Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT SA MAZA GUDU littafi na daya(1) Complete book Na Abdul Aziz sani madakin gini. Typing Suleiman zidane kd.. Whatsapp 09064179602... A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa a zamanin da babu wata huldar kasuwanci wacce tafi cinikin batayi,anyi wani babban birni mai suna Madinatul Zauwara. Birnin Madinatul Zauwara na karkashin mulkin wani gawurtaccen sarki ne ma'abocin jarumtaka wanda ya zamo gwarzon mayaki kuma dodo ha dukkan sarakunan dake nahiyar,ana kiran wanna sarki da suna Sharkuf bin Aufan. Duk wani abu najin dadin duniya Allah yabawa sarki Sharkuf,yanada 'ya'ya guda tara amma dukkaninsu mazane,sai mace guda daya.Babban dansa kuwa shekararsa talatin da takwas,ana kiransa da Lahaman. Lahaman ya gado maifinsa a sadaukantaka da jarumta kuma shine yake jagorantakar dakarun sarki a duk sa'adda za'a fita FARAUTAR BAYI. A tarihin fitarsa farautar bayi sau sittin da uku bai taba dawowa gida cikin rashin nasara ba,kuma duk sa'adda ya fita baya dawowa da kasa da bayi dubu uku,sau tari idan yarima Lahaman ya fita farautar bayi baya dawowa sai bayan wata biyu ko wata uku. Kasi daya cikin kaso uku na ribar bayin idan an siyar na yarima Lahaman ne,ragowar kason biyun kuwa na sarki Sharkuf ne.Saidai duk dakarun da aka fita wannan farauta dasu akan basu kyautar bayi bibbiyu. Bisa wannan dalili ne a gaba dayan 'ya'yan sarki Sharkuf babu mai kudin Lahaman,kuma wanda wanda mutane ke sa ran cewa za'a bashi gadon KARAGAR sarki to amma sho sarki Sharkuf yaki fadat wanda zai gajeshi. A gaba daya 'ya'yan sarki Sharkuf su tara babu wanda yafi soyuwa a cikin zuciyarsa sama da gimbiya Malika,duk abinda gimbiya Malika ta furta tanaso indai akwai shi anan duniyar sai sarki Sharkuf ya bata,kuma babu wata alfarma da zata nema wajensa ta rasa.Kai saboda tsananin kaunar da Sarki Sharkuf ke yiwa gimbiya Malika ko Fada zaije tare da ita yake zuwa,su zauna tare bisa KARAGAR MULKI,kuma duk taro mai mahimmanci idan bazai samu damar halartar ba,ita yake turawa ta wakilceshi.Sukan su ragowar 'ya'yan sarki idan suna son wani abu a wajen mahaifinsu saidai suyi kamun kafa da Malika,in ba haka ba kuwa bazasu samuba.Wannan dalili ne yasa dukkanninsu suke yi mata biyayyar dole duk da cewa sun girmeta. Yarima Lahaman ne kadai baya saurarenta kuma sai kiyayya da hassada ta shiga tsakaninsu,sabo da ganin kamara sarki zai iya hanashi karagar mulki ya bata. In badon Yarima Lahaman yana matukar tsoron sarki Sharkuf ba,da tuni yasa an hallaka Malika a asirrance,domin ya huta da fargabar dake zuciyarsa da kuma tsananin kiyayyar dake tsakaninsu,babban abinda yake kara baiwa Yarima Lahaman haushi shine duk abinda yake iyayi da kudi itama Malika tanayi,har ma tana iyayin abinda shi ba zai iyaba,saboda komai tsadat abu tana iya sayansa,saboda tanayin kasuwanci a boye ba tareda dashi kansa sarki ya sani na. Saida ya zamana cewa fiye ta rabin fataken birnin nata ne,kuma saida ya kasance a nahiyar gaba daya babu 'yar kasuwar da tafi Malika safarar kayan abinci da makaman yaki Bisa wannan dalili ne tayi sabo ainun da sarakuna da kuma manyan attajirai,ababan