Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin addininka.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa a wajen shi kuwa Hibairu kamuwa yayi da tsananin farin ciki nan take ya biyawa Sa Maza Gudu kalmar Shahada ya maimaita.(ALLAHU AKBAR).Adaidai wannan lokaci ne alkalin gasa ya dubi jama'a yace yanzu za'a tafi hutu na sa'a Uku sannan a dawo ayi wasan karshe tsakanin Jarumi Hibairu da Yarima Lahaman.Koda gama fadin hakan sai suka buga tambura aka buga algaita.Nan take sarki Kamzal ya mike tsaye yana kankame da abokinsa wannan mahayin doki wanda yazo duk jikinsa jini suka fice daga cikin filin gasar gimbiya Zuhuta na take masa baya.Nan da nan filin ya watse amma kokarin mutane shine su gano ko wanene wannan bako da yazo wajen sarki Kamzal amma hakan ya gagara. Zan dakata anan.Ko wani zai iya fada mana wanene wannan bakon da yazo a cikin jini? To me karatu muzo zagaye na 2 karshen wannan littafi Saura 9 C kawai yarage mushiga wani sabon littafin me suna...... kIBIYA RATSA MAZA amma sbd yadda azumi ya danno ina so mufara gobe jumma,a ko kuma bubarshi har zuwa bayan sallah meye ra,ayinku akai ga kadan daga sabon littafin namu na gobe ko bayan sallah KIBIYA RATSA MAZA Littafi na Daya(1) Part A Gudu takeyi iya karfinta domin ta ceci rayuwarta saboda bala'in dya biyo ta,babu abinda za'a kwatantashi dashi face ajali.Babu abinda zai baka mamaki face wannan budurwa dake wannan azababben gudu,kyakkyawa ce abar kwatance,kuma cikin shigar yaki take,ga takobi a hannunta tsirara ba'a ciki kufe ba.Saboda karfin gudun da takeyi tamkar tafin kafarta zai tabo keyarta,amma duk da haka waige waige takeyi a cikin alamun tsoro,duk da cewa kana mata kallo daya zaka gabe cewa jarumace ta kwarai mai kirar sadaukai.Kai bama ita ba hatta aljanu da tsuntsaye dake cikin wannan daji da take gudu a cikinsa tsoron dajin sukeyi da abinda ya biyota saboda masifu da bala'in dake tare dasu ballantana kuma bako irinta wanda bai tana shigowa dajin ba.daga naku Prince Auwal Prince Auwal Auwzab ★SA MAZA GUDU★!!! Littafi Na Tara (9) Part C TAKUN KARSHE. Prince Auwal Auwzab SUKA FICE DAGA CIKIN FILIN GASAR GIMBIYA ZUHURA NA TAKE MASA BAYA.NAN DA NAN FILIN YA WATSE AMMA KOKARIN MUTANE SHINE SU GANO KO WANENE WANNAN BAKO DA YAZO WAJEN SARKI KAMZAL AMMA HAKAN YA GAGARA.Kai tsaya sarki Kamzal ya wuce da bakonsa har kuryar turakarsa daga nan yasa kuyanginsa suka kaishi kewaye sukayi masa wanka sannan aka bashi wadansu tufafi masu daraja irin na sarki Kamzal ya sanya.Ba wani bane wannan bako face SARKI SHARKUF IBINI AFFAN Mahaifin Malika da Yarima Lahaman.Sarki Kamzal na zaune a cikin babban falonsa saiga sarki Sharkuf ya shigo cikin sauri ya mike tsaye ya tarye shi suka sake zama tare.Zamansu keda wuya sai kuyangin suka kawowa sarki Sharkuf abinci da abinsha mai daraja irin nasu na sarakai.Saida sarki Sharkuf ya ci yasha ya gamsu sosai sannan sarki Kamzal ya dubeshi cikin nutsuwa da alamun damuwa yace yakai abokina bani labarinka.Meya faru na ganka tsulum a birnina cikin jini kace kace?Koda jin wannan tambaya sai nan da nan idanun sarki Sharkuf suka ciko da kwalla saboda takaici sannan yace dana