Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a duk sa'adda kishirwa ta kamashi,abinda na lura dashi shine mu kacal ne kacal bamu sha ruwa ba kuma bamu ci abinci ba tunda aka fara gudun.Su kansu sauran manyan jaruman gasar ma wadanda suka kasance jajirtattu kuma zakwakurai sunyi matukar mamakin yadda akayi ni da Sa Maza Gudu muka jure wannan gudu na tsawon sa'a tara da rabi ba tare da mun tsaya mun huta ba ko munci abinci ko shan ruwa alhalin suma da yawansu saida suka rinka tsayawar.Lokacin da muka iso daidai wurin nan inda nayi arba da zaki Nurul Maut sai nayi turjiya na tsaya cak,dama nine kan gaba sai Sa Maza Gudu na biye dani da tazarar kamu uku kacal sai kuma sauran jaruman gasar wadanda adadinsu bai wuce mutum saba'in ba,alhalin da farko mun kai mu dubu goma sha da yan daruruwa,a can bayanmu kadan kuwa alkakan gasa ne su dari biyu bisa dawakai.Gaba dayan wadanann alkalan gasa basu gaji ba saboda kasancewarsu akan dawakai suke,kuma kowannensu bai fuskanci matsalar yunwa da kishi ba,amma dawakansu a jigace suke kuma sa'ar da sukayi a daidai inda aka tsaya din akwai wata katuwar korama don haka sai suka kama shan ruwan a cikinta.Har Sa Maza gudu ya giftani zai ci gaba da gudu zuwa gaba saiya fasa ya dawo da baya ya dubeni cikin nutsuwa yace,naji ance kuma ma'abota addinin musulunci bakwa yin karya kuma kuna da rike amana gami da cika alkawari saboda haka inason ka gaya min gaskiya,menene dalilin da yasa kayi turjiya anan ka tsaya?Koda jin wannan tambaya sai nayi dan guntun murmushi a gareshi nace,zakin da muke nema mu kashe yanan adaidai nan wurin dana tsaya kuma a koyaushe zai iya baiyana a garemu.Koda jin wannan batu sai kowa ya zare takobinsa,masu mashi suka rike da kyau,masu baka suka dana kibiyoyi aka kama kalle kalle na sama da kasa,gabas da yamma,kudu da arewa domin a gata ta inda zaki Nurul Maut zai fito a afka masa.Tsawon yan dakiku banji wannan gurnani ba wanda naji a dazu a farkon shigota dajin,al'amarin dayayi matukar bani mamaki kenan.Shi kuwa Sa Maza Gudu saiya dubeni a fusace ya daka mini tsawa yace,ta tabbata gaskiya cewa ku makaryata ne kuma mayaudara,ina zakin yake?kace damu anan yake,kafin Sa Maza Gudu ya gama rufe bakinsa sai mukaji wannan gurnani danaji nan take da yawa daga cikin jaruman gasar suka firgice suka zube a kasa tamkar an zare musu dukkanin karfin jikinsu,wasu kuwa saboda tsananin razana da sukayi kamewa sukayi a tsaye kamar gumaka.Wasu kuwa basu san sa'adda suka fara sakin fitsari ba a wando alhalin suna kiran kansu JARUMAI.Kalilan ne daga cikin jaruman suka iya zare makamansu na yaki suna kalle kalle da dube dube don ganin ta inda zakin zai bullo saboda kowa jikinsa ya bashi cewa lallai wannan gurnani bana komai bane face na ZAKI NURUL MAUT.Tsawon yan dakiku zaki bai bayyana ba,kuma ba'a sake jin gurnaninsa ba.Kwatsam sai akaji wadansu jaruman gasa kimanin su ashirin sun kwarara uban ihu.A firgice su Hibairu suka waiga suka dubesu,kawai sai sukaga ashe wani irin mugun haske ne ya faso gadon bayansu ya burma cikinsu saiga hanjin cikinsu na zubowa kasa.Dukkaninsu suka kife kasa matattu.Koda ganin wannan al'amari sai ragowar jaruman gasa da alkalan gasa dake can bayansu kadan suka firgita suka kama ihu da guje guje kowannensu ya rasa ma inda zai shiga ya buya saboda kidimewa har karo sukeyi da juna suna faduwa wasu kuma suka rinka karo da bishiyoyi,duwatsu,suna samun mugayen raunika wanda suka rinka zama sanadin ajalinsu.Wasu kuwa cikin ramuka suka rinka shigewa duk da cewa ma basu san ma menene a cikin ramin ba.Hakika