Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
domin ganin cewa Lahaman baiyi nasara ba?Ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu babu mai mulki Azzalumi mara imani kamar Yarima Lahaman aduk fadin wannan duniya sannan kuma babu wani matsafi mai karfin sihirinsa domin a yawon da yayi na neman ilmin tsafi babu wani bangare a duniya inda baije ba duk inda wani mashahurin matsafi yake sai yaje ya samu dukkan sihirin tsafinsa sannan kuma ya sami horon yaki na gaban tunani.Karo da Lahaman daidai yake da karo da GUGUWAR ANNOBA.Lokacin da gimbiya Zuhura tazo nan a zancenta sai sarki Kamzal yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubeta cikin alamun karayar zuci yace yake yata duk wannan abu da kika Prince Auwal auwzab fadi gaskiya yanzu nasan dasu kuma nasan da wadansu abubuwan ma wadanda ke baki sani ba.Tabbas idan Yarima Lahaman ya lashe wannan gasa ni ma bazan tsira ba kuma indai ina raye bazan taba yarda ki zamo abokiyar rayuwarsa ba,ni kaina da dukkan bokayen kasar nan munyi bincike a hallarar tsafinmu mun gano cewa babu wanda zai iya maganin Lahaman face Hibairu don haka a gobe ina tsoron karon Sa Maza Gudu da Lahaman.Ko kinsan cewa Lahaman yazo garin nan da dakarunsa na yaki kimanin su Miliyan uku suna can bayan gari sun yada sansani kawai jira yake ya lashe wannan gasa ya basu umarnin su shigo su ci birninmu da yaki.Koda jin wannan batu sai Sarki Kamzal ya gyada kai yace yadda duk kike zaton Yarima Lahaman ya wuce nan domin bai fito ba saida ya shirya,ina mai tabbatar miki da cewa inda gaba dayan dakarun duniyar nan zasu taru a kansa ba zasu iya kasheshi ba,mutum daya ne jal nake sa ran cewa zai iya ganin bayansa kuma ba wani bane face masoyinki Hibairu kuma shima zai sami nasara ne a kansa kawai da taimakon ubangijinsa ba wani da karfin damtsensa ba ko iya yakinsa.Yayin da Zuhura taji haka saita dubi mahaifin nata cikin mamaki tace shin yanzu kana nufin cewa kaima kayi imani da addinin Hibairu? Sa'adda sarki Kamzal yaji wannan tambaya sai ya sunkui da kansa kas yayi shiru kamar bazaice komai ba daga can saiya numfasa yace yake yata kiyi sani cewa ita gaskiya dokin karfe ce bata karyewa shi kuwa ramin karya kurarre ne.Fiye da shekaru dari uki da suka gabata addinin Hibairu shine kadai addinin da aka kasa shafeshi daga doron kasa gaba daya,banda wannan addinin babu wanda ba'a sauya shi ko aka shafeshi gaba daya ba.Iyayenmu da kakanninmu duk sunsan da hakan amma saboda son zuciya gami da son duniya sai suka ki yarda da wannan addinin na musulunci saboda sun san cewa addinin ne wanda zai hana su yin zalunci kuma ya hana su yin bushasha.Ni din nan yanzu idan nace zan karbi addinin musulunci bisa tabbatar miki da cewa yan uwana da fadawa na zasu hada kai da makiyana suga bayana.Babu mai iya kafa wannan addinin a wannan birni namu face irin su Jarumi Hibairu kuma shima bazai iyayin hakan ba face an zubar da jini kamar yadda akayi a garinsu Marigayiya Gimbiya Lasmin.Ni yanzu babban tashin hankali na shine na tabbatar da cewa shi kansa Yarima Lahaman babu wanda yake shakka face Jarumi Hibairu don haka kafin goben nan zai iya bin hanyoyi da yawa na ganin ya hallakashi bisa wannan dalili na tura dakaruna da yawa akan su baiwa Hibairu tsaro a masaukinsa.Haka itama Gimbiya Malika da Masoyinta Sarki Hilairu rayuwarsu na cikin mugun hadari domin suma zai iya fara kashesu.Koda Gimbiya Zuhura taji wannan batu sai hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe