dole na kauda Ahmad na wani lokaci, saboda Nasreen ta zama jaruma ta ƙwaci yancin kanta. Ahmad so yake a yi wa Faruk hulɗi, kuna ganin hakan mafita ne a gareta? In har aka yi masa hulɗi suka rabu Nasreen ta yi experiencing rayuwa kuwa? Karfa ku manta wanda za ta kuma haɗu da shi wato Damir a dalilin ta matarsa ta mutu har ya tsane ta. Kuna ganin a haka har za ta iya fuskartar ƙalubalen da zai faru, kafin soyayyarsu ta ƙullu? Dole tana buƙatar ta tsaya ta zama jaruma don ta iya fuskantar ko wace irin rayuwa ta tsinci kanta a ciki. Na gode da yadda ku ke kuke bibiyar WASU MAZAN haƙiƙa comments ɗinku yana sanya ni cikin duniyar nishaɗi. Fatana na faranta muku ta hanyar tsara muku labarin domin farincikinku.❤️❤️❤️❤️❤️💃💃💃💃💃💃💃💃👏👏👏👏
*WASU MAZAN*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 21
"Taimakon ki na yi, kuma da kike wannan maganar mata nawa suke zaman ƙunci a rayuwar aurensu kuma suke haƙuri? Wasu matan babu abinci babu sutura, amma hakanan suke zama a gidajensu."
"Ka yi haƙuri Baba, ba zan iya komawa gidansa ba."
"Ni kuma wallahi ba za ki zauna mini a gida ba, sai dai ki nemi wani gidan uban, sannan in har kika faɗi haka, yarannan a yau za ki mayar masa da 'ya'yansa."
Sosai take kuka jin abin da ya ce. Kallon yaran ta yi tana jin duk wuya, duk rintsi ba za ta rabu da su ba. Ahmad ya faɗo mata a rai, ta san cewar da yana nan, Baba bai isa ya yi mata dole ba."
"Nasreen ba za ta koma gidan Faruk ba, sai dai duk abin da za ka yi ka yi." Ya ji muryar Mama tana faɗin haka.
"Au ke kike ɗauke mata gindi ko?"
"Haba ka tausaya mata mana. Yaron nan ya nuna baya ƙaunarsa, kan dole sai ta yi rayuwa da shi?"
"Ke mai ya sa ba ki rabu da ni ba? Tun da kullum gaya mini kike ba kya son halina? Sai ita ki sanya ta kashe aurenta. Kina ganin yadda maza suka yi wahala.To wallahi gara tun wuri ki farka da ga barin da kike yi. Kar ki yadda ta ɗora ki a kan keken ɓera."
"Sai dai in ka sake ni, amma Nasreen ba za ta koma gida sa ba."
"Mene ne abin tada jijiyar wuya? In har kin shirya biyansa kuɗi sai ki kai shi kotu." Ya ce yana ɗaya kafaɗarsa alamun bai da mu ba.
Gabanta ne ya faɗi tunawa da hakan. Hawaye ta share tare da kama hannunta ta miƙar da ita, wacce take kuka kamar ranta zai fita."Ta shi ki daina kuka ba za ki koma ba."
"Mama, na san cewa ba ji da gata, tun da Yaya Ahmad ya ɓata. Baba so yake ya raba ni da yarana, ba zan iya kai su gidan ubansa ba, saboda na san Faruk ba zai iya riƙe su ba. In har zai sanya dole na mayar da su, zan koma gidansa ne don kawai bamu da kuɗin da zamu biya sa, amma ba don na ci gaba da biyayar aure ba. Ba zan iya jure rashin mutuncin sa, idan ma yana ganin ba zan iya rayuwa babu yarana ba, zan haƙura da su na yi musu addu'a. Ya Ahmad ya ɓata zan tsaya tsayin daka na ƙwaci 'yancina da yake mafarkin samar mini"
"Allah yana tare dake ki yi addu'a, in sha Allah ba za ki rabu da yaranki ba." Mama ta furta mata cikin rashin ƙarin gwiya.
