Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
miƙe don ta ɗauki kofi ta jiƙa mata. "Yadda za a yi da kuɗinnan, Ya Ahmad ka karɓe su duka ka ci gaba da nema mata magani, Allah ya ba da lada kana matuƙar ƙoƙari." "Haka ya kamata ko wane ɗan mai son ya gama da iyayen sa lafiya ya kasance Nasreen. Mama ita ce fatanmu a duniya. Kina ganin Baba bai damu da rayuwarmu ba, kasan kawai ya sani. Sam bai san haƙƙin 'ya'yan da ya haifa ba. In har bamu nema mata lafiya ba wa zai nema mata?" "Haka ne, Allah ya shirya iyaye masu halinsa ya sanya su gane cewa. Aure da 'ya'ya duk a ranar lahira sai Ubangiji ya tambayeka yadda ka kula da su, kuma Ubangiji ya ce dukkanninku makiyaya ne ranar gobe kiyama zai tambayi kiwon da aka baku. Amma abin takaici da alhini har da zaman makoki WASU MAZAN sun ɗauki rayuwar aure don biyan buƙatunsu sa ba wai ibada ba. Sun mata cewa aure bauta ce ta Ubangiji ne, haka kula da yara duk Allah ya azurtata ya kuma ka ce ka kula da su." "Haka ne Ya Ahmad, da yawa WASU MAZAN yanxu don buƙatar kansu suke aure ba don bauta ba." "Allah ya sa su gane, su ɗauki auren a matsayin bauta sai a taru a gudu tare kuma a tsira tare." "Amin," Ta furta. "Wallahi tallahi a gidan nan daidai na ke da uban kowa. 'Yan iskan yara matsiyata mara sa mutunci." Suka ji muryar Baba yana faɗin haka daidai lokacin da ya iso ƙofar ɗakin. Da sauri suka haɗa idanu Nasreen ta kai hannu za ta ɓoye kuɗin da abincin, amma sai dai ba ta yi nasarar ɓoye kuɗin, ban da abincin da fruit ɗin, ya riga ya banko ɗakin babu sallama yana mazurai. "Haba Baban Ahmad, ya kamata ka daina zagin yaran nan ka san babu kyau haka?" "Ban yi magana dake ba don haka ki ji da ciwon ki, tun kafin na yi miki tijara. Ba dole na yi magana ba. Ɗan bazan yaron Aminu, na gani ya dawo daga kasuwa ya samu kuɗi, na tare shi ya bani naira dubu na sha shayi, amma ya rantse mini ba zai bayar ba, wai zai biya kuɗin islamiya." "Haba Baban Ahmad, kai ya kamata ka kula da karatunsa, ba ka biya ba, ya samu kuma zai biya sai ya zama tsiya?" Harara ya zabga mata jin abin da ta ce,"Ai to laifina za ki gani ko? Ai dama kullum ni mai lafi ne a gurin ki. Yanzu ma na tabbata kun haɗu ne ke da yaranki kuna zagina. Wallahi kin bani mamaki ƙwarai, domin ban san lokacin da kika canza ba. Ace wai da yaran da na haifa za ki zauna kina gulmata?" "Gaskiya ce ba ka so, amma ba gulman ka muke yi ba. Haƙƙinka da ka kasa saukewa a matsayinka na uba muke magana a kai." "Ba ni da shi zan yi ma kaina dole ne? Ko sata kike so na je na yi? Ai na riga na gaya muku koya ya yi ta kansa, domin wallahi Allah bai yi ni mai arziki ba, ba zan je na kashe kaina ba." "Amma ka san ba ka da shi Baba ka rinƙa aure-aure kana tara yara? Duk da yadda rayuwarsu suka zama Allah sai ya tambaye ka." "To fitsarrare mara kunya! Ai ni na yi mamakin tun da ka na shigo maka yi mini fitsara ba. Ɗan banza wanda ya fitsare ƙafarsa. Sunnar ma'aikin da na ɗanbaƙa, shi ne kake ɓakincikin da ladar da zan samu. Manzon tsira ya ce,"mu yi aure mu hayayyafa ranar gobe kiyama ya yi alfahari da mu." "Baba, ba irin yaran da kake haifa ba. Kana ganin halin da kake sanya