Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kike." "Let's go and do shower then eating." "No, shower then sleeping am very tire. Bacci ne kawai zai dawo dani daidai." Hannunsa ta kama duka haye sama yana rungume da ita. Ji yake kamar ya kasheta don so. Tun da yake bai taba son abu kamar ta ba sai ƙanwarsa Marwana. Hakika yana matuƙar don waɗannan halittu guda biyu kafin kuma ya haifa masa babu girl ya sanya mata, little Marwana da babu na biyu ta a duniyar sa. Bayan ya yi wankan, ba ta barshi ya kwanta ba sai da ta ba shi tea mai zafi yana kauda fuska tana rarrashinsa. Sannan ya subbaci Marwana da ta yi bacci ya ɗauke ta. "Bari na kaiwa Baba Azumi ita na dawo ki bani labarin baby na kuma tabbatar da lafiyarta, saboda shi zai watstsake mini gajiyata." Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba sai raka shi da idanu da ta yi cikin so da ƙauna. "Gaya mini duk abin da ya faru da bana nan?" "Babu sai kewarka da kwana rungume da filo tun da babu kai." "Karki damu jaririyata. Yau za ki yi filo dani har ki gaji." Ya ƙarshe maganar yana tusa kansa a cikin yar yaloluea rigarta. "Kin je check up?" Ya yi mata tambayar bayan ya ɗago kansa tare da mayar da hankalinsa gareta. "Na je Muhsin Hajiya ta Turo ta ya kaini. Likitan ya ƙara tabbatar mini aiki dole za a yi mini. Kamar na Marwana." "Kar ki damu,ni kaina na fi so ayi miki aikin. Kin ga ba ki da wata isashshiyar lafiya ga condition ɗin ki. I think aikin will be saved." "Ok," Ta ce tare da share hawayen da ya zubo mata. "Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi muna tare ba zan taba rabuwa dake ba. Kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare." WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 4 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Please kar mu yi haka dake. Na gaya miki duk wuya duk rintsi, muna tare ba zan taba rabuwa dake ba, kuma in sha Allahu za mu yi tsawon rayuwar da zamu tsufa tare." "Ina fatan haka ina fatan na kasance da kai har abada mijina. Ka ci gaba da bani kulawar da kake bani, wanda na san ko akwai matan da suke samun kamarka ƙalilan ne. Ina sonka mijina yadda kake nuna mini tsantsan so da ƙauna. Zan yi kishin ka duk ranar da ka nuna kana son wata 'ya mace." "Ke kadai kin ishe ni Batula, na gaya miki bani da ra'ayin ƙara mace. Kin ji kuma na rantse miki ba zan taba miki kishiya ba."Ya karashe maganar yana haɗe bakinsu. An sha soyayya tare da biyan bashin kwanakin da ba su a tare. Bayan sun yi wanka suka rungume junansu bacci mai dadi ya tafi dasu. Ba su tashi ba har ƙarfe huɗu saura. Shi ma bugun ƙofar Marwana ya tashe su. "Daddy and Mommy, wake up." Suka ji tana fadi tare da buga ƙofar tana rungume da teddynta da sauri tana kiran su. "Innalillahi! See time ban gaya wa Baba Azumi ba abin da za ta girka ba." Ta faɗa tana dan dukan filon da yake ya tashi. Juyi ya yi tare da kai hannunsa zai rungume ta." Ban gaji da baccin ba, kar ki damu da abinci. Please mu kwanta." "Subuhanallahi! Ashe har an yi la'asar." Zubbur ya mike yana zare ido tare da ɗaukan agogo ya duba." Kai ina da an kira dole na tashi." Dariya ta saki tare da sauka daga gadon." Ga shi nan na