"Au komawa za ki yi don ki gurza masa rashin mutunci?" Dariya ya saki jin abin da ta ce, sai ya ɗora da cewa,"Da yake ta yaro kyau take ba ta ƙarko. Kina sane da halin sa, saboda ban taɓa ganin tijararren irin sa ba, duk jarabata wallahi ya fini. Ɗan banza mara tarbiyya, amma a haka yake kiran 'yata ba ta da tarbiyya."
Kallonsa Mama ta yi cikin takaici jin abin da ya ce."Saboda ba ka riƙe mutuncin ka bane, duk wannan wulaƙancin da yake mata, ai kai ka janyo mata shi, saboda da ace ka riƙe talaucinka ba ka roƙonsa, wallahi babu yadda za a yi ya rinƙa maka rashin mutunci, amma saboda mutuwar zuciya wai suruki kake gaya ma ya taimaka maka, ba ka ci abinci ba. Ai dole ya wulaƙanta ta, tun da ya san uban da ya ubanta, shi ma rokonsa yake abincin da zai ci."
"Au tijara kike son yi mini kenan?" Ya tambaye ta cikin borin kunya yana kumfar baki.
"Gaskiya nake gaya maka wallahi in har ba za ka canza ba, za ka yi nadama saboda abin da kake yi babu kyau."
Banza da ita ya yi domin gaskiya ta faɗa, ba shi da abin da zai ce. Kallon Nasreen ya yi ya ce,"Oho, yanzu dai shawara ta rage wa mai shiga rijiya. Da na ban yi mata dole ba, zaɓi na ba ta." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da ga ɗakin.
Kuka take yi sosai, ta san cewa ba ta da zaɓi da ya wuce ta koma gidansa. Ba ta da kuɗin da za ta biya shi, da kanshi dole ya saketa, saboda a halin yanzu babu wanda ta tsana fiye da shi."
Miƙewa ta yi, bayan ta share hawaye ta zauna tana tunanin rayuwarta. Da dadddare tana zaune ta ranka tagumi ta yi nisa a cikin duniyar tunani. Ƙarar motar Faruk ya dawo da ita hayyacinta. Gabanta ya faɗi sosai har sai da ta dafe gurin. Idanunta suka fito, don ta san zuwansa ba alkhairi zai gaya mata ba. Kafin ta yi wani yunƙuri ya shiga sakin hon ba ƙaukautawa. Da sauri Baba ya fito daga cikin ɗaki yana ƙoƙarin saka takalmi."Ga wancan tijararren ya iso, bari na yi sauri kafin ya kurmantar da mutanen unguwa." Ya ce tare da ficewa.
Raka shi da idanun cikin tsananin takaici ta yi. Ta san cewa da ace Faruk yana da sakin hannu, sujjada ce kawai ba zai yi masa ba, amma yadda yake da mugun son abin duniya, babu abin da ba zai yi masa ba.
Da sauri ya ƙarasa gurin motar nasa. Yana cikin motar ya ƙure waƙa yana ji."Ashe ka zo? Sannu da zuwa bari a kira ta."
"Ita ba ta san ƙarar motana ba, sai na kira ta? Ko rashin tarbiyar za ta nuna mini?"
"Bacci take yi." Ya yi masa ƙaryata hakan yana kallon sa.
Tsaki ya yi, ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da shan waƙarsa.
Ganin haka ya juya ciki a lokacin da ya isa cikin ɗakin Mama. Tana zaune a falo tana kuka. Mama ke gefenta tana ba ta baki. Tsaki ya yi sannan ya sannan ya kalle su," Ke Nasreen mijin ki na waje ya zo biko, kuma wallahi kika yi masa rashin mutunci sai kin sani."