misalai.Da yawa daga cikin sarakunan da attajiran basa ganinta sai a karshen shekara.a wannan lokacine take kai ziyara kasa kasa tana karbat cinikin da aka tara a hannun wakilanta dake tafiyar mata da kasuwancinta.Sarki Sharkuf duk bai san wannan kasuwancin da take yiba,abinda yasani kawai shine duk karshen shekara tana shirya tafiya ta kai ziyara izuwa manyan kasashe hudu,don ziyartar manyan takunan bauta dake birnin Kisra,Farisa,Yemen da kuma Misra. A wannan lokacin ba'a barin kowa ya shiga cikin wadannan dakunan bauta face sarakai,manyan attajirai,manyan jarumai,da kuma kasaitattun bokaye.Duk sa'adda gimbiya Malika zata fita izuwa wannan gagaruman tafiya sarkin yakin birnin Madinatul zauwara ne yake yi mata rakiya tare da dakaru dubu uku domin tsaron lafiyarta,dama babban boka na kasar wanda ake kira Muzambil bin Samrad. Wannan gawurtaccen shiri da ake yiwa Gimbiya Malika na tsautsauran matakan tsaro,shi yasa Yarima Lahaman ya kasa kai mata hari,saboda ya tabbatar da cewar shi kadaine zai iya tarar sarkin yakin nasu da kuma bokansu kuma in dai ya tare su sai sun gane shi tunda sun san irin yanayin yakinsa da irin sihirn tsafinsa,idan kuma yaransa ya tuea sai asirinsa ya tonu an gane shi ya tura su. Burin Yarima Lahaman shine sarki ya mutu ya gaje karagarsa,to abinda ya aiyana a ransa shine a ranar zaisa a kama Gimbiya Malika da uwarta a kaisu kurkuku,bisa hukuncin daurin rai batare da sun aikata laifin komaiba,sauran kannensa kuwa zai tursasasu suyi masa biyayya,duk wanda yaki dole ne cikon biyu abu guda ya sameshi,kodai a batar dashi ko kuma shima a kaishi kurkuku ya karasa rayuwarsa a can. A ranar da ya rage sauran kwan uku kacal Gimbiya Malika ta tafi ziyartar da ta sabayi a karshen shekara ne,yarima Lahaman ya dawo daga farautar bayi.A wannan karon wata nahiya daban suka je suka riski wata karamar kasa kawai sai suka afkawa kasar da tsakiyar dare sukayi mummunar barna. A daren ne sarkin garin yayi sabon aure yana tare da amaryasa suna shirin more amarcinsu kenan Lahaman ya bayyana tsulum a gabansu.Nan take aka kama sarkin aka daure shi a gaban idanunsa yanaji yana gani kuma yana kuka Yarima Lahaman ya yiwa matarsa Fyade kuma yana gamawa da ita ya zare wuka ya lumamata a ciki,take ta sulale kasa matacciya.Koda sarki Hilairu yaga na kashe masoyiyarsa sai shima ya sulale kasa sumamme,Lahaman ya bushe da dariya,ya dubi yaransa yave"ku kama shi ku saka masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai mayar da sarki nawa. Suleiman zidane... Lahaman ya dubi yaransa yace "ku kamashi kusaka masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai mayar da sarki bawa,kuma nine GUGUWAR ANNOBA mai zuwa babu sallama.Haka dai yarima Lahaman yayita yiwa kansa kirari,har suka gama kama bayin dasuke bukata kimanin dubu hudu maza da mata a cikin wannan karamin gari,bayan sun kone gidaje da yawa sun kwashe dukiyoyi da yawa,nan take suka tusa keyar bayin harda sarki Hilairu suka fice daga birnin mai suna Baitul Laharas suka juyi suka nufi kasar Madinatul Zauwara. Bisa al'adar yarima Lahaman duk macen da yayiwa fyade take yake kasheta,har a birnin Madinatul Zaurawa kowa ya