Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sarki zai bashi auren 'yarsa Gimbiya Lasmin,sannan zai raba wannan birni na Kisra biyu ya bashi mulkinsa,sannan ya maidashi daya daga cikin manyan fadawa.Koda gama gadin haka sai aka buga tambari,kuma aka busa algaita.Faruwar hakan keda wuya saiga Gimbiya Lasmin 'yar sarki Zaldasi ta fito daga cikin gidan sarautar ta ratso cikin tsakiyar fadar kuyangi da dakaru na musamman na take mata baya.Wohoho Allah shine ke ikonsa,hakika halittun Allah yawa garesu,babu wanda yasan adadinsu saidai shida ya halicci kayansa.Lokacin da Gimbiya Lasmin ta ratso cikin tsakiyar fadar sarki Zaldasi,sai gaba dayan mazajen dake wajen suka dimauce suka fita daga haiyacinsu saboda ganin tsananin kyawunta da kyawun siffar jikinta.Wasu da yawa basu san sa'adda suka wangame bakunansu ba suna dalalar yawu,wasu kuwa sambatu suka kamayi kamar sun zautu.Kyawun Gimbiya Lasmin yafi karfin a wassafashi,saidai abinda idanu suka ganiKawai.Jama'a da yawa suna zargin cewa Lasmin ba mutum bace zalla saboda ganin yadda kyawun nata ya wuce tunanin mai tunani,babu wani abu wanda mutum zai iya kwatantashi don baiyana kyawunta. Nima ganin tsananin kyawunta yasa na gigice na tsaya cak ina kallonta saboda tsananin mamakin kyawunta.thanks agode Tohm mun ci wajen fiye da rabin Sa Maza Gudu littafi na Biyar,dan anyi rubutun da yawa.. Daga: SA MAZA GUDU Littafi na biyar (5) Part B Kyawunta ya wuce tunanin mai tunani.Babu wani abu wanda mutum zai iya kwatantashi don baiyana kyawunta.Kai tsaye gimbiya Lasmin ta wuce izuwa inda Sarki Zaldasi ke zaune fuskarta cike da annuri tamkar wata daren sha biyu tana tayin wani irin murmushi mai taushin gaske Wanda ka iya sa mutum ya manta da duk wani bakin cikin rayuwarsa.Lasmin ta zauna akan kujera dake daf da karagar sarki sukayi kus kus irin na 'da da mahaifi cikin raha da annashuwa,sannan ta waigo ta fara kallon jaruman gasar dake cikin fadar tun daga kan jarumi na farko.Koda tazo kaina sai ta tsaya kyam ta kura mini ido ko kiftawa batayi a lokacin da ni kaina naji zuciyata ta buga da karfi,kuma kunya ta baibayeni don haka sai nayi kasa na sunkui da kaina kas.A wannan lokaci Sa Maza Gudu ne a kusa ni don haka shine jarumi na gaba wanda ya kamata ta kalla amma sai taki ta daina kallona,hakane tasa jarumi Sa Maza Gudu ya fusata ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone nan taje yaji ya tsane ni kamar yadda ya tsani mutuwarsa saboda tsananin kishi.Kawai sai ji nayi yayi mini rada a kunne yace,kai yaro na fuskanci cewa sa'arka tana da yawa a cikinmu nan gana dayan jaruman gasa,kai ne kadai wanda Gimbiya Lasmin ta kura maka idanu tana raba da kai ta daina cigaba da kallonmu,to kasani cewa na rantse da darajar iyayena idan har ban lashe wannan gasa ba na mallaki Gimbiya Lasmin to babu wanda ya isa ya mallaketa saidai mutum ya sami wani ladan dabam.Koda naji wannan batu sai na dubi Sa Maza Gudu cikin murmushi nace,ai kuwa kishi zai kasheka a banza domin ina ji a jikina cewa nine zan lashe wannan gasa,kuma sai na mallaki Gimbiya Lasmin kanaji kana gani.Kafin Sa Maza Gudu ya bude baki ya sake maida min da wani martani sai kawai muka ji wannan bafade na sarki yace,yaku jama'a sarki yace nayi muk albishir da cewa gobe za'ayi shiri a tafi dajin Sairul domin fara yin wannan gasa kuma za'a