tashe ka." Shi ma dariya ya yi yana shafa sunan kansa."Kin san lafiya ai." Buɗe dakin ta yi Marwana ta nufa da sauri ta faɗa jikinsa. "Baby, bari na sanar da Baba, Azumi abin da za ta girka." "Kar ki damu ki gaya mata ta huta mu je na hada mana lunch." "Don Allah ka gaji ka bari sai gobe." Karki damu just give me two minutes lemme go to resting room. Ba tare da ya ji mai za ta ce ba ya shige bayin, ita kuma ta fita daga dakin bayan ta kama hannun Marwana. "Baba, Azumi kin ga na sha bacci ko?" "Eh, ai na so na taso ki, sai kuma na ga tun da mai gida yana nan bari na kyale ku. Na yi mana girki ni da masu aiki. Kuma Marwana ma ta ci, amma saboda ban san me kuke so ba sai barshi, don na san wataƙila mai gida zai yi da kansa." Murmushi ta yi tana kallonta."Aiko Gara da ba ki yi ba don ya ce ki huta." "Sanin hali, ai yafi sanin kama. Allah dai ya barku tare." Ta ce tare da komawa ta zauna, amma ganin ya shigo kicin din sai ta miƙe. "Baby ina afron?" Ya yi mata tambayar yana amsa gaisuwar da azumi ke masa. Dauko masa ta yi tare da ɗaukar masa sannan ta tsaya tana kallonsa. Tana mishi hira tare da taimaka masa suka haɗa lafiyyayen abinci sannan suka dawo dining. Shi ya rinƙa ba ta abincin, har ta ci ta ƙoshi sannan ya ci. Bayan ya ci suka koma falo suka zauna. "Kin san rigimammiyar nan wai ni zan dauko ta a school, tun da na kira Hajiya, na gaya mata na dawo ta sanya rigima sai na zo, dama motarta ta samu matsala ba ta je da ita ba." Dariya ta yi."Rigimarta ne kawai ya tashi, amma ko jiya a motarta muka je gidan Anty Ƴahanasu. Watakila canza mata take son ayi." "Zan je na duba motar in tana bukatar canxawar ai sai ayi." 'Gaskiya ya kamata." Ta ce. "Bari na shirya Little Marwana sai mu je tare." "Ok, ka dawo lafiya." Ta furta tare da jan remote don ta canza tasha. Shiga ya yi ta alfarma cikin suit masu kyau baƙaƙe. Wayarsa da key ɗin motarsa ya ɗauka. Ganin kyau da ya yi Batula ta sauya wayarta za ta yi mishi hoto. "Kai ka yi kyau matuƙa gaskiya Allah na gode maka da ka bani wannan gayen." Ta ce tare da jan kumatunsa. Dariya ya yi ya ce," Ke ma kina da kyau ai." Ya ƙarshe maganar yana sumbatar ƙuncinta . Har bakin mota ta raka su. "Bye Mommy I will buy you chocolate." "Ok baby, promise?" Ta ce mata tana daga mata hannu. Juyawa ta yi cikin farinciki ta koma ciki. Nasreen kuwa, a lokacin da mai mashin ya sauke ta da sauri ta saɓa Musaddik ta fara tafiya. Tana tafiya ta tana kallon agogo ganin lokaci ya wuce har da minti goma. Ta san Malamin yana da tsananin zafi Allah ya sa ya barta. Cikin sa'a ta shige ciki lokacin hankalinsa na kan ɗalibai da yake raba musu gurin zama. Da sauri ta ji an kama hannunta ana faɗin," Ummu Hairan, zo mu zauna a nan." Ta ce mata tare da jan hannunta suka zauna. Lecturer na kallonta ba tare da ya ce komai ba. "Kin yi matuƙar latti, har na fara tunanin ko ba za ki zo ba? Ina ta waige-waige na kuma tambayi wannan matar auren da kuke zuwa tare, sai ta ce mini wai ta kira numbarki ba ya shiga. Wannan dalilin ya sa ya na ban karɓi numbarki ba." Yaƙe ta yi mata jin abin da ta ce, tana mamakin maganar da ta yi mata, domin za ta iya irga maganar da suka yi. Shi ma