Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
domin gaba daya birnin namu bai wuce matsayin wata yar karamar unguwa ba a cikin nasu garin,haka muke samun labarin a bakin fatakensu.A ranar dana shike shekaru goma sha takwas ne muka shiga daji tare da mahaifina da dukkan mai farauta domin yin wata farauta rin wacce ba'a taba yin mai tsananin wahalarta ba,kuma har dashi kansa a cikin gasar,wanda duk ya kashe dabbobi uku da sukafi na kowa girma da hadari shi kadai ba tare da taimakon kowa ba shi ne ya lashe gasar.A wannan rana da yawa daga cikin mafarautanmu sun kusan rasa rayukansu domin kowannensu da kyar ya dawo gida jikinsa cike da raunika,shi kansa mahaifina saida ya sami manyan raunika guda uku.Nine kadai na dawo gida cikin koshin lafiya babu ko rauni daya a jikina,alhalin nayi gumurzu da yaki.Damisa da kura Da Zaki kuma duk na kashesu na janyo gawarwakinsu a kas har cikin gari gefin magriba ne na shigo cikin gari janye da wadannan dabbobi uku,Tun daga nesa na hango gaba daya mafarautan zaune a kofar gari suna jinyar jikinsu,wasu na dinke musu raunika,wasu ana samusu magani.A gefe daya kuma mutanen gari ne suka taru sukayi cincirindo suka zuba ido domin suga wanda zai lashe gasar.Kuma dokar gasar itace indai rana ta fadi gaba daya mutum bai shigo gari ba to ya fadi gasar sannan kuma anasa ran cewa mutum sakamakon gumurzun da dabbobin dajin saidai a tafi neman gawarsa.Adaidai wannan lokaci mahaifiyata na tsaye daf da mahaifina wanda ke zaune bisa kujera likta na dinke raunikan jikinsa kuma shima dakyar ya kwaso manyan damisoshi guda biyu.Koda mahaifiyata taga cewa saura kiris rana ta gama faduwa amma babu ni babu doriyata sai nan take idanunta suka ciko da kwallah ta fara zubar da hawaye,Sa'dda hawayen nata ya diga a kan kafadar mahaifina sai ya daga kai ya dubeta cikin murmushi yace,kwantar da hankalinki yake uwar gida,zuba idanunki da kyau izuea can cikin daji zaki ga wata kura na tashi,takun sawayen danki ne Hibairu da kuma dabbobin da yake ja a kas.Ai kuwa mahaifina bai gama rufe bakinsa ba sai jama'a suka hangoni a tafe ina layi kamar zan fadi saboda tsananin gajiya,kuma na daure da gawar zaki,kura da damisa da wata igiya ina janyosu a bayana.Koda jama'a sukayi arba dani sai suka rude da shewa gami da tafi da jinjina ana tayani murnar lashe wannan gasa,hatta sarki garinmu a wannan lokaci baisan sa'adda ya rinka daga hannunsa ba yanayi mini jinjina,ita kuwa mahaifiyata rugowa tayi da gudu ta rungumeni ni kuma ta fashe da kukan farin ciki. Mu hadu a cikin Littafi na biyar (5) don jin cigaban wannan labari.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTMAZA GUDU Littafi na Biyar (5) Part A •Ita kuwa mahaifiyata rugowa tayi da gudu ta rungumeni kuma ta fashe da kukan farin ciki.Bayan an bani kambun Sarauta na gasa,wato mahaifina da kansa ya kwance kambun daga jikin hannunsa ya daura a nawa,sai mutane suka rude da kabbara aka cigaba dayi mini jinjina,a lokacin ne mahaifina ya daga kansa da hannayensa sama yayiwa Allah godiya cikin matukar farin ciki daya sanya dansa ya gajeshi.Kwatsam a na cikin wannan dimbin farinciki ne aka hango wani mahayi ya durfafo cikin garin a guje bisa wani ingarman doki,tun daga nesa aka gane cewa bako ne kuma yana sanye da tufafi irin na dakarun birnin Kisra.Da isowar wannan badakare daf da sarkinmu sai ya tsayar