya fitar da kudade masu yawa daga gidan sarautar batare da sarki ya gane dukkan shirinta ba?Idan tace kogon ta na dukiya zataje ta debo kudin tafiyar mai tsawon gaske ce,ba zai yiyu ba.Bisa wannan dalili ne yasa Gimbiya Malika ta kama zarya a cikin babban falo na turakarta ta kasa zaune ko tsaye.Kuma Hankalinta ya DUGUNZUMA,taji kamar ta fashe da kuka saboda bata da wani buri da kuma 'doki wanda yafi taje ta gana da wancan bakon bawa ko don ma ta sake ganin fuskarsa,Zuciya rta ta huta da tsananin begensa da tunaninsa.Malika na cikin wannan hali ne Shugabar kuyanginta wata mace yar kimanin shekara arba'in da daya mai suna Lasmira ta shigo cikin falon tare da wadansu kuyanci guda uku,domin su gabatar da irin aiyukan da suka sabayi kullum.Koda Lasmira taga gimbiya a tsaye tana kaii kawo cikin alamun damuwa,sai ta sallami wadannan kuyangi guda uku dake tare da ita,suka juya da baya suka fice daga cikin falon.Lasmira ta karasa gaban Malika ta dubeta tace,Ya shugabata menene ya dameki haka harzaki kasa zama ko tsayuwa?Koda jin wannan tambayar,sai Malika ta koma kan kujera ta zauna tayi shiru kamar baza tace komai ba,tana mai kurawa Lasmira idanu.Daga can sai tayi gyaran murya ta dubi Lasmira cikin nutsuwa tace,yake Lasmira kiyi sani cewa na yarda dake kuma nasan zaki iya rufe sirrina tunda tun ina yarinya karama kike aiki a karkashin Mahaifiya,kuma ban taba jinta tayi korafi akankin yi mata wani laifi ba,bisa wannan dalili yanzu zan sanar dake abinda ke damuna akan amana kuma ina son ki bani shawarar abinda zanyi na sami mafita.Nan take Gimbiya Malika ta zaiyanawa Lasmira duk bukatunta.Koda jin wannan bayanin nata,saiLasmirata kyalkyale ta dariya.Al'amarin daya bawa Malika haushi da mamaki kenan tace,mene kuma abin dariya a cikin wannan Al'amarin?Lasmira tace,ai gani nayi ga magani a gonar yaro amma bai sanshi ba,ai warware wannan matsala taki abu nemai sauki tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai.Abinda nake so dake kawai shine kibi duk irin umarnin dana baki,in kikayi haka dake da duk adadin kudin da kike bukata zaku isa kofar gidan Yarima na can bayan gari a asirrance kuma zaki dawo a asirrance batare da kowa ya sani ba.Ko jin wannan batu,sai farincik ya lullube Malika ta dubi Lasmira cikin zumudi tace,Fadi duk irin abida kike so nayi.Lasmira tayi murmushi tace,yanzu dai da farko ina son ki bani Dinare dubu goma kacal wanda zanje na aiwatar da wadansu ayyuka a cikin gidan nan dasu,zan dawo nan da kafin cikar rabin sa"a.Batare da gardamar komai ba kuwa sai Malika ta shiga cikin kuryar turakarta ta debo dinare dubu goma a cikin jakar kudi ta mikawa Lasmira.Lasmira na karbar wannan kudi sai ta boyesu acikin rigarta sannan ta juya ta fice daga cikin turarkar.Lasmira bata zame ko ina ba sai can kofar dakin shugaban dakarun dake tsaron gidan sarautar,wani barden jarumi wanda ake kira da suna Mahutur bin Kauzif.Da isarta sai ta kwankwasa kofar dakin sau biyu kacal,faruwar hakan ke da wuya sai Muhutur yayi magana daga ciki yace,to Lasmira shugabar yan cuwacuwar gidan nan yau kuma dame aka zo mini don nasan cewa unguwa bata jewar banza.Lasmira tace ai sai ka fito waje kaji abinda nazo dashi.Muhutur yace ai zaifi kyau ki shigo daga ciki komai zaifi sirri.Idan kuma matarka tazo ta ganmu fa sai ta zata amanarta zanci kuma ka sani cewa kawata ce ko?Haka ne to bari na kimtsa gani nan fitowa.Jin kadan saiga Muhutur ya fito yana goge bakinsa ga