tayi shiru tana tunani da nazari har izuwa lokaci mai tsawo.Daga can sai ta dago kai ta dubi mahaifin nata tace ko kadan bana shakkar Hibairu domin nasan cewa ubangijinsa zai iya kareshi daga dukkan sharrin Yarima Lahaman Amma ina shakkar cewa gimbiya Malika da sarki Hilairu zasu iya kare kansu don haka lallai ka tura dakarunka su basu tsaro.Sa'adda Sarki Kamzal yaji haka sai ya numfasa yace ai sarki Hilairu yana tare da dan uwansa Sa Maza Gudu don haka yana da kariya,ita kuwa gimbiya Malika ai masaukinta anan cikin gidan yake ko kuwa kin manta ne da hakan.Idan har wani abu zai taba lafiyarta to lallai zai taba tamu kenan,ki kwantar da hankalinki kuma kiyi addu'a akan Hibairu ya sami nasara akan Lahaman gobe.Koda gama fadin hakan sai sarki Kamzal ya juya ya nufi bangaren da turakarsa take.Koda ganin haka sai itama Gimbiya zuhura ta tafi izuwa tata turakar amma sai taji kamar ta fasa zuwa turakar tata ta juya da baya ta tafi neman inda masaukin Hibairu yake saboda tunaninsa da begensa ne suka turnuke zuciyarta.Haka dai ta karasa cikin turakar tata ta shige kewaye kuyangi sukayi mata wanka suka shafeta da mai sannan suka kawo mata abinci taci dan kadan saboda tunani.Daga can sukaje suka kwantar da ita akan gado domin tayi bacci amma sai baccin ya gagara domin da zarar ta rufe idanunta babu abinda take gani face Jarumi Hibairu,idan kuma ta bude idanun nata sai taga Jarumi Hibairu a zahiri tsaye a gefe guda yana yi mata murmushi(Hmm SO kenan).Da zarar ta mike tsaye sai ta gane cewa lallai tsananin begensa ne yasa take ganinsa a zahiri don haka sai ta kama kai kawo ta kasa kwanciya ta kasa zama.A karshe dai saita yanke hukuncin cewa duk RINTSI DA TSANANI ba zatayi bacci ba a daren yau face taga jarumi Hibairu kuma taji muryarsa. *Al'amarin Yarima Lahaman kuwa bayan filin gasar jarumta ya watse ya tafi izuwa masaukinsa a wani gida dake can bayan gari sai kuyanginsa sukayi masa wanka suka wanke duk jinin dake jikinsa suka sauya masa tufafi yayi fes dashi tamkar jikinsa bai taba baci da jini ba.Daga nan sai Lahaman ya dawo cikin filin gidan wanda ya kayatu ainun ya zauna akan wata doguwar kujera nan take aka kawo masa abin sha sama da kala goma aka zube a gabansa bisa wani dan teburi mai fadi.Ba tare da bata wani lokaci ba Lahaman ya fara kimtsa cikinsa cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali tamkar babu wani abu da yake damunsa a rayuwa,yana cikin wannan hali ne babban hadiminsa da ake kira Zamnas ya iso kofar gidan a sukwane bisa doki kallo daya mutum zai yiwa Zamnas ya gane cewa daga doguwar tafiya yake domin hatta guzurin da yake dauke dashi akan dokin irin na matafiya ne.Take Zamnas ya baiyanawa Lahaman cewa komai ya kammala akan aikin da yasa su.Sannan kuma sun gamu da yaran gimbiya Malika mun kama su mun daure kuma mun kwace duk dukiyar dake hannunsu mun adana maka ita.Koda Prince AUWAL AUW.ZAB wannan batu sai farin ciki ya turnuke Lahaman baisan sa'adda ya kurma ihu ba ya rungume Zamnas yana mai cewa da Zamnas aikinka yayi kyau nayi maka alkawari bayan na hau kan karagar mulkina kaine zaka zamo waziri na.Ina labarin mahaifina ina fatan dai ka kiyaye duk abubuwan dana shaida maka don kada ya gano shirina? Zamnas ya risina yace na tafiyar da komai daidai kamar yadda ka umarceni amma dole ne ka sauya tsarin shirinka domin a halin yanzu sarki Sharkif ya yanke shawarar tahowa nan birnin domin yaga wannan gasa ta karshe da za'ayi ina mai tabbatar