da dokinsa ya sauko kasa da sauri ya zube a gaban sarki ya kwashi gaisuwa,sannan yace,ya shugabana,Sarki Zaldasi Bin Auzir na birnin Kisra ya aiko ni gareka da wasika,ni manzo ne daga gareshi don haka ina jiran amsar da zan maida masa.Koda gama fadin hakan sai badakaren ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo wasika a cikin fata mai inganci da daraja ya mikawa sarkinmu.Nan take kowa dake wajen ya cika da dinbin mamaki da tsoro saboda wannan ne karo na farko da kasar Kisra ta aiko da manzo izuwa birnin Nurul Islam.Hannun sarkinmu na karkarwa ya karbi wasikar ya warwareta sannan ya fara karantata a fili yadda kowa ke iya sauraro kamar haka:"Wasika daga hannun sarkin sarakuna mai daraja ta daya kuma mai birnin Kisra Zaldasi bin Auzir,zuwa ga sarki Hayat Usman na Birnin Nurul Islam.Bayan gaisuwa da fatan Alheri,ina mai farin cikin gaiyatarku a karo na farko izuwa kasata domin halattar GASAR FARAUTA irin wacce ba'a tabayin kamarta ba a wannan nahiya gaba daya.Saboda girman wannan Gasa ne yasa nayi alwashin saina gaiyaci duk kasashen dake nahiyar,har da taka kasar wacce bamu taba hulda da ita ba,ka sani cewa duk jarumin daya lashe wannan gasa yanada zabi uku,ko dai na raba kasata biyu ba bashi rabi ya mulka,ko na bashi dukiyar da zuri'arsa gaba daya har su kare bazasuyi rashi ba.Ko kuma na bashi rikon kasuwancin nahiyar nan gaba daya,lallai ka tsaya ka tantance ka zabo jarumin daka tabbatar dazai iya shiga wannan gasar saboda hadarinta daidai yake da TUNKARAR AJALI.Duk jarumin dayazo birnina yaji yanayin wannan gasa kuma ya tsorata yace bazai iya ba hukuncin kisa ne a kansa."Koda sarki yazo nan a zancensa sai hankalin gaba dayan jama'ar garin ya DUGUNZUMA ainun,shi kuwa sarki sai ya kama murmushin mugunta da farinciki ya dubi mahaifina Uraisu yace,ai shike nan yar manuniya ta nuna.Babu wanda yafi cancanta daya wakilcemu a wannan gasa sama da danka Hibairu tunda yanzun nan ya zama sarki mafarautarmu ma'ana ya gajeka.Koda jin haka sai Mahaifina yace haba ranka ya dade,yaza'ayi a tura Hibairu izuwa wannan gasa wacce za'a tara manyan jaruman duniya alhalin shi yaro ne karami dan shekara goma sha takwas kacal,kada ka manta fa cewa shine babban dana kuma babu wanda zai iya karbar matsayinsa daga cikin kannensa,shine kadai zai iya ci gaba da ruke wannan babbar sana'a tamu ta farauta a wannan birnin namu mai albarka tunda ni yanzu girma ya fara kamani.Sarki Zaldashi bai fadi yanayin wannan gasa ba bare musan irin hadarin dake cikinta ba,baka tunanin cewa idan muka tura Hibairu tamkar mun turashi izuwa FARAUTAR AJALINsa ne?Koda mahaifina yazo nan a jawabinsa sai gaba dayan sauran jama'a suka goyi da bayansa suna masu nuna cewa basu amince a tafi dani ba izuwa wannan gasa.Al'amarin da yasa ran sarkinmu ya baci kenan ya daka tsawa kowa yayi shiru sannan ya ce,idan har Hibairu bazaije wannan gasa ba,saidai mahaifinsa ya wakilceshi,tunda bamu da wani GWARZON JARUMI masanin farauta dayakai daya daga cikinsu in ba haka ba kuwa saidai a fasa tura kowa in yaso sarki Zaldasi ya dauki matakin dayaga ya dace a kanmu.Koda jin wannan batu sai ran mahaifina ya baci,ya dubi Sarki a karo na farko a zamantakewarsu ya daka masa tsawa yace,ban taba sanin cewa kiyayyarka a kaina da ahalina takai haka ba sai yau,yanzu saboda kawai kaga baya na ka yarda ayi asarar daruruwan