dukkan alamun abinci ya gama ci.Maimakon Lasmira ta bude baki tace wani abu,sai ta dauko kudin Dinare dubu uku ta mika masa.Cikin kaduwa da Mamaki Muhutur ya karbi kudin yana mai jinjina su akan tafin hannunsa,sannan yayi waige waige da dube dube yai sauri ya Soka kudin a cikin aljihun wandonsa ya dubeta yace,wannan kuma fa na menene?shin wani abu za'a siyowa Gimbiya a boye?Lasmira tace a'a itace da kanta take son ta fita daga cikin gidan sarautar nan tare da dukiya mai yawa saboda taje ta siyo wani bawa a can gidan Yarima dake bayan gari,kuma komai ana sin ayi shine a asirrance ba tare da sarki ya sani ba. Koda Lasmira tazo nan a zancenta,sai hankalin Badakare Muhutur ya DUGUNZUMA ainun ya rasa abinda ke masa dadi domin yasan cewa hadarin dake cikin wannan aikiyana da yawa saboda ko yaya aka sami akasi ya rasa aikinsa kenan .Don haka sai ya murtuke fuskarsa kuma ya murza gashin bakinsa yace,kai ungo kudinki bazan yi wannan aiki ba,hadarin dake cikinsa yafi abinda kika bani.Koda jin haka,sai Lasmira ta sake saka hannunta cikin aljihunta ta dauko wani damin kudin Dinare dubu uku ta wurga masa tace,ga wadansu dinare dubu ukun kaga ke nan inka hada dana farko sun zama dinare dubu shida daidai albashinka na shekara biyu kenan,shin ka amince yanzu zakayi wannan aiki?Koda jin wannan tambaya,sai jikin Muhutur ya kama kyarma ya rasa hukuncin da zai yankewa kansa,saida yayi duru duru yayi gaba yayi baya sannan ya juyo ya fuskanci Lasmira yace,to ina kudin dakarun dake aiki a yau?kinsan cewa suma sai na raba musu wani abun sannan zasu ki duba duk abinda za'a wuce dashi.Koda jin haka sai Lasmira ta zura hannu cikin aljihun rigarta ta dauko wani kullin kudi na dinare dubu ta mikawa Muhutur tace,wannan dinare dubu ne nasan ya isa ka raba musu,wane lokaci za'a fito da Gimbiya da dukiyarta?Muhutur yayi shiru yana tunani sannan yace,ai yau talata ce kuma duk ranar talata da yammaci ne sakalaiya Sarki ke kwanciya domin ya huta ba zai sake fitowa waje ba sai gobe da safe don haka a daidai wannan lokaci za'a fito da Gimbiya.Lasmira tayi murmushin farin ciki ta juya da baya da gudu taje ta sanar da Gimbiya Malika duk abinda ya faru tsakaninta da shugaban dakaru Muhutur.Sannan sai ta dauko wani shudin magani a cikin wata yar karamar kwalba ta mikawa Malika tace,ungo wannan kisha makurwa biyu kacal,batare da gardamar komai ba ko tsoron wani abu sai kawai Malika ta karbi ruwan maganin ta cire murfin kwalbar tasa a bakinta tasha makurwa biyun kamar yadda aka umarce ta.Bayan kamar dakika ashirin da faruwar hakan sai Malika ta fara jin jiri,ta kama tangadi daga tsaya sannan ta tafi luu.. zata fadi,amma sai Lasmira ta tafa hannunta sau uku,saiga wadansu hadiman gidan su Gimbiya Malikan guda uku karti sun shigo,dayansu dauke da wata doguwar akwatin katako.Da zuwansu sai suka ajiye akwatin suka bude shi saiga matattun beraye,kyankyasai da sauran kananan kwari masu addabar mutane a gidan.Kawai sai suka daga abinda ke dauke da wadannan kwari daga cikin akwatin sai ga katon fiki a kasan akwatin aka saka gimbiya Malika a ciki sannan suka dauko katakon dake dauke da matattun kwarin suka dora a saman Gimbiya Malika ya zauna darama.Komai kallon kurilla,mutum bai isa ya iya ganewa cewa akwai wani abu a kasan akwatin,saidai ayi tunanin cewa akwatin cike take da wadannan kwari babu komai a kasanta.Bayan an rufe Malika a cikin wannan akwati sai kuma wannan hadimai uku suka shiga can