Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ashe ta san da bikin ba ta gaya mata ba, in shi ya ƙi sanar da ita, yadda ta ɗauke ta 'yar'uwa ai ya kamata ta sanar mata. Dangin miji kenan. "Ni ma ban san zai ƙara aure ba, hasashen haka kawai na ke yi, don bai gaya mini ba." Ta ce tana hawaye. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Amma Faruk ya cika tantiri. Wannan wane irin rashin dalci ne? Wallahi tun da ya je mini da maganar ƙarin aure nan, na yi masa tatas da na ga ba zan iya hana shi ba, tun da addini ya ba shi dama. Sai na ja masa kunne kan ya yi adalci ya sanar miki kuma ya yi miki kayan faɗar kishiya." "Hmmmmh!" Kawai ta ce tana share hawaye. Ganin ba ta ce komai ba sai ta kalle ta ta ce,"Nufin shi haka zai ƙara auren ba tare da kin yi taro ba?" Ba ta ce mata komai ba don bata dan me za ta ce mata ba. "Bar ni dashi bari na kira sa ɗan ƙwal uba." Ta ce cikin takaici. Ciki suka shiga ta zauna, daidai lokacin da kiran wayar ya shiga. Kira har sau bakwai ta yi masa ba a ɗaya ba. Tana zaune cikin takaici tana jin kamar ta je ta duke shi, sai ga shi ya kira ta."Hello Anty Asiya, an ɗaura na zama mijin Rashida." Ya ce mata cikin tsananin farin ciki. Maganar da ya yi ta ji kamar ya soka mata allura."Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ta furta sai hawaye shar! Da sauri ta share don karta gani, amma ta makara domin idanunta na kanta. Tausayi da kunyar abin da ya aikata, ya sa ta ta lailayo ashra ta yi masa."Ashe ba ka da kirki Faruk? Kan me za ka ƙara aure ba tare da ka sanar da uwargidanka ba?" "Haba Anty Asiya, saboda wannan kike so ki ɓata mini ranar farinciki? Ina gaya mata mai za ta yi? Na san dai iyayenta talakawa ne ba su da abin da za su yi mata. Ballantana na sa ran za a kawo mata wani abu. Zuwa kawai za su yi su ɓata mini gida su cinye abinci." Takaici da haushi da ya sanya ta ce,"Uwarka na ce Faruk! Wai mai yasa ba ka da mutunci ne?" Ta ce masa cikin tsananin kunyar abin da ya faɗa. "Kin ga Anty ina cikin taro zan kira ki." Ya ce yana ƙoƙarin kashe wayar. Kafin ta yi magana ya datse wayar. Dafa Nasreen ta yi da take kuka sosai, jin abin da ya ce."Ki yi haƙuri kin ji wallahi dole ya dawo, sai ya yi miki kayan faɗar kishiya kuma sai ya san bai kyauta ba." Ta ce tana mamakinsa. "Ki barshi kawai, fatana Allah yasa ya zaɓo wacce za mu zauna lafiya da ita." "In sha Allahu ina fatan haka nima, kuma ki ci gaba da haƙuri. Kin san dole in aka ƙara wa mace kishiya ta yi haƙuri." "To," Ta ce tana share hawaye. Zama ta yi tana ta bata baki har ta ji kishin ya ragu. Wayarta ta ɗauka ta kira mahaifiyarsa ta zayyane mata komai. Sosai ranta ya ɓace ta ce,"Ki bar ni da shi, wallahi dole ya ɗaya tarewar nan, har sai ya yi mata kayan faɗan kishiya, kuma ya ba ta abin da zata dafa ta tara mutane. Wannan wane irin rashin mutunci ne? Ga duka ga mari ga tsinka haka. Ko da cinya ya barta suka yi taro ai za ta ji daɗi." "Faruk ba ya kyautawa Mama." Ta ce mata jin abin da ta ce. "Ki ƙyale shi zan kira shi. Mika mata wayar." Ba musu ta miƙa mata ita kuma ta karɓa. Sosai ta ba ta baki sannan