maka da cewa kafin dare ya raba zai iso nan kuma dakaru dubu dari ne kacal sukayi masa rakiya.Koda jin wannan batu sai yarima Lahaman ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya dubi zamnas cikin murna yace ai babu bukatar na sauya tsarin komai nawa domin sarki ya tafka babban kuskure daya fito daga cikin birninmu a wannan lokaci,abinda nake so dakai shine yanzu kayi sauri ka koma can baya inda dakaruna guda MILIYAN BIYU suka yada sansani ka jagorance su ku danawa su sarki Sharkuf tarko da zarar sun iso daidai kusa da sansanin ku kashe gaba dayan dakarun nasa shi kuma ku kamashi a raye ku daure shi sai ku shigo dashi cikin garin nan ku kawoshi har filin gasa so nake ya gani da idanunsa lokacin da zan fillewa gimbiya Malika kanta a sannan ne zan rama wulakancin daya dade yanayi mini na fifita Malika akaina shima na sare kansa na tsire shi akan mashi kowa ya gani.Tabbas duniya zata tsorata dani idan akaji cewa na kashe mahaifina da hannuna.Zamnas najin haka saiya risina yace angama ya shugabana.Nan take Zamnas ya juya da sauri ya fice daga cikin gidan.fitar zamnas keda wuya sai Yarima Lahaman ya mike tsaye yaje ya dauko wata katuwar bakar akwati ya ajiyeta a gabansa sannan ya budeta ya fiddo wani murtukeken dogon maciji bakin kirin mai faskeken kai,hakika wannan maciji yana da matukar kwarjini.A cikin yaren tsafi Lahaman yakama ambaton sunan Jarumi Hibairu.Kawai saiya ajiye macijin a kas faruwar hakan keda wuya sai macijin ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Da ganin haka sai Yarima Lahaman ya bushe da dariyar mugunta yayi ta kyakyatawa kamar bazai daina ba har saida wata babbar kuyangarsa tazo ta zauna daf dashi ta kama shafa gashin kansa ta dubeshi tace ya shugabana waishin murnar me kakeyi ne?Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lahaman yayi shiru ga barin yin dariyar ya dubi kuyangar cikin nutsuwa da murmushi yace kinga wancan macijin sihirin dana saki yanzu duk mutumin daya sara take zai mutu a cikin dakika biyar domin babu wani abu da zai iya magance dafinsa,ina mai tabbatar miki da cewa macijin wajen Jarumi Hibairu ya tafi kuma nan da cikar sa'a guda zai shiga har cikin masaukisa ya sareshi.Lallai gobe da safe wasa daya zanyi domin daya abokin gamin nawa mutuwa zaiyi nan da cikar sa'a daya.Koda jin haka sai kuyangar ta kamu da tsananin farin ciki ta rungume Lahaman tana mai cewa ai kuwa idan Hibairu ya mutu a cikin wannan dare kwana zamuyi muna walima saboda munsan cewa saura kwanaki kadan ka zame sarkin wannan nahiya gaba daya.Dajin haka sai Lahaman ya sake kankame kuyangar a kirjinsa yana mai cigaba da kyalkyala dariyar murna kuma ya sunkuti tambula na ruwan giya ya kafa a bakinsa ya kama sha. *A Can Masaukin Jarumi Sa Maza Gudu kuwa lokacin da suka shiga cikin turakarsa shida dan uwansa sarki Hilairu sai suka ci suka sha suka sami nutsuwa sannan Hilairu ya dubeshi yace yakai dan uwana kayi sani cewa rayuwarmu gaba daya tana cikin mummunan hadari ina tsoron karonka da yarima Lahaman.Koda jin wannan batu sai Sa Maza Gudu ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace ya kai dan uwana kasani cewa tun muna yara ban taba yin FADUWAR GABA ba kuma duk abinda nasa a gabana sainayi nasara.Na sani cewa zansha bakar wahala yayin gumurzuna da Yarima Lahaman amma ban taba cire saran samun nasara ba.Kuma nayi alkawari shima bazaiyi nasara akaina ba.Fargabata guda daya ce kawai sa'a uku ne kacal akeyi ana fafatawa a wannan gasa