Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita kuma ya takarkare ya kwarara Kabbara mai karfi,Hatta jarumi Sa maza gudu baisan sa'adda ya fadi kasa ba Saboda tsananin razana da mamaki bisa ganin irin gagarumin karfin da Hibaiur ya samu wanda ko a tarihin SADAUKAN DUNIYA bai taba jin mai irin saba.Nan take fadar ta yamutse gaba dayan dakarun sarki Zaldasi suka zare takubbansu suka afkawa Hibairu aka ruguntsume da azababban yaki.Shidai Hibairu sarkokin dake hannayensa ne suka zamo makamansa ya rinka kare sara yana kai naushi dasu,bama mutum ba ko dirkar gini Hibairu ya nausa take take karyewa ta zube kasa.Wohoho bala'i da masifa ba'a sa musu rana tabbas duk wanda kaji yana cewa Allah ya kawo yaki to baisan shi ba domin kuwa shi yaki masifa ce wacce ke shafar kowa da komai.Sakamakon rushewar da gidan sarautar keyi diraka manya manya na fadawa kan gidajen birnin sai suma sauran gidajen mutune suka kama rushewa sai gashi mutane maza da mta yara da manya na hallaka a cikin gidajen.Hakan ne kuma yasa haddasa gagarumar girgizar kasa saboda tun fitowar manyan dirkokin gini daga cikin karkashin kasa bai bama mutane ba hatta dabbobi da tsuntsaye guje guje suka kamayi suna neman tsira amma tsiran ya gagara mutuwa ce kawai ke cin kasuwarta.A wannan lokaci da kyar sarki Zaldasi da Jarumi Sa Maza Gudu suka ruga izuwa kan wani katon mumbari suka zare takubbansu suka zuba ido suma kallon yadda karshen gumurzun Hibairu zai kasance da dakarun sarki.Babban abinda yafi daga musu hankali shine Hibairu cigaba yake da ragargazar dakarun domin duk inda yasa gabansa saidai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona.Koda ganin haka sai sarki Zaldasi ya dubi Sa maza gudu cikin alamun karayar zuciya yace idan muka cigaba da zuba ido nan da kankanin lokaci Hibairu zai gama da gaba dayan dakarunka.Bamu da wani zabi wanda yafi mu hada karfi da karfi mu yaki Hiabairu mu jarraba sa'armu akansa,amma tabbas wannan siddabarun nasa yafi gaban sanina da tunanina.Koda gama fadin hakan sai duk su biyun suka daka tsalle sama daga kan mumbarin da suke suka dira a gaban Hibairu suka rufeshi da sara da suka amma sai sukaga yana tare dukkan hare haren nasu cikin bakin zafin nama da jarumtaka taban al'ajabi yana mai maida musu da martani.Nanfa aka rasa daya daga cikinsu wanda zai iya koda shafar jikinsa kuwa duk da irin tsananin jarumtakarsu da iya yakinsu sai gashi da kyar suke iya kare naushinsa da bugunsa.Ana cikin hakane Hibairu ya shammacesu ya daka tsalle sama ya doki fuskokinsu da kafafunsa.Saboda karfin wannan bufu dayayi musu saida kowannensu yayi katantanwa a sama sau uku sannan suka fado kasa suka kife da rub da ciki jini na yoyo ta cikin hancinsu da bakinsu a cikin tsananin galabaita.Adaidai wannan lokaci ne ragowar tsirarun dakarun sarki Zaldasi da suka rage a filin dagar suka yarda makamansu sukayi saranda bisa ganin sarkinsu zube a kasa wanwar.Kawai sai Hibairu ya hango Gimbiya Lasmin ta fito da gudu daga cikin gidan sarautar ta nufo inda yake kuma gashi kasa na cigaba da girgiza tana zabtarewa gidaje na cigaba da rushewa tana neman ta hallaka.Koda sarki Zaldasi ya dago kai ya hango yarsa ta nufo inda suke sai yayi lambo saida tazo daf