rayukan jama'a a garin nan,shin ka manta ne cewa kai musulmi ne wanda bai yarda da azubar da digon jinin mumini ba a banza,shike nan tunda abin yazo da haka ni na amince zan wakilci garin nan a wannan gasa,domin bani da burin dayafi dana ya gajeni kuma ya ci gaba da karfafa tattalin arzikin garinmu.Koda jin wannan batu sai jama'a suka rude da shewa suna masu nuna gamsuwarsu,kawai sai akaga na kama hannun mahaifina na jashi izuwa can gefe daya inda babu wanda zaiji abinda zamu tattauna,sannan na dubeshi a cikin nutsuwa nace,yakai Abbana shin ka manta ne ka gaya mini cewa akwai wani babban nauyi a kan gaba dayan mutanen garin nan wanda a ranar gobe kiyama sai Allah ya tuhume mu a kansa,wannan nauyi kuwa ba na komai bane face na yada addinin Allah a wannan nahiya.Saboda tsoron karya doka da yarjejeniyar dake tsakaninmu da manyan kasashen nahiyar nanne yasa muka kasa tallata addinin Allah a garesu.Na sani cewa ka dauki alkawari ga iyayenka da sarkinmu daya gabata cewa zaka kiyaye wannan yarjejeniya to amma aini ban dauki wannan alkawari ba a garesu,ko a gareka,ka sani cewa wannan gasa da zanje nayi itace kadai hanyar dazanyi amfani da ita wajen yada addinin Allah ga sauran kasashen.Na sani cewa gasar daza'ayi wahalarta da hadarinta yafi gaban tunanin kowa,KARFI ko TSAFI bazai sa mutum ya sami nasara ba face da taimakon Allah.Zan roki Allah a kan ya bani sa'a da nasara a cikin wannan gasa,idan kuwa nayi nasara agaban miliyoyin jama'a da suka taru daga sassan duniya zan fadi cewa babu wanda ya bani sa'a da nasara a cikin wannan gasa face ubangijin Musulunchi.Kaga kuwa ko kasheni akayi a wajen na gama samun nasara gami da babban rabo domin MUTUWAR SHAHADA zanyi.Tabbas idan na fadi hakan miliyoyin jama'a zasuyi imani su karbi musulunci.Yakai Abbana shin kana so na sami wannan shahada ko kuwa kafison mu tafi lahira da wannan babban nauyi.Allah ya tuhumemu a kansa? Koda nazo nan a zancena sai hawaye ya zubowa mahaifina take ya rungumeni a lokacin dani ma na fara zubar da hawaye yana mai cewa.Yakai dana hakika yau ka nuna mini cewa na dade a cikin sabon Allah don haka daga yau zanyi ta istigifari har izuwa ranar mutuwa ta,tabbas mu da iyayenmu da suka gabata muna dauke da katon nauyi wanda kai kadai ne a yanzu zaka iya sauke mana shi.Idan jama'r birnin Nurul Islam suka shude gaba daya ba rahamar Allah,saboda haka na yarje maka ka tafi izuwa wannan gasa,RAI da MUTUWA duk na Allah ne,dama fatanmu kawai shine mu sami yardar Allah.Koda gama fadin haka sai mahaifina ya kama hannuna ya jani izuwa gaban sarki ya damka ni a hannunsa yace,da izinina da kuma yardata na baka dana Hibairu a tafi dashi izuwa Birnin Kisra domin ya wakilci garin nan namu mai albarka a wannan gasa.Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da matukar mamaki,mahaifiyata kuwa sai ta rugo ta rungumeni ta fashe da matsanancin kuka ta dubi sarki tace,ina neman alfarmar ka barmin dana daga nan zuwa wayewar gari domin muyi bankwana saboda nasa cewa in ya tafi bazai dawo.Koda jin haka sai tausayinta ya kama kowa a wajen,da yawan jama'a suka kama kuka,shi kuwa sarkinmu sai farinciki ya lullubeshi ya dubi mahaifiyata yace,jeki da danki kiyi masa kallon karshe amma ki sani cewa ana idar da sallar asuba zan hadashi da wannan manzo na sarki Zaldasi su tafi izuwa birnin Kisra.Sarki na gama fadin hakan sai