kuma idan lokaci ya cika dayanmu bai sami nasara ba tsayar da gumurzun za'ayi a yi wasa na gaba.Ina tsoron kada muyi ragas a cikin sa'a ukun don haka duk yadda zanyi sainayi a cikin sa'a uku naga bayan Lahaman sannan kuma naga bayan Hibairu na mallaki masoyiyata.Loka cin da sa maza gudu yazo nan a zancensa sai sarki Hilairu yayi ajiyar numfashi cikin alamun tsananin damuwa gami da sunkui da kansa kasa yace yakai dan uwana har yanzu dai ashe kana kan bakanka nason ganin bayan Hibairu wannan shine babban kuskurenka a rayuwa domin kana sone ka kawar da wanda yake yaki da zalunci ina mai tabbatar maka da cewa har abada adalci baya kayar da adalci saidai ya kayar da zalunci ko kuma zalunci ya kayar da dan uwansa,tun farkon duniya haka abin ya kasance kuma har karshenta haka zata kasance.Azzalumai basa dorewa saidai suyi shahara izuwa wani lokaci kafin wani zamanin yazo ya shafesu,ka kiyayi Hibairu domin ya wuce yadda duk kake zato.Hibairu ikon Allah ne kuma wata baiwa ce daga mahaliccinsa kuma mahaliccin nasa shine wanda babu kamarsa.Koda jin wannan batu sai sa maza gudu ya kamu da tsananin mamaki kuma ransa ya baci ainun don haka bai san sa'adda ya dakawa Hilairu tsawa ba yace kada dai kace dani kaima ka karbi wannan addinin na Hibairu?Hilairu ya girgiza kai yace ban karbi addininsa ba amma zan karba da zarar naga ya sami nasarar kashe Yarima Lahaman.Cikin fushi Sa Maza Gudu ya cakumi kwalar Hilairu ya girgiza shi da karfi yace nine zan kashe Hilairu a gobe da safe kafin ma ya kashe Lahaman. To masu karatu Yau zamugama wannan littafin Saura post 2 mugama wannan labarin mushiga wani me suna...........KIBIYA RATSA MAZA wannan shine sunan littafin da zamufara gobe idan da rai da lafiya ko kuma kuna ganin mukaishi bayan sallah karama Sbd azumi da zamushiga????ga dan kadan daga cikin sabon littafin da zamushiga gobe............... KIBIYA RATSA MAZA Littafi na Daya(1) Part A Gudu takeyi iya karfinta domin ta ceci rayuwarta saboda bala'in dya biyo ta,babu abinda za'a kwatantashi dashi face ajali.Babu abinda zai baka mamaki face wannan budurwa dake wannan azababben gudu,kyakkyawa ce abar kwatance,kuma cikin shigar yaki take,ga takobi a hannunta tsirara ba'a ciki kufe ba.Saboda karfin gudun da takeyi tamkar tafin kafarta zai tabo keyarta,amma duk da haka waige waige takeyi a cikin alamun tsoro,duk da cewa kana mata kallo daya zaka gabe cewa jarumace ta kwarai mai kirar sadaukai.Kai bama ita ba hatta aljanu da tsuntsaye dake cikin wannan daji da take gudu a cikinsa tsoron dajin sukeyi da abinda ya biyota saboda masifu da bala'in dake tare dasu ballantana kuma bako irinta wanda bai tana shigowa dajin ba. ★SA MAZA GUDU★!!! Littafi Na Tara (9) Part B. prince AUWAL AUW.ZAB NINE ZAN KASHE HILAIRU A GOBE DA SAFE KAFIN MA YA KASHE LAHAMAN.KADA KA SAKEYI MIN WANNAN MAGANA.KODA GAMA FADIN HAKAN SAI SA MAZA GUDU YA TAFA HANNUNSA SAU UKU.NAN TAKE DAYA DAGA CIKIN DAKARUN DAKE TSARON LAFIYARSA YA SHIGO CIKIN TANTIN WANI DOGON SADAUKI NE MAI KWARJINI.Badakaren ya zube kasa a gabansa cikin biyayya shi kuma saiya dubeshi yace ni zan kwanta nayi bacci yanzu,kusa ido sosai akan aikinku kada ku bar mutum ko daya ya shigo cikin gidan nan kuma kada ku bar dan uwana ya fita.Badakaren ya risina yace an gama ya shugabana kawai saiya mike tsaye ya fice daga cikin turakar fitarsa keda wuya sai Hilairu ya dubi sa maza gudu yace saboda me zaka kafa mini dokar kin fita alhalin inason naje naga masoyiyata gimbiya