cikin kuryar turakar gimbiya suka rinka fito sa irin akwatunan har guda arba'in,ashe kowacce a kasanta lu'u lu'u aka zuba dunkim a samanta kuma aka zuba matattun kwarin.Akwatuna guda arba'in da daya aka loda su a kan keken shanu aka tunkari kofar fita daga cikin gidan sarautar.Saida aka wuce ta cikin kofofi tara,kuma duk kofar da akazo ko tsayar da keken shanun ba'ayi,da an hango su daga nesa sai a bude musu kofa tun kafin ma su iso.Saida kawai su wuce.Haka dai direban keken shanun ya cigaba da wucewa har ya iso kofar karshe,har masu gadin sun janyo kofar sun bude masa zai fita kenan,sai sukaji an daka mus tsawa,a firgice direban keken shanun tare da dukkan masu gadin kofar kimanin su dari suka waiga suka duba inda sautun tsawar ya fito saboda sun dauki murya.Ba muryar wani bace face ta sarki Sharkuf yana tahowa daga cikin gidan sarautar bangaren da turakarsa take.Sarki Sharkuf ya kara so garesu fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri,ya dubi direban keken shanun ya sake daka masa tsawa a karo na biyu yace,ya kai Zarhus yau kuma wace irin sharace za'a fitar da ita da wannan yammaci sakaliya haka?Koda jin wannan tambaya,sai jikin Zarhus ya kama tsuma ya sauko daga kan keken shanun ya zube a kasa gaba Sarki tamkar zai masa sujjada,sannan ya bude baki cikin rawar murya yace,Ya shugabana sharace ta matattun kwari kuma tayi yawa ne shi yasa kafin mu gama kwasheta lokacin ya kure mana.Koda jin wannan batu,sai Sarki Sharkuf ya sake bata rai yace,ban yarda ba a bude akwatunan gaba dayansu na gani.Dajin haka sai dakaru suka rugo izuwa kan keken shanun suka kama bude akwatunan sarki Sharkuf yazo kan akwatin farko wacce a karkashinta ne Gimbiya Malika ke kwance tana fama sharar barci kamar gawa.Koda sarki Sharkuf yaga matattun beraye da kunamai da kyankyasai har sun fara doyi sai yayi sauri ya toshe hancinsa.Har ya yunkura zai duna cikin ta biyu sai ya dawo da baya ya daga kwagirinsa da nufin ya lumata cikin akwatin farko domin ya jiyo karshen zurfinta,kawai sai yaji an kwala masa kira,yana waigawa baya yaga ashe shugaban tsaro na gidan ne ya tawo da gudu yana sassarfa da tuntube kamar wanda zai fadi yana cewa,ka gafarceni ya shugabana nayi kusjure da baka riskeni ba anan bakin kofa.Koda jin wannan batu,sai sarki Sharkuf ya basa luma kwagirinsa a cikin akwatin ya juyo ya fuskanci Badakare Muhutur yana mai kyalkyala dariya yace haba yakai Muhuru ai bazaka tabayin laifi ba a wajena saboda yau shekara arba'in da biyar kenan kana aikinka na tabbatar da tsaro,ba'a taba kama da laifi ba,wata almundahana ko rashin gaskiya ba.Shin ka caje wadannan akwatunan guda arba'in da daya na shara ka tabbatar cewa sharace zalla a ciki ba'a boye wani abu ba?Muhutur ya gyada kai yace,na caje su gaba daya ya shugabana,babu wani abu a ciki sabanin wanda ka gani.Koda jin haka sai Sarki Sharkuf ya saki ransa,hankalinsa ya kwanta,ya kyalkyale da dariya sannan ya dafa kafadar Muhutur yace,na yarda dakai dari bisa dari nasan cewa ba zaka taba cin amana taba,kuma bazaka taba yarda ayi wani abu ba wanda zai cutar dani koya cutar da wani nawa.Koda gama fadin haka sai Sarki Sharkuf ya dubi Zarhus yace ko kayan laifi ka dauko a yaudai ka sha.Zarhus ya risina yayi godiya sannan ya sake hawa kan keken shanun ya saki linzami ya fice daga cikin gidan sarautar.Sarki Sharkuf ya bishi da kallo kawai a lokacin da Muhutur yaji idanunsa sun ciko da kwalla kamar ya fashe da kuka,saboda