sanshi da wannan muguwar dabi'a.Saida sarki Sharkuf ya kafawa Yarima Lahaman doka cewa idan ya sake yiwa wata 'ya mace fyade ko ya kasheta zai cireshi daga matsayin yarima kuma ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kurkuki,sannan matan birnin suka samu nutsuwa da kwanciyar hankali.Bakomai ne yasa Yarima Lahaman ya tsani mata ba yake yi musu fyade kuma ya kashe su ba,sai saboda kiyayyarsa da da 'yar uwarsa gimbuya Malika itama tasan hakan kuma yin hakan da yake yi ne yasa taji ta dada tsanarsa fiye da kowa a duniya. Da yammaci ne sakaliya Yarima Lahaman ya shigo cikin birnin madinatul zauwara tare da rundunarsa ta mayaka da kuma bayin daya kama a daure cikin sarka nan bugunsu da bulala ana ingiza su,kai da ganin bayin kasan cewa sunsja bakar wahala,domin duksun rame akwai alamun sunsha yunwa a wanannar doguwar tafiya da sukayi,shi kuwa sarki Hilairu sau uku yana yunkurun kashe kansa saboda bakin ciki amma dakarun Lahaman na hanshi da karfin tsiya su tattakashi cikin wulakanci da muzantawa ,duk sa'adda sarki Hilairu ya tuna cewa an kashe masa matarsa Zailat wacce yake matukar SO DA KAUNA,kuma ya tuna cewa an rabashi da mulkinsa,dukiyarsa,kuma shi da jama'arsa da yawa an maishe dasu nayi,dakarunsa na yaki kuwa kusan gaba dayansu aka kashe.ko ina a cikin birnin nasa gawarwakine da jini,sai ya fashe da matsanancin kuka yaji ya tsani kansa da rayuwarsa gaba daya. Sarki Hilairu ya kasance Kyakkyawan saurayi abin kwantance mai kwarjini da haiba irin ta sadaukai amma ko kadan bai kasance jarumi ba,kuma bai taba yin yakiba a rayuwarsa,sarautar ma tsintarta yayi a sama ba gado yayi ba.Sarkinsu na da bashi da 'da ko jika,kuma bashi da wani dan'uwa face Hilairu.Mahaifiyar Hilairu ta kasance Kuyangar Sarkin da ya mutu,don haka shi dan baiwane,ba dan wata 'yantacciya ba,ta haka ne ya gaji wannan sarauta. A daidai wannan lokaci yarima Lahaman ya shigo cikin birnin madinatul zauwara sai akayi akasi gimbiya Malika ta fito rangadi zata fita izuwa bayan gari domin yin garauta a daji.A wannan lokaci tana tare da tsirarun dakaru wandan basu fi su arba'in ba.A daidai kofar shiga cikin birnin sukayi kicibus.A wannan lokaci yarima Lahaman na cikin tsananin farinciki bisa ganin dinbin dukiyar daya samo wacce baitaba samun kamartaba,gami da lafiyayyun bayin da yasan cewa zai siyar dasu da darajar gaske.Koda yarima Lahaman da gimbiya Malika suka hadu sai kowannensu ya murtuke fuska suka bata rai kamar an aiko musu da sakon mutuwa,da ko magana basayi da juna.Koda Gimbiya Malika ta dubi tarin dukiyar da Yarima Lahaman ya samo gami da tarin bayi,sai takaici ya kamata saboda tasan ce Allah ne kadai yasan irin mugun zaluncin da akayi wajen samosu,Kwatsam sai idanun Malika suka kai kan sarki Hilairu,tana hada ido dashi sai zuciyar ta ta buga da karfi nan take a karon farko a rayuwarta taji ta kamu da tsananin son 'da namiji don haka batsan sa'adda ta kura masa idanuba har suka gifta juna tana waigensa.Abinda ya kara mata sonsa mashi ne shima ya kura mata idanu,cikinalamun tsananin kaduwa da mamaki,har ya tsaya cak ya daina tafiya sai da ka buga masa kulki aka hankadashi gaba yana turjewa na