"Baba, don Allah ka sanya Faruk ya sake ni wallahi na tsani zama da shi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
"Hmmmmh!Kina dai ganin turjiyar da Ahmad ya nuna kan zai raba aurenki, amma daga karshe kin ga an neme shi an rasa. Ko wannan bai isa ya nuna miki aurenki da Faruk, mutu ka raba ba?"
"Shikenan, cikin ƙunci zan ƙarashe rayuwata? Ban sha ta daɗi ba, a lokcin da na ke ni kaɗai a gurinsu, ballantana yanzu da yake da wata matar?"
"Sai ki je ki yi hakuri, kuma Nasreen in an bi ta ɓarawo, abu ta ma bi sahu, don shegen kafiya ce da ke, wataƙila ɗiban albarka kike masa."
Takaici ya sanya ba ta amsa masa ba, sai kuka tana share hawaye."Ki je yana jiran ki, kuma wallahi kika yi masa rashin kunya, kin san shi ma ba kanwar lasa bane." Ya ƙarashe maganar tare da juyawa ya fice.
Kallon Mama ta yi sai ta fashe da kuka, tare da faɗawa jikinta."Mama, ki yi mini addu'a, kar na koma gidansa na kwaso zunubi duk bana jin akwai sausauci a tsakanina da shi. A dalilin a biya shi kudinsa, Ya Ahmad ya ƙarfafa tafiyar nan, duk lokacin da na tuna ji nake kamar na shaƙe sa ya mutu."
Kuka take yi sosai tana tausayinta."Ki yi hakuri ki ci gaba da addu'a, kin ga yanzu ina kafe dole ya sake ki, ba mu da kuɗin da za mu yi masa hulɗi. Allah yana tare da ke, tun da ya halicce. Ko ci gaba da kai masa kuka, watarana zai ji kukan ki, domin baya zalinci kuma ba ya barin ayi."
"To,"Ta ce ba don ta haƙura ba, sai dai ba yadda za ta yi. Ta san cewa tun da Ahmad ya ɓata, ba ta da sauran gata, sai dai zuciyarta na ƙarfafa mata ita ce kawai gatanta a duniya. Ita za ta tashi ta ƙwaci 'yancinta, tun da Baba bai damu da rayuwar ta ba.
Wanke fuskarta ta yi sannan ta sanya hijabi ta fita. A lokacin har ya tada mota zai bar gurin. Ganinta bai sanya ya fasa ba, har sai da ya fara tafiya. Ko mai ya tuna oho ya ja ya tsaya.
Ganin shiru bai tafi ba sai ta ƙarasa gurin motar. Tamkar wani baƙo a gurinta ta tsaya ba tare da ta ƙarasa ba. Zuciyarta bugu take mata tare da wani irin tsanarsa. da haushinsa suka haɗu suka sanya zuciyarta tafasa. Don kawai ta san Faruk ba zai taɓa sace Ahmad ɗin ya ci gaba da zama da ita ba, saboda ta san ba ya sonta, kawai yana zama da ita ne don ya wulakanta rayuwarta, amma za ta iya zargin shi ya sace shi.
"Ke an gaya miki zan cigaba da jure wulaƙancin ki ne?" Ya furta daidai lokacin da ya buɗe ƙofar yana mata kallo tamkar ya ga kashi. Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai kallonsa take yadda ya ƙara kyau har tumbi ya ɗan yi.
Tsaki ya saka yana kallonta."Dubi yadda kika lalace kika koma wata tsohuwa dake. Ɗan watannin da kika yi, ya sa ya kika koma haka? Wannan in da za ki yi shekara sai an tausaya miki, kuma a haka kike mini wulaƙanci har kike wani banza gardi can da aurenki ya ba ki jininsa? Kin san ba ki da gatan da ya wuce zaman gidana. Ita wacce take zuga ki tana ina? Ta bar ƙasar bayan ta lalata miki rayuwar auren ki." Ya numfasa yana watsa mata mugun kallo ko za ta ce wani abu.