dashi sannan ya mike tsaye zumbur ya shakota ya dora kaifin takobinsa akan wuyanta ya dubi Hibairu yace idan ka sakeyin wani yunkuri saina kasheta.Koda jin haka sai jikin Hibairu yayi sanyi ya tsaya cak a inda yake ita kuwa gimbiya Lasmin saita dubi Hibairu tace kada ka yarda dashi karye yakeyi bazai iya kasheni ba saboda nice kadai yarsa a duniya kuma babu abinda yake so sama dani.Kawai kazo ka kashe shi tunda nasan cewa har abada bazai karbi addinin gaskiya ba kuma zai taba daina zalunci ba.Koda jin haka sai sarki Zaldasi ya yanki cinyar Lasmin da takobinsa wajen ya dare jini yayi tsartuwa ta kurma ihu sakamakon tsananin zafin da taji.Sarki Zaldasi ya kara shake mata wuya da hannaunsa kuma ya bushe da dariya sannan yace ke yarinya ashe kin manta da abinda na gaya miki kenan a baya cewa zan iya hakura da komai nawa akan na rasa karagata,raina da addinina.Na rantse da darajar iyayena idan Hibairu yayi wani yunkuri saina kasheki.Ki sani cewa ke idan na rasaki zan iya samun wata yar anan gaba,raina,mulkina da addinina kuwa idan na rasasu a yanzu bazan sake samunsu ba,kai jarumin jarumai maza ka mike tsaye da sauri ka yiwa wannan babban makiyi namu kisan gilla a gaban idanuna.Koda jin haka sai Sa Maza Gudu ya mike tsaye zumbur da dukkan karfinsa yana mai kwarara uban ihu gami da goge jinin dake yoyo a hancinsa.Kawai saiya daga takobinsa sama ya rugo izuwa inda Hibairu ke tsaye.Kaico hakika SO masifa ne,duk da cewa Hibairu yasan cewa ga sa maza gudu nan ya durfafoshi zai hallakashi ko waigawa bayansa baiyi ba kawai saiya kurawa Gimbiya Lasmin idanu yana yi mata kallon karshe domin ya saddakar da rayuwarsa don ceton tata,ita kuwa Lasmin a lokacin data kurawa Hibairu idanu hawaye ne yake zubo mata saboda tuni ta gama aiyana abinda zatayi don ceton rayuwar Hibairu ta hanyar sallama tata rayuwar.Ashe tuni Lasmin ta kula da cewa bayansu inda suke tsaye ita da sarki Zaldasi rami ne mai zurfi wanda ya samu sakamakon girgizar kasar da akayi kuma cikin can rami duwatsu ne da karyayyun itatuwa wanda indai mutum ya fada kansu dole ne ya hallaka.Shi kuwa Hibairu abinda ya daure masa kai shine Lasmin Murmushi takeyi masa duk da cewar tana zubar da hawaye a idanuwanta.Koda ya rage saura baifi taku biyar ba Jarumi Sa Maza Gudu ya riske Hibairu sai gimbiya Lasmin ta danno mahaifinta baya da dukkan karfinta nan take duk su biyun wato ita da sarki Zaldasi suka fada cikin wannan rami suna masu tsandara uban ihu,adaidai wannan lokaci ne sa maza gudu ya dako tsalle sama ya daga takobinsa sama da nufin ya sare kan Hibairu amma dayaga masoyiyarsa ta fada cikin wannan rami tare da mahaifinta saiya kasa aiwatar da nufinsa bai san sa'adda ya saki takobinsa ba ta fado kasa shima ya diro kasa ya kama ihu ya fashe da matsanancin kuka.Shima Jarumi Hibairu baisan sa'adda ya kwala ihu ba kuma ya rugo da gudu izuwa bakin ramin yana lekawa kasan ramin saiya hango gimbiya Lasmin da sarki Zaldasi a mace dirakan gini sun soke kirazansu.Kawai sai Hibairu ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa ya fashe da matsanancin kuka,jarumi sa maza gudu ya karaso bakin ramin dakyar koda ya leka ya hango gawar Lasmin saiya sake kwala ihu a karo na biyu kuma ya fashe da kuka ya zamana cewa duk su biyun suna tayin kuka ba sassauci tamkar ba zasu daina ba.