Yarima Lahaman ne yake shirin yi mini JUYIN MULKI domin ya haye karagata kuma yake kokarin kashe yar uwarsa gimbiya Malika.Burinsa shine ya kashe gaba dayan sarakunan dake wannan nahiya tamu ya mulki duk kasashenmu,ina can birnina bokan ya nuna mini dukkan shirinsa.Koda sarki Sharkuf yazo nan a jawabinsa sai sarki Kamzal yayi doguwar ajiyar zuciya yace tabbas nasan cewa Lahaman ya ajiye dakaru da yawa a bayan birnina don yakata amma ban taba sanin cewa karfin shirin Lahaman yakai yadda ka fada min ba yanzu.Lallai bamu da abinyi face addu'a a kan Hibairu ya sami nasara akan Lahaman. *Lokacin da Lahaman ya koma masaukinsa yayi bincike a hallarar tsafi yaga yadda mahaifinsa da bokansa suka sami nasarar kashe gaba dayan dakarunsa saiya kurma uban ihu ya zama kamar mahaukaci ya rinka dukan dakarun dake tsaronsa da kyar suka shawo kansa ya dawo cikin haiyacinsa.Sa'a uku bata cika ba filin gasar ya sake cika ya tumbatsa ya zamana cewa kowa ya hallara Jarumi Hibairu tare da yarima Lahaman na tsaye a filin gasar ruke da makamansu suna kallon juna.Nan take aka buga ganga suka kacame da masifaffen yaki ai kuwa sai jama'a suka kaure da ihu gami da shewa tafi da jinjina irin wanda ba'a tabayi ba.Saida suka shafe rabin sa'a suna mugun artabu babu mai nasara.Kwatsam sai Lahaman ya shammaci Hibairu ya sunkuya kasa ya danki kasa ya watsawa Hibairu a idanu.Kafin Hibairu yayi wani yunkuri tuni ya dankara masa sara a cinyarsa ta dama take kuwa wajen ya dare jini yai tsartuwa.Hibairu ya fadi kasa yana mitsittsika idanunsa domin su washe amma sunki.Lahaman ya dako tsalle sama domin sare kan Hibairu.Ba zato ba tsammani sai akaga Gimbiya Zuhura a sama ruke da takobi ta kare saran da Lahaman ya kawo masa kuma take ta sare hannun Lahaman wanda ke ruke da takobin hannun ya tsinke ya fado kasa.Lahaman ya kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji.Zuhura na dira a kasa sai ta sake dukan Kirjin Lahaman da kafarta guda.Saboda tsananin dukan saida yayi baya ya bugu da katangar filin gasar ya kife kasa yana amon jini a lokacin da gundulmin hannunsa ke shatatar da jini.Kawai sai gimbiya Zuhura ta dubi Lahaman tace ba kaine kadai jarumi ba kuma ka sani komai sammakonka wani a tafe ya kwana.Tana gama fadin hakan sai ta yar da takobinta taje inda Hibairu ke zaune a kasa dirshan a lokacin da idanuwansa sun washe gaban miliyoyin jama'ar dake wajen sai gimbiya Zuhura ta sumbaci Jarumi Hibairu a goshi da bakinsa sannan ta dubeshi tace masoyiyarka marigayiya Lasmin sau daya ta ceci rayuwarka ni kuwa sau biyu na ceci rayuwarka.Lasmin bata taba sumbatarka ba a gaban iyayenta da miliyoyin jama'a ni kuwa gashi yanzu na aikta hakan,shin yanzu ka yarda da cewa nafi marigayiya kaunarka? Koda jin wannan tambaya sai jarumi Hibairu yayi murmushi yace tabbas yanzu na yarda cewa son da kike mini yafi wanda marigayiya take yimini,waishin yaya akayi kika sami wannan gagarumin karfi da jarumtaka?Dama can ke jaruma ce ban sani ba?Koda jin wannan tambaya sai gimbiya Zuhura tayi murmushi tace kamar yadda kayi mamakin jarumtakata haka kowa anan yayi hatta uwata da ubana basu taba sanin cewa ni basadaukiya bace kuma