yaranka, saboda ba ka tsaya ka inganta rayuwar mu ba. Jiya fa haka Ashiru ya dawo gidan na yana tangaɗi. Ga Na'ima kwana biyu ba ta kwana a gida ba, kuma ko ajinka hankalinka kwance." "Au to so kake na mutu? Ai duniya ce duk wanda ya ce lalacewa zai yi ya je duniya ce, ta ishi bagaruwa jima." "Amma dai kai ka haife su kana da haƙkin ka kula da su." Cewar Nasreen cikin damuwa tana kallonsa. "Nasreen! Au ke ma fitsarar za ki yi mini? Wai tsaya yaushe kika zo ma cikin gidan nan? Allah ya sa mijinki ya sani, don wallahi ya zo ya yi mini tijara sai na yi mugun saɓa miki, in kuma kika kuskura ya sako ki sai dai ki nemi wani gidan uban. Kin san dai ba za ki yi mini zawarci a gidana ba, domin na gaya muku dama alla-alla na ke na aurar da ku, tun da kuma na samu waɗanda suka ɗibe ku, babu shegiyar da za ta dawo mini gida. Ballantana ta zo mini da 'ya'ya." Shiru ta yi ta matsa cewa komai, sai hawaye shar suka wanke mata fuska. "Da ma na san ba ni da gatan da ya fi zaman aurena." Ta furta tana share hawaye. Ganin babu wanda ya tanka masa, ya ci gaba da kallon da yake yi ma abincin da ayabar. "Tuni na san cewa ni a gidan nan. Babu mai ƙaunata. Duk ɗan da zai shigo gidan nan sai dai ya kawo wa uwarsa abu, amma ni ba ku da mu da na ci ba ko na mutu oho!" "Kai ya kamata ka basu, in ba ka basu ba, dole mu nemo ko a wuta mu basu, don kar mu rasa su." "Ni kuma inna mutu ba ku da damuwa." Ya ce ba tare da ya kalle su ba ya ɗauki ayabar ya ɓare tare da jefawa a baki. Zama ya yi a gefen gadon yana zare idanu."Wannan abincin na cikin farar robar nan. Tak away ake ce mata ko take way?" Ya ɗauki abincin tare da ɗauke cinyar kazar. "Ikon Allah masu kuɗi na sha'aninsu." Ya ce tare da kai loma. "Ke Nasreen, ba dai ke kika kawo wannan abincin ba, domin na san wannan ɗan iskar maƙoƙon mijin na ki ba zai iya ba ki wannan abincin ba. Mara mutunci shekaranjiya na kira shi ya bani bashin dubu goma, amma ƙememe ya ce ba shi da kuɗi. Wallahi bacin bana son ki yi zawarci da saina raba ki da shi na aura mai kuɗi irin mijin Nadiya, saboda shi ina ce ya bani za ki ga ya miƙa mini." "Ta ya ya zan yi daraja a guri sa Baba, kana zubar mini da mutunci kana cin bashi a gurinsu? Bana haƙuri kawai na ke yi a zaman aure a, amma wallahi zaman gidan yari yafi mini zama da Faruk." "Kuma ba ki da zaɓin da ya wuce zama da shi." Ya furta tare da kai lomar abincin. Cikin takaici suke kallonsa tamkar za su rufe shi da duka suke ji. Haƙiƙa ba su yi dacen uba na gari ba." Tsananin mamaki da ya kama su, ganin yana shirin cinye abincin nan, ya na zuba surutu mara ma'ana. "Baba, abincin nan na Mama ne domin shi za ta ci ta sha magani." "Ni ma bani da lafiyar ai. Jiya da na je gurin yaran nan Tukur mai kyamis ya ce yunwa takama ni. In kuma so kuke na mutu shikenan dama na san baku da asara." Ya furta ba tare da ya ƙara magana ba, sai da ya cinye abincin nan tas! Ya tsaki wata mahaukaciyar gatsa yana shafa tunbinsa. "Yauwa, ku yi wa mahaifiyarmu magana ta cire wannan damuwar banzar da ta sanya ma kaina, saboda ita kanta ta san cewa da ace zan canza halina da tuni na canza, don haka ban ga abin da zai sanya ta sawa