(Tsananin Tausàyi Nima Yasani Hawaye)Saida suka shafe sama da sa'a guda suna kuka gami da begen masoyiyarsu sannan jarumi sa maza gudu ua dago kai ya dubi Hibairu cikin tsananin kiyayya da bakin ciki yace yakai abokin gaba kayi sani cewa masoyiyata ta sallama rayuwarta ne domin tserar da taka wannan ya nuna cewa tana kaunarka fiye da kowa da komai a wannan duniya.Tabbas ka dasa mini bakin cikin da babu abinda zai gusar mini dashi har abada,daga nan har izuwa karshen rayuwata,ka sani cewa yanzu ne wutar gaba a tsakanina dakai zata fara ruruwa kuma babu wani ruwa dazai iya kasheta a cikin wannan duniya komai yawansa da karfinsa.A yau babu sauran yaki a tsakanina dakai zan jira wani lokacin daya dace anan gaba idan mun sake saduwa.Ka sami nasarar yada addininka a wannan birni amma nayi murna daya kasance a dalilinka jama'ar wannan gari sun rasa dubunnan rayuka ba zasu taba mancewa dakai ba.Koda gama fadin hakan sai jarumi sa maza gudu ya mike tsaye a bakin ramin ya sake kurawa gawar Lasmin idanu yana mai cigaba da zubar da hawaye izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma saiya juya ya nufi hanyar fita daga cikin birnin gaba daya.Nanfa Hibairu ya bishi da kallo harya kule ya bace masa da gani.Sannan shima ya juya ya kurawa gawar Lasmin idanu.Nan take hawaye ya subuto masa ya daga kansa sama yace ya Allah ga Lasmin nan baiwarka ce kuma ta karfi addininka kafin mutuwarta amma gashi ta kashe kanta domin ceton tawa rayuwar.Allah kaine maiyin rahama ga bayinsa,kai kasan irin hukuncin da zakayi mata,ka gafarta mata da irin gafararka.Koda gama fadin hakan sai Hibairu ya mike tsaye ya nufi inda mutane suka nutse a cikin kasa ya taimaka wajen tono su saida dare ya raba har gari ya waye ana tonosu daga cikin karkashin kasa.Wasu a mave ake tonosu wasu kuma a kakkarye wandasu dauke da raunika.Bayan an kammala wannan aiki ne an binne gawarwaki kuma an yiwa marasa lafiya magani sannan jarumi Hibairu ya tara gaba dayan mutanen birnin ya kadamar da addinin musulunci a kofar gidan sarautar.Daga wannan rana Hibairu ya zauna a birnin har tsawon wata uku yana koyar da mutane ibada gami da ilmin addinin musulunci.A tsawon wannan lokaci ne mutanen birnin Misra suka gane cewa ashe da a cikin muguwar rayuwa suke ta bakin jahilci da zalunci da kuma kazanta suka gane cewa addinin musulunci shine addinin dayafi dacewa da dukkan al'ummar duniya saboda adalcinsa.A lokacin ne kuma jama'ar suka shaku ainun da jarumi Hibairu suka kaunace shi ainun don haka sai suka bukaci daya zauna ya zama sarkinsu.Koda jin wannan batu sai Hibairu ya kwashe tarihin rayuwarsa ya zaiyane musu da kuma dalilin da yasa ya baro kasarsa da iyayensa.Bisa dole mutanen birnin Misra sukayi bankwana da Hibairu suna kuka shima yana kuka suka rakoshi har karshen gari ya hau dokinsa ya nausa cikin daji suna kallonsa har saida ya bace musu da gani.Lokacin da Jarumi Hibairu yazo nan a cikin labarin da yake baiwa sarki Kamzal da 'yarsa Gimbiya Zuhura saiya duk su biyun suna zubar da hawaye saboda tausayinsa gami da abin al'ajabin dake cikin labarin.Sai bayan kimanin dakiku arba'in da biyar sannan