basu taba sani cewa ni da gagarumar MAYAKIYA ce ba.Kuma kasurgumar MATSAFIYA,duk abinda zai faru yau din nan na ganshi a madubin tsafi na fiye da watanni uku baya amma daga yau nayi watsi da dukkan tsafi don haka na umarceka daka shigar dani cikin addininka.Tana gama fadin hakan saita juya ta dubi Yarima Lahaman wanda ke kakarin mutuwa sakamakon jinin daya zuba a jikinsa mai yawa tace mutuwa ce sakamakonka bisa muggan aiyukan daka shuka a doron kasa.Aikuwa bata gama rufe bakinta ba sai kan Lahaman ya lankwabe ya kife kasa gaba dayan jikinsa ya sandare ya zama gawa.Nan yake aka kafa tutar musulunci a birnin Sarki Kamzal kowa ya karfi addinin Allah.A dalilin wannan abu daya faru ne gaba dayan kasashen dake nahiyarma suka karbi addinin musulunci.Hibairu ya auri gimbiya Zuhura shi kuma sarki Hilairu ya auri gimbiya Malika bayan sun koma birnin Madinatul Saura anyi bikin nadin sarauta.Kamar yadda Malika tayi alkawari saida ta raka sarki Hilairu har mahaifarsa aka sake gina garin amma saiya baiwa Sa Maza Gudu karagarsa ta mulki ya biyo matarsa izuwa birnin Madinatul Sauwara inda ya tayata tafiyar da harkokinta na mulki kuma sukayi zamansu na aure cikin jin dadi da kwanciyar hankali.Shima jarumi Hibairu saida ya koma mahaifarsa ya hadu da iyayensa inda jamaarsu sukayi farin ciki da dawowarsa Prince Auwal Auwzab Auwzab kuma sukayi masa jinjina bisa babbar nasarar daya samu ta jaddada ADDININ ALLAH a nahiyar gaba daya.ko nima AUW.ZAB nayi tawa jinjinar ga hibairu. Shi kuwa Sarkin garin nasu kunya ce ta kama shi bisa gabar daya dauka dashi da mahaifinsa don haka saiya durkusa bisa guiwoyinsa a gaban Hibairu ya nemi gafararsa.Take Hibairu ya yafe masa sannan yayi bankwana ga kowa ya koma can birnin Misra wajen amaryarsa gimbiya Zuhura ya cigaba da rayuwarsa da ita cikin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa. ALHAMDULILLAH Dukkan Godiya Ta tabbata ga Allah subahanu wata'ala.Tsarki ya kara tabbata akan fiyayyen halittu Annabi Muhammad (S.A.W) Anan Muka kawo karshen wannan Littafi Mai suna SA MAZA GUDU.Dafatan Littafin ya Wa'azantar,ya Nishadantar kuma ya Kayatar daku. Sai Mun Hadu a wani littafin Insha Allah. GA sunan littafin da zamushiga a Yau basai gobe ba dan haka kowa ya shirya da daddare kawai sai kunjini nine naku Prince AUWAL AUW.ZAB KIBIYA RATSA MAZA Littafi na Daya(1) Part A Gudu takeyi iya karfinta domin ta ceci rayuwarta saboda bala'in dya biyo ta,babu abinda za'a kwatantashi dashi face ajali.Babu abinda zai baka mamaki face wannan budurwa dake wannan azababben gudu,kyakkyawa ce abar kwatance,kuma cikin shigar yaki take,ga takobi a hannunta tsirara ba'a ciki kufe ba.Saboda karfin gudun da takeyi tamkar tafin kafarta zai tabo keyarta,amma duk da haka waige waige takeyi a cikin alamun tsoro,duk da cewa kana mata kallo daya zaka gabe cewa jarumace ta kwarai mai kirar sadaukai.Kai bama ita ba hatta aljanu da tsuntsaye dake cikin wannan daji da take gudu a cikinsa tsoron dajin sukeyi da abinda ya biyota saboda masifu da bala'in dake tare dasu ballantana kuma bako irinta wanda bai tana shigowa dajin ba.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19