Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sun yi ciki da ita. Ganin yadda Marwana ta tayar da hankalinta kamar za ta yi hauka. Ya sanya shi jawo ta ya rungume daidai lokacin da ta yi kamar za ta shiga ciki "Take easy za ta samu sauƙi. Kina sonta da yawa." "Yaya Nasreen ba ta da gata sai Allah. Kai kanka in har ka ji rayuwarta za ka tausaya mata." "Allah ya kawo mata ɗauki, amma ina mijinta yake a wannan lokacin? Ya san matarsa na da ciki ya tafi ya barta." "Ban sani ba ta ce ya yi tafiya." Jinjina kansa ya yi, ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Sun daɗe a gurin sannan likitan ya fito yana share zufa. Da sauri suka yi burinsa. "Doctor how is she?" Damir ya riga ta tambayar ganin yadda ta damu da ita. "She is getting better. Mun yi ƙoƙarin mun tsayar da jinin, yanzu so muke ta ɗan huta ayi mata wankin ciki." Tausayinta ya sanya ta ja numfashi."Ok please do." Damir ya ce yana cusa hannunsa a aljihunsa. "We will." Likitan ya amsa tare da ba shi hannu ya koma ciki. "Marwana I think I will take my leave. Kin ga halin da Mommy Little Marwana take, bai kamata na barta a ita kaɗai ba." "Ok Yaya, amma kwana zan yi saboda ba zan iya barin ta ba." "Ƙarki damu zan dawo na kawo muku breakfast. Sai ki sanar da iyayenta, ki dawo gida." "To Yaya, Please drive safe." Ta ce masa tana kallon sa. Har ya kai baƙin ƙofa, sai ya dawo da ya tuna yaran suna cikin mota."Ina ga zan wuce da yaranta, tun da bai kamata su kwana a kwana asibiti ba." "Haka ne Yaya, ka wuce da su da safe sai ka kawo mini su." Kaɗa kansa ya yi, ba tare da ya ce komai ba, ya fice daga asibitin. A lokacin da ya isa gida sai ya kashe motar, bayan ya yi parking. Yaran ya ɗauka ya shiga ciki da su. A lokacin da ya shigo cikin ɗakin, da ta farka ta shafa inda yake kwance ta ji babu shi. Tana tunanin yana bayi ne, don haka ta koma ta kwanta tana jiran ya fito. Jin shiru sai ta fara shiga damuwa. A hankali ta miƙe ta shiga cikin bayin amma ba ya nan. Falo ta duba nan ma ba ya nan. Wayarta ta ɗauko tana ƙoƙarin kira, ganin sha biyu saura sai ta ji ƙarar motarsa. Daidai fitowar ta falon ta gan shi ya shigo da sallama rungume da yara. Gabanta ya yi mugun faɗi, ta ƙara da burinsa daidai lokacin da ya kwantar da su. Kallon yaran ta yi ganin su kyawawa sosai kuma farare. "Baby, ina ka samu yara?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa, da yayin da zuciyarta ke kimtsa mata mugun tunani. Yana ƙoƙarin amsawa sai ta katse shi da cewa,"Wai ina ka je da daddaren nan? Hankalina ya tashi ina ta nemanka." Kallon yaran ya yi, yana mamakin kyawun yaran, domin suna da kyau sosai, musamman Raihan da har wani tsanwa take yi, kuma da ma Musaddik ya taɓa ganinsa. Tunani yake haka uwarsu take, amma mijin ta yake wulaƙanta su. "Yaran ƙawar Marwana ne. Ina bacci ta tashe ni ta yi ɓari, kuma mijinta ba ya nan ya yi tafiya. Shi ne na ce su je da direba, amma kin san halin ta da rigima, kan dole ta sa ta muka je. Wallahi da muka je na tausaya mata sosai. Kai gaskiya wa WASU MAZAN ba sa yi wa matansu adalci. Jin ta yi ba ya ce, sai ba ta ce komai ba, tana kallon yaran da ya kasa ɗauke idanunsa. Ta ja numfashi ta fesar sai kuma ta daure."Ikon Allah." Ta ce sai kuma ta kalle shi ta