dada bugunsa sannan ya janye.Ashe ba wani abu ne yasa Sarki Hilairu ya kura mata idanu ba face kamanninta yazo iri daya sak da matarsa wacce yarima Lahaman ya kashe tamkar an tsaga kara.Dama tun acan birinin na sarki Hilairu yaran Lahaman suka yita tsegumin suna cewa matar sarki Hilairu tana kama da Gimbiya Malika.Yana daga cikin dalilin ma da ysa Yarima Lahaman ya kasheta,tun da ya tsani Malika,Ya tsani duk mai kama da ita.Har su yarima Lahaman suke kule gimbiya Malika baya daina waigensu ba,kuma zuciyarta bata daina bugawa ba,da zafi,nan dai ta kudurci aranta cewar ta kowanne hali sai ta mallaki wancan bawa wanda ita yanzu ta kamu da tsananin son sa farat daya a farkon haduwa.Babban tashin hankalin ta shine tasan cewa ko nawa zata siyeshi yarima Lahaman bazai siyar mata ba,saboda kiyayyar dake tsakaninsu. Al'amarin Yarima Lahaman kuwa lokacin da yaga gimbiya Malika ta fito rangadi daga cikin gari tare da tsirarun dakaru,sai wani abu ya fado masa a rai.Nan take yayi tunanin ya batar da kamanninsa ya dawo cikin dajin ya afkawa masu tsaronta,amma sai wata zuciyar tace dashi a'a,yin hakan abune mai matukar hadari,domin idan asirinsa ya tonu ba zatayi masa kyauba.Domin akwai lokacin da kwatankwacin hakan ta faru da kyar ya samu kubuta daga zargin sarki.Al'amarin ya faru ne wata rana sa'adda ana zaune a fada,duk su biyun shida Gimbiya Malika suna zaune a fadar tare da sarki,Malika na daman Sarki shi kuwa yana hagunsa,sai ga wani mao gadin kofar gari ya shigo cikin fadar a guje cikin gigita,da zuwansa sai ya zube kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa,muryarsa na rawa kuma kansa a sunkuye ya bude baki yace,"Ya shugabana,kayi sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka hango. Suleiman zidane kd Yace,ya shugabana kayi sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka hango wadansu bakin dakaru acikin shigar bakaken kaya,bisa dawakai sun rufe fuskokinsu sun nufo kofar gari,koda muka hango su muka yunkura zamu busa kahon yaki,sai suka ja baya suka nausa cikin daji suka bace bat tamkat basu taba wanzuwa ba.Bisa wannan dalili ne yasa muka kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,shi yasa muka ga ya dace muzo mu sanar da kai domin kasan matakin da ya kamata a dauka.Kodajin labarin,sai sarki Sharkuf ya bushe da dariya,sannan yace,ai kua tasan gidan mai babar sanda,tsoro suka ji shi yasa suka juya da baya.To amma akwai wani boyayyan al'amari a tare dasu,domin ko da wasa ba'a taba samun 'yan fashi ko 'yan harin da suka taba kusantar kusa da kofar garin nan ba,saidai suyi shawagi a can wajen gari ciki dazuzzuka,lallai ruwa baya tsamin banza,kuma da dan gari akanci gari.Akwai wani munafuncin da ake shiryawa tare da waninmu.Koda gama fadin haka,sai sarki ya dubi yarima Lahaman yace,ya kai yarima,maza ka dibi dakari dubu kuje ku bi sawun wadannan dakarun sumame,idan sun fice daga yankin kasata ku kyalesu,idan kuma suna ciki ku yakesu ku kashe su,kada kubar mutum daya ya tsira da rayuwarsa.Koda jin wannan umarni,sai yarima Lahaman ya mike tsaye zumbur da nufin yaje yayi shiri,amma sai Gimbiya Malika ma ta mike zumbur tasha Gabansa tace,ya akai