ta yi mata alkawarin ta sa ya shi dole ya yi. Bayan an gama ɗaurin auren aka je dinner. Daga dinner a mota sai da ya ji kamar zai karɓi haƙkinsa, saboda yadda ta rinƙa masa. Shi kan yasan ya zu ya yi aure, tun kafin ta shigo cikin gidansa. Da ƙyar suka rabu bayan ya fara more sadakinsa. A hanya Mama ta kira shi. Da ya ɗaga ya gaishe ta. Tatas ta yi masa sannan ta kafa masa cewar dole a ɗaga tarewar har sai ya yi mata. Ransa ya ɓaci sosai jin abin da tace. A ransa ya sanya hakan ba zai faru ba, wai gurguwa da auren nesa. Yadda ya ƙosa a kawo ta ya more sadakinsa. Don shi kadai ya san zumuɗin da yake yi. Sauri yake yi ya koma don sun ce za su kawo kaya. Cikin ɓacin rai ya shiga cikin gidan. Bai samu ya yi mata rashin mutunci ba, saboda masu kawo kaya da suka iso. Nasreen na ganin kayan ta tabbatar da auren na sa. Ɗaki ta koma har suka gama jera kayan a ɗayan ɗakin da ya gyara. Da yake gidan four bedrooms ne. Nata sai na yara da kuma na sa. Ɗaya tun da ya fara burin aure ya rufe shi. Ya zama za su rinƙa sharing falo da kicin. Bayan an gama jera kayan ya shigo cikin ɗakin. Tana zaune da carbi a hannunta tana ja. Ɗayan hannun kuma tsaƙon da Marwana ta tura mata na assignment da ta yi take dubawa, duk da cewar hankalinta ba shi sosai a kan wayar. Ganin ya shigo ya sanya ta miƙe."Saboda na aure ki ba zan yi aure ba, ko kuma ke kike aure na da dole sai na gaya miki zan ƙara aure?" Ya yi mata tambayar yana zare idanunsa. Miƙewa ta yi cikin tsoro tana kallonsa sai kuma hawaye."Abban Raihan, ni fa matarka ce ina da haƙƙi a kanka, ya kamata ka gaya mini." "Ashe da sauƙi tun da matata kike ikona. Na ɗauka uwata za ki ce?" Ya yi mata tambayar yana zare mata idanu. Jin abin da ya ce ya sanya ta share hawayenta tare da zubowar wasu."Look Nasreen, kin san yanzu ba ɗaya bane da da, saboda ina da wata matar, ba zan jure rashin mutunci ba, don ban ga amfanin ki a gidannan ba, sai dai ki ci ki yi kashi ki tara mini yara?" Jin bin da ya ce ta kalle shi,"To mene auren Faruk? Ai samun zuriya shi ne albarkar aure." "Ni ba wannan bane albarkar aure. Na huta da matata ta yi mini biyayya, kuma ta so duk abin da nake so." Kallonsa kawai ta yi cikin rashin hayyaci ba tare da ta ce masa komai. Ganin haka ya sa shi harararta. "Kin san Allah ba zan ba ki ko ƙwandala ki tara mini gayyar talauci ba, kin hana na tare da amarya saboda baƙin kishinki. Hotel za mu je don yau babu abin da zai hana ban more sadakina ba, kuma kika ƙara sanar wa Mama waje za ki yi sai ki je ki yi zawarci, na ga uban da zai ƙara aurenki, a yadda kika yangwaɗe babu mamora a jikin ki, dubi fa yadda kika dawo komai ya shafe, gabakiɗaya kin haɗe da ko'ina, kuma kike kishin kar na auri wata? "Kallonsa ta yi cikin tsananin mamakin abin da ya furta."A haka ka aure ni Faruk? Lokacin da ka aure ni a haka na ke? Kai da kanka ka sha yabon surata, ita ma kanta wacce za ka auri za ta dawo haka matuƙar za ta yi ciki ta haihu, kuma ka kasa ba ta kulawar da ya kama." Kallonta yake yi kamar wata mahaukaciya."Sai aka ce miki mahaukaci ne ni da zan barta ta haihu? To ki jira ki zuba idanu