Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yau ya ƙazanta. "Abba, don Allah ka daina dukan Umma." Cewar Raihan tare da kama hannunsa. Ba tare da ya kalli Raihan da take kuka ba ya ce, "Allah ya kaimu safiya, da asuba zan kaiki gidan na tsare Ahmad, na ji ko shi ya siyan miki." Ya faɗa tare da yarda bulalar. Saboda tsoron karya dawo a ranar kusan a bayi ta kwana. Ta yi kuka har ta bawa uku lada. Gabakiɗaya jikinta ciwo suke mata. Kwata-kwata ba ta yi tunanin zai ɗauki zafi sosai haka ba, in ya ga ta da su. Matuƙar nadama da dana sani suka cika ta. Tun da ya ce za su je gurin Ahmad, take ta kiran wayarsa ta sanar masa maganar, amma cikin rashin sama wayar ta sa a kashe Ga shi dama shi kadai yake da wayar a gidan. Kiran sallar asuba ya tashi ya rinƙa buga mata ƙofar ta buɗe. Tsananin mamaki da ya kamata, domin in dai da asuba ne sam baya tashi da wuri. "Ki buɗe ƙofar nan, muje na tambayesa in kika ƙara sakan biyar wallahi a igiyoyin aurenki..." Bai gama maganar ba ta fito, da hijabinta da ta yi sallah jin abin da ya ce."Da ki zauna kar ki fito, sai na ga gidan uban da za ki in na sake ki." Tsaki ya yi ya juya ya fice, ganin haka ta ƙarashe goya Musaddik tana hawaye ta bi bayansa. Yana isa ƙofar gidan ya fara sakin hon babu ƙaƙƙautawa. Jin hon ɗin ya farkar da Baba, da yake ta sharan bacci, ya ƙi tashi ya yi sallah, duk da nacin tashin da Mama take mishi. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Yau kuma mai Nasreen ta yi wa wannan tsinannen mijin nata?" Ya yi tambayar tare da miƙewa yana zare ido. Mama ita kanta jin hon ɗin na sa hankalinta ya yi matuƙar tashi. Fita ya yi tare da ɗaukar rigarta yana da sanyawa. "Yau wallahi yadda ba ni da ƙo ƙwandala, ya ce zai yi mini rashin kunya sai na ci ubansa." Ya faɗa tare da fita wajen. "To isasshe ɗan ƙaruna. Ka kashe motar ma ka fito ba za ka iya ba, sai dai ka damu mutane da hon, kamar wanda ya zo da jirgin sama." "A gurinku ai kamar tafi jirgin tun da ko keke ba ka da shi." Ya bashi amsa fuska a tamke, tamkar ba da surukinsa yake magana ba. "Ka san ba mutunci ne da ni ba ko Faruk? Wallahi yanzu zan maka rashin mutunci. Da ma ba ka san haushinsa na ke ji ba. Ƙiri-kiri na nemi aro dubu goma ka hana. Sai kace dubu ɗari na nema." "A kan me zan ba ka kuɗin bayan 'yarka da ka aura mini tana gasa mini gasa a hannu? Tambayeta rabon da ta bani haƙƙina kwana biyar kenan, saboda ta samu mazan jami'a, tana iskanci da su suna biya mata bukatunka." Kallon mamaki ya yi mata jin abin da ya ce. "Baba, wallahi ba haka ba ne, Baba bana kula ko wane ɗa namiji." Ta faɗa cikin muryar kuka tana gyara goyon Musaddik. "Ƙarya zan yi miki kenan?" Ya ce tare da kai mata duka ta kauce. "Faruk! Ko mutuwa tana jin kunyar mahaifi a gabana za ka duketa?" "Ƙarya ta zan iya yi, domin zuciyata gaba take da ta bani shawarar na yi ajalinta. Matuƙar ba za ta gaya mini, wanda ya siya mata waɗannan ba." Ya ce tare da nuna masa. Zare idanunsa ya yi, yana kallon wayar da laptop ɗin sai kuma ya juya yana kallonta. "Zina take yi suka siya mata." "Wallahi Baba ba zina na yi ba." Ta ƙara