yasan cewa tabbas yasha cin amanar sarki ana shigowa gidan da abubuwan da basu dace ba ko kuma a fitar da wasu. Tafiyar rabin sa'a kacal direba Zarhus yayi ya iso kofar gidan yarima Lahaman dake bayan gari.Da isowarsa sai shugaban masu gadin gidan ya dubeshi ya daka masa tsawa yace,kai kuma wane irin wawa ne da zaka kawo shara nan gidan? Waye ya baka umarnin yin hakan?To kayi sauri ka bace daga nan tun kafin Yarima ya fito ya ganka yasa takobi ya sareka.Maimakon Zarhus yace wani abu sai kawai ya sauko daga kan keken shanun ya bude wannan akwatin ta farko.Yana budewa saiga Gimbiya Malika kwance a ciki tamkar gawa bayan ya dauke matattun kwarin dake samanta.Cikin kaduwa da mutukar firgici masu gadin gidan sukayi kamar su ruga izuwa cikin gidan amma sai suka fasa sakamakon ganin Malika zaune a cikin akwatin tamkar gawa ta faso kabari.Ashe dama can kuyanga Lasmira ta auna iya tsawon lokacin da Malika zatayi barcin kuma ta farka adaidai lokacin da Zarhus ya iso kofar gidan Yarima Lahaman.Shiyasa tace da ita tasha wannan maganin barcin makurwa biyu.Koda Malika ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin keken shanu,ga akwatuna arba'in a bayanta kuma gata a kofar gidan Yarima Lahaman,sai farin ciki ya lullubeta ta sako kasa daga kan keken shanun sannan ta dubi shugaban masu gadin ta daka masa tsawa tace zakaje ka gayawa ubangidan naka cewa gani na iso ko aa?Kodajin haka sai badakaren ya juya da sauri ya fada cikin gidan. Acan cikin gidan kuwa sarki Hilairu tare da ragowar jama'arsa bayi mutum dari na zaune sunyi jugum jugum suna tunanin halin da suka tsinci kansu ta rayuwar kunci,damuwa dakuma wahala.A yau dinma tun safe da aka basu abinci ba'a sake basu ba.Gashi har rana ta fadi magariba ta doso kal.Dukkanninsu jikinsu yayi sanyi lagwab tamkar jikakkun tsumokara musamman matan cikinsu wadanda dole ne mutum ya kamu da tausayinsu Idan ya kallesu saboda su masu rauni ne basu da juriya irinta maza. Kwatsam sai ga Yarima Lahaman ya shigo cikin dakin dakarunsa na take masa baya fuskarsa a murtuke babu alamar annuri.Kai tsaye Lahaman ya durfafi inda sarki Hilairu ke zaune ya dube shi yace,ya kai wannan sarki naga alama cewa kai mutum ne mai sa'a domin gashi ina shirin na siyar dakai gobe ga manyan attajiran da zan sami babbar riba,amma sai gashi 'yar uwata tazo yanzu domin ta siyeka.To ka sani cewa karkon kifi zakayi domin babu wani abu da ya taba shigowa hannuna kuma ya kubuta.Nayi maka alkawarin ko ka subuce mini yanzu nan,ba da dadewa ba saika dawo hannuna,kuma saina siyar dakai ga inda za'a tafi daku izuwa wani bangaren na duniya mai nisan gaske inda ko duriyarka ba za'a sake jiba.Koda gama fadin hakan,sai Yarima Lahaman ya fice daga cikin dakin tare da dakarunsa masu take masa baya suka nufi can wajen gidan.Gimbiya Malika na tsaye kusa da keken shanunta mai dauke da akwatunan kudi saiga yarima Lahaman ya fito daga cikin gidan.Koda yaga Malika a gaban keken shanu mai daukar akwatunan sharar gidan sarauta saiya bushe da dariya yace,yanzu yar sarki ce guda a cikin kekn daukan shara,to yanzu ina kudin da zaki siyi bawan?Koda jin wannan tambaya,sai Malika ta turbune fuskarta tace,a ina ka taba ganin anyi cinikin kifi a ruwa,muje ka nuna min abinda nazo siya na ganshi a raye cikin koshin lafiya sannan muyi cinikin ba biya.Koda jin haka,sai Yarima Lahaman yayi murmushi yace,Tabbas kina da wayo da dabara ki biyo ni a baya muje kiga muradinki.Yana