ce,"Shi ne ta rasa wacce za ta kira sai ƙawa? Ita ba ta da kowa ne?" Tambayar da ta yi masa ya sanya ransa ya ɗan ɓaci, duk da cewar shi ma ya yi tunanin haka. "Please dare ya yi bacci na ke son na yi. Ina ga wannan tambayar inta dawo sai ki yi mata. Yaran nan bari na kai su ɗakin little Marwana." Ba tare da ta ce masa komai ba, ta juya ta shiga cikin ɗakinta. Zama ta yi tana jin yadda zuciyarta ke suya. Duk da cewar matar aure ce, amma ta ji babu daɗi, saboda ba ta son mijinta ya yi hurɗa da kowa ce ya mace." Raka ta da idanu ya yi, ganin yadda fuskarta ya canca."Mata.." Ya ce tare da girgiza kansa. Har ɗauki ya kai su ya kwantar, sannan ya ja musu ƙofa, bayan ya yi musu addu'ar bacci. Da ya tura ɗakin ya shiga, sai ya same ta a zaune ta zabga damuwa.Da sauri ya ƙarasa ya janye mata tagumi."Kin san yanayin da kike ciki za ki sanya wa kanki damuwa?" Hawaye ya gani suna zubowa a fuskarta." Yarannan da ka shigo da su ya sanya na ji kamar watarana za ka shigo da su a matsayin 'ya'yanka, waɗanda wata macen ta haifa maka. Wallahi ba zan iya jurar ranar ba, fatana gara ace na mutu za ka ƙara aure. " Ta ƙarashe maganar tare da rungume shi ta saka kuka. Jin abin da ta ce hankalinsa ya tashi matuƙa gaske! Ƙara matseta ya yi ajalinsa yana saukar da numfashi. "Mai ya sa kike tunanin zan iya ƙara aure? Wallahi kin ji na rantse miki. Ko babu ke a cikin duniyar nan ba zan iya kallon wata 'ya mace da sunan aure ba. Ina sonki ban taɓa kallon wata 'ya mace da sunan soyayya ba. Ke ce mace ɗaya wacce zuciyata take bugawa saboda da ita. Tun lokacin da ba haɗu dake tausayinki da ƙaunarki suka cika raina. Ina sonki kuka zan yi miki alƙawarin da zai sanya ki yadda da soyayyarsa. Ni Damir ba zan taɓa kallon wata 'ya mace da sunan ina sonta ba, ko da ace bakya raye. Zan rayu ni kaɗai har lokacin da Allah zai ɗauki raina, na je gare ki sai mu ci gaba da rayuwarmu a Aljanna." Jin abin da ya ce sai ta share hawaye."Karka ga laifina da son kaina. Kishinka da sonka suka sanya nake jin haka, saboda lalurata kuma na ke jin kamar ba zan yi tsawon rai ba." "Shiri!!!" Ya ce da sauri bayan ya sanya hannunsa a bakinta yana mata wani irin kallo wanda yake sanya ta ji ta ƙara zurmawa a sonsa. "Mai ya sa kike yawan tunanin mutuwa za ta raba mu? Ki daina tunanin haka saboda duk lokacin da kika faɗa mini, sai na ji kamar ki ma wa'adina ya cika. Kina tunanin zan rayu a duniya in babu ke?" "Dole za mu mutu babyna." "Amma ba yanzu ba, sai mun ga jikokinmu har da tattaɓa kunni." Yadda ya yi maganar, yansa ta saki murmushi, tare da rungume shi tana haɗa hancinsa guri ɗaya suna jin saukar numfashinsu. Ƙara haɗata da jikinsa ya yi yana shaƙar ƙamshinta ya ce,"To ki kwantar da hankalinki. Mijin ki na ki ke ke kaɗai, kuma za ki yi tsawon rayuwar da za mu tsufa tare. Bayan ya tafi ta zauna a bakin ƙofar tana tunanin halin da take ciki.Ta kasa bacci tunani kawai take yi. Har zuwa asuba sannan ta samu ta kwanta bayan ta yi sallah. Da gari ya waye ta miƙs daidai lokacin da wayarta ta yi ƙara. Rungumeta ya yi ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta, kamar wata jaririyar da yake son ta yi bacci. Tana kwance a kan ƙirjinsa hawaye ya bin ƙuncinta. Ji take yi kamar za ta mutu