idan masifa takai masifa hankali gushewa yake kuma indai mutum yaga ajalinsa tofa zai iyayin komai danganin ya tsere masa.Wasu daga cikin jama'ar da suka shigo cikin wannan daji sai gasu suna falfala mugun gudun da basu tabayin kamarsa ba a rayuwarsu tamkar zasu tashi sama.kash duk wannan kokari da mutane suka rinkayi domin su tsira da rayuwarsu duk sai ya zamo na banza saboda saidai kawai kaga haske ya burma ciki da kirjin mutum ya fadi kasa a sa'adda yake falfala gudu,ko kuma kaga an zaro mutum daga cikin ramin daya buya komai zurfin ramin an kwakule komai na cikinsa anyi jifa da gawarsa babu kyan gani.Nanfa zaki Nurul Maut ya cigaba dayin mummunar barna yayi ta kashe jama'ar da suke shigo cikin wannan daji suna zubewa kasa mattatu tamkar ana sassabe a gona.Duk wannan bau dake faruwa Jarumi Hibairu da Sa Maza Gudu na tsaye a waje daya kyam suna kallon duk abinda yake faruwa.Sudai basuyi yunkurin guduwa ba kuma basu zare takubbansu ba domin su yaki zaki Nurul Maut.Ko Jarumi Hibairu yaga zakin yana ta kashe dubunnan daruruwan mutane sai ya kamu da tsananin tausayi har idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye,shi kansa yasan cewa Allah ne kawai ya kubutar dashi daga sharrin wannan zakin sakamakon addu'o'in da yake ta karantawa a ransa.Koda ya kura da Jarumi Alkas wato Sa Maza Gudu sai yaga shi kuma ashe wadansu kalmomin tsafi yake ta karantawa a fili ma har yana iya jiyo sautin kalmomin kuma duk da haka a tsorace yake domin kafafunsa na karkarwa.Duk sa'adda zakin ya yunkura kamar zai afkawa Sa Maza Gudu sai ya fasa ya sake afkawa sauran jama'a kuma ko kadan ma baya kusantar inda Jarumi Hibairu ke tsaye domin da zarar ya doshe shi sai yaji kamar jikinsa zai narke saboda wani azababben hucin zafi da yake fesowa.Lokacin da zaki Nurul Maut yacigaba da kashe jama'a ya zamana cewa ya kashe kusan kaso daya da rabi daga cikin kaso shida na jama'ar da suka shigo cikin dajin sai hankalin Jarumi Hibairu ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa bai san sa'adda ya yunkura ba cikin zafin nama ya kwala kabbar da karfi a fili.Faruwar hakan keda wuya zaki Nurul Maut ya fadi kasa,amma saiya mike da sauri ya tsaya cak a inda yake ya kuma ya rikide ya zama haske kuma ya kuwa Hibairu idanu yana wani irin gurnani mai ban tsoro fiye da wanda yakeyi.shi kuwa sa maza gudu sai ya noke ya zubawa Jarumi Hibairu idanu yaga abinda zai faruwa.A cikin zuciyarsa yana cewa ya samu tsuntsu daga sama gasasshe,kawai zai jira Hibairu ya kashe zakin sannan shima ya kashe shi ya dauki gawar zakin yaje ya kaiwa sarki Zaldasi kuma ya cinye gasa.Haka akayi kallon kalo tsakanin Zaki Nurul Maut da Jarumi Hibairu tsawon yan dakiku sai kowannensu ya rugo da gudu izuwa kan juna cikin mugun nufi.koda ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu duk su biyun suka daka tsalle sama tamkar an harbo su daga cikin baka.Shidai Zakin wangame bakinsa yayi da nufin ya danki wuyan Hibairu ya luma masa hakoransa akai,shi kuma Hibairu takobinsa ya daga sama yakai masa wawar suka a ciki.Wani ikon na Allah suna haduwa a saman sai ya zamana cewa babu wanda ya sami nasarar aiwatar da abinda yayi nufi,domin lokacin da zakin ya kawowa Hibairu cizo da hakoransa a wuya sai ya goce cikin zafin nama,zakin ya kadeta tayi tsalle can gefe daya ta fadi suka rukunkume juna a saman suka fado kasa tim kuma suka kacame da kokowa wannan ya danne wannan wancan ya juye da wannan,sukayi ta birgima a kasa kowannensu na kokarin kashe dan'uwansa.Koda Sa Maza Gudu yaga irin gagarumar jarumtakar da Hibairu