gama fadin hakan sai ya juya ya shige cikin gidan.Kawai sai Malika ta dubi dakarun dake kofar gidan tace,ba baku ajiyar keken shanuna da direbansa,idan na fito na iske wani abu ya taba lafiyarsu abaka cin rayuwarku.Tana gama fadin hakan sai tabi bayan Yarima Lahaman da sauri har suka iso dakin dasu Sarki Hilairu ke ciki.Da zuwansu aka bude musu kofa suna shiga sai Sarki Hilairu da Gimbiya suka hada Idanu take yaji zuciyarsa ta buga da karfi karo na biyu na haduwarsu.Ita kuwa Malika ji tayi gaba dayan tsigar jikinta ta tashi kuma sai kwarjinin Hilairu da tsananin kyawun fuskarsa suka dimantata tayi sauri ta dauke mazansu da matansu.Take taji ta kamu da tsananin tausayinsu don haka sai ta dubi yarima Lahaman tace ciniki ya sauya salo yanzu ba mutum saya kadai nake so ka siyar min ba,gaba dayan bayin dake cikin dakinnan nake bukata.Koda jin wannan batu,sai yarima Lahaman ya bushe da dariyar keta yace,yaya ke da bakizo da kudin siyan mutum daya ba ma amma kike tunanin siyan mutum dari?Malika tace,ai sai ka bari mu gama cinikin tukunna idan kaga na kasa biyanka kudinka shine kake da bakin magana.Lahaman yayi gyaran Murya sannan yace,shidai wannan saurayi ma'abocin kyawu da kike son ki fansa sai kin biyani kudi dinare dubu dari biyar.Su kuwa ragowar yan'uwan nasa ko wane dayansu sai kin biya dinare dubu hamsin sannan zaki mallake su.Koda jin wannan batu,sai Gimbiya Malika ta dubu Yarima Lahaman cikin alamaun fishi da bakin ciki tace,haba yakai yarima ai ko ranar kasuwar garin nan ba'a taba siyar da bawan da darajarsa takai dinari dubu biyar ba amma kai yanzu gashi kace na siyi kowane daya akan farashin dubu hamsin.Shidai wanacan saurayin ma'abocin kyau da kwarjini na yarda na siye shi a farashin da ka fada,domin darajarsa ma tafi haka,amma ina neman sassauci akan ragowar bayin.Koda jin haka sai Yarima Lahaman ya turbune fuskarsa yace,ai ba neman kai nake yi ba dasu,idan ba zaki iya siyansu ba a wannan farashin saidai ki hakura gaba daya.kuma inda kina bukatarsu sai ki biya kudinsu yanzu take sannan ki kada ki tafi dasu.Malika tayi murmushi tace,kudi ba matsalata bane yadda zan kashe su shine matsalata.muje wajen keken shanun na biyaka kudinka duka,amma lallai kasa a kwance wadan nan bayi daga cikin sarkoki su biyo mu izuwa waye.Batare da wata gardamar komai ba,yarima Lahaman yasa dakarunsa suka kwance bayin daga cikin sarkoko aka tusa keyarsu izuwa wajen gidan Sarki Hilairu ne akan gaba ana ingiza keyarsa ana kai masa bugu.Da fitowarsu kofar gidan sai aka jera bayin akan layi sahi sahu sannan Lahaman ya tsaya a gabansu dakarunsa kuma suka yiwa bayin KAWANYA,nan take Malika ta dubi Zarhus tace ina dukiyata?Zarhus na jin wannan tambaya sai ya sauko daga keken shanun ya bude akwati ta biyu ya cire shimfidar sama mai dauke da matattun kwari,sai ga lu'u lu'u birjik a kasan mai yawan gaske wanda ya isa Malika ta biya gaba daya kudin da aka siyar mata da bayin gaba dayansu har sarki Hilairu kuwa.Koda Yarima Lahaman da dakarunsa sukayi arba da wannan duki mai yawa haka,sai suka cika da tsananin mamaki yadda akayi ta mallaketa.Kawai sai Malika ta dubi Lahaman tace,kasa yaranka amintattu su debi iyakar kudin daka siyar mini da wadannan bayi duka su bar mini ragowar.Cikin rawar jik Lahaman ya dubi wasu mutum biyu daga ckin su yace,ku kirga adadin dinare dubu dari biyar da kuma dinare dubu hamsin sau dari.Nan taje kuwa dakarun biyu suka shiga kirga lu'u lu'u suna