gaisuwa ne in sun haɗu a masallaci sai kuma in tana son assignment ta tambaye ta. "Kin san am manna mana result?" Ta yi mata tamabayar cikin murna. "A'a." Ta ce mata tana kallonta tare da kallon kayan alfarmar dake jikinta. "Wallahi an manna. Ai tun jiya muke sa rai. Yau kuwa tun asuba na sanya Ya Muhsin ya kawo ni, na duba daga ke sai ni." "Alhamdulillah!" Ta ce mata. "Gaskiya kina da ilmi sosai kamata ya yi da result da kike beating gwamnati ta ɗauki nauyin karatunki, but you know how situation we are in Nigeria." "Haka ne Allah ya rufa mana asiri." Ta ce tare da kama bakinta, ganin yadda yan ajin suke kallonta don Marwana ba ta cika kula kowa ba harkar gabanta take yi. "Mu fara test ɗin." Ta ce bayan an rubuta a allo. Ajin ya yi shiru, kowa na ƙoƙarin nuna ilmin da yake da shi, yi sai kuma masu ƙuskus 'yan satan amsa. Marwana tana rubutu tana satan kallonta, dama so take ta ga satan amsa take yi, ko ƙoƙarin ta yake ba ta result ɗin, saboda so take ta ga babu wanda yake gabanta a result ta yadda Ƴaƴanta zai kaita abroad ta yi masters. Ta cika mamakin ganin yadda ta cika paper. Ta yaba da ƙoƙarin ta domin tun da ta fuskar da kanta ba ta ɗago ba. Ganin gulma zai sanya ta ɓata lokacin ta ya sa ta fara rubutawa. Bayan sun gama sun fito." Zo mu je mu ci abu yunwa na ke ji." "No karki damu bana jin yunwa." "To don Allah ki raka ni." Ta ce tare da karbar Musaddik da ta ije shi a gurin wata yar ajinsu kafin ita su shiga. Murmushi yaƙe ta sake yi ganin yadda idanun ke kallonta. Lura da hakan Marwana ta yi, sai ta kamo hannunta, suka fara tafiya har suka isa cafateria. Abincin da ta yi oder ya yi matuƙar razana ta. "No sis ba zan ci ba, na ci abinci daga gida." Bata rai ta yi tana kallonta." Sheɗan ne kawai yake maida hannun kyauta baya."Ta ce tare da yin raurau alamun za ta yi kuka. Dariya ta ɓata tana mamaki shagwaɓa irin na 'ya'yan masu da shi. "Na ƙoshi ne fa so kike na yi amai?" "Ok, ba damuwa bari na sa ayi miki a sanya mini a leda. Sai ki bawa kyakkyawan yaron ki ya ci. " Murmushi ta yi ba ta ce komai ba. Mamakinta ta yi ganin yadda take ci tana bawa Musaddik a baki ba tare da ƙyamar sa ba. "Kin ga kishin ki na ke yi fa." Jin abin da ta ce ya sa ta ɗago tana kallonta da sauri. "Kishi kuma ni? Mai na ke da shi har da kyakkyawar mace kamar ki, wacce take da kyau kamar an kyankyaso ki aka yi za ta yi kishi da ni?" "Ilmin ki mana. Wallahi tun muna hundred level na ke jin haushi ke ce kike zuwa a gabana, domin da ni ce top a ajinmu yanzu ina abroad, kuma kin ga irin wannan kishin ai ya halasta ko addini sai na dage na wuce ki." "To shi ne na ba ki da matsala. Wannan semester zan yi yadda za ki wuce ni sai ki cika burinki." "Wow, sis you are so kind." Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Wayarta ya yi ƙara sai kuma ta mike."Yauwa Yaya Damir ya iso. Zo mu je ku gaisa." "No, kar ki damu kawo shi kawai." Ta ce mata bayan ta miƙe. Ita sam ba ta son shiga harkar masu da shi. Gara ta tsaya a matsayinta. Za ta riƙe ta sai ta ga ta canza fuska. "Bari na je kawai tun da ba kya son zuwa, amma zan je da Musaddik." "Ok, ki gaishe shi." Ta furta tare da wucewa. "Oyoyo Yayana." Ta ce tare da rungume shi. "Marwana, yaushe kika fara ɗaukar yara?" Ya yi mata tambayar yana kallon babyn. Dariya ta yi ita ma shi take kallo." Ka ganshi kyakkyawa ko?" Ta furta tare da miƙa masa shi. Hannu ya sa ya amsa yana fadin,"Eh, Allah ya sanya Mommy Little Marwana ta haifa mini kalarsa." Hannunsa ta kama suka shiga cikin makarantar tana faɗin,"Mu je ka ga result ɗin mu." Babu musu suka shiga ya tsaya yana dubawa."Gaskiya ƙanwata kanki na ja, amma wace ce wacce ta sha miki gaba?. Ni kuwa zan so na ganta." "Maman yaron nan ne, kuma abin mamaki daga shigarta ba matar mai kuɗi bane" Ta nuna Musaddik dake hannunsa, bari na kira ta.". "Ai shi Allah ba ruwan shi da duba wannan ya ba ka ilmi. Ki dage ki wuce ta kin ji." "To bari na kira ta." "No matar aure ce ba zai kin kira ba, amma kuwa zan yi mata kyauta ta musamman, domin kamata ya yi gwamnati ta ɗauki nauyinta." "Gaskiya Yaya." "Gobe sai ki shirya mune ki zaɓi duk motar da kike so, in kuma na Muhsin da kika na ce sai ya bar miki dama motar mata ya je ya siya." "No bana sonta, ba ka ga ya je ya ƙuje ta ba?" "Ok, tom sai ki shirya goben." " Na gode Allah ya ƙara budi." Tace masa cikin tsananin murna. "Ina little Marwana?" "Tun da muka shiga gidan Hajiya, ta ga za ta fita sai ta manne mata, kin santa da son yawo da Hajiya." "Hajiya da ita ai sai Allah." "Yanzu kin gama ne?" "Eh bari na kai mata yaron." "Ok," Ya ce tare da sanya hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi 'yan dubu-dubu har 20k. "Ga shi a siya masa chocolate." "Thanks Yaya." Da sauri ta shiga cikin abin tana nemansa. Ganin ta can a gefe ta ciro jigattaciyar wayarta taba ƙoƙarin kiran Ya Ahmad. Ba tare da ta ji zuwa ta ba sai dai kawai ta ji maganarta. "Ga shi zan wuce gida." Da sauri ta shiga tare da ɓoye wayar a jaka. "Sannu ya wahalar da ke ko?" Ta yi tambayar tana ƙoƙarin ɗaukar shi. "Kai haba wane wahala." Ta ce mata tare da miƙa mata kuɗin. "Ya Damir ya ba wa Musaddik." Zare idanunta ta yi tana kallon kuɗin tare da haɗiye miyau da ƙyar. "Kai haba duka wannan uban kuɗin ai sun yi yawa." "Kar ki damu Yaya zai iya ba shi fiye da haka." "Gaskiya ba zan karɓa ba." "Saboda me?" "Saboda sun yi yawa, kuma daga haɗuwa da ke yau, sai ki yi mini kyautar wannan kuɗin." "Musaddik ya yi ma kyautar, don haka ya zama dole ki karba, kuma kin san wane ne Ya Damir da kuɗin da yake da shi? Ban ba ki san shi bane." Ta ƙarashe maganar, tare da cusa mata kuɗin a jaka, sannan ta juya ta fara tafiya tana faɗin. "Sai gobe zan wuce." A ranta ji ta yi kamar za ta sume ganin kuɗin, domin rabin ta da ta samu irin wannan kuɗin har ta manta." Miƙewa ta yi ta goya Musaddik sannan ta ɗauki jakarta ta tafi. A hanya ta ciro wayarta ta kira numbar Faruk da yake zaune a ofis ɗinsa yana waya. Yana ganin kiran na shigowa, amma bai damu ba ya ci gaba da wayarsa, har lokacin da ya gama, sannan ya kashe tare da sakin wawan tsaki. "Ko uban me za ta ce mini oho? Ana magana da mata ba ke kamar sandar rake ba ki addabe da..." Maganar ta katse sakamakon kiran da ya ƙara shigowa. "Wai mene kin addabe ni, ko ke makauniya ce? Tun da kin ga ina waya ba sai ki yi haƙuri ba." "Ka yi haƙuri kiran ne