sarki Kamzal ya dago kai ya dubi Hibairu a lokacin da yayi ajiyar zuciya sannan yace yakai wannan babban jarumi kayi sani cewa wannan labari naka dana ji izina ne ga dukkan sarakunan duniya da kuma duk wanda yake ja da ubangijinka da kuma addininka.Tabbas nayi imani da ubangijinka kuma lallai zan kaddamar da wannan addinin naka a birnina bayan an kammala wannan gasa dana shirya,yanzu dai kaga yadda kukayi ragas da jarumi sa maza gudu ya zamana cewa saura kiris duk ku biyun ku rasa rayukanki.Shin kana ganin cewa nan gaba zaka sami nasara a kansa?Koda jin wannan tambaya sai gimbiya Zuhura tayi caraf ta tari numfashin sarki Kamzal tace haba yakai Abbana idan har kana yin shakka akan nasarar Hibairu akan sa maza gudu tamkar kana shakku ne a kan addininsa da ubangijinsa.Ni yanzu inaso na yi wata magana da Hibairu inda bazaka damuwa ba.Koda jin haka sai sarki Kamzal yayi murmushi kawao saoya mike tsaye ya basu wuri ba tare da uffan ba.Koda Gimbiya Zuhura taga mahaifinta ya fice daga cikin turakar ya barsu su biyu kadai saita dubi Hibairu cikin murtuke fuska tace menene tsakaninka da gimbiya Malika?Koda jin wannan tambaya sai Hibairu yayi murmushi yace kwantar da hankalinki Gimbiya ki ajiye kishinki a gefe daya ki sani cewa babu komai a tsakanina da Malika face tana bukatar kawai na koya mata yaki domin ta kare kanta daga sharrin dan uwanta Yarima Lahaman wanda ke kokarin ganin bayanta da kuma bayan Masoyinta.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Zuhuta tace wanene wannan masoyin nata kuma me yasa dan uwanta Yarima Lahaman yake son ganin bayansu?Sa'adda Hibairu yaji wannan tambaya sai yayi doguwar ajiyar zuciya sannan yace labari ne mai tsawo amma kiyi mini hakuri yanzu ki bari sai bayan an gama wannan gasar jarumtaka sannan zan baki labarin.Koda gama fadin hakan sai Hibairu ya yunkura da nufin ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar amma sai Zuhura tayi wuf ta ruko hannunsa ta zaunar dashi kasa tace ai ban sallameka ba harda kake son ka tafi.Inason ka sani cewa nice zan maye maka gurbin marigayiya Gimbiya Lasmin don haka inason kayi mini wani alkawari guda daya.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT★SA MAZA GUDU★!!! Littafi Na Tara (9) Part A. Prince Auwal Auwzab KODA LAHAMAN YAGA YA SAMI WANNAN NASARA SAIYA DAGA TAKOBINSA SAMA YA TAKARKARE YA KWARARA UBAN IHU SANNAN YA SHIGA YIWA KANSA KIRARI YANA MAI CEWA INA RAGOWAR JARUMAN GASAR NE,IDAN SUN ISA SU SHIGO SU DUKA NI KADAI NA ISHE SU.Na rantse da karagar Ubana yanzun nan zan kashe su na lashe wannan gasa.Lokacin da Yarima Lahaman ya fara yin wannan kuri sai Sa Maza Gudu ya fusata ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa cikin tsananin fushi ya zare takobinsa ya yunkura zai ruga izuwa cikin filin gasar amma sai alkalan gasar suka sha gabansa suka hanashi.A lokacin ne suka kurawa juna idanu shida Lahaman suna harara kamar zasu cinye kansu danye.Shi kuwa Jarumi Hibairu yana tsaye kusa da Malika cikin nutsuwa ko kaduwa baiyi ba sai murmushi ma yakeyi.Ita kuwa Gimbiya Malika hankalinta yafi na kowa tashi bisa ganin cewa Yarima Lahaman shine babban makiyinta a duniya kuma gashi ya sami jarumtakar da babu mai kamarta.Lokacin da