cewa." Baba kuwa mamaki sosai ya kama shi, sai ya shiga tunanin wa ya siya mata, don ya san Ahmad ba shi da kudin da zai iya siyan mata. "Nasreen, wa ya siya miki?" "Na'am eh Ya Ahmad ne." Ta ba su amsa cikin kuka. "Ahmad?" Ya yi tambayar yana kallonta. Kafin ya ce wani abu Ahmad da ya dawo daga Masallaci, rike da karbi yana ja a hannunsa, ya ƙaraso da sauri ganin motarsa. Harara suka ba ka ma junansu, domin tamkar mage da ɓera suke. Faruk yana ɗan shakkar Ahmad, saboda ba sa gama maciji, kuma ya san shi kamar zawayi yake. Sai ya ɗan rage hargowar da yake yi. Ba tare da ya kalli Faruk ko Baba, ba ya karasa gurinta da ganinsa, ya sa ta fashe da kuka tare da kama hannunsa. "Nasreen, mene ne?" "Mazan jami'a take bi suka saya mata waya da laptop mai tsada." Maganar ta buge shi, musamman da ya nuna masa wayar da laptop ɗin Shi kansa ya razana da ganin wayar. "Ya Ahmad ka san halin ba zan taɓa bin wani ɗa namijin da aurenka ba. Na gaya mishi kai ka siya mini, amma ya ƙi yarda." Jin abin da ta fada, ya sa shi ƙoƙarin shanye mamakin inda ta samo su. "Ƙarya ne ba shi da kuɗin da zai iya siya miki." Faruk ya ce yana kaɗai makullin motarsa. "Saboda ka mayar dani matsiyaci ko, sannan ka manta dare ɗaya Allah kan yi Bature? To ni na siya mata tun da kai ka kasa. Adashi na kwasa na siya mata, tun da kai ka kasa." Kallon mamaki suka yi masa har da Baba. "Yanzu dama Amadu, kana da kudin siyen waɗannan na yi da kai, jiya ka bani naira dubu shegiya ka hana?" Ba tare da ya amsa masa ba, ya juya gurin Faruk."Na gaya maka ka daina dukanta, domin ita ba jaka bace." "Dole na duketa, tun da ko addini ya bamu damar in mata mu suka ɓata mana mu duke su." "Wannan fatawar na ka ya sanya na gane kai babban jahili ne. Ilmin boko kawai kake takama da shi." "Na gode ma Allah tun da na yi bokon, kai kuma da ubanka ya kasa ba ka duka f.." Kafin ya ƙarashe ya ɗaya hannunsa zai kai masa mari, amma sai ya doje. "Wallahi in har ka yi kuskuren marina, sai na kashe ƙanwarka da duka kuma ka yi zaman burtsuna." "Kai Amadu wai mai ke damunka ne?In ka tunzura shi ya saketa, wallahi kai da ita sai dai ku bar mini gidana." "Baba, Allah zai kama ka a kan haƙƙin Nasreen. Ka ba shi dama yana cutar da rayuwarta." "Ka fita idona ɗan iska kawai! Uban me ka sani game da aure. In ta rabu da shi kasan mijin da za ta ƙara aure?" "Ba..." "Kar na ƙara jin muryarka. Wulaƙantaccen yaro kawai." Ya daka masa tsawa yana faɗin haka. Ransa ne ya ɓaci hannunta ya ja za su shiga ciki. "Kai Amadu! Gidan uban wa za ka kai ta?" Ya yi masa tambayar cikin ɓaci rai. "Ka barshi ya shiga da ita ciki, ta zauna har illa ma sha'a. Ki an gaya masa amfani take mini? Ci da ita kawai zai zamar masa aiki." Ya ce yana ƙoƙarin shiga cikin motarsa. "Ke Nasreen dawo ki tsaya kai kuma wuce." Ya ce mishi cikin tsawa. Idanunsa suka kawo ruwa, ya kalle ta da take ta kuka, ganin har mutane sun fara tsayawa ana kallonsu. Tausayinta ya sanya hawayensa zuba. Girgiza kansa ya yi, tare da wucewa ba tare da ya ƙara cewa komai ba. "In kin san ba shi ya saya miki ba ki bawa mijinki hakuri, sannan ki