ya juya ya nufi cikin gari,fadawansa da dakarunsa na take masa baya tare da wannan manzo na sarki Zaldasi.Nanfa jama'a suka fara yiwa iyayena jaje tamkar ma na mutu,saboda gani ake lallai bazan dawo ba gida a raye ba,dani da iyaye na da sauran jama'ar gari muka dawo gida a cikin jimami da bakin ciki,amma ni a cikin zuciyata ko kadan bani da tunanin idan na tafi bazan dawo baAbinda nayi imani dashi shine babu abinda zai gagari Allah.A wannan rana dai mahaifiyata batayi barci ba,duk sa'adda na farka daga barci saidai na ganta a zaune a gefen gadona ta kura mini idanuwa tana zubar da hawaye,da kyar na rarrasheta muka kwanta tare tana rungume dani har barci ya saceni bata sani ba.Mahaifiyata Samsira tana tsananin kaunata,saboda nine kadai danta a duniya,kuma daga kaina Allah bai sake bata haihuwa ba,bata da kowa a duniya face ni da mahaifina don haka duk abinda taga zai rabamu shine babban makiyinta.Bayan anyi sallar asuba mun dawo daga masallaci nida mahaifina,sai muka iske mahaifiyata zaune a falo fuskarta a murtuke kuma idanunta sunyi sharkaf da hawaye,koda ta hangomu mun shigo falon sai ta taso da sauri ta taremu ta dubi mahaifina a fusace karo na farko a rayuwarta tace saboda me zaka bayar da dana shi daya jal daga cikin 'ya'yanka goma sha biyu domin aje a kashe shi?Ashe dama baka kaunarsa haka ban sani ba kuma nima baka kaunata tunda kanaso ka rabani da rabin jikina?Koda mahaifiyata tazo nan a zancenta sai nida mahaifina muka kamu da tsananin tausayinta saboda munsan cewa tsananin soyayyarta a gareni ce yasa tayin wannan kalami.Nan take mahaifina ya janyota ya rungumeta a kan kirjinsa a lokacin da hawaye ya subuto masa.Cikin rada yadda babu mai jin abida yake gaya mata ya zaiyane mata duk maganganun da yasa ya amince na tafi izuwa wannan gasa.Koda mahaifiyata taji cewa wannan tafiya da zanyi daidai take da JIHADI,sai farin ciki ya lullubeta ta janye jikinta daga cikin na mahaifina ta rungumeni tana mai sa mini albarka gami dayi mini fatan sa'a da nasara.A gidanmu gaba daya saida aka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda mahaifiyata ta daina bakin cikin wannan tafiya tawa,ya zamana cewa ta dawo tana farin ciki fiye da kowa,kuma bata sake zubar da hawaye ba,har saida muka zo yin bankwana na karshe a lokacin datayi mini sallama ta juyo mini baya ina kan doki,saida ta kusan shigewa cikin gida sannan ta waigo naga hawayen a cikin idanunta.Daga wannan rana kawo iyanzu dana cika shekara ashirin da biyar ban sake ganin iyaye na ba kuma ban sami labarin su bare nasan halin da birninmu ya shiga ba bayan tafiyata saboda babban bala'in dana fuskanta.Lokacin da Jarumi Hibairu yazo daidai nan a labarinsa sai ya daga kai ya dubi Gimbiya Zuhura da sarki,bisa mamaki saiyaga idanun Zuhura cike da hawaye saboda tausayi,amma shi sarki Kamzal idanunsa a bushe suka kuma fuskarsa a murtuke take babu annuri.Kawai sai ya dubi Hibairu cikin zakuwa yace,ina sauraronka maza ka cigaba da bani wannan labari mai ban Al'ajabi.Da kuka isa birnin Kisra me ya faru kuma yaya yanayin wannan gasa ya kasance.Koda jin wannan tambaya sai na dubi sarki Kamzal cikin alamun rashin yarda nace yanzu kana nufin kace dani baka halacci wannan taro ba alhalin a nahiyar nan kaf babu sarki da bai amsa gaiyatar sarki Zaldasi ba a wannan lokaci.Cikin rawar murya da alamun rashin gaskiya