wata ta samu tsadadden mijinta. Tana sonsa da mugun kishinsa, sai dai a jikinta ba ta jin za su yi tsawon rayuwa. Bayan ta yi bacci ya kwantar da ita ya miƙe. Bayi ya shiga ya ɗauro alwala, sannan ya shiga cikin ɗakin yaran. A lokacin Musaddik ya farka yana kwance a kan gadon "Umma," Ya ke kira da muryar gwarancinsa. Da sauri ya ƙarasa kan gadon ya ɗauki yaron ya rungume. "Ka tashi baby boy?" Ya yi masa tambayar yana tunanin sunan shi da Marwana ta gaya masa. Kallonsa ya yi kuma yana kallon ɗakin. Da sauri ya ɗauke shi. Ganin bai san shi ba sai ya saka kuka. Da ƙyar ya samu ya yi shiru. Kicin ya nufa yana ƙoƙarin haɗa masa tea, Baba ta shigo tana goge idanunta. "Sannu Alhaji." Ta ce masa ganinsa ɗauke da yaro yana jijjiga shi. "Yauwa Baba, don Allah ki kula da shi." "To Alhaji, baƙin yara muka samu ne?" Ta yi masa tambaya tana kallon yaron. "Eh, ki ba shi abinci, da alama nono yake son sha, kuma mahaifiyarsa na asibiti babu lafiya." "Ashsha! Allah ya kawo sauƙi." Ta ce bayan ta karɓi yaron. "Amin," Ya amsa sannan ya koma cikin ɗakin ya fara sallah. Sai da ya kai kusan ukun dare, sannan ya miƙe ya kwanta. Bai ta shi ba sai da aka kira sallar farko. Bayi ya shiga ya yi alwala, sannan ya zauna yana jiran a kira sallah. Bayan gari ya waye wayarsa ya ɗauki ya danna layin Marwana. Ganin Damir ne ya sanya ta saki murmushi."Hello Yaya," Ta ce bayan ta ɗauki wayar. "Marwana kun kwana lafiya? Ya mai jikin?" "Da sauƙi har yanzu ban ganta ba. Cikin dare suka yi mata wankin cikin kuma sun ba ta rest bed. "Okay, Allah ya ƙara sauƙi, bari na sa ya Baba ta haɗa muku breakfast sai na kawo muku." "To, Yaya don Allah da kayan da zan canza da kuma ita." "Ok zan kawo miki." Ya ce tare da kashe wayar. Bayan ya kashe wayar, miƙewa ya yi ya ƙarasa gurin ta da take zaune a kan kafet tana azkar, hannunta ɗauke da Hisnul Muslim. Hijabinta ya cire tare da kai hannunsa kan cikinta."Da fatan tauraruwar mata gimbiya ta shi lafiya?" Murmushi ta yi masa tana kallon sa. Bakinta ta kai saman goshinsa ta sumbata. Ya rintse idanunsa yana jin kiss ɗin har zuciyarsa. WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 14 Wancan group ɗin ya cika an buɗe wannan, masu son shiga sai su bi link. BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Bayan ya kashe wayar, miƙewa ya yi ya ƙarasa gurin ta da take zaune a kan kafet tana azkar, hannunta ɗauke da Hisnul Muslim. Hijabinta ya cire tare da kai hannunsa kan cikinta."Da fatan tauraruwar mata gimbiya ta shi lafiya?" Murmushi ta yi masa tana kallon sa. Bakinta ta kai saman goshinsa ta sumbata. Ya rintse idanunsa yana jin kiss ɗin har zuciyarsa. "Ina lafiya lau my Nurii.""Daddy, yana son ya ji ɗumin babbynsa?" Yadda ya yi maganar ya ba ta kunya ta kalle shi."Baby ya ce kar daddy ya wahalar da mommynsa." Jin abin da ta ce sai ya yi murmushi ya miƙe yana faɗin,"Kar Baby ya damu, Daddy zai ƙara masa ƙarfi ne." Cak ya ɗauke ta duk ƙaton cikinta, ya ɗora a gadon tare da yin mata rumfa. Bayan ya kasheta da kalar soyayyarsa ya miƙe ya shiga bayi. Wanka suka yi, a tare sannan suka shirya suka fito don su karya. "A dining suka zauna ganin Baba Azumi ta shirya musu abin kari." Ƙwala mata kira ya yi. Ta fito da sauri ta ce,"Alhaji