da'uwana ina rokonka ka tafi tare dani,domin idanuna suna son ganin ko suwaye wadannan marasa kunya da rashin tsoro har suke tunanin zasu iya kawo mana hari.Koda jin haka,sai kowa ya cika da mamaki a fadar musamman ma sarki Sharkuf wanda a saninsa ko magana Yarima da Gimbiya basayi,amma yau wai itace ke rokonsa akan ya tafi da ita wajen gari don yakar abokan gaba.Lokacin da yarima Lahaman yaji bukatar gimbiya,sai ya dubi sarki domin yaji ta bakinsa ko zai amince ya tafi ta itan,Bisa ga mamaki sai gashi sarki ya Amince.Abin ya baiwa kowa mamaki a fadar,soboda ansan cewa a duniya babu abinda sarki Sharkuf ke so sama da gimbiya Malika,kuma baya yarda taje wani wuri mai hadari,kuma yasan irin kiyayyar dake tsakaninta da dan'uwanta Yarima Lahaman,to amma me yasa yanzu ya amince ya tafi tare da ita izuwa yaki?Ita kanta Gimbiya Malikan saida ta yiwa kanta wannan tambayar a cikin zuciyarta,nan dai Malika tabi Yarima Lahaman a bya cikin farinciki suke fice daga cikin fadar.Suna fita Lahaman yayi shigar yaki ya tara dakaru dubu sukayi hawa itama Malika sai aka kawo mata nata dokin ta hau suka fice daga cikin gidan sarautar suka nausa cikin dajin suna masu bin sawun dawakan da suka gani.Koda suka iso wani wuri inda hanya ta rabu biyu,sai Lahaman yaja limzamin dokinsa ya tsaya cak yayi nazarin hanyoyin sannan ya juya ya dubi gimbiya Malika yace,Daki tsaya anan ke da rabin dakaruna dan tabbar da tsaron lafiyarki,ni kuma da sauran dakarun zamu shiga ciki harsai mun isa inda wadannan abokan gaba suka buya.Kodajin wannan batu,sai Malika ta ce a'a ba haka za'ayiba,ai yanzu baka da tabbacin cewa hanyar da zakabi can abokan gabar suke,saidai muma mubi daya hanyar idan muka riske su,sai mu yakesu,in kuma kaine ka riskesu ka yakesu.Sa'adda yarima Lahaman yaji wannan batu,sai yayi murmushi yace ,idan wani tsautsayi ya sameki kada kiga laifina tunda dai ni ga inda nace ki tsaya kuma kika ki.Malika ta maidawa Lahaman martanin Murmushin tace,Saki ranka tamkar tsumma a randa domin shi kansa tsautsayin baya zuwa kusa da Malika,in kuwa yazo saidai ya shafi waninta amma ba ita ba.Anyi gumurzu a cikin dajin an kashe gaba dayan dakarun dake tare da Malika amma ita ta tsira da rayuwarta da lafiyarta,aka dawi gida da kyar yarima ya kubuta daga zargin sarki,bayan yasa tambayoyi har yana hada gumi duk da yarima yayi wannan tunanin sai ya kudirce a ransa sai ya dawo cikin dajin ya kashesu farat daya,sannan itama ya kasheta,kuma ya alakanta mutuwarta da 'yanfashi ko miyagun dabbobin daji.Abu na biyu kuma da ya fado masa a rai shine koda bai kasheta ba,to lallai bazai bari ta mallaki wannan bawa nasa ba wato sarki Hilairu saboda ya lura da irin kallon da take masa ya gane cewa ta kamu da sonsa.Lokacin da yarima Lahaman ya isa gida sai ya ware bayi maza guda saba'in mata guda talatin wadanda sune mafi lafiya,da kwarjin da kyawu.Yasa aka kaisu can wani gida nasa na musamman wanda ba kowa bane yasan da shi,aka boye su a can da zummar cewa baza'a sake fitowa dasuba sai ranar da babbar kasuwar birnin take ci,domin ya sayar dasu da daraja ga manyana attajirai.Daga cikin bayin gudu darin kuwa harda sarki Hilairu. Sa'adda