Sarki Kamzal yace tabbas na amsa gaiyatar sarki Zaldasi kuma na isa birnin Kisra amma akasin da aka samu shine har aka gama gasar ina kwance a masaukina banda lafiya,ban sami damar halattar dajin da akayi gasar ba.Koda jin wannan batu sai jarumi Hibairu ya ajiye numfashi gami da gyaran murya sannan ya ciga da bayar da labari kamar haka."Ni da manzon Sarki Zaldasi ne kadai muka kama hanya muka baro birnin Nurul Islam.Lokacin da muka iso bakin gabar kogin daya zagaye birninmu,muka iske wani babban jirgin ruwa na fatake,ba tare da bata lokaci ba wannan manzo ya biya aka shigar damu cikin jirgin harda dawakanmu a ka cigaba da tafiya a cikin tekun.Fataken dake cikin wannan jirgi sunkai a kalla mutum saba'in da biyar,kuma maza ne da mata,matasa da tsofaffi,kowa ka gani a cikin jirgin yana dauke da guzurinsa kuma da yake jirgin na sarkin Birnin Kisra ne akwai dakaru a cikinsa masu tabbatar da tsaro don haka babu wani bafatake dake cikin tsoron salwantar da dukiyarsa.Daga kasarmu ta Nurul Islam zuwa birnin kisra a jirgin ruwa sai da muka shafe kwani goma sha daya muna ratsa teku,mu sauka a wancan gari mu huta mu cigaba da tafiya har muka isa can.Ana sauke mu a gabar ruwa aka fito da dawakanmu muka hau,ina biye da manzo Imsar a baya muda sauran fataken muka nufi hanyar dazata kaimu cikin birnin kisra.A wannan lokaci dare ya raba kuma wannan shine karon farko a gareni dana tabayin tafiya mai nisa duk yawona baya wuce iyakar wadansu yan kauyukan dake kusa da garinmu amma ban taba zuwa wani babban birni ba saidai naji ana labarinsu a na cewa sun kawata da gine gine na zamani.Tun daga nesa na hango birnin kisra na zama cikakken dan kauye saboda hango gidaje masu hawa hawa na gani tubali,duk da cewa dare ne amma an kawata birnin da fitulu tamkar rana,su kansu fitulun da akayisu a cikin wadansu irin kwalabe mamaki suka rinka ba.Abinda na aiyana a cikin raina shine anya kuwa ba aljanu bane suka kawata wannan birni?Da muka iso bakin kofar garin saida dakarun tsaro suka duba kowa kuma aka duba kayan kowa sannan aka bude mana kofa muka shiga.Wohoho ai muna shiga cikin birni na kisra na wangame baki saboda tsananin mamaki,musamman muka durfafi hanyar zuwa gidan sarautarsu,duk inda muke takawa da kafafun dawakanmu babu kasa.Ko ina dutsen Jauhar ne aka shimfida a katangar gidan sarautar kowacce da dutsen murjani akayi ta,muna shiga cikin harabar gidan sarautar kuwa sau naga gaba daya ginin gidajen ciki da dutsen Yakutu akayi su,duk kofar da muka iso sai mun iske masu gadi a kalla mutum arba'in kuma sun kasance samudawan dakaru masu tsananin kwarjini da kira ta sadaukai dauke da muggan kayan yaki amma da zarar sunga manzo Imsar sai su bude mana kofa mu shiga.A haka dai saida muka ratsa ta cikin kofofi tara,fadoji goma sha daya,ina ta kalle kallen abin al'ajabi ina mamakin yadda mutane suke shagala da duniya haka tamkar bazasu mutu ba a binne su cikin kasa.Abinda zuciyata ke wassafani shine wai shin yaya cikin turakar sarkin Kisra zata kasance kuma a cikin wacce irin daula 'ya'yansa da matansa suke.Lokacin da muka iso fada ta goma sha daya ne aka tsayar damu,muka sauko daga kan dawakanmu wadansu bayi biyu suka karbi dawakan suka tafi dasu.Kawai sai Imsar ya kama hannuna ya jani izuwa wani bangare dabam yakai ni izuwa cikin wani kasaitaccen gida,ashe nanne masaukina.Koda ya shiga