kammala tane a cikin kwanaki uku rak,duk jarumin daya sami nasarar kashe wannan zaki mai suna Nurul Maut kafin rana ta fadi bai iso nan fada ba to yasha wahalar banza,A wannan rana ta uku,da wannan nake muku sallamar kowa sai goben da safe ake bukatar kowa yazo nan fada domin ayi wannan gagarumar tafiya izuwa cikin dajin Sairul.Koda gama fadin hakan sai sarki Zaldasi tare da 'yarsa Gimbiya Lasmin suka mike tsaye suka sauko daga kan tudun da kujerun suke suka nufi hanyar fita daga cikin fadar suna rike da hannun juna a lokacin da gaba dayan jama'ar dake cikin fadar suka dukar da kawunansu kas saboda biyayya.Saida Lasmin ta iso bakin kofar fita daga cikin fadar sannan ta waigo,ai kuwa sai muka hada idanu dani da ita tayi mini wani irin murmushi mai taushi mai dauke da alamar tambaya wanda ya dimautani,naji kamar an bani sarautar duniya sannan ta juya suka kule mana da gani gaba daya.A sannan ne taro ya watse kowa ya kama gabansa,mutanen gari suka tafi izuwa gidajensu,mu kuma baki muka tafi izuwa masaukinmu.Lokacin dana isa masaukina sai kuyangi suka kawo mini abinci mai rai da lafiya,amma sai na kurawa abincin idanu na kasa ci,ba komai ne ya haddasa hakan ba face da zarar na dauko loma guda zan kai bakina saina rinka ganin hoton fuskar gimbiya Lasmin akai.Koda ganin haka sai hankalina ya dugunzuma ainun saboda na gane cewa tabbas na kamu da tsananin son wannan 'yar sarki,wata zuciyar tace dani amma dai kai wawa ne kuma shashasha,akan wane dalili zaka kamu dason abinda bazaka samu ba,shin bakaga irin gawurtattun jaruman da suka shiga wannan gasa bane wadanda suka fika karfi,jarumta,tsafi da komai? Ai ko a mafarki ma kada kayi tunanin zaka iya mallakar gimbiya Lasmin,haka dai na cigaba da wannan tunani har na gaji sannan naci abincin naje nayi alwala nayi Sallah.Bayan na idar da Sallah saina daga hannayena sama na shiga yiwa Allah kirari ina mai ambaton sunayensa tsarkaka nace,Ya Sarki da bashida abokin taraiya,kaine mai Daukakawa da kaskantarwa,babu wani abu dazai gagareka,Allah ka sani cewa karfina da wayo na bazai sa su bani nasarar komai ba a cikin wannan gasa,don haka bani da wani abin dogaro sai kai.Na mika dukkan lamarina a gareka Allah sani cewa idan na lashe wannan gasa na sami babbar dama dazan tallata addininka da ita,saboda haka ka karfafeni da karfinka na sami wannan nasara.Burina shine na jaddada kalmarka a doron kasa,koda kuwa bazan mallaki Gimbiya Lasmin ba,haka dai Jarumi Hibairu ya cika addu'arsa da sake kiran sunayen Allah sannan yaje ya kwanta.wa shegari kuwa da safe kofar gidan sarautar Sarki Zaldasi ya tumbatsa da mutane ana jiran sarki ya fito a tafi izuwa bakin dajin Sairul inda za'a gabatar da gasar farauta.Inda ace mutum na tsaye a wannan wuri idan yaga dumbin jama'ar da sukayi dandazo sai ya zata gaba dayan mutanen duniyar ne suka taru.Hakika masu mulki sunayin abinda suka gadama kuma duk wanda ya tumbatsa a mulki da kudi dole ne ayi masa biyayya tunda sawun giwa dole ne ya take na rakumi.Gaba daya manyan sarakunan da sukazo wannan gasa saida suka yi jiran fitowar sarki Zaldasi har tsawon sa'a biyu sannan ya fito bayan kowannensu ransa ya baci bisa ganin yadda aka kaskantar da darajarsu.Da fitowar sarki Zaldasi,sai aka ganshi tare da 'yarsa Gimbiya Lasmin bisa ingarman dawakai farare guda biyu tare da dakaru,bayi,borori