zubawa a cikin buhu saida suka shafe sa'a uku suna wannan aiki sannan suka kammala amma duk da haka sai da suka gama dibar iyakan adadin da aka umarce su kuma suka rage kudade da yawa.Bayan an dankawa yarima Lahaman ya karba yana ta farin ciki da walwala sannan an saki bayin sunzo bayan Malika sun tsaya.Sai Malika ta bude ragowar akwatunan da hannunta sai gashi kowacce akwati cike take da dinare da lu'u lu'u fal wadanda in da za'a bawa mutum guda daya jal to zai shafe shekaru dubu a rayuwarsa yana cin abinci yana sa irin suturar dayake so yana walwala batare da sun kareba. Koda Yarima Lahaman ya kyallara ido yaga wannan dukiya mai dumbin yawa sai kishi ya turnukeshi gami da tsananin mamaki yadda akayi Malika ta tara wannan dukiya.Shidai ya sani cewa babu yadda za'ayi sarki Sharkuf ya iya bata duk irin tsananin son da yake mata saboda ya kasance mutum mai kwatanta adalci a tsakanin 'ya'yansa.Bayan Malika ta gama nunwa Yarima Lahaman wannan dukiya sai ta dubeshu tace,Ya kai Yarima ashe burinka gajere ne ban sani ba.A zatona zaka bukaci dukiya mai yawan da tafi wannan danazo da ita,kuma tabbas dana baka na sake baka wata ninkinta,saboda ina da ira ninkin baninkin.Ina so ka sani cewa ni Gimbiya Malika MURUCIN KAN DUTSE nake ban fito ba sai dana shirya.Kabar ganin cewa babu kamarka a harkokin cinikin bayi a wannan nahiyar har kayi tunanin cewa kafi kowa kudi da arziki.,to ina mai tabbatar maka da cewa ni Malika a halin yanzu na tara dukiya da baka da kaso daya cikin gomanta.Duk harkokin na cinikin abinci dana kayan yaki da ake yi da manyan Kasashen duniya a wannan zamani nice babbar dilar da babu kamarta.Itama harkar cinikin bayin ka zauna cikin shiri kwanan nan zan karbeta na zama na ni ke sarrafata a duniya,ba don komai ba sai domin nayi maganin manyan azzalumai irinku.Yanzu dai gani ni kadaice na zo babu wani badakare ko guda daya daya rakoni don bani tsaro.Idan ka gadama ka turo min gaba daya dakarun naka su tare mini hanya kafin na isa cikin gari suce zasu kwaci wannan dukiya da wadannan bayin dana siya wajenka.Na rantse dabgemun Mahaifinmu dayansu bazai tsira da rayuwarsa ba.Idan kuma kana ganin cewa kai ne da kanka zaka tareni to ina jiranka ai KAR TA SAN KAR ce kuma shege ka fasa.Koda Malika tazo nan a jawabinta sai ta dubi su sarki Hilairu tace,wuce gaba mu tafi izuwa inda zan ajiye ku.Cikin tsananin farin ciki su sarki Hilairu suka wuce gaba sannan Malika ta hau kan keken shanu Zarhus ya tuka suka bi bayan su Hilairu.Dama tunda Gimbiya Malika ta fara bayaninta ga Yarima Lahaman sai jikinsa ya kama tsuma,idanunsa suka kada sukayi jawur ya kamu da tsananin bakin ciki kuma ya rinka ji kamar ya zare takobinsa yaje ya afka mata da yaki,amma sai ya daure ya hakura sa'adda ta fadi kalma mai zafi da muni a gareshi sai dakarunsa su yunkuro zasu afka mata,amma sai ya dannesu,saboda yasan cewa AJALIN su zasu gaiyata kuma shi kansa bazai iya karesu ba da komai.Har Saida Malika tayi nisa da barin kofar wannan gidan nasa har ya daina hangosu ita da dukan bayin data siya a hannunsa,sannan ya takarkare ya kwarar uban ihu mai tsananin ban tsoro sannan kuma ya durkushe kasa bisa guiwowinsa ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki.Adaidai wannan lokaci ne hadari ya gangamo aka fara tafka walkiya da tsawo amma saboda tsananin bakin ciki sai Yarima Lahaman yaki tashi ya shiga cikin wannan gida nasa.Aikuwa take aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya,koda