Raihan ce ta fito daga cikin gidan da sauri ta ƙara so."Abba," Ta ce tare da kama hannunsa.
Da sauri ya fisge yana kallonta kamar zai yi amai."Kina gani ko Nasreen, kina ganin irin rayuwar talauci da ƙaskancin da kika zaɓi yarana su kasance. Dubi jikin Raihan kamar wacce ta shekara ba ta yi wanka ba? A haka kike son ki wulaƙanta rayuwarsu. Su taso cikin talauci da dauɗa kamar yadda kai taso."
Hawaye share suke ƙoƙarin zubo mata jin tozarcin da yake mata yana ɗaya murya. Juyawa ta yi za ta shige ciki ba tare da ya ce komai ba. Da sauri ya fito ya sha gabanta."Zaman wahala da kika yi a gidanku, har yanzu ba ki zama mai biyayya ba, saboda iskanci ina magana za ki wuce."
"Ba ni da abin da zan ce maka Faruk, duk abin da kake yi mini Ubangiji yana kallonka kuma ya san halin da na ke ciki. Kana amfani da rashin iyayena kana wulaƙanta rayuwata, saboda ƙofar da mahaifina ya ba ka. Na san cewa watarana za ka yi dana sani mara amfani, domin aikin alkhairi kawai mutum zai aikata ba tare da ya yi nadama ba, amma watarana za ka yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙare wa ɗankada, kuma tusa ta ƙarewa bodari.
Wata mahaukaciyar dariya ya saki tare da buga bayan motar sa."Matuƙar kika ce haka kin yaudari kanki. Abu biyu zai sanya ki gane ba zan taɓa nadama, yadda ɓacewar Ahmad ta zo miki bazata, wadanda suke miki ingiza mai kantu suka gudu."
"Akwai wanda ba ya bacci kuma ba ya barin mai zalinci, da Ni kaina Faruk. In har sun kauce a rayuwata. Ubangiji yana nan domin shi ya yi wa masu hakuri da cewa su ci gaba da hakuri, sannan ya yi musu busharar samun sauƙi a rayuwa. Akwai wanda zai iya sanya maka soyayya ta a lokacin da na yi maka nisa, a lokacin da wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Allah zai iya jarrabar ka da mutuwar sona.."
"Ƙarya kike yi matuƙar ina da kuɗi zan iya auren matan da suka fi ki kyau da ƙuruciya, kamar yadda na auri Rashida wacce take bin duk abin da na ke so, kuma take cike mini gurbin da duk macen ƙwarai ta kama ta."
"Kuɗi ba sa maganin komai Faruk, yadda kake wulaƙanta rayuwata ina kaiwa Allah kukana. Ina ji a jikina za ka yi nadama mara amfani. Watarana zai zo ka durƙusa a gaban kana roƙona a lokacin da ba zan saurari kukanka ba"
"Na lura ɓacewar Ahmad ya zautar da ƙwaƙwalwarki. Ya kamata kafin na mayar da ke gidana, aje a duba ki kar ki zo ki cutar da matata." .
Jin abin da ya ce hawayen suka wanke mata fuska."Ni kuma zan tuna maka da wannan ranar karka manta da kalaman da ka gaya mini, saboda zan tuna maka da su, watakila a nan ko a wani guri."
"Ba za ki tuna mini ba, don na yi wa kaina alƙawarin wulaƙanta rayuwarki, sai na canza miki kamanni ta yarda babu wanda zai iya kallonki da sunan yana sonki. Sai na mayar da rayuwarmu abar tausayi na ɓata ki a idanun kowa, sannan zan yarda ƙwallon mangaro na huta da ƙuta.
Murmushi mai ciwo ta yi tana faɗin,"Wannan shi ne soyayyar da kake mini kafin ka aure ni? Dama soyayya yana zama ƙiyyaya Faruk?Mai na yi maka ka zaɓi ka wulaƙanta rayuwata?" Ta yi masa tambayar tare da durƙushewa a gurin.