sarki Hilairu ya fahimci cewar hankalin Malika ya dugunzuma saiyazo kusa dasu ya tsaya sannan ya dubeta yace kwantar da hankalinki ya masoyiyata ni nasan cewa ko dan uwana Sa Maza gudu zai iya maganin Lahaman.Dajin haka sai Hibairu ya dubeshi yace kai ai san an gwada akan san na kwarai.Ni kaina ban taba ganin mutum mai mugun zafin nama da karfin damtse ba irin wanda Lahaman kedashi yanzu abin ma yafi gaban misali.Anya kuwa ba aikin sihiri bane wannan?Malika tayi ajiyar zuciya tace tabbas wannan aikin sihiri ne domin kuwa ni kaina nasan cewa na fishi jarumtaka ada amma yanzu bazan iya tararsa ba.Gama fadin hakan keda wuya saiga sadauki Aryan yazo garesu duk jikinsa ya baci da jini sakamakon raunikan biyar da Lahaman yayi masa a lokacin daya shiga cikin zugar dakaru dubu da suka yakeshi duk raunikan biyar an dinkesu.Cikin murna Malika ta dubeshi tace nayi murna daka tsira da rayuwarka daga hannun wannan azzalumin.Aryan ya gyada kai yace ya shugabata ai in badon na gudu ba so yayi yayi min kisan gillah ina mai shawartarku da kada ku kuskura ku cigaba da yin wannan gasa.Koda jin wannan batu sai Hibairu yayi murmushi yace babu abinda zai tsaida ni akan tunkarar kowane jarumi koda kuwa sabon jarumi zai sake baiyana wanda ya ninka Lahaman Jarumtaka sau dubu domin ubangijina dashi na dogara.Koda jin wannan batu sai sarki Hilairu ya tafi izuwa inda Sa Maza Gudu yake yazo daf dashi suka kurawa juna idanu.Nan take kowannensu idanunsa suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye kawai sai suka rungume junansu saida suka shafe yan dakiku a rungume da juna a wannan lokaci ne alkalan gasa sun ware gefe gyda suna ta tattaunawa akan yadda ya kamata su bullowa wannan gasa tunda duk tsarin gasar ya sauya bisa yadda aka shirya shi da farko.A tsakiyar filin gasar kuwa an kwashe gawarwakin dakarun da Lahaman ya kashe babu kowa a wajen sai shi kadai a tsaye ruke da takobinsa yana muzurai yagaji da surutunsa na kirari sai huci yake kamar wani rikakken zaki.Sarki Hilairu ya janye jikinsa daga cikin na sa maza gudu suka fuskanci juna sannan yace yakai dan uwana ina mai rokonka daka fita daga cikin wannan gasa domin idanuwa na bazasu iya ganin mutuwarka,ka tuna cewa bani da kowa a duniya yanzu face kai na rushe kasarmu an tarwatsa jama'armu kuma nasan cewa kaima kana da burin mu koma mahaifarmu mu sake rayata.Inason ka manta da komai da kowa kazo mu sulale mubar garin nan mu koma kasarmu.Sa'adda sarki Hilairu yazo nan a zancensa sai Jarumi Sa Maza Gudu ya bushe da dariya.Al'amarin daya sake razana Hilairu kenan lokaci guda sa maza gudu ya turbune fuskarsa ya dubi Hilairu a fusace yace kana sone muyi gudun gara mu tarar da zago,to ka sani cewa ko mun gudu sai yarima Lahaman yabimu har can kasar tamu ya kashemu ya sake baje komai kaga kenan munyi aikin banzaWaishin ma ka manta da suna na ne wato SA MAZA GUDU,har abada bazan taba gudar wani da namiji ba komai jarumtakarsa.Ina mai tabbatar maka da cewa komai jarumtakar Lahaman kuma komai karfin sihirin tsafinsa baikai na Hibairu ba.Tunda naki gudun Hibairu bazan guji Lahaman ba har sai na dauki fansar jinin matarka daya kashe da kuma jini jama'armu kasani cewa bayan na rasa gimbiya Lasmin a yanzu