kanta hawan jini ba." Ba tare da sun ce masa uffan ba suka ci gaba da kallonsa. Har zai fita sai ya dawo ya kalli Ahmad." Ɗan bani naira ɗari biyar na sha ruwan bunu." "Bani da shi saboda na kashe duk kuɗin a asibiti. Yanzu haka ma akwai maganin da ban siya ba." "Ai sai ka ba da himma." Ya ce yana harararsa. "Ke dai na san ba samu zan yi ba, don haka ba zan ɓata bakina ba." Ya ce mata tare da ficewa daga ɗakin. "Kai halin Baba sai shi. Allah ya shirya mana mahaifinmu." "Rashin ilimi da sanin darajar aure yake damunsa." Cewar Mama tana hawaye. Sun kasa rarrashinta su kansu hawaye suke yi. Tun da suka taso suke cikin wannan rayuwar har zuwa girmansa ba ta sake zabi ba. "Yanzu kin ga yadda za a yi da kuɗin nan. Ki bawa mama, dubu goma ta ije a gurinta, ta rinƙa siyan abinci tana ci. Sannan dubu biyar ki ɗauka ke ma kina buƙatar kuɗin. Dubu uku kuma a bawa Zainab ta je ta biya kuɗin islamiya da hadda." "To Yaya Ahmad, kai kuma fa? Kana bukatar kuɗi?" "Kar ki damu da ni. Namiji na ke zan kula da kaina." "Amma ko dubu biyu ka karɓa." Murmushi ya yi yana girgiza mata kai, wanda ta tabbatar ba zai karɓa ba tun da ya ce. "Yaya Ahmad, Allah ya buɗe maka saboda kula da mu da kake yi." "Amin," Shi da Mama suka amsa har da Zainab. Miƙewa ta yi da sauri kamar an tsikareta ta ce,"Bari na tafi gida Raihan na can zan biya na ɗauke ta, kuma ban yi abinci ba." "Har yanzu dai yana nan yana ba ki abinci tazarce ko?" Mama ta tambaya cikin ƙunar rai. "Ai Mama, yadda yake mini ya wuce tazarce. Girki ɗaya zan yi sai kuma gobe. Ga shi ba ya isanmu sai dai na haƙura." "Allah ya kawo mafita ki kammala karatun ki. Ko koyarwa kika samu a makarantar gashin kai, za ki samu sauƙin rayuwa." "Amin Allah kuma ya sa ya yarda." "Inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Ahmad da sauri. "To, mai za ka yi masa? Matarsa ce fa. Kai dai Allah ya sanya ya amince ɗin dai." "Hmmmmh! Aiko da wuya, gurguwa da auren nesa." "Ashe ko za a kwashi 'yan kallo ni da shi. Don yadda na ke kashe kuɗi a karatunta dole ta amfani da shi." "Allah ya sa." Mama ta ce tana nishi da ƙyar. "Mama, na tafi zan dawo in sha Ubangiji ya ƙara sauki." "A gaida gida na gode, kuma ki gaishe mini da kishiyata." "Za ta ji." Ta ce tana ƙoƙarin goya Musaddik tare da kallon Ahmad da ya miƙe. "Bari na taka miki har ki samu mashin." "Yauwa ɗan'uwa rabin jiki." Ta ce tana dariya. Fitowa suka yi a tare suka jera duk da cewar ba magana suke yi ba. Sai da suka fita daga gidan sannan ta kalle shi ta ce,"Ina son na je gidan Yaya Sha'awa na ƙara duba mijinta." "Ni ma ina so na ƙara zuwa ciwon Mama ya sanya ban je ba, saboda ya kamata na kai mata wani abu." "Allah dai ya biya ka ƙoƙarin da kake yi." "Amin," "Bari na ɗan yi cefane dubu uku sai na ije dubu biyu." "Ok, ki sayi abu a shagon Habu." Ya ce mata tare da yin shagon. Biskit ta siyasa Raihan na ɗari biyar, sai ta sayi indomie na dubu da ɗari biyar. Dubu ɗaya ta tsinci ashana, suga da gishiri. Sai ƙaramin makilin da ta saya musu don na su ya ƙare. Bayan sun fito da ga shagon, ya tsayar mata da adaidaita ta shiga tana ɗaya masa hannu. Da ta isa daidai unguwarsu ta sauka sannan