keyi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya fuskanci cewar tabbas zai iya kashe wannan zaki,bisa sa'a kwatsam kuma sai yji motsin sawun dawakai a bayansu a firgice ya waigo sai yaga ashe wadannan alkalan gasa ne guda biyu masu shegen naci da taurin rai tsaye a bayansu,su biyu rak suka rage a wajen basu gudu ba alhalin dasu da dawakan nasu duk manyan raunika ne a jikinsu,jini na zuba amma sun zuba ido suga yadda Hibairu zai kash wannan zakin domin suje sukai labari.Nanfa hankalin Sa Maza Gudu ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ya kamata yayi,shidai a rayuwarsa baya cin zarafin wanda bai takaleshi ba,don haka baya son ya kashe wadannan alkalan gasa amma kuma yanzu idan ya barsu da rai ya kasance Hibairu ne ya kashe wannan zaki a gaban idanunsu zasuje sukai labari.Koda gama aiyna hakan a cikin zuciyarsa sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama ya kaiwa zakin wawan sara a gadon baya,maimakon takobin ta tsarge zakin gida biyu sai ta karye ta rabe biyu,wata irin karace tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu.A fusace zakin ya juyo ya mangare Sa Maza Gudu da hannu daya yayi tsalle sama can da bya ya fado kasa yana man jini domin kirjinsa zakin ya nausa da mugun karfi,nan fa sa maza gudu yaji kamar kirjin nasa fadowa kasa zaiyi saboda mugun radadi da zogin da yakeji.Don haka sai ya kasa mikewa tsaye bare yaje yacigaba da taimakon Hibairu wajen yakar zakin.Haka dai Hibairu da zaki Nurul Maut suka cigaba da yin bakin gumurzu a kasa ya zamana cewa zakin yana samin nasarar kartar sassan jikin Hibairu da faratan hannunsa yanayi masa raunkia a jiki,shi kuma ya rinka samin nasarar gabzawa zakin mugayen naushi harma yayi sa'ar fasa kwayar ido guda ya tsiyaye nan take.Saidai suka shafe sa'a guda suna wannan fafatawa ya zamana cewa karfi ya kusan zuwa daya domin kowannensu ya jigata ainu,har takai cewa da kyar suke motsawa.A na cikin hakanne Hibairu ya fahimci cewa indai suka cigaba da wannan gumurzu a haka to tabbas zasu iyayin RAGAS,saboda jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin dake zuba a kansa.Koda gama aiyana hakan kuwa sai ya shiga yiwaAllah kirari a fili yana mai cewa Ya ubangijin Musulinci ka karfafeni da karfinka ka bani sa'a da nasara akan wannan zaki.Koda wadannan alkalan gasa guda biyu da suka rage sukaji Hibairu na ambaton ubangijin musulunci sai suka cika da tsananin mamaki kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun.Ba komai ne ya basu mamaki ba face sun gane cewa ashe duk wadannan gagarumin karfi da Hibairu yake amfani dashi akan sihirtaccen zakin nurul maut ba karfinsaa bane na sihiri,karfin ne daga abin bautarsa ubangijin musulunci.Abind a ya dugunzuma hankalinsu kuwa shine da wane bakin zasuje su gawaya sarki Zaldasi cewa da karfin ubangijin musulunci Hibairu ya sami nasarar kashe wannan zaki alhalin sarki zaldasi ya tsani musulunci da musulmai kamar yadda ya tsani mutuwarsa kai ko labari ya samu cewa ma'abota addinin musulunci zasu gifta ta gefan birninsa turawa yake a kashe mazajensu a kamo matansu a matsayin bayi,dukiyarsu kuwa ta zama ganinma.Kwatsam ba zato ba tsammani sai Alkalan gasar biyu da sa maza gudu sukaga Hibairu ya suri kafafun zakin na baya ya kama hajijiya dashi a sama,take sa maza gudu ya gano cewa hibairu so yake ya fyada zakin akan wani katon dutse dake daf dashi,idan kuwa ya sani nasarar yin hakan take kan zakin zai dagargaje ya mutu,cikin hanzari ya mike tsaye zumbur ya ruga izuwa inda takobinsa take ya sureta ya sake rugowa izuwa inda Hibairu ke