kuma nayi arba da gimbiya Zuhura yar sarkin wannan gari sai naji na kamu da tsananin sonta fiye da yadda ma naso Lasmin don haka dole ne kota wane hali na lashe wannan gasa.Yanzu makiya na sun zama gudu biyu wadanda babu gudu babu jada baya dole sai naga bayansu.Koda sa maza gudu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa sarki Hilairu yace ai kuwa ganin bayan wadannan jarumai biyu a wajenka daidai yake da neman jaki mai kaho.Nasani cewa bakayin magana biyu kuma duk abinda kayi niyar yi ko zaka mutu saika aiwatar dashi din haka ban isa na hanaka ba amma ina mai shawartarka daka janye gabarka akan jarumi Hibairu saboda shi bai kasance azzalumi ba kamar yadda lahaman ya kasance.Ka tuna cewa ba komai ne ya haddasa kiyayya a tsakaninku ba face Soyayya dakai dashi duk kunyi asarar wacce kuke so,shin yanzu ma kana so ne ku sakeyin asarar wacce kuke so din? Idan har soyayyarka akan gimbiya Zuhura ta gaskiya ce ai ba zaka so bakin cikinta ba ko salwantar rayuwarta,kaje kayi tunani.Koda sarki Hilairu yazo daidai nan a zancensa sai sukaga shugaban alkalan gasar ya shigo cikin tsakiyar filin gasar ya tsaya.Nan take kuwa filin gasar yayi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa saboda kowa ya saurara yaji hukuncin da aka yanke akan wannan gasa.Alkalin gasar yayi gyaran murya sannan yace yaku jama'a kamar yadda kuka gani a idanu a halin yanzu saura mutum hudu kacal suka rage a cikin Prince Auwal Auwzab Auwzab wannan gasa kuma a cikin mace guda daya ce.Maza uku,Mazan sune Jarumi Hibairu,Sa Maza Gudu da Kuma bakon jarumi Yarima Lahaman mai jarumtakar ban al'ajabi dole ne a cikin wadannan jarumai hudu a fitar da mutum biyu wadanda zasu yi wasan karshe saboda haka yanzu mu alkalan gasa mun yake hukuncin cewa yanzu gimbiya Malika zata sake karawa da Hibairu a zagaye na biyun karshe Jarumi Sa Maza Gudu zai kara da Yarima Lahaman wanda sukayi nasara sune zasuyi wasa na karshe a gobe.Koda jin wannan batu sai filin wasan ya kaure da shewa gami da ihu da tafi.Shi kuwa sarki Hilairu hankalinsa ne ya dugunzuma ainun bisa jin cewa dan uwansa zai kara da Lahaman amma a bangaren masoyiyarsa gimbiya Malika ko kadan bai damu ba saboda yasan cewa Hibairu bazai kasheta ba.Nan take batare da bata wani lokaci ba aka buga gangar fara gumurzu aka kirawo gimbiya Malika da Jarumi Hibairu don haka sai Yarima Lahaman ya fito daga cikin filin gasar ya basu wuri.Maimakon Lahaman yaje inda jaruman gasa suke tsayawa saiya nufi inda Sa Maza Gudu yake yazo daf dashi yadda suna iya jin numfashin juna suka kurawa junansu idanu cikin tsananin kiyayya da fushi har fuskokinsu nayi gyatsinewa.Lahaman yace nasan cewa ka dade kana farautata domin ka daukarwa dan uwanka da jama'arku fansa ni kuma na dade ina neman yadda zanga bayan yar uwata Malika na haye kan Karagar Ubana sai gashi na rigaku samun abinda nake nema.Ayau din nan zan kashe ka sannan na kashe Jarumi Hibairu na mallaki Gimbiya Zuhuran da kukeso ku biyun.Asannan ne zan zama GAGARABADAU kuma dodon dukkan sarakunan da jaruman Nahiya.Lallai zan sami dukiyar da babu mai irinta kuma zan shimfida mulki irin wanda ba'a taba yin kamarsa ba a duk nahiyoyin dake nan.Koda Lahaman yazo nan a zancensa sai Sa