ta biya kudin. Gidan Maman Muwadda ta nufa don ta ɗauki Raihan. Da sallama ta shiga cikin gidan, ganin babu kowa a tsakar gidan sai ƙarar tibi, da kuma surutun da take ji a falon ya sa ta tura ta shiga. "Yar Halas! Da ma yanzu Raihan take mini ƙorafin yau Ummanta ta daɗe a makaranta." Ta ƙarashe maganar daidai lokacin da Raihan ta miƙe, tare da rugawa ta isa gareta tana faɗin,"Oyoyo Umma." Rungume ta yi ta ce,"Ke dai bari kawai. Ciwon Mama ya tashi na biya na dubata." "Allah Sarki ya jikin?" "Da sauƙi." Zama ta yi gefen kujerar da Maman Muwadda take tana kallonta. "Bari na kawo miki abinci dama yanzu na sauke." "Da kin barshi Rainah ta ci kuma sai na ci?" Ta ce mata tana murmushi. "Haba dai! Kin fi ƙarfin abinci a gidan nan, domin mun zama 'yan'uwa. "Allah dai ya saka miki da abin da kike mini, domin shi kawai zai iya biyanki." Murmushi ta yi, ba tare da ta ce komai ba, sai ta miƙe ta shiga kicin ta ɗauki kula ta zuba mata abincin. "Yau rigimar oga ta tashi. Sai da rana ta yi ya aiko mini da kayan ciki wai waina da miya zan yi mishi. Kin ga yadda na ji haushi kuwa? Don ma Allah ya so ni, lokacin tashin Baba Talatu bai yi ba." Dariya ta yi cikin tsananin sha'awarta. Duk da cewar Faruk ya fishi matsayi a gurin aiki, amma yana matuƙar ƙoƙarin kula da iyalinsa, don ko kayan da suke sakawa sun bambanta da nasu. Ga shi mutum ne mai tsananin kula da abincin da iyalinsa za su ci. Sam ba ya muguwar cima, wannan ya sa ya kullum kicin ɗinta, shaƙe da kayan abinci. Tana matuƙar sha'awar rayuwarsu, musamman yadda yake mata magana cikin taushi da soyayya. Ko ita da take maƙociyarta da mutunci yake kallonta. Saɓanin Faruk da rashin mutunci da ba ya tashi sai in ya ga ta yi baki. "Bari na wuce dare ya fara yi." "To shi ke nan Allah ya kaimu gobe. Ya kamata in za ki koma duba Mama na biki." "Ai da kin barshi duka yaushe kika je?" "Haba kar ki damu. Allah ya ba ta lafiya." Amsawa ta yi sannan ta fita daga gidan. "Umma kin yi mini tsaraba?" "Eh, na yi miki kuma Mama ta ba da ayabar da lemu na kawo miki." "Yauwa Ummata." Ta ce tana tsallen murna. Addu'ar shiga gida suka yi, sannan ta buɗe musu get suka shiga ciki. Hutawa ta yi, ta ɗan ƙara gyara gidan, ganin kafin ya fita sai da ya ƙara ɓata gidan. Tana wanke filet ɗin da ya ci abinci aka kira sallah. Gama wanke wa ta yi, sannan ta shiga bayi, ta ɗauro alwala bayan ta taimaka ma Raihan ta yi. Da suka idar da sallar, suka zauna a falo, suka ci abincin da Maman Muwadda ta ba su. "Na ga kamar an kawo wuta a maƙota, amma babu a gidan nan. Raihan, zo ki haska mini na duba mita ko ya ƙare." WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 GE 6 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 6 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Miƙewa ta yi, tare da karɓar wayar ta nufi inda take zuwa don ta haska mata. "Ikon Allah ɗage wutan ya yi kenan?" Ta tambayi kanta cikin tsanani mamaki. Ba ta kunna wutar ba, don ta san mai zai haifar. Komawa ta yi ta zauna tana mamakin mugun halinsa. Kasancewar sun ci sun ƙoshi, sai ba ta jira shi ba. Suka yi isha'i ta yi kwanciyarta tana karatu har bacci ya kwashe ta. Ba