"Wannan shi ne sakamakon macen da ba za ta bi umurnin mijinta ba, har za ta iya yarda a sanya mata jinin wani ƙarto, bayan ta gana cin ama...."
"Faruk, kar ka zarge ni da mutumin da na yi maka rantsuwar ɗan musulmi ban taɓa ganinsa ba sai a ranar. Kar ka zarge ni da mutumin da halin yanzu ba shi da maƙiya kamata. Ya yi mini rana na saka masa da dare, ta hanyar yin sanadin matarsa, wacce yake so fiye da komai. Mutumin da na sanya ƙasarsa ta yi masa baƙi har ya yi hijira duk adalilina da na zamo masa butulu, ya yi ninyar mini alkhairi sai na saka masa da sharri na zaman masa tauraruwa mai wutsiya. Kar ka zamo WASU MAZAN da babu yarda da amana a tsakaninsu da matansu. Kar ka zamo WASU MAZAN da suke wulaƙanta iyalansu..
Hannun ya sanya ya ture ta yana faɗin,"Ba zan yi sausauci a gareki ba, sannan ina gargaɗinki da ki zama mai ladabi da biyayya ga matata, in kuka ba haka ba, sai ki fara irga kanki a cikin zawarawa, don ina sonta ba zan lamunci ki wulaƙanta mini ita ba.
"Akwai Allah yana kallon ka shi zai kawo mini mafita. Zan koma gidanka saboda tursasa ni da Baba ya yi, amma ka sani wallahi ba zan ɗauki wulakanci da gurinka ba, da matarka saboda a yanzu na shirya don na ƙwaci 'yancina. Ina da daraja da ƙima 'ya mace na ke sam ba zan wulaƙanta kaina. A yanzu zan tsaya da kaina na ƙwatar wa kaina 'yanci
"Ashe kuwa kin dawo ne don na ƙarasa yanke igiyar dake tsakaninmu, saboda kin san a lokacin da kike ke kaɗai ban ɗauki raini ba, ballantana yanzu da nake da wacce take share mini hawaye. Wallahi kin mini rashin kunya sakin ki xan yi ki je can gidanku ki yi zawarci."
"Murmushi mai ciwo ta yi tana girgiza kanta ta ce,"Ashirye na ke Faruk! A yanzu a shirye na ke na yi rayuwata ni kaɗai matuƙar zan samu farin ciki. A yanzu na ƙuna bana jiran wake. Tursasar mahaifina kawai zan sanya na koma gidanka. Zawarci kaina farau? Mata nawa suke zawarcin kuma suke samu ingantacciyar rayuwa, sannan suka samu ci gaba? Sannan suke cikin farin ciki ba na tsoron zawarci in har Allah ya ƙaddara mini. In don talaucin iyayenta ne a ciki ka ganni. Yanzu da na koma gida mutuwa na yi? Da zaman aure irin na gidan ka Gara na mutu babu aure."
Wani kallon wulaƙanci ya yi mata yana dariyar rainin wayo." Nasreen marabinki da gawa rai ne kawai, amma dubi yadda kika koma tamkar mai ƙanjamau?"
Jin abin da ya ce ya yi masa kallon wulaƙanci ta juya kawai ta shiga cikin zauren gidan su. Kuka ta fashe shi, duk da cewar ta yi alƙawarin ta daina yi masa kika, amma maganar da ya gaya mata yi mata ciwo. Yana goranta mata talauci kamar ita ta ke ba da arziki.. Muryarta ya shaƙe yi kamar ta ta sha guba ta mutu. Ji take yi rayuwa ba ta mata adalci. Anya za ta kurɓi ruwan daɗi a cikinta, yaushe za ta yi farincikin da mata suke yi a gidan mazajensu.? Yaushe za ta zamo ɗaya daga cikin matan da WASU MAZAN suke nuna wa ƙauna, suke shayar da su madarar ƙauna da tafi zuma daɗi. Anya hakan zai faru? Tarin tambayoyin da suka cika ƙwaƙwalwarta kenan har suka sanya ba ta ganin abin da ke gabanta.