ki ga yadda za mu more rayuwa, saboda ban aure ta ba don ta haihu." "In har tana da hankali ba za ta yarda da hakan ba, saboda babu macen da za ta yarda da wannan. So kake ta kare rayuwar ta ba tare da ta haihu ba? Akwai sufa da yanayin rayuwar da mutum yake shiga, dole yaranka kawai za su taimaka maka." "Ki bar ni in na shiga lokacin sai ki zo ki gaya mini haka. Ina da kuɗi da kyau sam ba zan tagayyara ba." "Ba komai kuɗi suke yi ba kuka dukkaninsu masu wucewa ne." Ta ce masa tana kallon sa. Tsaki ya ja yana harararta."Na dai gaya miki sai ki san yadda za ki zauna a cikin gidan nan. Don wallahi in har kika yi gigin da na sake ki, ba za ki taɓa samun miji irin na." Kuka kawai take yi ta kasa furta kalami. Ganin haka ya saki tsaki ya fice tare da buga ƙofar. Rintse idanunta ta yi cikin tsananin bakin ciki. Ta ɗauka wasa yake mata, amma sai ta ga ya kwashi tarkacen da zai kwana da shi ya fice. Kuka take yi tun tana yi har ta ji idanunta sun ƙafe. Ita kanta ba ta san tana da kishi haka ba. Bayan kiran sallar Isha sai ga kiran Ahmad. Tana ganin kiran ta ki wasu zafafan hawaye sun wanke mata fuska. Da ƙyar ta samu ta tsayar da hawayen ta yi sallama "Hello Nasreen, da gaske Faruk ya ƙara aure?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta fashe da kuka. Jin kukan ya sanya shi yarda da jita-jitar da ya ji. "Haba Nasreen amma kika kasa sanar damu? Wata ƙawar Mama ta sanar mata, don ta san matar da ya aura." "Ni ma bai gaya mini ba." Ta ce masa cikin muryar kuka. Jin abin da ya ce sai tausayinta ta ƙamashi. Daga ji ya san tasha kuka. Ƙoƙarin kwantar mata da hankali ya shiga yi. Sai da ya ji ta ɗan saki sannan ya ce,"Wayata babu caji bari na kai shagon Ado mai caji, zan kira ki in na karɓo." "To Yaya, ka gaida su Mama." "In Sha Allahu." Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinsa. Mama da ke gefensa tana jin abin da take faɗi. Ganin ya kashe wayar ya sanya ta saki salati. "Kai amma Faruk, ba shi da kirki. Ace za ka ƙara wa mace kishiya, amma ka kasa sanar mata. Haba wannan zaluncin ya yi yawa. Ko taro ta yi ai ta rage raɗaɗi." Ina zai gaya mata tun da ya raina ƙuranmu? Ya san bamu da abin da za mu kawo mata, da ya san za a kawo mata abin duniya zai gaya mata." Ya karashe maganar cikin ɓacin rai yana tausayin ta. "Wallahi Baba ya cuci Nasreen." Ya ƙara cewa. Mama dai shiru ta yi ɗin maganar ma babu amfani sai ɓacin rai. Tana kwance tana juyi tamkar kasa. Wani irin tsananin kishinsa take ji. Miƙewa ta yi don ta ɗauro alwala ta yi sallah. Don in ba haka ta yi ba wataƙila kafin wayewar gari zuciyarta ta buga. "Ashe haka mata suke ji in aka ƙara musu kishiya?" Ta ce a ranta tana share hawaye. A bayi wanka ta yi saboda yadda take jin zafi yana keto mata. Tana ƙoƙarin alwala sai ta ji kamar zubowar abu a ƙasanta. Tsoro ta ji din dama tana tunanin ciki ne da ita. Kusan wata uku ba ta ga al'adarta ba. Duk da cewar tun haihuwar Musaddik sai ta yi wata huɗu ba ta gani ba. Wannan dalilin ya sanya ta shiga kokwanto ko ciki ne da ita. Ganin jini ne gabanta ya faɗi. Ta rintse idanunta daidai lokacin da cikinta