kawo ni zan san yadda zan yi dasu." Ya faɗa tare da fatan Allah ya sa ta bashi ya siyar. "Shi ne Baba." "To ka ji ka yi hakuri kamata ya yi ya gaya maka." Kallonsa ya yi don har yanzu bai yarda ba. Ba tare da ya ce komai ba ya fara ƙoƙarin shiga motarsa. "Za ki shiga ki bi mijinki shashasha kawai! Kuma wallahi kika ƙara barin ya kawo ƙarni sai na saɓa miki." Da sauri ta shiga tana kuka. Ganin ya shiga motar har ya tada ya sanya shi duƙawa. "Faruk, tafiya za ka yi? Maganar kuɗin nan fa. Har gida zan zo na ja mata kunni." "Ni fa kana isata 'yar ka babu tarbiya, amma kullum buƙatar da kake kawo mini daban. Wallahi na yi dana-sanin auren zuriyarka." "Ka yi hakuri ba za ta ƙara ba." Hannu ya sanya a aljihunsa, ya ciro kudi da yawa kamar zai bashi sai kuma ya fara irga dubu biyar. "Iya wannan zan ba ka, kuma na rantse in ba ka dawo mini da su ba. Karka ƙara tunanin zan baka rance, tun da ba biya kake ba." Ya ce tare da kunna motarsu ya fara tafiya. "Raba mugu da makami, ibada. Kuma wallahi ko kafi maye maita ba zan bayar ba. Ni zan yi dana sani da na ɗauka gidan da zan rinƙa zuwa maula na aurar da ita. Ashe ɗan Iskan ƙalƙo na aura mawa." Ya faɗa yana aika ma motar mugun kallo. "Kai Allah na gode maka. Na tashi bani da ko fincika, amma na samu kudin da zan kashe har kwana uku.Na yarda da cewar dare ɗaya Allah kan yi Bature." Suna hanya yana gudu sosai ya juyo ya kalleta."Kina ganin halin ubanki? Kina kallon duk abin da yake faruwa? Kin san baki da gatan da ya wuce gidana, amma ba za ki yi mini biyayya ba mu zauna lafiya. Wallahi in har kika ce saba mini za ki rinƙa yi sai na lahira yafi ki jin dadi." Shiru ta yi ba tare da ta ce masa komai ba. Kuka take yi sosai har idanunta sun kubbura. Dana sanin zuwa ta duniya da tunanin makomar rayuwarta sun addabi zuciyarta, domin matuƙar mahaifinta zai cigaba da haka. Ba ta da kima da daraja a idanunsa. Da suka isa gida, duk kukan da take yi haka ta taso ta buɗe masa ƙofa. Fita ya yi daga motar, ba tare da ya kulle ba ya kalle ta ya ce," Ki wanke mini mota, tun da ba ki da amfani a matsayin matata, ba kya iya ɗauke mini damuwata, don haka komai ke za ki rinƙa mini." "To," Ta furta tana share hawaye don wanke motar ba shi ne na farko ba Har ya tafi ya dawo ya karbi wayar da laptop ɗin ya shige. "Na shiga uku! Da na sani da ban ƙarfi kyautar nan ba. Dama ance dana sani ƙeya ce." Ta furta tana share hawaye. "Umma, ki bar kuka ina girma sai na sanya 'yan sanda sun kama Abba." Raihan ta faɗa tana share mata hawaye. Da ta gama wankin motar. Ƙullin kayansa ya ji ga mata ta wanke. "Kuma ki goge kafin na dawo." Ya ce mata tare da ficewa daga gidan. Tun da ya fita take kuka. In ta tuna toxarcin da ya yi mata sai hawaye. Saboda fitan da suka yi Nasreen ba ta je makaranta ba. Ita kuma ba su da lecture sai ƙwara ɗaya kuma presentation suke yi group ɗin su sun yi. Tana kwance bayan ta gama wankin tana jiran su bushe ta yi gugar. Maman Muwadda ta yi sallama ta shigo. Gani ta ya karyar mata da zuciya ta fashe da kuka tare da rungume ta. "Lafiya mai kuma ya ƙara faruwa?" Kuka sosai take yi