ta san lokacin da ya dawo ba. Cikin bacci ta ji an ɗauka mata duka mai ƙarfi. Da sauri ta tashi tana salati tare da sosai wurin. "Mai na yi maka za ka duke ni ina baccina?" Cikin muryar kuka ta yi masa tambayar. "Ok, tambayata kike ko? To bari na yi miki wanda ya fishi sai ki yi tambayar mai dalili." Ya ce tare da ƙara kai hannunsa wanda ya sa ta miƙe da sauri. "Uban wa ya ce ki ƙi tashi kina jin ina ta hon?" "Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe ni, saboda na gaji sosai." Ta ba shi amsa cikin muryar kuka. "Sai aka ce miki hakan ya dame ni, ko ni na ce dole ki nace sai kin yi boko? Kamata ya yi ki zauna a cikin gidanki, ki nemi lada ki zama full house wife, kamar yadda kowa ce mace ƙwarai take yi." Ba ta ce masa komai ba ta tsaya tana mazurai. "Oya, ma za wuce ki buɗe mini get don ban shigo da mota ta ba, a waje na ije ta, don ga ki ba zan wahalar da kaina ba." Miƙewa ta yi, jin abin da ya ce ta sanya hijabi bayan ta ɗaura zani. Get ɗin ta buɗe masa, bayan ya shigo ya kashe motar, ta buɗe bayan motar ta kwashi kayan da ya shigo da shi. Wucewa ya yi gurin motar ya kunna wutar sannan ya shigo cikin falon. "Abban Raihan, saboda me ka kashe wutar?" "Akwai uban da ke biya mini ne?" "A'a, mamaki dai na yi da ka kashe, saboda matarka da yaranka za su ga haske. Raihan tana ta damuna na kunna mata kallo." "Shi ma kallon daga yau na daina bari kuyi, domin matuƙar ba za ki zama mace mai tarbiyya ba, ni kuma ƙwandalata ba za ta yi ciwo ba." "Mai na ke maka Abban Raihan? Iya kokari ina yi na ga cewar ban shiga haƙƙinka ba, amma kullum maganarka ni ba mace ƙwarai ba ce." "Ok, da ma kina yaudarar kanki kenan? To bari ki ji matuƙar ni zan ɗaga ƙafarsa ki shiga aljanna, babu ke babu samunta, domin ba ki da kirki sam ba kya jin maganata Nasreen." Ranta ne ya ɓace, ba tare da ta ce masa komai ba, ta juya za ta koma ɗakinta. "Nasreen!" Ya kira sunata da ƙarfi yana huci. "Har kin isa ina magana ki tafi?" "Bacci zan yi na gaji yau." "Bacci?"Ya maimaita yana mata kallon ƙaskanci. "Bacci saboda kina hauka ba ki yi girki ba?" "Na gaji ba zan iya girki ba." "Ki dai gaya mini kin yi rokon da kika saba, don na san a gidanku babu abincin da za ki samu. In ma kin samu ba ci za ki iya ba." "Saboda ba a gidan na girma na rayu ba? Wallahi babu rayuwar da ba zan iya fuskanta a cikin gidan ba." "Bana tunanin za ki iya, saboda shi kanshi maigidan da ya aje ku, ya kasa ci daku, ba iya haƙura yake yi ba. Na tabbata ƙila ya tambaye ki ko kin kai masa kuɗin da ya tambaye ni?" Ba ta ce komai ba, sai ta fara hawaye tana baƙincinkin halinsa da yake ja mata tozarci. "Ki gaya masa ba zan iya ci da mutane biyu ba. Ke kaɗai na aura, kuma ina da abin yi da kuɗina. Kar ya ƙara tambayata bashi." "Ka gaya masa da bakinka tun da shi ya roƙa ba ni ba." "Amma saboda ina aurenki ne ko? Ai tushiya mafarkin dawa." Sosai ta fashe da kuka ta kasa cewa komai sai kallon sa take yi. Tsaki ya ja tare da zama a kan kujera."in kin gama kukan kike ki ɗora mini girki, kuma yau tuwo da miya na ke jin ci." Zare idanunta ta yi tana kallonsa tare da barin kukan."Tuwo da miya fa kace a wannan daren. Yau