Malika?Sa maza gudu ya juyo ya dubi Hilairu a fusace cikin daga murya yace shin baka san cewa rayuwarka na cikin hadari bane?To ka sani ana farautar rayuwarka a halin yanzu kamar yadda mai jin kishi ke neman ruwa ko don saboda a kunsa mini bakin ciki.Sa maza gudu na gama fadin hakan saiya kwanta akan shimfidarsa ya runtse idanunsa ai kuwa kafin cikar dakika dari da ashirin tuni ya fara munshari abinsa tamkar babu wani abin damuwa a cikin zuciyarsa.Al'amarin dayayi matukar baiwa sarki Hilairu mamaki kenan yace waishin wannan dan uwan nawa wane irin mutum ne shi wanda KARFIN ZUCIYARsa yafi na zaki.Ban taba ganin ranar da zuciyarsa ta karaya ba kuma ban taba ganin ranar da yaji tsoron wani abu mai rai ba walau mutum ko Aljan,dabba ko kwaro.Wannan shine abinda ya faru tsakanin jarumi sa maza gudu da dan uwansa sarki Hilairu acan masaukinsu. *Al'amarin jarumi Hibairu kuwa lokacin daya tafi nasa masaukin wanda ke can wani bangare daban na gidan sarautar.Bayan ya idar da sallar magriba sai yayi addu'a ya roki Allah akan ya kareshi daga sharrin abokan gaba kuma ya bashi nasara bisa abinda yasa a gabansa na jaddada Addinin Musulunci a nahiyar gaba daya kuma ya bashi ikon komawa gida lafiya domin ya sadu da iyayensa.Koda gama wannan addu'a sai ya sake karanta wata addu'ar ta musamman ta neman tsari ya tofa a jikinsa ya shafe ko ina sannan ya kwanta domin ya dan huta.Faruwar hakan keda wuya sai bacci ya daukeshi sakamakon tsananin gajiyar dake jikinsa. *Acan turakar Gimbiya Zuhura kuwa lokacin da taga ta kasa yin komai sakamakon tunani da begen Hibairu daya addabi zuciyarta sai kawai tasa aka kirawo mata shugaban dakarun dake tsoron lafiyarta Barde Sharmas ta dubeshi tace inason kayi mini rakiya yanzu izuwa masaukin jarumi Hibairu domin inason nayi magana dashi.Koda jin wannan batu sai idanun Barde Sharmas suka zazzaro ya dubeta cikin alamun matukar tsoro yace ya shugabata sarki yayi mana gargadi a kan kada mu bari ki tafi ko ina saboda hadarin da ake ciki,idan har wani tsautsayi ya sameki zan iya fuskantar babban hukunci.Cikin matukar fushi gimbiya Zuhura ta dubi Barde Sharmas tace haka kuma zaka fuskanci kaidi irin namu na mata idan baka bi umarni na ba a yanzu,shin kasan sharrin da zanyi maka kuwa yanzu idan kaki rakani masaukin Hibairu?Koda jin wannan batu sai jikin Barde Sharmas ya kama karkarwa muryarsa na rawa yace ke kuwa wane irin sharri zakiyi mini.Gimbiya Zuhura tace zan yayyaga tufafin jikina kuma na fasa bakina da hancina su kama yoyon jini sannan na kwala ihu nace kayi yunkurin yi mini fyade.(Uhmm Kuji Kadan daga Kaidin Mata).Koda jin haka sai Barde Sharmas ya durkusa bisa guiwoyinsa ya kama rokon gimbiya akan ta rufa masa asiri kada tayi masa wannan sharri.Koda ganin haka sai tayi murmushi tace ka cika umarnina idan kana son ka kubuta.Ba tare da gardamar komai ba sharmas ya mike tsaye cikin alamun tsananin sanyin jiki ya juya ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi a baya da sauri.Duk inda suka ratsa a cikin gidan sarautar sai suga dakaru,bayi da hadimai suna kallonsu cikin mamaki saboda sani dokar da sarki ya kafa amma sai aka rinka ratsewa ana basu hanya kuma ana gaishe da gimbiya haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso kofar turakar da jarumi Hibairu ke ciki.Da isowarsu sai masu gadin dakin suka dare suka basu hanya.Kawai sai Gimbiya Zuhura ta dakatar da Barde Sharmas tace ka tsaya anan ka jira ni bazan dade ba zan fito mu tafi.Cikin