gani." "Yauwa don Allah ki haɗa abinci a kai wa su Marwana, sannan yaran nan ki shirya su, kuma sun ci abinci.?" "Eh, na sanya musu kayan Marwana. Na mijin ne dai na duba a cikin kayanta na jarintaka, na sanya masa su." "Ok, ba matsala bari na gama karyarwa na kai su gurin mahaifiyarsu." "To Alhaji." Ta ce tare da juyawa. Cikin so da ƙauna suka ciyar da junansu. Da ya kammala aka kawo mishi su Raihan. Kallo su ya yi yana sha'awa yaran. Kallon su suke yi cikin rashin sabo. Raihan ta kalle shi ta ce,"Daddy good morning?" Mamaki da sha'awar yarinyar ya kama shi. Hannunta ya kama yana shafa kanta."Morning How are you?" "Fine, ina Ummata?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa. "Ummarki ba ta da lafiya, yanzu zai kai ku gurinta." Ɓata fuska ta yi jin ba ta da lafiya."Allah ya ba ta lafiya." Ta ce tare da zama kan kujerar. Kallonta ya rinƙa yi cikin sha'awa, yana ji ina ma ace duka yaronsa ne. Ita ma kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kanta. Ba ta ce komai ba, har ya yi mata sallama ya fice. A gidan gaba ya sanya su duka, har da Little Marwana da ta na ce da ita za a je. A hanya sai da ya tsaya ya yi musu soyayya sosai, sannan suka tafi asibitin. Marwana bayan ta gama waya da shi likita ya kira ta. Binsa a baya ta yi cikin murna dama burinta ta ganta. Tana kwance kamar gawa. Idanunta kawai ke motsi. Tsananin mamaki ta ke yi yaushe har ta samu ciki ya girma ba tare da ta sani ba?Addu'a ta yi wa Allah da ya fita, domin ta san tsaf Faruk zai iya cewa ba cikinsa bane, ganin ko ita ba ta san da shi ba. "Marwana!" Ta furta cikin rawar murya sai kuma kuka. Ƙarasawa ta yi kan gadon ta zaunar da ita."Jiya kin tsorata ni! Na ɗauka mutuwa za ki yi." Ta ƙarashe maganar cikin hawaye tana rike da hannunta. "Ni na na ɗauka mutuwa zan yi Marwana, ina su Raihan?" "A gidan Yaya Damir suka kwana yana hanya zai kawo su." Kuka ta fashe da shi."Na gode da kika taimake ki. Haƙiƙa kin zamo mini 'yar'uwa. Bacin ke jiya da na mutu. Faruk zai kashe ni sam baya ƙaunata. A jiya aka ɗaura masa aure ba tare da ya gaya mini ba.Yana can da amaryarsa a hotel suna amarci, saboda mahaifiyarsa ta rantse sai ya yi mini kayan faɗar kishiya, kuma na yi taro. Na kira wayar da ya fi a ƙirga, amma bai ɗaya ba. Amarci ya fi masa lafiyata, ya san ko na mutu ba shi da asara." "Aure?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki. "Aure ya ƙara ya gaya mini ba ni da ƙima da matsayi a zuciyarsa. In na ga dama na zauna da shi, in kuma bana buƙata yanzu ya san ya yi aure." Jin abin da ta ce sai ta kama hannunta "Please ki haƙura da Faruk ki canza sabuwar rayuwa." " Ina son mijina ina fatan na rayuwa da yarana. In har na rabu da shi ba zai bar mini su ba. Kuma ba ni da fatan da zan riƙe su a gidanmu. Bayan haka ina son shi jiya tsananin kishinsa ya sanya na yi ɓari.". Jin abin da ta ce ya sa ta ji haushinta matukar gaske!"To zama za ki yi ya yi ta wulaƙanta ta ki? Nasreen ina son ki ƙwaci yancin kanki tun da ƙuruciyarki, kar sai kin tsufa ya tsotse kallon mangwaro ya huta da ƙuda." "Ba za ki gane halin da na ke ciki ba. Rayuwata tana cikin gaba kura, baya siyaki. Zaman gidanmu shi ma ba mafita bace, sannan ina tausayawa rayuwar su Raihan bana son su ta so a hannun matar uba. mahaifiyata ta sha wahala sosai a hannun matar babanta." Shiru kawai ta yi ta kasa cewa koma. Ta buɗe baki za ta yi magana, daidai lokacin da aka ƙwankwansa ƙofa. Sanin Damir ne ya sanya ta ce,"Yes come in." Bayan ta sanya mata hijabinta. Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo. Yana rungume da Musaddik da ya fara bacci a kafaɗarsa. Idanunsa a kan Marwana, domin haka nan ya ji sam ba ya son ya kalle ta. Haka zuciyarsa ta kitsa masa kuma ya bi, don samun maslaha. "Ya Damir, welcome." Ta ce tare da ƙarasawa ta kai hannu za ta karɓi Musaddik. Idanu ta zuba masa da nufin ta yi masa kallo ɗaya, amma sai ta kasa ɗauke idanunta. Wani irin abu mai ƙwarjini ta gani a cikin idanunnasa. Zuciyarta ya fara bugu fiye da wanda take yi. Rintse idanunta ta yi tana son kauda idanunta gare shi, amma ta kasa kallon sa take cikin tsananin sha'awar ina ma ace shi ne mijinta, mahaifin 'ya'yanta. Ganin yadda ya rungume shi cikin tsananin so da ƙauna. Namiji Kyakkyawan gaske ingarma da shi ga shi dogo sosai, mai faffaɗar ƙirji. Shigarsa da kamarsa suka sanya ya ke ɗauke da wata irin charisma dake sanya masa ƙima da daraja ga duk wanda ya kalle shi.Wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, tare da ta'awizi a zuciyarta, domin ta san sheɗan yake ƙoƙarin ƙitsa mata surarsa a zuciyarta. "Haƙiƙa matarka tafi ko wace mace sa'a, duniya samun miji kamarsa ba ƙaramin tagomashin bane. "Ta furta a cikin zuciyarta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta saki tare da rintse idanunta. Da sauri suka kalle ta har da shi da bai yi ninya ba. Gabansa ya yi matuƙar faɗi. Ganinta mace kyakkyawar gaske! Mai manya idanu masu tsananin ƙwarjini. Ƙara kallonta ya yi, duk da ba ta da lafiya, amma hakan bai hana bayyana kyawunta ba. Jikinsa ya yi sanyi, sanyin da ya hana shi jirgawa. Ganin hakan ya sanya Marwana ta ƙarasa gabansa ta karɓi Musaddik ta kwantar da shi. Yana tsaye a gurin kamar gunki yana kallonta da ta fuskar da kanta ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta. "Ya Damir, ga ƙawata wacce na ɗauke kamar 'yar'uwata Nasreen. Nasreen, ga Yana Damir, wanda ba ni da kamarsa. " Ta ce ganin ko wannensu ya kasa motsi. Ɗago idanunsa ya yi, ya ƙara kallonta daidai lokacin da, ita ma ta yi nasarar kallonsa. Zuciyarsu ta buga a tare. "Sannu ya jikin ki?" Ta ji muryarsa mai kama da sarewa yana faɗin haka. "Da sauƙi," Ta ce cikin sanyin murya, don bai ji abin da ta faɗa ba, don kawai yana kallon bakinta ne. "Ya jikinta mai likitan ya ce?" Ya yi wa Marwana tambayar haka yana mai da idanunsa gareta. "Jikin da sauki, amma kuma ya ce sai an ƙara mata jini." "Ok, ba matsala bane, amma kin kira mijinta?" "A'a, tun jiya dai." "Sai ki kira shi, ya san halin da matarsa take ciki, duk inda ya je ai dole ya dawo." Kallonsa ta yi sai hawaye shar. Marwana hannunsa ta kama suka fita."What? Kina nufin mijinta aure ya ƙara ya tafi ya barta a cikin wannan halin?