ganin yadda ruwa yake dukan Yarima Lahaman kuma gashi ruwa ne mai karfin gaske dauke da iska,sai daya daga cikin wannan dakarun nasa ya matsa daf dashi yace,ya shugabana zaifi kyau ka tashi daga cikin ruwan nan domin zai iya cutar da lafiyar...Kafin badakaren ya gama rufe bakinsa tuni Yarima Lahaman ya shammaceshi cikin bakin ZAFIN NAMA ya zare takobinsa ya share masa makogwaro,kawai sai gani akayi jini yayi feshi daga cikin wuyan badakaren sannan ya fadi matacce.A sannanne Yarima Lahaman ya mike tsaye ya goge jinin dake jikin takobinsa akan gawar badakaren sannan ya mayar da takobin cikin kufe ya daga kansa sama yayi KURURUWA mai razanarwa tamkar zaki yayi GUNJI a dawa.Nan take duk wani abu mai rai dake kusa ya dimauce,hatta ragowar dakarunsa dake tsaye a wajen da wanda ke cikin gidan saida suka firgice suka rikirkice suna neman su cika wandonsu da iska,amma sabida tsoro sai suka kasa guduwa izuwa ko ina.A sannanne Yarima Lahaman yayi rantsuwa da darajar uwarsa yace,daga yau Malika baza ta sake yi masa wulakanci ba,kuma komai dadewa sai ya kasheta da hannayensa ya huce takaicinta,koda samun nasarar yin hakan na nufin mutuwar duk wani abu mai rai dake cikin kasar nan.Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya shige izuwa cikin wannan gida nasa. Al'amarin Gimbiya Malika kuwa lokacin da suka yi dan nisa ga barin gidan Yarima Lahaman tare dasu sarki Hilairu itana bisa keken shaun su kuma suna tafiya a kasa bisa kafafunsu kuma taga hadari ua gangamo an fara walkiya,sai ta bayar da umarni aka rugu cikin wani kogon dutse domin a fake.Ai kuwa suna gama shiga cikin kogon dutsen nan ruwan saman ya tsuge,nan fa kowannansu maza da mata ya sami wuri ya zauna,aikuwa aka fara ruwan saman mai dauke da iska mai sanyi ya addabi kowa.Koda ganin haka sai Malika tayi amfani da karfin sihirinta na tsafi ta kunna wutar jin dumi har guda uku.Daya sai gaba dayan matan suka kewayeta dayar kuma sai mazan suka kewayeta,ya zamana cewa zaura wutar guda daya babu kowa a gabanta,shi kansa Zarhus tuni ya zaro bargo a cikin keken shanunsa ya kwanta ya lullube jikinsa gaba daya.Nan fa ya rage saura Gimbiya Malika da sarki Hilairu a tsaye a can gefe daban daban suna kallon juna,kuma suna kallon wannan wuta guda daya data rage wacce babu kowa a gabanta,kamar hadin baki sai duk su biyun suka taho izuwa gaban wutar a lokaci guda suka zauna suna jin dumin kuma suna fuskantar juna.Tsawon 'yan dakiku dayansu bece uffan ba kawunansu na sunkuye suna kallon kasa.Kawai sai suka dago kai a tare kuma kowannasu ya bude baki da nufin yace wani abu,koda muryoyinsu suka sarke a lokaci guda sai suka kyalkyale da dariya saboda mamakin yadda al'amarin ya kasance haka.A sannane Gimbiya Malika ta dubi Sarki Hilairu cikin murmushi mai taushi tace,ya kawai wannan saurayi Ma'abocin kyau da kwarjini waye kai kuma yaya akayi ka tsinci kanka a cikin wannan rayuwa ta bauta?Kasani cewa a karon farko dana ganka jikina ya bani cewa ka fito daga babban gida kuma asalinka baka kasance bawa ba.Koda Malika tazo nan a zancenta sai taga hawaye a zubowa sarki Hilairu,al'amarin daya karya zuciyar kenan taji ta kara kamuwa da tsananin tausayinsa.Ta dubi Sarki Hilairu cike da tsananin tausayi tace,yakai wannan sarki me yasa kake zubar da hawayenka alhalin ka tsira daga hannun dan uwana kuma kasan cewa bazan taba cutar dakai ba,kayi sani cewar bana kubutar dakai bane

Chapter 4 of 19