karayar zuciya Barde Sharmas ya sunkui da kansa kasa ya kasa cewa komai saboda ya tsorata da Gimbiya Zuhura.Take gimbiya Zuhura ta kunna kai cikin turakar tana mai murmushi taje kansa ta tsaya ta kura masa idanu.Kwatsam ba zato ba tsammani sai taji wani irin mugun huci a bayanta gami da wani babban motsi,a firgice ta juyo da baya da sauri kawai sai tayi arba da wani murtukeken bakin dogon maciji ya fasa kansa zai kaiwa Hibairu sara,kawai sai Gimbiya Zuhura ta daka tsalle tasha gaban macijin ai kuwa sai ya sareta akan kafadarta.Take ta kurma ihu,kafin macijin ya juya ya sari Hibairu tuni Hibairu ya daka tsalle sama daga kan gadon da yake kwance.Yana saman ya zare takobinsa yana mai kwala kabbara ya sare kan macijin take macijin ya sulale kasa matacce.Adaidai wannan lokaci ne su barde Sharmas suka fado cikin daki a gigice ruke da makamansu tsirara.Koda sukayi arba da gawar macijin sai suka kame,shi kuwa Hibairu sai yaga Gimbiya Zuhura ta sulale kasa ta baje kamar gawa kuma yayi arba da inda macijin ya sareta kan kafadarta.Sai ya durkusa ya kafa hakoransa akan wajen ya rinka zuko dafin macijin yana furzarwa a kasa saida Hibairu ya zuko dafin sau tara yana furzarwa a kas.Su kuwa su barde Sharmas sun zuba idanu kawai cikin alamun tsananin tsoro.Yana gama cire mata dafin sai su kaga shima ya sulale kasa ya baje jikinsa na Prince Auwal Auwzab makyarkyata alamar cewa shima dafin ya shige cikinsa.Adaidai wannan lokaci ne gimbiya Zuhura ta farfado daga dogon suman da tayi ta mike zaune zumbur tamkar wani abu bai sameta ba.Koda taga Hibairu kwance a kasa yana makyarkyata sai ta fada kansa ta rungumeshi kuma ta fashe da matsanancin kuka.Ba zato ba tsammani sai taga Hibairu ya kama yin kumallo.Nan take ya amayar da dukkanin dafin daya shiga cikinsa a kas wanda ya kasance bakin kirin tamkar an jika shuni.Nan take ya sami lafiya ya dawo cikin haiyacinsa.Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube zuhura ta rungumeshi tana mai rusa dariyar murna.Cikin hanzari Hibairu ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta a cikin fishi yace menene ya kawo ki dakina kuma saboda me zaki siyar da rayuwarki don kare tawa?Lokacin da gimbiya Zuhura taji wannan tambaya saita bushe da dariya a karo na biyu sannan tace na kasa zama na kasa kwanciya na kasa tsayuwa kuma na kasa tafiya duk saboda tsananin begenka da tunaninka wannan shine dalilin da yasa na baro turakata na taho nan.Na siyar da rayuwata don kare taka domin na tabbatar maka da cewa ina kaunarka kamar yadda Marigayiya gimbiya Lasmin ke kaunarka,shin yanzu ka gamsu cewa nafi Lasmin sonka?Sa'adda Gimbiya Zuhura tazo nan a jawabinta sai idanun su barde Sharmas ya zazzaro suka cika da tsananin mamaki,shi kuwa jarumi Hibairu saiya dubeta cikin murmushi yace na yarda kina kaunata tamkar yadda marigayiya ke kaunata amma ban yarda cewa kin fita kaunata ba.Dajin haka sai gimbiya Zuhura ta mike tsaye zumbur a fusace ta dakawa Hibairu harara tace shikenan sai gobe a filin gasa zan tabbatarwa da duniya cewa babu wata 'ya mace dake kaunarka sama dani.Tana gama fadin jakan sai ta juya ta fice daga cikin dakin da sauri shima BARDE Sharmas saiya ruga ya take mata baya.Dul wannan abu da yake faru a turakar Hibairu Yarima Lahaman ya gani a cikin MADUBIN TSAFI.Koda yaga cewa wannan maciji bai sami nasarar kashe Hibairu ba kuma yaga yadda Zuhura ta sallama rayuwarta don kare ta Hibairu saboda soyayya sai zuciyarsa ta kama tafarfasa bai san