aka kai su Hilairu wannan gida aka watsa su izuwa cikin daki,sai suka ga an kawo musu abinci da abin sha lafiyayye,wanda rabonsa da su ci irinsa yafi kwana arba'in tun kafin akawowa birninsu Hari.Nan fa bayin suka rude suka kama wawason abincin suna ci kamar dabbobi,mazansu da matansu har suna kokawa.Shi kuwa sarki Hilairu sai ya zuba musu idanuwa kawai yana kallonsu shashashu.Ya rike kimarsa ta sarki kuma yaki neman abincin dukda yunwar yakeji.Kawai sai ya koma gefe daya ya zauna ya daga kansa sama yana tunani.Ba komai yake tunowa ba face fuskar gimbiya Malika.Take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,wai shin matata bata mutu ba ko kuwa wacce na gani dazu aljanace,da har zata biyo ni tana dada yaudarata?Ashe yarima Lahaman yasa dakarunsa su zuba ido sosai akan sarki Hilairu saboda kada ya kashe kanso ko yayi yunkurin guduwa ko kuma a turo a sace shi.Sarki Hilairu na zaune cikin wannan hali na tunani sai daya daga cikin bayin wani katon matashi mai.. Zidane kd Suna Kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin zafin nama,juriya,bajinta da jarumta.Nan da nan suka fara lalata duk kayan kawar dake cikin turakar.Karar takubbansu kuwa ya firgita dakaru,suka rugo da gudu izuwa cikin turakar rike da makamai tsirara domin zatonsu wasu 'yan simame ne suka hauro cikin gidan sarautar.Amma duk wanda ya shigo cikin turakar sai yaga ashe sarki ne da Malika suke yaki.Sai ya kamu da tsananin Mamaki ya koma gefe daya ya rakube yana kallon ikon Allah,amma da yakin ya sake nutsuwa sai kallon ma ya gagara ,kuma hankali ya dugunzuma domin tun suna gumurzu a cikin kuryar daki saida suka dawo babban falo,daga nan suka fito waje,sai gasu a cikin harabar.Ba komai ne ya dugunzuma hankalin gaba daya jama'ar dake cikin gidan sarautar ba face ganin yadda sarki da Malika ke kaiwa junansu mugayen hare hare irin na abokan gabar dake son hallaka juna farat daya.Lokacin da aka shafe rabin sa'a ana wannan dauki na dadi,sai sai salon fadan ya sauya domin a sannan ne gimbiya Malika ta gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane saboda ji tayi alamun ta fara gajiya har takai cewa da kyar take iya tare saran sarki saboda Karfinsa da nauyinsa.Duk sa'adda ya kawo mata saran ta tare sai taji kamar katon dutse ya kwado mata.Amma saboda bakin naci da muguwar juriya taki yarda ya fadi kasa kuma bata daina yunkurin maida martani ba.Duk da cewa wani lokacin har durkushewa kasa take bisa guiwarta amma sai kaga ta mike zumbur a haka.Saida suka sake shafe wata rabin sa'ar bataje kasa ba,amma kuma ta gaji likis.Ana cikin haka ne sarki ya shammaci Malika ya kwarfi kafafunta a tayi sama da baya taje ta gwara bayanta a jikin katangar gidan sarautar ta fado kasa a mutukar galabaice ta kasa tashi.Koda faruwar hakan,sai sarki Sharkud ya sauke takobinsa kasa yayi jifa da ita sannan ya kama yiwa Malika tafi.Nan fa gaba dayan Jama'ar gidan sarautar suka kama yiwa Malika tafi.Sarki Sharkuf ya nufo Malika fuskarsa cike da murmushi yazo daf da ita ya mika mata hannu ta kama,ya tashe ta tsaye suka rungume juna,sannan ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace,Ina tayaki