da kuyangi suna take musu baya.Ba tare da bata wani lokaci ba sarki Zaldasi ya dubi sarakunan da sauran manyan baki cikin izza da jinkai tade da takama yace,kuyi hakuri na bata muku lokaci ban fito da wuri ba,hakan ya faru ne sakamakon 'yata Gimbiya yau ta makaro bata tashi daga barci da wuri ba.Nasan cewa kowa ya fito da shirin yin kwana uku a bakin dajin Sairul,to amma ina mai yi muku albishir da cewa duk abinda kowa zaici yasha a cikin wannan daji na tsawon kwana ukun ni zan samar dashi,koda gama fadin hakan sai Sarki Zaldasi ya daga hannu yana mai bada inkiya a fara tafiya.Nan take kuwa dakaru suka fara wucewa gaba sannan alkalan gasa,jaruman gasa,sai muna yan kallo na jama'ar gari da sauran baki.A wannan rana Gimbiya Lasmin tayi shigar kayane masu launin ruwan kwai,hatta mayafinta,takalminta da abin adon gashinta duk launin ruwan kwai ne,hakika shigar ta kara mata kyau matuka,kuma hakanne yasa mazaje suka sake dimautacewa musamman jaruman gasa domin nan take suka aiyana a ransu daidai su rasa gimbiya Lasmin gwara ma su rasa rayuwarsu a wannan kasa.( Nikam bakin ciki ne ya ishe da ban shiga wannan gasa ba).Koda Gimbiya Lasmin taga kowa ita yake kallo amma shi jarumi Hibairu ko kallonta baiyi ba sai ta kamu da tsananin mamaki,kuma hankalinta ya dugunzuma domin wannane karo na farko data taba ganin saurayin da bai dimauce ba sakamakon yin arba da ita.Abinda bata sani ba shine tsananin kunya da kawaici ne yasa baya son ya rinka kallonta kuma baya son sonta da begenta su ci gaba da addabar zuciyarsa kamar yadda sauran mazajen dake wajen,domin ya lura da yadda samari da yawa suke neman zaucewa akanta.Saida aka shafe sa'a uku da rabi ana tafiya daga birnin Sarki Zaldasi sannan aka iso bakin farkon Dajin Sairul.Da isowa sai aka yada sansani aka shiga kafa tantuna,kowanne sarki da jama'arsa suka kafa tantuna a wuri dabam haka ma sauran manyan baki da sauran baki.Nan take akaga bayi da kuyangin sarki Zaldasi sun fara dora manyan tukwane bisa murhu ana kunna wuta don cin abinci.A sannan ne kuma wasunsu suka fara fito da yayan itatuwa iri iri tare da ruwan sha suna rabawa izuwa kowanne sansani,saida ya zamana cewa ko ina da ina abinci da abin sha ya yalwata babu wanda ya taba jakar guzurinsa.Tunda Sarki Zaldasi da 'yarsa Gimbiya Lasmin suka shiga cikin tanti basu fito ba har saida rana ta fadi,dajin yayi sanyi a lokacin da wata irin iska mai karfi ke kadawa,sannan aka busa algaita aka buga tambari.Koda jin haka sai kowa ya shiga shiri aka mimmike tsaye aka taho izuwa sansanin sarki Zaldasi,ba tare da bata wani lokaci ba sarki Zaldasi da gimbiya suka fito daga cikin tanti suka tsaya,take Zaldasi yasa ka kirawo gaba dayan jaruman gasar suka taru a gabansa.A wannan lokaci ne Gimbiya Lasmin ta fara kallonsu daya bayan daya domin taga Jarumi Hibairu amma sai taga babu shi a cikinsu sai Jarumi Sa Maza Gudu wanda shine kusan sa'ansa.Kuma tana hada idanu dashi taga ya kura mata idanu yana murmushi,kawai sai ta daka masa harara ta kauda kai tana mai cigaba da kallon sauran jaruman gasar cikinalamun damuwa.Nan take Sa Maza Gudu yaji wani irin kishi ya turnukeshi saboda ya gane cewa ni takeso ta gani,kuma rashin ganin nawa ne ya daga mata hankali ainun.Ba komai ne yasa na makara ba wajen amsa wannan kira ba na sarki Zaldasi face tun lokacin da aka