gumurzu da zakin.Adaidai wannan lokaci ne Hibairu ya maka kan zakin akan wannan katon dutsen kuma a sannan ne sa maza gudu ya dankawara zakin sara a gadon bayansa ya tsargeshi biyu,sai gashi kan zakin ya dagargaje kuma gangar jikinsa ta rabe biyu.Nan fa gardama ta sarke a tsakanin Hibairu da sa maza gudu kowannensu na cewa shine ya kashe zakin.Adaidai wannan lokaci ne wadannan alkalan gasa suka yunkuro da dawakansu suka karaso daf dasu Hibairu suka sauko daga kan dawakansu suka shiga kokarin tsayar da jinin dake zuba a jikinsu domin su ceto rayuwarsu sakamakon mugayen raunikan dake jikinsu.Dawakan na suma sarewa sukayi suka fadi kasa suna kakarin mutuwa saboda duk jikinsu a cike yake da rauninkan da reshinan bishiyoyi sukayi musu a lokacin da dajin ya hargitse kowa na gudun ceton ransa.Har izuwa wannan lokaci jarumi hibairu layi yake yi domin jiri bai daina dibarsa ba saboda jinin dake zuba.Koda sa maza gudu ya dubi hibairu da wadannan alkalan gasa yaga halin da suke ciki,ya tabbatar da cewa shine kadai mai cikakkiyar lafiyar dazai iya komawa can bakin dajin dauke da gawar wannan zaki indasu sarki zaldasi suke kafa sansani,sai ya bushe da dariyar farinciki ya dubi alkakan gasa yace,yanzu zan dauki gawar wannan zaki na tafi tare daku gaban sarki ku shaida masa cewa nine na lashe wannan gasa.Koda jin wannan batu sai alkalan gasar suka zazzaro idanun kuma suka dubi jarumi sa maza gudu cikin alamun rashin gamsuwa,daya daga cikinsu yace,yaza'ayi kace kaine ka kashe wannan zaki alhalin kafin kaifin takobinka ya dira a kan gadon bayan zakin tuni Hibairu ya maka kansa akan dutse ya dagargaje kaga kenan shine ya kashe zaki bakai ba,kuma dole ne muje mu bayar da shaidar hakan.Kafin wannan alkalin gasa ya gama rufe bakinsa tuni sa maza gudu ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa ya ce ashe kuwa daku da hibairu duk zaku mutu anan ni kadai ne zan koma sansani a raye dauke da gawar nurul maut.Koda gama fadin hakan sai sa maza gudu ya ruga da gudu izuwa kan wadannan alkalan gasa ya daka tsalle izuwa samansu yakai musu wawan sara da takobinsa da nufin ya fille musu kai kawai sai yaji an doki kirjinsa da wani irin wawan mugu.Saboda karfin dukan saida yayi sama da baya ya fado kasa tim a cikin galabaita yana dafe da kirjin nasa sakamakon mugun zafi da radadi dayaji.Yana dago kansa yaga ashe jarumi hibairu ne yayi masa wannan wawan bugu kuma yana tsaye a kansa rike da takobi tamkar jiri baya dibarsa alhalin har a sannan jiki bai daina diga ba daga cikin raunikan sassan jikinsa.Jarumi Hibairu ya dubi sa maza gudu a fusace yace,rai da ajali duk a hannun ubangijin musulunci suke don haka kai baka isa ka kashe mu ba face da yardar ubangijina,ina mai tabbatar maka da cewa indai ina numfashi a doron kasa baka isa ka kwace gawar wannan zaki ba bare har ka cika burinka na lashe wannan gasa saidai dayanmu ya rasa rayuwarsa a nan ko kuma muyi ragas.Koda jin wannan batu sai jikin sa maza gudu yayi sanyi saboda ya fuskanci cewar lallai abinda hibairu ya fada zai iya faruwa hakan.cikin kankantar da kai kuma cikin karamar murya sai sa maza gudu yace,yakai abokina kayi sani cewa nasan abindake cikin ranka kuma nasan babban dalilin da yasa ka shiga wannan gasa.Ka shigeta ne bawai don ka mallaki gimbiya Lasmin ba ko don ka mallaki dukiya ko mulki ba,sai domin kawai ka sami damar yada addininku na musulunci,abinda daya gagareku kenan tun iyaye da kakanni tsawon shekara da shekaru,ni kuwa bani da burin da yafi na mallaki gimbiya Lasmin saboda tun ban fi shekara shida ba a duniya na