ya yi wani irin murɗawa. "Wayyo Allah!" Ta ce cikin tsananin ruɗani. Jin yadda mararta ta ƙulle. Fasa alwalar ta yi ta koma ta kwanta, amma sai bacci ya gagara. Tana kwance tana juyi tana kiran sunan Allah. Ko jirgawa ta ɗauki wayarta ta kasa. Salatin ta ya farkar da Raihan. "Umma, ba ki da lafiya ne?" Ya ce mata tana kallonta. "Eh Raihan, ɗauko mini wayata na kira Ya Ahmad, ya zo ya kai kai ni asibiti." "To," ta ce tare da miƙewa tana tangaɗi ta ɗauko mata wayar inda ta nuna mata. "Umma, in je in ta so Abba?" Ta ce mata ganin yadda take masoso. "Abba bai kwana gida ba." "To ki kira shi." "Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye. Ba ta fahimci komai ba sai ta yi shiru tana kallonta. Yau pages ɗin masu kishiya ne a fito masu kishiya a gaya mana abin da aka ji da mijinki zai ƙara aure. Akwai wacce mijinta ya ɓoye mata kamar Nasreen? In akwai wane mataki ta ɗauka? Ga Nasreen duk da ba ta zama da shi na daɗi, amma zafin kishi ya sanya ta yi ɓari. Tana ta kiran ango yana can gurin amarya ya ji sabon guri🙈🙈🙈💃💃 to ko zai zo ya taimaka mata ko kuma amarcinsa zai sha da amaryarsa Rashida? Faruk sau a sausauta don ma bazawara ce 😆😆 makar ta duk da na yi da tsayi in kuka tashi kaina zan iya antayo muku next page don mu ji yadda za ta kaya. Aci gaba da comments ina murmushi ina shan ganta ina karantawa. Na gode muku sosai Allah ya bar ƙauna. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 13 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Raihan ba zai zo ba, yau ya samu wacce ta fini." Ta faɗi hakan tana hawaye. Ba ta fahimci komai ba sai ta yi shiru tana kallonta. Da ta kira wayar sai ta ji a kashe. Tunawa da ta yi ya ce ba shi da caji, ya sanya ta yi tunanin ƙila bai karɓa ba. "Wa zan kira?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali, domin har ta fara fita hayyacinta. Maman Muwaddat ta faɗo mata. Da sauri ta nemi layinta, amma cikin rashin sa'a wayar a kashe. Juyi take tana salati. Ƙoƙarin miƙewa ta yi don ta je ta ƙwankwansa musu, amma da sauri ta kwanta jin ba za ta iya tafiya ba. Kwanciya ta yi kan gadon ta ce,"Wash Allah zan mutu!" Kuka take yi sosai ta sadaƙar mutuwa za ta yi. Wayar ta ƙara janyowa ta nemi layinsa don ganin za ta mutu. A lokacin yana kwance ya rungume amarya Rashida da take ji kamar za ta mayar da shi ciki, musamman ganin kalar soyayyar da yake nuna mata. Kiran ya shigo daidai lokacin da ya ƙara rungumota ya haɗa bakinsu. Jin su suke a wata duniyar. Haƙiƙa ji yake yau ya samu matar da yake so, wacce za ta yi masa duk abin da yake muradi a makwanci. Ganin yadda ta cire kunya take nuna masa kalar basirar ta, wacce ya yi farincikin da samun mace mai irin basirar. Sun yi nisa su shiga wata duniyar. Ana ta durzar amarci ba tare da ya kula da kiran Nasreen da yake ta shigowa ba. Ko da hankalinsu ya dawo jikinsu, Rashida ba ta barshi ya rintsa ba domin so take ta nuna masa ya samu kalar macen da take fata, don a daren cinye shi ne kawai ba ta yi ba. Jin sa yake cikin aminci ya rinƙa takaicin kansa da ya zauna ya auri mace Bahaushiya, wacce ba ta san komai ba, sai