dani cikin dakin barci nayi arba da wani luntsumemen gado mai dauke da shimfidu masu tashi sai yace dani anan zaka kwana sai gobe da safe zanzo na kaika wajen sarki na gabatar masa da kai.Koda jin haka sai tsoro ya kamani domin gani nake ina hawa kan gadon zai hadiye ni.Kafin na budi baki nace wani abu tuni Imsar ya janyo kofar dakin ya rufe ruf ya barni ni kadai a cikin dakin cikin alamun tsananin tsoro.Naje na rinka danna shimfidar gadon da hannayena biyu domin na gani ko bazai cutar dani ba,koda naga babu wata matsala sai na fada kan gadon ba kwanta.Abinka da gajiyayye nanda nan barci ya sace ni ban farka ba saida gari ya waye,hasken rana ya shigo cikin dakin ta taga ya bugi fuskata,a firgice na mike zaune zumbur,kawai sai nayi arba da wadansu kyawawan kuyangi guda uka a tsaye a gabana ga abinci a faranti a hannun kowacce.Nan take suka ke suka ajiye abincin bisa wani babban tebur dake kusa da gadon barcina,sannan suka kamani suka tasheni tsaye suka kaini keaye da nufin suyi mini wanka,kawai sai na daka musu tsawa suka firgita na korasu waje sannan nayi wankana,a zuciyata cewa nakeyi in banda aikin kafirci yaza'ayi ace 'YAN MATA su yiwa SAURAYI kamata wanka.Bayan na gama wanka na kintsa kuma na gama cin abinci kenan sai na jiyo tambura gami da bushin algaita daga can wani bangere na gidan sarautar.Hakan ne yasa na gane cewa Sarki Zaldasi ya fito fada.Faruwar hakan keda wuya saiga Imsar ya shigo da sauri a cikin tufafi irin na fadawan sarki Zaldasi,cikin hanzari ya kama hannuna muka fice muka nufi fadar,muna sauri sauri gudu gudu muka nufi babbar fada ta gidan sarautar.Nanfa na rinka ganin mutane da yawa ka kala daga sassan duniya duk sun nufi babbar fadar ta sarki Zaldasi.Idan mutum yaga tsananin yawan jama'ar dake kokarin shiga wannan fada sai yayi zaton cewa mutanen duniya ne kaf zasuyi taro.Lokacin da muka shigo cikin wangamemiyar fadar kuwa wacce girmanta ya ninka na birninmu Nurul Islam sau uku sai na cika da dimbin al'ajabi abinda ya firgita ni shine dutsen lu'u lu'u ne saboda haskensa da kyallinsa ma mutum na iya ganin fuskarsa da jikinsa akai tamkar madubi,saman rufi fadar kuwa gaba daya da jan Zinare akayi shi.Kafin mu kusanci inda karagar sarki Zaldasi take saida mukayi tafiyar sa'a uku a kasa har saida na gaji kuma na kosa,A gefen dama na fadar tun daga farkonta har izuwa inda karagar mulki take fadawan sarki Zaldasi ne a tsaitsaye gaba da baya.A bangaren hannu hagu kuwa jaruman gasar farautar ne a jere su da yawa,a bayansu kuwa dakarun sarki Zaldasi ne wadanda suka zagaye fadar gaba daya.Koda na dubi jaruman gasar sai zuciyata ta buga da karfi kuma hankalina ya DUGUNZUMA ainun,ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin cewa gaba dayan jaruman gasar babu dan kasa da shekara ashirin da biyar,kuma duk kaninsu sun kasance girda girda,wato dogaye ga kauri kuma ga kira ta sadaukantaka,kuma kowannensu hannayensa,kaurinsa da kugunsa cike yake da guraye da layu na tsafi,ni kuwa in banda wata yar guntuwar laya guda daya dake wuyaba bani da komai,ita ma wannan laya ba komai be a cikinta ba Face KALMAR SHAHADA.Haka mahaifina ya bani labari.Hakai dai nayi ta wuce yan'uwana jaruman gasa ina kare musu kallo zuciyata nacigaba da daka.Su kuwa sai kyalkyala mini dariya sukeyi suna nuni cewa ga wani yaro wanda iyayensa suka gaji dashi.Ni dai ban