murna saboda kece jaruma ta farko wacce ta iya jure yin gumurzu dani har tsawon sa'a guda.Hatta yayanki Yarima Lahaman da kyar ya jure tsawon rabin sa'a.Bani labari yake 'yata yaya akayi kika iya yaki haka da jarumtaka?Koda jin wannan tambaya,sai Malika tayi Murmushi sannan ta zaiyana masa a wuraren da ta koyo yaki kamar yadda ta gayawa Yarima Lahaman,lokutan da take fita ziyara kasashe.A karshe ta kara da dace batun Jarumtaka kuwa ai kaima kasan cewa barewa batayi gudu ba danta yayi rarrafe.Na gaji sadaukantaka ne a wajenka da wajen kakana na uwa.Koda jin wannan batu,sai Sarki Sharkuf ya kyalkyale da dariya yace,Tabbas maganarki dutse ce,to naji wannan yaya kuma batun wannan rauni dake hannunki da kuma batun dakarun da suka yi miki rakiya izuwa farautar?Koda jin wannan tambaya,sai Malika tayi ajiyar zuciya tace,'yan fashi ne suka kawo mana harin bazato kafin muyi wani yunkuri sun kashe gaba daya dakarun nawa.Ni kuwa saina afka musu muka ruguntsume da azababban yaki.Da suka ga nafi karinsu,sai suka girgiza suka bace bat na nemesu na rasa.Lokacin da Malika tazo nan a zancenta,sai taga sarki yayi mata wani irin kallo na rashin yarda sannan yace,yake 'yata ta yadda naga irin jarumtakarki a yanzu babu wasu 'yanfashi a wannan nahiyar da zasu tareki da yaki batare da kin samu nasarar kashe koda mutum dayaba daga cikinsu a cikin dakiku kadan bare harma wani daga cikinsu ya sami nasarar yi miki wannan raunin.Shin yanzu idan akaje wajen da kukayi gumurzun za'a sami gawar koda mutum daya daga cikinsu?koda wannan tambaya sai Malika ta gyada kai tace,Ai muna fara yakin suka bace kawai sa'a ce tasa shugabansu yayi nasarar yimini wannan rauni.Sarki Sharkuf yayi dan guntun murmushi mai nuna alamun rashin yarda,sannan ya dubi Malika yace,A nahiyar nan gaba daya mutum daya ne zai iya fafatawa dake ya samu nasarar yi miki wannan rauni,kuma ba wani bane face dan'uwanki Yarima Lahaman.Fada min gaskiya shine Lahaman yakai miki harin bazato ne?Malika ta girgiza kai tace,Ta yaya Lahaman zai kai min hari alhalin lokacin da nake shirin fita daga cikin garin nanne ya dawo daga Tafiyarsa ta FARAUTAR BAYI,a bakin kofar gari muka yi sabani,shin baizo gareka bane a lokacin? Sarki ya daga kai yace tabbas yazo gareni harma naga dumbin dukiyar daya samo gami da bayi masu daraja amma ai bansan abinda zai iya aikwata ba bayan mun rabu.Malika tace na gaya maka cewa Lahaman bashi da hannu a wannan hari da aka kai mini.Ya kamata ka sani cewa duniya kullum sauyawa takeyi, a koda yaushe za'a iya samun bakin Jarumai na Al'ajbi,koda jin wannan batu,sai jikin sarki Sharkuf yayi sanyi yayi murmushi yace,kin fini gaskia yake 'yata,yanzu me kike bukata daga cikin ganimar da yayanki ya samo a wannan farautar bayi da ya fita?Shin dukiya kike so ko bayi.Koda jin wannan tambaya sai jikin Malika yayi sanyi,ta sunkui da kanta kasa tayi shiru kamar bazata ce komai ba.Daga can kuma sai ta kama hannun sarki Sharkuf taja shi izuwa inda wadansu kujeru na shakatawa suke,suka zauna tare sannan ta dube shi a lokacin da idanunta suka ciko da kwalla tace,ya kai abbana kayi min aikin gafara bisa abubuwa biyu dana aikata

Chapter 1 of 19