kamu da tsananin sonta kuma nake fama da begenta dare da rana,bani da wata dama ta mallakarta face wannan,ina mai rokonka daka taimaka mini ka barni na zama zakaran wannan gasa don cika burina ni kuma nayi maka alkawarin cewa da zarar na auri gimbiya Lasmin zan karbi addininka kuma na jaddashi a nan birnin.koda kuwa yin hakan zai janyo na yaki sirikina sarki zaldasi tare da taimakonka.Lokacin da jarumi sa maza gudu yazo nan a zancensa sai jarumi hibairu yaji kamar ya daure shi da jijoyoyin wuyan jikinsa,don haka sai yayi shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon yan dakiku daga can sai ya dago kai ya dubi sa maza gudu yace,babu yanda za'ayi na baka yardata da amincina saboda zaka iya yaudarata ka zamo mara alkawari,ka sani cewa kamar uadda kake tsananin son gimbiya Lasmin to nima yanzu na kamu da tsananin sonta har takai cewa dare da rana ina ganinta a cikin barcina da zahiri tamkar tanayi min fatalwa.idan bazaka iya rungumar kaddara ba ka yarda dacewa nine na lashe wannan gasa to kayi duk abinda zakayi wanda kake ganin cewa shine zai fissheka.Sa'adda Jarumi Hibairu yazo nan a zancensa sai sa maza gudu ya gyara tsayuwarsa kuma ya murtuke fuskarsa ya fuskanci hibairu yace,ai kuwa saidai mu mutu anan nida kai kowa ya rasa.Koda gama fadin hakan sai sa maza gudu ya gyara tsayuwarsa ya daga takobinsa da hannayensa biyu ya riketa da kyau,awannan lokaci hibairu maye yake yana layi daga tsaye kamar zai bingire kasa,amma sai yacigaba da kiran sunayen Allah yana mai neman taimakonsa,aikuwa nan take yaji wani sabon gagarumin karfi ya shige shi.A lokaci guda duk su biyun suka ja da bya taku uku uku suna yiwa junansu wani irin kallo na kar ta sankar kuma kowannensu na lura da irin motsin da dan'uwansa zaiyi.Kawai sai suka rugo da gudu suka ruguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi.Hakika duk sa'adda zarto ya hadu da gwarzo dole ne ayi bakin artabun da zai firgita komai da kowa dake wajen domin ana fara wannan gumurzu ne bishiyoyi da koramai dake cikin wannan daji suka san cewa babbar masifa tazo don sa'adda zaki nurul maut ya baiyana ba'a hargitse haka ba,saidai kawai kaga bishiya komai tsawonta ta karye ta fadi,ruwan koramai da fadamomi kuwa ya rinka fantsama a lokacin da wata irin iska mai karfin gaske ta addabi duk wani abu mai rai dake wajen.Duk sa'adda takubban jaruman biyu suka hadu kuwa saidai kaga tarwatsin wuta na tashi gami da tsawa,ba komai ne ya haddasa hakan ba face sihirin tsafin da sa maza gudu ke amfani dashi don ganin ya hallaka jarumi hibairu,shi kuma Allah na bashi kariya sakamakon adduar da yake tayi.Saida suka shafe sa'a biyi da yan dakiku masu yawa suna wannan mugun yaki ba tare da dayansu ya sami nasarar komai ba,har ya zamana cewa sun gaki likis da kyar ma suke iya daga takubban nasu suka kacame da kokawa su fadi can su mirgina nan duk inda sukayi wadannan alkalan gasa na biye dasu a firgice duk da cewa suma a galabaice suke ainun,kawai fatansu shine hibairu ya sami nasarar kashe sa maza gudu domin suma su tsira da rayuwarsu.Haka dai Hibairu da sa maza gudu suka cigaba da fafatawa har suka sake mikewa tsaye suka rinka gabzawa junansu naushi da bugu da hannu da kafa duk wanda aka yiwa mugun naushi a fuska saidai kaga yana furzar da ruwan jini.Nanda nan fuskokinsu da idanunsu suka kumbura tun suna tsaye saida suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu suka cigaba da gabzar juna har saida takai cewa sun baje kasa sumammu.Jim kadan da faruwar hakan sai duk su biyun suka fardado a lokaci guda cikin shammace da