maza gudu ya bushe da dariya lokaci gudu kuma ya turbune fuska yace kai wawa ka manta da wani abu guda daya karfin damtse da karfin sihirin tsafi bashi kadai suke kai mutum ga samun nasarar abinda yasa a gabansa ba.Akwai sa'a da rabo saboda haka kasa wannan aranka ina mai tabbatar maka da cewa gobe idan muka hadu idan har ban kasheka ba kaima ba zaka kasheni ba saidai muyi RAGAS.Rana bata karya saidai uwar ya taji kunya.Gama fadin hakan keda wuya sai sukaji an buga gangar fara gumurzu a filin daga don haka sai suka juya suka fuskanci filin gasar.Malika da Hibairu na tsaye a tsakiyar filin kowannensu na ruke da takobi da garkuwa kuma tazarar dake tsakaninsu takai taku goma sha biyar.Koda sukaji an buga gangar fara gumurzun sai suka rugo da gudu izuwa kan junansu suka kacame da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro domin nan take suka rinka kaiwa junansu sara da suka da dukkan karfinsu sai kace dama can sun kasance tsofaffun abokan gaba masu farautar rayukan juna.Koda ganin yadda sukayin wannan gumurzu sai hankalin sarki Hilairu ya dugunzuma saboda bai taba zaton cewa hakan zasuyi wannan yaki ba domin a koyaushe dayansu zai iya cutar da wani amma koda suka shafe yan dakiku suna fafatawa sai yakin ya sauya salo.Domin nan take karfin saran Hibairu ya danne na Malika ya zamana cewa da kyar take iya karewa kuma bata iya maida martani.Ana cikin hakan ne Hibairu ya shammace ta ya daka tsalle sama ya gabza mata wani wawan naushi a fuskarta da kafarsa.Saboda karfin naushin saida tayi katantanwa a sama sannan ta fado kasa ta baje sumammiya.Koda ganin haka sai filin ya kaure da shewa gami da tafi aka rinka yiwa Hibairu jinjina.A guje likitoci suka shigo cikin filin suka tsaya akan Malika amma anan aka yayyafa mata ruwa saida ta farfado kuma ta mike zaune zumbur tana mai goge jini akan hancinta.Koda Sarki Hilairu yaga ta mike tsaye saiya cika da farin ciki.Nan take Malika ta mike tsaye da kafafunta ta fice daga cikin filin gasar.Nan dai filin gasar ya watse jama'a suka tafi suna ta tattaunawa akan gasar karshe da za'ayi ta gobe wasu suna cewa ai tabbas Yarima Lahaman ne zai lashe wannan gasa wasu suna cewa ai Hibairu ne zai lashe gasar wasu kuma suka rinka cewa ai saidai an ga abinda ya faru tsakanin Lahaman da sa maza gudu tukunna kafin ayi wasa na karshe.Lokacin da sarki Kamzar tare da yarsa Gimbiya Zuhura suka isa cikin gidan sarautar sai duk suka tsaya cak a inda suka saba rabuwa domin kowa ya tafi izuwa turakarsa.A tare suka dubi junansu suna mamakin dalilin da yasa suka kasa tafiya kawai sai sarki ya dubeta yace yake yata waishin menene yake yawo a cikin zuciyarki?Lallai akwai magana a cikin bakin nan naki.Ashe har akwai wani abu da zaki iya boye min?Sa'adda gimbiya Zuhura taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya sannan ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace yakai abbana kayi sani cewa tunda aka shirya gasar jarumtaka a duniya ba'a taba shirya mai hadarin wannan ba.Nayi bincike na gano cewa idan wannan bakon jarumi wato yarima Lahaman ya lashe wannan gasa to gaba dayan kasashen dake nahiyoyin sai sun zama a karkashin mulkinsa yanzu babu wata dabara da kake ganin zamuyi

Chapter 17 of 19