ta ci ta tara masa yara. Ai matan yare sune ka aure su zaka more aure, babu kunya a baka kalar rayuwar da kake so. Ganin ba zai ɗauka ba, ya sanya ta daina kiran tare da takaicin kiransa. Kishi da tunanin halin da suke ciki yanzu ya ƙara rikita jikinta. Ganin za ta mutu ya sanya ta nemi layin Marwana. Marwana dake zaune a falon Damir tana kallo. Little Marwana kwance a cinyarsa tana shafa kanta. Tun da cikin ya girma sai Hajiya ta sanya ta dawo gidan. Sosai cikin ya girma ga kumbura da take yi. Likita ya sanar da su ba za ta iya haihuwa ba, dole sai dai a cire cikin. Ɗin haka ya shawarci Damir da zarar cikin ya shiga wata tara za a yi mata C.A. A yanzu haka shirye-shirye tafiya suke yi zuwa waje, don har ya yi musu viser lokaci kawai yake jira. Wayarta a hannunta bayan sun gama waya da masoyinta. Har ta ije sai kuma ta ɗauka tana kallon hotunan da ya turo mata. Ganin kiran Nasreen ya tsorata. Kallon agogo ta yi tana mamakin dalilin da ya sanya ta kira ta. Tunawa da ta kirata da rana, amma ba ta ɗaga ba, ya sanya ta danna kiran tana dariya. "Hello Sahibata.."Maganar ta tsaya sakamakon ji da ta yi tana numfashi da ƙarfi ta ce,"Wash Allah! Marwana zan mutu cikina, don Allah ki sa ya direbana gidanku ya zo ya kaini asibiti. Na kira wayar ya Ahmad a kashe. Ɓari na yi." Ta ƙarshe maganar tare da sakin gigitaccen ƙarar da ya tayar da hankalinta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Nasreen ɓari ina Faruk?" "Ki taimaka mini Faruk ba ya nan." Ta ce tare da kashe wayar. Ruɗewa ta yi ta rasa yadda za ta yi. Har ta fita don ta sanar da direba ya fito su je, amma kuma sai ta fasa ta koma ciki. Ɗakin Damir ta shiga ƙwankwansawa cikin tashin hankali tana kiransa. Damir da yake kwace rungume da matarsa yana tunanin halin da take ciki. Fatansa Ubangiji ya sauke ta lafiya, don ba zai iya rayuwa babu ita ba. Tun lokacin da ya haɗu da ita yake jin matuƙar ƙaunarta, ko lokacin da ya san cewar ita sikila ce, bai ji sonta ya ragu ba, sai dai tausayi. Soyayyarta daga Allah ne. Fatansa ta yi tsawon rayuwa, domin ba zai iya auren wata mace ba in har babu ita, ji yake da ta mutu gara ace shi ya rigata. Kullum tunani yake ina ma da za a ba shi damar ya zaɓi ciwon ya dawo jikinsa. Kai bakinsa ya yi ya sumbaci goshinta yana shafa kanta. Ƙwankwasa ƙofa da kiran da Marwana take masa, ya sanya hankalinsa tashi matuƙar gaske! Shi a tunaninsa wani ne ya mutu. Da sauri ya miƙe tare da sanya rigar da ya fito." Lafiya Marwana?" Ya ce mata tare da riƙeta ganin yadda ta ruɗe. "Ya Damir, ƙawata Nasreen ba ta da lafiya za ta mutu, don Allah mu je mu kaita asibiti." "Ke Marwana ki natsu ki yi mini bayani." Jin bin da ya ce yana girgiza ta ya sanya ta fashe masa da kuka."Nasreen ƙawata 'yar ajinmu ta kira ni tana kuka za ta mutu ta yi ɓari jini yana ta zuba." "Ɓari? " Ya yi mata tambayar cikin tsananin tashin hankali, sabida yana tausayin mata a wannan condition na ciki da haihuwa. Ya san cewa a wannan lokacin suna cikin tsakanin mutuwa da siraɗi. "Ɓari ta yi Ya Damir." Ta ce masa tana share hawaye "Ina mijinta?" "Baya nan." Ta ba shi amsa. "Kalli lokaci dare ya yi, kuma bai kamata mu fita ba, ina ga ba ri na kira Doctor Sadik ya je da ambulance a kai..." "Please, Yaya ba zan iya kwana ba, ba tare da na san halin da take ciki ba. Babu nisa sosai kuma duka yanzu ten ta yi, don Allah ka taimaka mata kar ta mutu. Mijinta bai damu da ita ba, kuma wallahi in don ta shi zai iya barin ta mutu." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa. Shuri ya yi yana jinjina lamari."Amma kin san abin da ya faru ko? Bana son matsala in kuma kin nace sai ku je da Idi direba." "Please, Ya Damir don Allah mu je da kai, za ka fi gudu a mota, kuma ko asibiti muka je za a fi kula ta." "Haba Marwa..." "I insist Yaya Damir, please." Ta ce tare da haɗa hannunsa. "Ba zan iya fita na bar ta ita kaɗai ba." "Don Allah ka taimaka yanzu za mu dawo, kuma Baba tana nan." Babu yadda zai yi, kan dole ya shiga ciki ya canza kayansa. A hankali ya ja mata ƙofar suka fice. Duk gudun da yake yi gani take ba ya gudu. "Don Allah ka yi sauri kar ta mutu." Da sauri ya kalleta yana mamakin abin da ta ce, tare da mamakin yadda take sonta. Shi a iya saninsa Marwana ba ta tara ƙawaye, sai ga shi ta yi ƙawa mace mai aure. "Duk iya gudun da na ke yi kin raina? So kike na je na watsar damu? In kin raina sai ki karɓi tuƙin." Jin ya yi magana cikin fushi ya sa ta ce,"Am sorry." Da suka shiga cikin unguwar a lokacin goma har da minti goma. Kallonta ya yi, daidai lokacin da ya yi parking ba ta jira ya gama ba ta fice daga motar. A lokacin Nasreen ta yi nasarar fitowa ta buɗe get ɗin gidan. A hanyar falo ta kusan tuntunɓe da ita. Har ta tsorata sai ta duƙa ta kama hannunta fahimtar ita ce a gurin. "Nasreen ya jikin ki?' ta kama hannunta ta yi mata tambayar cikin tashin hankali ganin yadda ta koma. "Marwana zan mutu ki taimake ni." Ta furta tana nishi da ƙyar. "Ba za ki mutu ba." Ta ce tare da kama hannunta. Bayan shigarta gidan Damir ya bi get ɗin gidan da kallo cikin mamaki. Shi kansa bai taɓa tunanin gidan mai kyau take ba, jin yadda take na shi labarin tana wahala. Sai ya jinjina kansa cikin mamaki yana mamakin WASU MAZAN da suke ƙuntatawa matansu alhalin suna da shi. Yana wannan tunanin ya hange su, sun fita kusan a jikin Marwana take. Da ƙyar Marwana take janta Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi, har sai da ya dafe gurin, yana jin yadda take masa zillo tamkar za ta fito waje. Hango ta ya yi a cikin duhun, amma sai ya ji ya tasa sukuninsa. Wani yana yi ya tsinci kansa wanda ya rasa wani irin yanayi ne. "Please Ya Damir, ka buɗe bayan motar." Muryar Marwana ta katse shi tana faɗin haka. Cikin hayyacinsa ya dawo, da sauri ya zagaya ya buɗe mata motar ta sanya ta a ciki. "Marwana yarana suna ciki kuma babu kowa a gidan." Ta ce mata tana cige bakinta. Jin abin da ta faɗa da sauri ta koma ciki. Yaran ta ɗauko ta sanya su cikin mota. Shiga cikin motar ya yi, sannan ya tada tamkar wanda yake jin bacci. Ganin halin da take ciki domin a wannan lokacin ta fita hayyacinta. Kai tsaye asibiti su ya kaita. Suna isa likitoci suka karɓe ta tare da gungurata a kan gado

Chapter 9 of 17