matukar zafin nama,sa maza gudu ya zaro wata siririyar wuka daga cikin rigarsa ya kawai hibairu suka a ciki,hibairu ya yunkura domin ya kaucewa sukar amma sai da wukar ta nutse a cinyarsa,hibairu ya kurma uban ihu sakamakon bakin zafin da yaji,amma sai yayi ta maza yayi wuf ya zare wukar jini yayi tsartuwa daga cikin cinyar tasa,shi ma ya lumawa sa maza gudu wukar a tasa cinyar ta dama har saida ta bullo ta bayan cinyar.Sa maza gudu ya rusa uban ihu a lokacin da duk su biyu suka zube kasa a matukar galabaice suka kasa ci gaba da yakar juna.Kowannensu ya kasa mikewa tsaye sakamakon jini dake zuba a jikin cinyoyinsu mai yawa.A guje wadannan alkalan gasa suka rugo izuwa kan jarumi hibairu suka taimaka masa suka daure raunin dake kan cinyar tasa suka tsaida jini suka tashe shi tsaye,sannan suka zare takubbansu suka nufi kan sa maza gudu da nufin su kashe shi,amma sai hibairu ya daka musu tsawa.Cikin matukar takaici suka sauke takubbansu kas,suka jiyo suka dubi hibairu sukace saboda me ka hanamu kashe makiyinmu alhalin yayi furucin kashe mu a gabanka?Hibairu yace ai bana son ku kashe shi da hannunku saboda kasancewarsa babban jarumi,lallai bai kamata manyan mazaje suyi mutuwar banza ba a hannun wadanda basu da karfin iya kashe su,ku kyaleshi ya mutu sakamakon jinin dake zuba a jikinsa mai yawa,tunda babu mai taimakonsa anan dajin,idan ya mutu a nan yayi irin mutuwar da sauran jaruman gasa sukayi kunga kenan za'a tabbatar da cewar jarumatakarsa bata kai tawa ba,kuma lallai ya kasa fafatawa da zaki nurul maut,ta tabbata kenan nine makashin nurul maut bashi ba.Koda gama fadin hakan sai jarumi hibairu ya dingisa kafarsa da kyar yaje ya dauko rabi gangar jikin zaki Nurul Maut mai hade da dagargajajjen kansa ya rataya a gadon bayansa suma alkalan gasar sai suka taimaka masa suka dora hannayensa akan kafadunsu suka juya suka nufi hanyar dazata kaisu can inda sansanin sarki zaldasi yake suka bar jarumi sa maza gudu kwance a kas yana aman jini yana mutsu mutsu tamkar ruhinsa na daf da makoshinsa.Haka dai jarumi hibairu dalkakan gasa suka cigaba da tafiya da kyar cikin matukar karfin hali,wani lokacin har yanke jiki sukeyi suna faduwa kasa saboda galabaita,kishirwa da yunwa,amma saboda naci da matukar juriya saikaga sun sake mikewa sunci gaba da tafiya.A haka dai suka samu suka fara hango sansanin su sarki zaldasi daga nesa kadan.Al'amarin dayayi matukar jefasu cikin matukar farinciki kenan suka kara sauri domin su isa can din,nan fa suka fara bude bakunan su suka kwala kira domin a kawo musu agajin gaggawa,amma saboda bakinsu ya bushe kuma muryoyinsu sun dashe babu wanda ya jiyosu.Ana cikin wannan hali ne kwatsam jarumi Hibairu yaji wadannan alkalan gasa biyu sun kife kasa da rub da ciki a gabansa,kawai sai ganin kibiyoyi yayi a gadon bayansu.A firgice ya waigo bayansa yayi arba da wanda ya harbosu su ba wani bane ba face....rike da KWARI DA BAKA. Anan zan dakata,anyi fiye da rabin littafi na shida,sai mu tara a part B. Littafi na Shida (6) Part B Ba wani bane face Jarumi Sa Maza Gudu rike da wata KWARI DA BAKA yana dingisa kafarsa da kyar kuma ga rabin gawar zaki nurul maut rataye a kafadarsa fuskarsa cike da annuri sa murmushin mugunta yake yiwa Hibairu.Tsananin mamaki ne yasa Hibairu ya kasa yin wani yunkurin komai har ya iso daf dashi domin bai taba zaton cewa zai sake ganin jarumi Sa Maza Gudu ba a raye sakamakon halin daya baro shi a can dajin Sairul.Sa Maza Gudu ya cigaba da dingisa kafarsa da kyar har ya iso daf da jarumi Hibairu ya dubeshi yace,kana dauke da rabin zaki