sauka a bakin wannan daji sa'adda aka shiga tantuna sainaji na kagu dana shiga cikin dajin na Sairul ba don komai ba sai saboda a iya yawan farautar danayi a can birninmu ban taba ganin daji mai ban sha'awa ba kamar wannan na Sairul saboda komai nasa dabam ne dana irin sauran dazuzzuka.Dajin na dauke da manyan bishiyoyi dogaye ababen sha'awa sannan akwai manyan koramai da fadamomi,ga tsuntsaye da sauran kananun dabbobi amma manya dabbobin ma tamkar babusu a cikin dajin.Babu wanda yasan lokacin dana shiga cikin dajin Sairul batare danaji an baiwa sauran jaruman gasa umarnin shiga ba,saida na shafe sa'a tara da rabi ina tafiya acikin dajin ban hadu da dabbar data haura kare a girma ba face manyan macizai wadanda ta gabansu nake giftawa amma ko kallo ban isheshu ba.Sudai wadannan macizai sun kasance manya manya msu faska faskan kawuna da kuma kwala kwalan idanu ababan tsoro,suna da matukar kwarjini daban tsoro,koma jarumtakar mutum idan yayi arba dasu saiya firgita amma sai gashi cikin ikon Allah ina wuce ta gabansu lafiya lau ko kyakyawan motsi basuyi ba bare su kawo mini hari.Duk sa'adda naji yunwa ko kishirwa saina bude wata yar karamar jakata ta guzuru wadda na rataya a kafadata na dauko gasasshen nama ko ruwa,ko sau daya ban yada zango ba.Tunda na shigo cikin jejin nake ta karanta addu'o'i ina neman tsari a cikin zuciyata,hakan ne ma yasa naji ko tsoro banaji.Kwatsam ina cikin wannan tafiya sai naji wani irin gurnani mai tsananin ban tsoro ya cika dajin gaba daya,ba wai gurnanin bane ya tsorata ni face rashin sanin daga inda ya fiot da kuma rashin ganin dabbar da tayishi.Gurnanin naji shine a gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasa,hakan na nufin cewa abin tsoro yana nan a ko ina kuma akoda yaushe zai iya fitowa ta ko ina.Cikin sa'a sai naji bakina yaci gaba da kiran sunayen Allah ina neman tsarinsa da taimakonsa,maimakon nacigaba da tafiya sai na tsaya cak a inda nake na dafa kufen takobina ina mai gyara tsayuwar,kawai jira nake naga ta inda dabbar zata taso mini na tareta mu fafata.Tsulum!sai naga wani narkeken zaki ya baiyan a gabana,tazarar dake tsakaninmu bata wuce taku ashirin ba,tunda nazo duniya bantaba ganin zaki mai girma,kwarjini da ban tsoro ba irinsa.Kallo daya nayiwa zakin na tabbatar da cewa rikakke ne kuma tsohon gaske,Allah ne kadai zai iya cewa ga iya adadin shekarunsa a duniya,kai da gani kasan cewa yawan dadewar zakin nada nasaba da karfin sihirin tsafin dake jikinsa.Take na gane cewa lallai wannan zakin ne da ya gagari kowa kuma shi ake so a kashe cikin wannan gasa ta farauta wadda sarki Zaldasi ya shirya.Nanfa muka kurawa juna idanu nida zakin aka rasa Wanda zai afkawa wani tsakaminmu muka rinka yin kallon kallo,shin shakkar juna mukeyi ko kuwa kowannenmu akwai shirin da yakeyi. Nima ganin wannan gawurtaccen Zaki yasa na tsorata na tsaya anan.Mu hadu a part c. SA MAZA GUDU Littafi na Biyar (5) Pat C Ko kuwa kowannenmu akwai shirin da yakeyine? Amsar dana kasa baiwa kaina kenan,kawai sai na jiyo sautin bugun tambarin sarki gami da bushin algaita daga can farkon dajin,kawai sai na jiyo da baya na falfalo da azababben gudu ina mai karanta wata addua ta musamman ai kuwa sai gashi inayin wani irin gudu na ban al'ajabi tamkar gudun kibiya yayin da aka sakota daga cikin baka da gawurtaccen sadauki ya