Da gudu ta shige cikin gida tana kuka. Tsaki ya ja tare da shiga cikin motar da ya tafi. Mama ta yi turus! Cikin damuwa tana kallonta."Na ɗauka ya zo tafiya da ke ne? Amma sai kuka na ga kina kuka."
Hawaye ta share tana kallonta."Mama Faruk ba zai canza halinsa ba, a yanzu rayuwata sai ta fi muni a gidansa, domin ya gaya mini cewar ko na zauna ko ya sake ni. Zaɓi ya ba ni, saboda ya ce yanzu ya samu kalar macen da yake so."
"Haƙuri za ki yi, kina gaya wa Allah kukan ki, saboda yanzu kamar yadda ya ce ba ke kaɗai ba ne, kuma sai kin yi hakuri saboda yawa WASU MAZAN in suka yi sabon aure suna juya wa matansu baya."
"Faruk, bai ƙara aure ba yana wulaƙanta ni, ina ga ya samu matar da yake so. Na san cewa rayuwar da zan yi a gidansa, Ubangiji ne kawai gatana, amma ki sani Mama a wannan karon ba zan yi masa biyayya ba, saboda na gaji da cin kashin da yake mini. Ni ma fa mutum ce mai daraja. A rayuwar aure sai a yi ta cewa mace ta yi haƙuri, bayan an san miji yana cutar ta. Shi ya sa asibiti muka yi yawa mama. Ciwon depression ya yi yawa a cikin mata. Mata suna wani irin rayuwa sai kaga mace tana tafiya tana magana kamar zarrariya. Namiji ya ƙunsa mata baƙin ciki in ta zo gida iyayenta ba za su ƙwato mata haƙƙinta ba, sai a ce ta yi haƙuri. A aure mata kawai ya kamata su rinƙa haƙuri? Mama ba zan yarda ciwon depression ya kamanni ba, na haukace a banza su Raihan suna bukata. ."
"Ki mai da lamuranki ga Allah, duk wanda ya yi haƙuri ba zai taɓe ba."
Kuka ta fashe da shi,"Allah Sarki Ya Ahmad! Ubangiji ya bayyana ka haƙiƙa na yi rashin jigo, amma na yi maka alƙawarin ba zan ƙara zama Faruk ya wulaƙanta rayuwata ba, zan ƙwaci 'yancina, domin tun da na rasa ka bana tunanin a yanzu, akwai abin da ba zan iya rabuwa da shi ba. A yadda nake ji ko ni kaɗai ne a cikin duniya, zan rayu kuma na sanyawa kaina farinciki. "
"To ya za mu yi? Ubangijin kawai ya san yana raye ko ya mutu, fatanmu Allah ya bayyana shi." Cewar Mama tana share hawaye.
A daren ranar ta gama shirye-shirye ta. Kasa bacci ta yi sai juye-juye take yi. Tana tunanin yadda zamansu zai kasance, don ba zata yarda ta ƙara wulakanta ba. Sallah ta yi ta roƙi Allah ya ba ta haƙurin jure duk abin da za ta gani, sannan ya ƙara cire mata tsoron Faruk ta ƙwaci 'yancinta.
Washegari da safe duk yadda Mama ta yi da ita don ta yi kitso da lalli, amma ta ƙi don ba da ninyar zaman auren za ta koma ba, ballanatana ta yi abin da zai burge shi. Kallon kanta ta yi yadda ta rame, duk da cewar ta ciki ba kamar lokacin da ɓacewar Ahmad take sabo ba. Da dadddare Baba ya tsareta sai da ta shirya. Shi da kansa ya kaita har ƙofar gida, sannan ya buga ƙofar."In kin ga dama ki yi hakuri ki zauna da mijin ki, in kuma kin sanya kishi ya sake ki, wallahi kin ji na rantse miki sai dai ki samu wani uban, domin kin san Faruk ba zai karɓi 'ya'yansa ba, ni kuma ba zan riƙe ɗan uban kowa ba, musamman shi da ba shi da ta ido. Kina dai ganin zawaran layinmu sun yi yawa, saboda yanzu maza sun yi ƙaranci. 'Yan matan ma, da yaya suke samun maza, ballanatana zawarawa, kuma in..." Maganar ta maƙale masa sakamakon jin ya buɗe get ɗin.