nurul maut,nima haka kuma ga alkalan gasar da zasu bayar da shaidar zakara a cikinmu kwance a kasa matattu.Ta yaya za'a gane wanda shine ya kashe zakin bisa gaskiya.?Kamar yadda kace dani in dai kana raye a doron kasa burina bazai taba cika ba,to kaima naka bazai cika ba muddin ina raye,bakar wahalar zubar da jini basu ne mutuwa ba,rai baya gushewa face wa'adinsa ya cika kamar yadda kukayi imani da addininku.Koda gama fadin hakan sai jarumi sa maza gudu ya wuce gaba yana mai cewa zomu karasa sansanin inyaso muga wanda za'a baiwa kambun wannan gasa tsananin nida kai.Zamu ga wanda zai zamo mijin gimbiya Lasmin.Nan take jarumi Hibairu yabi sa maza gudu suka jera tare suka durfafi sansanin.Daga nesa kadan suka hango su sarki Zaldasi tare da tsirarun dakarun da suka je dajin Sairul suka tsira da rayuwakansu da kyar amma gaba daya yan kallon da sukaje da alkalan gasa dayansu bai dawo ba a raye.Koda su sarki Zaldasi suka hango Jarumai biyu kacal sun dawo daga cikin dajin Sairul kuma kowannensu na dauke da rabin gangar jikin zaki nurul maut,sai suka cika da tsananin al'ajabi.Nanfa mutane suka rude da shewa gami da tafi da jinjina,duk wanda ya dubi Hibairu da sa maza gudu yaga irin mugayen raunikan dake jikinsu sai ya kamu da matukar tausayinsu,kuma ya jinjina musu ainun.Ita kuwa gimbiya Lasmin koda ta hango jarumi Hibairu a raye ya durfafo sansanin goye da kan zaki nurul maut a kan kafadarsa sai ta kamu da tsananin farin ciki mara misaltuwa,bata san sa'adda ta yunkura ba da nufin ta ruga da gudu ta rungume Hibairu,amma sai sarki Zaldasi yayi wuf ya riko hannunta ya dubeta a fusace yana mai yi mata rada a kunne,yace,baki da hankali ne ko kuwa kin makance ne bakya gani,to ba Hibairu bane kadai ya dawo cikin nasara ba dubi can bayansa ga jarumi Alkas can tafe goye da wani bangaren na zakin nurul maut.Dole sai mun bincike mun gano ainihin wanda shine ya kashe zakin bisa gaskiya sannan mu bashi aurenki.Kafin sarki Zaldasi ya gama rufe bakinsa sai aka hango Jarumi Hibairu da Jarumi Sa Maza Gudu sun yanke jiki sun fadi kasa sumammu,nan take sarki Zaldasi ya bayar da umarni aka ruga aka dauko su a ka shigar dasu cikin tanti,likitoci suka dukufa a kansa.Al'amarin sarki zaldasi kuwa cikin rudewa ya hada taro na gaggawa ya hada gaba dayan manyan sarakuna da manyan bakin da suka halacci wannan gasa da kuma dukkanin attajiran gasa suka taru a tsakiyar sansanin suka zazzauna domin a tattauna akan wannan al'amari.Sarki Zaldasi ya mike tsaye fuskarsa a murtuke,kana kallonsa kasan cewa ransa a bace yake,ba komai ne ya bata masa rai ba face ganin abinda yake son ya faru bai baru ba,shi a tunaninsa dole ne su jarumi Hibairu su mutu a cikin dajin sairul a hannun zaki nurul maut,amma sai gashi sun dawo a raye,kuma gaba dayan jama'arsa daya tura dajin da jaruman gasa duk sun mutu kalilan ne suka dawo.Tuni Sarki Zaldasi ya aiyana a ransa cewa zai aurar da Gimbiya Lasmin ne ga dan kaninsa Yarima Zaiyan,farin cikinsa guda daya ne jal an kashe zaki nurul maut,zakin daya gagare shi kashewa tsawon shekara da shekaru.Gaba daya sansain sai yayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi wajen ana sauraron aji bayanin dazaiyi.Sarki Zaldasi yayi gyaran murya sannan yace,yaku jama'a kun gani da idanunku cewa a gaba dayan jaruman da suka tafi wannan gasa mutum biyu ne kacal suka dawo a raye kuma dukkaninsu suna dauke da rabin gangar jikin zaki nurul maut.Alkalan gasa kuwa ko mutum daya jal bai dawo ba a raye,a kallah mutum dubu dari shida da sittin da uku ne suka rasa rayuwarsu a cikin wannan