tabe.Nan danan cikin dakiku kadan naga na iso inda muka kafa sansani,cikin sauri na kutsa ta cikin mutane na isa can gaba inda jaruma gasa suke na shiga cikinsu na tsaya ina fama haki zuciyata cike da zulumi da tunani,ba komai nake tunani ba face waishin wannan zaki ya biyo ni kuwa.Amma ai inda ya biyo ni koda bai cimmini ba ya kamata ace shima yanzu ya iso nan.A daidai wannan lokaci ne sarki Zaldasi ya bude baki yace,yaku jaruman wannan gasa kuyi sani cewa yanzu ne zan baku umarnin shiga wannan daji domin ku farauto zakin nan Nurul Maut wanda duk ya sami nasarar kashe shi daga cikinku yazo dashi nan gabana shine zakaran gasa,wanda zai zamo mijin gimbiya kuma ya mulki rabin kasata ko ya karbi dukiya mai tsananin yawan da bayansa ma bazasuyi talauci ba.Zaku shiga cikin wannan daji tare da jajurtattun alkalan gasa wadanda sune zasu bayar da tabbacin wanda ya lashe gasa bisa gaskiya.Da wannan furuci nakeyi muku bankwana,wanda duk ya rasa rayuwarsa a cikin wannan daji zamu girmama gawarsa kuma mu daraja kabarinsa yadda har abada baza' manta dashi ba.Kuma da tsawon kwanaki uku na farautar Nurul Maut a cikin wannan daji.Koda gama fadin hakan sai Sarki Zaldasi ya daga hannun take kuwa aka busa wani kaho irin na mafarauta,take gaba dayan jaruman gasar suka juya da baya suka ruga izuwa cikin dajin Hairul.Koda wajen da jaruman ke tsaitsaye ya zama wayan sai ya rage saura mutum daya jal a tsaya kuma ba wani bane ba face Jarumai Hibairu,kawia sai ya dukar da kansa kas cikin girmamawa ya gaida sarki Zaldasi da gimbiya Lasmin sannan ya dago kai ya dubi Lasmin yayi mata wani irin kallo mai dauke da murmushi kuma ya daga mata hannu yana mai yi mata nuni da cewa lallai zai lashe wannan gasa.Kawai sai Hibairu ya juya da baya ya falfala da masifaffen gudu,bisa mamaki sai akaga nan da nan Hibairu ya riske sauran yan'uwansa abokan gasar ya kutsa ta tsakiyarsu har ya riski wadanda suke kan gaba.Cikin kaduwa Gimbiya Lasmin ta dubi Sarki Zaldasi tace,yakai Abbana anya kuwa wanann matashin saurayin mutum ne,dubi fa yadda yake yin wani irin gudu na ban al'ajabi har yana tserewa manyan zaratan jarumai.Koda jin wannan tambaya sai Sarki Zaldasi ya bushe da dariya.Al'amarin daya baiwa Lasmin mamaki kenan,daga can kuma sai taga ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin dariyar kuma ya dubeta cikin nutsuwa yace,ai wannan karfin gudunsa ba komai bane ba,abin bukata kawai shine yazo da gawar zaki Nurul Maut.Wata kila da yawa daga cikin jaruman gasar sun fishi karfin gudu,kawai sunki nuna wane saboda ai sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo,me akayi yanzu wasa farin girki.Kada ki manta cewa kwana uku za'ayi a cikin wannan daji ana farautar zakin,kinga ashe duk jarumin daya baiyana dukkanin karfinsa da dukkan shirinsa a yanzu ya zama cikakken wawa,koda jin wannan batu sai Lasmin ta gyada kai tace,kai nidai ina ganin cewa juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,akwai alamun cewa wannan yaro zai iya tabuka abin kirki.Koda jin haka sai sarki Zaldasi ya murtuke fuska ya dubi Lasmin a fusace a karon farko a rayuwarsa a gareta.Al'amarin daya razanata kenan ainun,jikinta ya kama kyarma.Sarki Zaldasi yace,inda kinsan wanene Hibairu da kuma hadarin da zamu shiga idan ya lashe wannan gasa da baki fadi haka ba,idan ma baki san dalilin