da mahimmanci zan gaya maka ina son na je na duba Mama jikinta ya tsananta." "Wannan ne kira mai mahimmanci?" Ya yi mata tambayar cikin tsawa wanda ya sanya ta yi sororo sai kuma ta ce," Mahaifiyata ce fa ba lafiya?" "To ni ina ruwana in kin so kar ki dawo ba ta shafe ni ba. Kin ga sai na huta da ci da ke." Yana faɗin haka ya kashe wayar tare da ƙara jan tsuka mai ƙarfi ya kashe wayar. Ranta ne ya ƙara ɓaci, ta kalli wayar hawaye na son zubowa a fuskarta, amma sai ta daure ganin yau rana ce ta musamman, domin ko babu komai za ta taimaka a ciwon Mama. Tsayawa ta yi, ta sayi lemo da ayaba na dubu ɗaya, sannan ta siya mata gashashshen nama da dubu. A ƙofar gida ta kusa cin karo da Zainab. "Ina za ki je kike sauri haka har za ki buge ni?" Ta ce mata daidai lokacin da suka ci karo. "Oyoyo Anti Nasreen." Ta furta tare da rungume ta tana shafa kan Musaddik. "Zan siyo ruwan gishiri Mama ce za ta sha. Ta ce jikinta babu ƙarfi." "Sai kin dawo to." "Anty kawo shi." Ta ce tana miƙa hannu ta Kwanto mata shi. "A'a, ki yi sauri ki dawo." "To," Ta ce tare da shafa kanshi ta ruga da sauri. Da sallama ta shiga cikin tsakar gidan, da Mama Dije take zaune tana ƙoƙarin hura wuta. "Yau 'yan boko ne a gidan? Ko da yake dole ki zo tun da tsohuwa babu lafiya." Ta faɗa tana yatsina bakinta. "Ina wuni?" Kawai ta ce mata ba tare da ta ji abin da za ta faɗa ba ta shige. Rakata ta yi da kallo ba ta amsa gaisuwar ba. Ɗakin ta buɗe ta shiga, tare da saurin ƙarasawa, kan lamushashiyar katifar da Mama take kwance. "Sannu Mama, ya jikin ki?" Ta yi mata tambayar tana daga goshinta da ya ɗauki zafi kamar tukubar mai tsire. "Yauwa ya gidan?" WASU MAZAN" Labari ne a kan rayuwar Nasreen wacce ta haɗu da jarrabawar rayuwa. Nasreen tasha jarrabawa a rayuwar aurenta da Faruk. Wanda faruwar haka yana da nasaba da rashin bango mai kyau abin jingina da ba ta samu ba, wato mahaifinta da ya kasa cike gurbin da ya kamata ya cike. Rayuwar aurenta madubi ne ga wasu matan da suke shan wahala ko rashin sama lafiya da mazajensu. Duk da ƙoƙarin su na son su zauna a ɗakinsu don gudun ZAWARCI da kuma fargabar rayuwar 'ya'yansu yadda za su kasance in ba su, da kuma fargabar mijin da za su aura bayan aurensu ya mutu. Wannan dalilin ya sanya ta jure zaman gidan aurenta don ta samu ta rayu da 'ya'yanta. Sai dai ƙaddara ba ta wuce mutum dole afkuwarsa tabbataciyace tun da Ubangiji ya tsara tun a Lauful Mahfuz. Duk yadda ta so ta kaucewa ƙaddara faruwar hakan ya ci tura. Ta shiga cikin tsananin rayuwa da fidda tsammani. Ta haɗu da wacce ta kira hasken da ya haska fitilar rayuwarta, amma sai dai a garin ta kawo hasken, ta sanya rayuwarta cikin tsarƙaƙiyar da ya zama tsarƙen da ya jefa rayuwar ta cikin tsarƙaƙiyar soyayyar mai kama da ƙiyayya. Sai dai Ubangiji ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki cewar,"Duk tsakani, akwai sauƙin." Haka ta kasance a lokacin da ta fidda tsammani a cikin rayuwarta, sai Allah ya kawo haske mai walƙiya da ya canza tubalin ƙaddararta da ga duhu zuwa haske. Ta kuma sha ruwan zuman da take tunanin ba za ta taɓa shan sa ba, bayan ta kwankwaɗi na maɗaci, wanda ya gauraye dukkan rayuwarta har ta fidda tsammanin shan zuma. A cikin littafin akwai wata irin soyayya mai tsuma zuciya. Masoyana karku sake a baku labarin littafin "WASU MAZAN" Domin na wasa ƙwaƙwalwa ta na zauna na tsara shi ta yadda zai sa ya ku tausayi da nishadi har ma ya zama darasi. Ku kasance masu bibiyar littafin domin jin yadda tubalin ginin rayuwarta zai kasance. Kun san dai alkalamin Jamila lawal Zango ba ya rubuta shirme. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *WASU MAZAN* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... And now Wasu mazan 08144072423 PAGE 5 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Sannu Mama, ya jikin ki?" Ta yi mata tambayar tana daga goshinta da ya ɗauki zafi kamar tukubar mai tsire. "Yauwa ya gidan?" Ta amsa cikin rawar murya. "Allah ya ƙara sauki." "Yaya Ahmad mai ke damunta?" Bayan ta yi mata fatan samun sauƙi, ta juya tana kallonsa tare da tambayarsa hakan. "Ciwon nan dai nata. Yanzu likitanma ya ce gaba take da zuciyarta ta buga, matuƙar ba za ta cire damuwarta ba." Ya ba ta amsa yana share hawaye. "Haba Mama! Sanya damuwa a cikin ranki ba shi zai kawo karshen matsalar nan ba. Mama, iya tsawon shekarun da kika yi da Baba ya kamata ki yi hakuri ki rungumi ƙaddararki." "Ya zan yi Nasreen? A halin da na ke ciki na fi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata, domin ban zaɓawa rayuwata da na yarana bango mai kyau ba. Ina dana sanin auren mahaifinku, kamar yadda na tabbata ke ma dana sanin da za ki yi kenan. Na cuci rayuwata wanda a dalilin haka na sanya ki da yaranki cikin halin ƙaƙa na iya." "Mama, babu wanda ya isa ya tsayawa kansa rayuwa. Kowa da kika ganshi rayuwa yake yi ba tare da ya tsara wa kansa ba. Allah ya ƙaddara shi ne mijinki, kamar yadda babu makawa sai na auri Faruk. Ki kauda damuwa mu rungumi ƙaddara da Allah ya ɗora mana." Kuka ta fashe da shi ganin Nasreen na hawaye. "Ina tausaya wa makomar rayuwar ki da 'ya'yanki kamar yadda na ke tausaya wa kaina." "Mu roki Allah kuma mu mai da lamuranmu ga Ubangiji." Ta ce tare da buɗe jakarta ta cire lemu da ayaba da kuma ƙunshi nama. "Ina kika samu kuɗi? Ke da ake taimaka miki?" Murmushi ta yi jin abin da ta ce, tana kallon Ahmad da ya kashe ta da ido. "Ai yau na haɗu da gamdatakar!" Ta ce tare da fito da dubu goma sha takwas ta ɗora a gado. Zare idanunsu suka yi. Mama cikin ƙarfin zuciya ta miƙa wanda ganin haka ya sanya ta jingina mata filo a bayanta. Take ta kwashe kaf abin da ya faru ta gaya musu. "Kin san bana son leƙen rayuwar wasu? Ki tsaya a matsugunin da Allah ya ije ki, domin yawancin masu kuɗi wulakantattu ne." "Wallahi Mama sai da na ce mata ba zan amsa ba. Kin ga ko abincin da ta siya mana ƙin ci na yi, amma ta kafe na kaiwa yarana gida." Ta ƙarashe maganar tana miƙa mata take away ɗin abincin "Ga shi ƙila ki samu kici." Ta ce bayan ta ije mata. "An ya wani abu zai iya shiga cikin nan?" "Ki daure rayuwa dole sai da abinci." Gyara. Nasreen ta ɗauki cokali sannan ta iba tare da kai mata bakinta. Buɗe bakinta ta yi a hankali ta karɓa."Yauwa Mama, ko ke fa. Allah ya ba ki lafiya." "Amin," Nasreen ta amsa tare da miƙewa bayan ta karɓi ruwan gishiri ta ta

Chapter 3 of 17