daji na Sairul,yanzu tunda dai an kashe zaki Nurul Maut zan aika da dakaru su debo gawarwakin jama'a domin azo ayi musu jana'iza.Dangane da bayar da kambun gasa kuwa dolene mu jira wadannan jarumai guda biyu sun sami lafiya kuma hankalinsu ya dawo jikinsu,sannan dole ne muyi bincike na gaskiya domin mu tabbatar da wanda ya kashe zakin bisa gaskiya tsakanin jarumi hibairu da jarumi alkas.Da wannan furuci nake baiwa kowa umarnin yayi shirin barin bakin wannan daji domin tafiya izuwa cikin birninmu mai albarka,sakamakon wannan gasa kuwa sai nan da cikar kwanaki uku za'a bayyana shi.Koda gama fadin hakan sai jama'a suka rude da shewa,wasu kuwa da yawa a wannan lokaci yan gari da baki kuka sukeyi da bakin ciki sakamakon yan uwansu da suka rasa a cikin dajin sairul.Duk wannan bayani da sarki zaldasi yayi ni da sa maza gudu muna jiyo su daga can cikin tantin da aka kwantar damu sa'adda likitoci keta kokarin ceto rayuwarmu.Koda naji wannan bayani na sarki Zaldasi sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda na fusakanci cewar akwai yiyuwar a rushe dukkan shirina da burina.Abu na farko dai akwai alamun cewa babu tabbacin za'a bani zakaran wannan gasa,tunda babu cikakkiyar shaidar da zata tabbatar da cewa nine na lashe gasar.Abu na biyu kuma a yanzu yadda nake a kwance cikin jinya za'a iya shirya mini wata manakisar dazan kasa aiwatar da nufina na jaddada kalmar Allah a cikin bainar taron miliyoyin jama'a da zasu halac ci filin sanar da sakamakon gasar.Idan ma na fadi cewa ubangijin musulunci ne ya bani sa'a da karfinsa har na iya kashe zaki nurul maut,babu mai bayar da shaidar hakan tunda sa maza gudu ya kashe alkalan gasa biyu wadanda sukaga faruwar hakan da idanunsu.Koda nazo nan a tunanin zucina sai hankalina ya dugunzuma ainun na rasa babinda yake mini dadi a duniya amma dana tuna cewa komai da kowa na karkashin ikon Allah saina kama yin addu'a a cikin raina,nan take hankalina ya kwanta na sami nutsuwa.A ranar da muka koma cikin birnin Kisra aka kaini masaukina shima sa maza gudu aka kaishi masaukinsa daga sannan bamu sake haduwa ba sai bayan kwanaki uku cur a tsakiyar filin gidan sarautar sarki Zaldashi.A wannan rana birnin gaba daya ya cika makil ya batse da tarin bil'adama fiye da ranar ma da aka gabatar da wannan gasa ta farauta,duk inda ka gusa a birnin saidai kaga kawunan bil'adama fululu babu masakar tsinke sai da kyar mutum zai iya kutsawa ta cikin mutane ya wuce.A cikin kwanaki ukun dana yi a masaukina naga tashin hankali domin sau goma sha daya ana kawo mini hari domin a hallaka ni amma sai Allah ya rinka kareni amma ba karfina bane ko dabarata.Bayan ga wannan kuma sai na tsinci kaina a cikin rashin ishesshen bacci,zulumi da fargaba da yawan tunani,ba komai ne ya haddasa mini hakan ba face yawan begen gimbiya Lasmin da kuma tunanin yadda karshen al'amura zasu kasance.Duk da cewa zargi haramun ne sai dana rinki zargin jarumi sa maza gudu da sarki zaldasi bisa laifin kokarin kashe ni da akayi saboda basa son ya kasance nine na lashe wannan gasa.Lokacin dana baro masaukina na durfafi fadar sarki zaldasi ni kadai ina kutsawa ta cikin miliyoyin jama'a sai naji zuciyata tayi fari sakamakon dalilai guda biyu. Dalili na farko shine zanje naga fuskar masoyiyata gimbiya Lasmin wacce nake fama da azabar begenta da kewarta dare da rana,dalili na biyu kuma shine ina murna gami da godiya ga ubangiji na wanda ya bani kariya har kawo izuwa wannan rana domin in ba don kariyarsa ba a yanzu haka nake yin wannan tafiya makiya zasu iya shammata ta

Chapter 13 of 19