sa'adda ya rotsa madubin tsafin nasa a kasa ba ya kma tattakaeshi da kafafunsa yana huci da gurnani tamkar bakin kumurci.Kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto filin gasar jarumta ya cika ya batse da mutane babu inda za'a iya sanya koda tsinke.Ba komai ne ya janyo hakan ba face zumudi da dokin al'umma nason ganin yadda karshen wannan gasa zai kasance.Saida gari ya waye sosai rana ta take sannan sarki Kamzal da jama'arsa suka shigo cikin filin gasar da kyar dakaru suka buda musu hanya suka isa inda mazauninsu yake saboda cikowa.A wannan lokaci sarki Kamzal na ruke da hannun yarsa gimbiya Zuhura suna ta kalle kallen filin gasar suna mamakin irin tsananin cikowar da akayi wacce ba'a taba yin kamar taba a tsawon shekaru goma sha biyar da fara shirya wannan gasa.Saida sarki da mukarrabansa sukaje suka zauna a mazauninsu sannan aka buga tambari jaruman gasa suka fito mutun uku ne kacal jaruman gasar kuma ba wadansu bane face jarumi Hibairu,Jarumi Sa Maza Gud da kuma Yarima Lahaman.Dukkani nsu sunyi gagarumar shigar yaki mai tsananin kwarjini.Koda shigowarsu cikin filin gasar sai jama'a suka kaure da shewa gami da tafi kowa na koda gwaninsa.A wannan rana attajiran caca kuwa sunfi mutum dubu arba'in kuma kowannensu saida ya zazzage gaba dayan dukiyarsa don gudanar da wannan caca.Bayan jaruma gasa sunje sun tsaya a inda suka saba tsayawa suna kallon juna cikin harara sai alkalin gasa ya shigo tsakiyar fili ya tsaya domin ya gabatar da gasar.Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka hango wani mahayi ya surfano doki a sukwane izuwa cikin taron jama'a gaba daya jikin mahayin a rine yake da jini hatta fuskarsa da dokinsa kuwa.Har dakarun sarki Kamzal sun yunkura zasu tareshi sai sarki ya daga hannu sama yayi musu inkiyar su tsaya.Kai tsaye mahayin ya durfafo inda sarki Kamzal yake da isowarsa sai sarki Kamzal ya mike da sauri ya ruke masa dokin da kansa ya sauka sannan suka rungume juna.Nan take sarki Kamzal yaja mahayin har izuwa kan kujerarsa suka zauna tare.Kawai sai sarki Kamzal yace a cigaba da gabatar da gasa.Al'amarin daya daurewa kowa kai kenan domin hankalin kowa ya tashi bisa ganin mahayin a cikin jini kace kace gashi ko fuskarsa ba'a iya gani bare a gane ko waye.Alkalin gasa ya duni jama'a yace yanzu zamu kirawo jarumi sa maza gudu tare da yarima Lahaman domin su fafata a zagaye na biyun karshe.Nan take aka buga tambari sa maza gudu da Lahaman suka shigo cikin tsakiyar filin,a guje alkalin gasar ya fice daga cikin filin.Ai kuwa yana fita sai sa maza gudu da Lahaman suka rugo izuwa kan junansu suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi.Saida suka shafe sa'a guda cif suna kaiwa junansu sara da suka batare da dayansu ya sami wata nasara ba har takubbansu suka dakushe garkuwoyinsu suka farfashe amma ko alamar gajiya babu a tare dasu,bisa dole suka watsar da takubban da garkuwoyin suka kacame da naushi gami da bugun juna ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina suka galabaita ainun amma saboda bakin naci da tsananin juriya da jarumtaka har wata sa'a gudan ta sake shudewa dayansu baije kasa ba.Adaidai wannan lokaci ne aka buga ganga suka tsaya ga barin fadan,alkalin gasa ya shigo ya dubesu yace yanzu saura sa'a daya kacal gumurzun ya kare kuna bukatar a sake baku makami?Cikin hadin baki sai sukace suna so nan take aka kawo musu manyan takubba da manyan garkuwoyi sababbi suka buda,alkalin gasa ya sake rugawa waje aka