har ta jin zuciyarta na yi mata zafi tamkar za ta fito waje. "Ni dai ban yi sa'ar zuwan duniya ba, domin na kasance daga cikin wadanda suke karɓan ruwan mara daɗi a cikinta. Zaman aurena ba shi da maraba da bauta. Mijina bai bai ɗauke ni da wata daraja ba. Zuciyata zafi take yi tamkar za ta fito waje." "Ki yi shiru ka yi mini bayani." Sai da tasha kuka son ranta sannan ta kwashe lamarin ta gaya mata. "Allah Sarki! Ita kuwa wannan wace ce ta shigo rayuwarki? Haƙiƙa na yi miki farincikin. Allah ya sanya ta zama sanadin da za ta kawo haske a cikin rayuwarki." Ta furta cikin tsananin farin ciki. "Zan matar mata ba zan iya jurar toxarcin da nake fuskanta ba." "Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradi rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinkk ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki. Faruk! Rayuwar aure na ƙargin bauta bane da za ka mayar da mace tamkar jaka. Masu hali irin na Bana haƙiƙa suna kawa 'ya'yansu gori da tozarci. Makaranta innsha Allahu yau zan yi posting safe da yamma a cigaba da surbubuɗo comments ❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃 WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 9 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Saboda me za ki mayar masa? Wallahi ina gaya miki matuƙar ba ki tashi kin nuna wa Faruk, ko babu shi za ki iya rayuwa ba. To rayuwarki na cikin siradin rayuwa. Nasreen, kina da kyan ki da ilmin ki. Sannan kuma da kyawawan halaye. Ko da ace mahaifinki ya kore ki ba za ki rasa inda za ki zauna ba, har ki samu miji ki yi aure. Faruk ba mijin da mace za ta zauna da shi bane, domin so yake ya tsotse ƙwallon mangaron ya huta da ƙuda. Ki tashi ki nuna masa kema mace ce kina da gata. Talauci da 'ya'ya ba hauka bane da za ki kashe kanki saboda su. In har kika nuna masa ko babu shi za ki iya rayuwa, zai rage abin da yake yi, domin yana sonki. Tsabar jahilci da rashin sanin darajar mace da kuma ɗaukar aure a matsayin ibada ba, ya sanya yake wulaƙanta rayuwarki." Kamata ta yi ta rungume tana shafa bayan ta sannan ta ɗora da cewa,"Guda nawa kike da har za ki fuskanci wulaƙancin ɗa na miji?" Kuka take yi sosai har ta gaji ta yi shiru sai ajiyar zuciya. Ba ta baki ta shiga yi har ta samu sauki a cikin zuciyarta. Wayarta ta ɗaya ta kira babbar 'yarta ta kawo musu abinci. Ta daɗe tana gidan tana kwantar mata da hankali, sai da aka kusa kiran magariba sannan ta yi mata sallama ta tafi. Bayan tafiyarsa ta gama gugan ta yi alwala ta yi sallah. Sannan ta ɗauki qur'ani tana karantawa har kusan a kira isha'i. Ƙwankwasa get ɗin gidan da ake yi da dutse ya sa ta tashi ta je ta bude da tunanin waye cikin daren nan "Wane ne?" Ta furta daidai lokacin da ta isa bakin get ɗin. "Ahmad ne." Ya ba ta amsa tare da jefar da dutsen Tana buɗe get ɗin gidan ta saka mishi kuka tare da faɗawa jikin shi. "Mai ya sa kika aikata haka? Kin san za ku zo ai da kin kira ni." "Na yi ta kira ka wayar a kashe." Ta ce masa cikin muryar kuka. Kama hannunta ya yi suka shiga ciki. Zaunar da ita ya yi, sannan ya zauna a gefenta. "Faɗa mini wa ya