da yasa na kaiwa kasarsu takardar gaiyata ba izuwa wannan gasa to yanzu ki sani cewa bisa binciken da nayi a hallarar tsafina na gano cewa nan gaba mutanen kasar zasuyi karfi sosai har suzo su mulki wannan nahiya gaba daya,kuma su rushe addininmu da al'adarmu wadanda muka gada tun iyaye da kakanni su shimfida tasu,hanya daya ce zamu bi muga bayansu,ba wata hanya bace face mu kama sarkin mafarautansu da dukkanin zuri'arsa mu kashe su saboda ta tsatson sane za'a sami wanda zai kawar da komai namu.Bisa binciken nawa sarkin mafarautan nasu matarsa daya jal a duniya kuma dan sama daya ne jal kuma ba wani bane dan nasa face wannan yaro Hibairu wanda suka turo ya wakilci kasartasu a wannan gasa.Burina shine Hibairu ya mutu a cikin wannan gasa a cikin dajin Hairul,kuma tabbas nasan cewa mutuwar zaiyi tunda duk duniyar nan banga wanda zai iya kashe Zaki Nurul Maut ba kuma kin sani cewa duk wanda yayi arba dashi sai ya mutu.Ina mai tabbatar miki da cewa gaba dayan jaruman gasar nan har dama alkalan gasar da suka bisu mutuwa zasuyi.Koda Sarki Zaldasi yazo nan a zancensa sai hankalin Gimbiya Lasmin ya DUGUNZUMA ainun,tausayin gaba dayan jama'ar da suka shiga dajin ya kamata nan take idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata ta dubi sarki Zaldasi cikin fishi tace,haba yakai Abbana yanzu ashe saboda rai guda jal kakeson ka hallakar da wadansu dubban rayuwakan kuma shine kadai dalilin da yasa ka shirya wannan gasa ashe badon ka samo mini mijin aure bane?Idan har wannan saurayi Hibairu kakeso ka kashe me yasa ba zaka kashe shi ba shi kadai ka bar sauran jama'ar su koma izuwa garuruwansu?Kada faka manta cewa zaka raba iyaye da yayansu ne kuma zaka raba mataye da mazajensu,ka mai dasu gwagware,kuma zaka zama BAKIN TAKOBI mai raba yan uwa da masoya.Koda tazo nan a zancenta sai mahaifinta ya juyo a fusace ya dubeta,wannan dalili yasa tayi shiru cikin shakku. Nima ganin Sarki Zaldasi ya fusata,ni dake bayan Gimbiya Lasmin yasa na firgiçe na tsaya tsak.Wannan shine karshen Sa Maza Gudu 5 Mu hadu a Sa Maza Gudu littafi na shida(6) don jin cigaban wannan kasaitaccen kayataccen labari. Insha Allahu anjima zamu cigabaAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTSA MAZA GUDU Littafi na Shida (6) Part A KAFIN Lasmin ta gama rufe bakinta tuni Sarki Zaldasi ya tari numfashinta yana mai daka mata tsawa yace,shin kin manta ne cewa tun kafin zamanin ubana ma ba'a hulda da mutanen kasar su Jarumi Hibairu akan auratayya,iyayenmu da kakanninmu sun hane mu da hakan kuna sun tabbatar mana da cewa mu zage dantse don gano hanyar da zamuga bayansu kafin suzo su shafe addininmu da mulkinmu.Idan har na ce zan kashe wannan yaro da hannuna ko nasa wadansu su kashe shi to bazan yi nasara ba amma na gano cewa tabbas wancan Zakin Nurul Maut zai iya kashe shiDa farko nayi farin ciki dana ga zuciyarki a kansa ne kadai ta karkata amma da na tuna illarsa a tare damu sai bakin ciki ya baibayeni naji na tsaneshi fiye da komai.Koda gama fadin hakan sai sarki Zaldasi ya bushe da dariyar mugunta har ya juya ya koma cikin tantin bai daina yin dariyar ba.Ita kuwa Gimbiya Lasmin sai ta bishi da kallo kawai cikin tsananin takaici a karo na farko taji ta tsaneshi duk da kasancewarsa mahaifinta wanda ke nuna mata tsananin kauna.Nan taje Lasmin taji kamar ta ruga da gudu