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa. "Eh, yana hotel yana cin amarcinsa." "Kai wannan mutumin ba abinda imani. Matarka na cikin wani hali a kira ka, amma ka kasa amsawa saboda kana amarci? Akwai abin da ya fi iyalinsa mahimmanci?" "Yaya sai ka yi mamaki wallahi auren bai gaya mata ba." "Ikon Allah! Amma WASU MAZAN suna matuƙar ba ni mamaki." Shiru suka yi kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa. Can ya sauke numfashi ɗauko wayarta ki kira shi. Ba musu ta juya ta ɗauko wayar. Ta yi masa kiran duniya, amma bai ɗaya ba. A lokacin sun ta shi daga bacci kenan. Saboda gajiyar da suka yi, babu wanda ya iya motsawa har aka kira sallah aka idar. Sai gurin tara saura suka ta shi. Ganin bai yi sallah ba, hakan bai dame ta, domin ita ma ba ta damu da sallar ba. Bayan sun yi wanka sannan suka yi sallah. Matsawa kusa da shi ta yi tare da janyo shi ta haɗa bakinsu, tana masa wani irin salo. Janye jikinsa ya yi tare da ture ta."Please, baby ki bari na huta, kuma yunwa na ke ji." Jin abin da ya ce ta ɓata fuska ta matsa can ta zauna. Ganin ta ɓata rai ya janyota. Babu yadda zai yi, haka nan ya biye mata, amma shi kansa ya san yana buƙatar hutu. Kamar yadda lamarin ya faru cikin daren juya haka suka gudanar. Sam babu tsari na addini suka rinƙa ihu. Ita ta fara dama haka yake sosai ya biye mata. Ya sha fama da Nasreen kan hakan, amma ta ƙi tare da yi masa nasihar hakan ba koyarwa bace ta addinin Musulunci, sai dai Yahudu da suka kawo wannan salon, ɗin su ɓata tarbiyarmu da tsarin Islama. Da ƙara ya iya ɗaukar wayarsa ya sanya aka kawo musu abinci. A nan ya ga tarin kira sau babu adadi. Tsuka ya ja tare da jifa da wayar. "Shashashar banza! Ba ina gaya miki da ma akwai lokacin da za ki yi sani sani ba? Wato tun jiya idanunki sun raina fata? Ai dama za ki gani. Baƙincikin kishinta sanya kin kasa bacci sai kirana kike yi. Ai kin riga kin makaro, tun da na samu macen da za ta yi mini duk abin da na ke so. In har ba ki takatsantsan ba, walllahi saf zan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda." Shi kaɗai yake ta maganar. Rashida ta kalle shi."Babya magana kake?" Ta yi masa tambayar tana masa wani irin kallo tare da hura masa kiss. "Ni da wancan shashashar ce. Kira yafi sau ɗari." Dariya ta yi ba ce komai ba tana kallon sa. Ya buɗe baki zai yi magana sai kiranta ya shigo. Kin ɗagawa ya yi har aka kira sau bakwai. Ganin ta na ce sai ya kai hannu ya ce,"Bari na ɗaga na ji uban me za ta ce mini." Carab ta riƙe hannun sa."Ni baby, kishi ne kawai yake damunta. Ba ta son mu ci amarci. Ka shareta, don ni na fi son mu yi amarcinmu anan. Ka san matan Hausawa suna da kishin tsiya." "Ok, babyna yadda kika ce haka za a yi. Ai ni in har za ki iya sarrafa ni a gado kin riga kin samu kaina har da ƙafafuwana. Ita shashashar sai dai ta kwanta kamar gunki. Kai matan Hausawa sam ba su yi ba." Dariya ta yi jin abin da ya ce, tana masa salon da take son ya bambanta ta da matan Hausawa. "Ikon Allah! Har yanzu ba ya amsa Calls din." Marwana ta ce cikin takaici. "Ungo wayata kira shi da nawa." Ya ce mata yana miƙa mata wayar. Karɓa ta yi tare da cire password ɗin. Ta danna numbobinsa a wayar. Cikin mamaki ta ga ya ɗaga wayar da sallama. Kallon junansu suka yi cikin mamakin rashin ba ta daraja. Ta san zai iya tuna muryarta sai ta miƙa masa wayar. Ƙin karɓa ya yi."Ki yi magana kin san ba shi da mutunci, zai iya mini wata fassarar, kuma bai kamata na yi masa magana." Babu musu ta yi

Chapter 10 of 17