ba ki waya da laptop masu tsada haka?" "Ka yarda da ni Yaya Ah.." "Da ma na zarge ki ne? Na san wace ce ke. Ko Baba ya rantse ba za ki taɓa kauce hanya ba. So kawai na ke na san inda kika samo su." Cikin kuka ta sanar masa wanda ya cika da mamakin kyautar. "Da kin sani da ni kika kawo mawa, sai na kawo masa na ce na saya miki, amma dama ko wane namiji ya ga matarsa, da abu mai tsada haka dole ya tambaye ta ba'asi." "Na yi kuskure Yaya." Ta furta tana share hawaye. Kwantar mata da hankali ya shiga yi har ta samu ta saki. Ledar awara ya miƙa mata yana faɗin," Ga shi ki samu ki ci na san wataƙila ba ki ci komai ba." "Maƙociyarta ta kawo mini." "Allah ya saka mata da alkhairi." "Amin," Ta furta tare da miƙewa ganin ya miƙe. Ko da suka zo bakin get nasiha ya yi ta mata, sannan ya kawo Naira ɗari biyar ya ba ta. Koma ɗauki ta yi ta kwanta yayin da hannunta ɗauke da carbi tana lazimi. Faruk kuwa tun da ya fita ya rasa sukuni. Kallon wayar yake yi cikin tsananin mamaki, saboda wayar mai tsada ce. A yadda Ahmad ya ɗan nuna alamun rashin gaskiya, ya sa ya shi kokwanto kan siya mata da ya ce ya yi. Sannan ko da bai nuna ko kokwanto ba. Sam ba zai yarda ba don ba, shi da arzikin da zai iya sigar ko da wayarce. A hanya yanke shawarar dole ya sa ya ta ta yi rantsuwa da qur'ani shi ya siya mata. Saboda jaraba yana dawowa ɗakinta ya shiga, wacce ta yi nisa a duniyar tunani ba ta ji hon ɗin motarsa ba. Ballantana shigowarsa. Ganinsa ya sa ta tsorata tare da miƙewa tamkar za ta ruga. "Ka yi hakuri ban san ka..." "Rufe mini baki banziya kawai! Da ma kina jin maganata ne? Ai kin raina ni duka kuwa kin saba kamar jaka!" "Kawo qur'anin." Ya ce mata. Mika masa da sauri ta yi tana ƙare kanta da hannu a tunaninta dukanta zai yi. "Ka yi haƙuri don Allah." "Ungo." Ya ce mata. Da sauri ta karɓa a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya ya karɓar da ya yi. "So na ke ki rantse da qur'anin nan Ahmad ya siya miki." Zare idanu ta yi har ta saki qur'anin zai faɗi, ta yi maza ta riƙe da sauri jikinta na mazari. Ganin yadda ta firgita, ta shiga cikin tsananin tashin hankali, tare da hawaye ya sanya masa shakku a ransa. "Ma za rantse na ce, saboda shi zai sanya na yarda dake. Na san yadda kike daraja qur'ani da kuma wanda ya yi, sam ba za ki iya rantse wa kan ƙarya ba. In har kika rantse yanzu zan ba ki na yi miki fatan alkhairi." Ta yi shiru tana zare ido, a ranta ta fara tunanin ta gaya masa gaskiya ko ba zai yarda ba, domin ko da suka zai sanya mata a maƙoshi ba za ta rantse ba. Tana tsane da ko a kan gaskiya mutum ya rantse Allah zai iya hukunta shi, domin Alqur'ani ba abin wasa bane. "Ki rantse na ce." Ya daka mata tsawar da ya ƙara firgita ta. Ije wa ta yi tare da ƙara sakin kuka."Zan gaya maka gaskiya." Ta ce tana ɗaya yatsunta, kamar wata ƙaramar yarinya. "Ina jin ki." Ya furta cikin mamaki yana kallonta. "Wallahi wata 'yar ajinmu ta bani. Kuma in har ba ka yarda ba. Mu je makarantar na ma mayar mata." "Ta ya ya zan yarda, in kun haɗa baki ne ita ke ɗora ki a hanya fa? Yar iska da aurena za ki ci amanata." Ya kai mata mari yana faɗin haka. "Wallahi ban taɓa cin amanar ka ba. Ba zan iya rantse wa kan wayar ba, amma zan rantse da qur'anin tun da na aurenka ban taɓa kallon wani ɗa namiji da sunan sha'awa ba. Kai ne namijin da na fara sani, kuma har yau ban taɓa kula wani ba. Ka yarda da..." Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon hamɓarin da ya kai mata a ciki. Duƙawa ta yi tana jin yadda kayan cikinta ke juyawa. Jiri ya ibe ta. Da sauri ta dafe cikin tana faɗin,"Wayyo Allah! cikina za ka kashe ni." "Eh gara na kashe ki don babu amfanin ki a duniya. Matar da take cin amanar mijinta, mutuwa ya fi a gareta. Kin ga ko banza na yi maganin irinku." Kuka take yi sosai yana dukanta yana haurinta. Tun maƙota na jin kukan suka daurewa har suka gaza. Cikin kuka Maman Muwadda ta kalli mijinta. "Kuna jin zai kashe ta? Saboda tsoron sa da masifarsa. Shi Allah ne? Wallahi zan fita na ɗauki icce na ragije shi." Ta furta cikin tsananin kuka. "Me kike so na yi? Yaron nan mahaukaci ne. Kin san ba zai bar kowa ya shiga cikin gidan ba, kulle gidan yake yi. Kina sane da tozartar da ya yi mana da Alhaji Munir, saboda mun yi mishi nasiha. Ba zan shiga cikin rayuwar iyalin sa ba. Shi mahaifin na ta wane irin dabba ne?" "Nasreen, ba da gata sai Allah. Ubangiji shi ne kawai gatanta, domin tana cikin wani mawuyacin hali. Wallahi in har ba ku taimaka wa rayuwarta ba sai Allah ya hukunta ku." Miƙewa ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya fice daga gidan. Buga ƙofar da ya ji an dame shi ya sa ya daina dukanta, wacce ta yi lamo kukan ya gagareta sai nishi take yi. "Gobe zan ɗauke ki muje cikin makarantar na tabbatar. Kuma wallahi in har ƙarya kike yi, sai na lahira yafi ki jin daɗi." "Na yarda zan mayar mata, in haka zai sanya ka haƙura." Ta ce tana share hawaye a wahalce. A daren ranar ta yi kuka har ta ji babu dadi. A gurin da ya gama dukanta ta samu da ƙyar baccin wahala ya ɗauke ta. Baccin mai kama suma ta yi, sai da sanyin asuba ya fara sannan ta farfaɗo. Cikin ƙarfin hali ta mike ta dafa ruwan zafi sosai ta gaza jikinta. Kallon fuskarta ta yi, da yake mata wani irin zugi sai ta ga ashe ya fasa mata gefen idanunta. Bayan ta yi wanka, ta shirya ta yi sallah tana kuka. Komawa ta yi ta kwanta har gari ya waye. Ƙarfe tara na yi, ya sanya a cikin mota suka nufi makarantar. Saboda yadda ya fasa mata jiki. Niƙabi ta sanya ta rufe fuskarta. Cikin sa'a yana parking da motarsa, sai ga Marwana ta shigo gurin parking ɗin. "Ga wacce ta bani can." Ta furta tana nuna ta da yatsa Da ya ga motar da take hawa sai da gabanshi ya faɗi. Bai gama firgita ba sai da ya ga wata tsuleliya kyakkyawar gaske, fara mai kyawun diri da shiga ta alfarma ta fito Idanunsa ya zare tare da kallonta, sosai bayan ya cire gilashin da ya sanya. Jikinsa ya kama rawa yana kallonta." Irin wannan baby ɗin ne take kulata? Kai ina ni ya kamata na ta kula, amma ita ba."Ya ce yana ƙare mata kallo kamar maye. "Ma za ki je ki bata." "To," Ta amsa cikin sanyi tare da buɗe ƙofar ta fita. Tun da ta fito Marwana ta bi ta da kallo, saboda tafiyarta ya yi

Chapter 6 of 17