taje ta gayawa jaruman gasar da sauran alkaln gasa da yan kallo duk sirrin da mahaifinta ya gaya mata yanzu domin su fasa shiga cikin dajin na Sairul domin su tsira da rayuwarsa.Kamar Sarki Zaldasi yasan abindake cikin zuciyar Lasmin har yaje ya kwanta a cikin tantinsa da nufin yasa akirawo makada da mawaka su debe masa kewa ta farin ciki bisa zai cika burinsa daya gagari iyayensa da kakaninsa,sai ya fasa ya kirawo manyan dakarunsa yace dasu,kuje kusa a zuba ido sosai akan 'yata kada a kuskura a barta tabi bayan jama'ar da suka nufi cikin daji nan don kada ta baiyana sirrinmu ga dayansu.Dakarun suka risina suka an gama ya shugabanmu,nan take suka juya suka fice daga cikin tantin suka rarrabu a cikin sansanin don tabbatar da tsaro,ita kuwa gimbiya Lasmin sai ta juya ta koma cikin nata tantin zuciyarta cike da tsananin bakin ciki gami da jin kiyayyar mahaifinta saboda bataga hujjar da zatasa ya hallaka dubunnan daruruwan rayuka ba saboda rai guda daya jal.Baya ga haka kuma saitaji ta kara kamuwa da tsananin son Jarumi Hibairu fiye da karon farkon ganinta ma dashi don haka sai ta aiyana a cikin ranta cewa idan har wadannan mutane da suka shiga cikin dajin Sairul suka mutu kuma ya zamana cewa Jarumi Hibairu bai lashe wannan gasa ba itama kashe kanta zatayi,wannan alkawari ne ta daukarwa kanta a cikin zuciyarta.Koda gama aiyana hakan sai Lasmin ta kwanta akan shimfidarta dake cikin tantin a lokacin da kuyanginta suka baibayeta suka zazzauna suka zagayeta suna jiran kowane irin umarni amma sai sukaji tayi shiru.Jim kadan kuma sai sukaga Hawaye na zuba daga cikin idanunta.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalinsu kenan,shugabar kuyangin ta dubeta tace,ya shugabata wanene ya bata miki rai haka ki gaya mana ko wanene muje mu gayawa sarki yanzun nan yasa ayi masa KISAN GILLA.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Lasmin tayi ajiyar zuciya tace,idan na gaya muku abinda yasani zubar da wannan hawaye nawa sai kun tsani komai da kowa hatta rayuwarku kuwa don haka kawai ku bar wannan magana sirri karku sanar da kowa.Tana gama fadin hakan sai ta lumshe idanunta tamkar so take tayi barci,amma a zahiri bata sone kuyanginta su cigaba da ganin zubar hawayenta.Wannan shine abinda ya faru a sansanin su Sarki Zaldasi.Al'amarin jaruman gasa,alkalan gasa da sauran yan kallo kuwa masu taurin rai da karfin zuciya,lokacin da muka nausa cikin dajin Sairul muna ta tsala gudu baji ba gani saida aka shafe sa'a uku ana gudu ba tare da an tsaya ba,wadanda basu saba yin gudu ba kuwa suka fara sarewa suna faduwa saboda gajiya da rashin sabo.Sudai jaruman gasar sunayin wannan gudu ne saboda kowannensu burinsa shine ya kasance shine jarumin farko da yayi arba da zaki Nurul Maut domin ya sami nasarar kashe shi ya dauko gawarsa.Tabbas inda wannan jaruma gasar sunsan yaya zaki Nurul Maut yake da basuyi tunanin yin arba dashi ba.Da tuni ma kowa ya hakura da shiga wannan gasa,saboda ninasan abinda na gani,ni kaina karfin imani ne yasa na cigaba da gudu a cikin dajin ina fuskantar inda zakin yake.Lokacin da muka shafe sa'a tara da rabi muna tayin gudu zallah a cikin dajin sai kusan kasa biyu cikin kaso uku na jaruman gasar suka sare suka fadi kasa saboda tsananin gajiya duk da cewa kuwa kowa na tafe tare da battar ruwansa yanasha

Chapter 12 of 19