buga tambari.Wohoho idan karfi ya hadu da karfi sadaukantaka da tadu da Prince Auwal Auwzab Auwzab takwaranta kuma tsafi yayi karo da tsafi dole ne gumurzu yayi zafi.Saida sa maza gudu suka sake shafe rabin sa'a suna mugun artabu cikin sauya salon yaki iri iri sannan kowannensu ya sami nasarar yiwa abokin gwaminsa rauni uku.Gashi dai jini na zuba a jikinsu amma basu fasa kokarin hallaka junan suba duk da cewa jiri na dibarsu suna layi kamar zasu fadi.A lokacin da jini ke zuba a jikinsu ne lokaci na dab da cika ne Lahaman ya shammaci sa maza gudu ya doki kafafunsa sa maza gudu yayi sama ya wurkila jikinsa kafin ya diro kasa Lahaman ya daka tsalle sama ya doki kirjinsa ya fado kasa a matukar galabaice.A daidai wannan lokaci ne aka buga gangar tsayar da gumurzun saboda lokacin ya cika amma duk da haka sai Yarima Lahaman ya falfalo da gudu izuwa kansa yai sama yana mai daga takobinsa domin ya soke cikin sa maza gudu.A wannan lokaci sa maza gudu bazai iya kare kansa ba saboda ko kada babu karfi a jikinsa idanunsa ma lumshewa sukeyi yana gani dishi dishi.Koda Hibairu ya hango abinda ke shirin faruwa sai ya falfalo da azababben gudu ya dako wawan tsalle daga inda yake tamkar an harbo shi daga cikin BAKA.Saura kiris tsinin takobin Lahaman ya tsire sa maza gudu sai kawai akaga Hibairu ya doki kirjin Lahaman da kafarsa guda saboda karfin duka saida Lahaman yayi baya tamkar an janyeshi da majaujawa kuma ya fado kasa a galabaice ya furzar da gudan jini daga bakinsa.A sannan ne Hibairu ya diro da kafafunsa ya dubi Yarima Lahaman yace ka karya dokar gasa kayi yunkurin kashe abokin gwaminka yayin da lokacinku ya cika.Kaje likitanka yayi maka magani kuma ka sami hutu sannan kazo muyi wasan karshe.Koda jama'a sukaji wannan batu na Hibairu sai suka rushe da ihu gami dayi masa jinjina shi kuwa yarima Lahaman bakin ciki ne ya turnuke shi ya mike tsaye a fusace ya nuna Hibaiur da dan yatsa yace zanje na dawo nayi maka alkawari sai nayi maka kisan gilla irin wanda ba'a taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa ba.Yana fadin hakan saiya juya ya fice daga cikin filin gasar ya nufi inda likitansa ke zaune.Shi kuwa jarumi Sa Maza Gudu tun sa'adda yaga Hibairu ya ceci rayuwarsa a lokacin da Yarima Lahaman ya dako tsalle zai tsire shi da takobin a ciki.Mamaki ya turnuke shi saboda bai taba zaton cewa akwai ranar da wannan babban makiyansa zai iya yi masa wani taimakon ba.Nan take jikin sa maza gudu yayi sanyi kuma ya kurawa Hibairu idanun kawai yana mai tambayar kansa a cikin zuciyarsa yace waishin su wadannan ma'abota addinin musuluncin wace irin zuciya ce dasu haka mai tausayi da imani?Yana cikin wannan tunani ne yaga Hibairu ya durfafo shi koda ya iso gareshi saiya kama hannayensa ya tashe shi tsaye sannan ya goyashi a bayansa yakai shi har inda likitansa yake yana kwalawa likitan kira cikin tsawa akan ya gaggauta yi masa magani.Saida Hibairu yaga an gama dinke raunikan jikin sa maza gudu ansa masa magani sannan ya juya zai koma cikin filin gasa kawai sai Hibairu yaji sa maza gudu ya riko hannunsa.Cikin tsananin mamaki ya juyo ya dubeshi sai yaga yanayi masa murmushi kuma hawaye na zuba a idanunsa.Sa maza gudu ya dubi Hibairu yace sai yau ne na tabbatar da cewa makiya na iya zama masoyi,yakai Hibairu ina neman gafara a gareka bisa duk abubuwan danayi maka kuma halaiyarka da karfin imaninka akan addininka sunsa yanzu take nayi imani da ubangijinka maza ka shigar dani

Chapter 18 of 19