ma fa ba ka dawo da wuri ba, dubi lokaci sha biyu saura?" "Ai kin san makaho ne ni. Kuma ai ba a dare a girki. Shi na ke jin ci, kwana biyu ba ci ba." "Na gaji ni ba zan iya ba." Ta furta masa. A ranta kuwa cewa ta yi." Bana jin yunwa babu wanda ya isa ya sanya ni dole. Da ace ina jin yunwa ne dole na yi don cikina da 'ya'yana." "Ke!" Ya daka mata tsawan da ya sanya ta tsaya cak. "Wuce ki ɗora mini tuwo." Ya ce tare da nuna kicin yana zare mata ido. Zumɓura baki ta yi, ta tsaya ba tare da ta ce masa komai ba. Ganin haka ya shiga ƙoƙarin neman abun duka. Da sauri ta shige tana hawaye. Ruwa ta sanya a kettle sannan ta fara jajjage. Kafin ta gama ya tausa ta yi tankaɗe ta yi dame, tare da ɗora ruwan miyan a dayan murhun. Tana girkin tana gyangyaɗi, har ta kamalla tuwon da taimakon Allah ta kawo masa. "Allah ya sa ba ɗanye kira yi mini ba." Ya duba agogo ganin ɗaya ta yi. Ba tare da ta tanka masa ba ta juya ta shige ciki. Bayan ya gama cin abinci ya zauna yana kallo har ƙarfe biyu da rabi. Kashe kayan kallon ya yi, sannan ya shiga ɗakinsa ya kulle ƙofa. Da asuba da ta tashi ta yi sallar asuba, don har ta so ta makara saboda girkin da ta yi. Tana ji yana wanka. Takaici da kishin sa ya kamata don ta san waya ya kwana yi da 'yan mata sa ya sanya shi wanka. Tana ta sauraren ko zai fito sallah, amma har ta cire tsammani, ta ɗauki qur'aninta ta haye kan gadon yana karatu har lokacin tashi ta yi aiki ya yi. Kicin ta nufa ta yi ɗumamen tuwon da ta yi, sannan ta ɗora ruwan indomie ta dafa wa Raihan ta sanya mata a kula.Wanka ta yi ta shirya ta tafi makaranta. Marwana da Damir suna kan hanya zai kai ta makaranta. Hira take masa. Yawancin jiran kan karatunta ne, shi kuma yana ta dariya. "Yauwa Yayana." Ta ce tare da kamo hannu sa ta riƙe wanda ba ya tuki. "Akwai magana kenan" Ya yi mata maganar yana murmushi tare da kallonta sai kuma ya mayar kan hanya. "Eh," "Ina jin ki ƙanwata." "Ba ka ce za ka yi wa wannan matar kyauta ba?" "Wacce?" Ya tambaya don shi ya manta da maganar da suka yi. "Wannan 'yar makarantarmu." "Ok, na gane ta." Ya ba ta masa tare da shiga get ɗin gidansu. "Waya nake son na ka saya mata." Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce."Waya kuma? Ita ta ce miki tana buƙatar haka ?" "A'a." Ta ba shi amsa tana girgiza kai. "Saboda me ya sa kika buƙata?" "Dacewar hakan na gane Yaya, saboda ba ka wayar da take amfani da shi ba. Ko almajirin gidanmu ba zai rike ta ba." Dariya sosai ya yi musamman yadda take yatsina fuska." Marwana rigima! Duk a gurin ki little Marwana, ta gaji nata rigimar. Ke in ban da abin ki. Allah bai halicce mu duka ɗaya ba. A haka da take da wannan wayar kar ki yi mamakin irin rayuwar farincikin da take yi, saboda Allah ya halicci mutane daban-daban, kuma rayuwarsu daban-daban." "Na sani Ya Damir, amma ita tana da bukatar wayar. Tun da ka ga karatu take yi, in za ta yi assignment da karatu tana shan wahala." "Duk da hakan ba ta wayar kamar shishshigi ne a rayuwarta." "Ni dai Please Ya Damir, sai dai kuma in ba ka yi ninya ba." "Na isa? Zan siya mata system da waya hakan ya yi miki?" "Really?" "Sure, for you

Chapter 4 of 17