Ganinsu ya sanya shi canza fuska, ya tokare get ɗin yana kallonsu. Dariya Baba ya yi."Ga shi na dawo da ita a rinƙa haƙuri, na ɗauka da ka zo tafiya da ita za ka yi?"
"Saboda ni na kaita ko? Sharuɗɗa na kafa mata, don wallahi yanzu ba zan ɗauki rashin mutunci ba, ina da matar kirki da take faranta mini tana mini duk abin da na ke so."
Ɗago idanunta ta yi cikin tsana tana kallonsa."Eh ki ji da kyau ɗin haka ki san zaman da za ki yi." Ya ce mata ganin shi take kallonta.
"Ayi dai haƙuri komai ya wuce. Ke Nasreen shiga ciki." Ya ce mata.
Jin hakan ya sa ta fara tafiya za ta shiga. Ganin haka ya matsa ya ba ta hanya yana harararta.
Da ta dumfari gidan gabanta ya fara wani irin sauti. Tana zaune a falo mace ƙatuwar mai jiki sosai. A yadda fuskarta ta nuna ta girmi Nasreen sosai. Tana da ƙiba da kuma ƙirji, sannan ko ina na ta a cike yake. Fuskarta fara ce sosai, domin an dade ana mai. Sanye take cikin wando skin tie ya matse ta dosai, domin kusan yana bayyana surarta, sai riga iya cibi. Kanta babu ɗankwali sai uban attach da aka yi mata kitso ƙanana da su. Tana riƙe da remote a hannunta tana kallon Nigeria film.Tsoro firgici da tashin hankali ya kama ta har sai da ta ji kamar za ta yi hauka. Wani juwa ya kamata har ba ta gani abin da ke gabanta, sai kuma ta dake don ta sanya a ranta daga yanzu ba lokacin da wani a duniya zai tsorata ta bane, ballanatana wata jibgegiyar matarsa ta tsorata ta. Ta riga ta kama yankewa ko zai kasheta ba za ta yi zaman wahala a gidansa ba, don a yanzu ko a mutu ko a yi rai. Za ta nemi farinciki a duk inda take. Ba za ta ƙara yarda wani ɗa namiji ya sanya ta kuka ba. Ita ma mace ce, kuma mace mutum ce da take da daraja.
Tana wannan tunani, Faruk ya ƙaraso cikin falon yana ƙoƙarin cire jallabiyar da ya zura. Da ya cire sai ya rage da ga shi sai gajeren wando. Zama ya yi kusa da ita yana watsa wa Nasreen mugun kallo. Peck ya ba ta gashi tare da sakin mata murmushi, ita kuma ta kamo hannunsa. Zan iya hakuri na zauna kuwa?" Ta furta hakan cikin tsanannin tashin hankali tana ƙaranto duk addu'ar da ta fito bakinta. Basarwa ta yi kamar ba ta gani ba.
Rashida ta mike zuɓbur tana kallonta. Lokaci ɗaya suka ƙara kallon juna. Tun kafin ya aure ta ta so ya nuna mata hoton Nasreen, amma ya yi mata rantsuwar babu hotonta a wayarsa. Da fari ba ta yarda ba, amma da ta karɓi wayar sai ta yarda da maganarsa cewar ba zai sa ya hotonta ba, abokansa su ga ni su yi masa dariyar matarsa mai kama da taɓarya,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 17