tankawa dayansu ba har muka iso daf da karagar sarki Zaldasi muka zube a kasa bisa guiwoyinmu don girmama shi.Ina dago kaina nayi arba da wani jarumin gasar a gefen hagun sarki Zaldasi wanda yayi matukar girgizani ya bani mamaki,ba wani bane face matashin sarauyi wanda shima shekarunsa ba zasu haura nawa ba.Ko riga babu a jikinsa sai tarin guraye da layu na tsafi,jikinsa a murde yake fiye fa nawa,ya tara kwanji da jijiyoyi.Kai da ganinsa kasan cewa ya cika SADAUKI.Ina hada ido dashi sai ya murtuke fuska tamkar yaga bakin kumurci,koda ganin haka saina yi sauri na sake sunkuyar da kaina kasa.Adaidai wannan lokaci ne Imsar ya gabatar dani a gaban sarki Zaldasi a matsayin jarumin gasar dazai wakilci birnin Nurul Islam.koda jin haka sai sarki Zaldasi ya mike tsaye daga kan karagarsa ya taka gajeriyar matattakalar dake gabansa ya sauko ya kama kafaduna Ya tashe ni tsaye ya kura mini idanu,kawai sai ya bushe da dariya.Aikuwa sai fadawansa da sauran gaba dayan jama'ar dake cikin fadar ma suka kama kyalkyala dariya.Harsaida sarki Zaldasi ya tsuke bakinsa sannan fadar tayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi a cikinta.A sannan ne Zaldasi ya nuna mini wannan jarumin gasa sa'annan yace kaga wancan yaron shine SA MAZA GUDU,kabar ganinsa yaro kamar kai ka raina shi to yafi manya da yawa a cikin jaruman nan hadari kuma zai iya lashe wannan gasa.Tabbas mutanen birninku sunyi ganganci da suka turoka ka wakilcesu kuma inda basu turo kowa ba da saina afka musu na baje garin gaba daya,duk da cewa garinku ne kadai garin da yake baiwa dukkanin sarakunan nahiyar nan tsoro.Tabbas iyayenka da sarkinku basa kaunarka kawai so suke ka mutu.Kofa gama fadin hakan sai sarki Zaldasi ya juya ya koma izuwa kan karagarsa ta mulki ya zauna sannan ya dubi wani bafadensa yayi masa inkiya.Take bafaden ya fito tsakiyar filin fadar ya tsaya ya dubi jama'a sannan ya dubi jaruman gasar yace,manyan baki daga sassan kasashen duniya,sarakuna,atta­ jirai,talakawa da jaruman gasa sarki Zaldasi ya gaisheku kuma yanayi muku lale marhaban da kuka amsa gaiyatarsa kuka halacci wannan gagarumar gasa ta farauta wacce ba taba yin kamarta ba a duniya.A halin yanzu muna da jaruman gasa mutum dubu Ashirin da daya,da saba'in da bakwai daga birane dabam dabam na wannan nahiya tamu da sauran nahiyoyi na duniya.Ina mai sanar daku cewa gobe za'a fara wannan gasa,za'a shiga cikin dajin Sairul ne gaba daya wato jaruman gasa,alkalan gasa da kuma yan kallo wadanda zasu iya siyar da rayukansu ko su kare kansu domin morewa idanuwansu da kallo.Yanayin wannan gasa shine za'a shiga farautar wani takadarin Zaki ne mai suna NURUL MAUT domin a kashe shi azo da gawarsa nan gaban sarki Zaldasi.Fiye da shekaru tamanin baya wannan zaki mai suna Nurul Maut ya hana shiga dajin Sairul,domin duk wanda ya shiga baya fitowa kuma har abada ya bata kenan ko gawarsa ba za'a gani ba.Shidai wannan zaki sihirtaccene an tabbar da cewa KAIFI da TSINI basa tasiri a jikinsa,kuma komai yawan dakaru,komai iya yakinsu da karfin sihirinsu indai sukayi arba dashi sunansu gawa.Shi kansa Zaldasi kimanin shekaru bakwai baya daya shiga dajin Sairul domin ya kashe Nurul Maut da kyar ya dawo gida a raye cikin mugayen raunika.Bisa wannan dalili ne sarki Zaldasi ya shirya wannan gasa kuma duk wanda ya kashe wannan zaki ladansa shine

Chapter 11 of 19